Author : Sumayya Abdulkadir Category : Taskar Novels
kyarar juna. Bai
taba jin sun yi maganar arziki a tsakanin su ba tun zuwan su asibitin, ko sentence daya balle a
je ga batun gaida juna. Basa amsa sallamar junan su sai a cikin cikin su. Babu mai ragawa dan
uwan sa. Gara shi Mukhy yana rage uzzura mata a dalilin kaifin idon Alhaji.
Data fito daga toilet ficewa ta yi ta bar musu dakin ta koma reception din asibitin ta zauna a
kujera nesa da jamaa ta kira Hamida Balewa. Hamida ta ce mutuniyas ina kika shiga ne?
kwana biyu ban ji complain din dan Alhaji ba Da 'yar damuwa a muryar tace tana asibiti tare da
Daddy a France, Daddy na ya samu stroke Hamdy ki yi masa addua na san ke mai addua ce
mai yawan sallah ce da tsayuwar dare Hamida ta shiga juyayi, a karshe ta jajantawa aminiyar
ta, ta ce ke da Haj. Rabi kuke jinyar kenan?
Wani mikakken tsaki ya fito kai tsaye daga bakin Amani, tace cikin dan daga murya kema kin
san ko da waye, ko baki tambaye ni ba, ni da waye kuwa banda bare ka fi dan gida, yana nan
ya hana ni sakat, ya hana ni samun ladan uba na, masifar yau daban ta gobe daban, ke sai ki
rantse da Allah yana da gadon Daddy ko tare Alhaji ya haife mu, tare kuma yake so mu rayu
dole, ya shiga komai na gidan mu yayi kane-kane ya fi ni iko da uba na yanzu sai ta kama
matsar kwallah, Hamida tana so ta yi dariya sabida wannan sakalci na Amani, amma ta san
Amani bata cikin mood din da take bukatar a yi mata dariya, don tsakanin ta da Allah take
sharing mata damuwar ta, don bata da inda zata je ta fada ta ji sanyi, wannan Mukhy! Ya addabi
aminiyar ta, ita kuma haka nan yake burge ta, bata ganin laifin sa ko kankani, da kullum Amanin
ke nanatawa, wanda duk ciki in ka saurareta zaka fahimci ba komai ke damun ta ba sai kishin
son da mahaifin ta ke ma Mukhtar din.
Hamida ta nisa tace kin san Allah Amani, idan har na isa in baki shawara ki dauka to ki koma
girmama Mukhtar, ki kaunace shi matsayin dan uwan dake taimakawa Daddyn ki, ki bashi
gurbin Yayan da baki da shi, ku zamawa Alhaji Yaya da kanwar sa.
I'm sure duk da ban sani ba Alhaji haka yake so ya gan ku, musamman a yanzu da bashi da
lafiya ku biyu ne a kans a kuke jinyar sa.
Idan ya bar miki jinyar bazaki iya ke kadai ba dole sai namiji dan uwan sa idan ana maganan
stroke.
Kuma kin ga wannan fadan da kuke ta yi a kan idon Alhaji yana saka shi a damuwa
musamman cikin yanayin da yake a yanzu, shi fa Daddy in na fahimta saboda Allah yake son
Mukhtar din nan. Hayagagar ki bata isa tasa ya kore shi ba, da zai kore shi da tuntuni ya kora
don gudun bacin ran ki. To fadan da yafi karfin ka hausawa suka ce ka maida shi wasa, sai ka zauna lafiya.
My friend I want you to stay cool and healthy, kada Mukhy yasa jinin ki ya hau, zuciyar ki ta
buga a banza ya yi wa Alhaji da kan sa asara. Ta karasa cikin dariya ta kuma yi maza ta kashe
wayar ta. Amani na kururuwar sai tagaya mata me take nufi da hawan jinin ta ta ko bugawar
zuciyar ta zata zamo asara ga Mukhtar. Meye manufar ta? Hamida nata dariya ita kadai ta tura mata text. Ga abinda ta rubuta mata.
kan ki ake ji kullum a kan sa, kin hana kan ki zaman lafiya saboda shi, watch your actions
over him, you care too much for him, listen to your heart and understand the actual feelings.
-Yours Hamdy.
