Aliyu Gadanga Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   12 / 34

33K to 36K   out of 101.5K words

cika tsawo ba,ammh yadace da kyakyawan Fuskarta tana gashin gira hade dana ido Masu kyau da Tsari bakinta dan karami ne,ammh leben sama yafi na kasa girma da kadan,in ta tsuke bakin sai ya birgeka yakuma baka Sha"awa doguwa ce bata da jiki,ammh tana Fadin kugu da kirji mai kyau kirjinta ba"a cike yake ba,sakamakon nonuwanta basu da wani girma na azo agani ammh Suna tsaye cur dasu,zarazaran yatsun hannunta yakoma yanabi da kallo kawai lokaci daya yaji ya tsaida kallonsa kan dokin wuyanta yadda wasu kananun gashi suka kwanta awajen,cikin kankanin lokaci tsigar jikinsa tafara tashi lumshe manyan idanunsa yayi kafin yakira sunanta.

? "AZEEMA...."Cikin Sanyin murya da muradi bata amsa ba,ammh sai tadago tana kallonshi saboda jin muryan dayayi amfani da ita wajen kiranta idanunsa ya bude fess akanta yana kallonta sadda kai tayi kasa kafin ta amsa.

? "Na"am..."gyara zama yayi kafin yace"Don Allah tambayanki zanyi waht i want is to tell me,d truth kinji ko.."Gyada mai kai tayi kafin tace"Toh insha Allahu."good yafada kafin yaciga ba da cewa,"Ina so kifadamin hakikanin meke damunki?mekike bukata?me kika nema na Halin Rayuwa kika Rasa Azeema,in mganar Gidanku ne,yanzu kin dawo nan buh ammh har yanzu abubuwanki basa raguwa sai karuwa don Allah kifadamin meye ke damunki kokuma miye matsalarki? kudi? mkranta kikeson achanza miki? kokuwa baki son zama da goggon ne natafi dake kaduna ai zaki zauna abariki ko? Duk Abunda yake fada tanajin sa,wani tsausayin kanta ya kamata tare da Tsausayin yaya captain,jin Abunda yace na karshe ne yasata dago kanta tana mirmishi ammh hawaye sun cikamata ido kai tsaye ta girgiza kai batayi mgana ba,Hade naman goshinsa yayi kafin yace"To meye? kifadamin meke damunki kinganni nan banda yawan mgana i know ahaka halittata take buh ur own Azeema yayi yawa baki da sakewa ko kadan.."Yafada da alamar Abun ya dameshi.

? Dago kanta tayi tana kallonsa kafin tace"Hakika in nace nayi rashin wani Abu toh na zama butula babu Abunda na nema na rasa kuma ni babu Abunda ke damuna,in akwai Abunda na Rasa arayuwata abu dayane yaya captain..'kallonta yayi kafin yace"Maza fadamin meyeshi nikuma nayi miki alqawarin mgance miki duk wani Abunda ke damunki.."tadade kanta asunkuye kafin tadago idanunta na fitar da amon hawaye tace muryanta na Fitar da amon kuka.. *UWA...UWA..* ita na rasa yaya captain na rasa uwa wacce zata nunamin banyi daidai ba in gyara! na rasa uwa wacce zatamin fada ko tabani shawaran in wata mtsala ta sameni!,na rasa uwa wacce zan kwanta bisa kafadanta nayi kuka ta lallasheni!na rasa uwa wacce zata kalle ni ta sakamin albarka,duka na rasa wannan yaya captain na taso arayuwata nikadai nake gudanarshi,babana yana Sona ammh tsoron inna ramatu baya barinsa ya kebe dani ballatana har yasan damuwata na kasance duk wani damuwa da zan Shiga sai dai nayi kuka adaki ni kadai na lallashi kaina bani da dan"uwa ko wani Shakiki da zan Fadama damuwata yabani Shawara haka nake rayuwata nikadai,toyaya kewa tare da damuwa bazasu taru sunman yawa ba,ka fadamin yaya captain Tayaya...?Tafada tana Rushewa da kuka kamar zata shide.

