Rayuwar Raihana Part 2 Hausa Novels by Takori Kabara.pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   9 / 11

24K to 27K   out of 31.3K words


kalle shi ta wuce, yana da kimar da babu mai ita a idanunta a duniya idan ka dauke iyayenta.
Don haka ta ja ta tsaya idonta cike da hawayen da suka kasa tsagaitawa. Har Baba Dacta ya
iso inda take ya kama hannunta idanunsa shima sun kada sunyi jawur, amma ba hawaye a
cikinsu.
Sha’aban ya koma ya matso da motar har inda suke. Baba Dacta ya bude kofar baya ya shigar
da ita ya rufe, shi kuma ya zauna wajen mai zaman banza, Sha’aban ya ja motar suka hau titi.
Cikowar da ta ga kofar gidan Hakimi ta yi da bil-adama bai zamo bako a gareta ba, domin an
saba yin bukukuwa da daurin aure a gidan Hakimin.
Sha’aban ya yi parking, wannan karon ma hannunta cikin na Baban suka shiga gidan. A dakin
Hajiya Karima ta tadda Hakimi da kansa da sauran ‘ya’yansa wadanda suke kusa ba na nesa
irin su Hibbah ba, har da Nabilah, da sauran iyayensu mata.
Ga Nabilah na suma ana yayyafa mata ruwa kamar mai iskokai, idan ta farfado ta yi surutai sai
ta kara sumewa. Fuskar marikiyarta Inna Indo kamar hadari ta dubi Rahanen da Dacta ya shigo
da ita shekeke!. Sai Haj. Karima Maman Nabilan ta asali ce ta nuna mata wajen zama, ta zauna
a darare tana ta kuka. Dacta yake gayawa dan’uwansa a bakin titi suka ganta dama ya kintaci lokacin tahowarsu ne
da awoyin da za su dauka kamin su iso, ya je tashar ya daukota sai ya hangota bisa titi.
Hakimi ya ce, “Sannu Rayhanatu kin ji, insha Allahu kin yi sallama da rayuwar maraici, tunda kin
samu uba irin MANSUR da nagartaccen miji irin IBRAHEEM da kuma ni surukinki Abdulkadir.
Share hawayen nan Rahane, daga yau na tabbatar miki haka kawai ba za su kara zuba ba. Sai
ko a kan wata kaddarar daban ba ta maraici da rashin dangi ba. Muna yi miki barka da zuwa cikin zuri’armu ta alfarma wadda kudurinta shine kiyaye martaba da
mutuncin talakawanta. Sannan muna farin cikin shaida miki cewa, mun samu kanwar
mahaifiyarki Zinaru wadda ta hanyarta aka samu dangin mahaifiyarki. Sha’aban jeka shigo
dasu”. Ya mike da kansa ya iso har gabanta, ya dora mata warawaren farin zinare (bangles) a kan
cinyarta.
“Ga sadakinki, mun daura aurenki da IBRAHEEM MANSUR TAKAI. Babanki ya karbi waliccin
ki, na karbi na Da na Ibraheemu. Shaidar da Babanki Mansur ya yi miki ta kyawawan halaye,
tarbiyya, biyayya da hakuri, ina fatan ta dore har a gidan aurenki.
Yadda Ibraheem ya karbi zabin da mahaifinsa ya yi masa hannu bibbiyu, muke fatan kema ki
karba. Ki yarda cewa baka auren mijin da ba naka ba, kamar yadda baka auren macen da ba
taka ba. Komai na rayuwar Dan Adam tun fil’azal rubutacce ne a (Lauhul-Mahfouz). Muna son
jin ta bakinki Rayhanah, shin kin amince da zabin Babanki ko kina da uzirin da zai hana ki yin
hakan?”

