Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
gama girkinta ta jera a dining dan
karami na mutum biyu (mai kujeru biyu kacal) dake can gefe a falon. Duk shiga da ficen da take
sai ta ganta yadda ta barta, zuwa lokacin kuma ta gaji da kukan ta yi shiru, sai ajiyar rai take.
Kararrawar kofa ta soma kara, ai kuwa ta yi fit, ta yi dakinta kamar filfilwa. Inna ta bude kofa,
Ibaheem ne a gaba Daddy na bayansa, dukkansu rike da manyan ledojin cefanen da suka
yiwowa Inna na African-Food.
Da hanzari Inna ta amshe su tana musu sannu da dawowa. Sai a lokacin Ibraheem ya dube
ta sosai, sai ya gane ita ce Juman da Daddy ya nuna mishi hotonta. Sai ya yi murmushi. Ya ce a
ransa,
“Lallai yarinyar nan ja’ira ce, wato ita ce Juman”.
Da yake sun yi sallar isha’i kan su shigo a wani masallaci, dining suka hau suka soma cin
funkason Inna da miyar ganye da aka yi da manja da kaji zuku-zuku a ciki. Loma biyar Baba
Dacta ya kai ya dakata ya soma kwalawa Rayhanah kira.
Ai ji ta yi hanjin cikinta ya nannade waje guda ta kara kudundunewa a cikin bargon ta. Kira
har sau uku ta ki amsawa. Sai ya ce,
“Ibraheem je ka zo min da amaryar nan taka. Na lura yau surukuta take yi dani, ko gaisheni
ba ta yi ba”.
Ya fada yana nuna masa dakin. Kamar ba zai je ba, ko tunanin me yayi sai kuma ya tsame
hannunsa daga plate dinsa ya ciri tissue ya goge, ya sha ruwa sosai sannan ya mike ya nufi
dakin.
Murda kofar ya yi ya shiga dakin, tana can karshen gadon ta kudundune cikin blanket mai
bala’in taushi kamar curin alkaki, dariya ta kama Ibrahim, gata a Singapore amma ashe
bagidajiya ce. Abin da bai sani ba, Rayhanah ko a ina ta tsinci kanta ba abin da zai canza mata
akida ko dabi’a, ko al’ada ta kasar haihuwarta. Ita Rayhanah ba ta yarda da wani abu wai shi wayewa ba, abin da ta sani shine ita musulma
ce kuma Bahaushiya, amma tana karatun boko don fita daga duhun jahilci, ba abinda zai canza
mata wannan perception (belief). Ba za ta aro wata dabi’a ba wai don ta burge ko a ce mata
wayayya, masu yin hakan ma a Informatics Institute mahaukata take kallon su. Bargon ya kama ya zare shi ta karfin tsiya tana rikewa yana fizgewa ya cillar. Ya zauna a
gefen gado ya ce,
“Toh ke Rayhanah kuma haka zamu yi dake? Haka ake tarbar miji? Ko gaisheni baki yi ba
Rayhanaah, ga dukkan alamu ma bakin ciki kike da zuwana zan takura miki......”
Shiru kake ji, ta juya bayanta ta cure jikinta.
“Juyo nan, Allah-wallahi kada ki sa in kai hannu jikinki da sunan duka, ko in dauke ki a hannu
in kai wa Daddyn ke......”
Nan ma shiru ta yi masa. Bugun zuciyarta na kara tsananta..... tabbas shine suke magana a
waya, wanda muryarsa kadai ta yi tasirori masu yawa a zuciya da gangar jikinta.
Ya ce,
“Wato wai ke Jumah ko? To Allah yasa Jummai ce yau gani-gaki, ki kara yi min karya ki gani
in ban cinye bakinki ba. Wai ke ga wadda ta matsu miji ya zo har kike tambaya nine Ibrahim???
In ma Ibro ne ga ni, me za ki yi min? Me za ki bani kike nemana???”
Haushi ya kama Rahane, ba ta juyo ba ta ce (cikin kunkuni)
“Ni ban ce ka zo ba, ban ce ina nemanka ba. Tambayarka kawai na yi don in san da wa nake
magana ba don wai wani Ibraheem ya zo ba.
Da za ka koma in da ka fito ka sakar min mara in yi karatuna yadda na faro shi ba tare da an
takura min ba da na fi farin ciki.......”
