Aliyu Gadanga Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   19 / 34

54K to 57K   out of 101.5K words

wacce ta taka arayuwarshi irinta,ita goggo Amtsayinta na uwa wacce ta haifeshi kuma ta raineshi,Itako Azeema amtsayin Matar kaddara,ta Rufin Asiri kuma uwa uba kuma macen Sauke Nauyi da bukata,Domin ta shayar dashi zumar da babu macen data taba shayar da wani irinta..Anaka zaton kenan ba Ruwana Dota Rahma na jinka=??=??
? ??

juyawa yayi zai Fita daga bedroom din sakamakon wayarsa datakeneman Dauki,har zai Fita saiya waigo yana fadin"In kin gama Shiryawan,ki Sameni Afalo..."

??

?? *Comment,Share and Vote...*
?? *Janafty....*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty=???_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA=??Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*'

? ? ? *Chapter 22*

? ""Yagama amsa wayan kenan Ta fito da hanzari ta tsaya agabansa Tana fadin"Ya? kaganni yaya captain nayi kyau ko? fadin haka yasa ya dago yana kwaremata kallo ido ya zaro yana rike baki Abun mamaki sanye take da wasu riga da wando cikin kayansa Kayan Red and black ne na? JC ne Wandon yayimata Daidai buh rigarta tayimata yawa Don tayimata burmeme tana yawo aciki,Sai kirjinta daya taso,Wani Half cover din takalminta ta saka Wuyanta kuma yane da wani jan vail ta nadashi akanta sai yayi mata kamar Karamin breziya Hijab,Mirmishi take sakarmai Tana juyamai take kara cewa!Daga yau na samu kayan Motsa jiki yaya captain wlh sun man kyau"Tafada tana rike kugu.

Ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya saka hannu yana Shafa sajensa yace"Eh sun miki kyau kam,buh kinsan meyasa zan barki ki Fita haka..?"girgiza kai tayi tana kallonsa Mikewa yayi yana fadin!"Cuz kayan bai kamaki ba Sosai wlh tallahi da bazaki taba Fita dasu ba,kuma as From day ma ko kukan jini zakiyi ba inda zaki bini yarinya.."Yafada yana hade rai bai san meyasa yaji ranshi yabaci da shigarta ba,Saboda kishin yadda maza zasu ganta ahaka.

Kwabe Fuska tayi zata fara kukan Shagwabanta ya karkace kai yacemata"Don"t Start Ohhh.Don kina min kuka wlh zan canza Shawara.."jin haka yasa ta gintse baki tana gyada? kai Hanyar waje yayi yana Fadin"Ki sakomana Ruwa kizo mana dashi.."Jin haka yasa ta ruga kichen ta dauki wani karamin gwando ta saka musu Ruwa da lemuka ta zage gwandon ta dauko koda ta fito har Aliyu ya Fita da hanzari itama ta fito wulka idon ina zata ganshi A compound din gidan ta ganshi yana Tsaye ya juyamata baya bayan ya zuba duka hannuwansa cikin aljihu,Ganin haka sai tayi mirmishi bata sakama gidan key ba, sai ta barshi haka,Tunda ta lura yau mai gidan yana kan gaba ne,a natse ta cinmai Tana fadin"Oya let go Zauji..."

Jin Abunda tace ne yasa yadan kalleta kafin ya kada kai yafara gudu gudu kadan kadan itakuma tana binshi abaya,ganin yafara gudu da sauri yasa itama tafara gudun kadan kadan,bai waigo ba taji yace"Stop in bahaka ba zaki koma gida Juz wach me."Yafada muryansa A cushe,Cak ta tsaya tana kallonsa yacigaba da gudunsa,ya mike wani shatataletalen Titin dake gaban gidajen nasu har yabacema ganinta.

