Diddigar Kaya 1&2 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Complete Novels

Chapter   9 / 29

24K to 27K   out of 86.8K words

ki waye pls"

"tir da wayewar zina da shaye shaye, kun kuwa san azaba da fitinar dake cikin waennan abubuwa?"

Kallon juna sakina da rahama suka yi kan suka washe da dariya, sakina tace
"lallai ashe ?ar gidan malamai ce"

Tafiya tayi gaban kayan ta ta fara HaWawa ba tare da tace komai ba.

"HaWa kayan me kike? Cewar rahama

"gidanmu zan koma."

"Amma ai sati guda muka ce zamu yi"

"ba zan yin ba".

Tunda ta fara basu amsa a haka sun san in suka cigaba be gameta ba su samu gagarumin matsala se suka kyale ta.

Knocking aka yi, Raham taje ta buWe, samarin guda uku ne, duk suka janye en matansu suka bar ta ita da Zubair a Wakin.

Gabanta yaje ya durkusa bisa gwiwowinshi, cikin lalama yace
"am very sorry! Na san ban kyauta miki ba amma wallahi ba da wani mugun nufi na baki ba, na zata kina sha a lokacin ne kawai ba kiyi niyyar sha ba shiyasa na baki don na tsokane ki, zuciyata zafi take min ina ganinki cikin wannan yanayi Fauxa, na tuba please"

"leave me alone zubair"
Ta faWa calmly Dukda fuskanta a mugun haWe yake.

Kanshi ya du?ar daidai kafafunta sai digar ruwa taji.

Da sauri ta Wago, a take yayi deceiving Winta da crocodile tear Winshi yace
"am sorry please Fauza"

Tace
"Abunda ya faru ya riga ya faru"

"Kin yafe min?"

Ya tambaya cikin murmushi da yayi mata kyau, kanta kawai ta mayar kan wayanta, hannu ya sa a aljihu ya ciro wani box me kyau daga idanu zaka san ba karamin kuWi ya ci ba yace
"accept this as my apologies dear"

?agowa ta sake yi ta kare mishi kallo, ba laifi Zubair kyakyawa ne, sai de kallo Waya zaka mishi ka san crook ne, ga kuWi ga iskanci.

Hannu ta sa ta karSa ta buWe, kasa Soye excitment Winta tayi tace
"isn't it that necklace..?"

Wadda take kallo jiya har yake cewa ze mata kyau.

Murmushi ya saki ganin ta saki ranta, ta mishi godiya.

Zama yayi a gefenta suna hira jefi jefi, duk yadda suka so su hanata tafiya a washegarin tace ita sam gida zata koma.

Duk abunda take chan Kasar zuciyarta bakin ciki ne fal na kayan maye da ta sha, ga sallar asuba gari ya gama wayewa, se istigrafi take yi haka dae Zubair yayi ta lallaSata yana yaudararta bata yi wani fushi mai nisa da shi ba..

Washegari da safe da kanshi ya kaisu har Airport ya mata sayayya mai yawa ya hada da kuWi, duk da ya burgeta, sai de fa bata nuna ba.

Sauri sauri ya shigo Airport Win don shi ze tu?a Max Air Win zuwa birnin Yola daga Abuja, gashi ya so yayi letti, a cikin jirgin ya haWu da sauran crew Win da kuma wadda ze taimaka mishi suka gaisa, he supposed to be a mazauninshi tunda har an soma shiga amma se ya tsaya daga bakin kofan, waya yake amsawa lokaci lokaci ya kan Waga idanunshin nan ya kalli masu shigowa Waya bayan Waya.

Gudu gudu suka karaso don ana final announcement ne, Sakina ce a gaba sai Rahama kan ita, loggage Winsu bai da nauyi so kowacce na ri?e da nata ne a hannu, Sakina ce ta fara wucewa ta mika ticket Winta, aka bata na seat number Winta ta shige, rahama ma ta shigo tayi hakan sai Fauza ta sanyo kafafunta cikin jirgin....

