RAYUWA DA GIÆI BY BATUL MAMMAN

Author :  BATUL MAMMAN Category :  African Stories & Novels

Chapter   28 / 42

81K to 84K   out of 124.8K words

bata amsa"

"""Ai ta ce tana tafe jibi. Ita ma ba za ta bari su yi haWuwar wajen biki ba tunda an riga an Waura."" Ta"

"nunawa Hamdi kujera ""Zauna ba a rasa abin faWa miki ba. Sai dai in kuma kara ce ba za ki yiwa Mama ba."" Cewar Hajiya ga Inna."

Bayan ta fita Hamdi taji kunyar da tafi ta sauran Wakunan. Innar Taj tana da wani irin kwarjini da cika ido.

"""Kina da zaSin kalar kayan Wakin da ki ke so?"""

Tambayar a bazata ta zo mata. Ta Waga kai daga sunkuyon da tayi.

"""A'a."""

"""Taso ki gani"" Inna ta nuna mata waje kusa da ita akan makeken gadonta da tun shigowar Hamdi take"

santinsa a zuciyarta.

Kasa tashi tayi sai da Inna ta maimaita maganar tare da umarnin lallai ta taso. A Wofane ta zauna. Inna ta

buWe catalogue ta Wora mata a cinya.

"""BuWe ki zaSi wanda ya yi miki. Sai kuma ki zaSarwa mijinki."""

Yawu ta haWiya. Jikinta har wani rawa yake tana jin sanyi sanyi na ratsa ™asusuwanta. Wannan fa ita ta

haifi Taj. Da Yaya za ta ga zaman da tayi kusa da ita irin wannan ™arshenta sai ta Sallata.

"""Hamdi"""

Ita kaWai ta kirata da sunan da ake kiranta a gida. Wannan yasa taji ranta ya an sake.

"Inna ta cigaba da magana ""kin shiga Wakuna uku na surukai. Nan kuma Wakin na mamanki ne. Don Allah"

"ki Waukeni a matsayinta domin hakan ne kaWai zai bani damar yi miki ri™on ´ar cikina."""

"Cikin rashin jindaWi Hamdi ta ce ""Ki yi ha™uri."""

"""Ba fushi nayi ba. So nake ki ajiye komai ki saurareni da kyau."""

Hamdi ta mi™a mata hankalinta kacokan. Inna ta fara da yiwa Abba da Yaya addu'a da su ka haifi matar

da ta auri Taj. Saboda ta jima tana tsoron kada aurensa ya tashi iyayen ´ar su fasa saboda korarsa da mahaifins ya yi. Abu na biyu kuwa fito mata tayi a mutum. So take Hamdi ta amsa sunanta na matar Taj ba tare da taji War a zuciyarta ba.

"""Indai mijinki ne to ki manta da matsayinsa ki kama abinki a hannu. Na san komai da ´an uwana su ke"

Soyewa game da sharaWin da Alhaji ya bawa mahaifinki. Ni kuma in Allah Yaso Ya yarda kin shigo kenan. Allah ba zai bawa kowa damar ganin ™arshen auren ba ballantana su cigaba da Wora zarginsu. Hatta ´an uwanki ina yi musu fatan samun nasarar zaman gidajensu. Abu ™an™ani ne zai faru a Worawa babanku

"laifi. Idan kuwa ta Sangarenki ne to da uba da miji duka a kunnuwanki za ki ji ana cin zarafinsu."""

"Darasi mai girma Inna ta Wora mata, saSanin su Hajiya da aikin da su ka bata ne mai girman. Akan"

shekarunta taji kamar an ™ara mata ashirin saboda yadda take ganin ba za ta iya ba. Amma kuma ta sami ™warin gwiwa sosai.

"""Taj yana son ki. Ki sa ya ™ara ™aunarki Hamdi. Ki hana zuciyarsa sakat ta yadda aurenku ba zai sami"

"tangarWa daga yinsa ba don Allah."""