Girgiza kai take cikin kidima da gigicewa. Wannan fa shi ake kira reshe ya juye da mujiya….
Ana bikin duniya ake na kiyama….. Abinda ta samu harshenta na fadi ba tareda ta shirya

kalaman daga kwakwalwarta ba kawai shine,
“Idan ni din ban yi biyayya ga zabin Baba Dacta ba…., idan shi bai ji kyamar hadani da Dan da
ya fito daga jikinsa ba, duk da kauyancin da talaucin nawa, da lalurar dana samu kaina ciki a
baya…. ai ni ba zan ki karbar zabinsa ba ko da tura kaina cikin dakin Zakuna ne.
Yadda Allah zai tambayeni idan ban yiwa iyayen da suka tsugunna suka haifeni biyayya ba, na
tabbata haka zai tambaye ni idan ban yiwa Baba Dacta ba.......!” Ta ci gaba da kukan da bata
san dalilinsa ba. Ta barsu suna juya tasirin kalamanta a zukatan su.
Daidai lokacin da ta ji sallamar jama’a, ta daga kai a hankali tana kallon su. Wasu harbatsattsun
kauyawa ne babu wadda za a ce “gara ita”. Da kyar ta gane Zinaru a cikinsu saboda cindon
dake gefen hancinta.
Ji ta yi kamar anyi mata gafara ta mike tsaye tana kallon su idanu a warwaje. Zinaru ta karaso
ta rungumeta, wani hamami na baki da hammata ya nausheta, mugun naushi kuwa, rokonta
take ta yafe mata, alhakinsu ya sanya ta wulakanta a rayuwarta.

Abinki da ‘yar likitoci, da dai ta samu Zinaru ta saketa ai sa ta yi toilet din Haj. Karima da gudu
ta rika kelaya amai cikin sink kamar ta amayar da ‘yan hanjinta. Su sun dauka kuka ta je tana yi,
don haka ba wanda ya bi ta.
Da ta wanko fuskarta ta dawo ne Zinaru take mata bayanin sauran matan su hudu, biyu tsofaffi
biyu za suyi shekaru arba’in haka, amma wahalar rayuwar karkara tasa sun fi kama da tsofaffin.
Akwai mai fara’a sosai cikin dattijan mai amsa sunan Inna Juma, Zinaru ta ce, “Juma kanwar
kakarki ce wadda ta haifi ubanmu, Inna Hanne Yayar mahaifinmu ce, don haka uwa ce a gareni
ke kuma kaka a gareki. Ta-sidi da Kubra kannen mahaifiyarmu ne gasu duk a Albasu suke aure,
ni kuma a Jahun. An nemo ni Takai ta hanyar Inna Juma da yake ita tana nan Takai ko bayan mutuwar mijinta
Malam Saleh, bata taba haihuwa ba, mu kam akwai tarin iyali. Ina yi miki ta’aziyyar Iya Bilki da
Malam Rashidu, ki dubi Allah Rahane ki yafe mini..........”
Kuka sosai Zinaru take yi har Rahane ta ji zuciyarta ta girgiza. Ba ta son kukan babba ko kadan
balle Zinaru da take jin ta kamar mahaifiyarta. Duk da bata kasance mai kyautayi a gareta ba.
Ta yi saurin rike hannunta, “Na yafe miki Inna Zinaru, wallahi na yafe muku baki daya Allah ya
yafe mana”.
Juma ta ce, “Bar ‘yar banza da kukan munafurci, sai yanzu da kika ganta a matsayin mutum mai
daraja da kyawun gani kika san ta yafe miki? Kin taba zuwa kin ganta ko sau daya bayan
barinki gidansu? A matsayinta na diyar shakikiyarki?
Al’umma ban san bolar da muka kai zumunci a wannan zamanin ba, na cikin ka kawai shine
naka. Sau nawa ina tambayarki inda take kina cewa ba za ki rike ta ba? Duk ma inda take ta je
kowa ya yi ta kansa? Sai da na bi diddigi ta wajen marigayi Ado ya gaya min inda ta fada?
Kauce daga nan kada in maganre ki........” “Inna komai ya wuce”.
In ji Haj. Karima.
“Rayuwar duka ‘yar afuwa ce, kema ki yi hakuri. Mun godewa Allah da ya hada ku cikin sauki, a
taru duka a yafewa juna komai na duniya dan afuwa ne. Da Ubangijinmu baya yin afuwa a
garemu da bamu kawo yanzu ba”. (In ji Hakimi).
Duk cikinsu Rahane ji ta yi Inna Juma ta fi kwanta mata. Ita ce tsohuwar ciki, amma ta fi su

kwari da kyan gani, da alamun tsafta a tattare da ita kuma da jin cewa tana sane da ita, har tana
neman ta.