Gabadaya kalamanta ya Sakashi jin wani tsabar tsausayinta ya kara mamayeshi kallonta yake tana kuka lokaci daya Shima damuwarshi ta dawo sabuwa,yasani shi mahaifi ya rasa ammh Goggo da kawu bala basu taba bari yayi kukan maraici ba,koda aboye koda asarari ne,itafa bata da kowa ba uwa ba,ba uba mai kula ma dangi ba wani dan"uwa sai da wanda Allah yaduba ya tsausayamata tabbas tafishi jin dacin rashin Abun Aranta fiye da yadda yakejin nashi Aransa.

Saboda tsausayinta baisan sadda ya mika hannu ya rikota ba,ya kwantar da kanta bisa kafadanshi yana bubbuga bayanta yana fadin"shiiiii....am srry kinji Stop Craying i promise i won let u down insha Allahu..."Yake fada yana sharemata hawaye da hannusa,gyara mata zama yayi suna facing din juna yace yana riko hannuta"Yanzu Firstly do u luv me,zaki zauna dani duk da ana ce nidin bani da cikakken asali wasu ma cewa suke bani da uba..? dago kanta tayi tana kallonsa dan hararansa tayi kafin tace"injiwa..? haba dai suma wasa sukeyi.." karkatar dakai yayi yana fadin,"Eh mana ko,kin manta dalilin haka aka hanani Auren Ni"ima Shine ma dalilin dayasa Auren yakoma kanki.."yafada yana cije lebe,kallonsa tayi kafin tace"Kayi hakuri haka Allah ya kaddara itadin ba matarka bace,..Kayi kokarin cire sonta aranka sai kaga komai ya wuce.."Zuru yayimata da ido kafin yace"who told u cewa haryanzu am in luv wit Ni"ima.."Sadda kai tayi taki mgana girgiza hannunta yayi yana fadin"Kiyi mgana waya fadamiki.."Kai tsaye tace"Azeeza ce..."Ware ido yayi kafin yace"Ohh i seee... wato ita ta zaunar dake ta tsaramiki haka,to kila ni nafadamata ko.."?yafada Fuskarsa na chanzawa saurin cewa Azeema tayi"A"a ni batace kai kafadamata b..."Toh meyasa kike yarda da duk Abunda tace miki,kina zaton ita da mahaifiyarta suna kaunarki ne,kinga dole fa in kinaso tamu tazo daya dake Azeema u should learn how to respect ur self,kiwani zauna yarinya karama na zana miki zence kawai don ta maisheki mara wayau.."yafada cikin Fushi Saurin Sadda kai tayi kafin tace"Kayi hakuri baza akara ba.."tafada tana Kwace hannunta ita tsoronta kada ya zuciya ya kaftamata mari.

??

? ? Sakinta yayi yana fadin"it ok kikiyaye gaba,komai ta tambayeki as From today karki bata wata fuskan da zata sake sanin Sirrinki kina gaba da ita,ita din kanwarki ce so be carefully...'Yafada yana kauda kai shuru tayi tana wasa da hannunta kafin bazato yaji ta jehomai tambayar

? "Toh in kadaina son Ni"ima wakake so..? saurin kallonta yayi yana hade naman goshinsa Cike da mamaki saurin sadda kai tayi,cike da kunya Dan dariya yayi kafin yace"Ada nasota lokacin danake Tunanin Ita zatama abokiyar rayuwata buh tun lokacin da mahaifinta yanemi cimin zarafi naji tafita daga Raina,any way kobana sonki Azeema kinada wani babban mtsayi Araina keda mahaifinki domin kun sharemin kasan da mahaifin Ni"ina ya watsamin.."Yafada yana kallonta kur da ido,kallon ne yabata kunya tayi Saurin tashi ta fice waje da gudu,da wani kallo yabita yadda kugunta ke kadawa rausayar dakai yayi yana cije baki,nan take mganar Jabir ta fadomai Aranar da"aka daura musu aure....

? _Yarinyar tayi zaka samu duk Abunda kakeso wajen mace,tama fi Ni"imar komai..._Tuna haka dayayi ne yasashi shan mur yana kunkuni shidakai na yadda har jabir yarigashi gano Abunda shi yakamata yafara ganowa.