Bayan ta gama Waukar karatun mai girma sannan Inna ta kira Firdaus ta ce su koma falo. A can aka

cigaba da hira wadda ita dai amsarta bata wuce murmushi sai eh ko a'a. Tunanin da aka barta dashi yafi ™arfinta. Abu guda ta fahimta shi ne matan gidan duka basa son auren nan ya mutu. Gashi Abbanta ya tsorata da barazanar Alhaji yana ta yi mata tuni.

Cikin dabara aka sa Firdaus ta tambayeta size Win da ta™i turawa Taj. Da ™yar ita ma Win ta sanar da ita.

Sannan cikin ™anen Taj wata ta aunata gwajin riga da siket da na doguwar riga. Sai gashi kafin magrib ta soma sakewa dasu. Na™asun da aka samu bai wuce na rashin shigowar Kamal ko Salwa ba. Sannan ko

sau Waya Taj bai kirata ba. Ta sha™a tayi fam tana jiran ya tsikareta ta fashe.

Ita ma Anti Zahra har fargabar zuwan Ahmad Waukarsu take yi. Ta san shi sarai. Laifinta zai fara gani kafin

ya saukewa ™anwar tasa kwandon masifa.

***

Ikon Allah Taj da Kamal su ka gani yayinda Salwa ta soma kuka tun a bakin gate wai Taj yana wula™anta

ta. Aka yi ta rarrashinta ta™i shiru saboda makirci. A dole Kamal ya ce ta shiga motar. Shi ne su ka tafi

Happy Taj. Office Win Kamal dake cikin boutique Winsa su ka shiga. Ta sami wuri ta zauna tana goge

™walla.

"""Salwa tunda ku ke da Taj ya taSa cewa yana son ki?"""

Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta. Taj yaji a duniya yanzu babu abin da ya tsana kamar mace ta

dinga wasa da yatsunta. Tsaki ya ja ta dubi Kamal.

"""Kana ganin abin da yake yi min? Meye laifina don na ce ina son shi? Ba fa cewa nayi ya saki yarinyar da"

"ya aura ba."""

"""Ki dinga gyara kalamanki akan matata. Sannan kin fi kowa sanin cewa ba zan juyo ba. Ba yaudararki nayi"

"ba so don't give me that crap wai in haWaku."""

"""HaWamu ma bai taso ba tunda Alhaji ya ce..."""

"""A wurin wa ki ka ji wannan maganar?"" Ya tambayeta muryarsa a sama."

"""A wurin Yaya mana."" Ta bashi amsa tana tura baki."

"Kallonsu Kamal ya yi don bai gane komai ba ya ce ""wace magana ce Happy?"""

A ta™aice Taj ya yi masa bayanin da bai yi ba saboda rashin lafiyarsa.

"""Bana jin Yaya zai faWa mata."" Kamal ya faWi yana kallonta ""a ina ki ka ji?"""

Rigimar da Mami ta ce ta haddasa tsakanin Taj da duk wanda zai goyi bayan ya™i aurenta ta tuna. Ta

kuwa taSe baki cike da raini.

"""Ina ruwanka? Kai dai burinka ba ya saki Hamdi ka aura ba?"""

Duka su biyu zabura su ka yi cikin Sacin rai.

"""Salwa!"" Kamal ya yi mata tsawar da a tunaninta ba zai taSa iyawa ba saboda yafi Taj sanyin hali."

"""Ki kiyayeni wallahi."""

"""Idan na™i fa? Ya Kamal na fa san kana son yarinyar nan. Ko ba abin da ya kwantar da kai ba kenan? Me"

"yasa baka taSa yin wani ciwon allergy ba sai da Ya Taj ya aureta? Wallahi zan iya dafa izu sittin baka da wani allergy."""