Ajiyar Zuciya ta sauke kafin tafara Tafiya anatse dauke da kwandon ahannunta tana waige waige domin Sojojine keta wayo ammh ba sosai ba dayake ranar Hutune, yawancinsu basu Riga Sun Fito,tayi nesa hartabar layin gidajen bata saka Aliyu a idonta ba,Tana tafiya tana ta waige waige koda taci karo da wasu sojoji suna nasu Gudun rage Nauyi basama kallonta balle tasaka ran zasu yimata mgana,Tana waigen ne takusa yin Tuntube ta fadi,sai ta dawo daidai kana ta maida hankalinta agabanta gabanta ne ya fadi tayi baya zata juya sai kafarta ta hardeta tayi baya zata Fadi,da duka bakinta tasaki zata saka ihu? bayan Kwandon dake hannunta ya kufcemata,sai taji tafada kan wani Abu mai Taushi da kamshin dadi,lokaci daya yasaka tattausan hannunsa ya Rufemata baki yakuma jata jikinsa ya Rumgume yana sakin ajiyar Zuciya.

Kamshin Turarensa Shi yasa tagane ko waye dago kanta tayi tana kallonsa kafin tace wani Abu ya rigata da cewa"Sarkin Tsoro..."Yafada yana lakucemata hanci Shagwabe Fuska tayi kafin ta waiga tana kallon Hoton Sojan da"aka Zanashi da Dustse yana tsaye da kakin Soja Fuskarnan ba Fara"a ga bindiga ahannunsa irin Jigidarnan ya Saita ta dashi,lokacin data ganshi wlh ta zata mutum ne harbinta zaiyi Shiyasa ta tsorata.,kara kallon yaya captain tayi tana fadin"Wlh na tsorata ne yaya captain na zata mutum ne fa,ya saitani da bindiga zai harbeni.."Yar dariya yayi kafin ya duka ya dauko kwandon datayi wachakali dashi riko hannunta yayi yana fadin"oya mu koma gida,Tunkafin kijima kanki Rauni saboda Tsoro,don akwai irin wadanan dayawa acikin bariki nan.."Matse hannunshi tayi suka juya suna tafiya dora kanta tayi bisa kafadanshi tana fadin"Nifa Tun Asali dama ina da tsoron Soja don yana bani Tsoro.."kumatunta yaja yana fadin"Toh yanzu fa? bake ta mele tana fadin"laba'asa..."bata Rufe baki ya ciccibeta yana fadin"Muje sai ki tantace,yarinya kin mori soja ga karfi ga kuzari kina wani Basarwa ko."Dariya take tana riko wuyansa take fadin"Na Shiga uku,wlh ina son soja yanzu,koni na yada da karfinka.."Take fada tana dariya shima Dariyan yake,Duk sojan dayazo wucewa tunda yawancinsu suna karkashinsa ne,sai dai kaga yakame yasara kafin ya wuce,shiko ko kallo basu isheshi ba,Wo soja mazan Fama kenan.

?? Suna kawowa kofar Apartment din Jabir,sai gashi sun cikaro dashi ya fito yana daure igiyar takalminshi Aliyu na ganinshi sai ya barsa ta gabanshi suka wuce Azeema na kyalkyala dariya dagowa Jabir yayi jin muryan Aliyu na fadin"yau zaki sani ne yarinya haha..."Yake Fada yana kara riketa Da ido da baki yake binsu da kallo Hannunsa a kugunsa har suka isa kofar gidan Aliyu saboda mamaki Jabir harda leke yaga Aliyun kodai kama ne,aiko sai da Aliyu ya shiga kana ya waigo yama Jabir gwalo ya maida kofa ya rufe,baya Jabir yaja yana Sakin Huci kawai ya wuce yana ayyana Abubuwa dadama dazai rama Abunda Aliyu kemai in yayi Aure.

