Author : SA'ADATU I FULANI Category : KDP NOVELS
gabanshi,
Fatima tayi dariya tace ƙyale shi ya Nasser kamar a kunnen ya Aliyu,
umar yace to munafuka sai kin dawo,
Nasser ya kallesu dukan su yace musu kun San menene,"?
suka ce mai a'a yace musu wlh bro gata yayi muku,
Nasser yace
yanzu kai umar ka gama makaranta kayi candy
wannan shekaran,
mai ya rage Maka,"?
Umar ya hau washe baki yace saura jami'a Fatima tace ai shi mafarkin Shi kenan,
Nasser ya cigaba da cewa, amman ka san ba kai tsaye bro zai barka ka tafi jami'a ba,"?
Umar yayi shiru sai Nasser ya cigaba da cewa ni dai shawaran da zan baka,
itace karka nuna mai baka son wannan makarantar domin kuwa,
Idan kuma ka nuna mai baka so ka san abinda zai biyo baya,
Nasser
Ya kalli Fatima yace kefa,"?
Fatima tace ni wallahi banda zaɓi Nasser yace kin huta ma kanki shima ya tashi yayi ma mama sallama ya fita,
Umar ya kalli Fatima yace mata wallahi Ismael nake tausayawa domin na san baza su kwashe ta daɗin rai ba shida ya haydar,
Fatima tayi dariya ta bashi labarin abinda ya faru ɗazun,
Shima dariyan yayi yace kice anjima akwai kallo,"?
Fatima tace ai dukan su har yanzu basu san halin ya Aliyu ba,
umar yace na tina wani mari da ya taɓa mun sai da na suma,
Fatima tayi dariya Mama ita kanta sai da ta dara,
Fatima tace ni dai karka ƙullar mun da ciki bari in ɗauko Assignment ɗina Dan allah,
Fatima tashiga ciki ta fito da jaka tazo ta aje a gaban shi tace mai ya koya mata ne,
Fatima tana da wani ɗabi'a guda ɗaya,
ita ko abune bata iya ba bata cewa ayi mata,
Sai dai tace a koya mata saboda gaba,
Umar ya sau koh ƙasa ya zauna itama ta zauna a kusa dashi ta bude littafin ta suka fara,
Fatima tana SS two ne going to three ita kuma Amina JSS one
Ismael kuma tare suka zana jarabawa da umar,
Duk da shi zana mai a kayi umar kuma yace yafi son ya zana da kanshi,
Nasser kuma Degree yake ɗaurawa a cikin garin Jos,
Yana karantar fannin lafiya ne sannan ya iya gyaran wayoyi,
Yana zama a shagon abokin shi idan ya dawo makaranta,
Shi kuma umar shagon ɗinki yasa Aliyu ya kai shi yana koyan ɗinkin keke na maza,
Bayan sun gama Assignment din umar ya tashi yace ma Mama bari yaje shagon su ya dawo,
Mama tace yamma yayi magariba a ke shirin kira,
umar yace mata ba zama zaiyi ba yanzu zai dawo
Mama tace mai a dawo lafiya,
Fatima ta kwashe jakanta da kuma form ɗin da suka bari a parlourn ta shiga dasu ciki,
ta zuba su a cikin jakan ta na makaranta ta shiga bayi tayi alwala tadau Qur'an ta fito parlour tazo ta zauna kusa da mama,
A saman darduma irin darduman nanne mai faɗi da taushi,
Mama ta tashi ta shiga ciki Fatima kuma ta fara karatu cike da natsuwa,
Fatima bata da tsawo kamar ƴan uwanta sannan kuma tana da jiki ga diri masha allah,
itama tana da hanci
Daman duk ƴan dakin Mama suna da hanci,
kuma itama mama bata da tsawo kamar dai Fatima,
Amman dukan su suna kama da juna,
Bata jima da fara karatun ba aka kira sallah ta rufe Qur'anin,
ta tashi sai ga Mama ta fito daga bedroom, tazo ta hau darduman suka bi jam'i,
Bayan an idar Fatima ta kwaso littafan ta na addini tazo Mama tana mata bita,
Sun jima a hakan kafin Fatima ta mayar da littafan tazo ta fara azkar,
Bayan ta idar ta ɗauko chasbi ta naja har aka kira sallahr Isha'i,
Bayan sun idar da sallah sukayi nafila sannan Fatima ta tashi taje kitchen,
Tana zuwa ta samu Amina zata shiga ɗauko abincin baffa,
Fatima tana ganin Amina ta bata guri ta huce,
itama ta shiga ta ɗauko abincin su ta koma ɗaki,
tana shiga umar na shigowa shida Nasser,
suka gaida Mama suka zauna Fatima ta koma kitchen ta kwaso plate da spoon takoma,
Bayan ta kai sai ta shiga bedroom tana shiga umar ya mike yana cewa daɗin abun dai muna da hannu,
Mama da take gefe tayi murmushi Nasser kuma yace to acici mala'ikun tauna,
Fatima dake fitowa tayi dariya tace wallahi kuma sunan ya dace dashi,
umar bai tanka musu ba ya bude kular abincin,
shinkafa ne jallop na manja da wake,
ya zuba a plate ya koma ya zauna Fatima na ganin hakan ta bude fridge ta ɗauko zobo da ruwa tazo ta aje musu,
Umar yace kinyi taimako domin bana gane baƙin karatun shiyasa ban tsaya nai man ruwa ba,
Fatima ta kalli Nasser tace in zuba maka abincin,"?
