Author : SA'ADATU I FULANI Category : KDP NOVELS
RAYUWAR MU
🔺🔻🔺🔻🔺🔻
🔻🔺🔻🔺🔻
🔻🔺🔻
🔻🔺
🔺
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
*(J.W.A)*
_Wannan shine Whatsapp group ɗin da zaku samu cigaban wannan labarin. Ku taya ni shering Please👇._
https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT
Written by ✍️
SA'ADATU I FULANI
(Ta Batulu)
(Tafiyar ƙaddara kamar tafiyar ajali take, duk inda ka kai gurin guje mata sai ta risƙe ka. Komai na duniya yana da lokaci Kuma yana da iyaka, Rabbi ka yi daɗin salati ga shugaban kowa da komai, manzon tsira manzon Rahama Annabi Muhammad s a w.)
*Bismillahir Rahamanir Rahim.*
*Page 1-2*
Wata matashiyar budurwa ce tafe sanye da uniform ɗin makaranta blue black sai farin hijjabi wanda ya wuce guiwa,
kana gani ka san na islamiyya ne, ba za ta wuce shekara goma sha takwas ba duk da uniform ɗin sun koɗe amman babu datti ko kaɗan ajikinshi,
tana tafe tana yamutsa fuska,
da dukkanin alamu akwai gajiya a jikinta,
a bakin wani ƙaramin gida mai dakali guda biyu naga ta tsaya
tayi kusan minti tara a zaune akan ɗaya daga cikin da kalin kafin ta shiga gidan bakin ta ɗauke da sallama.
Wata mata ne zaune a kan kujera a ƙofar wani ɗaki
daga gani ɗakinta ne ta amsa sallamar tana cewa.
Shukrah har andawo?" wannan matashiyar da aka kira da shukrah sai ta ce
"Eh na dawo Umma sannu da gida"
Shukrah sai ta tsaya tana ƙarema ummanta kallo aƙalla za tai 39 years Amman ya na yin rayuwa yasa ta zama Kamar mai shekara 40 da wani abu,
Ɗakuna uku ne a gidan sai ban ɗaki a ƙarshen gidan,
kana shigowa akwai ɗakin farko nanne ɗakin babansu shukrah,
Daga ɓarayin dama Kuma nanne ɗakin umman shukrah
sai ta ɓangaren hagu shima ɗaki ne na amaryan ummansu shukrah ,
sai kitchen kusa da ɗakin babansu shukrah,
Umma tana ta magana shukrah ba taji taba, umma ta tashi ta kamo shukrah ta ce.
" ki rage ma kanki wannan tinanin bai da amfani." Shukrah ba ta ce komai ba ta shiga ɗakinsu two bedroom ne
Parlourn yana da faɗi ba laifi Amman kujeru biyu ne kawai a parlourn mai zaman mutum biyu,
sai mai zaman mutum uku masu ruwan toka
duk yaji jiki Amman tsaff suke Babu datti, sai cafet Shima mai ruwan toka da ratsin baƙi, Duk ya koɗe Amman babu Datti ajikinshi.
Akan kujera shukrah ta zauna tajin gina bayanta ta rufe idanun ta kamar tana bacci,
ba ta jima ba taji hayaniya na tashi a waje ta tashi ta shiga ɗaya daga cikin bedroom ɗin tana buga tsaki.
Tana shiga sai ga wasu matasan ƴan mata sun shigo da sallama mata ne su biyu sai namiji ɗaya,
sukai ma Umma sannu da gida Umma ta amsa tana cewa har kun dawo,
suka amsa da eh. "Umma mun je bata nan sai da muka jira ta."
Umma ta kali ƙaramin yaron ta ce.
"Mudan na ga kayi shiru hala sun gajiyar mun da kai?"
sai mudan ya rausayar dakai ya ce "Ehh wallahi umma Aunty Darraini sai jana ta keyi acikin ƴan matan da suka shigo wacce tafi girma acikin su,
ta taso tana cewa "Sai ta dake shi tinda sharri zai mata.
Umma ta tare ta tana faɗin ba zata dukar mata autan ta ba ai gaskiya ya faɗa,
mudan ya kalli Darraini yayi mata gwalo Darraini tai ƙwafa ba ta ce komai ba.
