Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
Netflix. Hamma dakinsa ya wuce cikin wani yanayi. Domin maganganun Aisha
bakidaya na yau sun zame masa food for thought.
Ya kasa barci a daren nan ya samu kansa da kallon selfie dinsu shi na birthday shida Aisha,
da tuna hirarrakin da suka gudana a tsakaninsu. A daren yau Prince yayi abinda bai taba yi ba,
wato yin rubutu a shafukansa na social media.
Domin bayan ya kasa daina kallon selfie din, sai ya budo status dinsa na whatsapp, yayi wani
rubutu mai matukar jan hankali da shikadai yasan ma’anar kayansa, a kasan hotonsu shi da
Aisha, bayan yayi covering fuskar Aisha, amma gangar jikinta ta fita gaban candle lit cake.
“Happenings at 43rd Birthday ….. !!!
The wife that is slowly becoming the centre of my universe”.
**** **** ****
Wani ikon Allah Taiwo ce ta fara ganin status din brothernta. Ta sha mamaki ganin yau
Kehinde ya dora status don baya yi sam. Don haka da doki da zaquwa ta bude don taga me
Kehinde zai daura?
Ta kuwa ci karo da wannan magana da hotonsa shida Aisha, da suka yi matukar daure mata
kai. Me Kehinde ke nufi? Ya folawa wannan yarinyar ko yaya ne? Nan take tayi screenshot cike
da takaici da tsegumi ta turawa Haseenah.
Washegarin ranar Kiki tayi musu sallama ta wuce makaranta bayan Kawun nata ya cikata da
duk abinda zata bukata, har ma da wanda yafi karfin bukatunta.
Bayan wucewar Kiki Aisha duk ta canza wa rayuwar gidan, dan fitowa falo da take yi duk ta
daina. Aisha ta maida kanta daddawar daka, gabadaya walwalar nan da ta ke yi sanda Kiki ta
ke nan ta dauke daga fuskarta ta komar da kanta yadda suka saba zama ita da Hamma tun
kafin zuwan Kiki. Duk inda miji yake sunansa miji, da soyayya ko babu, to hakan ce ta faru Prince Kehinde,
bayan tafiyar Kiki da canzawar yanayin Aisha, duk sai ya ji ya damu. Ya shiga takura da
canzawarta da rashin fitowarta falo yadda suka saba. Ko da ma can shi Aisha tausayi ta ke ba
shi, balle yanzu daya fara sanin wacece AISHA-SIDDIQAH. Zaman Kiki ya haifar mata da walwala mai yawa, ya fara bankado masa asirin dake kunshe a
zuciyar Aisha, ya ga excitement a tare da ita, irin wanda bai taba gani a tare da ita ba, kafin
zuwan Kiki. Sai Hamma yaga cewa zai yi kokari ya maye mata gurbin Kiki, wato ya zame mata
babban aboki kuma dan uwa, wanda zata iya yin dariya da walwala tare da shi idan har zata
yarda da hakan. It’s not easy a rabo ka da iyaye, dangi, kasarka da kowa naka sannan a barka
cikin damuwa.
Yau kwanan Kiki hudu da wucewa, kuma tun lokacin ganinsa da Aisha sau daya ne tak! Ya
zauna a falon har ba adadi domin ya ga gilmawarta ko don ya tabbatar da lafiyarta amma ko
kamshinta bai ji ba.
Aisha wadda ta koma daddawar daka tun bayan tafiyar Kiki Ruqayyyat, ko kiraye-kirayen
waya data ke wuni tana yi da jama’ar gidansu dana gidan Nenne yanzu ta rage. Ta fi yin tilawar
Alkur’ani da nafilfili a cikin dakinta, sai ta tabbatar Hamma ya fita ‘Ranch’ ta hanyar hango shi
cikin stable din dawakansa ta tagar dakinta take fita kitchen ta dafa taliyar indomie da bakin
ruwan tea, tayi maza ta juye a flask ta shige daki shikenan.
Dama Kiki ce ta matsa suke cin abinci tare dashi. A rashin Kiki kuwa, sai ta maida musu
rayuwarsu ta tun asali irin yadda suka fara ta.
Duk iya juriyar Prince da dakewa da jin sarauta, ya kasa yin biris da wannan silence din na
Aisha. Da canjin data kawo musu. Because it’s killing him inside.
A can dakinta ita kuma a kwanakin nan guda hudu, Aisha babu abin da ta ke yi sai sauraron
zuciyarta, tana ‘digesting’ maganganun Kiki na hankalin dana wautar. Tana daukar na hankalin,
tana watsar da na shirmen.
A ciki Kiki ta ce da ita kada ta kara yarda Hamma ya barta jiran gida. Ta dinga saka su
lingeries a cikin gida da sauransu.
