Diddigar Kaya 1&2 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Complete Novels

Chapter   22 / 29

63K to 66K   out of 86.8K words

mi?e taje jikin window se ta hangi motar shi na fita, ajiyar zuciya ta sauke ta dawo ta zauna da gaske fushi yayi? Ta tambayi kanta don ba zata Iya tuna sadda ya fita be gayamata ba tunda suka Wan fara shiri.

Gari yayi haske taje tayi wanka ta zo ta shirya cikin jalbab Winta dogo har ?asa don tana da lectures, fitowa tayi bayan ta sha cereal ta zuba chocolates masu yawa a jakan bayanta, Fatima ta gani zaune tana karyawa.

Kaman ba zata mata magana ba se kuma tace
"mun tashi lafiya?"
Ko kallonta Fatima bata yi ba, zama tayi tana jiran ta ko don ta san tana jiran ta ne ita kuwa ta fara jan lokaci, ganin zata Sata mata lokaci har a shiga lectures yasa ta mi?e ta fice.

Mai gadi ya gaida ta yana buWe mata gate ta taka da kafa har ta samu taxi ta Wauki shata ta wuce school.

Se karfe huWu ta dawo gidan nan ma da taxi don bata ga Fatima ba, Seda tayi sallah ta zo ta shiga kitchen ta fara girki sanin itace yau da girkin, tuwo tayi mishi na doya da miyar Wanyen kifi bayan ta gama taje tayi wanka tare da sallar magrib ta shirya cikin kananun kaya, ba karamin kyau tayi ba tayi isha kan ta fito ta zauna a parlorn saman Dukda bata ji motsin shi ba.

Se a lokacin Fatima ta shigo basu tankawa juna ba, ita dae Fatima ganinta yasa ta san bata san mijin da ake yiwa kwainanen baya ma ?asar ba, dariya ta sheke dashi tana cewa
"lallai kuwa za'a yi jiran gawon shanu"

Tana kai nan tayi wucewarta ciki, ganin har karfe tara be shigo ba yasa tayi Tunanin ko baya ?asar, ranta dae ba daaWi kaman yadda tun safe yake har Afnan take tambayarta tace babu komai, yau gabaWaya abu mai nauyi be shiga cikinta ba, tuwon ta dibi Wan kaWan ta ci kan ta tattara taje ta adana a frigde daga nan ta haura tayi shirin kwanciya ta kwanta.

Washegari bata yi breakfast ba miyan kifin ta yi microwaving ta ci da bread, yau ma bata jira Fatima ba tayi ficewarta yau ma dae haka ta kashe ranar da tunani, lectures Win ma bata wani fahimta..

A kwana na ukun har kuka tayi, ta rasa gabaWaya me ke damunta da fushin shi, da a gidansu ne da yanzu in duka ne an daketa an wuce wurin amma shi ba duka ba zagi kawai ya Sace mata ba tare da ta san inda yayi ba alhali yana fushi da ita.

Hadari ne sossai ya haWe garin har ana iska, Afnan ta riga ta wuce ita kuma tana tsaye tana neman taxi da sauri ta sanya hannu ganin motar Fatima amma ko bata tsaya ba tayi wucewarta kuma ta tabbatar ta ganta ba bata ganta ba, da kyar ta samu wani taxi Dukda ya tsula mata kuWi bata damu ba ta shige da sauri sbd ita bata son ruwa ya taSa ta, ko yaya ya ji?ata se tayi mugun zazzaSi.

***

Karfe shidda ya iso gidan yayi parking motan shi da dama Airport ya kan bari yayi tafiyar shi, Gaisawa suka yi da gate man kan ya wuce ciki yana kallon motar Fatima dake nuna alamun bata jima da shigowa ba.

Gidan ya shiga yana jin wani kewa chan ?asan ranshi da duk yadda yayi kokarin dannewa ya ?i dannuwa, lumshe idanu yayi ya buWe a sadda ya shaki sassanyar turaren wutan da ta kan yi anfani dashi wa gidan, a natse ya haura yana jin yadda aka tsuge da ruwan kaman da bakin ?warya.

