Author : MRS SAIF Category : KDP NOVELS
" kawai ta ce, ta shiga d'akin su jaka kawai ta ajiye ta fito fuskarta duk ta kumbura alamar ta yi kuka, ta nufi inda bak'on na ta ke zaune.
Ko da ta gama tad'in ba ta kwanta ba sai da ta wanke tulin kayan wankin Mama sannan ta kwanta cike da gajiya da tsantsar tunanin abinda ke shirin faruwa da ita.
Yanzu ba ta da wani buri da ya wuce ta ganta gidan Farouq a matsayin matarsa, yanda ta ke Jin kaunar Farouq a yanzu ko rabinta ba ta ji ba lokacin aurensu, tana matuk'ar son ta koma auren Farouq a karo na biyu ko don ta gyara kurakuran da ta yi, sai dai ina har yanzu zuciyarta ta kasa hasko mata mafita, dole tana ji tana gani za ta auri mutum da ba son sa ko d'igo a zuciyarta.
Wani hawaye ta ji yana bin fuskarta wanda ba ta damu da ta goge ba, Ansar da ke gefenta a kwance ta rungume tana Jin tsananin k'aunar mahaifinsa na ratsa ko ina na sassan jikinta.
Ta d'auki tsawon lokaci a haka, kafin daga bisani ta kwantar da shi, ta d'auro alwala ta tayar da Nafila, ta dad'e tana jera nafifili sannan ta yi sallama ta d'aga hannayenta sama cikin kuka ta fara addu'a.
"Ya Allah, ya mad'aukakin Sarki, ya mai amsa buk'atun bayinsa ya Allah ka fini kusa da jijiyar dake wuyana ya Allah ka san na yi nadamar abun da na aikata ya Allah ka kawo mun mafita mafi alkhairi, idan har komawa Farouq alkhairi ne ya Allah ka tabbatar mun, idan ba alkhairi ba ne ka sauya mun da mafi alkhairi".
Ta shafa addu'ar tare da sakin wani irin kuka mai ban tausayi...
Mum Twins
[10/16, 5:08 PM] mrm kd: [9/26, 7:24 PM] Mum Twins : ▪BALLAGAZAR MACE ▪73
©Mrs Saif
Da sauri - sauri ya ke shirin kasancewar ya d'an makara zuwa office, Fateema da ke zaune a gefen gadon d'akin tana kallonsa, sai wani ciccin magani take, yanda ta wani had'e fuska abun har ya so ya bawa Farouq dariya sai dai ya daure don kar ya tsokano wa kansa rigima don yasan k'iris take jira.
Sai da ya gama shirin tsaf, ya juya da kallonsa gareta ya ce
"Fatyna zan tafi, sai na dawo"?
K'ara tsuke fuska ta yi ta ce
"uhmm".
D'an zaro ido waje Farouq ya yi cikin mamaki ya ce
"yau ko daddad'ar addu'ar nan ba za a mun ba, bare kuma rakiya"??
Gyd'a kai ta yi alamar eh.
Murmushi Farouq ya yi ya ce "lallai yau sarautar ta motsa, tunda haka ne na fasa fitar nima," ya k'arashe maganar tare da ajiye briefcase d'in hannunsa ya fad'a kan gadon ya yi lamo kamar wanda zai yi barci.
Shirun da ta ji ya yi yawa ne yasa ta kai hannu ta juyowa da fuskarsa, ba barci yake yi ba amma idonsa a rufe yake, cikin muryar shagwa6a ta ce
"don Allah ni ka tashi ka tafi aikinka".
Bud'e idonsa ya yi ya d'ora akan fuskarta ya ce
"ba zan je ba har sai kin gaya mun dalilin wannan fushin".
"Ai ka fi ni sanin dalilin, wata nawa ina binka da magana d'aya amma ka k'i saurarata".
Ajiyar numfashi ya yi sannan ya ce
"Fateema ki share zancen na dawo da Nadeeya, kimanta da maganar don ba ya cikin tsarina gaskiya, haka kurum muna zaman zaman mu ki jaji6o mana ita ta zo ta wargaza mana jindad'in rayuwa, ba zan iya ba gaskiya".
