Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
Ibrahim bai ji ba.
Sai ji ya yi Baban yana makala masa, bayan ya makala nasa. A lokacin ne Ibrahim ya gane ‘he
is lost...... (ya yi nisa a tunani).
Ya kalli uban, shima ya kalle shi, sai suka yi ‘yar dariya a tare.
Bayan sun sauka motar hotel din da Daddy ya yi booking tun kafin su taho (Mandarin
Orchard Singapore) already tana jiransu, ta kwashesu da ‘yan jakunkunansu marasa nauyi
zuwa otel din.
Tun a hanya Daddy ke kiran wayar Rayhanah ana gaya masa a kashe take. A lokacin ita
Rayhanah tana aji suna wata jarrabawar gwaji (test) domin gab suke da fara jarrabawar
karshen shekara. Kuma dama karatun na shekaru biyu ne kacal, da yake tana da diploma tare
dasu. Karfe shidda na yamma ta baro cikin institute din nasu ta kamo hanyar gida, ta tsaya ta
sayawa Inna roasted KFC, ita kuma ta sayawa kanta ‘wantanmee’ ko ‘wonton’ (yadda suka fi
kiransa), ‘chili crab’ da ‘fried hokkien mee,’ duka suna daga cikin (40 Singapore foods
Singaporeans cannot live without) abincin mutanen kasar Singapore guda arba’in da baza su
iya rayuwa basu ba, saboda ta ce da Innar yau kada ta yi musu girki za ta yo take away don ta
wayi gari ba ta jin dadi, sauri ma take ta isa gida don ta kaita clinic a duba ta.
Haka nan ta tsinci kanta da faduwar gaba a lokacin da ta doso gida. Sai da ta tsaya a kan
wani dan tudu ta zauna ta zube ledodin hannunta a kasa tana dan hutawa tana hango kofar
gidan nasu da bakuwar motar otel din (Mandarin Orchard) fara sol. Ta san hotel din da Daddy
ke sauka kenan, don haka jikinta ya ba ta Daddy ne ya zo. To amma wannan faduwar gaban da ta samu kanta a ciki ta mece ce? Ta so ta kunna
wayarta, sai ta tuna a gidan ta barota.
Sai kawai ta mike da dan kuzari tana cewa a ranta bari in karasa gidan, daman dai kuma ta
kwan biyu basu yi waya da Daddyn ba, har Inna kan tambayeta kwana biyu Baba Likita bai kira
ba, lafiya?
Ta kan ce lafiya sumul insha Allahu, kin manta Baban nawa busy doctor ne?’
Inna ta ce, “Allah yasa buzu ne ba busy ba, ki kira min shi kawai”.
Ta yi dariya ta ce,
“To ai ni yanzu bani da lokacin kunna waya idan ban gama tsarge tests din nan da suka sako
ni a gaba ba, na yi na yi ki koyi operating din waya da kanki kin ki saidai ki dameni in kira miki
wannan in kira miki wancan, yanzu sai ki yi zuciya ki koya”.
Duka Inna ta kai mata ta fice da gudu tana dariyarta. A haka suka rabu yau.
Ta mike ta ci gaba da tafiya a gefen titi a hankali don yunwa take ji sosai, ledodi da hand bag
dinta kamar ta watsar dasu don nauyin da su kai mata, musamman kwalin kazar Inna kaji biyu
ne a ciki. A haka ta daure ta ci gaba da tafiya at the same time, faduwar gabanta na kara
tsananta.
Ba wata kwalliya ba ce a jikinta, amma da ka ganta kai tsaye za ka kirata black-American.
Shigar jikinta usul shiga ce ta matan Singapore (Belted-Waist-Shirt) dark blue mai dogon hannu.
As a Muslim, sai ta sanya bakin dogon wando a ciki, ta kuma sanya karamin hijab na Larabawa
a kanta wanda ya tsaya iya kafadunta. Also kayan jikin nata are not expensive.....kuma basu nuna komai na jikinta ba, daka ganta
kasan Musulma ce cikakkiya. Singapore is very modern but dressing very sexily will not be
acceptable in certain places.... don haka matan kasar musamman musulmin can basu fiya yin
shiga ta tsiraici ba balle ita Rayhanah. Kafafunta rufe cikin bakin cover kuma flat takalmi Melissa (brand din ZALORA). Rahane ba
zuwa take ta sayo kayan nan ba, Dr. Mansur ke zuwa ya sayo da kansa a shaguna duk zuwan
da ya yi ya zo ya zube mata su, illa dai yana karbar size dinta har ya rike. Zamanta cikin dalibai
‘yan’uwanta musamman haifaffun Singapore shi yasa yau da gobe ta iya shigarsu. Fuskarta ko powder (hoda) babu, haka lebbanta babu danshin mai, but they are soft and
supple kamar tana basu wani extra care ne, amma babu ko daya. Babu gumi a fuskarta,
fuskarta tas fresh and choculate. Ba ta da dogon hanci, gashin nan dai dan madaidaici a
tsakanin idanunta. Gashin kanta a tsefe yake, baki mai karfi amma ta matse karshensa da
ribbon, hakan bai hana ya yi dan tudu ba, da yake ba ta taba sanya masa relaxer ba, haka yake
da karfi kamar reza na asalin Hausawan Kano jikokin barbushe da tsimbirbira.