"""Kinga Salwa, kalleni nan"" Taj ya yi mata magana yana cijewa don ta riga ta kai shi matakin da yake son"

taSa lafiyarta. Wani abu da bai taSa yi ba ko da wasa.

Idanunta a bushe ta kalle shi. Bai san bata tunkari wannan rigimar ba sai da ta shirya mata daga gida.

"""Ina jin ka"""

"""Zo ki tafi kafin wani cikinmu ya yi miki rauni."""

"""Please Taj kada ka biye mata. Ka bar zancen raunin nan kada wani ma yaji."" Kamal ya yi maganar da"

kana gani za ka gane yadda yake ™o™arin danne Sacin ransa.

"""Za ka aureni Ya Taj. Allah kuwa..."""

Kawai ta sa kai ta fita. Bayan tafiyarta Kamal ya zo zai yi masa rantsuwar zancenta ™arya ne Taj ya

dakatar dashi.

"""Idan kana tunanin na yarda da zancenta har ina bu™atar ka wanke kanka to gaskiya akwai matsala"

"tsakaninmu."""

"Murmushi Kamal ya yi ""Allah Ya huci zuciyarka."""

"""Amma wane irin ciwo gareka Happiness?"""

Koda Kamal ya juya ya kalli Taj sai yaga babu alamun wasa a tare dashi. Allah Ya taimake shi ya fara ajiye

magungunan allergy su antihistamine saboda rana irin wannan. Durowar magungunan ya buWe ya fiddosu duka.

"""Ka ce baka yarda da zancenta ba."""

"""Daga cikin addu'ar da nake yawan yi mana harda kada Allah Ya haWamu son abu guda da mutum biyu"

"basa tarayya a kansa. Zancen ciwo kuwa ai rantsuwa tayi. Tunda tana sa gaba gabas zancenta zai iya zama gaskiya."""

Šaya bayan Waya yabi magungunan ya dudduba. Pain relievers ne da wanda su ka danganci kwantar da

abin da ya shafi allergy.

"""Allah Ya baka lafiya Happiness."""

"""Amin."""

***

Tafiyar minti biyar a mota za ta kai mutum wani babban mall da ya yi shura a titin kafin a gina Happy Taj.

"³an Kano da son sabon abu na yayi kusan kowa ka taSa zai ce maka ya yi siyayya a Glory Mall. Wurin sha™e yake da kaya na alfarma. Sannan akwai snacks irinsu shawarma, small chops, popcorn, ice cream da sauransu. Har event centre garesu a ciki. Wurin mallakar wani hamsha™in Wan kasuwa ne da ya dam™awa babban Wansa alhakin kula da shi. Kuma a shekara biyu da rabin farko uban ya yi alfahari da"

Wansa. Ciniki ake yi na bugawa a jarida.

Komai ya soma taSarSare musu cikin abin da bai fi sati guda da buWe Happy Taj ba. Idan kaya ake so

boutique Win Kamal yana da na kowanne jinsi manya da yara. Abin da ya shafi abinci kuwa harda wanda mutane basu sani ba akwai a Sangaren Taj.

Kamar wasa su ka dinga tunanin ko irin abin nan ne na Wokin sabon waje. Idan an kwana biyu abu zai

koma normal. Sai aka yi rashin sa'a kasuwa da gaske take damawa da su Taj cikin albarkar Allah. Haka kawai mutane su ka fara janye jiki. Ciniki ya yi wani irin ja da baya mara daWi. Alh. Usaini ya shiga gagarumar matsala da mahaifinsa. Inda rashin tawakkali yasa uban ya taso shi a gaba da muggan kalamai da tsoratarwa. Indai ciniki bai daidaita ba to ya kwana da sanin zai karSe mall Winsa ne ya bawa wani daban cikin ´a´ansa. Wannan abu ya yi matu™ar tayar masa da hankali. Ya shiga faWi tashin hanyar dawo da martabar mall Winsu amma abu yaci tura. Har an kai wasu masu kai musu kaya sun fara janye

jiki.

