Chapter 12 Reading BALLAGAZAR MACE Kuskuren Zuciya by MRS SAIF HN Novels

BALLAGAZAR MACE Kuskuren Zuciya by MRS SAIF

Author :  MRS SAIF Category :  KDP NOVELS

Chapter   12 / 14

33K to 36K   out of 40.2K words

shirya tafiyar dukan su.


******

Suna daf da shiga mota wayar Farouq ta hau ringing alamar call ya shigo, hannu yasa ya d'auko wayar duk da bai san number ba haka ya d'aga.
A d'ayan 6angaren wanda ya kira shi ya ce
"don Allah da Farouq na ke magna?".
Da sauri Farouq ya ce "eh".
"okay, idan ba damuwa ka zo Aminu Kano yanzu 6angaren A&E".

Cikin rashin k'warin jiki Farouq ya ce
"me zan zo na yi Accident and Emergency kuma"??
Mutumin ya ce
"ba wani abun tashin hankali ba ne, matarka ce suka d'an samu matsala a hanya, amma ka kwantar da hankalinka ga ta ma ku yi magana".

Bai jira abinda Farouq zai ce ba ya mik'awa Nadeeya wayar, duk da muryar ta ba ta fita sosai sakamakon kukan da ta ci, amma hakan bai hana shi tambayar Basma ba tunda ya ji tata lafiyar, kukan da ta 6arke da shi yasa ya katse wayar a gurguje ya yiwa su Umma bayani, sannan suka shiga mota don zuwa asibitin, kowa zuciyarsa cunkushe da damuwa barin Fateema idan ban da kuka ba abinda take yi.

Innalillahi Wa'inna'ilaihirraji'un kawai suke maimaitawa sakamakon ganin gawar Basma da suka yi, gaba d'aya kuka suke yi har Umma idan ka cire Farouq da Nadeeya don ita Nadeeya ta yi kukan har idonta ya bushe sai na zuciya kuma, shi kuma Farouq hawayen ma ya kasa yi, sai tafasa da zuciyarsa ke yi tamkar za ta huda k'irjinsa ta fito, idonsa ya yi ja jajur addu'a yake yi Allah ya sa ya samu ko da d'igon hawaye ne ya fito daga idonsa ko ya samu ragin rad'ad'in da ya ke ji a zuciyarsa.

Fateema ce ta yi kukan kura ta cafko wuyan Nadeeya ta fara magana cikin ficewar hankali
"tunda kika kasheta nima sai na kasheki, kowa ya huta sai da na gayawa Farouq kasheta za ki yi ya ce mun ba haka ba wai mafarki ne, ai ga shi nan ya faru a zahiri".

Sosai Fateema ta shak'e wuyan Nadeeya tana wasu suratai tamkar ta6a66iya kuma duk cikin gunshek'ar kuka.
Jin Nadeeya ta fara wani kakari yasa Umma da Faty suka ruga kansu dan jaye hannun Fateema daga wuyan Nadeeya, da k'yar da taimakon wasu Nurses guda biyu suka 6an6are hannun Fateema daga wuyan Nadeeya.

Wani kuka Nadeeya ta saki wanda daga Jin fitar kukan ka san yana tattare da nadama da tarin bak'in ciki, cikin kukan ta fara magana
"Umma na cuci kaina na yiwa kaina gi6in da ba zai ta6a cikewa ba a rayuta, na yi nadama na yi danasani marar misaltuwa, da kun bar Fateema ta k'arasa ni da na fi farin ciki, don na san zan huta da wannan azababben rad'ad'in da zuciyata ke mun... Don Allah Fateema ki kasheni... Ki kasheni na huta kin ji.... Sai kuma ta zube a wurin tana wani irin kuka tare da fitar wani wahallallen numfashi kad'an-kad'an.
Da sauri Nurses d'in dake gurin suka yi kanta don ganin numfashinta na k'ok'arin d'aukewa, ashe ba su sa ni ba ita ma Fateema tuni ta suma anan, don tun lokacin da aka 6an6are Nadeeya daga hannunta, ta ji wani mugun jiri na d'ibanta wanda ya hana ta aiwatar da komai illa zubewa da ta yi anan.
Cikin tashin hankali aka bawa Nadeeya gado kafin daga bisani aka bawa Fateema na ta gadon, kuka kam kala_kala ba wanda Umma da Faty ba su yi ba.