Tundaga Falon sukafara Rikita juna,Aliyu ya Ruda Azeema da salon yadda yake shafata,itama ta Rudashi da salon yadda take lasan gefen wuyansa cikin kwarewa dakyar suka yada zango abedroom aka Shiga Second Round na biyu,lalle Azeema ta Fahimci gidan Soja ba wajen wargine bane sai da ta dinga hadawa da roko da kuka da magiya kana ya Saurarata mata,ammh bawai don ya gaji ba,Lakwas tayi ajikinsa tana kananun kuka ya Rumgumeta yana dariya yake fadin"Srry pretty Za"a bani na anjuma..."Harara ta dago ta makamai harda murgudamai baki,Saurin Cafke lebenta yayi yana Tsotsa sai da ya sha ma"ishi kafin ya saketa yana fadin"Horo mai hade da gargadi ko hararata kika kara wlh sai na kara.."Jin haka yasa tayi gum da bakinta tana kara lafewa akirjinsa Rikota yayi dakyau yana fadin"Afuwa Afuwan Zeema kaduna,Allah ya biyaki Kinji matata ngd sosai Nasan ke Jaruma ce,Tunda kike iya daukan Nauyi Aliyu.."Yafada yana leka Fuskatarta Kin yarda tayi saima kara dunkula kanta da take bisa kirjinsa tana shagwaba Shiko yana tsokanarta yana dariya Ahaka barci ya kwasheta Shiko Shuru yayi yana Nazarin yadda rayuwarsa ta chanza lokaci daya ta dalilin Azeema Kanta ya Sumbata yana fadin" *I LOVE U AZEEMA..Buh not Azeema gombe i mean ZEEMA KADUNA.* yafada yana dariya Shikadai.

??
___________________

? _Gombe_

? ? ??
? ""Azeeza tana ta Sauri zata gida tadawo daga shago inna ta aiketa Siyo suga alokacin da misalin karfe Goma ne na safe,Taji Sauki ba kamar da ba,ammh haryanzu ramanta na nan da yadda duk Fuskarta ta chanza,Saurin datake Shiyasa bataji karan hon din da suke zubamata ba,sai da suka zo gabda da ita suna Rangadamata sallama.

Afirgice ta waigo take kallonsu Suna zaune cikin wata bakar Venza mai kyau da yarari,Dukkansu matane,sanye kuma da bakaken abaya kowacce tayi Rolling din kanta da dan gyalen Abayan bisa kanta,kallo? Farko tayi musu ta Fahimci tsantsan wayewa tare da Hutawa atare dasu,wacce ke zaune gefen mai zaman banza ne,tacire wani babban glass wanda yakusa cinyema rabin fuskarta takalli Azeeza a karkace tace.

? "Ammr? don Allah baiwar Allah Tambaya muke? Da mamaki Azeeza ta tsaya tana gyara mataccen hijabin jikinta tana fadin"Toh Allah yasa na sani..."Kada kai tayi kafin tace"Gidan Su Captain Aliyu muke nema? Kur da ido Azeeza tayi musu tana kare musu kallo,lokaci daya zuciyarta da gangan jikinta suka bata Ni"ima ce,mirmishin Nasara ya subucemata kai tsaye tace

? "Wani Captain Aliyun? badai wanda ke aiki a barikin kaduna ba..? Saurin Amsamata Muneera tayi tana fadin"Yes Shikuwa don Allah ina ne inda mahaifiyarsa ke zaune..? Baya Azeeza taja tana nuna musu gidan goggo tada wuto tana fadin"Kun ma zo kan gaba ai ga gidan nan..'tafada tana wani mirmishi Waigawa sukayi Atare suna kallon gidan kan Munera tace"Ok tom mungode baiwar Allah..."Tafiya Azeema tafara tana fadin"Ah bakomai yiwa kaine.."Tafada tana kara Sauri ta Shige gida,Suko Ni"ima tayi Ribas suka koma gidan goggo dabaya baya,kafin kuma tayi kwana su Faka motar daidai kofar gidan,Dukkansu suka Firfito suna bin gidan da kallo,dama layin gabadaya Yamutsa Fuska munera tayi kafin tace"Tabdijam waima Ahaka wannan gidan shine Gra,Gaskiya na Raina samun Captain din naki.."

? Wani banzan kallo Ni"ima ta watsamata kafin tace"plz Sweetheart u better mind ur tok in bahaka ba zaki iya komawa gida nagode da taimakonki..."Kallonta Muneera tayi kafin tace"Au hakane toh Allah baki hakuri.."Daga haka taja bakinta ta Tsuke tana bin gidan da wani kallo,Ko kallonta Ni"ima batayi ba,Ta sanyama motar key din Rufewa kan Ta nufi gidansu Captain kai tsaye,bayanta Muneera tabi tana mamakin Soyayyar wahalar da Ni"ima take ma Captain,in don kyanshi ne akwai alot mazan da suke da kyau kuma suke hauka akanta buh ammh ita ta nacema Namiji kwara daya sai wahalar da ita yakeyi.