Bayyanar dangin Yalwati mahaifiyarta shi ya shafe firgicin da rudanin da zuciyarta ta shiga na
auren mutumin da rabonta da shi shekaru goma cif, wadanda tsayinsu da shudewar su basu
mantar da ita waye shi ba; Dan Mami! Wanda ta fi so fiye da kowa da komai a rayuwarta (YA
HEEMU). “An gudu ba a tsira ba, an rabu da Bukar an haifi Habu!!!”.
In ji masu iya magana. Har gara-gara ma Khalipha a kan son da Mami ke yiwa HEEMU da
burirrikan da ta ci a kanshi. Wadannan tunane-tunane basu bar zuciyar Rahane ta huta ba a
wannan dare, basu bar idanuwanta sun runtsa ba. Jin al’amarin take kamar almara.
Wane irin aure ne irin haka? An taba yin aure irin nata a duniya kuwa? Babu shiri? Babu zato
babu tsammani? Babu so babu kauna daga kowanne bangare? Babu shakuwa babu alaqa?
HIMU? I.M? IBRAHEEM MANSUR? Wai shine mijinta? Ya ALLAH! Idan mafarki nake kayi
gaggawar farkar dani kafin na zama zautacciya!!! Rayhanah ta fada a fili tana mai kaiwa da
komowa kamar mai yin safah da marwah a dakin data ke ciki.
Wane irin matsayi Baba Dacta ya bata ne a zuciyarsa haka? Me take das hi day a bata
wannnan matsayin? Ba ta cancance shi ba, matsayinta bai kai nan ba! Hadin bai yi matching ba
sam..... Ibrahim ya fi karfin ta!! Sau dubu gara Khalipha. Shi wannan ko babu komai akwai
shakuwa da fahimtar juna akwai kuma shimfidar fuska idan babu ta tabarma ba wannan
zundumemen dan bokon ba.
Ta daga hannunta na dama a hankali ta kalli warawaran farin zinare da Haj. Karima ta zura
mata, wadanda Hakimi ya ce Sadakinta kenan. Sai walainiya suke a hannunta cikin rangwamen
hasken lantarkin dake dakin da take kwance (bedroom din Haj. Karima). Wadanda karbarsu da
ta yi sun tabbatar da cewa ta zama matar IBRHEEM, ba Khalipha ba. Mafarke-mafarken da ta rinka yi a Informatics farkon kulluwar soyayyarsu da Khalipha a kan
Ibraheem suka shiga dawo mata filla-filla, wadanda a yau ta fassarasu da cewa, Allah ne yake
nuna mata Ibrahim shine uban ‘ya’yanta ba Khalipha ba.
To ya za ta yi da son Yaya Khaliphan? A wannan sabon matsayin nata na matar kaninsa?
Daddy na nufin ta haka rami ta binne soyayyar Khalipha wanda har zuwa yanzu zuciyarta ta ki
yarda da cewa ya ki aurenta ne don yaudara, sai ko don wani muhimmin al’amari beyond his
ability. Haka nan zuciyarta ta yi masa wannan uzurin duba da tsayin lokacin da Khalipha ya diba
cikin soyayyarta tun tana kankanuwa, wannan ba yaudara ba ce.
Laifinsa daya ya ki su magantu balle ta san daga ina matsalar take? Sai dai kaso tamanin cikin
dari na zuciyarta ce mata yake “Daga Mami ne”.
To in daga Mami ne ya ya akai ta amince ayi da wanda ta fi so ta fi ciwa buri fiye da Khalipha?
Da ta ga wadannan lissafe-lissafe da saka da warwara da tunane-tunane na neman tarwatsa
mata kwakwalwa da wargaza kwanyar kanta, ba kuma zasu samar mata da amsoshin data ke
son sani ba, haka bazasu zamo solution ga halin da take ciki a yanzu ba, sai ta tattarasu duka
ta mikawa Allah! Wahidun Qahharun!! Mai tsarawa bawa rayuwa ta inda bai zata ba. Minsharin Inna Juma ya dameta, wadda suke kwance tare a dakin anyi mata shimfida a kan
kilishi da filo sai kwasar rabar A.C take tana kwararo minshari mai sauti.
Kallonta Rahane ke yi cikin shudiyar fitilar barci dake kunne tana jin wani sanyi a zuciyarta.

