Rayuwar Raihana Part 1 chapter A Complete Hausa Novels.pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 12

30K to 33K   out of 33K words

kake shaye-shaye ban sani ba? Me ya kawo ni ganin wannan bakin cikin? Me ya
kawo ni, ni Asma’u???”
Sai ta mike za ta fice idanunta jage-jage da hawaye. Da hanzarin gaske ya cimmata ya
rungume kafafunta.
“Wallahi Mami ki yarda dani, ban taba shan abin da zai fitar dani daga hankalina ba. Mami
damuwa ce bana cikin sukunin da zan iya sarrafa kaina. Ina sha ne kurum don ta rage min
damuwa. Marlboro ce kawai, wallahi Mami idan na taba shan wani abu bayan ita, Allah ya yi
miki sakayya a kan tarbiyyar da kika bani”. Ta tsaya da kukan, ta shiga nazarin falon baki dayansa cikin bakin-ciki marar misali, ta ce,
“Mene ne haka? Me zan gani haka? Kazami kuma ka koma? Me kake yi yau a gida ranar aiki
baka je office ba?”
Bai bata amsa ba, don bai san me zai ce mata ba.
Ta girgiza kai ta ce “ai Shi kenan, ni zan tafi, dama na zo in duba lafiyarka ne. Don na san
haka kawai ba za ka ki gaishemu ba. To na gani lafiyarka kalau bamu isa bane kawai mu ji
damuwar taka ka gwammace ka lalata rayuwarka”.
Da hanzari ta fita, bata barshi ya yi wani furuci ba. Kayan dake jikinsa kuwa ba za su barshi
ya bita ba. Ko hutawa bata yi ba, ko ruwa ba ta sha ba ta dauko hanyar Kano.
Allah ne kawai ya kawo Mami gida, amma ba nutsuwar zuciya ba. Wai Dan da ta haifa ne
yake shan taba bata taba sani ba. Ko tun tsahon yaushe yake sha?
Duk tsantseninta a kan ‘ya’yanta, duk jansu da take a jikinta don su zama abokan rayuwarta,
a yau Khalipha ya nuna mata aikin banza take, ya nuna mata yana da wata damuwar da ba ta
isa ya gaya mata ba, ya gwammace ya mutu a cikinta.
Da asubahin ranar ta ji Malam Dahiru ya bude get, ta daga labulen dakinta tana kallon
shigowar motarshi, wannan ya tabbatar mata tafiyar dare yayo, sai ta ji tausayi ya tsirga a
zuciyarta.
Har ya fito daga motar ya rufe ya ratayo bakar jakarshi ya shigo reception tana kallon shi. Ta
koma bakin gadonta ta zauna, ko minti biyu ba ta yi da zama ba ta tsinkayi sassanyar sallamar
sa a kofar dakinta. Babu kuzari sam a jikinta ta ce,

“Yes, come in”.
A yadda ya shigo din cikin kayan da ta baro shi ne, bakar rigar sanyi kawai ya dora a kai
wadda ta iso har gwiwarsa, bakin glass da bakin cover takalmi.
Sai ta nuna mishi toilet dinta, tana daga zaune “Go take a wudu’ (alwala), a brush, a shave
and a shower, then come to me….”. (Shiga ka yi wanka, ka yi brush, ka yi alwala, ka yi aski
sannan ka zo gareni).
Maimakon ya shiga nata toilet din sai ya juya nashi dakin ya bi umarninta.

