Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
'yanmatan.
Sau biyu babbar ciki na kallonta,itama sai ta maida kanta ga tab dinta,bata kuma sake dagowa ba,taso sosai ta daina kallon nasu don kada su tsargu,amma kuma ta gaza hakan,tana jin kamar ana fusgar idanuwanta ne.
Cikin haka taji maqogaronta ya dan bushe kadan,sai ta dubi fatima
"Bari na samo ruwa"
"Ehenn,ki tahomin dashi" a nutse ta miqe,ta fara takawa zuwa wajen dispenser dake girke a gefe guda,wadda daura take da matar da hankalinta keta daukuwa a kanta,dab da zata qarasa ja'afar din ya shigo wajen,da fari bata ganshi ba amma shi ya ganta,daga bisani ne taji kamar qamshinsa ya cika wajen,sai ta waiwaya,yana tsaye yana kallonta kansa tsaye,baya ko jin nauyin mutanen dake zazzaune a wajen.
Ta soma karantar da yawa daga cikin dabi'u da halayensa,murmushi yake mata,amma idan normal mutum ne ya kalleshi ba lallai kai tsaye ya fahimci murmushin ne,wani irin sirritaccen murmushi,sai ta dakata daga takun da take har ya cimmata,kansa tsaye ya saqalo hannunta cikin nasa,yadan ranqwafa kadan ya rage tsahonsa yakai.bakinsa ga kunnenta
"Banason ki dinga yawan zirga zirga,akwai idanuwa da yawa a nan,ina zaki?" Kaf yawun bakinta ya dauke,saboda yadda ya saukar mata da kasala,ya kuma aike mata da wani abu da ya sanya tsigar jikinta zubawa,musamman yadda yake murza tafin hannunsa cikin nata
"Ruwa zan sha" ta motsa labbanta ta fadi murya can qasa,bata ma zaci zaiji ba,sai taji yace
"Okay,muje na rakaki" tare suka jera suna takawa zuwa wajen,idanuwan mutane da yawa yayi kansu,musamman jajayen fatar dake wajen wadanda suka.kasa boye zalamarsu
"Nice couple,perfect match.....wow" sune irin sautukan da suka dinga fadi qasa qasa,duk wanann abun hankalinta nakan matar,har suka isa gaban dispenser din,ya dauki disposable cup din ya fara taara mata ruwan.
A hankali matar ta waiwayo tana duban yaran nata da idanuwanta dake nuna zallar jigata da damuwa irin wadda ke sanya idanu su xuge kamar ka shekara kana kuka
"Idan daddynku ya kira fa ku sanar mini" ta qarasa maganar idanuwanta na sauka kan fuskar maimunatu da ta waiwayo gaba daya zuwa gareta.
Cak tunaninta da kwanyarta suka daskare suka daina aiki na wucin gadi,kafin kuma su dawo dai dai,ta miqe tsaye zumbur tana duban maimunatu wadda ta zame hannunta daga na ja'afar,tanason qafafuwanta su dauketa su kaita inda matar ke tsaye amma sunqi mata wannan aikin
"Maim.... maimunatu ce?" Ta tambaya bakinta yana rawa don kawar da shakku
"Umma sa'adeee" ta fadi sunan da wani irin qarfi sannan ta kwasa da mugun gudu tayi wajenta,tana isa umma sa'aden ta bude hannuwanta ta kuma rungumeta da kyau,sannan dukkaninsu suka saki kuka a tare kamar ransu zai fice.
Kiran sunan juna sukeyi,kowa yana jin kamar a duniyar mafarki yake,yayin da yaran matar suka zubar da duk abinda sukeyi suka qaraso wajen,cikin tashin hankalin kukan da mamansu takeyi suka tsaya carko carko suna kallonta gami da kiran sunanta.
Tuni ja'afar ya riga jabir isowa wajen,shi da fatima na tsaye a bayansa shima cikin rashin fahimtar meke faruwa?,zaya matsa gaba kadan ganin yadda maimunatun sa ke kuka jabir ya riqeshi,saboda ambaton sunanta da maimunatu tayi ya tuna masa da ko wacece ita a rayuwar maimunatu.
