Rayuwar Raihana Part 2 Hausa Novels by Takori Kabara.pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 11

18K to 21K   out of 31.3K words

rufe dukkan
jikinta sai fuska da tafin hannu, amma ko kafafunta ba a gani, tana rike da Alkur’ani bugun Misra
tana karantawa amma ba a fili ba. Dai-dai lokacin da ladanin wani masallaci dake makwabtaka dasu ya kwalla kiran sallar
Asubahi. A yadda Mami ta nufota a fusace kamar kurar dake jin yunwa ya sata rufe Alkur’anin
da sauri ta aje gefe, tana karanto duk addu’ar da ta zo bakinta, don ta yi zaton Mami rufeta da
duka za ta yi. Bayan ita dinma bata da lafiya, adalilin duk wasu hanyoyin sadarwa tsakaninta da Khalipha sun
yanke. Baya neman ta, ita kuma idan abu ya dameta, bata iya gayawa kowa, kawai tasa a ranta
Khalipha ya gama yayinta ne dama ba aurenta zai yi ba, yaudara ce kawai irin tasu ta ‘ya’yan
gata. Ya samu wata dai-dai da shi, ita kuma ya rufe duniyarta. Wannan ciwon da Khalipha ya ji mata a zuciya, shi ya kassara ta, ciwo take a tsaitsaye duk da
bata kwanta ba. Wani bangare na zuciyar tata kuma sai ya ce, “To ai Khalipha ba shi da laifi, bai
yaudareki ba, ke kika yaudari kanki, da kika dauki dukkan amana da soyayyar duniya kika
bashi, da saninki kan cewa kina zaman ‘yar karo ne a gidansu amma kika zarme kika wuce
gona da iri, wai shine life-mate dinki......”
Wannan tunanin din dai, bai rage komi daga son da takewa Khalipha ba, sai beken kanta da
take gani. Ba ta gama tunane-tunanenta ba da mamakin abin da ya kawo Mami dakinsu yanzu
da asubahi haka kamar Damisa, ta ji Mamin ta finciko ta babu ko takalmi a kafarta.
Figarta kawai take har a kan step din bene wanda zai sadata da reception din gidan, tana

buguwa tana komai amma Mami ba ta fasa janta ba sai da ta dangana da gate.
Ta bude kofar wucewar mutum ta cillata wajen gidan tana cewa,
“Ki tafi gidan ubanki! In ya mutu ne ki nemi danginki. Ba nufina in wulakanta ki ba, amma ke kin
dauko hanyar wargaza min rayuwar iyali, kin rabani da mijina da ‘ya’yana da kwanciyar
hankalina.
Taimako ba hauka bane, Allah ya gani na yi iya wanda zan iya. Ina rokonki Rayhanah kada ki
sake waiwayen inda muke, ki je kauyenku ki yi aure ya fiye miki da ci gaba da zama cikin iyalina
kin ji na gaya miki”.
Garammm! Ta rufe kofar. Karar kofar kenan da ta razana Malam Dahiru dake sallah ya fito da
gudu ya ga shigewar Mami da kulle kofofin reception dinta da ta yi.
Sai kuma ya ji shesshekar kukan mace a wajen get dinsa. Da azama ya bude ya fita yana
haskatata da tocilan dinsa.
“Wace ce a nan?”
Ya tambaya cikin barazana, a lokacin da kwayar idonsa suka shaida wadda ke tsugunne a gefe
tana kuka.....
“Rayhanatu?”
Ya ambaci sunanta cikin kokwanto. Hawaye kadai ke zuba ta ce, “Taimakamin da kudin Motar
da zai kai ni Takai Malam Dahiru......... don Allah ba don ni ba......”
Ta ci gaba da kuka mai matukar ban tausayi.
A kidime ya ce, “Rayhanatu ba inda za ki, shigo daga nan, sai Dacta ya dawo koma mene ne ba
zan barki ki tafi ba don kin yi ma Mami laifi. Ki yi hakuri ki daina kukan ya dawo”.
Tana kuka sosai ta ce, “Malam Dahiru za ka iya bani ko ba za ka bani ba?”
Yadda ta fiddo masa manyan idanunta dake jike jagab da hawaye sun kuma kada sunyi jawur,
sai jikinsa ya hau bari.
Ya ce, “Zan shiga matsala ne Rayhanatu idan na barki kika tafi....... ki ceci hanyar cin abincina
ni da iyalina kada ki yi sanadin rabuwata da karimin mutum irin Babanku. Ita ma dai Hajiya
wane irin laifi danka zai yi maka ka kore shi? Korar ma cikin duhun Asubahi?”
Da ta ga Malam Dahiru ya tsaya ya tsinke mata da surutu mai ban haushi a gareta, ba kuma shi
da niyyar taimakon nata. Bakin ciki ya yi bakin ciki a zuciyar Rayhanah, sai kawai ta tattare
doguwar jallabiyyar dake jikinta ta yanka da gudu, gudun da ba ta taba zaton ta iya ba kamar
filfilwa a lokacin gari ya soma haske. Ko kabarin iyayenta ne ta yarda ta koma da ta kara kallon ko da get din gidan su Khalipha,
Abida da Mami, da suka yiwa zuciyarta rauni mai zurfi da ba zai taba warkewa ba.
Malam Dahiru dai girma ya soma cimmasa, ba zai iya wannan gudun da Rahane ta fyalla ba
balle ya kamata. Sai ya dau wayarsa ya kira Dacta ya gaya mishi iya abin da ya gani.
Ga mamakin Mal. Dahiru, Dacta bai wani razana ba, bai yi mamaki ko fadan da ya yi tsammani
ba, cewa ya yi da shi,
“Don me baka ba ta kudin motar ba? Hau babur dinka maza ka bita ka ba ta kudin ka yi
tafiyarka”.
Ya jefa waya a aljihunsa ya tashi babur aguje shima ya bi hanyar da ta bi wadda za ta sadata da
bakin titi.
Unguwar Lamido Crescent unguwa ce a Kano ta wadanda suka san muhimmancin BIRO (‘yan
boko). Babu ruwan kowa da kowa, ba cinkoso ba sa-ido kamar kana Abuja.