Umma ta kalli ɗayar yarinyar da tinda suka shigo ba ta ce komai ba ta ce mata.
"Manaheer lafiya ki kai shiru ba kice komai ba,
Wanda aka kira da manaheer sai ta zumɓuro baki tace .
"Ni da nake jin yunwa Inna naga bakin surutu.
Umma ta kau da kanta daga kallonta ta kalli Auta tace Mai autan maman shi ka najin yunwa sai mudan yace eh mana ummana"
Ni fa jina ke kamar banda hanji yana mudan yana faɗin hakan du kansu.
Suka kwashe mai da dariya Darraini Ta kalli Umma tace mata.
"Umma har yanzu Yaya bata dawo daga islamiyar ba,? "
Umma ta ce ta dawo tana ɗaki."
suna jin hakan Suma suka shiga ciki bakinsu ɗauke da sallama .
Basu ganta a parlour ba sai suka shiga ɗaya daga cikin bedroom ɗin,
suna shiga suka ganta ta kwanta rigingine fuskanta na kallon rufin ɗaki,
idonta biyu Manaheer tana ta magana amman shiru,
da alama tayi nisa
Domin tinda suka shigo bata motsa ba,
Ganin hakan sai Darraini taje ta taɓa ta tana taɓa ta taja ajiyan zuciya,
Duk sai suka hau kallon ta Shukrah ta kalli ƙanin nata guda biyu ta kau da kanta,
Ganin ba tace musu komai ba sai suka sata a tsakiya suka kewayeta,
ganin hakan sai shukrah ta tashi ta zauna tana
ƙarema musu kallo,
ba tace musu komai ba Sun san in zasu kwana a hakan shukrah ba za tace musu komai ba
" Darraini tace "Aunty Shukrah mai ke damunki ko baki da lafiya ne"?
Manaheer tai shiru tasa musu ido tana jiran taji abinda shukrah zatace,
duk da ta san abune Mai wahala ta faɗa musu damuwarta.
Babu zato taji muryar shukrah na faɗin yanzu haka zamu cigaba da Rayuwa kullum jiya iyau"?
Babu Wani cigaba a rayuwar mu,
Dukansu sun gane mai ta ke nufi Sai suka kasa bata amsa,
ta kalli manaheer tace
"tinda muka taso muke shan wahalar rayuwa har yanxu bamu san wani Abu wai Shi farin ciki ba,
ku duba ku gani yanda Umma take wahala akan mu kullum burinta yaya za ayi mu koma school amman hakan bai samu ba,
Itace cin mu da Shan mu itace sutturan mu itace maganin mu,
Komai itace Kuma kuna ganin babu wani,
Sana'ar da ta keyi kullum faɗi ta shi ta keyi akan mu,
tana gama faɗin hakan Kuka yaci ƙarfinta,
suka haɗe kawunan su suna ta kuka sunyi 20 minutes suna kuka,
Kawai ji su kayi an dafa su suna ɗagowa suka ga Umma tsaye a kansu tana ƙare musu kallo tace.