Amani ta kusa zagin Hamida, ta kira ta back yafi sau biyar Hamida ta ki dauka, kamar ta yi
hauka ita kadai wai Hamida ta zageta, zagin da baa taba yi mata irin sa ba, ta rasa wanda zata
ce ta saurari zuciyar ta a kan sa sai Mukhtar? Me zata saurara din banda bugun zuciyar ta dake
karuwa kullum a kan bacin ran da yake sanya ta kullum? Hamida daga inda take sai murmushi take yi rike da wayar hannun ta, ta dubi fuskar wayar
kamar Amani take kallo tana mata murmushin karfafa guiwa, haka kawai ta samu kan ta tana
ma aminiyar ta shaawar auren Mukhy din nan, duk da kasancewar sa a karkashin mahaifin ta,
ta shiga yi ma Amani adduar samun daidaiton raayi da fahimtar juna tsakanin ta da wanda take
ganin ya shige gabanta. A ganin Hamida ba wanda zai iya da ita da halayen ta duk duniya sai
wannan Mukhtar din, da tun yanzu yake juya Amani wanda hakan ke nuna zai iya jarumtakar
zama da Amani da dukkan halayen ta, ta san zama da Amani sai jarumin mutum, duk kawayen
su na makaranta babu wadda Amani bata yi fada da ita ba itama don ta zame mata kamar 'yar
uwa ne ko sun yi fada ita da kanta Amanin zata zo ta nemo ta su shirya. A ganin Hamida babu
mai iya auren Amani ya juya ta sai jarumin namiji saboda izzar ta. Ta kuma yabawa Mukhtar
wajen jure rayuwa kusa da Amani alhali kullum tana kyarar sa da gori kala-kala. To amma Alhaji
ya riga ya karbi maganar abokin sa ta kuma ce mata ta yi masa biyayya a kan maganar Alhaji
Sadi, yanzu kam ta fi mata shaawar auren Mukhtar yaro dan uwan ta mai halin manya.
Zata dukufa taya Amani adduar samun zabi mafi alkhairi a matsayin ta na aminiya ta kwarai.
Miji wanda zai taimaka ya saita musu hankalin ta, tarbiyyar ta, addinin ta da nutsuwar ta.
Wadanda duk ta rasa a dalilin rashin tashi gaban mahaifiya.
Sanda ta koma dakin maghriba ta kawo kai, Mukhtar na yima Alhaji alwallah zai yi sallah
yadda yake yi daga kwance, sai ya tabbatar Alhajin ya tada sallah sannan ya shiga ya dauro
tasa ya fito, sai ya tadda Amani ta ja ledar nashi abincin tana ci ba kunya ba tsoron Allah fuska
tamke, an ce yunwa ba kanwar uwa bace. Girgiza kai yayi ya shimfida dardumar da yake sallah a kai ya tada sallah a gefen gadon
Alhaji.
Ko da ya idar da sallah bai ce mata don me ta ci masa abinci ba, ya san dama in yunwar
cikin ta ta kama ta zata ci ne kullum haka take masa, ba don komai ba sai don kada tace ta
gode a duk lokacin da ya sayo masu abinci.
A haka sauki ke ta samuwa ga Alhaji Usman, bakin sa da ake ta gasawa ya fara fidda
magana sosai, likitocin sa sun ce duk bayan watanni shida zasu dinga zuwa check up, duk da
tafiya da kafafu bata samu ba don haka suka ce Alhaji zai dinga amfani da wheelchair.
Watan su guda kenan suna jinyar Alhaji amma ba abinda ya canza a alaqar su. Yau suka
sauka a gida Mukhtar na turo Alhaji a wheelchair inda Haj. Rabi taje ta taho dasu daga filin jirgi
tareda sauran ma'aikatan kamfanin Faskari. Kowa ya zo falo ya jajantawa Alhaji yayi masa
sannu da dawowa. Malam Tajuddeen shi ya gaya musu zuwan Alhaji Sadi Talle uku bai samu Alhajin ba, yace
kuma layin Alhajin da yake da shi baya tafiya, sun gaya masa Alhaji asibiti yaje babu lafiya, ya
ce duk ranar da suka dawo Malam Tajuddeen ya sanar da shi.
Ba Alhaji ne kadai fuskar sa ta sauya ba har da ta Mukhtar. Amani tunda ta haura sama ta
bar su bata kara saukowa ba.
**** **** ****
Washegari kuwa tunda safe Alhaji Sadi ya zo cikin rantsatstsiyar motar sa Acura, kai da
ganin irin kwalliyar da ya caba cikin sassalkar shadda fara kal, zaka san ba dubiya kadai ya zo
ba har da zance na saurayi ga budurwa don fara kafa gwamnatin sa.
