Diddigar Kaya 1&2 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Complete Novels

Chapter   6 / 29

15K to 18K   out of 86.8K words

na ukun ne Jaddah ta fito tana tambayar Fauziyya kam bacci tayi ne ana ta kira bata ji.

Ganin baccin take yasa ta Wauki wayan tare da amsawa ta kara a kunne, cikin kamillalliyar Muryarsa da se ka saurara zaka ji sbd rashin son hayaniyarsa yace
"Jaddah abincin fa? I've been waiting."

Jaddah ta kalli Fauza tace
"ba'a kawo bane? Tun fa Wazu na bayar a kai maka, ikon Allah.."

Yace
"wa kika bai wa?"

Ta fara jijjiga Fauziyya sbd nauyin baccin da ta riga ta sani tace
"Fauziyya! Ina abincin da na baki ki kaiwa yayanku ne?"

Juya keya tayi kan tace
"yana kan motanshi mana"

Ba tare da yace komai ba sbd yana jin duk abunda suke yi ya katse wayan, Jaddah na ta mamakin ikon Allah akan Fauxa se kawai sallamanshi taji, juyowa tayi zata yi magana taga ya nufo su hannunshi ri?e da ruwa me sanyi wadda ya fara kankanra na kamfanin Faro babba yana tafiya ne cikin ?asaitarshi yana me buWe murfin.

Kan Jaddah ta ankara ya fara tuttulawa fauxiyyan ruwan sanyin, a firgice ta mike zaune tana jan numfashi sbd sanyin ruwan gashi a duniya ta tsani ruwa ya taSa ta yanzu se tayi mura gashi ya zuba sossai a kanta da fuskanta, hawaye ta fara don sossai ta firgita sanyin ruwan kuma ya ratsa ta, ko a jikinshi cikin muryarshi me taushi yace

"wuce ki Wauko!"

Mikewa tayi tana share hawayenta ta fito, ko da ta Wauko abincin don tuna muguntan da ta mishi a ciki bata san sadda murmushi ya subuce mata ba, a gabanshi ta dire ta juya ta fice ya ja tsaki kan ya buWe ya zuba kaWan.

Spoon ya Wauka sbd shi fa irin mutanen nan ne da ko tuwo zasu ci seda spoon, da bismillah ya kai loman abincin bakinshi Sam be kula da bala'in dake ciki ba seda ya haWiye ya Waura na biyu a bakinshi.

A firgice ya dawo da abincin yana sakin tari kaman ze shiWe, da sauri Jaddah ta dauki ruwa ta mika mishi ya amsa ya sha sede ba sassauci, tari yake kaman ze mutu gabaWaya ya HaWa zufa, idanunshi sun rine sun zama jajazir, da kyar ya samu tarin ya lafa se kuma gefen cikinshi ya ri?e.

Salati Jaddah take tayi tace
"na shiga uku! Yaji ne a abincin ko me?"

"Zaliha! Zaliha!!"

Zaliha ta fito da gudu ta zube a ?asa Jaddah tace
"ke Zaliha kin saka attarugu a markaden kayan miyan nan ne?"

Girgiza kai tayi tace
"ban saka ba Jaddah ai kin ce yallaSai Faizan baya so, wlh ko kaWan ban saka ba"

Fauxa dake daga window tana ta dariyar cin nasara, kwanciya yayi a kan kujeran duk dauriyarshi ulcer na azabtar dashi shiyasa yake mugun kiyayewa.

Kaman wasa Seda Faizan yayi ciwo sossai kan ya samu sau?i, kaman yadda itama saida tayi mura da zazzaSi, kowa kuma Seda yayiwa Zaliha faWan saka attarugu a abincinshi baiwar Allah gata da gaskiya sede babu yadda ta iya haka take shiru take bada hakuri.

Zaune yake gaban baba prof kanshi a ?asa, baban ya tambayeshi jiki, cikin girmamawa ya amsa da da sauki Alhamdulillah, bayan shirun seconds kan yace.
"In Allah ya kaimu Laraba zan koma Abuja sbd akwai tafiyar da zamu yi da shugaban ?asa"

Murmushi baba ya saki, a ko menene ya kan yi alfahari da wannan yaron nashi, Faizan ba irin normal pilots bane, yana daga cikin manyan pilots da idan ba da su ba shugaban kasa baya tafiya ko ina, bayan nan yana da hannayen jari da kampanunnuka ba daya ba ba biyu ba, Sam be dogara da aiki Waya ba, yaro ne shi me tsantsan biyayya ga iyayenshi, babban Wabi'ar shi kuma kunya yanzu ya san akwai abunda yake son faWa mishi ne sede yana jin nauyin maganan shine yake ta kwana kwana.