Kiki ta manta duka wannan ana yi ne a inda akwai soyayya da kaunar juna. Ba ta haufin yau
da a ce Ishaq ta aura za ta iya yin fin abubuwan da Kiki ke koyar da ita. Ita ba bagidajiya ba ce
irin yadda kowa ke daukanta, ta san duk abin da ya kamata macen kwarai ta yi a dakin aurenta,
uzurinta kawai shi ne Prince ba sonta yake ba, ita ma kuma haka, sannan ba ta hango musu
wani canji a zamantakewarsu nan kusa ba, domin ita da shi duka danjuma ne da Danjummai.
Wato babu wanda ya damu da wani abu wai soyayya, ita a kan Ishaq duk wani tsuntsun
soyayyarta ya gama tashi.
Tana wannan tunanin mara adadi a zuciyarta ta ji motsin ana knocking kofarta kadan-kadan.
Kafin a shiga kwankwasawa sosai, a nitse Aisha ta tashi zaune daga kwanciyar da ta ke, ta isa
ga kofar ta bude don ta san babu mai yi mata knocking har kofar dakin barci a gidannan a kuma
daidai wannan lokacin da dare ya fara nisa in ba shi Hamma Prince din ba. Aisha ta taso ta bude wa Hamma kofa, ta rabe jikin kofar ta ba shi damar shigowa don alamu
sun nuna shigowar yake so zai yi dakin.
Sai da ya baza manyan idanunsa yana nazarin tsaftar dakin. Ba laifi Aisha ba ta watsar da
shirgi, komai nata neat. Don haka ya zabi sofa-bed guda daya dake dakin ya zauna, kafin ya
dago a hankali idanunshi a lumshe ya fuskanci inda take tsaye tana gaisheshi, bai amsa
gaisuwar ba yace, “Are you alright? Kwana biyu bana ganin wulgawarki a sitting room, baki ko gaisheni, ina
fatan dai lafiya?”.
Kan Aisha a sadde ta bada amsa, “Wallahi lafiya kalau Uncle, kawai ina kewar Kiki-Rukayyat
ne”.
Prince ya yi murmushi ya ce, “Ni kuma da kika daina fitowa kinsan ya nayi kewar ki? Na ga
alama jininki ya hadu da na Kiki, ga shi ba ki san ita yarinya ce mai kiriniya da rawar kai ba.
Kawancenku ba zai yi daidai ba, considering cewa ke din Uwa ce a gare ta.
Ba komai za ki dinga tattaunawa da Kiki ba akaina please, zan kai ki makaranta insha Allah
idan nagama hutuna mun koma inda nake aiki a Qatar, domin ki samu abin debe kewa”.
Godiya sosai Aisha ta hau yi, tana jin kamar Hamma ya mata bushara da kujerar makkah,
kwarai ta ke son komawa makaranta, ta dauka karshen karatunta a rayuwa kenan sakandire,
amma ta san wannan shekarar dai ta shige mata, sai ko shekara ta gaba. Prince yace yana
mikewa tsaye, hannunwansa biyu zube cikin aljihu, “ina fatan gobe da safe zan samu breakfast daga hannun Ayshah? Tunda Kiki ta tafi kika
daina bani, bayan kwana biyu kun shagwabani da kyawawan girke-girken nan naku”.
Ya fada yana kokarin saka idanunsa cikin na Aisha, ita kuma tana kokarin sunkuyar da kai ga
barin kallonsa.
Prince ya kai bakin kofa yana cewa “Good night Ayshah!”. Amma kuma ya kasa ficewa daga
dakin gabadaya, rabin jikinsa har lokacin yana cikin dakin. Wani bakon yanayi yana ziyartarsa.
Da kyar da dakiya da jan kafa da karfafa giyar mulkinsa kada ta gudu ta barshi, da
maintaining class dinsa kada ya bada kansa da yawa gaban little Aisha, Prince ya samu ya
fidda gangar jikinsa data makale a dakin, amma har washegari zuciyarsa na reto tsakanin
dakinsa zuwa na Aisha. Ji yake kamar ya dawo ya kwana a dakin tareda ita. A washegari kuma ya samu waya daga Ilorin cewa, Emir babu lafiya, ko fada baya iya fitowa,
yau kwana uku yana kwance saidai a kwantas a tayar.
Bai yi niyyar zuwa gida nan kusa ba, ko sake yin tafiya cikin hutunsa, amma sanin kowa ne
sha’ani in ya hada da Kakansa Emir daban yake a gare shi, balle magana ake ta lafiyar
Kakansa Maimartaba Sarki, ba zai iya kara wasu kwanaki bai je ya ganshi ba, a take Prince ya
soma neman jirgi mafi kusa domin tafiya Ilorin. Ya tuna Siddiqah, yaya zai yi da ita idan ya tafi? Wancan lokacin da Kiki, wannan kuma babu.
