Author : Khadija KMU Category : Love
komai nata ya bambamta bata tsoron kowa
acikinsu abinda takeso shi takeyi yasan tana aiki yanda ya kamata indai ta fannin aiki ne baza a
kamata da laifi ko ha’inci ba
Bata gaishe da kowa sannan bata kula kowa he can’t read her duk yanda yaso ya dan fahimce ta ya
kasa saboda ta rufe kowace kofa da dan mutum zai iya karantar ta
Saidai akwai abinda har yanzu yake bude wanda ta kasa rufe shi duka she’s lonely saidai kallo daya
idan kayi mata baza ka gane kadaicin dake tattare da ita ba saboda yadda ta rufeshi ta ko ina
Liya ce ta kallesu tace please Quit the game for now your food is ready Ammar ne yayi saurin tashi
yace daman yunwa nikeji ya nufo din dining su Hamdan da amrah suka biyo baya kowa yaja kujerar
shi ya zauna
Neela ce tazo ta zauna sannan Imad ne karshe Ammar ne ya dago zaiyi magana aiko cikin sa’a
idonshi akan na Hurriya wadda itama shi take kallo tana karantar shi saidai he looks very familiar to
her kamar tasanshi kallon imad tayi wanda ya zauna a wani miskilance ya lumshe ido yanajin saukar
idonta masu kaifi shima kallonshi tayi Dukansu tasansu amman A ina?Ganin idan fa tanason tagano
inda tasansu sai ta koma duniyar tunani wadda batasan hakan kwata kwata
Ammar dariya yayi yace Hurry ya jiki please come and join us
Hamdan yanajin ance hurry yayi saurin dagowa kamar hadin baki Dukansu suka rinka kallonta
Amrah ce ta taso tazo wurin Hurriya wanda ta kasa boye murnarta alamun zata rungume Hurriya
tayi saurin ja baya sannan tace kada ki tabani idan ba haka ba marinki zanyi daga mata kai amrah
tayi stiill tana farin cikin ganinta
Bude baki kowa yayi don jin furucin Hurriya na zata mari amrah saidai ba wanda yace kala saboda
sunsan halin amrah indai akan abun da takeso ne yanzu ko maganar banza idan sukayi ma Hurriya
to ba wanda zai kwana lafiya don idan ta farayi masu rigima da kuka to sai Allah
Bude bakinta amrah tayi sannan tace Hurry please grant me a wish tana daga mata hannu alamar
don Allah ta taimaka mata shiru Hurriya tayi ganin tayi shiru amrah sai tayi tunanin kilan Hurriya
batajin turanci sai tace don Allah kiyiman abu daya
Hurriya frowning brows dinta tayi ta kalleta mockingly tace mi kikeso dariya Amrah tayi tace don
Allah muci abinci tare shiru wurin yayi kowa na jiran amsarta Ammar ne yayi breaking silent din ta
hanyar cewa haba yar mai kyau please join us yana karya murya hade da kanne mata ido kamar
mace trying to look funny Hurriya gyara tsayuwarta tayi sannan tace you Better stop acting that way
if not I promise you’ll be a transgender by tomorrow morning saboda ka koma kamar wata amarachi
Dariya kowa ya dauka shikanshi Imad duk yanda yaso kada yayi dariya saida ya dara
Neela a ranta take maganar muryar Hurriya ta hadu ba karya don wani accent mai matukar dadi take
amfani dashi wurin magana Ammar ba karamin dadi yaji ba yadda tayi mashi magana don bai
tsammaci hakan ba don yarinya ya lura bata magana kwata kwata don idan bakayi dagaske ba zakayi
tunanin bebiya ce .
Hurriya zagayowa tayi taja kujera ta zauna kowa serving abincin shi yayi
Serving ta farayi ahankali don komai ahankali ta zuba tundaga kan appetize komai nata accordling
takeyinshi cikin tsari ba wanda bai kalli yadda ta fara cin abincinta ba don da appetizer ta fara sannan
taci kadan shima main dish kadan taci yadda zata ida cin komai don a doka tun suna kanana ake
koya masu table manners don shine yake determining they are from royalties kuma not an ordinary
royal family
Don haka they’ve to be always mindful of their table manners duk wanda yaga yadda take cin abinci
yasan she’s from an elegant family because he the way she held her spoon ba kowa ya iya irinshi ba
Ganin almost all of them are staring at her plate ya sanya a hankali tace bloody hell what am I doing
cikin wayau da dabara ta lalata plate din ta canza salon cin Abincin.