"Haba Farouq ka yi hak'uri ka yafe mata tunda ta yi nadama, ta rok'i afuwa ba sai a mata ba, Allah ma fa muna masa laifi kuma ya yafe mana, yawan nacin kirana da take yi ba dad'i sai ta ga kamar nima bana son ta dawo shi yasa na k'i mata kokarin shawo kan ka, tun tana kiranka ka na mata wulak'anci har ta hak'ura ta dawo kaina, don tabbacin da ta da shi na zan taimaka mata".
"ke ma yanzu idan ta kiraki ki ce kar ta kuma kiranki, don na k'i amincewa faqat, kin ga sai kuma ta nemi wani tunda aikinta kenan bibiyar dangina".
"gaskiya ni kam ba zan iya cewa kar ta kuma kirana ba, ai sai ta ga kamar na mata wulakanci".
"Okay, amma don Allah ni ko ta k'ara kiranki kar ki kuma gaya mun don bana son maganarta kwata_kwata don tuni na rufe shafinta a cikin rayuwata".
"Amma ai..... Farouq ya saurin katseta ta hanyar d'ora hannunsa akan lips d'in ta ya ce
"shhhhhhh! Babe yaushe ki ka fara musu ne? Bana son maganar nan abarta haka."
"alright, yanzu tashi mu je na rakaka domin lokaci sai tafiya ya ke".
Murmushi ya yi ya ce
"ko kefa, dama na san maganar duk ta k'arfin hali ce kike don dai Farouq na Fateema ne ita kad'ai".
Dariya Teema ta yi sosai don ko Farouq ya harbo jirginta, a ranta ta ce
"dama wa zai so kishiya sai dai idan ta zame ma dole ba yanda za ka yi".....
Mum Twins
[9/26, 7:24 PM] Mum Twins : ▪BALLAGAZAR MACE ▪74
©Mrs Saif
Three weeks later
******
Zuwa lokacin Nadeeya ta zama abin tausayi, don duk ta fige ta lalace, don ciwo take yi ba na wasa ba, kuma ba abinda ya yi sanadinsa irin damuwa da tunani, don bikinta da Alh Sani saura sati biyu kacal, tun Mama na shareta har ta fara tausayinta, kun san tsakanin d'a da mahaifi, sai dai ta san ciwon Nadeeyar ba na komai ba ne illa na son Farouq, kuma ga shi ta yi rantsuwa ba za ta kuma shiga maganar aurenta da Farouq ba.
Wasa - wasa ciwo har sai da ya kai ta da kwanciya asibiti,a lokacin gaba d'aya ta saduda da rayuwar kira kawai take a kira mata Farouq ta nemi afuwarsa kafin ta mutu.
Sosai Mama ta shiga damuwa ba shiri ta kira Umma a waya ta sanarda ita duk halin da ake ciki.
*******
Don haka ne yau tunda safe Umma ta kira Farouq ta ce "idan ya tashi daga aiki ya je tana nemansa".
Bayan sun gaisa ne Umma ta fara magana kamar haka
"Farouq ba komai yasa na kira ka ba sai don maganar Nadeeya, bana son takura maka a karo na biyu, shi yasa ka ga duk tsawon lokacin nan ban yi ma maganar ka dawo da ita ba, amma jiya labarin da na ji akanta abin ya girgiza ni matuk'ar gaske".
Anan ta kwashe labarin komai ta gaya masa, sannan ta cigaba da cewa
"don haka na ke nema mata alfarma ka yi hak'uri ka dawo da ita, ka manta da duk abinda ya faru a baya, insha Allah dawowarta zai zama alkhairi gare mu baki d'aya".
Ajiyar zuciya ya sauke tare da fad'in
"Umma ba na tunanin akwai wanda za ki nemawa alfarma a wurina na kasa yi miki matuk'ar abin bai fi k'arfina ba, don haka na amince da auren Nadeeya a karo na biyu Allah ya sa hakan ya zama alkhairi."
"ameen "
Umma to fad'a cikin jindad'i, sannan ta shafa kan sa ta ce" Allah ya maka albarka Omar Farouq, yasa ka samu yara masu maka biyayyya fiye da yanda ka ke mun".
"ameen, ameen Umma " ya fad'a tare da mik'ewa tsaye don tafiya.
Cikin d'an k'ank'anin lokaci aka sa tafiya dutse, da Faruk ya so ya waske ya k'i zuwa Umma ta ce dole ya je, ba yanda ya iya dole ya ajiye ayyukansa ya tafi.