Faruk kam rasa duniyar da yake ya yi, don wani irin juyawa kan sa ke yi, wanda bai ta6a Jin irin sa ba a rayuwarsa, da k'yar ya sa hannu ya dafe bangon wurin tare da lumshe ido, tuni hawayen da yake muradin zuwansu, suka wanke masa fuska......




Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: [9/22, 10:47 PM] Phatyma: â–ªBALLAGAZAR MACE â–ª68
©Mrs Saif

A dole aka yi wa dangin Nadeeya waya aka sanarda su halin da ake ciki, haka ma Fateema sai waya aka yiwa su Ummy aka sanarda su Fateema ba lafiya tana kwance a asibiti, ba su d'auki dogon lokaci ba suka iso hankali a tashe, daidai wannan lokacin ne aka ba da gawar Basma don yi mata jana'iza kamar yadda addini ya tanadar.


Bayan kwana uku da mutuwar Basma aka sallamo su Fateema daga asibiti, zuwa lokacin Fateema ta dangana don likita ya tabbatar mata tana d'auke da juna biyu, saboda haka ya ba ta shawarar ta rage yawan damuwa don samun ingatacciyar lafiyarta tare da ta d'an da ke cikinta.
Kaitsaye gida Ummy ta wuce da Fateema don ta samu kulawa sosai tunda har yanzu jikin na ta da saura.

Nadeeya ma tun ranar da abun ya faru, Mamansu ta iso, ranta ba k'aramin 6aci ya yi ba, akan abinda Nadeeya ta yi, fad'a sosai ta yi mata, don ma Umma na ta ba ta baki.
Ta ce "duk da Nadeeya ce sila amma Allah ya riga ya k'addaro hakan sai ya faru, don haka babu tsimi babu dabara".
Har kawo yau da aka ba su sallama, Maman ba ta wani saki ranta ba, sai haushin Nadeeya ta ke ji.
Sam Nadeeya ba ta Jin ciwon abinda Maman take mata don ita kanta haushin kanta take ji, duk ta wani rame ta rafke lokaci guda kamar wadda ta shekara tana cuta.

******

Zaune suke sun yi jugum-jugum, kowa da abinda yake sak'awa a ransa, tun d'azu da aka ba su sallama suke jiran Farouq ya zo ya biya kud'i su san tudun dafawa.

"ni kam Farouq ina ya je har zuwa yanzu bai k'araso ba"?? Umma ce ke wannan maganar bayan ta duba lokaci a agogon wayar da ke hannunta.

Murmushi Mama ta yi ta ce
"Halimatu kenan kin san fa yau akwai sabga a gabansa tunda yau ne uku, da yawan mutane sai yau za su zo masa gaisuwa".
Umma ta ce
"haka ne amma na ga su Fateema sun tafi tun d'azu".
Kafin Mama ta ce wani abu suka jiyo sallamar Farouq daga bakin k'ofa.
Bayan ya shigo ya gaishe da su Umma, Mama ta dad'a masa gaisuwa, sannan ya kalli Umma ya ce

"Umma don Allah ki yi mun gafara ki yafe mun, don na yanke wani hukuncin da na san ba zai miki dad'i ba, amma ni hakan shi zai samar mun da nutsuwa, don duk lokacin da na ganta zan na tunawa da abinda ya faru da Basma ta sanadinta".

"Farouq wai me ka ke son ka ce ne?,ka fayyace mun manufarka don ban fahimci bayanin ka ba".
Hannu ya sa a aljihu ya ciro wata farar takarda mai d'auke da rubutu ya mik'awa Nadeeya.

Jiki na rawa ta kar6a ta bud'e ta fara karantawa abinda ke ciki kamar haka :Ni Farouq na SAKI matata Nadeeya saki d'aya kamar yadda shari'ah ta ba ni dama, idan ta samu miji ta yi aure.....
[9/22, 10:47 PM] Phatyma: â–ªBALLAGAZAR MACE â–ª69
©Mrs Saif


Kukan da Nadeeya ta saki shi ya dawo da hankulan su Umma kanta, da sauri Umma ta kar6i takardar ta karanta, cikin razana ta yi kan Farouq idonunta cike da 6acin rai.
Da hanzari Mama ta sha gabanta tana fad'in "wai me ya faru"??.
" sakinta fa ya yi, bayan ban ba shi umurnin yin haka ba".
Murmushin takaici Mama ta saki ta ce
"akan wannan ki ke tada jijiyoyin wuya?, ki ma daina damun kan ki, domin abinda Farouq ya yi, yayi dai_dai sakamakonta kenan, dama ta dad'e tana neman sakin,
sai ta kai dubanta zuwa inda Nadeeya ke zaune ta cigaba da fad'in yau burinki ya cika sai ki d'ebi kayanki mu tafi".