Kama baki ya yi da mamaki mai yawa, dariya kuma ta kama shi da yadda take tura baki gaba
tana zumbura shi tana cunoshi yana girgiza kai yana dariyar ya mika hannu ya janyo tafin
kafarta keeey.... zuwa inda ya ke zaune, ya kama hannayenta biyu ya rike cikin tafin hannunsa
na dama ya soma dalle mata baki da yatsunsa na hagu.
Ya ce, “Say it again, ashe baki da ta ido? Watch your words mijinki ne ni ba saurayinki ba....’’
Azaba ta ishi Rahane har leben ta na sama ya dan kumbura..... wasu matsiyatan hawayen
azaba suka feso, kamin kuma ta yi aune Ibraheem ya rungumeta gaba dayanta cikin kirjinsa,
runguma so calm har baka hango ‘yar Rayhanah cikin physique chest din Ibrahim.
Sannan ya kai bakinsa cikin nata ya soma yin abin da ya fi so a rayuwarsa, wato mouth to
mouth kissing. Rikon da ya yi mata mai karfi ne da ta kasa kwatar kanta. Rayhanah ta tsinci
kanta a wata duniya ta daban da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba.
Abubuwa da yawa ke yawo a kwanya da zuciya da jikin Ibrahim a wannan lokacin. Wadanda
shi kansa ya kasa fassarasu, ya kasa daina sumbar kuma ya kasa rabata da jikinsa. A lokacin
ta fara kuka na ido, wato zubar hawaye, tunda kamar yadda ya ce din ne zai cinye bakin, ta
yarda tareda yin amanna da gaske yake cinyewar zai yi, in tayi la’akari da yanayin yadda yake
tafiyar dashi din. Ya ki sakin bakin balle ta koma magiya.
Hawayen da ke fita a idonta su suka sanyayar da jikinsa, ya daina abinda yake yi din ba don
ya gaji ko ya gamsu ba, he don’t actually know what he’s deriving in it but it’s something
pleasurable ever in his entire life...., amma hakan bai sa ya rabata da jikinsa ba. Data samu
hakan sai ta soma ba shi hakuri cikin kuka dole ya karaya ya cikata. Shi da kansa ya dauko ribbon din daya fadi ya tattara kakkarfan gashin da bai taba ganin
relaxer ba ya daure mata...... a ranshi yana ta mamakin yadda mace zata bar gashin kanta in
its naturality haka. Shi kuma ya koma da baya ya kwantar da bayansa a gadon kafafunsa na
kasa. Ya nuna mata hanyar kofa.......
“Ki je Daddy na kiranki”.
Ya fada da wani sauti kamar ba nasa ba.
Ta kokarta ta mike amma cira kafa ya gagara. Sai ya yunkura ya mike gaba dayansa yana
binta da kallo sosai, ya mika hannu ya kunna fitilar data fi kowacce haske a dakin (ressaince) ta
jikin ceiling, wadda haskenta yasa Rayhanah kai tafukan hannunta ta rufe fuskarta.
Doguwa ce sosai amma ya fita, siririya ce amma kirjinta da kugunta a cike suke. Har yanzu
sanye take da suturarta ta dazu (belted -waist -shirt) da dogon bakin wandon jeans. Ta zargo
belt din tsakiyar rigar ta daure. Sai ya kamo hannunta suka fito suka tadda Daddy da Inna suna
hira a falo, tuni ya gama cin abincin.
Rayhanah ba ta taba jin kunyar Daddy a duniya irin yau ba. Ga kanta babu kallabi, sai ta cure
a gefe daga can bayan Inna wai gaishe shi take, shi sam ma baya jiyota, balle ya San magana
take ya amsa mata.
Abin da ya ce shine,
“Rayhanatu yau Allah ya yanke mana komai ga Ibrahimu ko?”
Daga mishi kai ta yi ba tare da ta dago ta kalle shi ba. Ya yi murmushi na jin dadi da samun
kwanciyar hankali cikin kulawa yace
“Babu wata damuwa ko?” Ta sake daga mishi kai again. Da hanzari ya ce,
“Ki bari Rayhanah, kada ki bullo da wannan sabuwar mu’amalar tsakaninmu, wai saboda
Ibrahim ya zo.