Nasser yace a'a bari bro ya shigo daman tayi tinanin hakan,
indai suna gida basu cika cin abinci ba tare ba,
tazo ta ɗiba ta koma kusa da mama ta zauna ta faraci bayan tayi bismillahi
bata ci da yawa ba ta tashi ta shiga ciki sai gata da roban yaji,
umar na ganin hakan yace daman tin ɗazun nake tinanin inda zan samu yaji,
Dukan su suka mai dariya saboda tinda ya fara cin abinci baiyi magana ba,
Fatima ta ɗiba ta aje Mai roban yajin a gaban shi,
mama tace ma Fatima idan kin gama ki ɗaura mun Lipton,
Fatima tace ai muna dashi a cikin plask,
mama tace to gama ki ɗauko mun,
suna cikin hakan Aliyu yayi sallama ya shigo hannun shi riƙe da baƙar leda,
Yana zuwa ya miƙa ma Fatima
Ya gaida mama ya zauna kusa da Nasser suka gaisa,
umar kam sai da ya gama cin abinci,
Sannan yace sannu da dawowa,
Aliyu yayi murmushi yace an gaishe da acicin gidan mu,
Umar yace kuma banci da yawa ba,
Domin nasan zaka dawo mana da tsaraba,
Fatima da take shigowa ɗakin tace wallahi kaji tsoran allah ya umar duk irin abincin da kaci,"?
Umar ya kalleta yace to inna ruwanki dani,
Nasser yace haba Fatima ya zaki tona mai asiri,
Mama tayi dariya tace karku tasa mun ƴa a gaba,
Fatima ta zauna bayan ta shigo da babban plate ta juye abinda Aliyu ya shigo dashi,
Nama ne mai yawa sai ƙamshi yake tashi,
Mama tace ma Fatima ta diban ma Inna takai mata,
Fatima ta ɗau plate guda ɗaya a cikin wanda ta kwaso domin suci abinci ta ɗibo naman aciki ta fito,
ta shiga ɗakin Inna bakin ta ɗauke da sallama ,
Inna ta amsa sallamar ta ɗauke kai Fatima tace barka da dare Inna gashi inji mama tsaraban ya Aliyu,
Inna tace to aje kice angode Fatima ta fita daga ɗakin,
tana fita Amina ta sauko da sauri tazo ta bude plate ɗin taga nama ne,
aciki Inna tace Mai kike shirin yi,"?
Amina tasa hannu ta faraci tai banza da Inna,
tana cikin cin namar saiga Ismael ya shigo babu sallama baice musu Komai ba,
ya zauna kusa da Amina shima ya fara cin namar,
Ta Batulu ce🥰✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6o
💖💖RAYUWAR MU💖💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by ✍️
SA'ADATU I FULANI
(Ta Batulu🥰)
Page 9-10
Inna ta kalle su tace amman baku da zuciya,
Babu wanda ya kalle ta acikin su,
bayan sun gama cin namar,
Ismael yace Amina ta zuba mai abinci,
Amina ta ɓata fuska,
Inna ta kalli Amina tace bakiji ana magana ba,"?