Sosai Umma ta nuna damuwarta sai dai Maman Nadeeya tana ta nuna mata ba wata matsala har zuciyarta ta ga dacewar abinda Farouq ya yi don hakan da ya yi zai sa Nadeeyar ta k'ara koyon darasi akan rayuwa.,, duk da zuwa yanzu ta fahimci Nadeeyan na cikin tsananin nadama tare da datasani akan abubuwan da ta akaita, amma wannan ba zai zama hujjar da za ta nema mata afuwa ba gun Farouq, gwanda ta barta ta d'and'ani d'acin zawarci ta ji yadda ya ke, domin ko nan gaba idan ta yi wani auren ya zamar mata Izina.

Haka suka tattara yanasu - yanasu suka wuce tasha don zuwa Dutse.

Sai da Farouq ya je ya biya kud'ad'en da ake bi , sannan ya d'auki Umma a mota don maidata gida, a hanya ban da fad'a ba abinda Umma ke yi, shi dai Farouq ba shi da bakin magana, sai hak'uri ya ke ba ta don dama yasan dole za a yi haka, da k'yar ya shawo kanta ta daina mita, har ya d'an samu ta saki ranta kafin ya tafi.

Ko da ya koma gidansa sai ya ga gidan ya masa tangameme, ba ka Jin motsin kowa, nan da nan kewar mutanen gidan ta cika shi, saukowa ya yi daga saman sa ya bud'e side d'in Fateema ya shiga, yana shiga parlourn manyan toys d'in Basma tare da sauran tarkacen kayan wasanta suka yi masa welcome, wanda ko shi ko Fateema ke siya mata, wanda da yawa daga cikin kayan sun fi k'arfin watanninta.

Teddy d'aya ya d'auka ya rungume, sai ya ke ji kamar Basman sa ya rungume tuni mutuwarta ta dawo masa sabuwa fil, bai yi aune ba ya ji hawaye na bin kumatunsa, a fili ya ce
"ba zan iya rashin dukanku ba, Fateema ki yi hak'uri ki dawo gareni nima zan kula da ke kamar yadda Ummy za ta yi, tabbas idan na cigaba da zama ni d'aya na tabbatar da ciwon rashinku zai mun mummmunan kamu....




Mum Twins 😘
[10/16, 4:47 PM] mrm kd: [9/23, 9:53 PM] Phatyma: â–ªBALLAGAZAR MACE â–ª70
©Mrs Saif


Kuka sosai Farouq ya ke yana sambatu shi kad'ai har sai da ya fara Jin kansa na wani mugun sarawa sannan ya rarrashi kansa ya yi shiru, ya fi k'arfin 30mnts zaune a wurin daga k'arshe ya ga zaman na shi damuwa kawai ya ke k'ara masa saboda haka ya zari key d'in motarsa ya fita da zummar zuwa gidansu Fateema.

Ko da ya isa gidan Fateema ta yi barci, sai Ummy ya tarar, bayan sun gaisa ya ke sanarda ita buk'atarsa na son a maida masa da matarsa, don yana tsananin buk'atarta a kusa da shi.
Guri Ummy ta nema ta zauna sannan ta ce
"Farouq ka yi hak'uri Fateema ta d'an k'ara warwarewa ka san har yanzu akwai damuwa a tare da ita,tana buk'atar kulawa ta musamman, zamanta anan ina kyautata zaton zai taimaka mata wurin saurin mantawa da mutuwar Basma, ka yi hak'uri har a kwana biyu sai a dawo maka da ita, tunda ga Nadeeya.

Girgiza kai ya yi sannan ya ce
"Ummy mun rabu da Nadeeya".
"Subhannallah! Ummy ta fad'a cikin mamaki.
"Ai da ba ka saketa ba, komai ai muk'addari ne,dama haka Allah ya tsara bai mai nisan kwana ba ce yarinyar".