?akin Fatima ya fara shiga tana ganinshi cikin farin ciki ta tare shi tana mishi sannu da dawowa, ya amsa fuskanshi a sake kan yace bari ya duba Fauza se yaje yayi wanka.

Tace
"Ai ina ga bata dawo ba fa..."

"Bata dawo ba?" Ya watsa mata tambayar cikin mamaki.

Kanta ta mayar ?asa tace
"eh bata dawo ba don ban ji shigowarta ba"

Yace
"ban gane ba, ina ce tare kuke tafiya ku dawo? Ya aka yi ke kike gida ita bata nan? Me ze ajiye ta a waje har an yi magrib?"

Tace
"ni dae wlh ban sani ba, abunda na sani dae tunda ka tafi bata sake tsayawa mun tafi tare ba taxi take fita ta hau haka dashi take dawowa Dukda nayi kokarin jan hankalinta akan baka son Wabi'ar shine ma musababbin da yasa ka saya min mota amma taki saurare"

Be tanka ba sbd yadda ya sake jin sabon Sacin rai na rufe shi a kanta, duk yadda yake kokari akan yarinyar nan me yasa take so ta fara bashi matsala? Sau nawa ya gayamata baya so matarshi ta hau taxi? ?akinta ya wuce kamshin ta na tashi a Wakin wadda ya dawo mishi da sabon kewanta kaman yadda ya kashe kwanaki biyun cikin kewar nata ko abincin kirki bai iya ci.

A balcony Winta ya tsaya dake shine ke facing gate, ya rasa hukuncin da ya kamata ya Wauka a kanta, sheWan ke ta wassafa mishi kila tana chan da Zubair tunda har ta fara ambatarshi, hangar taxi yayi ya sauke ta, ba lema hannunta hakan yasa cikin hanzari ta iso gate Win ta fara bugawa saide gate man Win kaman baya kusa don baya jinta, ta kai mintuna biyu tsaye cikin ruwan tana knocking da ?arfi sede ?aran ruwa ya hana gate man Win ji, ya so ya kyale ta ruwan yayi ta ji?ata se kuma ya ga baze iya ba.

Da sauri ya juya ya nufi fita ganin ta juya itama ta bar gate Win da sauri sauri, da hanzari ya buWe gate Win ya fara duba ta, chan ya hangota tana tafiya tana dube dube ko zata samu inda zata fake kan ruwan ya tsagaita..

Sam bata san da isowar mutum ba se ji tayi an Waura mata wani suede me kauri wadda a take ta dena jin Sau?ar ruwan jikinta, a hankali ta Waga kai se suka HaWa idanu ruwan na zuba a jikinshi sossai.

"Yaa..."
Be bata daman magana ba ya ri?o hannunta suka juya suka yi gida, a kofan Wakinta ya saketa ba tare da ya bi ta kan suede Winshi ba ya shige dakinshi.

Ta Wan jima tsaye a wurin kan ta shige ta cire suede din ta ajiye ta wuce toilet ta cire kayanta da ya jike gabaWaya ta hada ruwa me zafi sossai tayi wanka, a Wakin ta HaWa tea me kauri da zafi ta sha jin jikinta ya fara rawa alamar zazzaSi.

Da kyar ta iya gabatar da sallah kan ta hau gado ta ja bargo ta shige tana rawar dari.

Yayi wanka shima ya sauya kaya ya fito ya duba Fatima yace ta sama mai wani abu marar nauyi don yana jin yunwa, ranta fal farin ciki sanin yayi fushi da fauza ne tunda girkin ta ne amma ya saka ita tayi mishi.

Kitchen ta shiga ta sama mai abinci yana zaune a parlor yana kallon Tvc news ta shigo ta ajiye mai, kallon kofan Fauza yayi kan ya maida kan abincinshi ya fara ci yana Tunanin me ya hanata fitowa ta nemi wani abu ta ci?

Har ya gama ci suna tare da Fatima, tana ta kokarin jan hankalinshi sede idanunshi ne kawai gareta, tana tattare kwanukan ya mi?e ya nufi Wakin Fauza Win.