? Azeema na Fita waje tacikaro da goggo daga gefe zaune kan wata kujerar roba dake wajen tana cin gyadanta soyayyiya hankalinta kwance baki Azeema ta rike kafin tace!la..Goggo yaushe kika dawo.."Kallonta tayi kafin tace"Na jima Azeema.."Karisawa Azeema tayi tana fadin"wlh goggo bamuji shigowarki ba.."Goggo tace"Ai bazaku ji ba,na Shigo ina ta rafka sallama har daga makota anajina,harfa leka dakin nayi naga ko barci kike sai na samu ana zantawa tsakanin mata da miji,shine nace toh toh..Bari nayi baya har kugama kada na katseku.."Tafada tana dariya kunya takama Azeema sai ta labe bayan goggo tana yar dariya.
?

? Gyadar goggo ta nunamata tana fadin"kega Abunda baba Ade tabani tace sai kinzo zaki karbi naki.."mikewa Azeema tayi tana fadin"la gyada goggo,yanzu kuwa zan mata dirar makiya sai tabani nawa.."tafada tana fadawa daki,koda ta shigo sai taga kamar gadanga na barci sai ta shige kurya tadauko Abayarta ta fito harta kai kofa zata fita taji ance daga bayanta.."Ina zaki..?"Saurin waigowa tayi still idanunsa na kulle,cewa tayi"Gidan Baba ade zani.."lalle yarinyarnan to ki koma ki cire hijabin sai gobe yanzu yammah tayi.."Ya bata amsa.

? Tura baki tayi da jin Abunda yake cewa,bude idanunsa yayi karaf ko suka hada ido dashi ga gudu ta kariswa bedroom din goggo tana dafe kirji,shiko mamakinta ne yacika ashe ta iya tsiwa dama,mirmishi yayi shi kadai kan yamike agajiye ya fice nan waje yaga goggo suka gaisawa alwala ya daura yafita sallar mangariba,itama goggo tayi nata ta shiga ciki tayi sallarta ita da Azeema wacce goggo kema gwalo da dariyan hanata fita da gadanga yayi sai mata kwalelen gyadan takeyi itako duk Haushi ya cikata sai da goggo tagama jan mata rai kana tabata gyadan,shiko gadanga a massallaci ya zauna har akayi issha,"i kafin yakoma gida,kuma bai ma koma barayin goggo ba yashige daki yayi Shirin kwanciya saboda gajiya.

? ? ? ****************

? "Oh my god Sweetheart don Allah kibar wannan kukan,bai da wani amfani juz keep praying in Captain mijinki ne,ko duk duniyanan zasu hadu wlh basu isa suhana ba,kuka bai da wani amfani..."Muneera take fada tana Riko Hannun Ni"ima,Share hawayenta Ni"ima tayi kafin ta dago idanunta jajir Tace"Ya zanyi Ya kikeso nayi Sweetheart..Wlh i love Captain Bazan iya hakurin rashinshi ba,bakiji menake fadamiki bane,he told me bazai taba Aureba Sweetheart,yayi Aurensa ya barni."Tafada wasu hawaye suna kwaranyomata, Rumgumeta muneera tayi tana lallashinta tana fadin.

? "Nidai ki daina yawan kukan nan Sweetheart..Wlh banijin dadi,insha Allahu captain Sai yazama naki da yardan Allah..."tafada tana bubbuga bayanta Lamo Ni"ima tayi tana Shesshekan kuka ahaka Mami tazo ta samesu Tana tsaye tace"Kingan ta nan Muneera haryanzu kukanta yaki karewa,Ni narasa wannan bala!in,sai kace Aliyun ne, kadai Namiji aduniya ko Rasashi Tamkar rasa rayuwace gabadaya,Allah tun inajin Tsausayinta hartakoma bani Haushi,ai sai kiyita kece keda wahala.."Tafada kafin tafice Cikin Fushi da nuna Abun ya dameta.