Mukhtar baya gida yana company don gudanar da ayyukan da suke jiran sa duk da cewa
yana rage ayyukan sa daga can asibiti ta kwamfuta wadanda sakataren sa ke tura masa,
musamman in Alhaji na barci, zaka same shi yana aiki cikin kwamfuta yayin da zaka samu
Amani na harkokin ta cikin wayar ta cikin dakin ba ya ko daga ido ya dube ta, amma a zuciyar
sa ya na takaicin ace mace bata da abun yi sai shiga social media, babu lazimi sam babu
karatun Alqurani, Amani fa ko addua take son yi sai dai ta roki Hamida tayi mata don a cewar ta
bata iya hana idon ta barci, kuma Hamida ta fi ta juriyar tsayuwar dare. A hakan da yake yi ya
samu ya rarrage ayyukan kamfani da yawa ta yadda yanzu da ya dawo ayyukan basu cude
masa ba, ko da yake yanzu ayyuka sun karu masa tunda shi yake gudanar da duk wanda Alhaji
ke yi da kan sa a lokacin da yake da lafiya.
Aka yi wa Alhaji Sadi iso falon Alhajin, bisa umarnin Alhajin. Yana shiga ya ga Alhaji cikin
wheelchair a zaune yana kallon talabijin. Alhaji Sadi ya ce Ya salamu sallim, ashe ciwon babba
ne haka? Yanzu da wadanne kafafu zaka yi takara? Kai bana jin ma jamiyya zata yarda in
tsayar da mai shanyayyen barin jiki kan kujerar gwamna tunda ba ni kadai ke da jamiyyar ba. Sannan ya zauna gefen sa ya bashi hannu yana fadin sannu, sannu yaya jikin naka? Kana
iya magana dai ko?
Alhaji ya ji ciwon wadannan maganganu na Alhaji Sadi, amma ko a fuskar sa bai nuna ba, sai
yayi murmushi yace ai ba sai ka gaya min na zama mara amfani ba yanzu, nima na sani, na
kuma yarda duniya da dan Adam duka ba a bakin komai suke ba, yau ne kake mutum gobe
zaka iya zama rabi gawa ko duka gawa, na yi kurakurai masu yawa a rayuwa ta dana ke neman
yafiyar ubangiji a yanzu ba takara ce a gaba na ba, tuni na dade da janyewa. Yanzu zan maida hankali na ne akan ibadah da neman guzurin lahira da nemawa diya ta
kyakkyawan Future.
Da kyau. In ji Sadi Talle, wannan tunani ne kayi mai kyau, amma ina fatan ba zai shafi
yarjejeniyar mu ba. Ka fadi duk abinda kake so daga gare ni in yi maka, koda tsayar da wannan
balaraben yaron naka ne na ga alamun sa jajirtacce ne kuma namijin duniya ne ko daga takun
sa, yana da leadership appearance, amma bayan ka bani auren Amani, yau da shiri na na zo
don muyi ganawa ta musamman da ita.
Alhaji yayi murmushi ya ce yadda na fasa takara haka na fasa aurar da ya ta, zan bata
yancin ta ne na tafiya karatu ta kuma kawo duk wanda take so da kanta na aura mata, ko da
kuwa kai din ne, don haka a adalci irin nawa, na baka damar ganawa da Amani yau, ka ji raa
yin ta a kan ka, ka nemi soyayyar ta, in ta amince zan fi kowa farin ciki tunda ba yau muke tare
ba na san baka da matsalar da zaa hana ka aure.
Idan kuma Amani ta ce bata yarda ba sai kayi hakuri ka nemi wata. Ina Mukhtar ina tsayawa
takarar gwamnan Katsina shi da ba ma dan kasar Najeriya ba? Baabzine ne fa!
Alhaji Sadi sai ya rasa abin cewa, amma tabbas ya ji dadi da Alhaji ya bashi damar ganin
Amani.
Ya dauki wayar sa ya kira Amani, da kyar ta daga cikin magagin barci, ta fara korafi Daddy ka
san gajiyar da ke jiki na kuwa ka tashe ni da safen nan? yi hakuri Tafisu, sauko yanzun nan
amma kisa mayafi don na san ki da shirme. Kafin ta ce komai ya kashe wayar sa ya barta da
mamakin ko lafiya yake fadin tasa mayafi? Saboda ya ji Mukhtar din sa na korafi shine shima
yau ya koya, wato duk inda takurawa take sai Mukhy ya nemo mata ta hanyar juya kan baban
ta da irin raayoyin sa na akida.