?

Goggo na cikin Daki ta hakimce Afalonta tana kallon Arewa Aminu shariff Momo,na gabatar da Shirin Sharhim Fina Finan mu,gurguru ne cikin wani dan Roba tana afawa abaki rabin hankalinta na wajen kallo,Taji ana ta sallama Daga dakin ta amsa tana mikewa,zanin leshin dake jikinta ta gyara kafin ta Daga labulen dakin tana Fadin"Wa"alaikas salam..."Tafada suna hada ido hudu da Ni"ima.

?? Kallon Sama da kasa Goggo ke jifan Ni"ima dashi kafin tace"Daga ina bayin Allah...? Muneera dake bayan Ni"ima ta bayyana Fuskarta dauke da wannan Gilashin tace"Muna neman mahaifiyar captain Aliyu ne..? karkace kai goggo tayi tana fadin"Ayyah Gani,Ina Fatan lafiya ko? ta Fada tana kallon Ni'ima wacce kanta ke kasa,Mirmishi Muneera tayi kafin tace"Eh toh lafiya ba lafiya kawata ce tazo Rokonki wata alfarma.."Sakin labulen Goggo tayi tana fadin"Ku Shigo ku zauna,Allah yasa zan iyamata alfarma datazo roko.."Haka kurum goggo Ranta yabata Ni"ima ce,Duk da bata taba ko ganinta ba.

Suko ganin Farko Da sukayima goggo suka ga kamarta da captain duk da A fizgene yake kama da ita,Falon suka Shigo Kai tsaye Ni"ima tanemi waje ta zauna,itako Muneera tana ta karema falon kallo tana yatsina baki,Kafin ta nemi waje ta zauna,Kichen goggo ta Shiga Ta dauko musu Ruwa kafin tazo ta zauna tana fadin"ga Ruwa kusha.."Dan mirmishi Ni"ima tayi tana fadin"mungode goggo,munsha Ruwa.."Tafada tana sadda kanta kasa.

?? Da ido Ni"ima tayi ta ma Muneera alamar tayi mgana,gyara zama tayi kafin tace"Sunana Muneera,ga Ni"ima nan Munzo rokonki alfarma ne Akan Don Allah kibama Captain hakuri yadawo ya Aureta wlh ba laifinta bane laifin Mahaifinta ne,kuma Shi yayi Nadama wannan karon bazai kara gaddama ba,Don Allah ki taimaketa Tunda Abun nan yafaru bata kara lafiya.."Tafada tana kallon kwayan idon goggo.


? ? ? Gyara zama goggo tayi tana fadin"Allah Sarki to ai ni bani da keda ikon zaban ma Gadanga Abunda yadace dashi ba,Da farko Shiya zaboki da kankishi don yana ganin kin dace da Ra"ayinshi,daga karshen mahaifinki ya hanasa ke,saboda wani dalili nasaa? mara tushe,toh barikiji na gayamiki koda gadanga bai yi Aure ba, ni mahaifiyarsa bazan taba bashi goyon bayan ya Aure ki ba,Saboda na nuna muku babu wanda aka haifa baida Uba,yanzu ku tashi kikoma wajen mahaifinki domin ni babu Abunda zanyi iya miki,Tunda haryanzu gadangar bai Kawo Asalin Uban nashi ba,ba Shi mahaifinki yace sai yakawo zai bashi ke ba.?.,"Tafada hankalinta kwance.

Tunda goggo Tafara mgana Idanuwan Ni"ima suka tara kwallah,tana gama mganar hawaye suka zubomata Mikewa goggo tayi tana fadin"Ngd ku gaida gida..."Daga haka tashige bedroom ranta bace,Muneera dake zaune ta mike ta isa ga Ni"ima tana rikota lokaci daya tana fadin"Kinji kingani ko? dama narigaya dana Fadamiki zamu wahalar da kanmu oya tashi mutafi..."Mikewa Ni'ima tayi tana kuka kamar ta Shide Hannunta muneera ta rike suka Fito daga dakin tana Fadin"Kinga ki cire Captain Aranki don ni banga alamun Nasara ba,Yadda yake baida Mutumci haka uwarsa take,gado yayi.."Tafada suna Ficewa daga gidan,Suna zuwa kofar gidan sukaci karo Da Azeeza jingine jikin motarsu tana kallonsu tana mirmishi,Cak suka? tsaya suna binta da kallon mamaki kusa dasu ta karisa tana fadin