A irin wannan yanayin na neman hanya kowacce iri ce Allah Ya haWa Alh. Usaini da Ummi. Cutar hassada

tayi mata lulluSi tun daga kai har tafin ™afa a lokacin da taji labarin auren Hamdi da mamallakin Happy

Taj. Ranar harda kuka sai da tayi. Zuciyarta a cunkushe tana fama da takaicin yadda ´ar Wan daudu ta

sami miji irin Taj. Ta taSa zuwa wajen da wani saurayinta. Yadda taga Taj ta san wadda ta fita ma bata isa

"ta aure shi ba, balle kuma Hamdin da bata kama ™afarta a gayu da rufin asiri ba."

Wani abin kayan haushin kuma jan kunne da gargaWin iyayenta da yayanta akan ™anwar Hamdi da ya

aura. Ko kallon banza ta yiwa Zee ya yi al™awarin canja mata kamanni.

"Ranar da ta haWu da Alh. Usaini, cikin jin zafin auren Hamdi ta fito ds niyyar zuwa Happy Taj ta Sata ta a"

gaban Taj. Sai da ta iso kuma ta rasa me ya kawo mata tsoro ta kasa ™arasawa. Haka kawai ™afafunta su

ka kaita Glory mall. Ta je wurin snacks ta sayi meatpie da lemo ta sami wuri tana ci. Amma hankalinta gabaWaya yana kan ginin Happy Taj.

"""Ki tafi can mana idan nan bai yi miki ba."""

Kallonsa Ummi tayi za ta faWi ba™ar sai ta adana. Mutumin zai yi shekara arba'in da biyar. Ya sha shadda

´ar ubansu da Winki na alhazawan birni. Ga ™amshi na waWanda naira ta tsaga jikinsu ta zauna da kyau.

"Murmushi tayi masa ""ba kallon son zuwa nake ba. Fatan abin da zai zo ya tayar da wurin gabaWaya koda"

"gobara ce nake yi."" Ta kashe masa ido."

"""Ko zan san dalili?"" Amsarta tasa ya sami interest akanta."

"""Kaji daWin kaini gaba? Allah Ya kiyaye."" Ta tashi tsaye."

"""Ko kusa. Nima burina kenan.."" ya kashe mata ido yadda tayi masa."

"""Dalili?"""

"""Sun kashe min kasuwar mall Wina mana."""

"Zama ta koma tayi ""nan wurinka ne?"""

"""Eh. Amma yana fuskantar barazanar rufewa saboda su."""

Dariyar mugunta Ummi tayi a zuci. Daga ranar su ka ™ulla ita da Alh. Usaini. Suna neman hanyar da za su

nakasa Taj domin su gurgunta masa sana'a.

"A wannan rana ta asabar da Salwa ta fito daga Happy Taj cikin Sacin rai, ta faWa Glory Mall saboda akwai"

mai POS daga bakin gate Winsu. Tana jiran mutumin ya idar daga sallar la'sar a gefen ´ar container Winsa take waya da Mami. A ciki take zayyane mata duk fa abin da ta ce tayi ta gwada amma ™arshe Taj yaci mutumcinta.

"""Ni dai Mami da kin barni naje masa a yadda nake. Na tabbata idan ina kwantar da kai zai dube ni."""

Zaginta Mamin tayi ta ce mata kuma ta kwantar da hankalinta. Ta sanar da mahaifinsu ya ce zai kira

Alhajin su yi magana. Tana da ya™inin yadda Alhaji yake ragawa Salwa don mutumcin babanta da yake gani nw. Duk taurin kansa ba zai ™i tayin ´a ba. Musamman tunda ba son wadda Taj Win ya aura yake yi

ba.

"""Kin nuna musu kin san baya son auren?"""