Baba yace
"masha Allah, Toh Allah ya kaimu ya nuna mana"

Yace
"Ameen baba!"

Baba ya kalleshi yace
"akwai wani abu ne kuma? Naga kaman kana son yin magana"

Kanshi ya dukar yana shafa kwantaccen Suman keyanshi yace
"dama akan maganan Fatima ne"

Murmushi baba ya fadada yace
"masha Allah, ka shirya auren kenan.. Toh tunda har ka furta wani satin in shaa Allah zamu je wurin mahaifinta mu tambayar maka ita, ai Fatima yarinyar kirki ce ta samu tarbiya me kyau daga Mahaifiyarta Allah ya tabbatar mana da alkhairi"

Da Ameen Faizan ya amsa, dukda maganan magana ne da ya kamata yayi farin ciki sede ko kaWan be wani ji daaWin hakan har chan ba, hira suka taSa kadan da baban har baba Alhj ya shigo suka kara tattaunawa kan ya musu sallama ya fice.

Bayan ya koma aiki da kwanaki biyar aka tambayar mishi Fatima kuma an bashi sede an ja auren se ta gama secondary school in ya so se ta fara jami'a a gidanshi.

****

Kwance take kan gadonta jikinta yayi tsami da bugun da ya Farhan ya mata da magrib Win saboda bin wata ?awarta da tayi gida bata dawo ba se da ana kiran sallahn magrib tun karfe 1:30, da farko basu so dukanta ba sede Sam ta ?i faWan inda taje hakan yasa ya Farhan da Ya Faraj suka zane ta har Seda Baba prof da za shi masallaci ya karSe ta, Allah ya isa take ta ja tana cin alwashi kala kala a kansu, fa'iza dake Wakin tun da suka dawo daga sallar isha'in bata ce mata komai ba...

Suna daga Wakin Fatima ta shigo a wurin Aunty Amarya da Ammi dake bisa taburma a tsakar gidan suna cin Tuwon dare ta zauna, tace
"waii wallahi Aunty mammi na jin jiki, ciwon kafan nan baya mata ta daaWi Wan zaman da na yi na awanni a wurintan nan baki ga ba, komai se an yi mata"

Ammi tace
"Allah sarki, Allah dae ya bata lafiya ai kafa shine komai a jikin mutum, Allah dae ya sa kaffara ne"

Aunty Amarya tace
"Ameen Ammi, Fatima se ki dinga zuwa kina taya Asiya (Wiyar Yayar mammi Win) kula da ita"

Fatima tace
"In shaa Allahu Aunty ai Mammi kaman uwa take a wurina, bari na shiga na dubo su Fa'iza mu ci abinci"

Mikewa tayi ta nufo Wakin nasu, tana shiga suka HaWa idanu da Faozia dake kallon kofan, Wauke kai Fatima tayi yayinda Faozia tayi tsaki me karfi tace
"Fa'iza kin san Allah ko?"

Fa'iza tace
"me aka yi kike tambayana na san shi mana"

Faozia tace
"DaaWina dake baki iya cin riban zance ba, ko da shike manta ma... Dama Tambayarki zan yi da munafukin Soye da na bayyane don Allah wanne ya fi?"

Fa'iza da bata fahimci zancen ta ba tace
"ai munafunci ko ya yake sunan shi munafunci kawai dae gwara wadda ze nuna maka a bayyane ka san dashi da wadda ze nuna maka Musa a fuska fir'auna a zuciya"

"sannan in zaka yi abu kayi don Allah da nufi Waya ni fa shiyasa bana son hulda da duk munafuki a duniya.." Fauza ta karasa

Fatima da ta tsaya kikam tana Kallonsu se hawaye ya fara kwaranya a fuskanta, Aunty ce ta fara shigowa ta buge Bakin Fa'iza tana cewa
"yanzu ?ar uwarki zaki HaWa kai ana cusguna mata a gidan nan Fa'iza? Tana gayamin ina karyatata ashe da gaske ne? Fa'iza..!"