? Bayanta Ni"ima tabi da kallo hawaye suna kwaranyomata,Zame jikinta tayi ta mike Tafada bedroom dinta tana sharan kwallah,bayanta Muneera tabi da kallo tana mamaki wani irin sone Ni"ima kema Captain data kasa hakura dashi Tunda yayimata nisa,gabadaya ta rame ta dishe ta lallace kamar ba ita ba,Abun nacimata Tuwo akwarya ammh babu yarda zatayi domin hartagaji da ba Ni"imar baki tahakura takoma ta zuramata ido saboda al"amarin nata yawuce duk yadda bawa zaiyi tsammani.

?? ______________

Azeeza ko alama bata ja da baya ba,Abunda yakara bata tsoro ko School Azeema bata nemeta ba Abun ya matukar Dauremata kai,tafara Tunanin kodai ta ganotane ammh duk da haka bata ja baya,ba washegari dataje mkrantar agaban idonta maikeken yazo yayi Dropin din Azeema kuma Abunda kowa bai sani ba Duk motsin Azeemar a idonta domin tana labe akofar gidansu tagazuwam mai keken yazo Daukan Azeema,batayi mamaki ba,tasan kila aikin yaya captain ne,don taga He is very smart yana da Saurin Ramfo mutum tana ganin Azeema ta Shigo cikin mkrantar ta nufi ajinsu sai ta chanza shawara sai tabaro ajinsu ta ratso ta tsakiyar mkranta kamar zata office din Principal nan sukacikaro da Azeema wacce ke kallon Azeezar Tunda daga nesa tasha mur tana kallonta ammh ta kauda mata kai.,Kiran ta Azeema tahauyi ammh Azeeza tayimata banza kamar bataji ba,da hanzari Azeema tatake mata baya da dan gudunta sai gashi tasha gabanta tana fadin"Haba Azeeza mgana fa nike miki ke man banza.."Wani kallo Azeeza ta maka mata kafin ta raba ta gefenta zata wuce,ammh sai Azeema taki bata damar haka Ta hanyar riko hannunta.

Cak Azeeza ta tsaya ammh bata waigo ba,juyo da ita Azeema tayi tana fadin"Wai Azeeza duk miye ya faru ne ? nine fa Addanki Azeema ai yaci komiye nayi miki bai dace nayi mgana acikin mutane ki tsinka ni ba.."Yamutsa Fuska Azeeza tayi kafin tace"Dole na Tsinka Adda Azeema naga kin zabi Namiji,Namijin ma bare akaina,kinga ai sai naja baya.."Ware ido Azeema tayi kafin tace"lala..Injiwane Duk duniyar nan ina da kamarki ne.."Bata Fuska Azeeza tayi kafin tace"ba gashi ba,Tunda har wanda aka lakaba miki amtsayin mijinki ya iya cimana mutumci dagani har ke da baba ba wanda ya ragamawa.."Tafada harda matso kwallah Zuramata ido Azeema tayi kafin tace"Shi yaya captain din? da hanzari Azeeza tace"eh mana Ranar dana biya miki yayi min kaca kaca hardacemin wai daga gani na watarana magajiyar karuwai zan zama..'Takarishe fada harda fashewa da kukan karya.