Kwance ya tarar da ita tana rawar Wari sossai, yaye bargo yayi ya taSa gefen wuyanta wani irin zafi jikinta yayi da har yayi saurin zare hannunshi, da kyar ta buWe idanu ta kalleshi..

Harara ya zabga mata, kan yayi tsaki ya wuce toilet Winta towel ya samo da ruwa ya zo ya karasa yaye bargon yana Wauke idanunshi daga kan santala santalan cinyoyinta da suka bayyana, Wagota yayi ya fara saka Towel nan a ruwa yana shafa mata, wani irin numfashi take saukewa wadda ke rikirkitashi ganin ruwan baze Sau?ar mata da zazzaSin ba gashi ta fara mishi kananun kukan fita hayyaci ya sa ya rufe ta da faWa don abubuwa dayawa ne suka haWu mai.

Sossai yake mata faWan abubuwan da ta aika ta Win, harda taurin kanta take shirin dawo mai dashi to baze Wauka ba, shi ba lusarin namiji bane da ze ke gindaya mata sharudda tana tsallakewa he could remember vividly yadda ya gayamata baya so matarshi ta hau taxi amma me ta aikata? Har tana tuna wani katon gardi Wan shaye shaye cikin gidanshi.

A hankali ta sabule daga hannunshi da yake rike da kafadunta ta faWa jikinshi tare da kankameshi tana kuka kawai don bazata iya magana ba.

Tsit haka maganan ya yanke mai, ya sanya hannu ya tarbeta, fuskanta take ta gogawa bisa kirjinshi alamar tana kara fita hayyacinta ne, da sauri ya kwantar da ita ya kashe wutan Wakin tare da zare jallabiyar jikinshi, ya saura daga shi se boxer, Rigan jikinta ya cire mata don bata taimakon body contact kan da safe su tafi asibiti.

In a romantic way ya sanya lallausar hannunshi ya Wagota a hankali ya kwanta kan yayi mata masauki a faffaWar kirjinshi, a tare suka sauke nannauyar ajiyar zuciya, mannewa ta sake yi ta shige jikinshi kaman zata tsaga shi ta shiga ciki sbd sanyi da taji jikin nashi na dashi wadda hakan ya bashi daman sake kanainayeta ya cusa fuskanci tsakanin wuyanta yana sauke numfashi me nauyi, cikin wani irin salo yake shafa mata sajen nashi a hankali hankali cikin wuyanta, siririn ?ara ta sake tana kara kankameshi jin ya saka babban Wan yatsan kafan shi yana wasa da tafin kafafunta, duk su biyun sun haukace da wannan masifaffen body contact da suke samu, shi da yayi da niyar taimako ma ya fi azabtuwa.

Hmmm wani irin moment ne suka yi spending wadda baze Mantu ba, gabaWaya seda ta gigitashi da albarkatun jikinta wadda duk ba cikin hayyacinta take hakan ba, ba jikinsu kaWai ba a lokacin ze iya rantsuwa cewa numfashi ma guda Waya suke yi ba biyu ba, Seda suka shafe mintuna sama da talatin suna rabawa juna temperature Winsu kan ya mirginata, hancinshi yake gogawa da nata yana jin yadda su biyun duka numfashi ta hanci yayi musu kaWan suna HaWawa da baki, a hankali ya fara brushing lip Winshi kan nata, yana kokarin haWe lip Winsu tayi wani mi?a da ya tabbatar da zazzaSin ya sauka, yaraf ta dawo kan pillow a take wani wahalallen bacci ya sure ta, zamewa yayi ya kwanta daga gefenta yana jin yadda zazzaSin tan ke shirin dawowa jikinshi.

Bacci me nauyi ne ya kwasheta yayinda shi kuwa yace be san zance ba, janyo ta ya sake yi jikinshi ya rufa musu bargo sbd jikinshi wani irin rawa yake yi... Ya fi awa kwance cikin wannan yanayi Ganin in yana cigaba da barin ta haka a jikinshi komai ze iya faruwa ya sa ya mi?e dafe da marar shi ya fice a Wakin.