Don haka ko gilmawar motoci babu a dai wannan lokacin. Sanda Mal. Dahiru ya hawo kan titi
ya hangota can gaba da shi tana bin gefen titi sauri-sauri gudu-gudu kamar mai yin Safah da
Marwah.
Ita kanta ba ta san ina take jefa kafarta ba, fatanta kawai ta ganta a Takai, koda akan iska ne,
kuma hawaye basu bar tsere a kan kundukukinta ba tana ta sharewa da zurmemen hijabinta.
Da ta ji karar babur a bayanta ai sai ta kara artawa a guje, shima kuma ya nuna mata mutum da
inji ba daya bane, ya sha gabanta har ya dan bugeta ta fadi a kan titin.
Ya taimaka mata ta tashi ya rike hannunta gam-gam domin kiciniyar kwacewa take tana
rokonsa kada ya maidata gidan Dr. Mansur, ya tafi ya kyaleta tunda ba zai taimaka mata ba.
Mal. Dahiru ya ce, “Na rantse da mahaliccina ba zan mai da ki ba. Hau bayana in kai ki tashar
Mariri in sa ki a motar Takai”.
Kukan dai bai tsaya ba, amma ta ji sa’ida a ranta. Ta dane bayan babur ya ja suka tafi. Lokacin
gari ya fara haske misalin karfe shida na safiyar Lahadi kenan.
A tasha Mal. Dahiru ya sata a motar Tsangaya, ya sanar dasu a Takai za su sauke ta. Ya kirgo
kudin da suka bukata ya basu ta shiga gefen taga daga baya ta zauna.
Tana share idonta tana dagawa Mal. Dahiru hannu da godiya. Ya zagayo tagar da take ya mika
mata naira dari biyu da kunshin kosai mai zafi. Hannu biyu tasa ta karba, tana gode masa. Ta
share hawaye ta ce,
“Sai wata rana...... Malam Dahiru na gode a gai da Sahura”. (Matarsa).
Bai bar tashar ba sai da ya ga tashinsu, bayan motar ta cika. Shima sai ya ji danshi a kan
fuskarsa, yarinya-yarinyar kirki, me ya raba ta da mutanen kirki irin wadannan? A fuskarta da
yanayinta dai ya nuna ko yatsa kasa mata a baki ba za ta ciza ba, in baka yi mata izini ba. To
me ya hadata da Dr. Asma’u haka? Ita ma ai mutuniyar kirki ce”. Haka ya yi ta sake-sakensa shi kadai har ya koma gida ya jingine babur dinsa ya ci gaba da
harkokin gabansa.