Ya idar da sallah ya yi addu’o’i masu yawa, yana rokon Allah yasa Mami ta fahimci ba shi ya
dorawa kanshi damuwar ba, Allah ne ya dora mishi.
Sannan ba shi da karfin zuciyar da zai sarrafata ko ya boyeta. Su kuma ba za su iya yi masa
maganinta a wannan lokacin ba. Don haka ba zai iya fada mata ba, don fadar bazata yi wani
amfani ba.
Mami ta ji shiru-shiru Khalipha bai fito ba. Ta kasa hakuri ta biyo bayanshi har dakin nasu.
A lokacin shi yana shirya abin da zai gaya mata ne don ba zai iya gaya mata gaskiya yanzu
ba. Ya san Mami da boko kamar Ibraheem, cewa za suyi Rayhanah ba ta isa aure ba ko su
kushe zabin nasa. Ko suce ‘child abuse’.
Don haka tuni ya tattara abin da zai gaya mata. Dai-dai lokacin da ta zauna gefen ‘sofa’
dinsa. Ya shafa addu’a ya ce, “Mami kin zo lafiya?” Ta ce, “Da ban zo lafiyar ba za ka ganni ne
har dakinka da kafafuna eyi?”
Ya yi murmushi, “Mami kin tayar min da hankali Allah, da baki tsaya kin ji uzirina ba balle
damuwar dake damun nawa. Mami in kika yi fushi dani ina zan sa raina? Jahannama fa Mami,
babu ni babu jin kamshin Aljannah. Mami don Allah kar ki kara yin fushi dani, kin ji Mami?”
Jikinta ya yi sanyi kalau, ta ce, “Mene ne ke damun naka?”
Ya ce, “Mami SOYAYYAH!”
Sai ta yi murmushi ta ce, “Alhakin Hibba ne, wace mai tsautsayin ce again?”
Ya ce, “Mami ban sameta ba, an kasa ni”.
Ta kara yin murmushin ta ce, “Ba ita kadai ce diya mace a duniya ba, Allah yasa hakan ya
zama mafi alkhairi. Wani zubin in Allah ya tsara abu, sai ka ga na gaban ya fiye maka amfani. Ni
tuni ai na yi maka mata Khalipha, jira nake ka zamo settled tukunna kafin in gabatar maka da
zancen”. Cikin Halifa ya karta ya bala’in kadawa. Da sauri ya ce, “Um-um Mami, bar zuciya da abin da
take so. Har yau din dai da nake gaya miki ban fidda rai da samunta ba. Wani sanadi zai iya
zuwa idan har matata ce Allah ya bani in aureta. Tunda an ce matar mutum kabarinsa”.
“Ya ya sunanta? A ina take Dattijo? Su waye iyayenta?”
Ya ce, “Mami tunda a yanzun bani da damar aurenta sanin wadannan amsoshin ba zai
amfaneki da komai ba”.
Cikin rashin damuwa da lamarin ta mike tana fadin, “Toh! Allah ya maganta maka, ni na
dauka wani muhimmin al’amari ne, zancen Radhiyyah kuwa na baka sati har biyu ka yi tunani a
kai”.
A cunkushe da zancen ya ce, “Radhiyyah kuma? Gaskiya Mami bana son ki sa ranki ga abin
da ba zai yiwu ba. Matakin iliminta ya wuce wanda nake so a macen da zan aura kafin in aure
ta. Nafison duk wani ilmi da mace zata yi bayan sakandire tayi shi a gida na. Kuma da kadan na

girmeta, in zan iya tunawa shekara uku na bata.
Haba Mami, ai an dena irin wannan hadin auren yanzu a kauye ma ba a birni ba, gaskiya ta
min tsufa.
A perception dinki ban zaci akwai irin wannan tunanin ba, na abubuwan da aka yi a can wani
karni can da ya shude. Na soyayyar ma yaya aka kare da shi balle na hadi?
Ki barni kawai in na samu wadda za ta maye min gurbinta da kaina zan gaya miki. Amma don
Allah Mami kada ki kara daga maganar nan, kada zumuncin da ke tsakaninku da Mamanta ya
lalace a kan abin da ba zai yiwu ba”.
Cikin mamaki Mami ta ce, “Ni kake cewa haka Dattijo?”
Da sauri ya gyara kuskurensa da cewa, “Ba nufina baki da iko a kai bane Mami, kawai ina
gaya miki abin da zuciyata ke gaya min a kan maganar. Ki yi hakuri idan kalamaina sun bata
miki rai, I’m sorry Mamee! Ki yi hakuri don Allah”.
Ta yi ajiyar zuciya sannan ta fita. Allah kadai ya san abin da take sakawa da warwarewa a
zuciyar nan tata. Mami na son ‘ya’yanta matuka, tana kishinsu irin kishin nan mara amfani,
wanda ya kimsa mata tunanin cewa da akidar cewa ba za ta bari su auri wadanda suke
mutuwar so ba, sai wadanda ke son su, don kar su rabata da su. Irin ‘yan’uwansu su Hibbah, Nabila da Radhiyyah diyar aminiyarta Dacta Halima wadda ta ki
auren minister saboda mahaukaciyar soyayyar da take yiwa Khalipha.
Mami na da wannan kudurin cikin ranta tuni, wanda kuma take da yakinin ko za ta yi yawo
tsirara ne sai ta cika shi. Saboda masifar son da take wa ‘ya’yanta.

