Author : SA'ADATU I FULANI Category : KDP NOVELS
ɗaga kai ya kalleta ba,
Inna tasa mai kuka ta na cewa saboda ita ba yarinyar so bane shiyasa yayi banza da ita amman da Fatima ne da tini ya fusata yayi waje.
Inna taci gaba da magana tana cemai wallahi yaji tsoron Allah ya daina nuna bam bamci a kan iyalan shi har tayi ta gama bai kalleta ba Inna tasa kai ta fita,
Bayan fitan ta Baffa ya tashi yaje ya tsaya a bakin ƙofa ya hango Rabi'a tana kwashe wanke wanke Ismael kuma yana zaune a inda yake tin ɗazun bai motsa ba,
Baffa ya kira Rabi'a ya ce "ta kira mishi Mama sannan ta kira mishi Amina a ɗakin Inna,
Baffa ya kalli Ismael ya ce "zoka kira mun gadanga ko Nasser a waya
Ismael ya tashi yabi bayan Baffa da ya shiga ɗaki,
Baffa ya bashi ƙaramar wayar da Aliyu ya siya mai ya ce maza kira mun su kabani wayar,
Ismael ya kira Aliyu ta shiga tana ringing bai ɗauka ba sai ya kira Nasser ringing ɗaya Nasser ya ɗauka Baffa ya karɓi wayar bai tsaya amsa gaisuwar da Nasser yake ba ya ce kazo gida ka sameni yanzu,
Nasser ya ce gayi nan zuwa Baffa yaba Ismael wayar Ismael ya amsa ya kashe wayar Mama tayi sallama ta shiga ɗakin.
Baffa ya samu guri ya zauna Mama ta zauna kusa dashi
Baffa ya kalli Ismael ya ce "ka gaya ma tsohuwarka ita nake jira.
Ismael ya fita yana ƙunshe dariya ɗakin Inna ya shiga ya same su zaune ta tasa Amina a gaba tana kallo ita kuma Amina ta nata kuka,
Ismael ya kalli Inna ya ce "Baffa yana jiranku keda wannan mara kunyar yana faɗin hakan yayi waje da sauri,
Inna tace daka sani ka tsaya kaga a binda zanyi maka ƙaramun mara kunya kawai
Inna ta hau lalaɓa Amina akan ta tashi suje kiran da Baffa yake musu.
Daman tin ɗazun take lalaɓa ta amman taki motsawa suna cikin hakan Nasser yayi sallama ya shigo ya tsaya bakin ƙofa.
Inna ta amsa sallamar ya duƙa har ƙasa ya gaishe ta Inna ta amsa ta tambaye shi iyali ya ce
Alhamdulellahi Nasser ya kalli Amina ya ce
waye sa'an wasanki a gidan nan da zaki shanya mutane zaman jiranki Amina ta duƙar da kai ƙasa.
Inna tai karaf ta ce "bacci ne ya ɗauke ta yanzu ta tashi Nasser bai kara magana ba ya fita Amina ta tashi tana tura baki tabi bayan shi Inna tabi ta a baya.
Amina tayi sallama ta shiga ɗakin ta gaishe da Baffa ta gaida Mama ta samu guri ta zauna Baffa ya kalli Amina ya ce "lafiya kika zo kina kuka kuma kinƙi magana Amina ta duƙar da kai tana hawaye ta ce
"Daman shi ya ce in zo gida sai ya nemeni Baffa ya kalli Nasser ya ce "kira mun mijinta muji gaskiyar zance,
Nasser ya miƙama Amina wayarshi ya ce "tasa mai number shi Amina taƙi karɓan wayar Baffa ya daka mata tsawa ya ce idan tai wasa yanzu nan zata ji a jikinta,
Hannu yana rawa ta karɓi wayar tasa number Nasser ya karɓa ya baɗe kiran gaba ɗaya sannan ya kira ringing ɗaya a ka ɗauka haɗe da sallama,
Suka gaisa da Nasser tin kafin Naseer yayi magana ya riga shi
Ya ce "Amina ta zo gida Nasser yayi banza dashi ya cigaba da cewa.
Wallahi Amina bata da mutunci ga rashin kunya ga rainuwa idan yayi mata abu sannan kuma ta raina mahaifiyar shi bai isa yasa ta ko ya hanata ba.
Duk abinda yayi mata bai iya ba ga hangen rayuwar wasu.
Ga faɗar baƙar magana hatta mahaifiyar shi gaya mata ta keyi dan Allah su barta a gida ta kwana biyu ko zata sanja hali amman shi gaskiya ya gaji da ita.
Nasser zaiyi magana Baffa ya hana sai da suka gama jin abinda ya faɗa sannan Baffa ya karɓi wayar ya ce " idan babu damuwa yana son ganinshi ko zuwa anjima Sager ya ce " in sha Allah zaiyi ƙoƙirin zuwa.
Bayan sun gama magana ya kalli Inna da ke tsaye a bakin ƙofa ya ce "ta shigo ya kalli Nasser da Amina tin kafin yayi magana suka fita.
Baffa ya kalli Inna ya ce " hanakalin ki ya kwanta kin ɓata mun tarbiyan yarinya Inna ta ce "tayaya daga faɗan magana zai hau kai ya zauna babu bincike ita yarinyar mana a tambayeta aji ta bakin ta.
Baffa ya kalli Inna ya ce "duk abinda ya faɗa bakiji ba Baffa ya cigaba da cewa wallahi kinji na rantse duk abinda ya faɗa ta aikata shi.
Baffa ya cigaba da cewa cikin yarana nasan halin kowa nasan abinda in a kace sun aikata zan yarda amman saboda ƙin gaskiya irin naki kince sharri a kai mata.
Inna ta fara hawaye Baffa ya ce "ta adana hawayenta domin lokacin zuban su baiyi ba ya ƙara da cewa ta fitan mishi a ɗaki zai zo ya sameta Inna ta fita tana kuka.
Mama ta kalli Baffa za tayi magana ya da katar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu ganin hakan Mama tayi shiru tana kallon shi.
Baffa ya ce " tasa Rabi'a ta kawo mishi tea idan ta fita.
Mama ta najin hakan ta miƙe tana cewa dan Allah yayi haƙuri kar yasa wannan damuwar a zuciyar shi tinda baida isashen lafiya.
Bayan fitan Mama daga ɗakin Baffa ɗakinta ta nufa ta samu Rabi'a tana guga Mama ta ce " ta haɗa ma Baffa Lipton ta kai mishi bata jira amsar da Rabi'a ke bata ba ta shige bedroom domin ta kwanta.
Rabi'a ta kashe socket ta fita kitchen ta shiga ta haɗa kamar yanda ta san yana so ta shiga ɗakin bayan tayi sallama ta samu Baffa zaune a inda Mama ta barshi.
Rabi'a ta duƙa tayi mishi sannu da jiki ta miƙa mishi tean Baffa ya karɓa yana samata albarka.
Rabi'a tana son Baffa saboda duk idan suka haɗu sai ya sa mata albarka ko gaishe shi taje yi da safe zaita mata addu'o'i.
Rabi'a ta koma ɗaki ta cigaba da aikin ta.
Bari mu koma gidan Aliyu
Ta Batulu ✍️