Ammi da ita ma ta shigo tayi kan Fauxa zata make tana cewa
"Ai ba ita zaki daka ba Auntynsu ita uwar iyayin nan zaki mara har se taga wuta.."

Dira Faozia tayi ta ?ayan gefen kan Ammi ta zagayo ta fice da gudu harda bangaje Aunty goshinta ya ?ume da kofa salati duk suka saki ita kam ko waiwaye babu tayi sashen Mammi da gudu.

DIDDIGAR ?AYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuWi ne..
Ze zo muku a Naira Wari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin
09039206763
Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taSa nadama ba>?p?

Karku sake a baku labari.


=???Gureenjoh=???
DIDDIGAR ?AYA
?? (Mai Wuyar Tsincewa)

(3E DDG 'D1-EF 'D1-JE

FATIMA MUHAMMAD GURIN.? ? ? ? ? ??
? ? ? ?? (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ?aya... Paid*

? ? ? ? ? ? ?? *Shafi Na Takwas*

*PAID BOOK*

?AN?ANO

**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI AUNTY HALILLOS GWANATA KUMA MALAMATA>?p?d'?**

Karshe dae Aunty bata iya bacci ba seda Baba Alhj ya danne mata goshin aka shafa man zafi, takaici ya hana shi cewa komai, ya aika a kira mishi Faozia Win aka tarar bata nan sede Jaddah bata ce bata nan ba kawai cewa tayi a ce tayi bacci Dukda bata san wani laifin ta sake aikatawa ba.

Ita kuwa Faozia tana zuwa wurin Mammi ta shagwaSe tana faWamata abunda ya faru, Mammi tace
"Gaskiya Farhan da Faraj basu kyauta ba ai da lafiyata ?alau babu wadda zan bari ya taSa ki su da suke gantalinsu akwai wadda ya hana su ne?"

Cikin jin daaWin goyon bayan da aka bata tace
"ai shine"
Mammi tace
"Faozia am ki rage nemarwa kanki magana kin ji? Bana son yadda kowa ya buWe baki yace Faozia, Faozia Win nan wallahi har raina bana jin daaWi"

Fauziyya tace
"In shaa Allahu Mammi bazan sake ba"
Mammi tayi murmushi Dukda ta san labarin kanzon kurege ne kullum haka take cewa baze hana gobe tana fita ta jajiSo wani tashin hankalin ba.

?in zuwa wurin jadda tayi wai tana fushi a lokacin da su Farhan ke bugunta jadda bata zo ta karSeta ba kuma ta tabbatar sarai tana ji.

Asiya mammi ta kira akan ta zo ta dubo wa Fauzan abunda zata ci.
Faozia tayi Charab tace
"Mammi bari na shiga kitchen Win da kaina"

Har ta fita ta dawo tace
"ke fa Mammi kin ci abinci?"

Tace
"Ina ga Tea zan sha Faozia kubewa suka girka a gidan ni kuma ba so nake ba, je kiyi abunda zaki yi ke kam"

Kitchen ta wuce, Asiya dake zaune a parlorn ta bita da harara ko Kulata Faozia bata yi ba don ta jima da sanin Asiya irin mutanen nan ne da suke bari hassadar wani ya gurSata musu rayuwa, ba tun yau ba ta fahimci Asiya bata ?aunar ta shiyasa itama bata shiga harkarta.

Hijab Winta ta ajiye ta fara dube dube a kitchen Win Seda ta fidda duk abunda zata bukata na aikin da take son yi kan ta fara aikin, Yawan bin kawaye da take har ana dukanta duk akan girki ne tana matukar kaunar girki babu abunda yake bata nishaWi a rayuwa irin ta ganta a katon kitchen tana girke girke, idan kaga Faozia a school ta natsu to kallon recipes take a wayan kawaye don gidansu kam ba'a abubuwan zamanin nan.

Shawarma da suka yi Wazu har sanadiyar shi aka Chasa ta tayi guda biyu na beef, banda kamshi babu abunda ke tashi a kitchen Win tana yin Shawarmanta kuwa tana biski ba me yawa tayi ba Wan kaWan ne sosai da kidney sauce, fancy plate ta Wauka ta zuba biskin daga gefe in a stylish way kan ta zuba kidney sauce Win shima a gefe ta watsa parsley a kai kaWan yadda ya bada wani garnish na burgewa.

