Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
hankali a falon.
A kujerar dake fuskantar shi Dacta da Mami suka zauna. Dacta ya dubi Mami ya ce,
“Rayhanah ta karya ne?”
Ta ce, “Anya? Bari in dubo ta”. Ta mike.
Da ta shiga dakin gani ta yi kamar ba kowa, can ta jiyo shesshekar kukanta can a kusurwar
gadon Jawahir.
Ta shiga ta tsugunna a gabanta ta kama hannunta ta ce, “Kuka Rayhanah? Me aka yi miki?”
Ta jata jikinta a hankali tana lallashinta. Dacta ma aje cokali ya yi ya nufo dakin don ya ga
Mamin ta jima.
Shima durkuso ya yi a gabanta ya ce, “Mene ne Rayha? Me ya same ki?”
Cikin kuka ta ce, “Iya za ni”.
Ya ce, “Daina kuka Rayhanah, addu’a za ki dinga yiwa Iya a duk lokacin da kika tunata.
Wanda ya riga ya mutu baya dawowa, sannan baya son kuka, addu’a yake bida.
Rayhanah kowa da kika gani yana yawo a doron kasa, wata rana za a wayi gari babu shi.
Har mu din kuwa. Ba Iya kadai ba, duk jiran wa’adinmu muke. Duk sanda kika yi sallah ki
karanta suratul Ikhlas kafa uku ki ce Allah ya kai mata ya fi ki dinga yi mata kuka. Addu’a take
so kin ji”. Ta daga kai. Ya ce, “Good! To taso muje ki ci abinci”.
Ya kamo hannunta har dining. Ai kuwa Ibraheem ya aje cokalinsa ya mike, don ba zai iya cin
abinci tana wajen ba. She is ugly at all (mummuna ce), ga ciwuka ga dafaffiyar fatar kauye.
Wannan abun haushi na Daddy da me ya yi kama?
Mami dake hadawa Rayhanah tea ta cira ido ta dube shi ta ce, “Ya ka tashi? Ka koshi ne?”
Tuni Daddy ya karance shi. Ya dauke fuska don baya son ganin ma inda yarinyar take kada
ya yi amai, ya wuce yana cewa “Eh, Mami”.
Ta turawa Rahane kofin shayin, ta zuba plantain da dankali ta tura mata “Ci maza ki sha
magani”.
Ta karba, amma sai ta dauko filet din da kofin ta zauna a kan marbles ta fara cin abinta.
Duk suka yi mata dariya, kuma basu ce da ita ta tashi ba. A wurin Rahane su suna kan kujera
ita ma ta hau kujera, ai ya zama rashin kunya.
Da suka kammala Dacta ya bai wa Mami ‘master card’ dinsa na (First Bank) ya ce ko nawa
ne ta cira ta sayawa Rahane sittiru da sauran kayan bukata.
Ta ce, “Ni wannan kan ma na fi damuwa da a wanke. Ba zai rasa dandruff da lices ba
(amosani da kwarkwata). Dubi yadda take ta sosa shi”.
Haka tasa Rahane a gaba suka tafi saloon din, ita ke jan motar. Ai kuwa kwarkwata ba a
magana. Haka ta yi ta biyo kumfar magani na musamman ana fidda ita.
Sai da suka tabbatar babu ko daya sannan suka gyara mata gashin. Ba ta da wata suma mai
yawa, sumarta ba ta fi a kama a ribbon ba, mai karfi sosai ta asalin Kanawa.
Daga nan shagon (Well-Care) ta shiga ta yi mata sayayyar kayan sanyawa masu kyau da
tsada. Dogayen riguna ne sai siket da riga, atamfa da les kuma ta ba da dinki a (Diallo) inda ake
wa su Abida.
Basu shigo gida ba sai bayan azahar. Tuni su Abida sun dawo har sunyi wanka, sai yanzu
Rahane ta ga wanda yake kawo abinci ya aza a tebir. Wani kabila ne sanye da Apron fes da shi
kamar ma’aikaci. Ta ji Azizah na ce masa Yohan.
Da gudu Jawahir ta rungumota ta zame dan kwalinta ta ce, “Rayha kin yi kyau, yau tunda na
je makaranta nake tunaninki. Don Allah Mami a kai Rayha makarantarmu”.
Mami ta ce, “Ku wuce ku ci abinci ko sai Malam Umar ya zo yana jiranku?”
Jawahir ta makale hannun Rahane suka zauna tare, ta ce, “In ce ko kin cire ‘Aid’ din sanda
za a yi wankin kan?”
Ta ce, “Eh, na cire”.
Abida sai cin magani take, ta yi tsaki ta debi abin da za ta iya ci ta yi daki, don ba za ta iya cin
abinci gaban wannan kazamar yarinyar ba. Azizah cinyar Rahane ta dare tana ta Alifun Ba’un
da A,B.C,D tana da son mutane.
