Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
RAYHAH......”
Ya fada a wahalce tare da mika mata hannun damansa wanda ke daure da ruwan kasar agogon
‘Swatch’.
Ba ta mika mishin ba, sai ta bude kofar motar tana fadin “An kira sallah Yaya K....... can I go?”
Ya shafo sumar kansa ahankali daga goshinsa har zuwa keyarsa idanunshi a lumshe, sun kada
sun zama brown dinsu ya ce a wahalce,
“Go to Masjid Rayhah........! tun kafin ki kashe ni da raina!!”.
****
[12/24/2019, 21:47] Takori: Wannan shine dan mabudin da ya bude kofar soyayyar Rayhah da
Khalipha. Alkunyarta, rashin son magana, saukin kai da kawaici, rikon addininta sune manyan
halayen ta da suka jawo Khalipha gaba daya ya afka a rijiyar soyayya ruwan ya sha shi har
wuyansa. Duk yadda ya yi tsammanin Rayhanah ta wuce nan a qualities din da yake hasashen tana dasu,
wadanda yake so a matar aurensa.
Washe garin ranar Daddy ya zo ya dauketa suka wuce Kano, ta kwana biyu ya maidota Talata
saboda Monday aiki bai barshi ya samu sukuni ba, ba kuma zai sata a motar haya ba.
Yadda Rayha ta ga Mami cikin kwanaki biyun nan da ta yi abin ya tsoratata. Completely Mami ta
canza kamar wahainiya, muraran take nuna ba ta son zaman Rayhanah a gidanta yanzu, duk
da Baba Dacta bai fito fili ya gaya mata Khalipha son ta yake ba. Amma ya ce da ita aure zai
mata ba za ta shiga B.U.K ba. Ta tambaye shi waye mijin? Ya ce da ita, “Time will tell you!” sai tasa mishi ido tana cewa a
ranta, “Kai ma lokacin zai gaya maka ko wace ce Anita Shiyana, tunda Asma’u ka sani.
Lallai gaskiyar Dr. Halima ta yi sakaci da yawa da Dr. Mansur, tana ganin cewa wai yana sonta,
ba za ta taba bin malamai a kansa ba. Yanzu kam ta yarda cewa ta yi sakacin, tunda ya fara
munafuntarta ya soma boye mata wasu al’amura da ya lura ba za ta yi na’am dasu ba.
Shi kuma har ga Allah zuciyarsa daya, bai ki gaya mata don munafurci ba sai don baya son
bacin ranta ko nasa cikin al’amarin, ya fi son sai komi ya kankama tukunna sannan ya zauna ya
yi mata bayani ya ba ta hakurin karya alkawarin da ya yi mata, a dalilin ajizanci irin na dan
Adam. Bai yi da niyya ba, bai hadasu ba su suka hada kansu. Shi dan bin umarnin Allah ne kawai da
sunnar ma’aiki da ya ce idan ‘ya’yanku sun nuna suna son aure, to ku yi musu cikin umarnin
Ubangiji.
Ban da haka shi bai taba hasaso Khalipha zai taba cewa yana son Rayhanah ba, yana dai da
nashi burin a kan Rayhanan amma tunda Khalipha ya riga ya furta to ya kashe waccan kudirin
nasa ya karbi wanda Allah ya bayyana.
Duk sati Khalipha na tafe, baya Abuja baya Kano, baya Kazaure. Wata muguwar shakuwa da
fahimtar juna ta wanzu tsakaninsa da Rayhanah. Duk da cewa kullum shine mai nuna son,
kalamanta tsada suke masa saboda kunyarta, in yana so ya ji furucin bakinta, to sai ya kirata da
Rahane, ko ya ce matar Audu, a nan kam ba ta jurewa sai ta bayyana masa kyawawan
hakoranta guda talatin da biyu.
Ba soyayya ce kadai tsakanin Khalipha da Rahane ba, akwai wani abu wai shi yarda da juna,
kusancin zuciya da zuciya da amincin da ya zarta soyayya.