Ni ban san shi ba ke na sani a matsayin ‘yata, in kuma kin canza min matsayi daga uba
zuwa suruki ne, ehh to ki gaya min?”.
Nan ma girgiza kai ta yi. Ya dai tabbatar yau Rayhanah surukuta ta musamman take yi da shi
ba zai samu matsayin baya da yake so ba.
Sai ya hakura ya mike a lokacin Ibrahim yana wajen socket ya kunna wayar Rayhanah a inda
tasa chaji ya dau lambarta ya zuba nashi lambobin a ciki na layin da ya saka anan Singapore,
amma bai sa suna ba.
Daddy ya ce, “To Ibrahim mu tafi masauki, tunda ka yi min firraqu ni da ‘yata, kaima ba zan
barka a gidan ba, wuce muje”.
Shi Ibraheem murmushi kawai ya yi ko Rayhan bai kara kallo ba ya yi gaba, ka rantse da
Allah ba shine wancan mai deep kisses din ba.
Shi yake tukasu zuwa otel din su, sai dai ya karanta hira tsakaninsu, ya fi mai da hankali ga
tukin.
Daddy ne kadai yake ta zuba yana gaya masa don Allah ya rike masa ‘ya amana, ya ji kanta
ya tausaya mata, ya tausayawa maraicin ta da raunin ta, ba ta da uwa ba ta da uba sai shi a
yanzu. Duk abin da ta nuna ba ta so don Allah kada ka takura mata.
Ibraheem ya ce a ransa,
“Saboda ni ba Da bane, tsinto ni ka yi a bola?”
*****
[12/27/2019, 17:59] Takori: Sabon dare a wajen Rayhanah! Bayan fitarsu ta dade ba ta motsa
daga inda take ba, wato bayan Inna Juma. Ita Juman kicin ta shiga ta ci gaba da ‘yan
kaye-kayenta da su wanke-wanke, tana yi tana ‘yan wakokinta.....
Wai “duk wayon amarya sai an sha manta....... na zama dauko riga, na zama dauko wando,
na zama dauko hula.... shekara mai zuwa war haka zan fara goyo da wankin kashi da share
tumbidi........”
Abin da Inna ba ta sani ba shine, ita Rahane ba jinta take ba don ta yi nisa cikin tunani mai
zurfi. Da ta gaji da zaman falon sai ta lallaba ta shige daki. Kwanciya ta yi a gadonta don ta
samu barci, amma idanun sun ce basu san wannan ba.
Duk motsin da ta yi, duk juyin da ta yi, jinta take a kirjin Ibraheem. Gaba dayanta ma in fact,
kamshin Ibrahim take, wani irin kamshi da ba ta taba jin mai sanyi da dadinsa a duniya ba, ba ta
kuma iya tantance kowanne turare ne ba. Ta kasa barci sai juyi a kan gado.
Jikinta, zuciyarta da kwakwalwarta ke karbar wani sabon sako mai kassara gabban jiki. Cikin
wannan halin, wayarta da Ibraheem ya aje a bed-side ta soma kira. Ba ta yi niyyar dagawa ba,
domin dare ya mika sosai, amma da kiran ya isheta sai ta mika hannu ta daga.
Sabuwar lamba ce, amma ta nan Singapore. Daddy ba zai kirata a irin wannan lokacin ba sai
dai in ba lafiya ba.
Wannan tunanin da ta yin shi yasa ta daukar wayar ta amsa cikin sanyi. Wajen minti biyu ba a
yi magana ba, za ta kashe ya ce,
“Rayhanah kada ki kashe min waya, zamu bata”. Da muryar da ta kasa amincewa cewa ta
Ibraheem ce.
A hankali ta ji idanunta sun lumshe da kansu. Ya kara cewa,
“Hira nake so muyi, Rayhaanah za ki yi min?”
Ta girgiza kai kamar yana ganinta. Amma ba tayi magana ba.
“Ba za ki amsa ni ba Rayhanahhh?”
Ya fada tun daga karkashin zuciyar sa in a subdued.
Ji tayi sunan yafi dadi a bakin sa fiyeda bakin kowa, fiyeda bakin duk wani Dan Adam data
taba jin ya furta sunan a kunnenta, tun bayan da Allah ya yayemata lalurar ta, jama’a suke
ambaton RAIHANAH!!!
“Ni fa barci nake yi, hirar me zan maka da tsakiyar dare haka Ya Himu?”
