Author : Sumayya Abdulkadir Category : Taskar Novels
iznin tafiya karatun digiri na biyu, ga
Alhaji Sadi na maganar aure nan kurkusa, so yake in bashi izni ya fara zuwa ganin ta na rasa ta
inda zan bullo mata.
Mukhtar kamar yayi dariya ya dai gintse ya ce Alhaji Amani yar ka ce, me yasa kake shayin
ta? Hakan bai dace ba ko kadan Alhaji yace rikicin ta nake tsoro, baka san ta bane, wanizubin
kamar sarka take fadi ki rikice ta fannin rikici, sau da dama in ta rikice min kamar mahaifiyar ta
take komawa, bana sanin ta ina zan shawo kan ta. Mukhtar na so ya ce ita siyasar dole ce da
zaa saida farin cikin ya domin ta? A fili kuma yace Alhaji kamata yayi ka kirawo ta ka zaunar da
ita ka gaya mata hujjojin ka kamar yadda ka gaya mini, na tabbata bayan rikicin, zata zo ta
fahimta tunda dai kana son takarar nan, in ya so daga baya in ta gama rikicin zata yi biyayya,
zan taya ka tausar ta.
Da wannan shawarar ta Mukhtar ya dogara, washegari ya kira Amani, ya kawo takardar
sabuwar mota da mukullin ta ya bata, ya ce Tafisu na ji kina korafin injin motar ki yana kara,
nace bari kawai a sake wata, kafin ki zama Amarya. Amani ta karbe mukulli da murna tace My
Daddy like no other, godiya nake, kamar ka san na dade ina son Lamborghini, Allah ya bar mini
kai Baba na yace ai yau kyautar ba daga ni ta fito ba, daga Alhaji Sadi ne, ai kin san shi ko?
Wannan abokin nawa da yazo satin da ya wuce?
Amani ta ce ni kuwa na san shi, wannan mai katon cikin kamar kwaryar kindirmo, da idanu
kamar na soyayyar gyada, yana kallon mutane tamkar mage ta ga bera. Alhaji ya kama baki
yace Amani ban san ki da cin zarafin na gaba ba, shi da ya gan ki ya yaba da ke ya nemi auren
ki cikin girma da daraja a hannu na da alkawarin zai tsaya min sai inda karfin sa ya kare in
samu takara. Idan na samu kujerar ai ke zaki fi kowa morewa da jin dadi.
Amani tayi sakale! Tana kallon bakin Alhaji tana cewa a ranta ko Daddy ya fara shaye-shaye
ne? A fili tace Daddy ban gane komai cikin maganar ka ba, wace Amanin? Ni? Kuma takarar
me ka ke magana? Alhaji ya sassauta murya cikin lallashi ya shiga yi mata bayanin yarjejeniyar
su yadda zata fahimta. Sai Amani ta sunkuya ta rike ciki ta daddage ta hau zuba dariya tana
cewa,
Daddy! Dariya ta ci karfin ta in ta tuno kamannin Alhaji Sadi, har ya fi Daddyn ta muni da
tsufa, da kyar ta tsahirta dariyar ta ce wato Daddy kawai kace ka sayarwa da abokin ka yar ka
Amani bisa yarjejeniyar siyasa, to wallahi ko shugaban kasa zai tsaya maka ka samu bazan
aure shi ba.
Ai ba mijin aure na rasa a duniya ba, da sani na nake korar su, don lokacin aure na bai yi ba.
Duk duniya ban ga mijin da zan iya so ba Daddy, mai yiwuwa ma baa haife shi ba, saboda ba
kowa zan iya aure ba sai wanda zuciya ta take matukar so.
Alhaji ya ce Amani kada ki yi min rashin kunya, tsakani na da Alhaji Sadi amana ce. abota ce
ta kwarai, yafi karfin ya nemi alfarmar auren ki in hana shi.
Amani da yake kunyar ta ragagga ce sai cewa tayi Daddy ka rage son duniya, na rantse da
Allah ba don abota ka amshi wannan maganar ba sai don son Mulki, ka manta cewa (power is
transient), ammma farin cikin yar ka guda daya (has to be eternal), ban san me kake nema
kuma a duniya ba, da zaka mayar da ni hajar siyasar ka. Ta soma kukan ta na halitta na shagwaba kamar marainiyar da aka fadawa mutuwar iyayen
ta, na yau har da sheshshekar kukan gaske. Kukan da ya fi komai dagawa Alhaji hankali. Cikin
kukan ta ce wallahi Daddy bana so, bazan aura ba, ta yaya recently na gaya maka na samu
admission ina so ka yi min izni in wuce Masters dina zaka kawo wannan maganar? Alhaji ya soma fusata yace to in ke kika haifi kan ki sai ki tafi Masters din mu gani, magana
na gama, na baiwa Alhaji Sadi auren ki, don kin ga ina sakar miki da yawa shi yasa kika raina
ni, karatu kin gama shi daga kwalin digiri ba kari, dama ana ta cewa na barki babu aure. Amani
ta mike tana cewa to Daddy sai ka zaba ko ni ko abokin ka, idan aka takura min kan maganar
nan na rantse zan sha poison in mutu ka huta, da dai in auri wannan mummunan tsohon.
