Masarautar Qamar Hausa Novel

Author :  Khadija KMU Category :  Love

Chapter   10 / 13

27K to 30K   out of 36.4K words

zuwa masarautar Heral ba saboda sai an ketare kasashe shin bama wannan ba
itadin wacece ba kowa bace face ma'aikaciya a masarautar Qamar sai kuma Qaddara da ta hadata da
long lost princess din Qasar 
Saidai Tana Addu'a Allah yabata ikon taimokon yar marainiyar yarinyar nan Allah kada ya sanya san
zuciya ya debeta ta tona mata asiri 
Su kuma su barira zatayi maganinsu Lallai da ace sun san wacece ita da ko hanya daya basu isa su
hada ba 
Don duk yan masarautar Qamar tafi karfinsu hatta sarkin idan tagadama tace a sauke shi daga kan
mulki to tabbas babu tantama za'a sauke shi don masarautar su tana mulkin masarautoci da yawa a

afirca so masarautar Qamar na ciki 
Ta dade tana tunanin sannan ta tashi ta fita tana fita saiga Bintu na shigowa dan sauke ajiyar zuciya
tayi sannan tace ki kula da ita don Allah.
Abun kamar wasa Amman har yanzu Hurriya bata bude idonta ba har anyi wata daya da sati daya 
Su barira suna sane da halin da Hurriya take ciki don har anfara yada jita jita su barira sunyi kisan kai
saidai da yake su din suna da power sosai ba wanda ya tarbesu da maganar 
Saukin Hurriya daya data samu Inna hanne tayi bake bake ganin taji sauki don lallabata take kamar
kwai kowa yana mamakin dalilin don baba hanne bata da irin wannan kirkin da take nuna ma Hurriya
don itama ba Ruwanta da kowa 
Bintu kam ta zuge ta rame tass kallo daya zakayi mata kasan cewar tana cikin matsinaciyar damuwa .
Imad kam shima ya shiga damuwar rashin ganin mai aikin nan don Hamdan da amrah duk sun gigita
su don yanzu a chamber shi suke kwana Neela kam batasan mi zatace ba a al-amarin don tun tana
kushe su yanzu ita kanta burinta da fatanta a samo Hurriya 
Imad yafi kowa damuwa don kowa kallo yake yasan inda take don yanzu haka suna tare da Ammar
ne a balcony Ammar ya kalleshi yace twin Imad kallonshi yayi yana daga mashi kai dafashi Ammar
yayi yace nifa na rasa gane mike faruwa wacece wannan yarinyar miye hadinta da Hamdan da Amrah
mi yasa suke sonta har haka yaran da basu damu da kowa ba rayuwarsu Amman sun damu da ita
fiye da yadda suka damu damu 
Shiru Imad yayi yana nazarin maganar saidai baisan yadda zai hada komai ya bashi ma'ana ba don
haka ba tare da karayin wani tunanin ba yace Allah yasa lafiya dai 
Shiru Ammar yayi sannan yace ka tambayi ma'aikatan ko lafiya? Girgiza kai yayi yace mashi Aa 
Shigowar Liya ne ya sanya  Dukansu suka juya suna kallonta cikin jumpsuit din Rimowa wanda sukayi
mata kyau sosai zuwa tayi gefen imad ta rike mashi hannu tace na samo labarin maid dinka ka
kwantar da hankalin ka 
Ammar ne ya zagayo ya rike ma Liya hannu yace lafiya miye ya faru shima rike mashi hannu tayi ,
murmushi tayi sannan ta gyara zama tace kwantar da hankalin ka tana cikin masarautar Qamar 

