Chapter 1 Reading BALLAGAZAR MACE Kuskuren Zuciya by MRS SAIF HN Novels

BALLAGAZAR MACE Kuskuren Zuciya by MRS SAIF

Author :  MRS SAIF Category :  KDP NOVELS

Chapter   1 / 14

1 to 3K   out of 40.2K words

BALLAGAZAR MACE COMPLETE
[10/16, 4:21 PM] mrm kd: ◾BALLAGAZAR MACE ◾ 1&2
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
©MRS SAIF
®NWA


wannan labarin zan iya cewa ya faru da gaske, Cox some episodes are non fiction, while some are fiction, don na yi k'arin gishiri a wasu wuraren saboda littafin ya fi d'and'ano 💋

SANARWA
Wannan labarin ban yi da wata manufa sai don fad'akar da 'yan uwana mata, musamman masu aure, da kuma ' yan matan da suke da niyyar yin aure, don haka ban yi don wata ta ji haushi ba, sai dai arashi ne da duk mai irin halin,Allah ya sa mu gyara ameen. 👏🏻


GARGAD'I
Ban yarda gardi ko gardiya su juya mun buk ba, ta ko wace siga, musamman masu editing su cire sunan writer, don Allah ku daina, ba abu mai kyau ba ne.




Tunda na jefa k'afata a cikin gidan na ke ta Karo da kwanika, ga sunan birjik a tsakar gidan, ba wanki, tamkar kwanikan da mutanen gari suka ci abinci, saboda tsananin yawansu,kuma abun da ya dad'a d'auremun kai, gurin da aka zuba kwanukan kwata_kwata bai yi kama da wurin wanke_wanke ba, cikin 2mints na k'arewa gidan kallo.

Madaidaicin gida ne, wanda kana shigowa za ka tarar da parking space wanda aqalla ya ci motoci hud'u, sai parlour d'auke da 4 bedrooms, kitchen, toilet and store.
Sai da muka shiga parlourn, na lek'a kitchen sai na ga ashe kusan duk kayan kitchen d'in ne a waje ba wanki.
Na juya na kalli sister maryam da muka je tare, na ce
"an ya kuwa nan ne gidan amarya da ko wata bata yi a gidan miji ba??
Maryam ta ce "nan ne don nan ta kwatanta mun da ta shiga lokacin ba kya nan".
Ban gama mamaki ba kuwa sai ga ta ta fito, tana washe ba ki, ta ce "maman Twins ashe ke ce a gidan na mu, ku shigo mana"
Murmushi na yi, na ce "eh Amarya, ai sister na ta ce kin zo har sau biyu ba ki same ni ba shi yasa na ce bari na lek'o".
Soshe_soshe ta fara kamar wadda ba ta yi wanka ba, tana fad'in "eh wallahi, zaman ne mutum d'aya ba dadi, shi yasa na ke so mu saba dake, tunda ni dai anguwar nan ban San kowa ba, kad'aici duk ya dameni, kin ga na yi kallon har na gaji, haka ma chat, don haka nake so na dan samu wurin zagawa, ta k'arashe maganar da sakin wata dariya.
Kallon_kallo muka tsaya yi da maryam, sannan cikin yak'e na ce
"haka ne gaskiya"
Sai kuma ta mik'e tana fad'in bari ta kawo mana ruwa, tafiyarta ta ba mu daman k'are ma parlourn kallo, ga parlor har parlour, amma rashin gyara yana barazanar hana a ga kyan parlourn, don TV kawai za ki kalla ki san parlourn yana buk'atar gyara, don k'urar da ke jjkinta tsaf zan rubuta sunayen writters da muke da su a jiki a kuma ga ne.

Ga shi tunda muka shigo wani bala'in zarni ke tashi, daga cikin kujerun da muke zaune, abin ya matuk'ar ba ni mamaki abinda ya kawo zarni d'akin amarya.
Bayan ta kawo mana ruwa muka d'an ta6a hira da ita, muka ce za mu tafi, ta ce
"to shike nan na gode, sai na shigo"
Na bita da to, sai da za mu fita na hango mage a cikin flowers d'in da ke harabar gidan, cikin raina na ce tabbas zarnin da muka ji, na fitsarin mage ne, don rashin kula har ta bari mage ta rik'a shiga d'aki tana lafta mata fitsari, haka muka kuma tsallake kwanikan nan muka wuce, ina tunanin ita kuwa tana aikin meye har wanke_wanke ya tarar mata haka kamar tun da aka kawo ta ba ta ta6a wanke kwanika ba , don set d'in warmers ga su nan kala_kala banda pots, plates, spoons, knives da sauran kayan amfani duk baja_baja kamar ana gwanjon su.