Ko Baba Dacta bai san Rahane yadda Khalipha ya yi mata kyakkyawan sani ba ciki da bai
dinta. Ya san halinta, ya san abin da take so da wanda ba ta so. Ba ta da yawan ado, kuma ba
ta cika kwalliya a jikinta, she is smart, and simple. Yana son Rayhanah har yadda ba zai iya
kwatantawa ba. Yana son Rayhanah yadda shi kansa bai san adadin ba. Yadda kwanaki ke gudu suna juyawa tamkar gare-gare abin wasan yara a wannan zamanin,
don haka bai zamo abin mamaki ba idan aka ce har ga watanni takwas sun cika. Rahane ta fito
da kwalin (International Diploma in Cyber Security) tare da admission na daukar ta degree a
babban reshensu dake kasar Singapore, a matsayinta na (overall student). Fadin irin farin cikin da Baba Dacta ya yi ba zai fadu ba, a take ya yiwa Khalipha waya yake
sanar masa ita ma Mami ya sanar da ita tun kafin su iso Kano daga Kazaure.
Mami ta dade zaune a bakin gadonta tana mamaki, don dai akwai ‘ya’yan kawayenta da dama
a Informatics fin shekaru uku sun kasa fita daga makarantar. A karshe sai bari suka yi aka yi
asarar dubunnai. Da gaske Dr. Halima take idan har ba ta raba yarinyar nan da gidanta ba, ba
ta gama shan mamaki ba. A take ta bugawa Dr. Halima take sanar mata. Ta ce da ita kada ta damu komai ya zo karshe,
amma ta shirya gobe su wuce Plateau (Jos) tushen Mami kenan, komai ya kammala karbowa
kawai za suyi.
Don haka da suka iso ba ta yi wani action negatively a kan nasarar Rayhanan ba. Sai dai shi a
can Khalipha ya shiga damuwa, yana tsoron kada Daddy ya yarda da batun tafiya yin digirin ba
tare da anyi aurensu ba.
Don haka ranar Juma’a ya baro dukkan ayyyukansa ya taho Kano, abin haushin Daddy baya
gari ya je Ireland wani taron karawa juna sani a kan cutar Otosclerosis a matsayinsa na ganau
ba jiyau ba a kan fidarta, da aka yi aka kuma ci nasara a yankin Braemar.
Khalipha ya yi sallama a bedroom din Mami ba ta ji ba tana waya, kuma da yake ta bai wa kofa
baya ba ta ga shigowar shi ba. Hirar da take yi a wayar bai fahimceta ba, amma kawai jikinshi
ya ji ya yi sanyi da ya ji Mami na cewa, “Ko zan yi yawo tsirara haihuwar uwa da uba na
Khalipha ba zai auri yarinyar nan ba”. Ta ajiye wayar tana huci, a lokacin ne ta ankara da shigowarsa. Ta kasa saisaita fushinta ta
kasa boye anger din da ta taso mata. Don haka kallon sa kawai ta yi ba ta ce masa komai ba.
A salube ya zauna a kusa da ita gwiwoyinsa babu kwari, duk da bai san wace yarinyar ake nufi
ba tunda Allah bai nufe shi da jin an kama suna ba.
Khalipha ya san iya rayuwar Mami ba ta da makiyi, ba ta da mugun hali. To a kan wa take cin
mugun alwashi haka? Ta dago idanunta jajir ta dube shi.
Cikin kakkausar murya ta ce, “ABDALLAH!”
A firgice ya dubeta saboda shi dai tsawon rayuwarsa bai taba ji ko da kuskure ta ambaci
sunansa na ainihi ba, sai ko ranar da ta je gidansa a Abuja ta kama shi da babban laifi. Fargaba
bata barshi ya amsa ba.
Ta ci gaba da cewa, “Duk abin da kuke ciki kai da ubanka na sani, tunda ban yi kama da wadda
ba ta je makarantar boko ba. Amma ina so in ji sahihiyar amsa daga bakin ka, tunda Allah ya
hana hukunci a kan zargi”.
Ya girgiza mata kai alamar yana sauraronta. Kafin ta jefo masa tambayar tata da ta shafe
taraddadinsa.
“Wace ce yarinyar da kake so ka aura?”
Ba tare da nuku-nuku ba kai tsaye ya ce, “Rayhanah!’