Amina ta tashi ta fita tana turo baki,
Ismael ya kalli Inna,
yace mata wallahi wata rana sai na karya wannan yarinyar gaba ɗaya ta raina mutane,
Inna tace ma Ismael ka dinga haƙuri dan allah koba ka ganin ita yarinya ne,"?
Inna taci gaba da cewa,
Ismael kaine babba dan allah kaja girmanka,
Amina ta shigo tana tura baki,
ta aje mai abincin gabanshi tashige Bedroom ɗin su,
Shima ɗakin irin na Mama ne komai da komai sai dai ya nayin kayan ɗakin,
wannan ɗakin duk yayi ƙura kamar babu masu rayuwa aciki ,
Domin Inna akwai ƙazanta kuma ta koya ma ƴarta,
Tarbiyya ana koya ne daga uwa ba daga uba ba
Domin na uba da ban naki da ban,
Duk yanda kike yi a gidan mijinki itama ƴarki haka za tayi a gidan nata mijin,
ubangiji ka datar damu, allah ka haɗamu da iyaye na gari,🙏
Inna ta kalli Ismael da yake cin abinci,
tace mai ya maganar makaranta, nifa nagaji da ganinka hakan,
bokon baka mayar da hankali ba islamiyyar ma hakan,
gashi kowa yana zuwa gurin sana'a amman banda kai,
Ismael yace mata nifa bana son wahala ne shiyasa,
kuma ni nagama makaranta sana'a kuma inna tinanin wanda zai dace dani ne,
Inna ki daina damun kanki a kaina,
Yana gama fada mata hakan yayi waje Inna tace zaka dawo ka same ni,
Ɗakin Mama bayan sun gama cin abinci mama ta kalli Aliyu tace karka manta da maganar mu ta ɗazun Aliyu yace mata ban manta ba,
Suka taɓa fira da ƴan uwan shi yana jadadda musu maganar tafiyansu islamiyya babu fashi su zauna cikin shiri,
Yayi musu sallama ya fita yana fita Naseer shima yayi musu sallama ya fita ,
Aliyu ɗaki ya shiga yaje ya ƙara shirya wa ya fita,
Mama tace ma umar ya duba mata ɗakin baffan su idan yana nan,
Umar na fita yaga Inna tana tsaye a bayan windows din ɗakin su,
Tana ganin umar ya ganta sai ta hau borin kunya tana ta zagin shi
, Umar baice mata komai ba ya huce,
Mama tana jinsu tai shiru tana ma Inna fatan shirya,
Umar ya shigo da sallama yace ma Fatima baffa yace ta kai mai Lipton,
mama tace ma Fatima ta kai mai wanda ta zuba mata idan ta dawo sai ta zuba mata wani,
Umar yace bari in zuba miki ita kuma Fatima ta dauki na baffa ta fita,
Fatima tai sallama ɗakin baffa ya amsa yace mata ta shigo,
tana shiga sai ga Inna ta shigo babu ko sallama Fatima tai kamar bata ganta ba,
Fatima ta matsa gaban baffa tace mai barka da dare ta aje kofin ta tashi ta fita,
Inna ta kalli baffa tace mai wannan zalunci ne ba adalci ba, kuma allah yana gani wallahi sai yayi mun sakayya,
baffa bai ce mata komai ba har ta gama maganar ta,
sai ma tashi da yayi ya shiga daga ciki hannun shi ɗauke da kofin da fatima ta kawo,
Inna tayi kwafa tace wallahi zaka dawo ka same ni,
Fatima tashiga ɗakin su bakinta ɗauke da sallama ta samu umar suna fira da Mama,
itama ta zauna suka cigaba da firan da ita,
tara da rabi baffa ya shigo ya zauna suka ɗan taɓa fira kafin yayi musu sai da safe,
Yana fita umar yayi musu sallama ya tafi ɗakin su,
Mama tayi alwala ta hau darduma Fatima tayi alwala ta kwanta,
Agurguje anyi auran Amina da Aliyu baffa ya basu gidan zama amman ba unguwa ɗaya suke ba,
Umar ya tafi jami'a Fatima juma ansa mata rana da saurayin da baffa ya zaɓan mata,
Duk da Aliyu baya gidan suna zuwa islamiyyar da ya sa su,