Tabbas shi ma ya ga canjin da ake cewa Nadeeya ta yi, don ta koma wata saliha ga nutsuwa har wani kunyarsa ta ke ji abun har mamaki ya bawa Farouq.
Matsala d'aya suka samu ta Alh Sani don ya tsaya kai da fata ba zai janyewa Farouq ba, tunda an riga an sa musu rana, da k'yar da sud'in goshi ya amince ya jaye.
Daga k'arshe aka yanke shawarar sati mai zuwa za a d'aura aure a yi bikin da ya sawwak'a amarya ta tare a gidan angonta.
[9/26, 7:24 PM] Mum Twins : ▪BALLAGAZAR MACE ▪75
©Mrs Saif
Haka aka yi kuwa sati na zagayowa aka d'aura aure aka sha biki amarya ta tare, daren farkon su Farouq ya k'ara tabbatar da chanzarwa Nadeeya, don sam ko alamar warin da take yi ada bai ji ba,,idan ban da k'amshi dake tashi daga kowacce ga6a ta jikinta ba abinda ya ke ji, dama gashi ta samu ingattatun magungunan mata ta yi amfani da su tsaf ta d'inke abinta kamar sabuwar budurwa.
Ai kam Farouq ya sha mamaki a daren ranar sai yake ji kamar wata Nadeeyar ce ta daban aka kawo masa ba wadda ya sani ada ba.
Washe gari ko da ya tashi sai ya tsinci kan sa cikin annushuwa, wacce ko a daren farkon auren su na fari bai yi ba, har Fateema sai da ta fuskanci haka.
Nan da nan ta ji wani kishin Farouq na nuk'urk'usarta,kun san an ce
"kishi kumallon mata".
Sai dai da ta yi tunanin duk abinda Nadeeya za ta yi daga baya ne, don ita ta riga ta wuce wannan shafin, ta riga ta wa Nadeeya nisa a zuciyar Farouq, nisan da duk gudunta ba za ta iya tarar da ita ba, sannan ita ma ai ba zama za ta yi ba, za ta d'ora ne a inda ta tsaya don ta riga ta gama sa nin Farouq cike da bai, saboda da haka hanyoyin mallakarsa a tafin hannunta suke, don haka me zai sa ta rik'a kishi ma da Nadeeya da sai yanzu ne take gane waye Farouq, da wannan tunanin ta watsar da duk wani abu da shaid'an ke bijiro mata da shi a zuciyarta.
*******
Zaman su suke yi lafiya Lau cike da fahimtar juna, domin tuni zaman na su ya sauya salo idan ka gansu kamar ba kishiyoyi ba, sai ka rantse da Allah ya da k'anwa ne, ko gidan ka shigo ba za ka ta6a gane mai girki ba don tare suke shiga kitchen, musamman yanzu da Fateema ta yi nauyi haihuwa ko yau ko gobe, Nadeeya ce ta kar6i girkin gaba d'aya ta ke yi, sai dai fateema ba ta son zaman kawai ba ta komai, don haka lokaci zuwa lokaci ta kan shiga kitchen d'in ta taya Nadeeya aiki koda ba mai wahala ba, Nadeeya ta yi ta mata mitar ta je ta zauna ta huta amma ta k'i, a dole take k'yalleta.
Farouq ne ya dawo daga aiki tunda parlour ya ke jiyo tashin hirarsu a hankali daga kitchen murmushi ya yi ya nufi kitchen d'in, dukkan suka jiyo suna masa sannu da zuwa, cikin fara'a ya amsa musu.
Fateema da ke zaune tana tsige d'ayan zogole a wani d'an k'aramin bowl ta yi k'ok'arin mik'ewa don kar6an ledojin hannunsa da sauri ya zaunar da ita yana fad'in "oh! Fatina ki zauna abin ki zan ajiye da kaina, ke kanki kamata ya yi na rik'a d'aukan ki duk inda za ki je,Allah ina tausaya miki cikin har ya fi ki girma". Ya k'arasa maganar tare da kai hannunsa kan cikin.
Dariya Nadeeya ta yi ta ce
"wallahi fa kamar ba na farin ba". Murmushi Farouq ya sakar mata ya ce
"Amryata wai me kuke dafa mana ne, na ji gidan ya d'umame da k'amshi".