Tana mitar tana komai ta saka Abaya da mayafin ta da silifas din bakin gado, tana saukowa
suka hada steps da Haj Rabi saura kadan Hajiyar ta bangaje ta, Amani ta kauce. Haj. Rabi ta
ce ji mana? Amani ta dan dakata da sauka daga steps din ba tare da ta juyo ba. Haj. Rabi ta
tako ta iso bayan ta ta soma magana cikin zafin murya. Jiya na nemi saki a gun Baban ki don na fi karfin yi wa mai shanyayyen jiki takaba ko jinya, ni
ba gado ba ba komai ba, ya ce magana tana hannun ki, ke kika hana shi sallama ta da tuni ya
sallame ni. To don uwar ki ke kike aure na da zaki hana a sake ni?
Da sauri Amani ta girgiza kai don bata taba jin wanda ya zagi uwar da ko gani bata taba yi ba
sai yau, wadda duk da bata san ta ba, zuciyar ta cike take da kaunarta.
Haj. Rabi ta cigaba da cewa.
idan kin haifu cikin Usman da Jalan yau ki sa ya rubuta min shika uku, idan kuwa kin ki, in
kun ki ji ba kwa ki gani ba. Don wallahi sai na saka masa filo a hanci na karasa shi, ko in saka
masa shinkafar bera a abinci ya ci ya karasa, kuma dole a bani tumunin takaba. Amani bata iya
ta karasa jin maganganun Hajiya Rabi masu neman fasa mata kwanya ba, ta wuce falon Alhaji
da sauri. Ta fado dakin cikin gigita tamkar an jefo ta.
Zata yi magana ta ga Alhaji Sadi a zaune, ai kuwa fushin ta ya kara ninkuwa, ta juya za ta
koma. Alhaji ya ce Tafisu bakon ka Annabin ka.
Ba don jikin ta yayi sanyi ba ta dawo ta zauna, sai don bata son kunyata Baban ta a idon
Sadi Talle. Ta daga ido tace me kake so a wajena Malam? Alhaji ya soma gurgura kujerar sa
mai tayoyi ya koma cikin dakin barcin sa ya bar su a falon.
Babu kunya babu tsoron Allah fuskar sa kamar gonar auduga ya ce me kuwa na ke so ban
da soyayyar ki Amani? Wadda nake fatan ta kai mu ga aure nan ba da jimawa ba?
Amani ta yi kuta, ta ce ina maka kallon Babana ba don haka ba da na ce an yi furfurar banza,
ka so hada ni rigima da Babana Allah ya fi ka, yana zaman zaman sa ka sa shi a damuwar data
kai shi ga faduwa, wani ya baka aure na ka bashi takara shin Katsinar taka ce? Halan bai gaya
maka cewa ta lafiyar sa yake ba yanzu ba ta sayar da yar sa ba? Aikin banza aikin wofi to bana
son naka, ko a kafa aka daura min kai zan kunce in zura da gudu Alhaji Sadi ya ce ke mara
kunya! Ya ishe ki haka, kada kimin gorin halitta don duk muni na ban kai na uban ki ba. gara ni
ina iya auren shi kuwa me yake kullawa matar sa sai dai ta je waje. Don haka kada ki sake ki
zage ni yanzu in tattaka ki a wurin nan.
Sai gani suka yi an daga labulen dakin an shigo da sallama. Mukhtar ya bayyana a falon
cikin bakaken shirt da wando na NEIMAN MARCUS, sumar nan nannadaddiya ta sha gyara da
Argan Oil tayi lub a kan sa har ta sauka kadan a kan wuyan sa. Amani na ganin shigowar sa,
bata san me yasa ba, sai taji duk wani rauni na duniya ya rufto mata, ga bakin cikin aj Haj. Rabi
da tsoron kalaman ta, ga na wannan mutumin, ji tayi tamkar wani savior ya zo gabanta don ya
kawo mata dauki, kawai sai ta mike ta nufi Mukhtar da azama ta rungume shi ta fashe da kuka
mai karfi.
Mukhtar ya kusa suma a tsayen da yake, sai kawai ya tsaya kamar an kafe shi a bakin kofar
ya rike Amani dake kara neman mafaka a kirjin sa, yana kokarin zamewa tana kara rike shi, sai
ya ga abin kamar a cikin mafarki amma duk da haka ya iya saita kan sa. Tsawa ya daka mata
ya ce sakar ni nace, bana son sakarci. Cikin jin kunya ta cika shi tana kuka tana nuna Alhaji Talle. Ka roki Alhaji ya yi min iyaka da
su,