Nai ta magana a fito ai sallah na ji shiru sai na shigo inga mai ya hana ku jin kiran sallah,"
Ashe kuna nan kuna aikin da kuka saba yi"
Umma tace
" Da ace kuka na maganin damuwa da tini ba ku da sauran damuwa a duniya,
Ku tashi kuje ku fuskanci ubangiji shiɗin maji roƙon bawa ne,
Kuma duk duniya Shi kaɗai zai yaye muku damuwarku"
tana gama faɗa musu hakan ta fita ta basu guri
ita kanta ƙarfin hali tayi ta rike kanta amman tin da suka fara magana take tsaye a kansu tazo tai musu magana akan suzo suyi sallah sai taji suna wannan firan,
Ita kanta haƙuri take da mahaifinsu tana da gatan ta da komai amman ta zaɓi zama dashi ko dan ƴaƴanta,
Basu motsa ba har sai da auta ya shigo yace musu Umma tace suje,
sannan suka tashi kowannen su jiki a san yaye suka fita parlour,
suka
same ta a saman darduma tana jan casbih,
Da ido kawai ta kalle su kowa yayi waje ya ɗau buta Shukrah ta shiga bayi ta fito bayan ta fito sai Darraini ta shiga tana fitowa,
Sai Manaheer ta tashi zata shiga har ta kai ƙofar bayin taji an bangajeta,
sai da ta faɗi aka rufe ƙofar bayin da ƙarfi sai da manaheer tai saurin janye ƙafarta"
Darraini na ganin hakan tai sauri taje ta faɗawa umma domin ta san halin manaheer bata yafiya Idan ka ta ɓata,
tana zuwa taga umman na Sallah sai ta tsaya tana jiran ta idar da sallah,
Ita kuma Shukrah taje ta ɗaga manaheer tace mata lallai Idan ki ka ƙyale wannan yarinyar keba jinin umman mu bane,
tana gama faɗa mata hakan ta tashi ta shiga ɗaki tana leƙen Umma taga Mai ta keyi'
tana leƙawa taga umman sallah take Darraini na gefen ta a zaune tai hamdala,
Ta koma tsakar gida ta sa kujera ta zauna tana kallon manaheer da ta kasa magana kawai toilet ɗinsu take kallo idanunta sunyi jajir kamar wanda aka zuba ma yaji,
Ita dai shukrah tana ta kallon manaheer domin ta san idan ta kama na cikin bayin nan sai Allah,
manaheer duk ta fisu jiki Kuma tafi su cika,
ƙaran buɗe toilet ɗinne ya mayar da shukrah cikin tinanin da tafara.
Allah allah take ta fito daga bayin taga abinda zai faru,
Shukrah bata gama tinanin da take ba taji wani gigitaccen ƙara sai da gidan ya amsa tana kallon manaheer taga abinda tayi sai da ta zaro ido,
Mimah ne a kwance a ƙasa manaheer nata du kan ta Shukrah ta ce.
"Yauwa sister baki daki bakin rashin kunyar ba,
ai manaheer najin hakan kamar an ƙara mata ƙarfi,
ta dinga jibgan Mimah Umma jin ihun yayi yawa ne yasa ta fitowa jiki na rawa,
Darraini da gyangyaɗi ya fara kama ta itama tayi waje da gudu,
Ganin a binda ke faruwa suke kamar a film duk da sun san manaheer ba tada haƙuri amman basu taɓa tinanin zatai ma Mimah wannan dukan ba,
ganin Umma ta fito yasa shukrah ɗaga murya tace sister bugun ƙarshe ga Umma nan,
Ai ko manaheer na jin hakan ta saɓi Mimah zata buga da ƙasa Umma ta buga mata tsawa tace mata kull kika aikata,
Manaheer ta saki Mimah ta faɗi a ƙasa kamar kayan wanki ta saki wani marayan kuka,
Umma ta wai ga ta kalli shukrah ganin Hakan sai shukrah tayi huff ta faɗa ɗaki,
Umma tace ma manaheer tazo ta huce,
sai Darraini tace ai ba tai alwalan ba,
Umma ta kaɗa kai tace yi alwalan mu huce ɗaki,
manaheer ta tsallake Mimah dake yashe a ƙasa tana ta gunjin juka ta shige bayin"
ta bugo ƙofa saura kaɗan ta bige ƙafar Mimah,
Umma taje ta kama Mimah ta miƙar da ita tana kakkaɓe mata ka yanta da yasha ƙura ta ce mata
"kiya haƙuri Mimah Dan allah Mimah ba tace Mata komai ba ta fisge jikinta ta shige ɗakin su,
Darraini ta Hau Dariya ta ɗaga murya tace amman fa Mimah sai kin gasa bakin ki da ruwan ɗumi.