Da wannan shiga, da wannan fuska, da wannan yanayi Rayhanah ta danna kararrawar shiga
falonta.
*****
Wanda ya bude kofar wani matashi ne baki mai tsayi sambal, mai wasu irin idanu masu
lumshewa da kansu, da budewa cikin nutsuwa cikin umartar kansu da yin hakan, cikin kwayar
idonshi akwai wani abu mai sheki kuma ba farare ne tas ba, ga dogon hanci kamar Dacta
Mansur, fatarshi ta nuna haifaffen Nigeria ne, gashi nan kamar Dr. Mansur (choculate in
complexion), duk da Dr. Mansur ya fishi haske.
Ya tara suma mai dan tudu a kanshi, ba kuma nannadaddiya ba ce ta ‘yan asalin
Northwest-Nigeria ce wato mai karfi, amma ta sha taza ta sha mai mai tausasa gashi
(ArganaVita) da ba a samun shi sai a kasashen ketare.
Sanye yake da farar shadda kal hilton dinkin Mohammed, rigar ta kusa kasa sai wandon a
ciki, kanshi babu hula, daure a damtsen hannunsa agogon ‘Calibre de Cartier’ ne da ya kwanta
cikin tattausar fatar hannunsa wadda lallausar bakin gashi ya kwanta a ciki.
Babban abin jan hankali a halittarsa, wannan tsagar bakin nasa ne da bakaken lebbansa
marasa kauri, sai kuma lallausar sajen da ya kwanta a gefen kunnuwansa bai iso habarsa ba,
wadda dan lotsawar nan na tsakiyar haba (cleft) ya bayyana a fili ko da bai motsa bakin don cin
abinci, dariya ko yin magana ba. Kallon-kallo ake tsakanin Rayhanah Rashid Takai da matashin da ya amsa sunan Ibraheem
Mansur. Kallon da bai da ma’ana at all. Kallon da kai tsaye za ka fassara shi da kallon zakuwa a
tantance juna kawai, ba na so ba, na kauna, ko akasin haka ba, kawai ‘eager to see each other,’
kuma ba tare da sun bar kallon ya tsawaita ba tunda ko da kalma ba ta shiga tsakani ba kowa
ya gane kowa, kuma kowa ya yi ‘quenching’eager dinsa.
Don haka Rayha ta yi saurin sadda kai wani abu yammmm! Na bin ilahirin jikinta, wanda ya fi
karfin tashin tsigar jiki sai circulating din jini abnormally da yadda ya saba aiki, domin bukatarsa
nason ya isar da sako ta kowanne hali (by all means) daga zuciya zuwa cikin gangar jiki da
kwakwalwa. Duk wadannan mintunan da suka kwashe a tsaye, Dr. Mansur da Inna na kallon su, addu’a
kowannensu ke yi cikin zuciyarsa Allah ya daidaita. Cikin Dr. Mansur ya fi na Inna Juma durar
ruwa, idan Ibraheem ya ce Rayhanah ba ta yi masa ba ina zai sa kansa? Amma ga HIMUN,
abin ba haka yake ba.
Kallon da ya yi mata na farko, eager look ne na neman tantancewa da kauda curiosity. Amma
as his eyes enter her’s much more deeply..., (da kwayar idanunshi ta shiga cikin tata sosai),
kokari kwakwalwarsa ta shiga yi wajen farfado masa da shekaru goma sha daya a baya.
Tabbas ya san fuskar, yasan wadannan idanun masu rauni da sanya kasala, ya san ‘yar
yarinyar nan ce RAHANE, data shigo cikin rayuwarsu daga asibitin Malsm Aminu Kano, mai
kula da ubanta a bargar dawakin Hakimi, mai yiwa ubanta wanki, yanke farce da taya shi
feeding horses (baiwa dawakin Hakimi Abdulqadir abinci). ‘Yar yarinyar nan ce da Daddy ya dauko daga Takai..... wadda ta rasa jinta dungurungum,
‘yar yarinyar nan ce mai amfani da HEARING AID....... wadda ta sa shi barin gida ba don ya so
ba, sai don ya ceci kansa ya ceci zuciyarsa daga fadawa soyayyah a inda bai dace ba, a kuma
lokacin da bai kamata ba.