*Toh Alhamdulillah! Free pages sun kare saura ni daku da kuka biya paid, na san kaunar da kuke yiwa labarin ne ya saka ku nuna wannan soyayya sai dai har yanzu ina kara jaddadawa ba zan san kuna kaunar littafin ba idan har baku comment, ni karan kaina ba zan ji kwarin gwiwar yi muku typing Win ba due to squeezing time kawai nake nake yi don ina aiki, bani da enough time na kaina, sannan typing in kun ga kun samu da rana to shikenan amma ka'ida sai dare in shaa Allah zan din ga yi don nafi samun time between magrib, isha. Looking forward for ur comments and love>?p?=?O?



DIDDIGAR ?AYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuWi ne..
Ze zo muku a Naira Wari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taSa nadama ba>?p?

Karku sake a baku labari.


=???Gureenjoh=???
D?

12

Daidai tana sanyo kafa shi kuma yana Juyawa, an tambayeshi wani code da se ya duba paper Win don be ri?e ba, har ta gama ta wuce seat Winta chan karshe be dawo ba.

"Ke kinga wani haWaWWen captain da ya tafi da ni? Wlh ya haWu karshen haduwa ina ma zan samu ko phone number Winshi ne"
Rahama dake kusa da ita ne ke maganan cikin koWa kyaun wadda take magana a kai da ita bata sani ba.

Tace
"ni ban ga wani captaina ba, kuna da matsala ai ku kam"
Ta faWa jin sakina ma ta karSa tana taya rahama gulman wadda bata gani ba ita kam.

Har suka sau?a yola basu daina maganan captain Win nan ba, Sakina Dan Tsoho hotel tayi don chan zata karasa satin da tace zatayi a gida, yayinda rahama tayi gida don duk iyayenta basa ?asar, cab ne ya sauke ta kofar gida ta sauka tare da mi?a mishi kudinshi ta Janyo loggage Winta tayi ciki.

Harabar gidan nasu tsabtsab ba kowa ta tabbatar yanzun haka suna school tunda kwata kwata karfe goma ne na safe, sashen jadda tayi direct a parlor ta taddata kan sallaya ta idar da walaha tana tasbihi, da gudu ta zo ta faWa jikinta tayi shiru tana sauke numfashi.

?ago fuskanta Jaddah tayi cikin farin cikin ganinta tace
"oyoyo oyoyo! Maraba da mutanen Gombe kune da safen nan?"

Kai kawai ta gyaWa ta sake mayarwa tayi lamo, Jaddah ta Wago ta gabaWaya tana kallonta
"lafiyan ki kuwa? Ko baki da lafiya ne kike hawaye?"

Hannu ta sa ta share kwallar tare da karya wuya tace a shagwabe
"kewarki nayi Jaddah na"

Dariya Jaddah tayi tace
"to ba gashi kin dawo ba? Ba shikenan ba? Oya tashi je kiyi wanka ki sauya kaya bari na sa zaliha ta sama miki abunda zaki ci"

Mikewa tayi ta nufi Wakinta tana cewa
"ya yi yaji pls"
Tana shiga ta jefar da Akwatin tare da dogon hijab da daga Airport ta sanyo shi zuwa gidan, ta shige toilet ta sakarwa kanta ruwa tana lumshe idanu, se yanzu take jin wani sukuni na rufe ta, lallai ta zalunci ahalinta tayi fatali da tarbiyar gidansu, tunda ta dawo daidai take jin rashin daaWi a zuciyarta na abunda ta aikata amma fa wani zuciyar na kwaWaita mata daaWin shi.

Bayan ta fito tayi shafe shafenta ta janyo tsarabar da Zubair ya HaWa ta dashi, chocolates ne daban daban se wasu designers perfume guda biyu se, hoodie ash na kamfanin Fendi.

Boyesu tayi a wardrobe Winta kan ta zaro riga ?arami fari da wando navy blue ta saka, wandon a kaurinta ya tsaya ya kuma matse ta ya fitar da duk wani shape Winta, gashinta ta taje ta sake shi, tana shirin kwanciya Call na Zubair na shigowa wayanta, da sauri taje kofa ta rufe da key kan ta dawo ta haye gado tare da shigewa bargo ta amsa.

A hankali suke waya tun bata saki jiki ba har ta sake saboda ya iya hira da sanya dariya ga kalamai, ta shagala sossai se jin bugun kofa tayi da sauri ta ce mai tana zuwa ta kashe wayar tare da boyeta cikin Rigan pillow ta dirka taje ta buWe kofan.