Gaban Alhaji ne yayi mummunar faduwa, exactly irin kalaman da mahaifiyar ta Jalan ta
furtawa nata mahaifin a gaban sa, ranar da ya bashi auren ta. Kuma tabbas ta sha poison din
bayan haihuwar Amani, bashi da tabbacin tana raye ko ta mutu, don tun ranar da ya kai ta
asibiti ya damka wa mahaifin ta takardar sakin ta, bayan ya dauke jaririyar yar sa, bai kara
waiwayar ta ba, a dalilin ta dade tana kunsa masa bakin ciki mai yawa saboda kawai ita
kyakkyawa ce shi ba kyakkyawa ba.
Allah wadaran masu aure don kyau, Alhaji ya fada a fili cikin tuno dararen da suka shude
tsakanin sa da Jal'an. Allah yasa kada Amani ta yo halin mahaifiyar ta tarihi ya maimaita kansa
tsakanin ta da Alhaji Sadi Talle, don shi aure da Alhaji Sadi ya riga ya gama zartar da hukuncin
yin sa ba zai fasa ba. Amani ta wuce zuwa sama ba tare da ta san halin tunanin data jefa mahaifin ta a ciki ba.
Ya dade a zaune a wajen yana tunanin mafita ko ta inda zai bullo mata ta yarda da auren
Alhaji Sadi, ba abinda yake hangowa kansa sai gashi a kan kujerar gwamna, ya tuna Mukhy ma
yace zai taya shi lallashin ta, da wannan tunanin ya shiga bayan gida toilet na dakin sa domin
ya yi wanka ya kwanta, yana sanya kafa cikin kwamin wankan ya zame ya fadi a ciki, wata irin
muguwar faduwa da ta yi sanadin kai Alhaji Usman asibiti cikin daren, Allah ne ya kawo Haj.
Rabi dakin taji karar da ya saki, ta fado bandakin tana salati.
Maigadi da mai ban ruwan shukoki ta kira suka kinkimi Alhaji suka sa a mota, Malam
Tajuddeen ya tuka motar suka yi asibiti da shi. Sai da suka isa asibitin Malam Tajuddeen ya kira
Mukhtar.
A gigice Mukhtar ya zo asibitin, shi yasa hannu ya biya komai likitoci suka soma baiwa Alhaji
taimakon gaggawa.
Zuwa safe babban likitan da ke duba Alhajin ya tabbatar ma Mukhtar Alhaji ya samu stroke
wato rabin jikin sa ya daina aiki. Kasancewar dama yana da hawan jini da suga masu tsanani.
Mukhtar ya saka fuskar sa cikin tafukan sa ya na ambaton innalillahi wainna ilaihi rajioun.
Tabbas dan Adam ba a bakin komai yake ba. Jiya jiyan nan suna tare da Alhaji lafiyar Allah
yana kasafta yadda zasu ci duniya da tsinke da kudin talakawa idan ya zama gwamna yau a ce
rabin jikin sa ya mutu? Amani tana gida bata san abinda ke faruwa ba, tun dare take waya da Hamidah tana kuka
tana gaya mata Daddy ya daina son ta, zai aurar da ita auren dole ga tsoho, kuma saan sa
saboda siyasa. Tace Hamida na tabbata ba zugar kowa bane wannan aikin annamimi Mukhtar
ne, don ni Daddy bai taba yi min zancen aure ba, na tabbata shi ya zuga shi tunda yanzu baya
jin maganar kowa sai tasa, kuma na tsole masa ido a gidan yana so a kawar da ni ya ji dadin
cuta ma uba na. Ta fyace hanci ta ce Hamdy na shiga damuwa don ban ga alamar Daddy da
wasa yake maganar nan ba, kamar auren da yake son yi min din is based on political aspiration
din sa.
Hamidah yarinya mai hankali tace "wato Bestie ba zaki daina tsanar bawan Allan nan ba
babu gaira babu dalili? Zato zunubi ne, how sure are you shi ya zuga Daddy? Ke da kan ki kin
ce is based on his political aspirations sai ki cire Mukhtar a ciki tunda shi ba dan siyasa bane.
