Aishah Saddiqa Part 3 by Takori Kabara .pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   12 / 16

33K to 36K   out of 46.5K words

za
ki tsaya kina kuka don yana fada? Ko ni ‘yar sa kin ga na yi kuka?
Haba mana kada ki bada Aishoshi. A sanina duk Aishoshi ba matsorata bane, ba wawaye
bane. Duk inda na san Aisha na san mace ce mai karfin zuciya da kwatar kanta wurin miji ta
hanyar kissa da iya kisisina. Sannan ta bada misali ga sauran mata saboda iya tarairayar miji,
ta riga ta sha gaban mijinta duk shekaru da sarautarsa. Kada ki manta kannen Nana Aisha kuke. Wadda kankantar shekarunta basu hanata zamowa
tauraruwa a idon Ma'aiki SAW ba, ke saboda kankantar shekarun nataa ne ma yasa yafi biye
mata".
Haka Kiki ta yi ta kwankwadawa kwakwalwar Aisha hudubarta, irin ta wayayyun ‘yammatan
yarbawa.
Wani abun ma in ta fada Aishar ta ke bari da jin kunya, wato sai ta barta da ji mata kunyar
duniyancin da ta ke so Aishan ta koma yi wa Hamma, da cirewa kanta rauni da tsoro a zamanta
da Prince Kahinde, musamman in yana fada.
Ta ce, “Baban nan nawa sai kin yi da gaske Aisha, don zuma ne ga zaki ga harbi, sannan ya
kwashe shekarun kuruciyarsa babu aure, yanzu da ya samu bazai rike shi da wasa ba kishinsa
akan matarsa yanzu ya fara.
Ki yi duk abin da ki ka san zai sayo miki martaba da kima da soyayya a idanunsa”.
Aisha ta zumburo baki, ta ce,
“Kiki, ni na ce miki ina son soyayya daga Babanki Hamma Abdul? Ai ki bar mu yadda ki ka
zo ki ka same mu kawai, ba abinda zai iya canzawa a tsakaninmu don duk zaman biyayya
muke yi ba neman canji muke ba”.
Kiki ta ce, “Taurin kanki shi yake ba ni haushi dake, amma na tabbata Uncle ya fara kamuwa
da sonki. Ko daga kishinki muraran da ya soma nunawa ba tare da ya san yana yi bama.
Tunda nake Uncle bai taba yi min jan ido ba sai yau a kanki. Wanda ke nuna zuciyarsa ta fara
sauyawa positively a kanki”.
Aisha bata ce komai ba, rokon Kiki ta ke a kan ta kara kwanaki, Kiki na cewa lokacin komawa
makarantarta ya yi. Zadai ta Kara kwana daya saboda gobe akwai wani surprise data keson
yiwa Uncle AK. Tsabar fadan sa na yau yasa ya manta (tomorrow is his 43rd birthday).
Washegari tunda safe Kiki ta soma shirye shiryenta a boye na shiryawa Hamma Candle Lit
Dinner. Na farko ta bada order din birthday cake mai kyau da tsada ta kuma sa Chef a kusa
dasu su shirya mata dinner na abinci da abin sha na alfarma, na iya mutum biyu zuwa uku, tun
kafin karfe bakwai na magariba aka kawo mata komai. Ta sa Pareto ya kai mata karamin dining table na farar roba da kujerunsa zagaye dashi a
wani bangare na korran ciyayi dake cikin Ranch din.