"""Eh, kuma ban faWa musu cewa waya naji Yaya Ahmad yana yi da matan gidansu yana sanar dasu ba. Har"

"wani cewa yake su yi wani abu kada a raba Taj da wadda yake so. Ni ko oho."""

"""Ki daina yin komai. Da kansu za su nemi ki idan babanki ya yi masa magana."""

Wayarta duka a kunnuwan Ummi da Alh. Usaini waWanda su ka yiwa juna wani irin kallo gami da

murmushi. Tana gama wayar Ummi ta matsa kusa da ita su ka gaisa. Sai ta nuna kamar ita ma mai POS

Win take jira. Abin ka da mata in an haWu. Hira a taSa nan a taSa can sai gashi sun yi exchanging number.

Bayan Salwa ta ciri kuWin ne ta fito Kamal ya kirata. Babu ja in ja ta faWa masa inda take. Shi ne su ka

Wauketa don darajar Ahmad kawai. A hanya harda basu ha™uri wai ranta ne ya Saci. Babu wanda ya kulata a cikinsu har su ka isa gidan. Taj ya yi zamansa a mota.

"""Happiness ka turo min ita in kaita gida kafin magrib."""

Salwa bata ce musu komai ba tayi wucewarta ciki. Ganin Kamal bai shigo ba ta tsaya ta goga hoda da

lipgloss kafin ta shiga ciki. Hayaniyar mutan gidan taji daga Wan korido Win da ake ajiye takalma kafin a

shiga falon. Ta ™ara yin tsaki. Bata san za ta ™i mutanen nan ba sai da taga yadda aka dinga kai kawo akan

zuwan Hamdi. Yanzu kuma da alama hirar ma da ita suke yi.

Sallama tayi ta shiga da wani irin farinciki a fuskarta. Bata sha wahalar haWa ido da Hamdi ba don ita ma

Win sallamar tasa ta Waga kai ta kalli ™ofa. Murmushin nasara ta sakar mata. Hamdi ta mayar mata. Daga

ita har Taj Win sai ta fanshe wannan Sacin ran da su ka sa ta wuni cikinsa.

"""Salwa ina ki ka je?"""

Šan firgita tayi domin kuwa Ahmad ne ya yi tambayar da kakkausar murya.

"""Da Ya Taj muka fita. Cewa ya yi na raka shi Happy Taj. Shi ne mu kaje harda Ya Kamal"""

"""Bangane ba? Ya zai kawo matarsa kuma ya yi wani wajen. To da izinin wa ma ki ka fita?"""

Kafin ta bawa Yaya Zulaiha amsa Kamal ya shigo. Sai ta canja akalar tambayar.

"""Ko dai soyayya ku ke da Kamal?"""

"Da wani irin sauri ya ce ""Allah Ya kiyaye. Ina da wadda nake so."""

Jama'ar falon su ka kama ihun murna. Harda masu cewa ko a dakatar da bikin Taj saboda dama indai da

amana tare ya kamata su yi aure.

Wannan amsa ta Kamal ta Sakanta ran Salwa. Yadda ya faWa tamkar wata abar ™yama. Ahmad kansa sai

da yaji babu daWi. Anti Zahra ta kallesu su biyun. Idan Salwa ta cigaba da zama dasu za a iya samun

matsala tsakaninsa da ´an uwansa. Ko me za ta yi ita ma jininsa ce.

"""Ku tashi mu tafi"" ya ce da Anti Zahra, bana son Magariba tayi min."

"""Kai Ahmad, kamar kana dawa? Don Allah ka zauna."""

"""Ai mun gaisa da ™anwar tawa ko?"" Ya yiwa Hamdi murmushi."

"""An kusa kira Yaya. So kake Ya Taj ya yi sallah shi kaWai?"" Bishir ya ce."

Fin ™arfi aka yiwa Ahmad. So yake kawai su shiga mota ya gamu da Salwa. A dole ya bi ™annensa waje su

ka tare cikin motar Taj abin tausayi suna hira.