Baki Azeema ta rike tana kallon Azeeza,Zuciyarta takasa gasgasata,Saboda Duk kalamanta babu gaskiya,ganin haka yasa Azeeza tashiga jerama Azeema rantsuwa hartana fadin yace kema wani Shiri kawai yake akanki da zarar yacinma burinshi zai baki takardanki,nidai don Allah Adda Azeema karki kuskura kiba dan iskan sojan nan kanki saboda bai da wani buri,illah ya maidaake karamar bazawara ya sakeki kuma Allah duk Abunda kikaga yanayi Duk shawaran uwarsace goggo..."Ai Sai Azeema tazama out of control zuciyarta tashiga zafi lokaci daya wani bangare na zuciyarta na amincewa da kalaman Azeeza wata kuma na kwabarta,Zuciyarta ta bata cewa in mganar Azeeza gaskiya ne,to ai yaya captain bai taba nuna wani zalama akanta ba asalima basu taba zaman Fahimta ba sai jiya,kodai kodau duk cikin plan nasa ne,Goggo kuma bazata taba cin amanarta ba,itace makwafin mahaifiyarta ta ci kashinta da fitsarinta goggo ta goyata da bayanta duk Abunda uwa zatayi ma danta shi goggo take mata,gaskiya bazata taba yarda da goggo za"a cuceta ba,to ammh mganar Azeeza Abun dubawane,domin akankantar Shekarunta bazata kitsa mgana kai tsaye ba,itako Azeeza ganin yadda Azeema tashiga Rudani Shiya bata damar kara mata famfo tana tsaro mata wasu mganganun wanda ita da kanta ta tsarasu,nan da nan Azeema ta amince da Azeeza ,100% harda kukanta tana fadama Azeeza ita yanzu yazatayi batasan ya rayuwarta zata je ba,shawara Azeeza tabata kan daga mkranta ta wuce gidan Baba Ade koda goggo taje ta tubure tace wlh bazata koma gidan goggo ba,bayan kwana biyu kuma ta bijuro da zencen sai yaya captain ya saketa.

Azeema ta yarda da shawaran Azeeza saboda yadda hakalinta yake atashema nan take tace Azeezar tazo ta rakata,Bakin Titi ta hau Abun hawa takoma gidan Baba ade,murna fal cikin Azeeza ta hanzari suka tafi office din principal,sukayi report kan Azeema bata da lafiya zata koma gida,nan da nan aka bata permission Azeeza ta rakata bakin Titi ta hau Keke tawuce gidan Baba Ade bayan Azeeza ta jaddadamata komai tambayan da za"a mata kada ta fadi dalili kawai tadai tada kayar baya,amsa mata tayi da cewa zatayi duk yadda suka tsara,Azeeza na dagamata hannu har suka bacema ganinta wata dariya ta kwashe dashi tana fadin,"Bye bye Adda Azeema i wish wannan karon bazaki tallakema tarko na ba..Yaya captain am coming iin to ur life Soon..."Tafada tana yar dariya kafin tajuya takoma cikin mkranta tana Dariyan Farinciki da nishadi.



?? _*Topha bala"i...Gaskiya my Fans sai yanzu nake ganin wautar Azeema dakuke tafadi,yarinya kamar kwalkwalarta ba Ta wani Tunani sai na Shirme,yanzu goggon zata gujema saboda dambala,...>??>??>??Lalle Azeeza yanzu kika Fara wasan naki,toh bari mugani Shin gadanga zaifiki zama player ko yaya? Hmmmm i don't know..,Sai mun hade a next page,love u all my Fans*_

? ? ? ? ? ? ?? *Comment,share and vote...*
? ? ? ? ? ? ?? *Janafty..,AKA...SHAKIRA..*=???
?*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty=???_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA=??Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*'

? ? ? ?? *Chapter 16*

? _Am srry For d typing errors ban samu na editashiba_ '

? ? ? "Aliyu yasha barci domin sai wajen karfe daya na Rana ya farka wanka kawai yayi agurguje ya sanya Shadda fara Dinki Muhammed riga da wando,da hula yatafi masallaci saboda ya samu jam"i,,koda aka idar da sallar bai Shigo gida ba,kofar gida yazauna yana waya da Haisam bayan sungama kiran Jabir ya Shigo wayarsa nan fa yazauna Sunata Fira,sun dau tsawon lokaci suna mgana kafin suyi sallama Akan sai sun hadu akaduna don kowannensu jibi yake san Ran komawa bakin aiki.

? ? Sun yanke kiran kenan sai ga KekenNapep din dayake Kai Azeema mkranta ya iso Faka keken yayi ya fito ya nufo Gadanga wanda yake binsa da kallon mamaki karisowa yayi yana mai sallama lokaci daya ya bashi hannu sukayi musabaha,bayansa Aliyu ke kallo yaga kota ina Azeema zata bullo ammh shuru,da kallon Tambayan Aliyu yake kallonsa kafin yace"Ah Ko Azeemar bataje mkrantar bane yau..?