They ate in silence tana gamawa tasha ruwa sannan ta tashi kallonta Dukansu sukayi Hamdan ne
yazo yasha gabanta sannan yace Hurriya we’re not done talking zaki bani diyarkin?i like you wani irin
kallon banza Hurriya tayi mashi Hamdan turo mata baki yayi yace please Hurriya banza tayi dashi ta
kama gabanta.
Zubaida da suka gama kallon duka scenes din abinda ya faru bakin ciki kam zuciyar ta har kuna
takeyi hmmm kawai take cewa cikin ranta
Hurriya kam tana komawa ana kiran sallahr magrib
Alwala tayi sannan tayi sallah bayan tagama ta nufi babban kitchen tareda crossing hannunta
abayanta kallon yadda kowa yake hada hada tayi haule reza naganinta tazo wurinta saida ta kalleta
tace yar nan naji ance kinsha ciwo Hurriya daga mata kai tayi
Kallon Haule reza tayi sannan tace aiki zamuyi zan biyaki haule najin kudi ta daga kai Hurriya bayani
tayi mata yadda komai zai kasance
Sannan ta koma daki Bintu ta bama kudi ta siyo mata sabuwar reza da omo klin sai lemun tsami da
gishiri kallonta Bintu tayi tana mamakin mi zatayi dasu saidai tasan kota tamabaye bata da amsa
indai Hurriya ce don haka taje ta siyo mata duka abinda ta aiketa
Isha’i Hurriya tayi sannan ta sanya earpiece a kunnenta tanabin waka Bintu tazo tayi mata saida safe
sannan ta nufi makwancin ta
Saida dare yayi sannan haule reza tazo da kularta wadda ta juyo tafasaasun ruwan zafinta
Wurin Hurriya taje inda Hurriya take kwance don kamar ita take jira tanajin nishinta ta tashi
Haule reza ta kalleta tace muje Hurriya daga ita sai hijab ta tashi hannunta rike da abinda ta aiki
Bintu suka nufi wurin wasila don da ita takeso afara Hurriya tsayawa tayi tana kallon yadda komai ya
fara gudana duk yadda Hurriya ta fada ma haule reza haka ta fara gudanar da ayyukanta don saida
ta fara Gangarawa ta daura ma wasila kyale ta dode mata baki wanda tana tabata ta tashi daga Bacci
tana zare ido saitin fuskarta wasila tazo ta kalla sannan ta kalli hurriya tace ayi anan? Hurriya girgiza
kai tayi
Haka haule reza ta rinka tambayarta saida tazo kan kafafunta sannan Hurriya ta daga mata kai
Hurriya matsowa tayi tanuna mata Daidai inda zata yanka wurare biyar ne wanda duk idan aka taba
ma mutum shi akafa tohm sai Allah haule reza kallonta ta rinkayi tana kallon rashin tsoro da rashin
tausayin dake cikin idonta
Wasila kam ihu ta rinkayi Amman sam baya fita kiyi mana inji Hurriya ba bata lokaci haule reza ta
daura sabuwar reza mai matukar kaifi sannan taja wurin da karfin tsiya wani irin azababben ihu ta
saki Amman to no avail saboda baya fita baba haule ta riketa
sannan Hurriya ta fasa klin dinta guda daya ta zuba mata shi wani irin uban kara ta saki tana shure
shure Hurriya murmushi tayi sannan ta barbada mata gishiri ta hada da matsa lemun tsami a ciwon
Saida ta sanya haule reza tayi mata yanka biyar sannan ta barbada mata ingredients dinta
Tun tana kuka har kukan ya daina fita ba imani kwata kwata tattare da Hurriya ta bude kular nan ta
debo tafasassun ruwa ta watsa mata akafafunta duka biyun ai wasila suma tayi
Haule reza kallon irin launin azabar da Hurriya take mata tayi tana mamakin rashin tsoro da rashin
imanin yarinyar nan. Ta tabbata zuwa gobe kafarta tayi mummunar konewa .