Aka sake tashi yin sallah. Hamdi ta koma Wakin Mama. Salwa sai ta faki ido ta bi bayanta. Su Mama suna

Wakin Umma ana ta shirye shirye.

"""Washhh. Wannan zirga zirga Ya Taj duk ya tara min gajiya."""

˜in kulata Hamdi tayi. Kowa yaci tuwo da ita ai miya ya sha. Darajar inda su ke yanzu yasa ta kama kanta.

Amma ramuwa kam zata yi gwargadon abin da aka yi mata!

***

Gayya guda aka rako Hamdi bakin gate da sha tara ta arzi™i. Har ta dinga jin wani iri saboda bata kawo

musu komai ba. Yawancin kowa a bayan mota ya ajiye kyautarsa. Banda likitar gidan. Yaya Kubra a

hannu ta dam™a mata wata ba™ar pepper bag da aka rubuta Scentmania a jiki. ˜amshi a take ya cika

gaban motar tun ba a buWe ba. Ya haWe da sanyin AC sai ya bada wani irin ni'imtaccen yanayi.

"""Zamu yi waya in miki bayanin turarukan kinji. Mun kuma gode da wannan ziyara."""

"""Nima nagode sosai. Allah Ya saka muku da alkhairi."""

Suna ta Wagawa juna hannu aka rabu a mutumce. Daga nan kuma motar ta koma ta kurame. Taga ta

zubawa idanu tana kallon gilmawar ababen hawa da fitilunsu. Taj ya kalleta yafi a ™irga ya tabbatar da

gaske shi ne bata son kulawa. Murmushi ya yi. Ya taSa wayarsa wanda Hamdi ta gani da wutsiyar ido amma ta share.

"""Hello, Salwa..."""

Iya abin da taji ya ce kenan ta juya a fusace su ka haWa ido. Wayar a gefe ya ajiyeta. Babu kuma wani abu

da zai nuna mata wayar yake yi. Dariyar kamata ya fara sai yaga babu fuska sam. Ta tsuke baki kawai ta sake juyawa. Har wani numfashi mai nauyi ya kula tana saukewa. GabaWaya sai yaji ya kasa sukuni. Dama

ya san za ta ji haushi. Amma ya yi zaton za ta jira bayani daga gare shi.

"""Mrs Happy"""

Shiru.

"""Hamdi"" sunan nan har tafin ™afarta take jinsa idan ya faWa amma ko motsi bata yi ba."

"""Please ki juyo.."" nan ma biris tayi dashi "" to kada ki ga laifina duk abin da ya biyo baya."""

Gyaran murya taji ya fara ta taSe baki. Wato zai fara yi mata daWin bakin maza da take ji katse mata

zancen zucin ya yi.

"""Dil ne yeh kaha hain dil se (my heart has said this to your heart)"""

"""Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Banda wa™ar India don Allah. Wallahi kunya ma nake ji. Bana son namiji"

"yana..."""

"""Mohabbat ho gayi hai tumse (I have fallen in love with you)"""

"""Na shiga uku"" Hamdi ta sanya hannuwanta biyu ta toshe kunnuwanta ""ka bari don Allah zan"

"saurareka."""

"""Meri jaan, mere dilbar (my life, my love)."""

"""Ya Taj wasa nake. Ba ma fushi nayi ba..."""

"""Mere aitbaar karlo (have faith in me)"""

"""Happyyy"" ta faWi kamar tayi kuka wai yau ita ce miji yake yiwa wa™ar india."

"""Jitna beqarar hoon main (how much restless I am)"""

Titi yake kallo abinsa yana sakin baiti. Ta rasa yadda zata yi dashi. Kawai sai ta kai hannuwanta ta

cupping fuskarsa wanda ya sanya shi Wauke wuta na wucin gadi.

"""Allah na ha™ura."" Ta fada a hankali."

Gefen titi ya gangara

28 / 42