? Sani mai KekenNapep yace"Shine Abunda yadauremin kai yallabai,ni dakaina na kaita mkranta yau da safe,ina kallo ta shige cikin haraban mkrantar,ammh Abun mamaki bayan antashesu naje daukota,ammh har duka Yan mkranta suka gama watsewa banganta ba,shine nazo nagani kodai tadawo gida da kanta ne.."Sororo Aliyu yayi kafin yace"How comes anya Azeema tadawo kuwa?bandai sani ba,buh bari na shiga na tambayi goggo naji wait for me.."Yafada da sauri yana fadawa gida,Tundaga nan yake kwalama goggo kira wacce ke daki ta zabga tagumi har lokacin dawowan Azeema yayi ammh shuru,da h??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????anzari Ta fito,zaninta ahannun yana neman Faduwa tana fadin"Gani gadanga lafiya irin wannan kira haka? tafada cikin tashin Hankali

Gabanta yaci burki yana fadin"Goggo ina Azeema.."? Fuskar damuwa ta bayyana ga goggo tace"Nima yanzu nake Shirin kiranka awaya Tundazu lokacin dawowarta yawuce ammh haryanzu shuru bata dawo ba,bakana da nombar mai Keken ba kirashi muji kowani aiki ne ya tsaidashi baije ya daukota ba."Kansa ya dafe yana fadin"Kash..Wayyo To ai goggo ga Sanin chan,yace shima yaje mkrantar su Azeemar ammh har kowa ya watse bai ganta ba.."Salati goggo ta fara tana fadin"Na shiga uku ni Suwaiba.,To yanzu ina yarinyar tashiga kuma ba dabi"arta bane biye biye,toh ina ma ta sani balle taje.."

? kallon goggo yayi kafin yace"Goggo kishiga gidansu kigani kila ta biyo yar"uwarta sun dawo tare.."Da hanzari goggo tace"Eh kila ta yuyu haka din ne,bari naje na gani.."Tafada Tana Fadawa daki,Hijabi ta sanyo ta fice da Sauri ta bar Aliyu na Dafe kansa baisan dalili ba yaji hankalinsa yatashi,goggo na fita taci karo da Dan adaidaita,yana ganinta yahau Fadin"Ah Hajiya an ganta ne..? ko kallonsa Goggo batayi ta fada gidansu Azeema tana zabga sallama ko izini ba"a bata ba,ta sakai cikin Filin tsakar gidan,nan ta iske Azeeza da Inna Ramatu suna zaune kan Tabarma suna cin dankali,suka ga goggo ta fado kai tsaye inna Ramatu ne takalli goggo tana cewa"A"a suwaiba lafiya naga kin fadomana gida,? tamkar wani ya biyoki daga waje.."

? hararanta goggo tayi kafin tace"Azeeza ina Azeema.."?Tun dazu bata dawo gida ba,ko kin ganta yau amkaranta.."?Tafada tana maida kallonta kan Azeeza,Jin haka yasa Ran Azeeza yayi fes Tsarinta yana tafiya kan tsari,Mikewa tayi tana fadin"wlh tallahi goggo yau kaf ban saka Adda Azeema a idona ba,dana ga banganta ba bayan antashi break,naje ajinsu ammh ban ganta ba,na tambayi yan ajinsu sukace batazo ba yau,dama taje mkranta ne yau..? Azeeza ta fada cike da makirci,baya goggo taja tana fadin"Armmm.,Bakomai.."Tana fadin haka tafice da sauri Inna Ramatu ta bita da kallo kafin ta maida kallonta kan Azeeza wacce ke mirmishi mai Fitar da amon Sauti Tabota inna tayi tana fadin"Ke nifa nashiga rudu mai wannan uwar sojan mara mutumci,take son Fada.."

? Kallonta Azeeza tayi kafin tace"Wai bakiji metake fadi bane Adda Azeema ne Tafita da niyyar zuwa mkranta,shine ta sanfe wani wajen haryanzu bata dawo ba..."Baki inna Ramatu ta kama tana fadin"Au hakane eh lalle yanzu

12 / 34