Yana ‘referring’ kowanne ‘motion’ na zuciyarsa a kanta da KARYA........ bayan kuma sau tari
tsoron kar zuciyarsa ta ce ya yi karyar yake kidima shi ya yi mata KARYAR......
Ya bar gida saboda kar zuciyarshi ta wulakantashi da kauna da soyayyar kwaila ‘yar kauye
mai lalurar JI, hade da wasu ‘extraordinary charismatic features’ (baiwarwaki da karama) da ake
kira ‘Rahane.’ A girl with a great mind!
To yaushe ta koma RAYHANAH? (Daddy ne ya canza mata suna), zuciyarsa ta yi saurin tuno
masa........
“Mene ne sunanki......?”
“Rahane”.
“Rayhanatu kenan ko?”
“A’a, Rahane.......”
“To ni ba zan iya kiranki Rahanen ba, don baida ma’ana at all sam-sam....... Rayhanah....!!!”
Ya tuno tattaunawar farko da mahaifinsa ya yi da ita a ranar da ta fara samun kanta daga
hatsarin da suka yi, a kuma ranar da Baban da abokinsa Dr. Imam suka makala mata ‘hearing
aid’. As soon as da suka fahimci she's hearing impaired!
Kafin Rayhanah ta ankara Ibraheem ya kai hannu gareta ya cire hijabinta yana duba
kunnenta da bayan kunnen, babu komai sai dan karamin dan kunne mai barima na farin dutse.
Ta saki ledodi da jakar hannunta kasa saboda razana.
“Where's your hearing aid?”.
Abin da ya tambayeta kenan da wata murya mai sanyi, harshensa da accent dinsa
(American), wato na Amurka ba na Birtaniya da ya fi saukin furtawa ba.
Hannuwanta biyu ta kai kan nata tana son rufe gashinta da ya tsiraita. Sai ya russuna yana
kwashe mata ledodin ta da jakarta da ta zubar ya bata hanya tareda yi mata alamar ta wuce, sai
ta rabe ta gefensa ta shige ciki.
Babu kowa a falon, Inna da Baba Dacta sun shige kicin tun sanda Ibraheem ya cizge hijabin
Rahane.
Ai ganin ba kowa a falon sai ta kara da gudu ta yi dakin barcinta ta rufo kofar ta jingina da ita
tana numfarfashi kamar wadda ta yi gudun mita duba. Idanunta ta lumshe tana ambaton
“Yaa Wahhabu......... Yaa jamilal munzarrr (Ya mafi kyawun masu gani)!”
Ya Himu ne, tabbas shine....Daddy ya kinkimo ya kawo mata tana zaman-zamanta lafiya, ita
ina ruwanta da wani Ibraheem. Tun can bai son ta, kyankyaminta yake, kalma wannan ba ta
taba shiga tsakaninsu ba tun saninta da shi a gidan Dacta Mansur, kawo barinsa gidan don ba
ta ishe shi ko da kallo ba. Ita fa wannan auren kawai ta dauke shi suna ne, biyan bukatar ran Daddy bata taba tunanin
zai zama reality ba.
Ta yi zaton haka za ta kare rayuwarta cikin kwanciyar hankali da neman ilmi da taimakon
Babanta Mansur da Innarta Juma. Ba ta taba kawowa ranta Ibraheem din zai shigo cikin
rayuwarta ba.......
Ta shiga uku....... wannan gundamemen Ba-amurken ne mijin nata da har Inna da Baba
Dacta za su fita su barta da shi a gida akan saninsu? To tace masa me? Ko tayi masa me? Tayi
yaya da shi?
Watakila ma dubawa ya yi in da hearing aid ya ce baya son ta. Duk Khalipha shi ya janyo
mata....... da sunyi aurensu na so da kauna da ganin mutunci da kimar juna ai da Daddy bai yi
mata AUREN HUCE HAUSHI da Ibrahim ba.
Sai ji ta yi hawaye na bin fuskarta. Bokon nashi har ya zarta misali, tsoro yake bata, kwarjinin
shi razanata yake, ba ta san inda Daddy ke nufi ta kai shi a matsayin life-partner ba. Wannan
gandamemen baqin bature haka wanda zai iya hadiyeta baki dayanta?
Ya yi biyun Yaya Khalipha a girma da tsayi, ba wai kiba ce da shi ba (physique).
