Aliyu Gadanga Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   20 / 34

57K to 60K   out of 101.5K words

tayi tana fadin"Daka tabbatar da ya ganka,kayi hanzarin Fitowa kabi nan hanyar Da zanbi zaka ga nayi parking din motata,zan barmaka abude sai ka bude ka shiga kana Fitowa kayi min text yadda zan Fito da hanzari, kayi kamar yadda muka Shigo kagane..? kai ya gyada mata kafin ta kada kai ta Figi motar da gudu,shiko sai da yadan tsaya yana kallon gefe ganin wasu sojoji zasu Wuce sai da suka wuce ya juya yaga Babu mai kallanshi kana ya Tunkari gidan Aliyu,Yana zuwa yaga Sunanshi Manne jikin kofar Wajen,ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya Fito da key daga aljihunsa wanda aka kera da karfe,ya saka yana juyashi sai ga kofa ya bude hamdala yayi kafin ya waiga yaga bamai kallonsa salaf salaf,ya Shigo falon ya maida kofar yadan Tura yadda bazata Rufe ba.

Falon babu kowa yana leke baiji motsin kowa ba,dayan bedroom din ya fara lekawa,sai yaji ga babu kowa,dayan yakoma ya bude ahankali ya leka sai yaga kaya akan gadon dakin,Shigowa yayi yana waige kamar barawo,Motsin Ruwa yaji a Tiolet,sai yakara kunnenshi yaji karan Saukan Ruwa,Tsalle yayi yana murnan jin dadi Rigarsa ya cire ya rage dagashi sai vest da dogon wondo,direct yayi Sufa ya haye gadon,harda Daukan rigar dake kan gadon yana Shinshina.

? Itako Muneera direct kofar gidan Conole Sulaiman ta faka motarta tana Fitowa daga motan sai gashi ya Fito dakanshi ya tarbeta zuwa cikin gidanshi,suna zuwa falon ya Rumgumeta yana Shinshinar wuyanta lokaci daya yana Fadin" Kai gaskiya nayi kewar wannan Lallausan jikin naki.."Yake tayi tana Rikoshi take fadin"Nima haka Sojan Fama"Tafada tana jansa kan kujera suka fada,yana Rumgume da ita,kamar wani zai kwaceta,itako gabadaya hankalinta na kan wayarta tana Jiran sakon ya Shigo mata.

Captain Aliyu shida Jabir suka jero suna tattaunawa kan Sojojin hadin gwiwan da Aka gayyato wanda akace za"a saukesu cikin wannan barikin,Toh alhakin Kula da komai yana Hannunsa,suna tattauna yadda Abubuwan zasu kasance,Suka karisa gidajensu,Nan suka rabu Jabir ya nufi gidanshi shima ya nufi nashi,yana zuwa kokarin ciro key yake ya bude kofar,ammh yana Tabata ta bude,cike da mamaki ya Shiga falon,yana mamakin samun kofar abude,jin Shuru Falon babu kowa yasa ya nufi bedroom yana fadin" pretty kina ina ne,? am back..?

jin Shuru yasa ya Nufi bedroom kai tsaye yana kiran Sunanta,Itama kuma Azeema tana kokarin Fitowa daga Tiolet din taji yaya captain na kiranta,tana gyara zaman karamin Towel din dake jikinta ta fada da karfi"Am here Yaya captain.."Tafada tana Rufe baki Tuna abayi take tana bude kofar Tiolet din yayi dai dai da bude kofar bedroom din da Aliyu yayi,ita Fuskarta na Kallon kofar Shigowa ne,tana sakarma Gadanga mirmishi shiko yana Shigowa yayi 4eyes da wani gardi kwance kan gadonsu na Sunnah ba riga,ga rigar da yafita yabar Azeema dashi ajikinsa yana shinshinawa,gabadaya Aliyu jinin jikinsa ne yaji ya daskare,saboda tsoro da dimautuwa,Hannu yadaga yana nuna wajen,bakinsa na rawa Jijiyoyinsa kansa Sun mike saboda bacin rai.