Farouq dai bai ce komai ba illa bin ummy da ido, don shi kad'ai yasan irin halin da yake ciki a yanzu.
Shiru ita ma Ummy ta yi tana nazari domin duk wanda ya ga Farouq dole ya tausaya masa musamman yanzu da ta ji sun rabu da Nadeeya ta tabbatar shima yana da buk'atar mai rarrashinsa, amma kuma idan ta amince masa Fateema ta koma a yanda take gaskiya akwai matsala don a yarda take aiki ko na kitchen ne ba kamata ta yi ba don cikin jikinta bai yi k'wari ba, ga shi likita ya ja musu kunne sosai akan kula da yanayin motsinta don ana son ta samu hutu sosai, don Allah ne ya kiyaye ba ta samu miscarriage ba,don haka gaba d'aya kan Ummy ya kulle ta ma rasa mai za ta ce da Farouq.

Kamar ya san abinda ta ke tunani ya ce
"Ummy kar ki sawa kan ki damuwa wallahi zan kula da Fateema sosai, duk wani abu da ya kamata a yi mata zan yi kokarin yi, kuma ba zan bar ta ta yi ko wane irin aiki ba, sannan zan kira Faty ta dawo gidan da zama har zuwa lokacin da za ta warware, zan kuma yiwa Umma magana ta tuntu6i su Raleeya idan ba yanzu za su dawo ba, a nemi wasu kawai".

Ajiyar zuciya Ummy ta sauke ta ce
"shi kenan ba matsala sai ta koma, amma sai zuwa gobe tunda ka ga yanzu ta yi barci".
Murmushi Farouq ya yi ya ce
"ba komai na gode Allah ya k'ara girma".

Har ya mik'e da zummar tafiya, Ummy ta ce
"Amma Farouq kafin ta dawo ka yi k'ok'arin kwashe duk wani kaya da ya shafi Basma a wurin da za ta iya gani, za ka iya kai su ko part d'in Nadeeya ne ka kulle".

"okay, to Ummy dama nima na yi wannan tunanin, insha Allah zan yi yadda kika ce".

Yana gab da fitowa daga parlourn, Abbansu Nadeeya ya dawo tare da yayyanta guda biyu, anan ya tsaya suka gaisa tare da k'ara masa gaisuwa, sannan ya fito daga gidan...
[9/23, 9:53 PM] Phatyma: â–ªBALLAGAZAR MACE â–ª71

Kwanaki na k'ara shud'ewa lokaci na tafiya, cikin Fateema yanzu har ya kai wata bakwai zuwa lokacin sun rubuta final exams d'in su, don haka yanzu ba su da wani lokaci da ya wuce na rainon cikinta, kullum Farouq na mak'ale da ita, idan har yana nan baya barin Fateema yin komai, da zarar za ta yi wani aiki zai kar6e ya ce shi zai yi ita ta zauna ta huta, ba yanda ta iya dole ta hak'ura ta bar masa ya yi.

Fateema ce zaune a parlourn Farouq akan rug ta mik'e k'afarta Farouq na matsa mata k'afar da ta d'an fara kumbura.
Dariya ya saki sannan ya ce
"babe an ya cikin nan ba 'yan hud'u ne a ciki ba, na ganshi wata bakwai amma kamar yau za ki haihu yayi wani k'atoto". Ya k'arasa maganar yana kwatanta girman cikin da hannunsa.

Pillow ta janyo daga kan kujera ta jefa mishi cikin sigar wasa ta ce
"wallahi ban ji bakin ka ba, duk son yarana hud'u sun mun yawa ni kam".

Dariya sosai Farouq ya yi ya ce
"ni dai in har ke za ki haifa mun ko goma ne ina so".

Dariya itama ta yi ta ce
"ni ban ma ta6a Jin d'an Adam ya haifi yara goma ba, sai ka ce Tinkiya"
Ai kuwa Farouq Me zai yi idan ban da dariya haka yai ta dariya Fateema na taya shi.

*****
DUTSE

Nadeeya ce a kitchen ke kiciniyar had'a girkin rana, don tun safe da ta tashi ba ta zauna ba ita ta yi share-sharen gidan da goge-goge, dama tun zuwanta ita Mama ta sakarwa aikin gidan, da kafin zuwanta yayyen ta ke yi wad'anda aka sako, to su yanzu Allah ya tarfawa garinsu nono don kuwa sun samu mazan aure sun d'aga sun bar Nadeeya.