Ba lallai ya zama Daddy bai da ra'ayi sai nasa ba, kamar kina exaggerating alaqar tasu. Sabida
kin damu da shi, kuma ba kya son sa".
Amani ta saki tsaki tace "na damu da shi a gidan wa? Ai ni kawai so nake ya bar gidan mu"
Hamida tace "ki ji da matsalar ki ta auren tsoho ki kyale bawan Allan nan ya sarara" "shawara
zaki bani ko zagi na za ki yi Balewa?" Hamidah na dariya tace "duk wanda kika zaba shi zamu
yi" ta ce "to shawara ta gaskiya nake so ki bani" "shawara ta itace ki yi wa mahaifin ki biyayya
whatsoever hujjar sa na aurar da ke ga abokin sa, wanda yayiwa iyayensa biyayya baya taba
tabewa.
A karshe ina so ni da ke duka muyi istikhara mu nemi dacewa da zabin Ubangiji ba abinda
zuciyar mu tafi karkata ba".
"Menene istikhara!" Amani ta tambayi Hamidah. "Sallah ce ta nafila da Annabi SAW ya koyar
ta neman zabin Allah kan kowanne al'amari da sulusin dare" Hamidah ta gaya mata yadda zata
yi. Ta kuma daure ta yi din. Ita da kan ta tayi mamaki ganin cewa zuwa washegari data tashi sai
taji ta wasai babu damuwa a dalilin istikharar data yi. Har jira take Alhaji Talle ya zo yayi mata
bayanin dalilin sa na kutsowa rayuwar ta. Da abinda yake nufi da Baban ta, na cewa wani suyi
yarjejeniya sai kace an gaya masa ita hajar sayarwa ce.
Mai aikin ta ce ta kwankwasa mata kofa. Tana budewa a fusace tace "lafiya da sassafe haka
kike damuna da bugun kofa?"
Rakiya ta karya wuya ta langabe cikin lallashi ta ce "kiyi hakuri, Haj. Ce tace in gaya miki ki
fito ku tafi asibiti Alhaji na can babu lafiya". Gaban Amani yayi mummunan faduwa, abinda ya
zo ran ta shine irin rabuwar da suka yi ita da Daddy din daren jiya, kada dai shi ya saka a ran sa
har ya kwantar da shi rashin lafiya? In haka ne kuwa zata yi masa biyayya iyakar iyawar ta ba Alhaji Sadi ba, ko kuturu ya kawo
ya aura mata zata yi biyayya da dai a ce wani abu ya faru da Daddyn ta a kan ta.
Sabida gigicewa a haka ta fito da kayan barci a jikin ta, sai Rakiya ce ta biyo ta da mayafi
bakin mota.
A yadda ta ga Mukhtar zaune a reception din asibitin ya hada kai da gwiwa, yayi jajawur abun
ki da farin mutum ainun, hatta idanun sa sun yi jawur ya tabbatar mata condition din na Alhaji ba
mai dadin ji bane.
Ita ta sani ko Uban sa sai haka, a irin halin da ta gan shi a ciki.
Suna hada ido ya sunkuyar da kai, ta karasa da sauri tana tambayar sa me ya samu mahaifin
ta?
Mukhtar ba baki sai ido ya bi ta da shi. Ta koma ga Haj Rabi tana tambaya. Babu wata
damuwa a tare da ita tace "sun ce ya samu stroke ne, barin jikin sa ya shanye, Amma zasu
dinga yi masa gashin kashi har ya samu lafiya".
Daidai lokacin da aka gangaro Alhajin a kan gadon marassa lafiya aka bashi daki na
musamman.
Amani ta rasa inda zata tsoma ran ta, sai kuka take yi a dakin. Haushin ta ya ishi Mukhtar
yace "ko ki yi shiru ki yi masa addu'a, ko ki koma gida" ta galla masa harara da jajayen idanun
ta tace "Uban ka ko nawa?" Ya ce "to zage ni" ta yi tsaki ta ce "in aka zage ka din me za'a yi?"
Kai tsaye yace "banida lokacin ki yanzu, amma ranar da kika kuskura kika zagenin, zaki ga me
za'a yin".
Haj Rabi ta yi salati tace "Amma ku kuwa an yi sakarkaru, ta yaya mutun yana kwance rai
kwakwai mutu kwakwai kuna neman dambe da juna a kan sa? Ku kuma irin naku hankalin
kenan maimakon ku dukufa yi masa addu'a?"
Mukhtar ya juya ya fita daga dakin ya bar su. Amani ta nufi Alhajin da sauri ta kura masa ido
yana barci kamar ba abinda ya faru da shi. Hawaye fal idonta ta soma magana.