Umma ta waigo ta kalli Darraini ganin kallon da Umma take mata yasa tai huff ta faɗa ɗaki tana ƙunshe dariya,
Tana Shiga ta samu Shukrah a saman darduma ta idar da sallah tana jan casbih,
Darraini ta kalli Shukrah ta kwashe da Dariya " tace mata sister a nata lazimi ne,
Shukrah ba tace mata komai ba taci gaba da jan casbih,
Suna cikin hakan sai ga Umma tashigo ita da manaheer Umma na gaba manaheer na baya,
Ganin Umma ta shigo yasa Darraini tayi shiru
manaheer ta ɗauki hijjab ɗin Umma taje gefen Shukrah ta tayar da sallah,
Darraini na ganin hakan ta tashi da sauri ta fita taje ta ɗau buta ta sake Sabon alwala,
Ta shiga ɗaki ta samu Umma zaune akan kujera
Darraini na ganin Umma ta duƙar da kanta Umma tai kamar bata ganta ba,
Darraini ta matsa kusa da Shukrah tace sister ɗan matsamun inyi Sallah,
Shukrah ta ɗago ta watsama Darraini harara sannan ta tashi ta koma kusa da Umma ta zauna a ƙasa,
Umma ta kalli manaheer data idar da sallah tace mata zoki zauna manaheer tazo ta zauna kusa da Shukrah,
Umma tai shiru ba tace komai ba sai ga Auta ya shigo da sallama a bakin shi Umma ta amsa ya shigo yazo ya kwanta a jikin manaheer"
Umma ta kalli auta tace daga inna kake Domin na san ba daga masallaci kake ba,"?
Sai auta yace bayan an idar da sallah ne,
naga banga bashir ba shine naje gidan su naga ko lafiya sai na ganshi bai da lafiya,
Umma najin hakan tai shiru ta maida dubanta gun Darraini,
Tana lura da ita ta san ta idar da sallah
Amman taƙi sallame wa Umma tai gyaran murya,
sai duk suka ɗago suka kalleta
Umma ta kalli Darraini tace mata baki idar da sallahr bane"?
sai Darraini itama tazo ta zauna a cikin su,
Umma ta kalli Shukrah tace ta kan ki zan fara saboda kece babba,
Umma tace yanzu ya dace a binda ki kayi du kan su suka duƙar da kai ƙasa,
Umma tace nayi tinanin ke mai tsawatarwa ne a gare su ba mai sawa suyi ba,
Idan kinga suna yin a binda bai dace ba sai kitsawatar musu a matsayin ki na babba
Amman abun ta kaici kece mai sawa suyi wallahi shukrah akan Hakan zan saɓa miki bazaki barni da abin surutu ba"
Yanzu a kan a binda kuka aikata kin san a binda zaije ya dawo,
Kuma kun san a kaina komai yake ƙarewa.
Maiyasa idan za kuyi abu bakwa tsayawa kuyi tinanin abinda zaije ya dawo?
,
Manaheer ne tai ƙarfin halin cewa kiya haƙuri Umma in sha allah baza mu ƙara ba,
Darraini ma tace Dan allah kiya haƙuri.
Auta ma yace Umma sun ce kiya haƙuri ba zasu ƙara ba,
Sai a lokacin Shukrah ta ɗago ta kalli Umma tace Dan allah ki yafe mana ɓata Miki ran da mukayi,
a nan Umma ta nuna ma kowa kuskurenshi Kuma sunyi mata alƙawarin ba zasu ƙaraba,
Darraini ta kalli Umma tace nifa cikina yana ciwo shukrah ta watsama Darraini harara.
Umma tace kije saman gado ta gefen matashina za kiga ɗari biyar ki ɗauko kije kisiyo garin kwaki da sugar,
Darraini taje ta ɗau ko tazo za ta fita Auta yace zai bita,
Suka fita tare suna fita Shukrah ta tashi taje ta ɗauko bokiti taɗiba ruwa ta shiga bayi tana fitowa,
taje wardrobe ɗin kayan su Wardrobe ne Mai ƙofa huɗu ta buɗe na farko ta ɗauko doguwar riga na yadi tasa,
tafito parlour tazo tanzauna kusa da Umma Manaheer ma taje ta watsa ruwan ta sanja kaya,
Umma na zaune da casbih a hannunta ta naja auta ne ya shigo bakinshi ɗauke da sallama,
Yazo ya zauna kusa da Umma
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT
🔺🔻RAYUWAR MU🔻🔺
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Written by
SA'ADATU IBRAHIM FULANI
(Ta Batulu)
Page 3-4
Can sai ga Darraini tayi sallama ta shigo hannunta riƙe da baƙar leda, tana zuwa ta aje
ta fita sai gata da kwano mai ɗan faɗi,
tazo ta juye wannan garin a ciki ta fita taje ta zuba ruwa a ciki,
Ta ɗauraye ta sake wani Ruwan sannan ta shigo ta zo ta saka sugar,
ta fita ta kwaso spoon ta shigo ta zo ta sa a cikin kwanon,
duk a binda take Umma na zaune tana kallonta,
Auta ya sauko ya zauna a ƙasa Manaheer ta zauna kusa dashi,
Darraini ta zauna kusa da Auta su kai Bismillah suka fara sha,
Shukrah na hakimce a gefe tana kallon su,
Umma ta kalli Shukrah tace "Hala kin ƙoshi ne.?"