A hankali ta zayyane masu duk abinda aka gaya mata ance bata lafiya har yanzu batasan inda kanta
yake ba tundaga ranar da ta ture Amrah 
Shiru sukayi suna kallon yadda takeyi masu bayani har takai karshe ba wanda yace kala Ammar ne
yace wani irin ciwo take Liya tace bansaniba Imad baice komai ba ya tashi ya bar masu wurin ba
wanda ya damu da tashin da yayi saboda susan halinshi na miskilanci 
Hamdan kam ko da yagama jin bayanin da Neela da Liya suka gama mashi sai ya fara sauke ajiyar
zuciya kallonshi suka rinkayi da mamaki don abinda basu taba gani bane 
Amrah ce ta shigo jikinta sanye da wani crazy jeans sai yar top kunnenta sakale da AirPod Dukansu
kallon yar autarsu da damuwa ta bayyana a fuskarta sukayi Hamdan ne ya tashi yaje saitin da take
sannan ya zare AirPod din kallon shi tayi ta dage mashi gira guda daya alamun lafiya 
Cikin muryar shi mai dadi yace I found her Amrah kallonshi take da alamar bata gane nufinshi ba
murmushi yayi mata sannan yace the beautiful young lady bude hakoranta tayi tana kallon hakimi
tace like seriously daga mata kai kawai yayi Amrah zuwa tayi ta rungume Hamdan tana mai tsananin
murna 
Inna Hanne zaune tayi tana kallon Hurriya wadda fuskarta tayi fayau gashin kanta da girarta kwance
sai bakinta da yayi pink  ta riga ta gama sawa a ranta idan har Hurriya ta cike wata biyu bata samu
sauki ba to zataje kauyensu ta taho da yayanta domin ya dubata 
Tausayin yarinyar takeji sosai don yarinya mai gata kamarta yaushe ne Zata jira wani maganin
gargajiya saidai da yanzu tana asibiti kasar waje Maganar Bintu da taji ya sanya ta dawo daga dogon
tunanin da ta shiga ta kalleta sannan tace kindai ci abinci ko? Daga mata kai tayi 
Wasba kije innani na kira wani karamin yaro ya gaya mata dauke kanta tayi daga kallonshi hawaye na
zuba a idonta yau tasan dukan tsiya zataci bare tun dazu innani take kiranta Amman taki zuwa ta
tsaya tana duba hanya ko zataga inda Hurriya zata bullo 
Tashi tayi tana kuka tana share majina har tazo dan karamin gidansu dake cikin masarautar Qamar 
Aiko tana shigowa innani ta rufeta da duka tana zaginta shegiya daga gidan ubanwa kike yar iska
matsiyaciya tsintarciyar mage kin raina mutane ko ta cigaba da dukanta ba tausayi bare tausayawa
har saida taga tana Neman daina numfashi ta daina dukanta.

Hurriya a hankali ta fara motsa yatsunta kafin ta bude idanunta Bintu dake zaune ta saki tagumi jin
motsin da tayi daga Hurriya ya sanya ta kalleta cikin mamaki taga idon Hurriya bude suna kallonta da
wani irin jin dadi da murna Bintu ta nufota girgiza mata kai Hurriya tayi tana mata kallon kada ki sake
ki tabani 
Daga mata kai Bintu tayi tana ta hamdala Hurriya kuma kallonta kawai take yadda take murna 
Shiru Hurriya tayi tana tunanin wadanda suka sanyata jinya inda ace a masarautar Heral ne to babu
abinda zai hana su bakunci lahira don abinda suka aikata hukuncinshi kisa ne how dare they messed
with Princess wani evil smirk tayi don ita she’s someone that doesn’t take nonsense from anybody
whether she’s princess or slave tasan sai tayi maganinsu ita batajira wani ya kwatar mata yanci da
kanta da hannunta zata kwatar ma kanta yanci 
Hurriya bata da dadi ko kadan idan ka tabata zatayi masu salon azabar da ko a masarautar Qamar
ba’a tabayi ma waninsu irinta ba because they almost killed her lamoniyar dake gareta is not an
ordinary lamoniya ciwo ne mai hade da poison wanda yake babbar barazana ga rayuwarta all this
while tasan Allah ke tsareta and nobody knows about her health condition don ko a masarautar
Heral ciwonta is a secret duk wanda yasan da ciwonta sai yabar masarautar tare dayin nesa sosai da
masarautar zatayi masu abinda idan akace gobe su kara bazasu kara ba tayi alkawarin sai sun biyata
with bigger price Dukansu sai sunyi jinyar da tafi tata tayi wani evil smirk tare da rufe idonta masu
kyau tana taune lebanta.
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: 🌚Masarautar Qamar
A story about a mysterious palace 
By Khadija (KMU)
25&26
Bintu kallom Hurriya kawai take with pure love Hurriya lumshe ido tayi tana yamutsa fuska alamar
jikinta na damunta Bintu tace bari in kira maki baba hanne ta kara dubaki 
Bintu aguje taje kitchen ta kira Baba hanne wadda take tuka tuwo ai tanajin ance Hurriya ta farfado
ta saki muciyar ta rugo aguje sai dakinsu Bintu murmushi tayi tana biyota a baya
A kwance suka iske Hurriya tadan tada kanta da bango ta lumshe idanunta dogayen lashes dinta
kwance sai kyalli suke sai pink lips dinta da take dan cijewa Inna hanne kara kallon Hurriya tayi don
ba karya tanada kyau kallonta ta karayi ganin irin kwarjini da kuma tsantsar mulki da yake bayyane
ajikinta dama saidai idan baka gani Amman kallo daya zakayi ma Hurriya kasan jini sarauta ce bude
idonta Hurriya tayi aiko da sauri inna Hanne ta sadda kanta kasa duk tasha jinin jikinta ta kasa motsi
Hurriya kallo daya tayi mata ta kauda kanta 
Hurriya Bintu ta kalla tace Bintu ki samo man ruwan zafi inyi wanka da sauri Bintu tace to inna hanne
ce tace kije kitchen kice nice na aiko ki a zuba maki ruwan zafi Bintu juyawa tayi ta fita domin amso
ma Hurriya ruwan wanka 
Inna Hanne kam kanta duke a kasa Hurriya batasan ma Allah yayi wata hallita a wurin ba har Bintu ta
kawo mata ruwan a hankali ta sauko kafarta wadda tayi mata nauyi da sanyi 