"Daddy in dai a kan auren da kake son yi min ne ka saka kan ka a wannan yanayin na roke
ka ka tashi mu tafi gida, na amince ka aura min duk wanda ka ga dama, don Allah Daddy".
Kuka ya ci karfin ta.
Haj Rabi tace "toh? Ashe ke kika jawo masa? To ta Allah ba taki ba ban shirya yin takaba
yanzu ba, in bai tashi nan da sati daya ba wallahi sai dai ku sallame ni don ban shirya yin
takaba yanzu ba".
Amani ta juyo ta dube ta da fusatattun idanu ta ce "in kika kara shiga sha'ani na sai na
karawa wannan katon bakin naki tsini, ina ruwan ki da ni? Ko ina shiga sabgar ki? In ni na jawo
masa Uban ki ko nawa? Ko kin haifa masa ko gunduren kashi ne? Ba tumunin takabar kike jira
ba me kike so in ba shi ba?" Haji. Rabi ta kama baki, tace "ke mara kunya, wadda bata ganin mutuncin kowa, na fi karfin
ki yimin diban albarka don uban ki nake aure, shashasha da bata san komai ba sai sangarta da
rashin kunya".
Likita ya shigo dakin ya na cewa "haba! Haba bayin Allah. Yaya zaku tsaya kan mara lafiya
kuna daga murya? To daga yau mun yafe zuwan ku. Mukhtar kawai muka yarda ya zo har sai
ya dawo gida".
Amani da ta riga ta zo wuya, ga haushin Mukhtar ga na Haj Rabi ga kuma na wannan likitan
yanzu. Ta ce "idan uban ka ne shi sai ka hana ni zuwa in gani" likita ya juya ya fita kafin yarinyar
ta soma kai duka, ya fara tunanin tanada aljanu amma na rashin kunya da rashin tarbiyya.
Ta yi tsaki tana fadin "Daddy zan sa a dauke ka daga rubabben asibitin su ka ji? Jidda zan kai
ka a duba ka sosai. Get well soon my Daddy". Ta sunkuya ta sumbaci goshin sa, ta gyara masa
rufuwa da bargo duk Alhaji na barcin allurar barci bai san me suke yi ba.
Waje ta fito tana tunanin abun yi, tana neman mataimaki da zai taimaka mata wajen fidda
Daddy saudiyyah. Amma Mukhtar shine yafi dacewa da ya taimaka mata din gashi ta gama
caccakar sa ta masa gorin Uba. Da sanyin jiki ta hau neman sa a reception amma bata gan shi
ba. Bata san ma shi a lokacin yana can yana cuku_cukun samun visar tafiya da Alhaji kasar
Faransa ba.
Ya gayawa Haj. Rabi niyyar sa ita kuma tace bazata jinya ba, saidai Amani ta je. Ko kwai
bata ajiye masa ba bazata jinyar shanyewar jikin sa ba, alhalin ko tumunin takaba bai rubuta a
bata ba komai na Amani ne. don haka ta karata da uban ta ita kadai.
Mamakinta ya kusa kashe Mukhtar a tsaye, to dama ya bata hakkinta ne a matsayin ta na
matar Alhajin. Amma Shima baya so ta bi shi don baya jin zata yiwa Alhaji kulawar data kamata,
wannan aikin sai namiji kakkarfa.
Yana tsaye a gate din gidan suna magana da Malam Tajudden yana gaya masa maganar zai
tafi Abuja da Alhaji don Nemo visar tafiya asibiti a Paris. Amani ta shigo gidan tare da Malam
Audi Mai baiwa shukoki ruwa wanda shi ya tuka su zuwa asibiti. Tajudden ya juya ya dan kalle
ta sai yace da Mukhtar din ka sanar da Amani?" Yace "kaima ka san wannan yarinyar bata cikin
'yan shirgi na saboda rashin kunyar ta. Dazu har zagi na ta kusa yi fa Tajudden".
Malam Tajudden ya dafa kafadar sa cikin lallashi yace "ka yi hakuri ka manta, na sha gaya
maka sai kayi hakuri da ita in dai kana son albarkar Alhaji. Daure ka gaya mata saboda hakkinta
ne ta sani, son samu ma ku tafi tare ta zama a kusa da mahaifin ta duk sanda ya bude idon sa
ya ganta don itace sanyin idaniyar sa". Malam Tajudden ya karasa inda Amani ke kokarin fitowa daga mota yace "ran ki ya dade
Malam Mukhtar na son magana da ke, a kan lafiyar Alhaji ne" Amani ta dalla masa harara tace
"shi kurma ne? Ko Kai ne bakin sa? Bana son kinibibi bace min da gani".
Mukhtar ya karaso wurin yana cewa