Shukrah ta turo baki tace "Ni ba naci." Umma tace "Mai kikaci.?" shukrah tai shiru Umma tace "kitashi
ko kuma yanzu ranki ya ɓacci."
Shukrah ta tashi tana turo baki taje kusa da Darraini ta zauna,
taɗau spoon dama sauran ɗaya ne,
Ta ɗiba ta kai baki tana ya mutsa Fuska ta mayar da spoon ta aje,
Manaheer ta tashi taje ta kuskure baki tazo ta zauna kusa da Umma,
sai Darraini ma ta tashi taje ta zauna kusa da Manaheer,
Shukrah ta tashi ta ɗau buta tai waje,
Umma tai ƙwafa ta dawo da kallon ta kan Auta,
Tace "Auta meke damun Bashir ɗin naji kace bai da lafiya.?"
kafin Auta yaba Umma amsa sukaji hayaniya na tashi,
a tsakar gida Umma tace "Allah ya ta ƙaita wannan abun."
Manaheer zata fita Umma ta hana tace su jirata taje taji,
Umma ta fita Auta yabi bayanta,
Amaryan ABBA ne mai suna Aisha ta keta masifa.
tana zagin shukrah da ta ke zaune a tsakar gidan,
tana ganin Umma ta fito tace "Yauwa ga babban munafukar nan tafito.
Ta nufo Umma tana cewa "Mene yarinya na ta muku za kuyi mata taron Dangi,
ku dake ta.?"
Umma ba tace komai ba tai shiru tana kallon Aisha tana jiran taga mai take Shirin yi,
tana zuwa gaban Umma taja ta tsaya ta gama zagin Umma tass,
Sannan ta shiga ɗaki tana cewa kujira mai gidan ya dawo wallahi sai ya yi mana iyaka daku."
Umma ta sauke kai ƙasa tana ajiyar zuciya,
Shukrah da tinda a ka fara bata iya ɗago da kai ba,
itace tazo ta kama Umma ta shiga da ita ɗaki,
tana zuwa ta zaunar da ita saman kujera ta zauna kusa da ita,
Ta kwantar da kan ta a jikin Umma ta fashe da Kuka,
ganin Shukrah na kuka yasa sauran suka matso kusa da Umma, suka dafa shukrah su kace "kiya haƙuri sister komai zai huce
Manaheer tace dan allah ki daina kuka, domin kukan ki raunine a garemu,
Muma munajin abinda ki keji a ranki."
Umma tasa hannu tana shafa kan shukrah tana cewa, "Babu Wani dauwamammen Abu a duniya.
Kuma Duk abinda ku kaga yayi farko to yana da ƙarshe." Auta yazo ya zauna ajikin Umma Shima yasa kuka,
Umma ta kalli Auta tace "Kaifa Jarumina ne ko ba kasan jarumi baya kuka ba.?" Sai Auta ya ce "To ai Umma kaɗan zanyi."
Suna jin hakan dukan su suka hau Dariya Shima autan Dariya ya yi,
Umma tace suzo suje su dubo Bashir da jiki,
Auta ya nata murna ya na tsalle Manaheer tasa hannu ta ran kwashe shi Akai,
Auta ya ɓata Fuska zaiyi kuka Umma ta ce "rabu da ita kaji haushi takeji kafita kyau."
Suka shirya su uku banda Shukrah da take jin gine, Da jikin Umma ita Ko motsi ba tayi