Kitchen ya shiga ya matsa lemon tsami a lipton ya kwankwade tunda yau ba kwanan Fatima bane bare ya rage wani abun, tunda yake be taSa jin irin wannan sha'awa ba se yau, Wakinshi ya shige ya zube rub da ciki bisa gadon shi yana juye juye.

Ita kuwa bacci tayi sossai, chan wuraren karfe uku na dare taji kaman ana kiran sunanta, cikin gigin bacci ta buWe idanunta se taga Wakin gabaWaya ya sauya mata ya koma wani irin ?ango me cike da abubuwan razanarwa, a firgice ta mi?e sede bata iya ambaton komai ba kaman Waure mata baki aka yi ko numfashi da kyar take iya ja amma bakinta ya ?i furta komai.

Wasu irin abubuwa taga suna motsi daga jikin ginin Wakin, sanyi taji me yawa a jikinta waigawar da zata yi taga wani irin hallita da bata taSa sanin akwai irin shi ba ba?i sidik, me munin gani da razanarwa, ?ara ta saki wadda taji muryar yayi amsa kuwwa iya Wakin, da sauri ta sau?a jikinta na rawa ta nemi riga ta saka ta suri hijab Win sallarta ta saka, jakan da ta dawo dashi jiya ta zara ta fice da sauri daga Wakin.

Parlorn kasa taje chan lungun dining ta makale ta takure Kaman wacce ta rasa gata, jikinta wani irin karkarwa yake gabaWaya bazata ce ta san me take yi ba, banda tsanar gidan da tsananin tsoronshi babu abunda take ji.

Tana nan har aka kira sallar asuba fuskanta har ya kumbura da kuka, kaman wuta ake rura mata a gidan haka take ji, tana ji ya sauko da nufin tafiya masallaci, da sauri ta mi?e ta bi bayanshi yana fita itama ta fice daga gidan ko waiwaye babu....

**Ayi comment in takarkare in baku na dare=??**


DIDDIGAR ?AYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuWi ne..
Ze zo muku a Naira Wari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taSa nadama ba>?p?

Karku sake a baku labari.


=???Gureenjoh=???
D?

28

Saboda rashin baccin da be samu ba jiya ya sa ko azkar da kyar ya iya yi ya mike ya dawo gidan, Wakinshi yayi direct ya kwanta ba shi ya tashi ba se wuraren karfe goma sha Waya, wasai haka ya ji shi Adu'a yayi kan ya sau?a ya wuce toilet ya watsa ruwa har a lokacin ze iya cewa yana jin tsadaddiyar jikinta cikin nashi, yana jin duk wani moment da suka yi spending a jiyan cikin ?ashi da Sargonshi.

Haka ya gama wankan ya fito ya shirya cikin kananun kaya, fitowa yayi yana baza kamshinshi me natsuwa da kwantar da hankali, Wakin Fatima ya fara dubawa bata nan da alama ta tafi school, Wakin Fauza ya nufa haka kawai ya tsinci kanshi da sakin murmushi.

A hankali ya tura kofan saide turus ya tsaya ganin kaman an yi wasan kura a Wakin, komai kaca kaca a wargaje abinda ba Wabi'arta ba.

Sunanta ya fara kira yana shiga ciki ciki sede bata kan gadon, bayin tura ya shiga nan ma bata nan.
Saukowa yayi kasa ya je wurin Peter yake tambayar shi ya ga fitan Fauza ko tare suka fita da Fatima?

Yace a'a Fatima ita kaWai ta fita kuma shi yana kofan tun asuba be ga fitan ta ba, hankalinshi ya fara tashi da sauri ya koma saman ya fara kwala kiran sunanta saide babu ita ba alamar ta.

Fitowa yayi ya shiga mota ya ja da matsiyacin gudu se makarantar su, Afnan yake ta nema ko ze gansu tare sede be ganta ba, wurin Faisal yaje yace ya kira mishi Afnan ko suna tare da fauza? Kiranta yayi tace tun jiya da suka rabu basu haWu ba, yau basu da lecture ma da safen.