? "Dama nasan bazakuyi Nasara ba,Don goggo bazata taba Sauraranku ba..."Kallon mamaki suka bita dashi kafin Ni"ima tace"Wacece ke? Mirmishin kasaita Azeeza tayi kafin tace"Sanin wacece ni bazai miki amfani ba,Abun da zaifi miki amfani Shine yadda zaki mallaki Abun Kaunarki Captain.."Zaro ido suka atare suna mata wani kallo ganin haka yasa ta juya tana fadin"Au naga baki Shirya ba,in kin Shirya kya nemeni,Sunana Azeeza..."Tana fadin Haka tafara Tafiya da hanzari Ni"ima tataka ta rikota tana fadin"Konawa kike bukata zan biyaki matukar zan mallaki Captain,.."Waigowa Azeeza tayi tana dariya kafin ta harde hannunuwanta akirji tana Fadin"Bada kudi nake so ki biyani ba,Zamu Taru ne mu Taimaki juna..."Da Hanzari Muneera tace"Kinga Baiwar go to d point,meke tafe dake."Mele baki Azeeza tayi kafin Tace" _KI RABASHI DA MATARSHI AZEEMA NI KUMA NAYI MIKI ALQAWARIN MALLAKANSHI AMATSAYIN MIJINKI.._"

? ?
Wani banzan kallo Muneera tayimata kafin tace"Toh mukuma meye hdinmu da matarsa,kinga Sweethrt muje inaga wannan yarinyar Mahaukaciyace.."kin tafiya Ni"ima tayi ta tsaya tana kallon Azeeza kur da ido kafin tace" Indai kin tabbata zaki Rike alqawari nikuma nayi miki alqawarin Farraqu tsakaninsa da matarsa.."Mirmishi Azeeza tayi ganin taci Nasara kawai sai ta juya tana fadin" Da Zarar hakan ya tabbata ina miki albishir da Kin gama mallakan Captain..."Tana gama Fadin haka tafara tafiya zuciyarta cike da Farinciki cin Nasara Allah ne yakawomata Ni'ima wacce zatayi Amfani da ita wajen cinma burinta daga karshe in tayi Nasaran Raba Aliyu da Azeema,ita kuma sai taji da Sauran Aikin domin na Ni"ima mai Sauki ne,wani lungu Azeema tabi kamar irin zata gidansu din,don bataso su gane gidansu.

Har Suka Shiga mota suka bar anguwan,Muneera nayima Ni"ima Fadar Sauraran Azeeza da tayi ko kallonta Ni"ima batayi ba ta Zurfafa Tunani lokaci daya takalli Muneera tana Fadin" *Aikin? CONOLE SULAIMAN ya tashi Sweetheart...'Wani kallon Muneera ta mata tana fadin"Bangane aikin S??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ulaiman ya tashi ba,me kike shirin aikatawa.."Bata kalleta ba tace" Shine zai Raba Tsakanin Captain dina da matarsa,kinsan yana gaba da Captain awajen aiki,so Shiga bariki bazai ma wanda zamu bama aikinmu wahala ba.."Kuri Muneera tamata ido,itama tana kallonta kafin su kwashe da dariya Atare Muneera tace"Indai ko hakane Rabuwa zasuyi har Abada balle kinsan Captain dinki da zuciya may be ma kila ya gangara da ita lahira.."Ni'ima ta amshe da Fadin"Ko kuma ta yanki Tikitin zama na Din din A asibitin kashi na kano ba.."Dariya Suka kara sakawa harda Tafawaa kafin su cigaba da tattaunawa yadda Abun zai kammallah cikin lokaci.


? ? Am Srry For d Typing Errors.