Bintu har tazo zata taimaka mata girgiza mata kai Hurriya tayi alamar bataso da kyar ta iya tashi ta
fara tafiya a hankali Bintu ta shiga ta ajiye mata ruwan sannan ta bata brush da macline sai sabulun
wanka 
Saida tayi brush sannan ta mika ma Bintu brush din ita kuma ta shiga toilet domin yin wanka 
Ta dade cikin toilette tana wanke jikinta saboda kyankyamin da takeji saida tayi kamar zataji ma
kanta ciwo saboda yadda take dirzar jikin sannan ta dauraye jikinta ta fito tana mai jin matukar
kyankyamin kayan da ta maida 
Hurriya dakinsu ta shigo inda tayi sa’a Bintu da inna hanne basu nan don inna hanne ce tacema
Bintu suje kitchen tare domin dafa ma Hurriya abinci dajin haka Bintu taita murna sannan tabi inna
hanne kitchen din kallon Bintu tayi sannan tace mi Hurriya tafiso acikin abinci shiru Bintu tayi sannan
ta girgiza ma inna hanne kai alamar batasani ba don bata taba ganin Hurriya na cin abi da farin ciki
ba don kullum cikin dacin rai take cin abinci kamar dole
Inna hanne murmushi tayi ta debo dankali wanda bai kai goma ba sannan ta fere.
Hurriya kallon ko ina tayi da yayi datti cikin yanayin natsuwarta ta amso tsintsiya wurin uwale da
murna uwale ta farayi mata ya jiki daga mata kai Hurriya kawai tayi tazo ta gyara dan wurin ta share
wurin tass 
Sannan ta cire kayan jikinta vaseline ta shafa ta bude ledar kayanta ta zaro jeans dark blue sai farar
top mai shara shara saida ta sanya inner wears hade da vest sannan ta sanya rigar 
Kwanciya tayi ta mike kafafunta ta lumshe idonta tunani take neman ta farayi wanda sam babu
lisaafin tunani a rayuwarta bude idonta tayi sai kam ga giftawar su barira kallonsu tayi Dukansu tana
karantar su 
Inna hanne ce ta shigo itada Bintu inna hanne rike da yar karamar kula mai kyau Bintu kuma
hannunta rike da ruwa da plate 
Da sallama suka shigo kallo daya Hurriya tayi mata tagane ta don itace matar da ta fara bata ruwan
zafi. acikin zuciyar ta take tambayar kanta mi takeyi anan Shiru tayi tana kallon matar sai sadda kai
take kamar munafuka tana durkusa mata alhalin ranar farko ba haka tayi mata ba 
Inna hanne ta zuba mata faten dankalin da tayi mata wanda yaji kayan miya ta mika mata Hurriya
kallonta tayi ba tare da ta amsa ba don haka Bintu da sauri ta amsa tazo ta mika mata amsa Hurriya
tayi sannan tace Bintu ta miko mata ledar kayanta ba musu Bintu  ta miko mata ledar kayanta spoon
ta dauka cikin kayanta  saida ta daurayeshi sannan ta faraci lumshe ido tayi ta cigaba daci wanda
alama ke nuni da tana enjoying abinci 