****
[12/24/2019, 21:47] Takori: Haj. Karima wadda ta amsa sunanta (Mai Karamci) kuma uwargida
abun alfahari ga miji da iyalanta, ta yi sallama dakin da amaryar take a lokacin Inna Juma na
faman yi mata fadan ta ki shan jarkar tsumin da Haj. Karima ta kawo tun jiya.
A sanyaye Rahane ta ce, “Inna zaki ne da shi mai yawa, bama shan sukari. Baba Dacta ya ce
yana sanya Diabetes (ciwon suga), kuma yana lahani cikin hakora”.
Inna Juma ta ce, “Ciwon sukarin ya ci uwatar, mu da muka shanye fiye da jarkoki dubu ai kin
gammu a asibiti”. Ta tsiyayo a kofi.
“Ungo kwankwade ki bani kofin, don kushewar Ubanki.........”
Ita Hajiya Karima sai dariya take da jin muhawarar tasu. Ta idasa shigowa cikin dakin tana ce
da Inna Juma.
“Kyaleta Inna, da kanta za ta ce ki bata idan ta san amfaninsa, sanda za ta kwankwade jarka
goma ma ba za ta sani ba”.
Rahane ta kyabe baki ta zumbaro shi ga Inna Juma, ta ce, “Don Allah Maman Anty Nabilah
mene ne amfaninsa a lafiyar dan-adam? Zaki yana sa basir da….......”
Ai buge bakinta Inna ta yi da mafici har leben kasan ya kumbura. Da sauri Haj. Karima ta kwace
maficin Inna na shirin kara mata, ta ce

“Rufa mata asiri Inna kada angon ya ganta da kumburarren baki ya ce ya fi son ki. Rayhanah
sha kawai rabu da Inna, ki sa a ranki kawai Inna ba za ta dage ki ci abu ba, alhalin ta san zai
cutar dake ba”.
Inna ta ce, “Sanabe a gun Rahane har da na tsiya, komai ta ce yana sa kaza yana sa kaza,
komai ka yi baka yi dai-dai ba sai ta kwakulo ma illah”.
Hajiya Karima na dariya ta ce, “Inna rainon likitoci ce fa, ‘yar likita (uwa da uba) matar likita,
kinga kuwa ko ba ta shiga aji don ta koyo likitanci ba za ta iya yi miki allura ta baki maganin
kowacce cuta, ai ke gaba ta kai ki, wai gobarar titi a Jos, babu ke babu hawa layin ganin likita a
asibiti”. Haka dai suka yi ta barkwanci, Inna da Haj. Karima, Rahane ba ta tsoma musu baki ba. Cewa
take cikin ranta; Haj. Karima daban ce cikin matan gidan nan wajen saukin kai da karamci, dole
mijinta ya sota fiye da su Haj. Indo. Don ta kama girmanta, ta iya zama da kowa dake samanta
ko karkashinta da zuciya daya. Kusa da Rahanen ta dawo ta zauna, ta ciro wasu tablet din na Indonesia tana cewa, “Rahane
maza kora wadannan da ruwa, kinga yanzu za a kai ki gidanki a Kano kafin sati mai zuwa
Daddy ya danka ki hannun angonki. A sannan ne wadannan magunguna da muke takura miki ki
sha za suyi miki amfani. Ki daina mai da kanki yarinya mana, kin girma fa, aure GIRMA ne, ko
shekaru basu kai ba”.
Rahane murmushi ta yi har fararen hakoranta suka bayyana, kanta ya kumbura, don tana son
GIRMA. Tana so a ce ta girma, she’s no more a kid now!!!
Ta karbi magungunan daga hannun Haj. Karima tana dubawa, ta kasa karanta rubutun chinese
dake jiki. Ta ce cikin ranta, “How can I take drugs without Doctor’s order?” Ta karba ta hambuda
su a baki, ta boye su a kasan harshenta ta kora da ruwa.
Haj. Karima na ba da baya domin ta je ta dawo ta yi toilet da gudu ta tofo su cikin masai ta yi
flushing ta wanke bakinta. Inna Juma da ta fahimceta ta hau salati da sallallami.
Rahane ta rungumeta tana rokonta kada ta gayawa Hajiya har da ‘yar kwallarta. Ta ce, “Inna ni
ba zan sha maganin da ban san na mene ne ba, ba zan sha tablet din da ba likita ne ya yi
Prescribing din ta gareni ba”.
Inna Juma ta tureta daga jikinta tace, “Ni da Allah daga ni, ai shi kenan ke kika sani. Ana miki
gata kina iyayi. Sai ki je wa mijin salam! Ina ruwan wani”.
Da dan mamaki a fuskarta ta ce, “Inna da da gishiri kike so in je masa?”
Inna Juma ta ce, “Eh mana, ai gara ki je da dandano ko ya so ki, tunda ba kiyo kyawun Yalwati
ba, kin dauko bakar fuskar ubanki. Ko da yake yanzu kin dan fara washewa ba kamar sanda
kina yarinya ba”.
Rahane na dariya ta ce, “Inna har da cin fuska?”
Inna ta ce, “Har da cin kafafuwa kuwa, idan kika yi wasa in kwace mijin idan ya yi mini. In ta
tsuma kaina yadda zai ji ni cau!”
Wadannan languages na Inna Rahane ta kasa gane musu, kuma Innar ta ki fitowa fili ta yi mata
bayani sai dukunkune maganar take. Ta je da dandano? Ta yi cau? Sai ka ce wata abinci. May
be Inna Juma bata iya Hausa ba.
Barorin gidan Hakimi ke ta shigowa da manyan jakunkuna. Haj. Karima ta biyo bayansu ta
zauna sosai tana bude jakunkunan tana fadawa Rayhanah cewa lefenta ne a dinke.
Ta dinga daga atamfofin super da swiss lace kamar debo su akai a kasuwa ba kudi aka sa