Haka Hurriya ta rinka binsu saida ta tabbata duka tayi masu azaba iri daya don duk saida haule ta
daure masu baki sannan tayi masu yanka biyar biyar Hurriya ta zuba masu omo hade da gishiri da
lemun tsami sannan ta kona kafafun da ruwan zafi
Bayan sun gama tace a a aske ma Hansa’u gashin kanta tass ita kuma wasila da Barira har yanzu tana
binsu bashi ta wuce ta nufi makwancinta
Haule reza kallon bayanta tayi yadda take tafiya kamar tana tausayin kasa haka take takawa tunda
take bata taba ganin mutum marar imanin Hurriya ba
Duk ihun da suke da neman ceton rai da suke ko dar bare gizau haka Hurriya ta rinkayi masu launin
azaba don tasan ba wanda bai suma ba acikinsu
Tabb inji haule tace akwai kallo dai wurin nan saidai sune suka ja ma kansu daman ance in kasa wata
ba kasan wataba.
Hello fans yanzu zan rinka posting from Monday to Thursday saidai daga Friday zuwa Sunday ba post
Idan kuma kun fiso a rinka skipping rana daya tohm I will be waiting for your opinions
Love xoxo❤️
[12/02, 4:54 PM] Khadyn Sp: Masarautar Qamar
A story about a mysterious palace
By Khadija (KMU)
27&28
Kwanciya tayi Hurriya tareda sauke ajiyar zuciya don yanzu ne zata iya Bacci cikin dadi don idan
batayi masu hukunci ba gaskiya ba sunanta Hurriya Faisait Hamood ba.
Haule reza kam tana mamakin inda yarinyar nan ta samo kalar launin azabar datayi masu don bata
taba ganin hakan ba saidai fa ba karya Hurriya muguwa ce tace sannan ta nufi makwancinta
Yau da safe da aka tashi aka iske duka yan click dinsu Barira suna jinya don kusan ihun wasila ya
tadasu don azaba ta ko ina takeji kuka kam yinshi take kawai don a halin da take ciki da za’a cire
kafar to da tanaso indai har zata rabu da ciwon da takeji.
Barira kam har garin Allah ya waye itada suwaiba to asume suke saida aka samu da kyar suka
farfado irin ciwo daya ne Dukansu suke fama dashi Dukansu saidai kowa na mamakin wanda yayi
masu wannan danyan aikin
Hurriya yau ta samu ta tashi da wuri don har sallahr asuba ta samu damar yinta da wuri. Tanajin sai
jaje akeyi Bintu ce tazo da gudu tana haki ta kalli Hurriya sannan tace naji abinda ya faru gasu barira
Amman don Allah kece?kice bake bace don Allah kice man haka Hurriya kallonta tayi sannan tace
nice Bintu And idan suka kara koda hararata abun da zanyi masu sai yafi wannan Bintu kallon
Hurriya tayi sannan tace haba Hurriya miyasa zakiyi haka kinga kafafunsu idan kika gani sai sun baki
tausayi wallahi dama kin kyalesu sunje da halinsu tunda yanzu suma zasu ce zasu rama kema zaki ce
zaki rama kuma ance sarkin yawa yafi sarkin karfi kuma ma kinsan kaura saurayin barira ne sai ance
shaho saurayin Hansa’u ne
Bintu batasan duk maganar da takeyi Hurriya tayi tafiyarta
Juyawar da zatayi taga ba Hurriya saidai ganin inuwar Hurriya tayi
Hurriya tana fitowa saiga hauke reza wadda ta taya danyan aikin jiya
Kallon Hurriya tayi tana washe baki sannan tace Hurriya naga sako nagode kuma don Allah inson
kibani dama yadda idon akace gobe su kara to bazasu kara ba
Hurriya shiru tayi mata har tagama babatunta batace komai ba
Kitchen taje inna hanne na kallonta tazo tace Hurriya an tashi naji danyan aikin da kika aikata baki
kyauta ba
Hurriya dage girarta tayi tace banzo don inji kyautawa da rashin kyautawa wurin ki ba malama ki
zuba min ruwan zafi in kama gabana
Inna Hanne kallonta take kamar statue zata iya cewa tunda Hurriya ta tashi daga rashin lafiya to
yaune ta samu jin muryarta mai tsayi har haka inna hanne wadda tayi curr tana kallonta tsarki ya
tabbata ga Allah sannan tace lallai kedin gimbiya ce duk aranta take maganar don kwata kwata bataji
haushi ba