ita, kuma Amina rashin kunya ya ƙaru tinda mai tsawatar wan yabar gidan,
Ismael kuma baffa ya kaishi garin zaria karatu bayan ansha fama da Inna,
Yanzu gidan daga Fatima sai Amina sai Nasser sannan umar,
Fatima tayi candy baffa yace idan taje ɗakin mijinta taci gaba a can yanzu Amina ka ɗai ke zuwa boko itama ba kullum ba,
Gidan Aliyu zama suke cike da Farin ciki da jin daɗi Amina tana girmama shi,
suna son junansu sosai, gashi allah ya fara dafa mai,
mai gidan shi ya bashi shago ya zuba mai kaya,
yace ya mayar mai da kuɗin kayan,
ya riƙe ribar shima ya kula da kanshi tinda yanzu ya aje iyali,
Bayan shekara uku anyi auren Nasser da budurwan Shi maryam har ma ta nada ƙaramin ciki,
Nasser ya gama makaranta ya kama sana'ar saida wayoyi a shagon da Aliyu ya buɗe mai,
Shima baffa ya bashi gida kusa da Aliyu daman gidan ya siyane domin su zauna aciki
Idan sun tashi aure,
Fatima tayi aure da mijinta Abubakar yana saida motoci suna zaman lafiya da mijinta,
Domin Fatima halin mahaifiyarta ne da ita,
Abubakar yana sonta sosai kuma yana kulawa da ita yanda ya dace,
Umar yana cigaba da karatu Ismael kuma yana Zaria,
Mama ta ɗauko Yar kanwarta mai suna Rabi'a tana taya ta zama,
Amina kuma anata tara samari a kofar gida tin baffa na fada,
Inna tana kareta ya gaji ya sama ta ido,
Acewar Inna gwanda ta zaɓa ta darje ta samo wanda yafi na Fatima kuɗi,
Gidan Aliyu suna rayuwa cike da farin ciki ƴar su ɗaya mai sunan mama suna cemata Shukrah,
Yarinya mai kama da babanta sakk,
Duk da itama uwan ba baya ba gurin kyau,
Amman idan kaga shukrah kana ganinta kasan waye Aliyu ne babanta,
Shekarun shukrah 2 a duniya Fatima tana son shukrah sosai, haka shima baffa yana sonta,
itace jika na farko a gurin baffa kuma ta fito daga gurin ɗa mafi soyuwa a zuciyar shi,
Ta Batulu 🥰 ce✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT
💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by ✍️
Sa'adatu I Fulani
(Ta Batulu🥰)
Page 11-12
Bayan wani lokaci abubuwa da yawa sun faru,
Dawowar Ismael gida auren Amina umar ya kammala karatu ya samu aikin banki,
Fatima ta haihu na miji sunansa Aliyu suna kiransa da Sajjad,
matan Nasser ma ta haihu na mace sunan yarinyar Khadija,
Yaran Aliyu biyu bayan shukrah sun ƙara samun Sa'adatu suna ce mata Darraini,
Tsufa ya ƙara kama baffa sosai domin yanzu yaran suke riƙe da gidan,
Amina tayi aure bayan ta gama ruwan ido ta zaɓo wani mai suna sager,
suna zaune a cikin garin Jos yana sana'ar sai da takalma,
Shima Naseer kudi sun fara zama,
Matan Aliyu da matan Nasser kan su a haɗe yake,
Duk da ka san cewar ba gida ɗaya suke zaune ba,
Amman suna zaman lafiya babu mai jin ƙan su,
Aliyu ya gina gidan shi mai kyau sun tare plat biyu,
Sai nasa plat ɗin daban, kowani plat two bedroom ne kowanne da toilet a ciki sai kitchen a parlourn,
Gidan yasha tayis ga famfo harda gate,
Yanzu haka shagunan Aliyu biyu ɗaya a garin su ɗayan kuma a Jos,
Yana ta tinanin ya ɗaura Ismael a shago ɗaya tinda duk cikin su kowa yana da abin yi amman banda shi,
Saboda shi yaƙi karatu ko yanzu da ya dawo gida babu abinda yake yi face zaman majalissa,