"Jadda tace ki fito ki ci abinci kar kiyi bacci baki ci ba"
Cewar zaliha.

Bayan zaliha ta bi suka fito tare, kan kujera ta zauna bayan ta Wauki abincin daga cikin tray da zaliha ta shirya ta fara ci, Jaddah na bata labarin irin kewar ta da suka yi gidan yayi shiru sossai a kwana biyu da bata nan.

"Ashe ana kewata amma in ina nan kowa ya buWe baki Fauxa kaza Fauxa kaza!"

Jadda zata yi magana wayanta ya fara ruri ta duba tace
"oh kai kuma se yau ka tuna dani"
Ko bata faWa ba Fauxa ta san waye don haka ta maida kanta kan TV Dukda wa'azi ne gwara ta ji da ta ji zancen da zasu yi.

Bata san ma jaddar ta kashe ba saida taji tana cewa
"Fauziyya yi sauri gama ki je ki sharewa Yayanku Waki ki wanke mai toilet yadda kwana biyu be zon nan ba na tabbatar yayi kura kuma kin san shi da rashin son datti, yace min ya shigo garin gida ne dae ze Wauki mintuna masu yawa kan ya karaso akwai abunda ze yi"

HaWe gabas da yamma tayi kaman zata yi kuka tace
"Jaddah ina Fatima da ni zan mishi aikin Waki yau? Allah ya kyauta wlh kin dae san kap rayuwata ban taSa taka kafa Wakin shi ba haka kawai ba zan fara yau ba..."

"Fitsararriya ajiye abincin nan ki wuce kan in HaWaki da abincin in take"
Cewar baba Alhj da yake shirin shigowa sallamar da ze yi ma be yi ba sbd abunda yaji Fauzar na faWawa Jaddah.

Da sauri ta mi?e tsaye
"ban hanaki saka waennan kayan ba?"

Da sauri ta wuce Waki tana tura baki seda ta shiga ta fara kunkuni, kaman zatayi kuka haka ta sanya hijab kato har ?asa ta fito, ta samu baba Alhj na cewa Jaddah

"Mama ni fa ba tsanar ta nayi ba, halayen ta ne bana so, a yadda Fauziyya ta Wauko rayuwarta wlh bata so gamawa da duniya lafiya ba, tun da ta sanya kafa ta bar sashena bata sake zuwa ko da gaisheni bane wai dani uban ta zatayi gaba? Har Fauziyya ta bar garin nan bata iya zuwa ta min sallama ba se a bakin mamanta nake ji?"

Kanta ?asa tace
"key!"

Jadda tace
"Kin san inda nake ajiyewa ai"

?akin Jaddar ta wuce ta Wauko ta zo ta fice jin Jaddah na bashi hakuri ta kuma tabbatar mishi da ta tura ta ta mishi sallama saide kila zuwan ne bata yi ba, zata mata faWa Adu'a da lallashi Fauza ke bukata ba faWa da duka ba.

Ita kam ta wuce abunta, ita fa a yanzu mahaifin ta bata san wani baabi ta saka shi ba, dukda tana son shi sossai da sossai saide wannan kiyayya da yake nuna mata yasa itama take jin babu ruwanta da shi (Subhanallah).

Direct Wakin Faizan ta wuce, a hankali ta tura kofan bayan ta murda key Win, kamshin room freshner da na turarukanshi ne suka bugeta, inda zata iya jinjina mishi kenan tsabta da kamshi, komai tsab tsab yake a Wakin Sam babu tarkace kaman ba Wakin namiji ba.

Gado ne a Wakin saSanin sauran Wakunan samarin gidan dake da katifa, daga gaban gadon akwai set na kujeru se TV manne jikin gini, daga gefe akwai Wan corridor inda drawer Winshi yake se kofar toilet, bedding ta fara cirewa ta chilla cikin kwando wankin dake gefen wardrobe Winshi tare da Waukan tsintsiya ta fara aikin Wakin, tana yi tana mita da masifa wlh ba don jadda ba da abunda zata mishi a dakin nan se ya kusa kasheta, sannan itama yanzu tana son lafiyar fatarta inda Allah ya taimake shi kenan.