A karshe ya ga gara ta zauna ita kadai din maimakon ya dauke ta yanzu zuwa Ilorin, ya yi
wuri ma ta je gida nan kusa, gara ma tun yanzu Aishah ta koyi zama ita kadai, don kuwa
tafiye-tafiyensa ba masu karewa ba ne.
Banda sauyukan dake faruwa dashi a ‘yan kwanakinnan a kanta, wato yanzu da ya fara
sabawa da ita, ya kuma fara fuskantar dadin mu’amalar da yarinyar keda shi, da ba zai damu
don ya tafi ya barta ita kadai cikin gidannan ba.
Zuwa yanzu Prince da kansa ya fara tantama a kan cikar lafiyarsa, don duk da tabbacin da
yake da shi na cewa Siddiqa matarsa ce, bai taba jin darsuwar wani abu game da ita a ransa ba
da ya danganci ‘sexual urge’. Ya dai fara jinta a ransa, ta manne a zuciyarsa. Watakila kuma ko
don ya riga da ya saba da yadda yake rayuwarsa ne tuntuni daga shi sai shi, sai ibadar
addininsa, sai lafiyar Dawakansa sai kuma zuwa Polo tournament sai aikinsa na ‘Qatar
Petroleum Refinery?’.
Bai gaya wa Siddiqah maganar tafiyarsa Ilorin ba sai bayan ya gama duk wani shiri yayi
(booking flight) dinsa na tafiyar, wato ana i-gobe zai tashi zuwa Ilorin.
Siddiqah tana kitchennett tana tana dauraye kofin Mug din data sha tea, ta ji motsin Prince ya
shigo inda take.
Kai tsaye firij ya nufa, ya bude ya dauki gorar ruwa ya rufe. Ta gama wankin kofin tana kife
shi a wurinsa taji motsinsa dab da gefenta. Siddiqa ta rusuna tana gaishe shi da irin gaisuwarsu
ta ce, “Ekaaro Uncle” (wato ina kwana)”. Wannan Uncle da Siddiqah ke lanqaya masa ba ya
son jin shi, har gara masa Hamma Abdul din da take kiransa dashi da fari kafin zuwan Kiki. A kan me za ta dinga ce masa Uncle sai ka ce wata Kiki? Uncle din nan da ta ke ce masa na
sawa ya ji kansa tsoho sosai a kanta sosai.
Amma wannan ba shi ne abin da ya kawo shi yanzu ba da yayi korafi, ya zo ne ya gaya
mata batun tafiyarshi duba Emir gobe. Tun shekaranjiya rabon shi da ganin Siddiqah. Jiyan da
shekaranjiyan duk bai karya kumallo a gidan ba, ya wuni ne a ‘Cathedral of Polo’, shi ya sa bai
ga gilmawarta ba, don ko babu komai koda bazata saki jiki dashi yadda yakeso ba yanzu, yana
son ganin gilmawarta a kitchen don dai ya tabbatar da lafiyarta.
Murya a tausashe ya ce, “Siddiqah, in baki ganni ba ba kya nemana cikin gidannan ko? In ma
mutuwa nayi cikin daki ko bani da lafiya duk ba damuwarki bane ba ko Ayshah?”.
Kiran sunan nata da ya yi har sau biyu yasa ta bashi hankalinta, don yau ne karo na biyu da
Prince ya ambaci sunanta. Ya kara matsowa dab da ita, ita kuma ta dan ja baya.
Ya ce, "daina ja da baya ba rike ki zan yi ba Pretty, so nake na gaya miki zan je Ilorin, zan
dubo jikin Kakana.
Ba na fatan in wuce kwanaki bakwai ban dawo ba, ko akwai abubuwan da ki ke bukata?”
Siddiqah kamar ta ce masa za ta bi shi, to amma ita ma tasan ya yi wuri su Nenne su ganta
yanzu, duk da cewa ba abin da ke hada su cikin gidan ta san akwai mutum, idan yana nan. Don
haka ta samu kanta da rashin jin dadin zancen tafiyarsa, haka ta daure ta ce,
“Bana bukatar komai Uncle, ka saya mana komai, ina maka addu’a Allah ya kiyaye hanya ya
bawa Emir lafiya, ina duba shi da jiki, in ka karasa wajen su Nenne, ina gaishe su bakidaya,
Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya”.
Prince ya ji kamar ya riko hannayenta ya sumbata, ganin damuwa karara a kyakkyawar
bafullatar fuskarta. Ashe haka mutum yake ji idan iyalinsa sun masa addu’a?