Haushi bai kashe Abida ba sai da ta ga an karo musu gado, wato na Rahane ne. Ta zauna
tana ta huci, da ta tuna kashedin babanta kuma sai ta fashe da kuka, don ta lura ba yadda za ta
yi, kuma da gaske tare Daddy ke nufin suyi rayuwa.
Karfe hudu dai-dai Malam Umar ya zo. Yana koyar dasu kira’a ne da Tajweed, sannan suyi
lesson a boko. Idan yana kwararo kira’a sai ka ce Ahmad Sulyman, haka idan yana baiwa
kowanne harafin Alkur’ani hukuncinsa, kamar marigayi (Malam Datti Ahmad Galadanci) Allah ya
yi masa rahama. Rahane na zaune gefe tana sauraron wannan malami, ta ce a ranta ashe mu a Allo shirme
muke yi. Ya ja aya ya kuma nuna Abida da ya lura hankalinta baya tare da ita tana ta sokawa
Rahane tsinke, ya ce, “Abida, wane hukunci ne da wannan ta’areef?’
Ta zabura ta ce, “Eye? Na’am?”
Ya sake maimaitawa. Ta yi tsit! Ya kuwa daddage ya tsula mata dorinar dake hannunsa,
bulalar ta shigeta sosai, ta zabura ta sa kuka.
Ya ce, “Ko ki rufe min baki ko in kara shauda miki”.
Ta toshe bakin da karfi tana kuka.
Ya ce, “Tun dazu ina lura dake babu karatun da kike sai tsokana, ko tausayin yarinyar nan ba
kya ji. Dubi raunin dake jikinta amma kike son huda mata jiki”.
Da mamaki Jawahir ta dubi Abida, don da hankalinta baya kansu. Ya ci gaba da cewa, “To
zan gayawa Dacta, don ke na lura fitinanniya ce”.
Tana kuka ta ce, “Don Allah Malam ka yi hakuri kada ka fadawa Daddy na daina”.
Ya ce, “To kin yi na karshe”.
Da haka karatun ya tashi.
[12/24/2019, 17:56] Takori: A rayuwar Ibraheem, bai taba damuwa da wani abu bayan
iyayensa da karatunsa ba kamar RAYHANAH! Kankanuwar yarinyar da ko kirgar dangi bata
fara ba, bata kuma da wani abu attractive da zai dau hankalin namiji ta fannin sura.......bai
yarda da kansa ba, don haka ya dauki duk wani motsin da zuciyarsa da gangar jikinsa ke yi a
kanta da KARYA........! Jawahir ta Khalipha su suka taimakawa Rayha ta wanke kashin da Abida ta yaba mata,
sannan ta yi wanka ta koma ta kudundune a bargonta ba ta ce komai ba. Sai ajiyar rai take.
Khalipha ya dora hannunsa a kan goshinta, zafi rau! Ya ce, “Tun yaushe kika fara ciwon kai
Rayha?’
A sanyaye ta ce, “Tun jiya”.
Ya umarci Jawahir ta kawo ruwa da panadol. Ya ba ta da kansa ta koma ta kwanta.
Abida na gefe tana ta kuka domin ta daku a hannun Khalipha ba kadan ba. Sai dai ko kadan
hakan bai sa zuciyarta ta russuna ba daga kiyayyar da take yiwa Rayha. Zuciyarta ce ma ta
kara tauri da kangarewa, don yarda da ta kara yi Rahane ta zame mata karfen-kafa.
Daddy ya daina shiri da ita saboda ita, yau ga Yaya Khalipha dan’uwanta da ba ta hada
soyayyarshi da ta kowa a zuciyarta ya yi mata dukan kawo wuka a kan RAYHANAH!
Khalipha ya dago idonshi jajir da bacin ran da har zuwa lokacin bai ji ya ragu ba, duk da
dukan da ya yiwa Abida.
Ya dube ta sosai tana ta kuka ya ce, “I’m warning you Abidah.... don’t repeat it! Don’t repeat
it!! Don’t repeat it!!!”
Ta ce, “To Yaya Khalipha”. Ya mike ya fita ya ja musu kofar.
****
A yau duk gidan shiri suke yi domin halartar bikin kammala karatun su Ibrahim, karshen kure
adaka ‘ya’yan Dr. Mansur sunyi. Duka sanye suke cikin English wears kowanne da design din
sa, sunyi kyau kwarai. Aziza samfurin ‘george’ Abida da Rayha ‘Mclaren’, Jawahid kuma H&M
ne duka riguna da wando domin zama da madaukin kanwa yau da gobe tilas ya koyar da
Rahane saka wando. Don su a wurin su (casual wear) ne da babu inda bazasu iya shiga dashi
ba. Dr. Mansur baya hana su shida kansa in ya fita waje yake sayo musu saidai ya kudure ya
kusan dakatar da hakan da zarar sun shiga sakandire.