Kafin wata sabuwar fargabar ta zo ta lullube mata zuciya........ yaushe za su hadu da Ibrahim?
Yaushe zai zo? Da wace fuska zai karbi al’amarin? Wace irin karba zai yiwa auren nasu?
Maganar so ma ta san babu ita in aka yi la’akari da irin yanayin rayuwarshi wadda ta sha
bambam da ta Khalipha ta kowanne bangare. Ita dai kam a yanzu zuciyarta neutral. Wato ba ta bayan kowanne bangare (neither tana son sa
nor ba ta son sa). Lamarin zai kasance ne da fuskar da ya zo mata, da ita za ta karbe shi. Babu
soyayya cikin zuciyarta kuma babu kiyayya, kai ita duk jinin Dr. Mansur ma abin so ne da
girmamawa a gareta. Ba don komi ba sai don cewa, su suka rufa mata asiri a lokacin da ta bude ido ta tsinci kanta
tare dasu, babu kowa nata.
Ba ta taba kullatar Mami ba ko ta sawa ranta Mami ba ta sonta. Rikon shekara goma shag Dan
da ba kai ka Haifa ba ba karamin sadaukarwa bane. Ta yarda da abin da Mami ke ikirari na
cewa ba kinta take ba, asalinta ne da tsohuwar lalurar ta ya sanya bata isa ta hada zuri’a da ita
ba. Ita ma kuma ta yarda da cewa asalin nata (idan aka hada da nasu) kaskantacce ne. Sannan
lalurar ta abin gudu ce ko don tsoron genetic wato gado. Sai dai kuma Mami ta mantacewa ba’a
yiwa Allah wayo itama bata gada ba iftila’I ne na Ubangiji. Hakan baya nufin suma ba mutane
ne da Ubangiji ya halitta don baya son su ba,kowa da kaddarar rayuwarsa in one way or the
other! Dukkanmu masu nakasu ne idan bata nan ba ta can. Maganar asali kuwa Ubangiji guda
ne ya halicce mu yana kuma son bayinsa bakidaya.
Ba don baya son su bane ya hana su ilimin, mulkin da arzikin, sai don cewa ko ‘yan yatsu bai yi
mana su kai daya ba. There is always hierarchy...... a tsakanin bani-Adam. Abin da ta yarda da
shi shine, “Inna akramakum indallahi atqakum”. Wato mafi girmanku a wajen Ubangiji shine
wanda yafi tsoron sa. Don haka zamu iya cewa, a wannan daren baki dayansa, idanuwan Rahane basu runtsa ba. A
kan kunnenta aka kira Asubahi, sai ta yi amfani da damar don gusarwa da kanta damuwar da ta
gallabeta ta addabeta, ba kuma za ta amfanata da komai ba.
Ta yo alwala ta fito ta tashi Inna Juma. Yayin da ta nabba’a a gaban mahaliccinta don nemawa
zuciya, kwakwalwa da rayuwarta sauki a wajen Mai duka. Tana rokon sa ya cire mata firgici da
faduwar gaban da take samun kanta a ciki, a duk lokacin da ta tuno ranar da zata yi arba da
IBRAHEEM MANSUR TAKAI. Har yanzu tana tantama tana kuma shakkun kasancewar wai
Ibraheem ne mijinta ba Khalipha ba.
A hankali ta kai duba ga warawaran hannun ta masu kara tabbatar mata da hakan, ta hanyar
fidda dan sauti kas-kas da walainiyar da sukeyi a duk kankanin motsin da ta yi. Abubuwan ban
mamakin rayuwa yawa garesu, wasu ma basu zo ba tukunna….. wasu ba’a fara su bama
RAYHANAAAAH!!! ****
Washe gari ya kasance litinin, su Daddy tun jiya bayan daurin aure suka wuce Kano aka daura
na Khalipha da Radhiyyah. Daddy shi ya biya sadaki da wara-waran zinare kamar yadda ya
biya na Rayhanah. A take kuma gidan su amarya suka zarce da biki na tsere ma sa’a.
Ita dai Mami har zuwa lokacin ta gaza nutsuwa da samun kwanciyar hankali, don har zuwa
lokacin Daddy bai bude baki ya ce mata komai game da Rayhanah ba, bai tambayeta ina
Rayhanah ba, bai gaya mata auren wa aka daura a Takai ba.