Aisha na fitowa daga wanka Kiki ta zabo mata wata gown ta wani jan material da ratsin baki,
budaddiya sosai daga kasa amma ta kama kirjinta sosai, cikin kayanta da tazo dasu daga
Lagos, tace tayiwa Allah su zata saka yanzu, sannan ta zaunar da ita bisa stool din mudubi
tanaso zata yi mata kwalliya. Kiki ta fara zizara mata sassanyar make-up, wato irin light make-up dinnan ba mai daukar ido
ba. A
isha dai tana kallon ikon Allah don Kiki bata gaya mata ko me take shiryawa ba.
A can kuma Pareto ya gama shirya table din da kwalliya ta ban kaye bisa umarnin
uwardakinsa Kiki-Ruqayyat. Ya shirya abincin da ya karbo order, ya aje katon cake a tsakiyar
table din. A jikin cake din Kiki tasa an rubuta “Happy 43rd Birthday Uncle AK”.
Kiki ta fara zuwa wajen ta tabbatar komai yayi yadda take so ya kuma tafi yadda ta tsara. Sai
tasa Pareto ya kashe mata wutar harabar wajen gabadaya. Sai wata 'yar kankanuwar ‘dim light’
ya bari.
Ta dawo daki tana cewa Aisha “Pretty biyo ni muje cikin Ranch, amma don Alah kada ki
tambayeni komai”.
“Kiki ho!” In ji Aisha, da alama dramomin Kiki ba masu karewa bane. Haka tabi bayan Kiki
zuwa cikin gidan gonar.
Kiki ta kama hannun Aisha ta zaunar da ita a kujera ta kuma karbe wayar Aisha ta rike don
ma kada Aisha ta haska wajen da wayartata.
Komawa tayi neman Uncle cikin gidan har dakinsa, acan ta samoshi idar da sallahr isha’insa
kenan yaji knocking din Kiki. Saida ya kwashi mintuna kafin ya taso ya bude don yasan bazai
wuce ita din ce ba.
Casual wears dinsa ne a jikinsa kamar kullum wato shirt da dogon wandona Mark Jacobs.
Harda farin karamin cazbaha a hannunsa. Yana bude kofar Kiki na kamo hannunsa.
“Uncle don Allah biyo ni, amma kada ka tambayeni komai”.
Inda sabo Prince ya saba da rigimar Kiki da dramarta kala-kala, haka ya yarda ya bi bayan
Kiki zuwa bangaren data keso suje na gidan.
Bai kuma tambayeta din ba har shima ta zaunar dashi a kusa da Aisha yana cewa,
"me ya faru aka kashe wutar wajen nan haka? Ina Pareto?"
Kiki tasa lighter tana kukkunna candles din cake din, sannan ta kunna fitilar wajen haske mai
ni’ima ya wadata ya gauraye wajen. Kiki na dariya tana clapping hannayenta. Ta soma wakar.
“Happy birthday Uncle AK!”.
Sai lokacin duk suka fahimci me take nufi. Da abinda ta shirya. Wato sai lokacin ma Hamma
ya tuna yaune zagayowar ranar haihuwarsa shekaru 43 a duniya.
Excitement dinsa ya kasa boyuwa, domin ko ba komai Kiki ta bashi babban surprise din da
ya sashi dariya, diyar nan tashi Ruqayyat tana matukar kaunarshi, ko bai haifi da ba a duniya ya
godewaTaiwo data haifa masa Kiki.
Kiki tana kula tana kuma sane da komai nasa, don shi ya manta ma.
Duk da ba wai yana celebrating ranar haihuwarsa bane a baya a kowacce shekara, amma
idan ranar ta zagayo, Nenne da Dade su kan kirashi suyi masa fatan alkhairi da addu’a,
shikuma ya kan kara ninka sadaqarsa ga gidan marayu, a kowacce ranar birthday dinsa.
To yau wayarsa tana kashe, domin ya baiwa kwakwalwarsa hutu.
Ta cikin hasken candle lit din ya juya yana duban Aisha dake gefensa, sai ya ga ta koma