Taga tagar da sa'ade zata fadi yasa maimunatu da yaranta tarota,ta samu ta tsaya sosai tana sake kiran sunan maimunatu,gami da dagowa tana riqe da fuskarta,wasu irin hawaye masu zafi suna mata zirya a kuncinta,tana kallon fuska mafi soyuwa a fuskar maimunatun,fuskar 'yar uwarta qwaya daya tal data mallaka wato shatu
"Umma ki zauna,kinga shirin faduwa kike" diyarta ta fada cikin damuwa,sai maimunatu ta kamata da kyau suka koma saman abun zama suka zauna,tana riqe gam da hannun maimunatun kamar zata sake bace mata.
Sai a sannan idanuwanta ya hangi su ja'afar dake tsaye,suma sai lokacin suka ga fuskarta da kyau
"Momma?" Jabir ya fada yana dubanta
"Jabir?" Itama sa'ade ta fada tana kallonsa,sai ya matsa daga inda fatima take ya tako gabanta
"Barka da rana momma"
"Jabir barka kadai,kai da waye?,daga ina haka kake?" Ta tambayeshi fuskarta jiqe da hawayen da taketa qoqarin tsaidasu,waiwayawa yayi ya kallo ja'afar da dukka hankalinsa yake kan maimunatu,kukan da take yana ta tabashi,banda jabir ya hanashi da tuni ya isa gareta ya janyeta
"Dude" yayi kiran ja'afar a tausashe,sai a sannan yakai fuskarsa kansu,ya gane fuskar matar,matar baaba ambassador ce,kuma tamkar uwa take a wajensa,sign jabir yayi masa na ya matso,don yana tsammanin ja'afar din bai ganeta ba,saboda yasan ba shiga sha'anin mutane yakeyi ba,sai ya waiwaya ga fatima itama ya kirayeta.
"Ja'afar?" Ta kira sunansa shima sand ya iso din
"Nigeria zamu wuce,munzo hutu ne na sati daya,ga mijin maimunatu" wata ajiyar zuciya me hade da qwalla sa'ade ta sauke
"Allah kai ne Allah,Allah mai yadda yaso da bayinsa,Allah mai qaddara dukkan abinda zai afku,ubangiji kai kasan kalar abinda ka shirya har ka qaddaro min matsalar da bazan iya fita daga qasar daka ajiyeni ba tsahon shekaru,sannan kuma ka qaddaramin fitowa daga wannan qasar a yau,Allah na gode maka" sai ta rungume maimunatun sosai suna sakin sabon kuka.
Idanu ja'afar ya runtse kana ya budesu,bayason kukan da maimunatu take ko kadan,yana jinsa yana sauka can tsakiyar zuciyarsa,kiran da akema wadanda zasu tashi a jirginsu ya katse komai,saidai kuma sa'ade taqi rabuwa da maimunatu,tana riqe gam a hannunta,har zuwa sanda aka kammala komai suka shige jirgi.
70
Seat din kusa da ita fareeda diyar sa'ade ta barwa maimunatu,dukkansu suna ta kallon maimunatu cike da zumudi a zukatansu,saboda suna da.labarinta sarai,sannan ita fareeda tana dan tuna wasu abubuwa da suka faru,tunda da dan wayonta suka bar gembu.
Cikin tafiyar awannin da suka cur hannun sa'ade yana cikin na maimunatu,kaf maimunatu ta labarta mata dukkan abinda take da buqatar sani,saade ta lumshe idanu hawaye masu dumi suna fita akan fuskarta
"Wata shari'ar sai a lahira,inno taci amanata taci amanar shatu,Allah ya jiqanki 'yar uwata,matsala na samu akan dukka abinda ya shafi bayanaina,aka samu wasu suka dauka sukayi amfani dasu suka aikata laifi,ya zamana ni ake zargi aketa nema,wannan dalili yasa abbansu yayimin kyakkyawan boyo,sannan akaci gaba da bincike,don yasan muddin ya fiddani aka kamani babu mai fitar dani sai Allah,wannan dalilin ya hanani dawowa gareku,saidai duk da haka nayi amfani da abbansu nayi aike gembu,waya kudi da kaya,ina amfani da wani boyayyen layi ina yawaita kiran inno akan yaya kuke ya lafiyarku?,koda yaushe nunamin take kuna nan lafiya,bana jimawa akan waya shi yasa bana samun damar cewa a bani ku,aike nake akai akai na kudi da kaya ashe baya samunku,ashe sun gama shirya abinda suka shirya,ashe sun cutar min da shatu na,sun kuma cutatar dake kema" sai suka sanya kuka gaba dayansu hannuwansu cikin na juna.