****


ASabar, biyar ga watan Yuli, rana ce ta ziyarar ‘yan makarantar kwana. Khalipha na tsaka da
aiki a Office kiran Mami ya shigo wayarsa. Ya dakatar da komai ya daga ya fara gaisheta.
A gurguje ta amsa tare da cewa, “An zabe ni zuwa karbar (Award of the best paediatrician of
Africa) a kasar Djbouti zamu tafi har Daddy gobe insha Allahu, so ba zamu samu zuwa ma yara
visiting Katsina ba, shine na ce ko za ka samu sararin lekasu can Katsina tunda ba ranar aiki ba
ce?” Khalipha ji ya yi kamar yana yawo a kan gajimare dan dadi. Ga dama ta samu ta ganin
Rayhanah wadda yau sati shida kenan bai dora ido a kanta ba, ba da tsimi ko dabararsa ba.
Domin dai Mami ba ta taba cewa yaje musu visiting ba, shi bama ya sanin yaushe ake yi sai
dai Mamin ta ba shi labarin cewa yara suna gaishe shi.
Amma sai ya dan danne farin cikinsa ya ce, “O,k, to ba matsala Mami zan yi kokari in gani ko
zan samu zuwan in b azan je gida ba, Congratulations Mami! Safe journey........”
Suna murmushi dukkansu suka aje wayar lokaci guda.
Aikin da ke gabansa kasa karasashi ya yi, ya hada komai ya rufe ya aje ya mike ya nufi gida.
Washe gari ranar ta kama Juma’a, bayan ya fito daga sallar Juma’a ya nufi Sahad ya soma
shopping. Ba kayan ci kadai ba, har da na amfani. Wani irin Shopping yake yi kamar ba sai ya yi
losing energy dinsa da lokacinsa ake ba shi kudin ba.
Sai dai kuma kayan abinci ne ya sayi komai na mutum uku, sauran kayan amfani kuwa sitturu
nena sanyawa a gida ko makaranta designers ‘yan gidan versace da channel hade da dogayen

riguna kala-kala da tafi amfani dasu.
Kayan shafa na Avon da coesmetics, deo-sprays duka ‘yan gidan Avon. Ya ma manta a
makaranta take. Shi kansa bai san adadin kudin da yake kashewa ba, burinsa kawai Rahane ta
koma irin yadda yake son ganin matarsa.
Filin makarantar ya cika ya batse da motoci da jama’a. Ba tun yau ba, tsarin Ulul-Abaab ke
burge Khalipha ba. Jama’a makil kowa nasa yake nema, sai manya-manyan coolers kawai ake
saukewa da katan-katan na kayan abinci da abin sha.
Lokacin da Khalipha ya iso karfe goma sha biyu dai-dai, tunanin Khalipha shine cikin wannan
bataliyar al’umma ina zai je ya nemo ‘yan kannen nashi?
Don haka ne kawai ya fito daga mota ya jingina jikin kofar direba ya harde hannayenshi a
kirji, don bai san ma wa zai tambaya ya nemo mishi su ba.
Sanye yake da shaddah getzner baka kar da bakar hula kalar shaddar dinkin Mohammed.
Khalipha fari ne sol mai wata irin fata jawur da ta fi kama da ta mutanen Hurghada (Middle
East). Hasken fatarshi ne kadai yasa ake danganta shi da Mami amma ba kamanni ba, domin
ya fita kyau nesa ba kusa ba, musamman kanannadaddiyar sumar kanshi. Haka yake kamar
ruwa biyu.
Kamar an ce da Khalipha juya, ya karyar da kai ya juya wani sashe daban. Rayhanah ce
zaune a gindin wata bishiyar lemon tsami mai karancin jama’a ta yi tagumi da hannuwanta biyu,
ko me take tunani? Allah masani.
Sanye take cikin uniform dinsu na daliban Ulul-Albaab da gajeren farin hijabi iya kafadunta. A
idanun Khalipha har tsayi da zati ta kara. Duk wasu alamu na cikar budurci sun bayyana a
jikinta. Kirar jiki dirarre wanda bai da alaka da kiba, cin kitse (cholestrol) ko over-eating duka
babu su a jikinta. Da ganinta ka ga rainon likitoci wadda ke cin komai moderately kuma cikin
tsarin balance diet na Bature.
Ya kai kallonshi ga fuskarta, kalarta choculate (wankan tarwada), fatarta fresh kamar ta yaran
goye. Ba ta da dogon karan hanci gashi nan dai dan matsakaici sai manyan idanu dake
lumshewa da kansu. Mai gazar-gazar din gashin gira dana ido bakake wul.
Rayhanah na da lebba masu dan kauri da sulbi kuma zagayayyu (kissable). Bayan wannan,
Rayhanah ba ta da wani mugun kyan da za a dorar.
Wannan ita ce irin matar da yake so, ya dade yana nema, yana lalube bai samu ba. Ashe
tana nan cikin gidansu. Duka wadannan nazarce-nazarce da ya yi, ya yi su ne cikin dan lokaci
da bai gaza mintuna biyar ba.
Zuciyarshi na bugu da sauri da sauri ya rintse idanunsa, kafin ya yi tattaki zuwa inda take
zaune. A lokacin ta sadda kanta kasa ne don haka ba ta ga tahowarshi ba, har ya tsugunna a
gabanta. Sassanyan kamshin Chrome Legend ya tsirga har cikin kanta.
Da sauri ta dago ido ta dube shi, “Yaya Khalipha!” Ta fada cike da al’ajabi da farin cikin da ta
gagara boyewa.
Murmushi ya yi, “Yaya Rahane”. Dariya ya bata sosai, don rabon da ta ji wani ya kira ta da
wanann sunan, tun ranar da Babanta ya bar duniya.