A zuciyarta kuwa hudubar Kiki ke ta mata aiki, na ta daina yarda yana tafiya yana barinta
gadin gidan gona, to amma kwarjinin Hamma da girmansa da ta ke gani cikin idanunta ya sa
kowanne hukunci ya yi ba ta da ja a kai, musamman a kan zuwansa Ilorin dinnan itama ta san
ya yi wuri a ce ta bi shi yanzu. Ta kalle shi a raunane, shi ma kallonta din yake yi da wani sabon yanayi cikin idanun Hamma
Abdulrasheed Prince, ya zuba dukkan hannayensa cikin aljihun wandonshi ya juya ya bar
kitchen din, yana kokarin maida wani abu da ke neman fita daga bakinsa, wato kalmar ‘I will
miss you’ da yake ganin bata dace ya furtawa Aisha ita ba. Amma tabbas zai yi kewar tata,
gashi yana son ya zauna tare da Kakansa a wannan lokacin ya kula da shi da kansa.
Prince ya tashi a washegarin ranar litinin Siddiqah ta tashi da azumin tadauwa’I a bakinta,
wajejen karfe sha daya na rana ta kammala shiryawa ta fito zuwa falo.
Ta kunna TV da taimakon remote tana kunnawa din kuma tashar Polo ta ‘PoloLine TV’ ce ta
kama, ga dukkan alamu ita ce tashar da ya fi kalla. Ta tarar ana gudanar da wasan tseren Doki.
Ta sha jin Nenne na ce mata Hamma yana polo, bata taba ganinsa a profession din ba sai yau,
gashinan tsaf ya fito cikin kayansa na polo. A lokacin ana gudanar da wasan ‘Concacap World
Polo Championship’. Kasancewar Helmet din kansa budaddiya ce ya bata damar gane
fuskarshi sosai cikin mahaya dawakan.
Dokin da yake kai wani farin kosasshen doki ne mai fatsi-fatsi, wanda a halin yanzu Prince
baya wasan Polo da shi, tun wancan lokacin da suka fadi tare shi da dokin nasa.
Siddiqah aka gyara zama ana kallon duk wani motsi na Prince Abdulrasheed Kehinde . Gudu
yake da doki cikin kwarewa da iyawa, kamar zai yi fiffike ya tashi sama.
“Wannan shi ne ake kira Polo kenan!” Inji Siddiqah. Kuma a koyaushe ta kalli wasan da aka
nuno zata ga cewa kusan Prince shi ne jagaban wasan, wato shi ne a sahun gaba na wadanda
ke neman isa goal.
Abin ya burge Siddiqa matuka don kuwa a wannan daren kusan kwana ta yi tana mafarkin
Prince Abdulrasheed a kan doki, yana mata murmushi da helmelt dinsa mai ban sha'awa a a
kansa.
Shi kuma Hamma tunda ya sauka a Ilorin bai samu sukunin da zai tuna kowa da komai bama
don jikin Emir ya yi tsanani, ko wayarsa bai iya ya bude ba.
A washegarin ranar ne Aisha ta fara fitowa ainahin kwaryar ‘Ranch house’ din, sabida kadaici
daya dameta, kallo sosai Siddiqah take na dabbobi kala-kala masu daraja, harda wadanda ko a
talabijin bata taba ganin irinsu ba.
Tana tafe a sannu itace har wurin stable din dawakai. Daga ganin farin doki mai fatsi-fatsi
“Saheeb” Siddiqah ta gane shi saboda irin kebewa da killacewar da aka yi masa. Wato an ware
shi daga ragowar. Ba wanda ya isa ya je inda yake ba tare da Saheeb ya harbe shi ba, daga
Prince sai Pareto. Amma daga nesa Pareto ya hango wani abin mamaki, wato Siddiqah ta isa har gaban
Saheeb bai harbe ta ba. The beautiful royal horse “Saheeb”, duk ya fi sauran dawakan girma da
mulmulallen jiki mai kyau.
Ga tsafta ta kama jikinsa saboda kulawar Pareto. Farcensa kansa tsaf-tsaf yake, sannan
yana zaune cikin korran ciyayi masu taushi da tsabta.
Nan Siddiqah ta shashance har lokacin sallar azahar tare da doki Saheeb a stable dinsa.
Pareto sai komawa ya yi da baya don ya ga tana jin dadin zaman wajen, sauran ma’aikatan
gidan gona kuwa kowa yana bisa aikinsa babu wanda ya ba ta hankalinsa.
Sai ya zamana daga ranar kullum da safe sai Siddiqah ta je stable din Saheeb, har dokin na
Prince ya fara gane ta. Da ya ga tahowarta zai fara haniniya yana daga kafafu sama irin yadda
yake yi idan ya ga Prince. Ba da sanin kowa ba cikin kwanaki hudu kacal da tafiyar Prince Ilorin
Aisha da Saheeb suka yi developing good bond. Har wajen