?
*Intelligent writers Asso.*
*Janafty....*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty=???_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA=??Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*'

? ? ? ?? *Chapter...23*

*BAYAN WATA DAYA*

?? ""Acikin wata daya da Tarewar Azeema Fadar irin cigaba tare da zaman lafiya,dakuma wata soyayyah dasuke nuna ma juna bata baki ne,Tsayawa Lura da yadda suke kaffa kaffa da juna sai ka dauka sun Shekara goma ne,suna Soyayyar,uwa uba ga wata shakuwa daya Shiga tsakaninsu,Azeema ta yarda takamu da Son yaya captain kamar yadda Shima yakamu da Sonta duk da bai Furtaba tana gani a aikace.

? Taje gidajensu Anty madina da Anty mardiya sau daya,sai gidan Kawu dasukaje Sau biyu,dukkansu sun samu kwanciyar Hankali sunyi kiba sunyi kyau kamar basu ba,Kowannensu Kokariin Farantama dan"uwansa rai yakeyi kowa bayason ganin bacin ran Dan"uwansa baza"ace basu taba samun sabani ba,A'a Suna samu buh baya wani Tasiri suke bama juna hakuri domin dukkansu babu wanda zai iya Rashin dan"uwansa,Tuni Azeema ta Manta? da wata Aba Azeeza da inna Ramatu mahaifinta dai take kira taji yaya lafiyarsa sai goggo wanda bata iya kwana bata kirata ba,Tarigaya tazama wata ginshiki agareta.

Lokacin Jarabawansu ya kusa Aliyu sukayi mgana da goggo yace in lokacin yayi zaizo da kanshi yayimata Rigistration Allah barshi in lokacin Yin jarabawan yayi sai ya maidota ta Ta rubuta ahaka suka rabu,wanda ko Azeemar batasan kwanan zencen ba.

_________________

? Conole Sulaiman yana zaune cikin kayatattacen Falonshi na cikin Barikin,yana hutawa gefe daya kuma Sigarice Ahannunsa yana ta zuka yana Fidda hayaki,daga ganin yadda yake sarrafa zakasan ya kware, wayarsa dake gefensa tadau Tsuwa yana dagota ya zaro ido yana mamakin mai kiran da rawan jiki ya daga kiran yana fadin

? "Allah Taimaki Hajiya Muneera yar Mutan gombawa,yau kuma an Tuna dani ne, bayan tsawon lokaci An samu akwandon shara.."Wata dariyar kissa muneera tayi kafin tace"Har na isa?ka manta hausawa na cewa Da tsohuwar zuma ake mgaani,"Dariya ya saka yana Fadin"Hakane kuma ta wajena,Allah yasa wannan kiran an min ne,domin kashemin kishirruwan ki ko? Dariya ta sheke dashi kafin tace"Sha kuruminka Gani A main gate dinku an hanani Shigowa.."Yana jin haka ya mike yana washe baki yace"Karki wani damu bari nayi musu waya.."Yafada yana katse wayan,Chan main gate din ya kira yace Su barta ta Shigo bakuwarsa ne nan da nan ko suka wangale mata get,ta sulala ciki,haka sauran get din suma Tuni Umarni ya ishesu,Tana Shiga ciki dama Tuni tasan Apartment din na Conole Sulaiman,suna chan gaba Sai ansha tafiya akwai dan tazara tsakanin nasu dana su Captain Aliyu,Kuma kowanni gida yana da nombarsa da sunan Sojan dake zaune agidan,sai da tayi gaba kadan da Apartment din Aliyu kafin naga ta tsaya baya ta juya inda naji ta Furta.."Come out..."Tafada kai tsaye.

? Bayan motan naga Wani Saurayi ya Fito yana kara gyara wani bakin kyallen? dake Fuskarsa wanda yake sanye da Riga da wando black and white,Kallonsa tayi kafin tayi pointing din gidan Aliyu tana fadin"Ga gidan chan,Kayi maza kuma kayi komai da lura,and don't forget kada kabari akamaka ko aga Fuskarka saboda nan bariki ne,yana da tsaro sasai so u better Carefully kaji ko"gyada mata kai yayi yana fadin"Karki wani damu aikina ne fa,Glass din Fuskarta ta gyara kafin tace"Ok lokacinka yafara daga yanzu.."Tana fadar haka ya bude murfin mota ya Fito yana kalle kalle,lekowa

19 / 34