Ga shi yanzu ba irin da ba ne don komai tsaftsaf suke yin sa, domin Mama ta d'auki darasi yanzu ba ta ta6a barin yaro ya zauna haka nan sasakai musamman Nadeeya da gayya take sakata ayyuka masu wahala don ta gane kuskuranta.
Adalilin k'azantar da suka tafka yasa, sai da suka saida gidan su, suka siye wani a wata anguwar daban, saboda ba k'aramin tambari mutanen unguwar suka musu ba, takai ko zuwa neman auren 'yan gidan ba a yi, saboda tsegumin da ' yan unguwar ke kaiwa duk wanda ya fito neman aurensu, daga k'arshe suka yanke shawarar tashi daga unguwar.

"Mama don Allah khadija ta zo ta k'arasa soya funkasun nan, bayana har ya k'age ga shi ina son na je na yi wanka don duk na yi gumi". Nadeeya ce ke maganar daga cikin kitchen.

"wai sau nawa zan gaya miki sai kin gama aikin nan tsaf kin wanke kwanikan da aka yi amfani da su kin share kitchen d'in kin goge sannan ki yi maganar fitowa, gwanda ma ki yi sauri kafin lokacin zuwa makarantarki ya yi".

Sai da Nadeeya ta gama aikin nan tsaf ta yi shirin zuwa makaranta, da yake tana zuwa makarantar islamiyya mai suna Mar'atussaleh, ba abinda ba koyarwa ta fuskar addini sannan ana koyawa mata duk wasu sirrika na mallakar miji a sauk'ak'e ba boka ba Malam.

Sai a sannan Nadeeya ta fuskanci ta yi babban kuskure a baya da take tunanin shan maganin mata ne kawai zai sa miji ya so ka, sai yanzu ta gane ashe sam abun ba haka ba ne, shi yasa ta k'udire a ranta duk mijin da ta aura nan gaba za ta zame masa salihar MACE mai biyyya ga miji, ta kuma bi duk wasu matakai da ta koya na siye zuciyarsa miji.

Tunda ta jefa k'afarta cikin gidan ta ji mayataccen k'amshin turarensa, ko kallon gefen da yake ba ta yi ba, ta yi hanyar shiga d'akin su.
Shi ko sai d'ashe baki ya ke yi a dole ya ga masoyiyarsa.

"Nadeeya! Nadeeya!"Mama ke k'wala mata kira lokacin da ta hango shigewarta.
[9/23, 9:53 PM] Phatyma: â–ªBALLAGAZAR MACE â–ª72
©MRS SAIF


Dawowa ta yi ta tsaya ba tare da ta juya ba
Ta ce "ga ni mama".

"au yanzu wulak'ancin na ki ya kai ki na ganin mutum ki share shi ki wuce".
"ni fa Mama ban gan shi ba". Nadeeya ta fad'a tare da d'an turo baki.

"to barin in gaya miki ki shiga hankalinki, idan ba haka ba zan mugun sa6a ki, a wannan zamanin 'yan mata ma ya suka cika bare ke bazawara, don kin samu mashinshini shine har kike masa wulak'anci, to ahir na san hankalinki duk yana wurin tsohon mijinki, dama hak'ura kika yi da shi don na tabbatar zuwa yanzu Farouq ya manta da wata halitta ki, yana can da matarsa hankalinsa kwance, ko Ansar watansa nawa bai zo ya gan shi ba, ki na gani sai dai kakarsa ta zo duba shi, amma ni ban ga laifinsa ba, don duk ke ki ka jawo, don bahaushe ya ce na ji dad'i shine gari ba na saba ba".

Tunda Mama ta sako zancen Farouq Nadeeya ta fara share hawaye, don yanzu kuka akan Farouq ya zame mata jiki, ba ta da wani buri a duk duniyar nan da ya wuce ta kuma auren Farouq a karo na biyu, sai dai ita kanta ta san ya mata nisa, nisan da ba za iya tarar da shi ba.

Mama ce ta katse mata tunani ta hanyar fad'in
"yanzu haka maganar sa rana ya zo yi, kuma ni na ba shi damar gobe ya je gun baffa babba su yi magana yasso daga baya ya turo wakilansa kawai a d'aura aure ba wani abu da za a tsaya jira".
Ai kuwa tuni kukan Nadeeya ya tsananta fiye da d'azu.

"eh lallai! za ki wuce ki je ki same shi ko kuwa"?
"to

12 / 14