Bayan mun iso gida na kalli maryam na ce
"gaskiya matar nan akwai gyara a lamuranta, kalli fa gidanta tun kafin ta kai wata biyu da aure, ai dole na cigaba da bibiyarta don ganin irin annakiyar da zata yi, saboda na d'aukowa readers rahoto".....


Mum Twins 😍
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ◾BALLAGAZAR MACE ◾3&4

©MRS SAIF
®NWA

Wacece Nadeeya ???
Nadeeya 'ya ce a wurin Alhaji Sani Haruna, asalin su' yan garin dutsen jahar jigawa ne, domin dukkan su a can aka haifesu, su goma cif, mama Haleema ta haifa, su takwas ne mata, sai maza biyu, su ne manya.
Nadeeya ita ce ta bakwai a gidan, mahaifinsu yana da kud'i dai_dai gwargwado, don ba abun da baya musu na buk'atar su.
Mutum ne shi mai son farantawa iyali, don duk abinda ake ya yi, za ka gan shi a gurinsu, daga kan sutura kayan kyale_kyale ne, da na gyaran gida ne duk a wurin su za ka fara gani, sai dai kash!!! Maman su muguwar k'azama ce,da ko inkula akan komai, domin ko 'ya' yan ta, bata basu cikakkiyar kulawa,bare har su samu kyakkyawar tarbiyya, shi yasa suka taso da baud'add'un halaye duk abinda suka ga dama shi suke yi,Nadeeya ga azababben son yawon tsiya, barin ma aka ce biki, anan kuwa ko za a kasheta sai ta je matuqar ta san da bikin,baya da k'azanta da ta zama kamar gadon gidan su, don kusan dukkansu suna da wannan halin.
Don ma sun samu uba mai kashe musu, don duk abinda ya samo zai kawo gida, amma ina nan da nan abubuwa suke lalacewa da an kawo saboda rashin gyara, gida ga shi k'ato, ya kuma k'eru, amma daud'a duk ta kashe gidan, idan ka shiga gidan kamar shek'ar karnuka, don maman su ba ta iya komai sai dai ta saka 'yar aiki, gata da 'ya'ya mata Allah ya ba ta, amma ba ta saka su sai dai su ci su yi kallo, idan lokacin barci ya yi su je su kwanta.
Ga shi' yar aiki d'aya ta ke d'auka duk girman gidan, ita za ta yi komai, don akwai ta da son kud'i, ba ta son ta d'auki 'yan aiki da yawa ta san za su ci kud'i da yawa, shi yasa da sun fara sun ga baza su iya ba, sai su gudu.
Daga k'arshe ta hak'ura da maganar ' yan aikin, sai su ke damalmalaya ita da sakarkarun 'ya' yan ta, aikuwa a lokacin ne k'azanta ta samu gindin zama a gidan, don sai rana ta kusa fad'uwa suke fara shirin share_sharen gida, wanke_wanke kuwa sai dai duk wanda zai yi amfani da kwano ya je ya wanke da kan shi.

Shi kam mopping ba a ma maganarsa, don sai a yi wata gidan bai samu arzik'in mopping ba. Don idan ki na taka tiles d'in gidan, sai ki rantse gam aka zuba, saboda dank'o, don sai ki na d'aga k'afarki da k'arfi, gudun mannewa a jiki.

A unguwar ma idan ba ki ce gidan k'azamai ba, baza a gane gidan su Nadeeya ki ke nufi ba, tun mai gidan yana fad'a har ya saduda ya hak'ura, shi ma ya bi.
(kun san idan mace k'azama ce, ko da mijinta yana da tsafta sai ki ga a hankali ya fara rikidewa shima yana zama k'azami)kafin daga bisani Allah ya masa rasuwa, a lokacin Nadeeya na ss1.
To daga nan fa sai al'amura suka dad'a ta6arbarewa, don mai hana su wasu abubuwan ba ransa, sai abinda mama ta zartar ita kuma dama ga ta sai a hankali.