Kalar kayan kowanne daban, amma duka babu wadda ba yi kyau ba kamar ka lashe. Kai ka
ce irin yaran nan ne dake rayuwa a Honolulu.
Rahane ta kara da farin hijabi, wanda ya sauka a kan kafadunta. A zahiri duka su Abida sun
fita kyau, sun fita haske. Amma idan ka dubi Rahane a wannan lokacin sai ka kara marmarin
maimaitawa, saboda kalar fatar jikinta baka mai duhu amma mai sulbi kamar Somali, da dirin
jikinta da ya soma bayyana da wata irin kamala da nutsuwa hadi da kwarijini bayyananne daga
indallahi.
Taron, wanda aka gudanar a dakin taron (Musa Abdullahi Auditorium) dake cikin sabuwar
Jami’ar Bayero, ya samu halartar kusoshin ilimi na Najeriya da shuwagabanni, malamai da
sarakuna. Farfesoshi da Dactoci, har da mataimakin shugaban kasa.
A jawabin mai girma V.C Proffesor Attahiru Jega, ya ce yau shekaru ashirin kenan da jami’ar
ta ba da shaidar MBBS mai daraja ta daya, daga nan ba ta kara samu ba sai yau a kan Dr.
Ibraheem Mansur Takai. Don haka ‘chevening scholarship’ dake tallafawa hazikan ‘graduates’
na kasashe masu tasowa dake karkashin majalisar Turai ta bashi zabin duk kasar da yake so
ya yi specializing a duk fannin da ya zaba. V.Cn ya kare bayanin sa da cewa “Dr. Ibraheem
congratulations!”
Ya fada tare da mika masa hannu suka gaisa, sannan ya mika masa kwalinsa, ya karkata
masa hularsa. Sannan ya dafa kafadunsa yana girgizawa.
Sai da Nabila ta san yadda ta yi ta kutsa cikin jama’a tana daukar I.M da V.C hoto duk motsin
da sukayi, daga karsh Baba Dacta ya rungumo suka jero tare suna sakkowa daga kan steps din
zuwa wajen Mami, wadda ke tsaye harde da hannuwa a kirji, fuskarta ta kasa rabo da
kayataccen murmushin dake tattausan bakinta. Itama ta rungume shi Nabilan na ta daukar su
hoto.
Kwana biyu da taron Baba Dacta ya shiryawa I.M walima a nan reception din gidan. ‘yan’uwa
ne na jiki, abokan arziki da abokan aiki na Baba Dacta da Mami, dangin Mami daga Jos,
abokan Ibraheem da na Nabila, hatta Hakimin Takai ya zo da iyalansa.
Don haka Dacta ya kama musu daki a Tahir. Don duk girman gidan nan cika ya yi da
‘yan’uwa da abokan arziki.
Addu’o’i aka fara yi, sannan daya daga cikin malaman Ibraheem (Consultant Dr. Bello Sajoh)
ya ba da tarihin Ya Himu, hazakarsa da determinations dinsa kan karatunsa.
Sannan ya ja hankalin iyaye kan su karfafi ‘ya’yansu da karatu a fannin kiwon lafiya don
taimakon kasarmu da al’ummar mu. Ba wai bamu da masu hazaka bane a Arewa kamar ‘ya’yan
Kudu da sauran kasashen da suka ci gaba, a’a, determination wato (kuduri) yaran Kudu dana
sauran kasashen da suka cigaba suka fi namu da jajircewa kan goal attainment, sai kuma
ZUCIYA.
Ya ce,
“har yanzu Najeriya tana sahun underdeveloped societis, bai yarda da cewa tana shaun
developing ba, saboda rashin zuciya da lalaci irin namu, muyi ta diban miliyoyinmu muna kai wa
Turawa don suyi mana magani muna kara bunkasa su alhalin ba a fimu da komai ba.
Maimakon masu kudinmu da shuwagabanninmu su yi amfani da miliyoyin wajen gyara
asibitocinmu da kawo magunguna masu inganci da kayan aiki ko da a matsayin sadakatul jariya
ne. A’a, sai suke kaiwa Turawa suna karawa mai karfi-karfi, kasarmu kuwa da marasa hali ko
oho! Ka je asibitin gwamnati irin su Murtala da asibitocin koyarwar mu ka ga yadda ake wulakanta
talaka da masu haihuwa. Lafiya ita ce gaba da komai, karatun kiwon lafiya bai yi tsamarin da
al’umma ke duban shi da shi ba, nutsuwa kawai yake bukata da jajircewa.