Ta sake cewa, “Wane ne mijin da Dacta yake so ya aura mata?”
Ya nuna kirjinshi ba tare da ya yi magana ba wato “Shine”.
Mami ta girgiza kai, “Kai tsaye abin da zan iya cewa shine, ban amince ba! Watakila bai gaya
maka alkawarin da muka yi da shi ba kamin in yarda da zaman yarinyar nan tare da mu. Kai
kuma da fari ka munafunce ni, tunda har Abuja na taka na je saboda kai da damuwa da halin da
kake ciki, amma ka ninke ni a bai-bai, saboda ka raina min hankali. Me ka gani a jikin wannan yarinyar Khalipha ban da son zubar mana da kima da mutunci?
Kaskantaccen asali, ragowar cuta, babu iyaye babu dangi, an ce ‘yar Takai ce uwarta da ubanta
da kakarta sun rasu, to su daga sama suka fado kenan tunda basu da dangi?” Ta fidda manyan
idanunta. Khalipha tun daga kansa har yatsar kafarsa gumi yake, duk da sanyin split dake neman
daskarar da mutanen dakin. Tunda ta fara magana bai ce mata komai ba, haka da ta dire tana
sauraron jin ta bakinsa amma ya gaza ce mata komai.
Ta nuna shi da dan-alinta cikin matsanancin fushi ta ci gaba da magana, “Idan kana son zaman
lafiya dani, to ka bar maganar nan, ka kai wa ubanka maganar Radhiyyah, idan fa har ni na
haifeka na yi nakudarka bayan daukar ka cikin mahaifata har tsayin watanni tara cikin halin
kaka-nikayi. Ba ta yi isar da zan hada jini da ita ba. Wannan kawai ita ce magana. Idan ma ka je ka ce masa
ka fasa kai masa zancen Radhiyya, idan ka ki kuma kada ka ga laifina a kan duk abin da ya
biyo baya.
Kwanaki biyu kacal na baka ka je ka warware kullin naku kai da uban naka, in ba haka ba
wallahi za ku sha mamaki, na shirya karbar kowanne bacin rai na Dacta, na shirya masa kana
iya tafiya, wannan shine”.
****
Saboda gigicewa Khalipha bai tsaya kara ko mintuna biyar cikin gidan ba, ya juya kan motarshi
ya dauki hanyar Abuja.
Karfin zuciya irin ta namiji da karfin imani da tasirin addu’a su suka kawo Khalipha Abuja lafiya,
amma ba nutsuwar tuki ba.
Maganar a ce ya hakura da Rayha ma ba mai dadin ji ba ce a kunnensa, gara a soka mai allurai
dari ba daya da wannan furucin na Mami, wai ya ce da Baba Dacta ya fasa auren Rayhanah. Ta
ya ya? Ta ina? Ta wace hanya? Da wane bakin da wace fuskar zai je ya fadi hakan?”
Sai dai fa wani bangare na zuciyarsa na gaya masa, wannan fa umarni ne na MAHAIFIYA,
wanda bai isa ya musunta shi ba. Don haka Khalipha ya shiga wani irin tashin hankali da bai
taba shiga irinsa ba. Har kullum Mami da Daddy abin da suke so suke musu, don haka ba duka
kalubalen rayuwa suka sani ba. Basu san su so abu ko yaya su rasa ba balle soyayyar
zuciyarsa ga Rayhanah! Wadda yakeda yaqinin an halicci zuciyarsa ne tare da sonta, kowanne
bugunta kuma ke tafiya tareda kaunarta.
Don haka haqiqatan baima san takamaman inda son Rayhana yake ba specifically azuciyarsa,
balle yasa wuka ya yanko mata shi, tunda ya mamaye zuciyar duka, sai dai Mami ta tsigeta
gabadaya (zuciyar) daga shi har ita kowa ya huta.
Bayan kaduwa da tsorata, yana cikin mamakin ashe halin mutum yana canzawa haka farat
daya daga mai kirki da sanin ciwon kai zuwa mara kirki da tunani?