Aliyu ya tara ƴan uwan shi ya fada musu abinda ke cikin zuciyar shi game da Ismael,
Naseer ya ce shi a nashi shawaran ya fara jaraba shi ya bashi jari ko treda ya buɗe mai ya ga kamun kan shi kar yaje ya ɗaura shi a kan dukiyar shi a samu matsala,"
Shima umar haka ya ce,"
Aliyu ya ce musu zai je gida anjima gurin baffa,
Daga haka ya sallame su kowa ya kama gabansa,
Da daddare Aliyu ya shirya tsaff zai je gida sai Amina tace mai,
ita ma zata je domin ta kwana biyu bata je ta gaida baffa ba,
Aliyu yace mata tai sauri ta shirya yana jiranta,"
Amina tace to bata jima sosai ba ta fito hannunta riƙe da Darraini ɗayan kuma leda ne mai ɗan girma tana tafe shukrah ƴar shekara 8 na binta a baya,
Tsakanin Shukrah da kuma Darraini shekara 4
Aliyu ya ɗau shukrah ya fita ya ce ta same shi a waje,
Daman lokacin auren Amina ya sai mashin,"
Amina tana fitowa ta hau mashin ɗin shukrah na gaban mashin Darraini na tsakiyya suka tafi,
Bayan sun isa gida ya aje mashin ɗin ya riƙe shukrah suka shiga cikin gidan bakin su ɗauke da sallama,
babu kowa a tsakar gidan sai Ismael shima yana ganin su ya fara zare ido kana ganin shi kaga mara gaskiya,
Aliyu yayi kamar bai ganshi ba shukrah ta ƙwace hannunta ta shige ɗakin baffa tana kiran sunan shi,
Amina kuma ta nufi ɗakin mama hannunta riƙe da Darraini,"
Aliyu ya kalli Ismael yace mai ka keyi a nan,"?
Ismael yayi ƙasa da kai yace mai babu komai,"
Aliyu ya kalle shi yace mai kaji rani ina neman ka tinda kai baka zumunci da kowa,"
Ismael yace to
Aliyu ya huce ɗakin baffa yayi sallama ya shiga ya samu shukrah ta haye mai jiki tana ta surutu,
Aliyu yana mamakin yanda shukrah take sakewa da baffa take mai surutu,
Shukrah bata da yawan magana duk da ka san cewar Aliyu muskili ne,
Amman shukrah tafi shi,
domin ita ko magana kayi mata idan bai mata ba ko kallon ka baza tayi ba,
Amman idan kaji zancen ta tazo gurin baffa ne idan kaji dariyar ta mai yawa tana tare da baffa ne,
Aliyu ya kalli baffa yana zaune yana jan charbi duk ya tsufa domin wani lokacin ko fita ba yayi,"
Aliyu ya gaishe shi ya mai ya jiki baffa yace jiki Alhamdulellahi,"
Aliya yace ma baffa daman wata magana ne ke tafe dani baffa ya gyara zama yace Inajin ka,"
Aliyu ya faɗa mai shawaran da suka yanke da ƴan uwan shi,"
baffa yayi farin ciki sosai yayi murna daman abin yana damun baffa zaman shi hakan babu sana'a tinda shi yaƙi yin karatun gaba ɗaya,
Sauƙin ta ɗaya ma daya kai shi zaria babu laifi yayi karatun domin har sauka yayi,"
Baffa yasa musu albarka dukan su sannan ya ƙara mai da nasiha kamar yanda ya saba,"
Baffa yana yawan gaya ma Aliyu yaji tsoran allah ya kula da hakkin iyalin shi karya zalunce su,
domin suɗin amana ne a gurin shi kuma za a tambaye shi yanda ya tafiyar da wannan amanar da aka bashi,"
Aliyu yayi ƙasa da kai yace in sha allah zan kiyaye na gode baffa allah yaƙara nisan kwana,
baffa ya ce mai yaje ya gaisa da mutanan gidan yazo su tafi gida kar dare yayi musu a hanya,
Aliyu ya fita daga ɗakin baffa jiki a sanyaye"
Saboda har yanxu ya kasa saba wa da wannan nasihar na baffa,
Gani yake kamar wasiyya yake barin mai,
Aliyu ɗakin Inna ya shiga bayan yayi sallama an amsa ya shiga ya zauna a