Masu hazakarmu sun tattare a (Social Science) maimakon (Physical Science) da Arewa ke
bukata, ba don rashin kwakwalwa ba sai tsoro da muka sawa zuciyarmu a kan ilimin. Don haka
ne ‘yan Kudu suka fi mu ci gaba a fannin, suka fi yawa a kasashen ketare domin neman ilimin
Kimiyya. Dr. Bello ya ci gaba da cewa,
“a yanzu sabuwar gwamnatin da muke ciki ta yi alkawura na daukar nauyin daliban Arewa a
fannin kiwon lafiya, amma fa sai da hadin kan iyaye. Dutyn sune su ba wa ‘ya’yansu maza da
mata kwarin gwiwa a kan ilimin kimiyya, musamman mata a kan (Gynaecology) wanda yake
halastacce a addininmu.
Ya ba da misali da Ya Himu, kwata-kwata shekarunsa ashirin da bakwai amma saboda
samun kulawa da iyaye tsayayyu a kan al’amarinshi da kwarin gwiwar da ya sanyawa ransa da
zuciya yau ga shi a cikakken likita (General Practioner) da zai iya duba kowacce irin cuta ta
yara ko ta manya ya yi (prescribing) ya fadi maganinta, da yadda za ayi a kauce mata da kuma
yadda za a shawo kanta in ta yi qamari. Me ya fi wannan amfani ga al’umma? Me ya fi wannan
zama abin alfahari a zuciyar iyaye?”
Jama’ar sun ji dadin tunasarwar Dr. Bello, iyaye da yawa sun dauki shawararsa. Ba irin cimar
da ba a ci ba.
Ibraheem ya samu kyaututtuka na alfarma. Hakimi mukullin dalleliyar mota ne. Su su Rahane
yawo kawai suke cikin mutane ita ba ta ma san taron me ake yi ba sai da Jawahir ta gaya mata.
Yaya Khalipha ya tafi jihar Sokoto inda aka tura shi bautar kasa. Mami na zaune a falo tana
waya da Khalipha, Himu ya fito cikin shiri da alama fita zai yi.
Ta yi mishi alamar ya dakata ta karasa magana da Khalipha. Ta gama ta ajiye sannan ta
dube shi ta ce, “Ya za ka fita ba ka karya ba?’
Ya yi dan tsaki ya ce, “Ban jin cin abincin yanzu, heart burn ke damuna”.
Ta mike ta isa ga table ta hada mishi shayi mai kauri tana firfitawa ta ce, “Atleast ka sha
wannan, rashin cin abincinka ya fara damuna Ibrahim.
Wai me ke damun ka ne? Na lura tunda aka yi maganar auren nan duk ka bi ka rasa kuzari.
Nabilan ce ba ka so ko ya ya ne? Idan ka san ba sonta kake ba don me za ka bata mata lokaci
har zuwa yanzu kana yi mata yawo da hankali?
Yarinyar nan ta ki kowa sai kai, iyakar soyayya ta gaskiya ta nuna maka, ba ta cancanci rana
daya ka juya mata baya ba”.
Ta dauko GESTID tana girgizawa, shi kuma ya soma kurbar tean a tsaye. Sai da ya shanye
ta zuba gestid din a cokali ta ba shi da hannun ta cikin bakin sa. Fuskarsa da zuciyarsa cike da
jin dadin kauna da kulawar da uwarsu ke musu, kamar wasu kananan yara.
Ita kwata-kwata bata ganin girman su, kullum yadda take treating su Jawahid haka take
treating dinsu, wani zubin har sai Dr. Mansur ya ankarar da ita. Ya ce, “Mami nifa ba yanzu zan
yi aure ba, don haka ki ajiye zancen Nabila aside. In ta samu miji ku rufawa kanku asiri ku aurar
da ita. Ba zan taba auren macen da ta fara cewa tana sona ba!”. Baki Mami ta saki, ta ce, “Mai sonka kuwa ai shine masoyinka. Bakin da ya furta SO, baya
dawowa ya furta kiyayya”.
Murmushi ya yi, ya sumbaci goshinta ya yi gaba.
“Sai na dawo Mami ba nisa zan yi ba”.
Ta ce, “Nima rainin hankalin za ka yi mini Himu?”
Birki ya ja, sannan ya juyo. Cikin damuwa ya ce, “Mami ya ya za ayi na raina miki hankali?
Cewa nake ra’ayin da ke zuciyata kika tambaye ni? Na gaya miki gaskiyar abin da zuciyata ta
yarda da shi. Bayan wannan ma ba zan yi auren zumunci ba Mami”.
Ta ce, “Hujjah?”
Ya ce, (cikin bude ido kadan) “Hujjoji barkatai”.
“Kamar wanne da wanne?”