Shawarmanta guda biyu ta Wauko suma ta saka su a plate ta Waura Duka a tray ta Wauko ruwa masu rangwamen sanyi tare da daukawa kanta wani mango drinks ta nufi Wakin Mammi, tana zuwa ta ajiye tray Win tace

"Mammi guess what I made?"

Mammi tana murmushi tace
"Ina zan sani ina zaune a nan na dae ji kamshi na tashi kuma duk hasashe na na rasa gane menene.."

BuWe plate Win biski da kidney sauce tayi tana dariya cike da jin daaWi tace
"Tadaaa..!"
Tana dariya sossai wadda ya saka Mammi murmushi tace
"Masha Allah, Kice daughter na na shirin zama Chef eyee a ina kika koyi irin wannan delicious Win?"

ShagwaSe fuska tayi tace
"ba irin su bane na bi Zee koyo a gidansu kuma da nisa shine ban dawo da wuri ba su ya Farhan suka bugeni ba..!"

Mammi tace
"masha Allah, am impressed gaskiya karki damu in shaa Allah na miki Alkawari da kaina zan saka ki a catering school ?ata ta zama Chef Faoza.."

Murna Faozia ta fara harda tsalle, Mammi na ta dariya Faozia is such a wonderful child da zama da ita kaWai ka iya saka ka farin ciki she's so lively in har ka san yadda zaka tafi da ita, Mammi ta matsarwa plate Win tace
"bismillah Mammi"

"thank you bitty"
Spoon ta sa ta fara ci tana yabon hannun na Fauza a girki, itama Shawarmanta taci tas ta cinye ta sha mango juice Win kan ta tattare wurin ta fitar, da taimakonta Mammi taje toilet tayi duk wani abunda zata yi ta dawo da alwala, ita ta taimaka mata har ta kwanta...

Tana shirin shiga wanka se taji sallaman Baba Prof hijab ta saka, Seda ya shigo ta gaishe shi ya amsa da kulawa kan ta fice ta bar su da Mammi, Wakin yaya farida da babu abunda Mammi ta taSa ciki ta shiga, akan gyara akai akai hakan yasa ta nufi toilet Winta tayi wanka, bayan ta fito ta duba wardrobe Winta ta kuwa samu kayan bacci sabo dal a Leda Dukda ya Wan yi mata yawa haka ta saka.

Seda ta Sata lokaci mai yawa kan ta fito ta koma Wakin Mammi ta samu Baba prof ya tafi, Har zata juya Mammi tace
"Fauza"

Dawowa tayi tana cewa
"Na'am Mammi ko kina bukatar wani abu ne?"

Mammi tace
"A'a ki hau gado ki kwanta, kiyi Adu'a kin ji?"

Kai ta gyaWa tare da rage musu hasken Wakin ta hau gadon na Mammi ta kwanta tare da jan bargo.

Chan cikin dare Fauza ta tashi saboda fitsarin da ya matse ta se ta hangi Mammi zaune dafe da kai, da sauri ta mike tace
"Mammi!"

Mammi bata Wago ba, sau?a tayi ta nufe ta ta du?a a gabanta tace
"Mammi lafiya? Baki jin daaWi ne?"
Tayi maganan hawaye na cika mata idanu Mammi ta Wago idanunta duk sun sauya tace

"Na kasa bacci Fauxa kafana se harbawa yake"

Hawaye ne ya zubowa Fauxa cikin tausayin Mammi, zama tayi gaban kafan tace
"bari na miki Adu'a Mammi"

Bismillah tayi sau Uku kan ta Waura da
(P3REP 'DDG! (3E DDG!! (3E 'DDG!!!
"#N9OH0O (P''DDGP HNBO/R1N*PGP EPFR 4QP1P EN' #N,P/O HN#OG@Np0P1"

"Bismillah! Bismillah!! Bismillah!!!
Auzibillahi bi qudratihi min sharri ma ajidu wa uhadhir".
Kafa bakwai ta shafa mata a kafan ta kara da qulhuwa uku, falaki uku, da nasi uku.
Manzon Allah yace babu wani ciwon dake damunka da zaka dafa wurin ka karanta wannan Adu'a ba tare da Allah ya yaye maka ba, walau ciwon ciki, ciwon kai, ciwon kunne ko ma wani irin ciwo ne.