Inna Hanne daukar bokitin tayi ta zubo mata ruwan zafi suka jero tare inna hanne rike da ruwan
Hurriya kuma rike da kayan wankanta har suka zo toilet
Hurriya wanka ta shiga tayi sannan ta fito ta nufi daki
Sai kallonta akeyi don ba inda maganar bataje ba ita tayi masu Hansa’u wannan hukuncin wasu ta
burgesu wasu kuma ta basu tausayi wasu kuma zaginta kawai sukeyi but who cares
Shiryawa tayi cikin uniform dinta wadanda sukayi mata kyau Sosai
Comb ta dauka ta tsaga kanta hudu sannan tayi kalaba manya manya guda hudu wanda suka sauka
har gadon bayanta nade gashin tayi har saida ya dawo Daidai keyarta sannan ta fesa turarenta ta
fita
Sashen imad ta fara zuwa aikam cikin sa’a ta gyara ko ina har dayan dakin shi wanda yake bacci
Tanajin karar ruwa hakan ya tabattar mata da yana toilet don haka tana gama mopping ta fito ta
wuce part din zinariya wanda tunda ta fara aiki bata taba gifta kofar data wuce ta kitchen ba
Don haka tana zuwa tayi wanke wanke sannan ta fara hada breakfast tanajinsu suna gulma murya
can kasa kasa Amman sautim maganar su radam a kunnen Hurriya wata a cikin kuyangin ce tace
hmmm labari da dumi duminsa fa
Kowa cewa yayi munajinki subira ta kusa dawowa fa ance sati mai zuwa zata dawo, wata acikinsu ta
fara salati tana jajanta masu subira fa suna cikin matsala ta dade batazo kasar nan ba don haka
dayawa kilan sun manta wacece subira AI kuma ba lallai kowa ya iya manta subira ba saboda irin
record din da ta bari
Hurriya duk tanajinsu wata acikinsu tace shekara fa ta kusa zagayowa shiru Dukansu sukayi suna
zare ido wata acikinsu tace nidai bani da kyaun da za’a rasani a masarautar nan
Jakadiyar zinariya ce ta shigo ta kallesu tace me kukeyi ku wuce ku kai abincin Dukansu daga mata kai
sukayi itadai Hurriya na aikinta
Tana gama aikin ta fita ta nufi inda suke wanki tana zuwa ta iske wasba tana wasa da dan icce tana
ganin Hurriya wasba ta saki iccen ta rugo wurinta tana dariya tace tun dazu nike jiranki Hurriya bata
ko kalleta ba tayi gaba inda ta saba wanki
Kayan ta fara wankewa wasba kam ta samu wuri kusada Hurriya ta zauna tana ta bama Hurriya
tatsuniya mai ban dariya duk intayi sai taga Hurriya fuskarta daure sai tace bari in canza haka wasba
ta zauna tana bama Hurriya labarai masu ban dariya Amman Hurriya ko murmushi batayi ba bare
dariya
Wasba kuma taki tafiya sai can wani yaro yazo ya kirata ance ana kiranta tashi tayi ta ruga tana tsalle
ta juyo tayi ma Hurriya alama da hannu Inasonki
Hurriya tsoki tayi ta cigaba da wankinta tana waka
Yunwa ce ta fara galabaitar da Hurriya saboda tun tashinta yau bataci abinci ba don haka tana ida
shanya kayan ta nufo dakinsu
Harabar wurin tagani tasan cewar ba lafiya ba don haka ba tare da bata lokaci ba kutso wurin
Kowa ita yake jira a taron mutanen da akayi ta riga tasan da haka bata damu ba taja kai tana niyyar
shiga wurin shaho ne ya tare hanyar yana watsa mata idanunshi masu firgita ma mutane lissafi itama
kalloshi tayi tare da tsirtar da miyau a kafarshi tace disgusting kaura ne yazo a 360 don ranshi yana
matukar tafarfasa da wannan makirar yarinya mai kyau sai kace ita tayi kanta duk masarautar nan
waye ya isa ya taba barirarshi ya kwana lafiya babushi
Sai ita ta watsa mata tuwo a fuska gashi kuma tayi masu wani irin salon launin azaba tabbas yau sai
ya wulakanta
cikin zafin nama kaura ya daga dorinar shi zai zuba mata Hurriya da yau itama ranta yagama baci
don bazata iya tuna when last tayi irin bacin ran nan ba ta rike dorinar da karfi tanayi mashi
matsiyacin kallo wanda ke dauke da tsantsar mulki da kuma izza tace the moment you beat me with