"mai cikin gidan nan ce yau ke son dambu, ka ga kuwa dole na mik'e na dafa shi".
"wow! Gaskiya kin kyauta Amryata kin san nima na dad'e ban ci dambu ba, musamman dambun amare akwai dad'i". Ya k'arasa maganar yana kannewa Nadeeya ido d'aya."
Shiru ta masa ba ta amsa shi ba, ganin haka yasa Fateema kwashewa da dariya don ta san abinda yasa Nadeeya yi masa shiru.
"Maman Ansar gwanda fa ki hak'ura da amaryar nan don kin san yanzu ni ce uwargida sarautar mata sai sorry". Fateema ta k'arasa maganar tare da sakin wata dariyar mugunta.
Shi ma Faruk dariyar ya ke mata, don haka Nadeeya ta ajiye ludayin da ke hannunta ta juyo garesu ta ce
"Abban Ansar da kai da Teema ina tunanin sai na kai ku court alk'ali ya mana shari'a da ku sannan kuma ba ni certificate da zai tabbatar da ni ce Uwargida a gidan nan, ku kuma a saka muku hukuncin mai tsauri ga duk wanda ya k'ara kirana da Amarya".
Farouq da Fateema me za su yi idan ban da dariya, Teema dariya har da hawaye, tana cikin dariyar ne ta ji mararta ta wani murd'a, tuni d'an da ke cikinta ta ji yana mata wani mugun juyi, dama tunda ta tashi take Jin ciwon mara kad'an-kad'an sai dai na yanzu yayi tsamari, ba shiri ta cakumo rigar Farouq tare da ruk'unk'ume shi tana fad'in "Farouq bayan marata, washhh"!!!
Cikin tashin hankali Farouq ya d'agata ya sunkuceta sai cikin mota, Nadeeya kanta ta shiga rud'ani irin yadda ta ga fateema ta fita hayyacinta lokaci d'aya.
Cooker gas kawai ta kashe ta fito daga kitchen d'in da gudu ta yi part d'in ta sako hijabi don bin su.
Sai dai tana fitowa mai gadi na rufe gate alamar har sun fice.
Cikin gidan ta koma ta shiga part d'in Fateema ta had'a mata duk kayan da ake buk'ata kama daga na ta har na baby kasancewar komai an siya, don dai Farouq ya rud'e ne shi yasa ba su tsaya d'auka ba......
[9/26, 7:24 PM] Mum Twins : ▪BALLAGAZAR MACE ▪76
Kaitsaye labour room aka wuce da Teema, ko da aka dubata she's almost 8cm ashe a tsattsaye take labour, Farouq na tsaye yana safa da marwa wata Midwife ta fito ta ce
"kai ne ka kawo wadda aka shiga da ita yanzu nan".
Cikin zak'uwa Farouq ya ce
"eh".
Insha Allah muna sa ran haihuwarta nan da 20mnts, don haka sai ka kawo kayanta a shiga da shi zan turo a kar6a yanzu".
"to " kawai Farouq ya ce don shi sai yanzu ma ya tuna da zancen kaya. Cikin sauri ya koma inda yayi parking mota ya figa sai gida.
Yana isa Nadeeya ta gama shiri har kayan ta fito da shi zuwa main parlourn su, ta zuba ruwan zafi a teaflask, da kayan tea duk ta had'a komai na buk'ata.
Ai kuwa Farouq ya ji dad'i kayan kawai aka sa a booth, Nadeeya ta bawa su Raleeya Ansar ta ce "su lura da gida kafin ta dawo".
Fifteen minutes later
*****
Fateema ta haifo santaleliyar yarinyarta, sai dai abun mamakin Jin da ta yi midwives da ke gurin na cewa ta yi nishi ga wani kan baby nan tafe.
Cikin kid'ama da rud'ewa baki na rawa ta ce "wai... wai me... kuke nufi da... sai dai wani azababben ciwo ne ya hana ta k'arasa maganar, a dole ta saki wani wahalallan nishi da ya yi sanadin zuwan wata babyn.
Gaba d'aya midwives d'in suka hau ihun murna, wasu daga cikin su sai addu'a suke Allah ya ba su yara kamar babies d'in nan, nan da nan aka gyara yaran, suka fes identical Twins ba k'arya kyawawa kuma ajin farko.