Dukansu kallonta suke inna hanne kanta a kasa saida taci Sosai sannan ta ture plate din Bintu ta
kalleta sannan tace kin koshi daga ma Bintu kai Alamar Eh ta koshi 
Pure water inna hanne ta miko mata alamar ta ajiye tayi mata inna hanne ta ajiye mata dauka tayi ta
fasa ta shanye 
Inna hanne ta miko ma Hurriya magani ba tare da tayi musu ba ta amsa tayi chokali uku ta mika
mata murmushi inna hanne tayi tana mai jin dadi ganin Hurriya har tayi acknowledging dinta 
Kwanciya Hurriya tayi tareda lumshe idonta tana mai neman fadawa duniyar tunani tana tuna
lokacin da idan ciwon ta ya tashi yadda iyayenta ke shiga tashin hankali sosai ganin tana Neman ta
fada duniyar tunanin wanda bata cika son haka ba don haka ta tashi wayarta ta dauko wadda ta
dade batayi amfani da ita ba ta kunna waka sannan lumshe ido tana bin wakar fire on fire by sam
smith a haka har bacci ya dauketa 
Inna hanne bayan tagama aikinta ta shigo ta iske Hurriya kwance tana Bacci kamar karamar yarinya
duk da bacci take amman zaka iya gane yadda ta hade fuska murmushi tayi sannan tace rigimar
Duniya 
Hurriya bayan ta warke saida tayi kusan sati biyu bata fara zuwa aiki ba don so take sai sanyi ya
gama fita daga jikinta tasss don a lamarinta batasan weakness ko kuma ace wani ya gane weak point
dinta shiyasa saida ta tabattar da ta warke tasss sannan zata koma aiki
Bangaren kam inna hanne kam hidima takeyi  mata babu kakautawa don abinci masu dadi kala kala
takeyi ma Hurriya Ruwan wanka kam kullum ita take tafasa mata ta kai mata toilet hatta kayan
Hurriya kwana uku sukeyi sai ta daukesu ta wanke mata 
Duk hidimar da take ma Hurriya bata taba ce mata ta gode ba don kamar daman dolen ta ne ita
kuma Inna hanne bata taba kallon Rashin kulawar da Hurriyyar take mata ba as wani abu ba 
Tana addu’a kullum Allah ya bama Hurriya ikon yadda da ita duk da ta fahimci Hurriyar kamar bata
yadda da kowa ba 
A bangaren su Imad sun baza ido suna taso suga ko ta ina zata bullo don Liya ta bincika masu ance
ta warke don Hamdan da Amrah kullum sai sunce zasu je Amman yan’uwan sunki barinsu saboda zai
zama abun fadi a masarautar duk dasu ba ruwansu 

Fitowar ta daga wanka kenan daga ita sai zani sai kuma doguwar hijab dai dai zata shiga ciki  su kuma
suna fitowa Dukansu kallonta sukeyi tundaga dogayen kafafunta har zuwa kyakyawar fuskarta
wadda babu fara’a saidai zallah kyau da annurin dake fita kafe su tayi da idanunta masu masifar kyau
saidai baka iya jure kallonsu saboda yadda suke imnating danger flames ne kawai ke fita daga idanun
acikinsu ba wacce bataji shakkarta ba saboda wani kwarjini da ta karayi masu 
Saida ta kare masu kallo tass sannan ta shiga daga ciki inna hanne da Bintu na ganin dawowarta
suka tashi inna hanne ta kalli Hurriya sannan tace mi zakiyi yanzu cewa tayi sallah shimfida mata
dadduma tayi sannan suka fita domin bata wurin saboda shiryawa don sun san bata sanya kaya wani
na kallonta 
Wata doguwar riga ta sanya mai kyau saidai tana kama da abaya yau kawai taji tanason dan decent
dressing dankwali ta daura ma gashinta wanda yake ta kamshin mai na soulmate don Hurriya na
yawan wanke gashinta sai ta jirashi ya bushe ya gama shan iska tukuna ta shafa mai ta sharce shi.
Hijab ta sanya tayi sallah hade da rama sallahr da ake binta don daman yaune karshe idan ta rama
la’asar tohm sauran magriba da isha’i 
Tana gama sallahr inna hanne ta shigo wadda dama dama yanzu Hurriya na kula ta saboda tana kula
da ita duk wani motives nata tana kallo duk da tana nuna halin rashin damuwa gareta ganin batada
wani motives shiyasa ta kyaleta ta shigo rayuwarta kuma she knew she’s too smart itadin fa sunanta
Hurriya Faisait Hamood she’s her fathers daughter wanda zai iya cutar da ita yanzu ai sai yayi babban
shiri beside ba wanda yasan kowacece ita saidai she have to be very cautious duk dama ita din she’s
always cautious 
Turarenta ta fesa mai saukin kudi sannan ta fito domin samun iska wayarta kirar burin yar garuwa
sai a hannunta sai earpieces dake makale a kunnenta wakarta takeji wasba ce tazo inda take tana
kuka tana sharbar majina kallo daya Hurriya tayi mata taganeta 
wasba yar karamar yarinyar ta dukar da kanta tanata sharbar kuka Hurriya batace mata komai ba
har ta gama kukanta 
Saida tagama kukan sannan ta kalli Hurriya ta washe mata baki tace kinyi kyau kinfi kyau a haka
Hurriya batace mata kala ba Amman tana kallon yarinyar surutai wasba ta farayi mata tace ina kikaje
ne kullum sai nazo na jira inga ko zaki zo Amman baki taba zuwa ba sai yau yar dariya wasba tayi
tace bari muga kwana nawa nayi banganki ba hannunta ta fara kirgawa kamar wata yar baby har
saida ta kirga kwanakin da tayi bataga Hurriya ba tashi tsaye wasba tayi idonta na cika da kwalla
sannan tace ki yawaita yin addu’oi Saboda banason na rasaki irin fareedaa you’re beautiful ta sakar
mata murmushi sannan ta ruga ta tafi 