Dogon numfashi ja'afar dake daga can bayansu ya saki,tunda suka zauna hankalinsa da nutsuwarsa tana kansu,duk da baijin abinda suke fada amma yana iya fahimtar kuka suke,yana kuma ji a zuciyarsa maimunatun kuka take da gasken gaske,yana ta son ya daure amma ya gaza,yana jin kukan nata yana tabashi sosai
"Please,ka gaya mata ta daina sakata kuka haka" ja'afar ya fada idanuwansa a kansu,kallonsa jabir yayi baki galala
"Kai,surukarka ce fa,sannan kuma mamanka ta wani fannin,ita za'a cewa ta daina saka matarka kuka?,bazan iya ba" shuru ya ratsa tsakani,kawai sai ganin ja'afar jabir yayi yana miqewa tsaye,da alama zuwa zaiyi kenan ya shaidar mata da kansa.
Saurin damqoshi jabir yayi,don yasan tsaf xai aika
"Haba mana,kayi haquri mana romeo,dole fa suyi kuka,don bakasan komai bane" da mamaki ya juyo ya dubeshi,duba na son sanin abinda bai sani din ba,ba tare da yace komai ba jabir ya karanceshi,sai yace dashi
"Zauna na fada maka" ba musu ya koma ya zauna din,ya kuma tattara dukka hankalinsa ga jabir,yayin da jabir ya soma magana a nutse,dama.ya jima yana fatan zuwan wannan lokacin da ja'afar din zai san labarin maimunatu,yasan halinsa sarai,yana da wani irin tausayi na daban q zuciyarsa,sanin labarin nata zai sake haifar da wata alaqa mai girma a tsakaninsu,inda a baya ne,yasan halinsa......bazai taba tsaya ya saurareshi ba,coz bashi da interest,idan kuma yayi loosing interest akan abu babu mai sanyashi dole face mutum biyu zuwa uku a duniya,anni abbi da amma.
"Ashe nesa a kusa take?,ke din matar ja'afar ce,ja'afar kamar d'a yake a wajena,saboda dan qanwar abbansu fareeda ne"
"Amma?" Maimunatu ta fada tana dan fidda idanu cikin mamaki,a karon farko sa'ade ta gyada kai
"Qwarai,wala'alla banda matsalar dana samu.....wadda sai yanzu ta warware,dani za'ayi bikinku,nasan anyi bikin,amma ban san amaryar ba,don a sannan ba cikin hayyacina nake ba,yau sati daya kwata kwata da bayyanar gaskiya,aka kuma damqe wadanda suka aikata laifin,wanna shine ya bani 'yancina" kai maimunatu take jinjinawa,lallai soyayya ta gaskiya abace mai kima daraja da kuma wahala,ta jinjinawa abbansu fareeda da yadda ya bata dukkan kariya,duk da cewa basa a qasarsu,amma ya tsaya mata kai da fata don ganin ya kula da amanar da aka bashi
"Yaranki nawa diyam dita?,duk da nasan ba zai wuce guda daya ba tunda baku fi shekara da auren ba,saidai idan kinyo gadon dangin tamu daadar masu haifar twins" kunya ta kama maimunatu,saita kifa fuskarta a kafadar sa'ade,tana jin kamar ita da daadarta suke magana
"Babu ko daya" murmushi tayi tana gyada kai
"To Allah ya kawo masu amfani da albarka,yasa kiyita haifa mana bibbiyu,zuri'ar shatu na tayi dogon baya" tayi maganar cikin rauni dajin zafin mutuwar 'yar uwarta,wanda bata sani ba gaba daya sai kwanan nan.