Dama hausawa sun ce
"Da na gaba ake gane zurfin ruwa,"
Saboda haka k'azantar Nadeeya da duk wata ta6ara mai license ce, don tun daga gida ta debo ta, ku dai ku biyo ni don Jin irin tata annnakiyar, don bahaushe ya ce
"gado fi ya ke"


Mum Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪4&5

©MRS SAIF
®NWA

Misalin k'arfe 6 na yamma Faruk ya dawo daga aiki, ransa a matukar 6ace ya shiga parlourn gidan, akan kujera ya tarar da ita tana shan fruits, duk ta yi kaca_kaca da 6awon kankana da lemo, don gida biyu ta raba kankanar sai ta d'auki 6ari d'aya ta kafa kai tana sha.

Wata naunanniyyar ajiyar zuciya ya sauke, ganin da ya yi ita kanta ba abinda ya chanza a jikinta, don tun shekaran jiya ta saka kayan jikinta, amma har yau ta kasa cireshi, wani d'an k'aramin tsaki ya ja, da niyyar ratsewa ta gaban ta ya wuce d'akin sa.
Hakan ya yi dai_dai dawowar nadeeya daga duniyar da ta lula ta shan kankana, juyowa ta yi tana kallonsa tare da fad'in "Faruk har ka dawo ke nan, ta fad'a tare da washe baki.
Kai kawai ya gyda mata ya k'arasa shigewa d'akin sa, baki ta ta6e tare da fad'in" mutum sai shegen miskilancin tsiya maganar ma wahalar yi take masa".

Faruk kuwa yana shiga d'aki kayan sa, ya tu6e, ya shiga wanka, bayan ya gama ya d'oro alwalar magrib, farar jallabiya sol ya saka, sannan ya feshe jikinsa da perfumes d'in sa masu dadin k'amshi.
Parlourn dai ya kuma komawa, still tana nan yadda ya bar ta, sai remote da ta d'auka tana canja channel, kuma yanzu ta gama shan kankana, ayaba take ci.
Neman guri ya yi ya zauna a d'aya daga cikin kujerun parlourn, duk da bai Jin dadin yanayin tsamin dake ta shi daga cikin parlourn, amma haka ya daure ya zauna.

Ganin ya zauna ya sa Nadeeya Jin dad'i, don akwai ta da d'an banzan surutu, don dai Faruk ba ya sakar mata fuska ne, da ya sha hira.
Sai da ta gutsiri kusan rabin ayaba ta saka a bakinta sannan ta juyo tana shirin masa magana, hannu ya d'aga mata tare da mikewa tsaye yana fad'in "masallaci zan je yanzu, sai dai ki bari sai na dawo, kafin nan kin cinye abinda ya ke bakin ki". Don ya tabbatar idan ya cigaba da kallon yadda bakinta ya dame da ayaba hakan zai iya barazanar sa shi tashin zuciya, wanda zai iya kai shi da yin amai, don dai Faruk akwai shi da k'yank'yami tun yana yaro, hakan yasa ya dade yana neman macen da ta dace da ra'ayinsa amma Ummansa ta yi gajen hak'uri ta had'a shi da 'yar aminiyarta, wadda bai da tabbacin yadda yarinyar take, tun da ba a gari d'aya suke ba.Su Faruk suna kano, su kuma su Nadeeya' yan jigawa ne, kuma ita umman Faruk ba zuwa take yi ba, ummansu Nadeeya ce ke yawan zuwa, ko idan an yi hutu ta turo su Nadeeya.
Dan k'awancen na su dad'add'e ne, ya samo asali tun lokacin da suke boarding school na dala,
Da yake masu son xumunci ne sai ba su watsar ba,amma Faruk kam bai ma ta6a zuwa jigawan ba, sai ranar d'aurin aurensu.

Don ko lokacin da aka saka bikinsu, ba wani zuwa gurin ta ya ke yi ba, sa dai ya yi ta tura musu kud'i hakan ya saka ba su damu da sai ya zo ba. Nadeeyan ce ma mai damuwa don gaskiya tana tsananin son Faruk, sai dai kash bata san hanyoyin da zata bi don shawo kansa ba, a maimaikon haka sai ta sa a ranta ai da an kawota gidan sa shi kenan dole ya sauko ya bi ta, sai dai abinda ya ba ta mamaki ko bayan aurensu ba ta chanza zani ba.

Don haka ta tattara shi ta watsar, sabgar gaban ta kawai take yi, a cewar ta burin ta ya riga ya cika tun da ta aure shi.