Kuma ita bata taba yiwa kanta sha’awar rayuwa da wani Da namiji ba bayan Khalipha, shine
dai-dai ita, domin ta kowanne bangare bai tsaurara ba...... ga boko ga addini, ga simplicity bai
dauki kansa a bakin komai ba.
Rana daya wannan iftila’i ya ratsa, ta karbi zabin Daddy don biyayya da yakinin da take da
shi na cewa a haka za su kare rayuwar tasu ita da Innarta da Daddy Ibrahim ba zai zo ba. Yau
gata ga IBRAHIM MANSUR TAKAI.
Kokarin bude kofar ake, kofar da take jingine a jikinta. Ai da ta yi wata zabura guda daya sai
ganinta ta yi a toilet dinta na bedroom ta kulle kanta.
Inna ta shigo tana cewa,
“Yau na ga abin da ya isheni ni Juma, mijin kike gudu haka? Lallai kin hada kanki da aiki.
Fito ki ci abincin da kika siyo shi Ibraheemu ma ya dade da fita a gidan nan.......”
Ai kuwa ta bude kofar ta fito idanunta sun ci kuka sunyi jawur. Haka Inna ta yi ta lallamin ta
don ta ci abincin, amma ta kasa cin abin kirki duk soyayyarta da ‘wontonmee’ da ‘chili crab’. Ga
Inna ba ta iya cin wannan cakudedeniyar ba, barta dai a KFC (Kentucky Fried Chicken).
Sai ta tattara ta zuba mata a firij tana ta mita.......
[12/27/2019, 11:51] Takori: “Kuma shi kenan don Allah ya amsa addu’armu Ibraheem ya zo,
sai ki kuntatawa kanki?
Tun safe baki yi karin kumallon kirki ba kika fita, na kuma tabbata a can baki ci ba, kin sayo
abin dadin ki rimi-rimi sai ki ki ci Rahane?
Haba Rahane, an Rahane na! ‘yar gidan BABANTA!! Kina son Uba kina gudun Dan sa, anya
an taba yin haka?!!!”
Hawaye suka fitowa Rahane surrrrr...! Har daga cikin hanci, cikin dakushewar murya mai cike
da kuka ta ce,
“Inna ni dai na fi son Yaya Khalipha.......”
Sai bammm! Inna ta buge bakinta da hannun ta,
“Kina auren wani kina cewa wani kike so? Maza-maza ki yi istigfari. Wanene Yaya Khalipha
kuma? Shashashar banza, irin wannan zabgegen miji haka na likawa a goshi?
To ni ina son sa ki bar mini, ki ga yadda zan killace abina a daki kada wata ta tayi min
kwace...... idan baki godewa Allah kin godewa Baba Likita ba, to za ki ga ba dai-dai ba a
rayuwarki wallahi Allah ki dawo cikin nutsuwarki.
Haba an Rahane na? Ibraheem mai kyau da shi? Mai tarin ilmi. Daga yi min allura ya bani
kwayoyi na sha na nemi ciwon bayan dake damuna na rasa.
Ubangiji ya ce idan bamu godewa rahamarsa ba, la-shakka zamu godewa azabarsa.
Ki nutsu, ki manta da wani Khalipha Rahane ki karbi mijin da Allah ya baki.
Shi bai ce baya son ki ba, bai kamata ke ki fadi hakan ba. SO na Allah ne, shi ke sanya shi a
tsakanin bayinSa.
Je ki ki yi wanka Rahane, ki yi kwalliya ki tarbi mijinki, ki yi kwalliyarki ta ‘ya’yan Hausawa ya
san cewa tushensa ya aura. Tashi maza ki cire shirmen nan na jikinki ki yi wanka.....”
Rahane ta katseta cikin kuka,
“Ni wallahi babu wankan da zan yi, da can bana wanka sai don ya zo? Kuma ai gidan nan
babu dakin da zai sauka in ba naki za a ba shi ba ina zai je?”
Inna dai lallami take don haka ta gintse dariyar da ta cika mata ciki, ta ce,
“Na ji na ba shi nawan ni zan kwana a falo, ai ko wadannan lausasan kujerun sun isheni in yi
barcina har da saleba. To canza kayan tunda ba za ki yi wankan ba.......”
Ai kuwa ta rantse ba abin da za ta yi a ciki. Ran Inna ya soma baci, ta tashi ta rabu da ita ta
shiga kicin don yin abincin da Daddy ya ce ta yi musu kafin su dawo, ta barta nan ta sanya kai
cikin kafafu tana ta kuka.
Ta gama kular da Inna, don haka ta fita sha’anin ta har ta