Iyaka hangensa bai ga hujjar Mami kwakkwara guda ta haramta masa abin da yake so shekaru
har takwas da doriya ba, bayan kuma ya riga ya sanar da mahaifinsa ya yi na’am, me Mami
take so Daddy ya dauke shi?
Idan ya je ya ce ya fasa auren Rayhanah? Fiye da wannan ma, ya ya rayuwar za ta kasance
idan babu Rahane a ciki? Mene ne hujjar Mami na cewa lallai sai ya auri ‘yar kawarta? Ita ba
kwadayi ba, su ba kwadayi ba, me Mami take nufi ne? Ka taba auren wadda baka taba jin kana
so ba? To ta yaya za ku rayu? Shi fa ba wai so kawai yake yiwa Rayhanah ba, har da son ya tallafi rayuwarta ya ingantata,
idan bai aure ta ba wani ne can da bai san darajarta ba bai san mutuncinta ba zai aure ta.
A yadda mazan yanzu suka mayar da aure kamar sanya riga da tube ta ga ‘ya’yan gata ma ba
marayu marasa madafa irin Rayhanah ba, wane ne zai aure ta ya daraja ta? Ya rike musu ita
irin yadda sukeso shida Daddy???
Bai yi aune ba sai ji ya yi wani ruwa mai dumi yana fita daga idonsa. Da ya kai hannu ya
sharesu, wasu ne suka kara shimfidowa aguje. Wannan karon bai yi wata hobbasa ta hanasu
zubowar ba, kyalesu ya yi suka yi ta shatata, fitarsu na rage masa suyar da kirjinsa ke yi.
A gida ko ofis, cikin kwanaki biyun nan Khalipha ya gama fita daga hayyacinsa. Ya rufe waya,
ya kasa aiki a ofis, ga shi ya yiwa Mami alkawarin barin shan Marlboro balle ya sha ta wanke
mai zuciya. Maimakon hakan ya yanke shawarar fara shan zam-zam ya zamo masa ruwan
sha. A hankali sai ya ji tunanin da yai yawa da katutu cikin kwakwalwarsa da zuciyarsa na raguwa,
nutsuwa ta zo mishi, addu’a kawai yake da nafilfili Allah ya sauko da zuciyar Mami, don dai ya
kasa aiwatar da umarninta har yau.
An debi kwanaki har hudu, Khalipha bai cika umarnin Mami ba, ya kashe waya tun dawowarsa.
Itama Rahanen baya kiranta, don baya son ya zamo heart breaker a gareta. Ko da yake dai-dai
da second daya bai taba tunanin wai zai iya hakurin da ita ba.
Mami ta neme shi a waya har ta gaji, domin tana son aiwatar da kudirinta a kan Rayha da
Khalipha kamin Daddy ya dawo ne kada ya bata mata lamari. A yau saura kwanaki biyu Dr.
Mansur ya dawo Najeriya.
Cikin daren Khalipha ya kasa barci ya kuma kasa kunna waya. Ya lura Mami so take ta zurma
shi cikin laifin shi kadai wajen Daddy ba tare da sunanta ya fito ba.
“Ya Allah me ya samu mahaifiyata ne haka? Ya Allah me na yiwa Mami da a yau ta gwammace
in sarayar da farin cikin rayuwata a banza? Saboda Rayha ta fito daga tsattson talakawa, ta yi
cuta shine kawai hujjar a ki aurenta?
Mami ta manta ita ma tana da ‘ya’ya mata? Abin da ya faru da Rayha zai iya faruwa ga
‘ya’yanta, sai a ce kada a aure su?
Ita ‘yar masu kudin me za ta yi mata? Kudi za ta ba ta ko Makka za ta kaita? A iya sanin
Khalipha Mami ta fi uwarta albashi mai tsoka, ubanta ne dan siyasa (arzikinku na dan wani
lokaci) balle ya ce wani abu Mami ke hange a kan lamarin. Yadda take daukar al’amarin Dr.
Halima da muhimmanci ba ta daukar na mijinta haka yanzu. Ta zama wata irin masifaffiya, ya
tabbata muddin ya gayawa Daddy cewa ita ta ce ya yi kaza ya yi kaza Daddy zai sa mata
katanga ma ba birki ba.