Hawayen fuskarta ta dauke,ta waiwaya kadan baya inda su ja'afar suke
"Amma naji dadi da naga yadda ja'afar yake miki,da alama akwai tsaftatacciyar soyayya a tsakaninku" a kunyace ta saki murmushi tana yin qas da kanta,sai takejin kamar umma sa'aden tana iya karanto abinda ya faru tsakaninta da ja'afar din kwanaki biyar din da suka shude,don har yau bataji tafiyarta ta koma dai dai ba yadda take ada,sannan kuma ta fahimci akwai sauran dan ciwo ciwo a jikinta.
Jin bata amsa ba sai ta dora
"Haka nake fata,ki samu mijin marainiya,kuma ina da cikakken fatan cewa zaki samu haka daga ja'afar,indai yaro yana gadon dabi'u daga mahaifiyarsa,aishatu mutum ce nagartacciya,kawai qauna mai tsafta tsakanina da ita,bansan yaya zataji ba sanda labarin KE JININA CE ya risketa" sa'ade ta qarashe maganar tana gyada kai murmushi na kubce mata.
Duk yadda umma sa'ade taso ja'afar yabar mata maimunatu su wuce gidanta ko kwana daya suyi amma ya murje idanunsa,bai ma yarda ta ganshi ba,don tuni ya isa motarsa yayi zamansa a owners corner yana jiran isowarta,awannin data dauka ba tare dashi ba sai yake jinsa kamar wanda ya rasa wani sashe na jikinsa,ya sauke hannunsa da yake duban lokaci dai dai sanda take takowa zuwa gaban motar,fareeda da umma sa'aden suna biye da ita.
Sosai ya zuba mata idanu ransa yana motsuwa,yana kuma tuna labarinta da jabir ya bashi,wani irin nau'in tausayi na musamman na ratsa zuciyarsa kamar zai narkar da ita,how she survive?,rayuwa ba uwa ba uba?,babu yaya babu qani?,ba soyayya ba kulawa?.......tabbas ta cancanci samun komai,ta cancanci ta samu duk wani abu data rasa a baya,sai ya lumshe idanunsa sanda suke gab da motar,yana daukarma kansa wani alqawari,wanda ba wanda ya gayawa,tsakaninsa ne da ubangijinsa kawai.
"Ina fatan za'a kawomin ita ko ni ayimin alfarma nazo na ganta ko yallabai?" Sa'ade ta fada tana murmushi,kai ya jinjina mata da nashi miskilallen murmushin ya amsata a taqaice
"In sha Allah" tasan halinsa ba tun yau ba,don haka itama bata wani damu sosai ba,ta maida qofar ta rufe musu tana musu fatan sauka lafiya,kafin itama ta juya zuwa motocin da suka zo daukarta,zuciyarta cike fal da kewar maimunatu,wanda inda so samu ne su kasance tare,su kwana gado daya tana sake jin labarin rayuwarta.
Bata gama dai daita zamanta a cikin motar ba ta tsinci hannunta cikin nasa,ya daga hannun nata a hankali ya cusa cikin qirjinsa yana lumshe idanuwansa.
Shuru tayi kamar yadda shima yayi shurun,tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa fat fat da qarfi bisa qaramar tazara sosai a tsakani,mintuna kusan uku suka kwashe a haka sannan ya bude idanuwansa ya azasu a kanta
"Awa shida kawai?,ta yaya zan jurema wasu awannin da suka fi haka tsaho da yawa?" Ya fada da mugun taushin,salon maganar daya haifar mata da wata kasala da kuma wani yanayi na daban a zuciyarta,saidai ta share ta kuma danne,taso ta zame hannunta amma ya hana hakan faruwa,yaci gaba da riqon hannun nata cikin nasa.
^^^^^^^^^^Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke sanda ta fito daga wanka,gajiyar da bata jita ba a daxun yanzu tana sauko mata,ta bata kusan awa uku,tunda ta shigo dakin take waya da 'yan sannu da zuwa gami da zolaya a fakaice,su laila harma da afra,wanda wayar tasu ta sake qara mata kwadayin komawa makaranta,saboda ta bata labarin yadda aketa zuba karatu,don ba zasu jima ba zasu zana jarabawar qualifying su wuce zuwa ss three kai tsaye.
Tsaye tayi gaba mudubi sanye da towel hoodie robe fara tas,idanuwanta nakan kayanta data gama shiryawa tsaf na komawa makaranta tun kafin suyi wannan tafiyar,tafiyar data zame mata mabudi kuma mafari na kalolin rayuwa iri daban daban.