A rayuwarta kuma ba sunan da take so irin Rahanen. Suna ne na mahaifiyarta da bata taba
gani a duniya ba. Suna ne da Babanta ya zabar mata don kar ya manta da Yalwatinsa. Suna ne
da ake kiranta da shi a Takai da intonation daban-daban.

Muskutawa ta yi ta soma share masa kura da dan hankicin dake hannunta kan dan
kututturen itacen bishiyar da ta ke zaune.
“Sannu da zuwa Yaya Khalipha, yi maneji da nan ka ga duk an kwashe kujerun”.
Murmushi yake sosai, ya kwaikwayi ‘yar muryarta “Yi maneji da nan Yaya Khalipha”.
Kunya ce ta kama ta, ta rufe fuskarta da zara-zaran yatsunta.
“Ka sha hanya”.
Ta fada ba tare da ta daina murmushin da ke like a tattausar fatar bakinta ba.
“To ya za ayi? Ai ko bangon duniya Rahane ke karatu ba zan yi kasa a gwiwa wajen zuwa
ziyararta ba, balle Katsina”.
A zuci yake fadi, bai san a fili yake yi ba saboda azabar son da ke kara ruruwa a zuciyarsa.
Sai ta yi dan jim tana nazarin kalamansa don sun dan yi mata tsaurin fahimta.
Ya ankara da katobarar da ya yi, ya yi saurin gyarawa da cewa, “Ina su Abida kike zaune a
nan ke daya?”
Ta sadda kai ta ce, “Ni tun safe yau ban ga Abida ba, Jawahir muna zaune nan tare kawarta
Teemoh ta zo ta yi kiranta su gaisa da ‘yan gidansu”.
Ta fadi haka ne don ta kare Abida, a zahiri kuma Abidar mari ta zabga mata cikin (domitory) a
bainar jama’a, kan wai ta shafa vasiline dinta don nata ya kare. Jawahir kuma ba ta shafa
vasilne sai lotion, abin da ya kaita ga shafa na Abida kenan.
Wannan wulakancin da Abida ta yi mata shine dalilinta na kadaicewa, tana tunanin rayuwa,
canje-canjenta da juyinta, kamar rawar ‘yammata wai na gaba ya koma baya, da abebaden ban
tsoro dake faruwa a cikinta.
Abin nufi, kowa baya tunanin gaba, wato me gobe za ta haifar? Mutuwa na iya zuwar wa
bawa kowanne lokaci amma ta kasa gane me mutane masu irin halin Abida ke daukar duniya.
Da suke tozarta dan Adam don baya da shi, shi ba kowa ne ba. Sun manta da darajar da
Allah ya yiwa dan Adam, har ya fadi da kansa cikin Alkur’ani mai girma cewa, ‘Ya karrama dan
Adam…..’.
Da wannan tunanin da ta yi ne cikin ‘yan mintuna a gaban Khalipha idanuwanta suka kawo
ruwa, suka kada suka yi jajir. Tunda ta sunkuyar da kanta ba ta kara dagowa ta dubi Khalipha
ba kada ya gane bacin ranta.
Shi kuma Khalipha har zuwa lokacin kallon ta kawai yake cike da matsananciyar kauna cikin
kwayar idanunsa, zuciyarshi harbawa take da gudun gaske sakamakon ganewa da ya yi
Rahane kuka take.
Bai san sanda ya baje shaddarshi a kas, ya zauna dirshan agabanta ba, kiris ya rage su
dunkule waje daya. Gaba daya ya manta a inda suke. Da murya mai sanyi yake fadin.
“Daina tunanin komai cikin rayuwar nan Rayha, tunda ga ni, zan zame miki uwa, uba, kawa,
yar uwa, dan uwa, aminiya, masoyi, sannan MIJIN AURE.
Insha Allahu, daga ranar da aka daura mana aure (idan har kin amince) kin gama zubar da
hawaye a kan kalubalen rayuwa. Ina sonki Rayhanah, Rayhanah za ki aure ni???”

Mu biyo Rayhanah da Yaya Khalipha a littafi na biyu. Don jin amsar ta. Tare suke. Sumayyah
Abdulkadir ce Manan SAFAH da MARWAH. ke yi muku

11 / 12