Da wannan tunanin ya fice daga gidan ba ki d'aya, zuciyarsa cunkushe da tunanin wannan wace irin mace ce????
Aure ko wata 3 bai yi ba, amma ya fara Karo da matsaloli, gaskiya Nadeeya kwata_kwata ba ta dace da shi ba, don ta ko'ina ba ta yi kala da matar da ya ke muradin aure ba.

Don aurenta ya d'auke sa, a matsayin k'addara ce kawai, don akwai shi da biyayyar iyaye musamman mahaifiyyarsa da ita kadai ta rage masa sai k'anwarsa....


Mum Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪6&7

©MRS SAIF
®NWA

Bayan sun idar da sallah, ya fi k'arfin 30mnts yana zaune a parlor yana jiran Nadeeya ta kawo masa abincinsa, amma shiru ka ke ji, sai da ya lek'a d'akinta don ya sanarda ita ta kawo masa abinci, tunda ita kwata_kwata ba ta san abinda ya da ce.
Turus ya yi bayan shigar sa d'akin , yana duban abinda ke gabanta, taliya ce a gabanta wacce ake kira shar6u take kwasa, kusan rabinta duk ruwa ne, ga shi ta kwasota za ta kai baki ruwan taliyar har yana tsiyaya ta tsintsiyar hannunta.
Bud'e ido yayi yana kallonta, tare da fad'in "amma ni dai ba wannan abincin ki ka dafa da ni ba ko"???
Ita ma kallon nasa ta yi, tana cewa"au dama har wani dafa abinci ake kashi_kashi???
Ta cigaba da fad'in" tab! Wai aiki, don yau ka ji dad'i ma ban yi tazarce ba, don na ji ina son cin jaloup d'in taliya, shi yasa kk wannan maganar."

Dafe kan sa yayi, yana fad'in "yanzu kina nufin wannan k'azamain abincin zan ci "???
K'ara sul6ar taliyar ta yi, sannan ta ce" ni fa ban ce dole ba, idan ka ga xa ka iya ka ci, idan ba za ka iya ci ba, ka bar shi ba dole."
Kamar zai yi magana, kawai sai ya shareta ya fito daga d'akin.
Kitchen ya nufa ya hada tea ya sha don yunwa ce fal cikinsa, don yau bai samu ya ci abinci a office ba, saboda ayyukan da suka saka shi a gaba.

Tun asuba da ya tashi bai koma barci ba, don da wuri yake son fita, don haka da kan shi ya shiga kitchen ya d'ora ruwan zafi, don ya tashi Nadeeya ya kai so uku ta k'i tashi, tea dai ya kuma had'awa ya sha, a ransa yana cewa "shi bai ga amfanin auren da ya yi ba , har gwanda lokacin da yana gidansu sau dubu."

Har ya kusa gama shiri sannan ya jiyo,, katuwar hammar Nadeeya alamun ta tashi, k'amshin turarensa ne da ya cika gidan ya tabbatar mata da ya gama shiri don haka cikin azama ta diro daga kan gado ta yo waje, dai_dai lokacin Faruk ya fito sak'ale da jakarsa alamun ya gama shiri zai fita.

Kallo d'aya ya mata ya d'auke kan sa duk ta yi wani dagaje_dagaje da ita kamar wadda aka k'wato a bakin kura, gashin kan ta duk ya wani cukurkud'e, haka idonta duk kwantsa ya cikasa, bakin ta taf yawun barci take shirin yi masa magana, da sauri Faruk ya k'ara wuta zuwa k'ofar fita, yana fad'in "akwai kudi na nan na ajiye miki akan stool, ko da za ki yi wani amfanin".

Yana k'arasa maganar ya fice da sauri, don baya son cigaba da kallon yanayin da take ciki, don hakan yana haddasa masa tashin zuciya...........

Maman Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR MACE ▪8_10

©MRS SAIF
®NWA

Dama ita Nadeeya saurin da take yi, don ta kar6i kud'i ne, kafin ya fita, don haka Jin ya ajiye mata kud'in ya sa, ta shige toilet ba tare da ta kuma bi ta kansa ba.

Faruk kuwa driving ya ke, amma hankalinsa gaba d'aya baya kai, yana can yana tunanin halin da ya tsince kansa, a zuciyarsa yana cewa "wai yanzu a haka rayuwarsa zata cigaba da tafiya da wannan yarinyar"????

Tambayar da yake ta nanatawa a zuciyarsa kenan, sai dai kash ya kasa samo amsar tambayarsa, tunawa da yayi yanda mahaifiyarsa ke son aurensa da Nadeeyar , yasan ko giyar

1 / 14