Cikin ikon Allah bayan ta gama yi mata ta ci gaba da massaging kafan har Mammi ta Samu bacci ya Wauke ta, wani irin ciwon kafa ne wannan Fauxa tayi maganan a zuciyarta tana kallon tarin magungunan na Mammi, daga na Asibiti har na gargajiya zuwa na musulunci, komawa gadon da Fauxa bata yi ba kenan a nan kasa ta kwana se da Asuba taji Mammi na tashinta.

Mikewa zaune tayi tace
"Mammi ya kafan?"

Mammi tayi murmushi tace
"sannu Fauziyya! Sossai na ji daaWin Adu'ar da kika min kwanana hudu rabona da baccin dare se gashi yau nayi harda mafarki"

Murmushi Fauxa tayi tace
"to bari na sake miki"

Adu'ar ta fara mata yayinda ma ta zuba mata idanu tana kallo, ta rasa me take hangowa a rayuwar Fauxa wadda kowa baya hanga kowa kawai ya tashi Fauxa bata ji, Fauxa kaza Fauza kaza ita Sam banda haske babu abunda take gani a rayuwarta, yarinya ce me tarin Soyayyen baiwa amma influence na mutanen dake zagaye da ita ya hana shi bayyana.

Jin za'a shiga sallah yasa tace
"Fauza tashi je kiyi alwala ki tafi masallaci bari nima na mi?e"

Da taimakon Allah ta kai kanta bayi tayo alwala yayinda tuni Fauxa ta fice masallaci, anan tayi sallah ta sake kishingiWa tana me sake samun wani baccin saboda sau?in kafan.

Fauxa ko War bata ji ba ta wuce sashensu abunta, yau ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????itace da wanke wanke da kuma gyaran Wakin su, Seda ta fara shara da gyara Wakin tana cewa
"Wallahi in an ga dama a wargaza kan a tafi ba ruwan Fauxa"

Falaq tace
"amma kin san dole a shirin su Fakiha su wargaza Wakin nan kam ko?"

Cikin kunkuni tace
"suna da hannu ai, se su gyara! Ni de na san nayi"

Tana kai nan ta hau sharewa ta fitar da Sharan a memakon ta kwashe se ta watsa tsakar gida alhali Fatima ta riga ta wuce nan a shararta na tsakar gida, tana watsawa ta bi ta kan tsintsiyar Fatima da ta sake baki tana kallonta tayi wurin wanke wanke ta fara yi, dama kowa ya san wanke wankenta kwanuka kam se sun bugu iya buguwa in akwai na fashewa kuwa to se ya fashe.

Ammi da suke aikin kari da Fa'iza bata ce mata komai ba, don in tace zata yi magana kuka ze iya fin karfinta Fauziyya ta riga ta fi karfin duka yanzu kuma se Adu'a.

Da yamma bayan sun dawo makaranta Fatima na wankin uniform na su Fakiha yayinda fa'iza ke wanke wanke, ita kuwa uwar gayyar kitchen take tana taya Aunty Amarya sa magana tunda ba aikin take ba duk abunda Aunty Amarya ta saka ta se tayi mata shirme da gangan.

"Ni sumayya! Yanzu Fauziyya daka attarugu ma se kin zuzzubar a ?asa haka? Ai ko Faazila dake karama a gidan nan karankap zata daka min kayan miya in kwashe lafiya lau ke kam babu abunda kika iya goWe goWe dake se sa mutane magana? Wani irin jaraba ne wannan?khaih Allah ya shirya mana in na shiryuwa ne"

Kunkuni wadda Aunty Amarya bata ji ta hau yi. "Yen yen yen yen... Se ki zo ki shirya ai tunda charbi nake ko jigida" kawai se Aunty Amarya ta saki kuka. Baba Alhj da shigowar shi gidan kenan ya tarar da faWan da Aunty Amarya ke yi kuma yana kallon lokacin da take gungunin sede gudun kar ya ce ze buge ta yanzu ya karya ta yasa ya shige parlornshi kawai.

Aunty Amarya tace
"tashi ki tafi bana son aikin, in har aikin da zaki sani magana ne, nayi maganan kuma ki zage ni don

6 / 29