masa tamkar furen fulawa don kyau. Kamar an kara wanketa an canza mata launin fata,
sakamakon wannan sassanyar kwalliya mai tsari da Kiki tayi mata, serene make-up din ya
amsheta sosai. At long last! Yau shi Abdulrasheed ya cika shekaru arba’in da uku tare da matar
aure by his side (a gefensa). Auren da bai taba zaton yiwuwarsa gareshi a gidan duniya ba. Tabbas aure lokaci ne dashi
ga kowanne dan adam, komin tsarin daka yi masa, idan lokacinsa ya zo daga Allah ko mutum
yanaso ko baya so zai tabba dashi.
Prince ya sakarwa Aisha kyakkyawan murmushinsa, wanda bai san lokacin da ya subuto
masa daga zuciya zuwa fatar bakinsa ba, ganin itama kallon shi take yi yau da dukkan
admiration na mace ga miji cikin idanunta.
Ta kasa ce masa “happy birthday” din ita sabida kunya, amma a cikin zuciyarta ta fada ta
kuma maimaita, har ta kara da cewa,
“Allah ya karawa rayuwarka albarka the Great Prince of the Ilorin Emirate”.
Kiki ta hau hure candles din dake bisa kan cake tana cewa.
“Bari toh in huresu, a madadinka Uncle!”.
Ta hure candles din duka. Tace sai Uncle AK ya yanka cake dinnan nasa da kansa.
Nan ma dai Hamma dariya ce ta kama shi, da girmansa gemai-gemai za’a ce ya yanka cake!
Yace Aisha ta yanka a madadinsa.
“Lets the wife represents the husband”.
Kunya ce sosai ta kama Aisha irin wadda bata taba ji ta Hamma Prince ba, a yau da ya
dangantata da matarsa.
A karshe sai Aisha da Kiki ne suka hada hannu suka yanka cake din tare. Aisha ta zaftaro
katoto tayi bakin Kiki dashi, sai Kiki tayi kwana da hannun Aisha zuwa bakin Hamma
Abdulrasheed (Prince).
Ta kuma yi maza ta daukesu hoto. Aisha tayi dumu-dumu da bakin Hamma da cake. Daga
Aisha har Prince kunya ce ta kamasu da wannan hoton da Kiki ta dauka don idonsa yana kan
Aisha, babu irin wannan shaquwa da sakewar a tsakaninsu kafin zuwan Kiki. Don haka Kiki ta
zama rahma ga auren ma’auratan nan. Kiki ta cigaba da waka a wurin tana musu hotuna tana wakar.
“Happy Birthday Uncle Abdulrasheed Kehinde!”.
Daga nan ta bubbude foil paper da aka rurrufe abincin dashi, ta zauna itama tana fuskantarsu
suka soma cin dinner din tare.
Suna ci suna hira gwani ban sha’awa, Kiki nata basu dariya da hirarrakinta na wauta, suna
gamawa Prince ya kunna wayarsa ya zagayo hannunsa ta gaban Siddiqah, yace da Aisha,
“dan matso nan Siddiqah muyi selfie nida ke, cikin wayata saboda tarihi!”.
Ba karamar kunya ce ta lullube Aisha ba, lokacin da Hamma ya kashe kyawawan fuskokinsu
shi da Aisha da flash din dalleliyar camarar wayarsa
Idan da Kiki zata yi duba da duk abubuwan da ke faruwa yau, da wadanda suka faru tun
zuwanta, sai ta godewa Allah, domin kuwa ta samu ladan wadannan ma’auratan. Zuwanta yayi
riba.
Tayi silar abubuwa na farin ciki da yawa a gare su, da cigaba cikin irin zaman da ta tarar suna
yi. Don kafin zuwanta wani irin zama suke yi kamar na ‘jahiliyya period’.
Don yafi gaban a kira shi na doya da manja don baza’a kira shi zaman aure ba. don kuwa

alhakin juna suke dauka. Zuwan Kiki ya haska gidan. Ya hurawa zukatan ma’auratan ruhi. Sai
mu ce madallah da Kiki-Ruqayyat, madallah da zuwanta gidan a wannan lokacin.
Kiki zamewa tayi ta bar su a wurin da cewa zata je ta dawo. Ganin Prince duk hankalinsa na
kan Aisha. Yau Prince da Aisha ne zaune dab da juna, har ya samu kansa da janta da hira.
“Siddiqah bani labarinki mana? Tunda kikazo kin kunshe min baki, bansan kina walwala haka
ba sai bayan kawarki tazo ko?”
Aisha ta sunkuyar da kai tana wasa da siraran ‘yan yatsunta tace “Uncle me kake son sani a
kaina?” A takaice Prince ya ce da ita.
“Komai!
Tun daga labarin iyayenki, ‘yan gidanku, samarinki, kawayenki da makarantar ku.
Yadda kika tsinci kanki a auren Bayerabe alhalin kina bafullatana mai kin yarbawa da
sauransu.
Kin ga ni na tabbata kinsan komai a kaina a gidanmu, amma ni har yau bansan da wa nake
zaune ba, banda cewa ina tare da matar aure na kawai”.
Aisha ta rufe fuska da zara-zaran yatsunta tana cewa cikin murmushi.
“Hamma Abdul, banida labari ne ni, gidan mu ba kanne ba yayye, nikadai ce ‘ya a gidanmu.
Nice yar kaina nice kanwar kaina.
Samari kuma bana sauraron kowa sai Ishaq Nafada.
Kawayena na makaranta kuwa sunada yawa, babbar aminiyata a cikinsu Amintako ce, sai
Ramatu da Ruma, don ni dinnan da kake ganina shiru-shiru a gidan ka ‘gang leader’ ce dake
shugabantar fitinannun yara a makaranta.
Sunan makarantarmu FGC Billiri Gombe.
Yadda nayi na samu kaina da auren bayeraben miji bazan iya cewa ba, illah ince wata addu’a
ce ta Ummanka ta filin Arfah, ta fado a kaina ni Siddiqah, kamar yadda Ummata ta bani labari
nima”.
Prince ya soma dariya kamar bashi ba, bai zaci Aisha haka take da baki ba, yace “wato
Nenne addu’a tayi akaina, sai ta fado a kanki ko Aishahh?”
Ta sake rufe fuska tana dariya ta ce “exactly, sosai kuwa, wata irin zazzafar addu’a tayi a inda
Allah baya juyarda addu’a, don Ummana ta ce da ta ji Nenne tana addu’ar nan a lokacin, a take
a zuciyarta tace inama zata ganshi ko waye shi ta bashi PETEL dinta!
Sai Allah yayi ta tsara abubuwan daki-daki yadda ya ga dama, suka yi ta faruwa
subsequently (wani na bin wani).
A rayuwata ban taba jin wani abu mai kyau game da kabilar Yarbawa ba, sai bayan da Nenne
ta dauke ni zuwa gidanku a birnin Ikko.
A nan ne Yarbawa iri-iri suka goge min hadda, tun daga kan ma’aikata da masu girkin gidan,
na fahimci cewa Yoruba kabila ce mai matukar daraja a Nigeria, kamar Hausa/Fulani.
Dana zo Argentina na tadda Prince of the Ilorin Emirate, sai ya karasa wanke duk wata
negative hadda dake cikin kaina akan Yarbawa, don na gane cewa Prince din Bayerabene na
gaske, mai alfahari da kabilarsa. Da bakinsa ma ya fada min; he’s a proud Yoruba man.
Don haka ni yanzu duk inda naga Yarbawa tsakanina dasu girmamawa ce da karya hula,
sanadin kaunata dasu”.
Prince ya lumshe ido cikin murmushi, kowacce kalma dake fita daga bakianaata tana masa
dadi, ya budesu a kanta yana cewa.