Kallon bayan yarinyar da take gudu tayi wadda damuwa ta bayyana a duka fuskar yarinyar Hurriya
can kasan makoshinta tace what is wrong with the girl aranta tace ina ruwanki 
Kallon mutanen da suke wucewa suna kallonta tayi itadai  tanajin wakarta tana kallon kowa da kowa 
Hurriya ta dade zaune a wurin don har saida taga magrib ta tafi zuwa dakinsu 
Sallahr magrib tayi bayan tagama ta nufi part din Imad ganin taji sauki don haka bari yau ta koma
bakin aikinta 
Kitchen ta shiga ba sallama ba komai zubaida datake bakin kofa sakalau tayi da baki tana kallon
Hurriya wadda bazaka ce mata yar aiki bace yadda tayi wani irin kyau kuma sai kamshi takeyi zubaida
bakin ciki ne ya turniketa don bata manta yadda uban gidanta da Hamdan suka shiga damuwar
rashinta ba 
Ta tsani Hurriyar nan don batada mutunci ko kadan gashi duk inda taje ita ake kallo duk sauran
mutanen dake zaune sun zama banzaye indai tana wuri haka ko su Hamdan basu tabayi mata
magana ba karewa ko maganar Imad bata tabaji ba Amman ga yarinya da tazo jiya jiya tafi ta matsayi
abun gaskiya yana matukar bata mata rai Amman zatayi maganinta very soon don ba zata zuba mata
ido ba
Duk aranta take wannan sake saken
Baba RaBI ce ta kalli Hurriya tace ya jiki kinsha ciwo ko daga yanayin maganar ta zakasan ba har cikin
ranta tayi maganar ba jiran amsar Hurriya take saida tana juyowa taga batanan Dariya suka saki
Dukansu yan kitchen din shiru baba rabi tayi sannan ta daure fuska 
Store ta shiga ta debo basmati tayi continental rice sai vegetables spaghetti wadda taji namomi sai
kamshi take kowa kallonta yake amman ita kamar batasan anayi ba saboda earpiece ne ma makale a
kunnenta 
Saida ta gama suka jera trays din akace su shiga sukai masu ba musu Hurriya tabi bayansu da nata
tray din 
Basu tarar dasu a falo na farko ko a parlour na biyu basu nan sai a parlon na uku inda suka shiga
kansu duk a kasa 

Hurriya kallo daya tayi masu ta dauke kanta suka shiga jera abincin 
Saidai tanajin idanun dake binta 
Ludo sukeyi Dukansu su shiddan kallo daya zakayi masu kasan suna cikin farin ciki kuma suna
enjoying game din Hamdan ne yake kokarin cinye game din Neela kuma kiri kiri taki bashi dama 
Tunda Hurriya ta shigo Imad yasan ta shigo don lokacin data juyo ta kallesu with distaste yana
kallonta saidai bata lura dashi ba shidai yana mamakin halinta na iko da raini wayau Because he
never came across someone like her ba all his entire life 

10 / 13