Ganin haka yasa Azeema maida kallonta inda yake Nunawa Abunda tagani ne yakusa sawa towel dake jikinta ya subuce ya fadi,baya taja tadafe hannu akirji Tana zaro ido lokaci daya take fadin"innalillahi wa'inna Alaihirraju'un..."Take Fada jikinta narawa,shiko ganin yadda sukayi yasa ya kalli Azeema yana fadin"Bbby har kin Fito wanka,Toh wlh kizo na karayi don kinsan bai isheni ba.."Yafada yana Rumgume Filo cike da makirci ganin yadda tayi ne tana Rawan jiki,yasa yakalli barayin inda Aliyu yake,da hanzari ya mike yana raruman rigansa yana bayyana tashin hankalinsa,Ammh sai ya kalli Azeema yace"Baby ya haka?Kafin na yarda zanzo sai fa dakikacemin mijin ki bayanan,ammh yanzu ya na ganshi.."Haurowa gadon yayi zai Fita yana bin bango,sai da yazo gab kana Aliyu yayi kukan kura ya damkoshi ya durkusheshi akasa baiyi wata wata ba yafara bashi kulli Afuska,Jikinsa na rawa saboda tashin hankali,kokarin Cire masks din Fuskarsa yake,ammh yaki bari,ammh saboda yafisa karfi,sai da yasamu nasaran ciremai Fuskarsa ya bayyana shakesa Aliyu yayi yana fadin"I will kill u..." yake fada yana zaro ido,ganin yana neman kasheshine,yasanya kafarshi ya tokaraimai gaba da karfi,wanda ya saka dole Aliyu ya sakeshi ya rike gabanshi yana Runtse ido,shi yabashi damar tashi ya Fita da gudu,koda Aliyu yayi yunkurin binsa sai yakasa da hanzari ya Fito da waya yakira Jabir,jabir na dauka muryansa A haukace ya furta.."Jabir ka bada Umarnin Arufe kofofin barikin nan Right now.."gaban Jabir ya fadi da hanzari yace"Aliyu lafiya naji muryanka haka.?."Tsawa ya dakamai yana fadin"Kayi Abunda nace mallam.."yana gama Fadar haka ya kashe yana kokarin mikewa.

Itako Azeema wajen ta durkushe tana gunjin kuka hannunta bisa kanta,tana kiran sunan Allah,Kukantane yasa Aliyu ya dago yana kallonta da jajayen idanunsa,Yana jin kamar ya tashi yayimata dukan mutuwa ammh bazai iya ba,komawa yayi ya zauna yana cije baki kafin yace" Azeeeemmmmma...."Da karfi sai da ta Razana baya taja tana Rufe baki saboda kuka" kai ya sadda yana fadin"Dame na rageki da har zaki kawomin kato..?Girgizamai kai takeyi tana so tayi mgana ammh kuka yaci karfinta,Rarrafowa tafarayi zuwa gabanshi tana wani irin kuka tana girgiza kai,ganin haka yasa ya yunkura ya mike ya fice da hanzari yana dafe maransa,Bajewa anan Azeema tayi tana fadin" Hasbunallahu wani'imal wakil..."

? Koda Jabir ya Fito Tuni har gayen ya mike inda Muneera tabi Gudu kadan yayi sai gashi wajen motarta da hanzari ya bude ya Shiga,yana Shiga ya Fito da wayarsa ya turama Muneera Text da cewa" _Ki yi hanzari ki Fito aiki ya kammallah sai dai an kusa samun mtsala.._ Muneera dake Ta ribanta Sulaiman tana ganin Shigowar sako ta mike da hanzari tana kara wayan Akunne take fadin"hello mommy...Innalillahi ganin nan zuwa.."Tafada kafin ta kalli Sulaiman wanda ke kwance kan kujera yana kallonta tace"Zan Tafi yanzu Sistern mamata ta kirani wai Anyi Addmitting din mijinta a asibiti,kuma in banzo ba yanzu zata zargi wani Abu,Ammh dont worry zan dawo ko kazo mu hadu.."Tana gama fadar haka bata jira cewarsa ba ta fice da hanzari da gudu ta karisa wajen motar ta shiga tana kokarin bata Wuta ne take fadin"Garin yaya aka samu mtsala..? yana daga baya yace"karki damu mtsalan Fuskatace daya gani,kuma inaga don wannan ba wani damu.."zagi Muneera ta yanko tana fadin"are u mad,kasan waye Aliyu kuwa,he is very smart wlh,fuskarska kadai ta isheshi Shaida.."Take fada tana Figan Motar Jabir daya Fito daga gidansa dahanzari yana kokarin kiran waya motar tazo ta wucesa da gudu har sai da ya bita da kallo,kokafin yayi waya zuwa masu kula da Shige da Fice na barikin Tuni Muneera ta fice daga Barrak din Hankalinta atashe tana ta zazzagamai Masifa acikin mota Ammh hankalinta ya kwanta Tunda dai Aliyu ya ganshi dama su bukatansu kenan.