Tsab ta share Wakin ta gyara tare da kunna burner ta sa turaren wutar da ta gansu kan dressing mirror Winshi masu kamshi irin na asalin Maiduguri, ta kunna Ac take Wakin ya Wau kamshi, bayi zata shiga se ta cire hijab Winta ta ajiye kan cushion kan ta wuce bayin, komai tsabtsab, wankewa tayi tana yi tana masifa, haka dae ta gama ta nufi fita.

Tana sanyo kai Wakin shima yana sanyowa, a kan junansu idanunsu suka fara faWawa, wani irin disgusting look na me kike min a Waki ya fara watsa mata, ita kuma se ta so rikicewa don ko yaya Faizan na da wani kwarjini da babba ma se ya ji wani iri in ya zuba mai idanun nashi bare mace karama irin ta.

Bata saba gaishe shi ba don haka bazata fara yau ba, wucewa Tayi ta Wau hijab Winta zata sanya, se lokacin ya tuna abunda ya gani a Abuja don haka kai tsaye hannunta ya fara bi da kallo, kan ya maida idanunshi kan body shape Winta da ya bayyana sossai a wandon kaman yadda ya bayyana a wanchan kayan da ya gani, daga karshe ya kai kan gashin kanta daidai lokacin ta gama sa hijab tare da nufan kofa.

Kai tsaye yace
"Ke!"

Chak ta tsaya, ya fara takowa gabanta hannunshi zube bisa aljihun wandon shi.

"Ke! Sa gwiwowinki a ?asa"

Da sauri ta kalleshi kaman zata fashe da kuka tace
"Amma me na y...."

?as haka ya buge mata baki da sauri ta dafe bakin yace
"kin yi abunda nace ko se na tattaka ki?"

Da sauri tayi kneeling ranta duk ya gama Saci wani tsanar shi na sake mamayarta.

Shi bai damu da ita ba don haka be damu da ko ta gaishe shi ko bata gaishe shi ba, clearing thoughts Winshi kawai yake son yi..
"Me ya kaiki Abuja?"..

Rassss haka gabanta yayi wani irin mummunan faWuwa, hannayenta suka soma rawa, bata Wago ba don tana Wagowa firgicin idanunta tsab ze bayyana rashin gaskiyarta.

"Don't let me repeat myself... Uban me ya kaiki Abuja? Me kika je yi a Transcorp Hilton?"

GabaWaya wani irin zafi ne ya rufe ta kaman an sanya ta cikin Kasar tukuban tsire
"A...abu...ja kuma?"

Be yi magana ba, tace da sauri
"ni babu abunda ya kaini Abuja, ban je Abuja ba"

Duk yadda ya so ya firgita ta ta faWi gaskiya be samu nasara ba sbd ta kafe kai da fata ita bata je Abuja ba.

Tsaki me karfi ya ja yace
"get out of my sight"

Da sauri ta mi?e tayi kofa ya sake cewa.
"Ke!"

Chak ta tsaya, yace
"this is the last time da zan ga waennan singallin kafafun naki a Wakina bana son harka da kazamai kin gane ko?"

Kai ta gyaWa wani irin takaici na zuwar mata wuya, duk Jaddah ce ta ja mata.

Da sauri ta fice tayi sashen Jaddah kaman zata fashe don fushi da tashin hankali.
Taya aka yi Ya Faizan ya ganta a Abuja? Allah ka rufa min asiri.
Ta furta tana me shiga parlorn Jaddah har zata wuce jadda tace

"Fauziyya"
Dawowa tayi tana amsawa ganin jaddar is serious.
"Fauziyya kin san girman iyaye ko? Kin kuma san saSawa iyaye kaman saSawa mahallicci ne ko? Sannan kina gani irin yadda mahaifanki basu saSa mini ba meyasa kike shirin daukar wani hanyar saSa musu alhali ban koyar dake ba?"

Raurau tayi da idanu tace
"me nayi kuma Jaddah?"