“Karya kike idonki biyu!”.
Ya fada kai tsaye. Kamin ta ce wani abu ya ce.
“Hira irin wadda mata take wa mijinta, kamin yayi barci”.
Ji ta yi kamar ya kinkimo katon dutse ya dora mata aka. Don haka ba ta amsa mishi ba ma
wannan karon. A sanyaye ya ce,
“Rayhanah haka zamu yi da ke ko?”
Da likitan zai tsaga jikinta a wannan lokacin da ya ga yadda jininta ya daina ratsawa a jikinta.
Mene ne haka? Yau wane irin dare ne a rayuwarta? Me ke shirin faruwa da ita?
Shirun nata ya matukar tuke Ibrahim, ya ce a dan zafafe.....
“Allah idan ba za ki bude baki ki yi min magana ba zan zo yanzu Rayhanah mu kwana tare,
cikin bargo daya. Kin san kuma Inna ba za ta ki bude min kofa ba”.
Hawaye ya cicciko idanunta, wannan shine abin da ta fi tsoro a rayuwarta kenan yanzu (sake
kadaicewa da Ibrahim).
Cikin ‘yar rawar murya da karkarwar jiki ta ce,
“To me..... me zan ce maka Ya Himu?’
“Labarin rayuwarki ta baya, da saurayinki Yaya Khalipha.......”
Hannu ta kai ta toshe bakinta.... ta fidda ido alama razana.
“Ka daina irin wannan maganar don Allah..... babu kyau Ya Himu”.
Ibraheem ya lumshe idonsa a hankali ya ce,
“Na bari, to amma samarinki nawa a Kazaure?”
Da sauri ta ce,
“Allah mu bamu da saurayi, Daddy baya bari”.
Dariya ya yi, domin yadda ta yi maganar kuruciyarta ta fito sosai. Sai ya kara tausasa murya,
“Ai an gaya min ne wai da Yaya Khalipha ne zai aure ki......”
“To Allah bai yarda ba”.
Ta fada da sauri. Ta ce a ranta “ko da yake son nawa nima nake son sa, ai kai nake gani a
matsayin miji cikin mafarkaina, don haka ban mika masa soyayyar zuciyata gaba daya ba”.
Ba ta san cewa a fili ta fada ba.
Ibrahim ya runtse ido, cikin mamaki da hardewar harshe da nauyin American-accent dinsa
ya rinjaya ya ce,
“Har mafarkina kike yi Rayhanahhh?”
Sai a lokacin ta ankara da subutar bakinta, ta ce,
“Lah! Ni fa ba da kai nake ba”.
Ya ce,
“To na yarda ba da ni kike ba, tadin zuci ne ko? Amma ya ya kike ganina cikin mafarkin? Da
‘ya’ya, da jikoki ko Rayhahhh?”
Muryarta na rawa cikin kidima da daburcewa ta ce,
“Don Allah zan kwanta, gobe (8 am) ina da test”.
“Da izinin wa za ki je yin test din?
Da kam kina bisa umarnin Daddy albarkacin cewa bana nan, amma yanzu na dawo, babu
inda za ki kuma zuwa ba da amincewa ta ba, goben barin kasar ma zamu yi gobe insha
Allahu......”
Ai dama kiris take jira, sai ta soma magana cikin son kecewa da kuka....,,
“Idan ka yi min hakan ka zalunce ni Ya Himu, na wahala a kan karatun nan, ga shi na ci
karfinsa watanni tara suka rage min...”.Sai kuka.
Kyaleta ya yi ta yi ta yin abinta, bai kashe ba ita ma ba ta kashe ba. Gidan waya na ta kwasar
kudi. Saida ta yi shiru don kanta, sannan ya sassauta murya.
“Na ce zan rabaki da karatunki ne?”
“Eh, ba haka ka ce ba?”
Ya ce cikin ‘yar dariya,
“Ni ban ce haka ba, barin Singapore na ce”.
“Eh mana, am not a kid, barin kasar na nufin barin karatun!”.
Murmushi ya yi mai sauti.
“Rayhanah bani da wannan amsar yanzu, muyi hirar da na ce muyi”.
Jikinta ya yi sanyi kamar ta soma rokonsa amma kawai sai ta fasa, muryarta abin tausayi ta
ce,
“Tohh”.
“Has he ever held