*Am Srry For d late update,wlh Jiya nayi busy ne*


*,Janafty...*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty=???_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA=??Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*'

_*Daukaka wata abace,Ta dan lokaci in ta Aureka Duniya zata sanka sosai kayi more porpular,and One Time u bcome Cele by Force ohoo=?9?buh duk lokacin data sakeka kashima yafika Daraja,fans ma zasu daina zencen buk dinka balle akai ga zencenka kazama mar amfani garesu,Shiyasa ka/ki yi Fatan daukaka ko Shahara ita din kamar misalin Duniyace Rigar aroce,in tashiga wanchan gobe zata barkane ta shiga wata,...Shiyasa kazama mai aiki da Hankalinka,kayi komai don Allah sai gaka yama ka sakayyah da kyakyawan sakamako wanda bakayi Tsammani ba '>??=?O?,...Assalamu Alaikum Janafy Fans*_


? ? ? ? ? *Chapter 24*

? ? ""Adaddafe Aliyu ya Fito yana Tafe yana rike maransa,Da Jabir ya cikaro akofar apartment dinshi,yana ganinshi ya isa gareshi yana fadin"Wai captain meyake Faruwa ne? lafiya kake dukewa ko baka da lafiya ne? ina ita Azeemar? yafada yana leka kofar Shiga Falon.

? Ture hannunsa,Aliyu yana fadin"Kasa Ayi bincike acikin barikin nan,Kada abari wani ya Shigo kuma kada wani yafita,da anga wata bakuwar Fuska Juz ku sanar dani.."Yafada yana cije baki saboda azaba Hannunsa Jabir ya riko yana fadin"Look Aliyu nifa ba iya abokinka bane don Allah kafadamin meke Faruwa? Wani Mutum ne ya Shigo,dan Fashi ne,ko ko dai aikoshi akayi ne? Aliyu ya dago kansa idanunsa sunyi jawur,baya Jabir yaja ganin yanayin Aliyun baicemai komai ba ya koma cikin gida,ya Rufo kofar,nan ya sulale yana Rike kansa da hannu daya,Saboda yadda yake saramai,So yake yayi kuka,ammh yakasa zuwa Tunda yazo duniya bayan Abunda ya Faru Ranar Daurin Aurenshi da Ni"ima,bai taba Shiga tashin hankali irin na yau ba,dame ya rage Azeema?wata zuciyar tacemai ammh taya zaka yarda Azeema zata gayyato wani kato,karka manta kai kasameta a burduwa fa? toh ammh in ba hakabane babu wanda keda alhakin Shigo da wani cikin bariki nan sai da wanda yasan wajen? Toh ammh ai ita Azeema batasan ko"ina a barikin nan ba,Toh waye ya Shigo dashi yanunamai gidana? wata zuciyartace waye kuwa banda Azeema babu wanda zai gayyatoshi sama da ita.

Kansa ya Dora bisa Tafin hannunsa yana Kiran Sunan Allah,Yana zaune wajen yasamu kiran Jabir kan yazo Security offoce yanzu,da hanzari ya mike Fuskarsa tayi ja,saboda Bacin rai,koda yaje chan Nan jabir ke mai bayanin bakin Fuskar da"aka samu duk ziyara suka kawoma danginsu nan ya Shiga nunamai mutanen da suka Shigo barikin aranar,ammh baiga Fuskar wanda yake nema ba,da hannu yayima Jabir alamu da a sallamesu kuma abude get kowa ya fita,Jabir ya Shiga damuwa ganin Halin da Aliyu ke ciki,ammh bai bashi Fuskar sanin meke Faruwa ba,don Aliyu yace bazai iya kallon idon Jabir yacemai Azeema yakama da wani acikin gidansa ba,Shiyasa yakasa mai mgana sai dai kawai ya kalleshi yana kada kai.