"Meyasa zaki yi tafiya baki sanar da mahaifin ki ba? Ba wannan ba meyasa tunda kika dawo nan baki je kin gaida shi ko sau Waya ba? Kina son ganin haske a rayuwarki? Ya kamata ace kiyi nadama ki shiga alhini akan korar da yayi miki a sashenshi amma Fauziyya duk babu? Ko don kinga kina dani? Har fa rashin lafiya mahaifin ki yayi cikin wata biyar din nan ashe baki je kin gaishe shi ba?"

Bakinta kaman ze taSa gini tace
"amma Jaddah kina ji yace ko ganina baya son yi, taya zan kai mishi fuskar da baya son gani da sunan gaisuwa?"

"Fauziyya!"
Jaddah ta kirata ranta na Saci.

Hawaye saura kiris ya zuba mata, dama bata dawo ba da wannan damuwar da ta dawo ta riska kuma.
"Naji jadda zan gyara yanzu kullum da safe kan in tafi makaranta zan je in gaishe shi ba shikenan ba? Kin turani Wakin wanchan ya wulakanta ni kin huta!"

Tana kai nan ta tashi ta wuce fuuuu, girgiza kai Jaddah tayi tana furta
"Allah ya shirya Fauziyya"

Ita kuwa tana shiga ta rufe Wakin tare da yin wurin pillow ta dauki wayanta ta kira Zubair, shagwabewa tayi tana faWa mishi abunda Faizan yayi mata.

Lallashinta yayi tayi, dukda duk sun sha mamakin yadda aka yi ya ganta, tace ita bazata kara tafiya wani garin ba kuma amma shi Zubair ya tabbatar mata akwai hanyoyi dayawa da zasu bi ba me ganinta.

Satin Faizan biyu aka sanya bukin su da Fatima nan da wata biyu, sbd har sun fara waec.

A take duk bangarori aka fara shiri, ita dae Fauza kaman bata san ana yi ba harkokinta kawai take, ko da Fa'iza ta zo mata da maganan anko ma kai tsaye tace bazata yi ba, su karata chan daga Amaryar har Angon babu abunda ya HaWata dasu..

Jadda ce ta bada kuWin nata, Zubair ne yake shirin zuwa Dukda ta ?i ya ki, wai yayi missing Winta Dukda sukan yi waya, su yi video call duka.

GabaWaya ya lalatata da soyayyarsa, a gefe Waya babu abunda ya sauya daga abubuwan da take yi sai giyar da bata sake sha ba tun daga ranar da abunnan ya faru.

Babanta kuwa ta kan je kullum ta gaida shi, iyaka abunda ke hadasu kenan, wurin mammi ne take girke girkenta hakan ya sa mammi fahimtar abubuwa dayawa daga gareta, har yau bata manta wayar da suka yi da Faizan ba, hakan yasa lokuta dayawa ta kan ja ta da nasihu kala daban daban wadda ya kan kashe mata jiki amma daga ta bar sashen shikenan.

Faizan ya koma bakin aikinshi inda ya HaWa Fadila da haWe haWen kayan aure, dukda ta ce bazata samu zuwa ba sede zata turo ta jirgi se ya karSa.

Wasa wasa buki ya ?arato, Amarya da mahaifiyarta ana ta shiri, mutanen Maiduguri sun cika gidan kai ka ce bukin farko kenan a zuri'ar, ba karamin takura Fauza suka yi ba Dukda ta tsaya kai da fata tace babu me saukar mata a Waki bukin munafuka da azzalumi, hakan ko aka yi sbd gudun jarabar ta babu wadda ya sauka a Wakin nata.

Walima, saukar Qur'ani se reception wadda maza ne kawai zasu yi bayan Waurin aure aka shirya kaman yadda ake kowani buki a gidan.

Zaune take kan dressing mirror hannunta ri?e da waya tace
"ka fa san irin gidan da na fito Zubair, yanzu in bar gidan nan in same ka hotel kana Tunanin babu wadda ze fahimta?"

Yace
"ni dae ki san yadda zaki yi, Haba sweetheart in taso tun daga Abuja in zo har Adamawa don ke kaWai abinda zaki saka min da shi kenan? Ganinki ma yayi min wuya?"

Tace
"kayi hakuri! Zan san yadda za'a yi na fito"

Yace
"ko ke fa, ina Green land"

Tace "Toh"

Tsab

9 / 29