masu yawa aka saya ba. Takalma da jakunkuna ‘yan Italy abin sai wanda ya gani. Kayan
shafe-shafe, turaruka, gyaluluwa, sabulai abin ba’a magana. Ta gaya mata cewa duk nata ne.
To abin ya fi karfin Rayhanah ta yi magana sai ido, kuma shi ta zuba mata.
****
RAHANE A GIDAN AURENTA!
A al’adar babban gida musamman irin na sarauta, lokacin bikin aure an saba gwangwajewa a
cashe ayi almubazzaranci da dukiya. Amma wannan auren na ‘ya’yan Dr. Mansur biyu
(Khalipha da Ibraheem) ya zo da sabon sauyi, ko algaita ba a busa ba, ko kwarya ba a buga ba,
haka ko guda babu wanda ya rangada. Wannan kuma ya samo asali ne da yadda auren ya zo ba cikin shiri ba, ga kuma duka
angwayen babu ko daya. Gidan bangaren daya amaryar kam sun cashe sun gwangwaje yadda
ransu yake so, an wulakanta naira. Amarya ta daura sittiru na kece raini, anyi hotuna da
sauransu. Amma a bangaren daya amaryar ba ta da wannan gatan, ba ta ma sa-aka ba, ba ta ma kuma
da wanda za ta gayyato a duniya idan ba Jawahir ba, ga shi kuma watakila har abada ba za ta
koma inda Jawahir din take ba, da aminiyarta Azizah.
Sannan ‘ya’yan Hakimi da yawa da sauran matansa basa farin ciki da aurenta da Ibraheem
saboda Nabilah. Don haka ko taron wuni ba kowacce ce ta zo ba, wannan bai damu amaryar
ba, balle danginta da suka zo rakata gidan mijinta daga Albasu, Takai da Tsangaya
dukun-dukun da su, bayan su a wurinsu sun kure adaka. Hakimi da kansa yana gaban motar Dr. Mansur wanda ya zo daukar amaryar da kansa, a bayan
motar Haj. Karima ce, Inna Juma (wadda za ta zauna tare da ita) da Zinaru da babbar ‘yarta
Hansai. Bai tsaya ba sai farfajiyar wani matsakaicin mansion mai rufi ruwan kasa da fenti ruwan
madara. Guda biyu ne a jere amma cikin get daban-daban a unguwar ‘Farm Center’ dake
bayan shagon Kasa (Country Mall).
Babu yawaitar jama’a a unguwar babu cinkoso, yawanci ma duk gidajen ma’aikatan gwamnati
ne da sababbin gine-gine da aka fara ba a karasa ba. Sai kamfanoni da shaguna sababbi
wadanda ba a fi shekara da bubbude su ba.
Hannun Rahane cikin na Baba Dacta har dakin barcinta, cewa yake
“Da a Takai gidanki yake, a kan doki zan kai ki Rahane. Shiga gidanki kina mai neman aminci
daga Ubangijinki, ta hanyar cewa “Assalamu Alaikum”. Shiga gidanki cikin neman dukkan
alkhairan dake cikinsa, ki nemi tsari daga sharrinsa. Ta hanyar shiga da kafar dama.
Ina rokon Allah yasa mutuwa ce kadai za ta fitar dake din-din-din daga gidan mijinki, ita ma din
ina fatan ta dauke ku tare. Amma fa bayan kun bar min jikoki, tattaba kunne da uhm-hm-hm”.
Hakimi murmushi ya yi ya ce, “Har da uhm-hm-hm Mansur? Anya baka zarmewa duniyar ba?
Kana da hamsin da bakwai yanzu, amma kana neman wasu sittin a nan gaba?”
Dr. Mansur ya ce, “Yaya Abdulkadir ina son tsufa mai tsaho, tsufan dake da sanyin idaniya
(‘ya’ya da jikoki da tattaba kunne) dadi ne da shi, musamman idan suka baibaye ka suna jan
farin gemunka......... Hurry Rahane....... yearly! (wato tayi sauri duk shekara ta kawo jika)”.
Kowa dariya yake banda Rahanen, wadda take jin ina ma kasar ta tsage ta shige cikinta da
kunyar wannan magana da Baba Dacta ya yi. Ta sake kudundunewa cikin mayalwacin
mayafinta.
Doguwar addu’a Hakimi Abdulkadir Balarabe Sardauna ya ja aka shafa. Rahane ba ta tashi