? Azeema kuwa tunda tabaje akasa take kuka kamar Ranta zai Fita data Runtse ido Mutumin take gani da maganganun dayayimata,da sanda Aliyu ya dakamata tsawa,dataTuna haka sai ta toshe kunni tana sakin kuka,Tana nan kwance tana kuka har sai da muryanta ta Shide dakyar ta Tatashi ta Koma tiolet tayi alwala tazo tayi sallar la"asar tanayi tana kuka,Tana idarwa taji Shigowar yaya captain da hanzari ta mike ta Fito,tsakiyar Falon ta ganshi zaune ya dafe kai,Tunda daga kofar bedroom dinta ta durkushe tana kuka,Matsowa take idanuwanta na tsiyayar hawaye yana jin gunjin kukanta ammh yakasa dagowa ya kalleta saboda yadda zuciyarsa ke tafarfasa,Zumbur ya mike yana juyamata baya da wani irin karfi da Tsawa yace,"Kada ki kuskura kizo kusa dani..Azeema kin cuceni kin ha"inceni,kin kuma cucu aurenki da Yardan da mahaifinki da mahaifiyata sukayimiki,Dame na rage?,meye bana miki,?na baki abinci na baki lokacina nabaki kulawata kai hatta da soyayyata na baki Azeema why"!Why Azeema meyasa kika zabi ki cutar da zuciyata da Abunda zai kasheni har lahira.ehe..Why..? yafada muryansa Tafara rawa.

Juyowa yayi yana kallonta,Yake fadin"Sai dai, kuma bani kadai kika cuta ba Azeema harda kanki domin bazan cigaba da zama dake ba,domin zamanki tare dani watarana zan iya shakeki ki mutu saboda bakinciki gwara na tattaraki na maidama mahaifinki ke,ngda da sakayyah Azeema ngd da yardan dana baki kika cutar da zuciyata Allah nagani bantaba zina ba,kuma...Kuma Ni banta sha'awarta ba,Sai dai in shegentakan da"ake kirana dashi,shine yake bibiyar Rayuwata.."Yafada yana Runtse ido,Dakyar da sodin goshi sililin hawaye ya zubomai guda daya,Azeema da gabadaya hijabinta ya jike da hawaye ta rarrafa da gudu zuwa kafan yaya Captain takama da hannun bibbiyu tana fadin"A"a..A"a kada kayi haka..Wlh tallahi banda masaniya Akan komai,wlh ban..Ban san komai ba don Allah ka tsaya ka bincika don Darajan ma'aiki.."Take fada tana wani Gunjin kuka.

Tsaye yayi yana jin yadda zuciyarsa na Tafasa,Kafa yasa ya shureta tatafi ta bugu da kujera,center table din dake gabansa ya Saka kafa ya buga sai da ya rabe gida biyu,kallonta yayi yana fadin"Saboda haka ki tashi yanzu ki hada duka kayanki,duka nace banison ganin ko Silin gashinki agidan nan,Gobe zan maidake gombe domin Zuciyata bata da karfin gwiwan Sake zama dake.."Daga haka ya shuru kafa yafada daya bedroom din yana huci.

Hannu Azeema ta dora akai tana kuka tana fadin"Innlillahi...Na shiga uku,waye yayimin wannan kazafin,wlh kowaye bazan taba yafemai ba Har Duniya ta nade.."Take Fada tana kuka,kafin tatashi da gudu tashige daki,tafada bisa gado tana ihu tana buga kanta jikin katifa babu mai lallashinta,Shiko Aliyu tunda ya Shiga bedroom din yafada Tiolet ya sakarma kanshi Shower yana sakin ajiyar zuciya.

________________

?? Dai dai wajen anguwan Rimi bus stop ta saukeshi Ta damkamai wani Abu abakar leda tana Fadin"Mungode,in wani aikin yataso zamu nemeka,and don't forget ka lura Sosai inajin tsoron ganin Fuskarka dayayi.."Mirmishi yayi yana rike ledan dakyau yace"Bafa ki da mtsala Hajiya aikina ne nasaba.."Kada kai kawai tayi kafin taja motarta tayi cikin Anguwan Rimi.