your filthy hands you’re going to be executed ta matso tana mashi whispering tace kana kuskuren
dukana to hukuncika kisa
Ta saki bulalar ta tsotsi bakinta cikin isa da mulki tace duk wanda bai fasa dukana ba acikin ku
Amman ku tabbata duk wanda yayi gigin kara tabani a masarautar nan da sunan duka to sai ya
amshi laifin shi na taba lafiyar Hurriya Faisait Hamood this is a promise and try me and see ta watsa
masu wani wukantacen kallo tace jakuna daku matsiyata ta shige cikin dakin tana barin kowa baki
bude
Kaura da shaho kam kamar wasu duwatsu haka sukayi don sungani à idanun yarinyar duk wanda ya
kara tabata to kilan lahira zai bakunta yadda ta furta kisa kuma yadda ta nuna hukunci mai tsanani
mutum zai amsa saidai tayi matukar kunyata su
Shiru Dukansu sukayi tareda juyawa suka tafi cike da borin kunya
Ikon Allah yan wurin kowa ya rinka fada to miyasa basu daketa ba mi tace masu har haka watsewa
akayi kowa da alajabin wannan Hurriyar
Sa’ade da karime suna kallon komai sa’ade ce tace wallahi na tsani waccar shegiyar Hurriyar karime
tayi wata dariya tace naki akeji amman ki bari zamu yi maganinta a masarautar nan tunda kowa ya
gagara maganin shegiyar
Bintu ce ta gifto matsawa tayi saitin su tace kafin kuyi maganinta ni Zan sanya tayi maganin ku
mutanen kawai tana kallon yadda suka zare ido alamun shakka dariya tayi ta shige ciki
Sallah ta iske Hurriya nayi Bintu kallon yadda take sallar kawai tayi ta girgiza kai ta zauna tana jiran
tagama sallahr
Bayan ta sallame sallahr ta juyo ta kalli Bintu wadda take gyangyadi murmushi Hurriya tayi wanda
batasan tayi shi ba don da sauri ta maidashi sannan tace Bintu Bintu adan firgice Bintu ta tashi
Hurriya kallon katifa tayi sannan tayi ma Bintu alamu data kwanta
Ba musu Bintu ta kwanta wani irin bacccin gajiya ya dauketa murmushi Hurriya tayi sannan ta dauki
wayarta da ta amso chargy dazu wurin haule reza
Bude wayar tayi wani tunani yazo mata da sauri ta cire tunanin waka ta kunna ta kishingida nesa da
Bintu
Inna hanne ce tazo da plate da kula na abinci kallon Hurriya tayi da ta lumshe ido tanajin waka sam
batason wakar da Hurriya keji don akwai abubuwa da yawa gabanta karatun AlQur’ani ya kamata ta
rinka ji ba waka ba Amman Hurriya is not helping matters
Murmushi tayi ganin yadda take bin wakar
Inna hanne tace Hurriya Hurriya saida inna hanne ta daga murya Sosai Hurriya ta tashi kallonta tayi
ta dage mata gira alamun lafiya shigowa tayi tare da ajiye kular sannan tace abinci na kawo maki
daga mata kai Hurriya tayi sannan ta koma ta kwanta ta dade bata motsa ba don har inna hanne ta
tafi idonta rufe
Saida taji yunwa na damunta Sosai sannan ta bude idonta tare da cizon lebenta ta sauko ta zuba
shinkafa da mai da yaji hada maggi mai tauraro
Kamar tanajin tausayin cikinta haka ta fara cin abinci har saida taji ta koshi sannan ta ajiye cokalin
tasha Ruwa
Yau ya kama wata daya kenan da kona masu su barira da Hurriya tayi su kuma su shaho da kaura
tunda Hurriya tayi masu warning dinan basu kara zuwa ba Amman sun kudirta aransu abinda zasuyi
mata mai muni ne
Bintu kam da Hurriya sun zama tamkar yan uwa don Hurriya har ta fara bude mata wasu abubuwan
duk da she’s not allowed to do that saboda she’s not to trust anybody in this life saidai mi after all
she’s human being too tana amsa sunanta yar adam don haka itama tanada émotions kamar kowa
kawai ta iya boye émotions din nata saboda emotions dinta babbar barazana ce a rayuwarta bata
yadda ace wani Abu yafi karfinta ba tunda ita har takeda kanta so she have full control of herself don
haka she control everything around her herself her maids kowa