Tun Faizan na Wauka wasa sede hankalinshi yayi matukar tashi ganin da gaske bata nan Win, Faisal ne ya tuka shi suka je police station suka yi reporting, polisawan sun tabbatar saide in da kafafunta ta fice da sakacin me gadi in ba haka ba da shiga aka yi aka Wauke ta se an gane bare da yace har tsakiyar dare ma suna tare.

"Iyayen ku na nan garin ne?"
Dpo Win ya tambaya.

Faisal ne ya amsa da
"A'a suna Adamawa"

"to ko gida dae ta tafi?"
Dpo ya faWa.

Faizan da ranshi ya soma Saci yace a tsawace
"Me aka mata Win da zata tafi gida ba tare da sanina ba? Ni fa mijinta ne!!!"

Ya faWa cikin hargowa, Kafadanshi Faisal ya dafa yace
"Calm down please Faizan ka natsu, ban san ka da hayaniya haka ba.."

Yace
"Kar in yi hayaniya Faisal? Matata fa na nema na rasa na kawo musu report kuma me makon su yi aikinsu sun tsaya suna faWan wasu abubuwan da baze yiwu ba, ana tafiya gida haka kawai ne a aure?"

Dpo Win yace
"I'm so sorry, ka natsu please ka san komai na iya faruwa ne shiyasa muke maka waennan tambayoyi kila ka mata wani abin Sacin rai da ze sa ta bar gidan ta tafi gida ba tare da saninka ba, amma tunda kace ba hakan bane yanzu zamu fita mu fara bincike ka kwantar da hankalinka komai ze tafi daidai"

Fitowa suka yi sbd azahar da ake ta kira suka tsaya suka yi sallah, Faisal ya dube shi yadda gabaWaya kamananninshi ya sauya jijiyoyinshi suka tashi suka yi raWa raWa yace
"Faizan ko zamu kira su baba?"

Kai ya girgiza yace
"Ko gidan ta tafi in dae a mota ne zuwa yanzu be ci a ce ta isa ba... Amma me na mata da zata tafi gida?"
Ya faWa cikin sanyin murya.

Dafa kafadanshi Faisal yayi ya bubbuga alamun rarrashi kan suka mi?e suka fito se ga Jafar shima suka haWu suka fara yawon nemanta da polisawa, a Airport babu jirgin yola da ya tashi a ranar ma gabaWaya ya gayamusu amma basu yarda ba seda suka je suka gama binciken su kan suka nufi tasha...

***

Ita kuwa Fauza bazata ce ga takamammen Tunanin da take yi ba, Sam kaman makuwa tayi ne ko yaya haka dae ta mi?i hanya ta tafi sossai Dukda wani irin sanyi da ake zabgawa na asuba, bakin wani masallaci ta zauna ana sallar asuba limamin na karatu cikin Suratul baqara ayoyin ?arshe, a hankali take jin natsuwa na zuwa mata, itama ta karSa taci gaba da binshi har ya kai karshe yayi ruku'u.

Da sauri ta mi?e ta shiga ciki ta samu ruwa tayi alwala kan ta gabatar da sallar itama nan fa ta ji bakinta ya iya fara ambaton Allah amma zuciyarta har lokacin ba?i kirin babu abunda ta tsana irin Abuja da gidan Faizan.

Fita tayi daga masallacin ta tafi ta tari taxi yana tsayuwa tace
"Park zaka kaini"
Yace ta shiga, tashar Jabi ya kaita.

Ta biya shi sbd akwai kuWi a jakan, taje ta shiga mota nan da nan motar yola ya cika suka Wauki hanya, Seda ta tabbatar sun bar yankin Abuja kan ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya wani wahalallen bacci ya Wauke ta.

***

Su kuwa tashar mararraba suka fara zuwa duk motocin yola babu irin sunanta ma kuma duk yadda ya musu misalin kamanninta suka ce basu ga me irin kamannin anan ba.

Daga nan Suka yi dei-dei park nan ma neman duniya da kwatance suka ce basu ganta ba, suka nufi jabi Dukda shi kam Faizan hankalinshi Sam be bashi

22 / 29