? Wani Mamaken gida naga tazuba hon megadi yazo ya budemata get ta Sulala ciki,aparking space ta faka motar kafin ta Fito ta nufi cikin gidan,tana Tafe tana cilla key din motar sama cike da Nishadi,ababban Falom gidan ta cikaro da Kanwar mom din nata ita da yaranta,da gudu suka tashi suna mata oyoyo,itama ta rumgumesu tana dariya,dakyar sula barta ta kariso Falon,tana fadin"Mommy kinga Ya"yana zasu kada ni ko? wacce aka kira da mommy na kallah yar matashiyace,wacce bazata wuce Shekara 40 ba,Kallonta tayi kafin tace"Wai ina kika je ne muneera..? Juya idonta tayi kafin tace"Anguwan Sarki naje,gidan wata Friend dina Seeyama,wacce mukayi Sch tare da ita.."Gyada kai kawai matar tayi kafin ta juya ta Nufi hanyar kichen tana fadin"Allah yasa da gaske ne..."Rantsuwar karya Muneera tafara jeromata da hanzari ta dakatar da ita tana fadin"Nifa ba Rantsuwa na tambayeki ba,kawai cewa nayi Allah sa da gaske ne.."Da kallo muneera ta bita tana Tura baki,kafin taja jakarta ta haura sama,tana kunkuni.

Tana Shiga dakin,wayarta ta dauki kara,sai da tazauna bakin gadon ne,ta cirota cikin jaka ta duba ganin mai kiran ne yasa tayi mirmishi ta daga tana Fadin"Sweetheart komai ya tafi kan Tsari harma na sallame gayen.."Dariyan jin dadi Ni"ima tayi kafin tace"Job weldon Sweetheart..Yanzu yaushe zaki dawo mukoma wajen yarinyar...? ajiyar zuciya Muneera ta sauke tana fadin"Gobe insha Allahu,buh wani hanzari ba gudu ba,ita yarinya bafa musan inda zamu sameta ba,kuma bazamu yi Saurin zuwa mujira ko nan da Sati dayane,muga shin aikinmu yayi duk da ina da tabbacin ko ta kwana Akaduna yau,toh ina tabbatar miki gobe a gidan Ubanta zata kwana..."Dariya Ni"ima tayi kafin tace"Kema mganarki Abar dubawa ce,Shikenan sai kin dawon,mganar yarinyar kuma ai bamu da mtsala tafadamama Sunanta,na tabbata in anan area take zamu sameta.."Muneera tace"Ok sai munyi waya.."Daga haka suka yanke kiran zuciyarsu cike da samun Nasara.


?? *******************

?? ""Koda garin Allah ya waye yadda Aliyu yaga Rana haka yaga dare,Ballatana Azeema data kwana kuka durkushe bisa sujjadarta tana kaima Allah kukanta,ada bata taba Tsorata da al"amarin Azeeza ba koda Abunda yafaru abaya,bata tsorata da Abun ba,sai da Abunda yafaru jiya ya Faru,nan ta yarda duk wanda yayi mata wannan sharhi ta tabbata baya kaunarta,kuma bazai taba Sonta,ba ta yarda ta amince bata da wata mafita domin Anrigaya da ansha Shiryamata Ta yarda bata da yadda zata Fidda kanta.

Kokafin Gare ya waye Fuskarta ta kumbura saboda kuka,idanuwanta kuwa sunchanza kala saboda kuka da Tashin hankali,Shiko Aliyu Tunda ya Shiga dayan bedroom din nan ko motsinshi bataji ba,ta nan zaune bisa darduma bayan ta idar da sallar Asuba,tana addu"a tana kuka,karfe bakwai na safe taji bude kofar bedroom din da Aliyu ke ciki,bata fargaba taji Shigowarshi dakin bai ko kalli inda take ba,ya Furta cikin kakkausan murya.."Ki Fito mu tafi malama.."Yafada kafin ya juya zai Fita,jin ta Fashe da kuka ne,yasa ya dakata yana jin wani Abu na mai daci aransa,Kallonta yayi ta gefen ido kafin yace"Bake ya kamata kiyi kuka ba,nine yakamata na koka,don ni kika zalunta,ammh wannan kukan dakike sai ki dinga nuna Cewa ke aka zalunta.."Daga Haka yafice daga dakin yana jin kamar ya kwanta akasa yayi ta kuka.