Ya kuma lura ita ma ta shirya daukar kowanne hukunci daga Daddyn idan ya tuno da
kalamanta. Wanda ba zai so haka ba, a kan nasa auren ya raba na iyayensa. Kuma ta ce duk
abin da ya biyo baya idan ya ki bin umarninta kada a ga laifinta. Wato za ta iya korar Rayhanah
daga gidanta, ta fada wani hannu da basu sani ba tunda su ba mazauna bane daga shi har
Daddy.
Wannan tunani da Khalipha ya yi ya razana shi ba dan kadan ba. Bai san sanda ya mika hannu
ya dauko wayarsa daga kan center table ya kunnata ba. Bai tsaya karanta sakonnin dake ta
tuttudowa cikin wayar ba, ya yiwa Mami text ya tura mata ya sake rufe wayar da sauri a lokacin
da kiran Rayhanah ya shigo. Kuwa riris Khalipha yake yi wanda bai taba yin irinsa a rayuwarsa
ba.
****
A lokacin da sakon Khalipha ya shiga wayar Dr. Asma’u tana ofis dinta tare da Dr. Halima suna
ci gaba da kulle-kullensu na tsiya, a kan mutanen da basu ji ba basu gani ba, son zuciya kawai
da raina talaka.
“Ya rufe wayar har yau na kasa samun shi, fargabata gobe Dr. zai dawo, so nake mu gama
kafin ya dawo kada ya bata al’amarin don na rantse zai iya yin komai don ya nuna min bacin
ransa, mafi kankantar ciki shine SAKI, ni kuma na shirya masa”.
Dr. Halima ta ce, “Wallahi kuwa, ko yau kasuwar ta watse dan koli ya ci riba. Wa zai dube ki ya
ce kin haifi Jawahir ma balle Ibrahim da Khalipha? Wallahi za ki yi mamakin yadda consultants
za su yo rubdugu a kanki. Dr. Mansur ya raina ki, ki yarda da abin da na ce, ya raina ki”.
Fuskar Dr. Asma’u ta muzanta kwarai, ba abin da ta tsana a rayuwarta irin raini. Babbar hujjarta
ta kin Rahane kenan, ta fito daga tsatson raini, abin kunya cikin kawayenta da tsararrakin yin ta.
Shigowar sakon cikin wayarta yasa ta sassauta bacin fuskarta, ta dauki wayar ta bude.
“Uwata da na sani a baya farin cikina shine nata, babban tashin hankalinta shine shigata cikin
damuwa, ko wani hali na kaka- nikayi. Mami would never lose her temper to such an extent.......
shi yasa har yau na kasa yanke hukuncin yarda da abinda idanuwa da kunnuwa na suka jiye
mini daga Mami. Ina cikin tantamar, anya Mamina ce??? A cikin kwanakin da ban yanke hukunci ba, so nake idan mafarki nake Allah ya farkar dani.
Mamina ta asali za ta iya kadar da duk abin da ta mallaka saboda farin cikinmu. Sai nake
tambayar manazarta halayyar dan Adam cewa, shin dama halin mutum yana canzawa a lokaci
daya? Tunda dai na yarda cewa ba mafarkin nake yi ba, cikin biyayyarki da umarninki na hakura da
Rayhanah..... Allah ya ba ta wanda ya fini......ki ce Amin Mami ba don ni ba sai don
kasancewarta Musulma ‘yar musulmai ‘yan’uwanmu.
Ni kuma ki aura min duk wadda ta yi miki Mami........ na yi miki alkawarin zama da ita har
karshen rayuwata! Amma kada ki yi yunkurin raba gidan nan da Rahane Mami, ko don ki ceto
mana aurenki da kwanciyar hankalin Daddy. Idan akwai biyayyar da ta fi wannan Mami ina
rokon Allah ya bani ikon yi miki. A yau zan gayawa Daddy na hakura da RAYHANAH......na
karbi zabin ki Mami. Ina neman albarkarki. Dan ki.
-Khalipha.
Ta dade tana maimaita karanta sakon dake neman karya mata zuciya, Dr. Halima na ta magana
amma ba ta