tsinkewa da kuka ba sai da suka sa kafa suna fita daga dakin, bayan sun gama yi mata tofin
albarka.
Da gudu ta mike ta bi bayan Baba Dacta ta kama kafafunsa tana kuka sosai ta ce,
“Allah ya fini sanin alherin da ka yi mini. Don haka shi nake roko ya saka maka da fiye da shi.
Ina rokon ku idan na taba bata muku a shekarun da muka yi tare Baba Dacta kana gina
rayuwata positively… ka dubi Allah ka yafe mini, ka daina fushi da Mami a kaina don Allah
Daddy.......” Ta ci gaba da kuka mai keta zuciyar duk wani mai birbishin imani a zuciyarsa. Hannu biyu yasa ya dagata, “Bari kukan nan haka Rayhanatu bana son shi, in ma kin min laifin
ai afuwa ce har kullum tsakanin Uba da dansa. Guda dai-dai har dubu malala gashin tunkiya, na
yi miki ita Rayhanah, na yiwa Mamin ki, ban taba riketa da komai ba a kanki, sai ajizanci irin na
dan Adam. Ni na gaya miki WATARANA na zuwa da Asmau da kanta za ta goya ‘ya’yanki, MADALLAH! Da
zuciya mai tsafta irin taki Rayhanah!!!” Da sassarfa ya wuce ya bi bayan Hakimi. Don baya so
taga kwallar data sauko daga idaniyarsa.
Inna Juma ta bisu ta rufe kofofin gidan suka gaisa da maigadin Buzun Nijar ne. Ta dawo ta
kama hannunta suka koma dakin barcinta tana lallashinta.
Ta ce, “Gani ni dake zamu yi zaman mu, zama mai dadi cikin kwanciyar hankali har Allah ya
kawo mana angonmu lafiya. In kika yi sakwa-sakwa sai in kwace shi”.
Ta ce, “Daga ido Rahanen Yalwati, mai sunan Yalwati ki sha kallon gidan mijin da Allah ya baki”.
Ta yaye mata lullubin gaba daya ta nuna mata wani dan karamin hoto cikin dan ‘frame’ din dake
kan durowar gadonta. Ibraheem ne

7 / 11