Azeema na kuka,ta mike daga ita sai Rigar barci wata doguwa Fara mai Ratsin pink ajikinta,Wani dogon hijabinta ke jikinta wanda take sallah dashi,Akwatunanta dake kan gado ta Shiga saukewa akasa tana kuka,dama tun jiya tahada komai nata,Daukan akwatunan tayi daya bayan daya tana kaisu Falo,harda da kayan kwalliyanta babu abunda tabari,ta kwashe komai nata kamar yadda yace,Dan kit din dake hannunta Shine na karshe ta juya tana ma dakin kallon karshe kafin ta kada kai Tafito tana zubar kwallah,koda Tafito babu Aliyu afalon,kamar da Farko data ganshi tsaye,sabanin yanzu sai wani Soja tagani yanata jiddan akwatunanta zuwa waje,kasake tayi tana share kwallah kafin tabi bayanshi zuwa waje.

? ? Tana Fitowa ta iske shi Shida Jabir suna Tsaye suna mgana,ammh dukkanasu Fuskokinsu ba Annuri,balle walwala,baya Taja ta Tsaya tana sadda kanta kasa,Jabir yana ganin ta Fito yatako zuwa gabanta yafadin"Azeema ki taimakeni ki Fadamin Abunda ke Faruwa,tunda shi yaki fadamin,Tun jiya na lura wani abu na Faruwa ammh yamin Shuru yanzu kuma gashi kina kwashe kaya don Allah meya Faru..?"Dago idonta tayi dasuka chanza kala tana kallonsa,hawaye suna kwaranyomata,Wani Tsausayin Aliyu ya Tsirgamata,tana kallonsa tana Jin koba komai yayi mata karamci Tunda ya iya boye wannan Sirri,kasa mgana tayi sama jan kafanta datayi da gudu zuwa wajen motar ta bude gidan gaba Tashiga tana kuka mai cin rai,da ido Jabir ke kallonta yana mamakin wannan al"amari,yana kallo Aliyu yazo ya Rufe gidan kafin ya dawo har zai gotashi sai yadawo da baya ya dafa Jabir yana fadin'Am Srry Dude,bafa wani Abu bane wajen goggo zata koma ta Rubuta jarabawarsu ta candy,shine fa kaga munshiga damuwa,ammh babu wani abu ka kwantar da hankalinka yau insha Allahu zan dawo dazarar na kaita bazan tsaya ba.."Juyowa Jabir yayi yana Kallon Aliyu Shiko yaki yarda su hada ido,Girgiza kai kawai Jabir yayi kafin yace"Allah ya kiyaye hanya..." Daga haka kawai yakada kai ya Wuce,don kwata kwata bai yarda da kalaman Aliyu ba,ammh Tunda yana boyemai bazai kara neman yaji ba.

? Da Hanzari Aliyu ya isa ga motar ya Shiga bayan Sojan ya gama Dura kayan Azeema abayan motar,ganinta Zaune agidan gaba ta saka kanta tsakanin Cinyoyinta tana kuka yasa yayi gaggawar Fitowa yana fadin"Plz ki koma baya don Allah,i don"t want to see u in my Side again.."Tana jinsa tayi Saurin danne kukanta ta Fito da Sauri ta bude gidan baya tashiga tana boye Fuskarta cikin hijabi,Sai da ya bata lokaci kafin ya Shigo motar tana jnsa yana karanto addu''ar matafiya ya Daura Belt suka Sulala,basu bata lokaci ba Suka Fita daga cikin barikin kafin su dauki hanyar Gombe.


Karfe goma da wasu mintina Motar Aluyu tayi Parking akofar gidan na goggo,dayake lokacin yayi safe dayawa,shiyasa layin babu kowa,tsit kowa yatafi neman Halali,mataye kuma suna cikin gida,suna Dafa Abun sawa abaka,idonta biyu

20 / 34