1st born d'in aka fara mik'owa Fateema, saboda da kid'emewa sai da fatyma ta silmiyo daga kan gadon da take kwance, idonta ta k'ara maidawa kan yarinyar tabbbas ba idonta ke mata gizo ba, fuskar Basma ce a jikin babyn sak tamkar Basma na jaririya, tuni hawayen farin ciki da jindad'i ya zubo a fuskar Fateema, kwantar da babyn ta yi a gefe sannan ta kai goshinta k'asa tana mai yin 'sujudu-shshukur' ga Sarki Allah mai yanda yaso a lokacin da yaso.
Ba ta k'ara girmama al'amarin ba sai da aka kawo mata 2nd born, ba bambanci a tsakaninsu kamar kwabo da kwabo Allah ya so an musu alama da komai k'wak'war mutum ba zai gane wadda aka riga haihuwa a cikin su ba.
Wani murmushi ne ya su6ucewa Fateema don tuna. yadda Farouq zai ji yau ga Basman sa har biyu Allah ya dawo masa da ita.
[9/26, 7:24 PM] Mum Twins : ▪BALLAGAZAR MACE ▪77
©Mrs Saif
Suna tsaye shi da Nadeeya don ko zama sun kasa sai gani suka yi an fito da babies biyu an nufo inda suke, kan Nurses d'in su k'araso har Farouq ya k'arasa gun su, da sauri ya ce "Allah dai yasa ta haihu"
Da murmushi d'auke a fuskarsu suka ce
"ta haihu lafiya k'alau ga ma yaranka".
Cikin zaro ido waje Farouq ya ce "yarana??".
"sosai kuwa, don ko matarka ta haifi Twins duka mata, suka k'arasa maganar tare da mik'a masa babies d'in lokaci d'aya.
Diriricewa Farouq ya yi ya kalli wannan ya kalli waccan ya ma rasa wa zai kar6a a ciki, ganin haka Nadeeya ta mik'a hannu ta kar6i d'aya cike da tsantsar farin ciki, sai dai fuskar yarinyar da ta gani sosai ya yi masifar bata al'ajabi don sak Basma ba maraba da lokacin da take baby.
Tuni son yarinyar ya tsarga zuciyar Nadeeya, ba ta yi aune ba ta ji hawaye na bin kuncinta don tunawa da Basman ta da ta yi.
Wohoho! Farouq kam murna kusan zauta shi ta yi, kar6ar babies d'in ya yi ya had'a su ya rungume tsam a k'irjinsa, ba abinda ya ke yi da ya wuce Tasbihi, gaba d'aya kud'in jikinsa sai da ya rabawa mutanen da ke zaune tsakanin labour room da postnatal.
Wad'anda suka masa albishir da haihuwar kam cewa ya yi "su ba shi account number d'in su zuwa gobe da yardar Allah za su ji alert, haka suka yi godiya cike da murna suka bar wurin.
Nan da nan Farouq ya fara sanarda 'yan uwa a waya na ko wane bangare kan ka ce me an cika asibitin mak'il domin duk wanda ya ji sai ya cika da mamaki, uwa uba ya zo ya ga babies da idonsa, tsantsar k'auna kam da kulawa ba wadda Fateema ba ta gani ba daga kan Farouq har danginsa, ba a maganar danginta, hatta 'yan uwan Nadeeya sun mata kara sosai.
RANAR SUNA
*****
Tsayawa fad'in shagalin da aka kwasa ranar suna 6ata lokaci ne, yara sun ci sunan Fateema Zahra da Fateema Zuhra.
Tun a daren ranar da suka dawo daga asibiti Farouq ya ke gayawa Fateema sunan da ya sakawa yaran.
Cikin mamaki ta ce
"haba Qalby sunan bai yi yawa ba dukan su Fateema".
Murmushi ya yi tare da cewa
"l like the name, you're more than all the sweet names in the world."
Murmushin Teema ta mai da masa sannn ta ce
Thanks alots babe really appreciate".
Sai da ya yi pecking babies d'in a goshi sannan ya yi wa Fateema sai da safe ya ja musu k'ofar ya fice.
*****
Haka rayuwar su ta cigaba da garawa cikin kwanciyar hankali ba wani tashin hankali tsakaninsu kan su a had'e yake tsaf, kun san Zuhra ma a hannun Nadeeya ta ke, idan ka ganta a