Ba ta kara ganin Khalipha ba har zuwa lokacin, ya wuce Abuja ya mai da kansa kamar inji
saboda aiki, ya ki yarda zuciyarsa ta kadaice ko kadan balle ta samu filin saka mishi damuwa,
tashin hankalin jin cewa shi ba dan Baba Dacta bane ya shafe komi, wato ya fi karfin soyayyar
Rayhanah wadda ya kira da sunan bygone issue. Sawun Giwa ya take na Rakumi kuma gaba
da gabanta wai aljani ya taka wuta……….
Daddy ya gama masa komai tunda bai bar Rayhanah ta wulakanta ba, wanda shine babbar
damuwarsa kuma babban abinda ke kara ingizashi cikin son ya aure ta ya tallafi rayuwarta
bayan Kalmar SO, ya zaba mata miji na garari na likawa a goshi in ana likawa, wanda zurfin
tunaninsa bai taba bashi kasancewar hakan ba. Damuwarsa daya, wace irin tarba Ibraheem zai
yiwa Rahane ‘as a wife??? Yana yi mata fatan alheri.
Shi yanzu haka ma shirin zuwa Jos yake wajen dangin Mami na can don ya fara bincike a kan
al’amarin mahaifin nasa, ya dangana da Hurghada. Ya mance da wata aba can wai amarya
Radhiyyah.

Lafiya sumul Daddy ya tarbi Dr. Asma’u da fara’a da komai a sanda ya shigo gidan daga ofis
ranar da ya dawo daga Takai, ta yi mishi barka da zuwa. Rungumeta ma yayi, ya ce,
“Mami naaa.....”
Ita ma ta ce,
“Dacta naaah....”
Tana loosing tie din wuyan shi.
“Ya aka baro su Hakimi?”
“Kowa lafiya”.
Ya zagayeta da hannayenshi.kanshi cikin wuyanta yana sunsunar ta yake fadin;

“Gashin ba saloon..... Mami na tsami ba wanka, kayan jikinta yau kwana uku ba ta canja su ba.
Lebenta a bushe kyamas, kamar tayi sati bata sha ruwa ba! Allah ya isa........ tsakanina da duk
mai canza min Asma’u na zuwa Ta-ma’ule!”.
Ya dan ture ta ta yi taga-taga ta fada kan gado ya wuce toilet ya hada ruwa mai zafi ya zuba
dettol da sabulun ASDA, ya dauko Mami ya wanketa tas, ya wanke gashinta da kumfar
shampoo (pert-plus) ya nado ta cikin shawul ya jona dryer yana busar da gashin kanta. Ya
dauko doguwar riga ruwan madara mai kyau dinkin Dammam ya sanya mata, ya juyota ya
rungumeta.
Runguma mai karfi da tsanani. Kamar zai tsaga kirjinsa ya sanyata. Mami don tausayin Dacta,
sai tasa kuka.
Kyaleta ya yi ta yi kukanta mai isarta bai katse ta ba, tana rungume a kirjinsa.
“Ni kaina na rasa me ke damuna Dacta, na zama rikitacciya, abu kadan sai ya ruda ni, ya
tsorata ni. Kaina na gaya min abubuwa wadanda na kasa gane musu........”
Hannu ya kai ya toshe mata baki.
“Ba komai bane, sakaci da ibada ne, da rashin tsai da salloli biyar a kan lokaci. Mami ki nutsu ki
koma Asma’unki, you are not my precious Asma’u, Dacta guda da warin hammata???”
Ya fada yana dariya yana fesa mata ‘Carolina Herrera’ sai ta rungume shi kam’kam, da haka
al’amarin ya sauya. Ko bayan da suka koma cikin nutsuwarsu suka yi wanka suka yi sallah bai
gaya mata ya aurawa Ibrahim Rayhanah ba. Sai batun dauko amaryar Khalipha.

Gidan da Daddy ya ginawa Ibrahim da Khalipha na nan a (Farm Center). European Flat zallah,
mai dakin barci uku, falo, katon kitchen da bandaki, can ya ce a kai kayan Radhiyyah, har da
Mami a ‘yan jere da Dacta Haliman kanta. Naira kam ta sha kuka, aure na GIRMA da KASAITA
irin wanda Mami ke so. Washe gari aka kai amarya dakinta, sai dai babu ango babu alamarshi. Wayoyinsa duk a kulle,
basu sani ba shi a lokacin kwanansa biyu a Hurghada tare da Uncle Yohan Yayan Mami suna
binciken dangin Mukhlis Imran a birnin Hurghada.
Haka suka hakura suka baro amaryar ita kadai da ‘yan aiki a gidanta ta

9 / 11