“Aisha frank kenan! Naji wannan, na kuma taya yarbawa bakidayansu murna da kika cire
musu kabilanci daga dictionary dinki.
Bayan wannan zan so in san wane irin so kike yiwa Ishaq? Ina nufin yaya kike jinsa a ranki
kafin auren ki da Bayerabe da yanzu bayan auren?”
Aisha ta hau ‘yar dariya tana cewa.
“Uncle me yasa ka tambayeni wannan? Babu kyau binciken abinda yaa riga ya wuce”.
Kai tsaye Hamma ya saka idonsa cikin na Aisha ya dan budesu cikin nata. yace “because I
am extremely jealous of him!”.
Aisha ta sunkuyar da kai tana jin wani irin dadi a zuciyarta, amma tana so ta baiwa Prince
wannan amsar koda zai ji babu dadi. Ba don ta goge kishin da yace yana yi akan Ishaq ba, sai
don ita ‘yar keke da keke ce tun asalinta, bata da rufa-rufa (frank).
“Ina son shi sabida he is caring. Kullum muke tare sai ya gaya min how much he cares and
loves me. Baya gajiya da gayamin muhimmancina cikin rayuwarsa duk da kankantar
shekaruna.
Na taso na san shi a matsayin fiancé dina shikadai na saba da shi na kuma shaku da shi.
Rana daya aka ce an bada ni ga waninsa kuma Bayerabe da ban ko taba gani ba.
Ka gayamin in kaine ni yaya zaka yi? Ai dole ka yi dan protest ko? Musamman daka gane
cewa shi wannan da aka mallakaka gareshi din bai ma san da kai ba, bai damu da kai ba, bai
san kana existing ba, kuma baka cikin lissafinsa a rayuwa”.
Hawaye suka digo mata tace “it’s not easy, ina gaya maka Hamma, it’s not easy, don ma na
roki Allah juriyane, da danganar karbar rayuwa a duk yadda ta riske ni”.
Amma bayan nan ina dadewa ban tuna Ishaq ba, na yarda “he is my past, I don’t have a
present”.
Ba don komai nace haka ba Uncle sai don kasancewar Uncle AK da aka aurar dani gareshi
rana daya bana cikin lissafinsa.
Ya karbeni a gidansa ne kawai kan ba yadda zaiyi da umarnin mahaifinsa”.
Hamma yace cikin karfafawa.
“Prince Abdulrasheed yanada past mara dadi akan mata, kin zo rayuwarsa a lokacin da ya
tsani mata, bashi da sauran hope akansu. Amma duk da haka Prince zai yi kokari ya komar da
hannun agogo baya, wato ya yi kokarin manta past dinsa, ya karbeki a gidansa da rayuwarsa a
matsayin present dinsa, don radin kansa ba don tursasawar iyayensa ba, hakan zai faru ne only
ranar da kika daina yi masa kallon BABANKI!”
Da sauri Aisha ta rufe ido da tafukanta cikin jin kunya daidai lokacin da Kiki ke tahowa
garesu. Tana karasowa tace “Uncle AK zan dauki Uwata haka, lokacin barcinmu yayi, in ya so
ka kawo kayan zance sai in barka zuwa tadi!”
Hamma ya zaro ido yace “Kiki, kina maida ni Kakanki koh? Zan yi maganinki aure zan yi miki
soon”.
Koda suka koma cikin sitting room Aisha da Kiki kallo suka kunna a falon, suna kallon
girke-girke a

12 / 16