A hankali yake saukowa daga samansa hannunsa riqe da wayarsa yana dannawa,shima yayi wanka ya canza kayansa zuwa wata lallausar over size shirt da three quater wanda ya tsaya masa iya qaurinsa.
Karo na uku idanuwansa suka sauka a sashenta,ya sake canza akalar tafiyarsa zuwa qofar sassan,yayi knocking na wani lokaci,sannan yasa hannu ya murda handle din amma sai ya jishi a riqe gam,hannunsa ya daga yana kallon tafin hannunsa da ya danyi qura,mamaki ya kamashi,jikinsa kuma ya bashi lallai wajen ba kullewar dazu ko jiya bane,amma ina ta fita ba tare da izninsa ba?,ina taje?,bayan ya bar mata digits din da zata nemeshi?,bashi da wannan amsar,don haka ya juya yana barin wajen zuciyarsa na sosuwa,ransa kuma fal da bacin rai.
Samun kansa yayi da nufar sashenta,ya buda qofar ya tura,wannan sassanyan qamshin nata da ya kama sashen har yanzu yana nan daram,sai ya lumshe idanu yana nufar qofar dakin da yake jin tana ciki,tunda dashi tafi amfani.
Har ta gama igiyar robe din ta soma kwancewa taji an turo qofar dakin,sai ta tsaya cak cike da mamaki tana dubansa,don batayi tsammanin ganinsa a dai dai lokacin ba,tana ganin lokacine da zata sake tunda zaya zauna a sassansa.
Yana kuma kallonta yana sake takowa zuwa ciki,wani abu kuma yana narkar masa da zuciyarsa,wankan da tayi ya sake sawa fuskarta tayi fresh sosai,akwai sauran lema a gashin girarta da kuma gaban kanta,zuciyarta ta shiga bugawa sanda taga yana nufota direct,amma kuma sai ta gaza daga qafafuwanta har ya cimmata.
Dab da ita ya tsaya wanda taku daya zaiyi ya hade duk wata tazara dake tsakaninsu,a nutse ya daga hannunsa ya dora saman igiyar rigar,jaa daya yayi mata ta ware,rigar wankan ta fara ware kanta da kanta, tunda dama igiyar ke riqe da ita.
Cikin gigita ta sanya hannunta ta damqe gaban rigar,qaramin murmushi ne ya subuce masa yana duban idanuwanta da suka hautsine da tsoro,har yanzun da sauran aiki kenan ya raya a ransa,yana ci gaba da kallon nata ya zura hannunsa ta tsagar gaban rigar,bata ankara ba ta tsinci sassanyan tafin hannunsa saman cikinta saitin cibiyarta.
Cak numfashinta ya dauke na wucin gadi, kafin ta samu nasarar fusgoshi kuma hannunsa ya fara yin sama,har ya samu nasarar isa muhallin da taketa bawa kariyar,sai ji tayi ta ratsa hannuwan nasa a tsakaninsu da wani salo da ya sanyata dauke wuta.
Qugunta ya riqo da kyau sanda qafafunta suka soma rawa,ya matso da ita jikinsa sosai yana sanya hannunsa ya zare hannuwanta dake riqe da gaban rigar,sannan a hankali ya hada tafin hannunsa da ainihin fatarta mai santsi da laushi ya fara zame rigar gaba daya daga jikinta.
Qanqameshi tayi da kyau don hana faruwar hakan,ta tabbatar idan ya samu nasarar rabata da rigar komai zai iya faruwa,don babu wani abu daya rage a jikinta sai ita,cikin rarrabewar numfashi da yadda laushin fatarta ke shirin zautar dashi ya dora bakinsa saman kunnenta
"Don't scare,baccin gajiya kawai nazo muyi" sake qanqameshi tayi tsigar jikinta na tashi,bakinta na rawa tace
"Ammm.....bar.....bari na saka riga" dago fuskarta yayi da kyau yana duban tsakiyar idanuwanta da idanunsa da suka soma kaduwa,kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace
"Waye ya gaya miki saka riga ya halatta a irin wannan lokacin?,this is unfair....kamar ha'inci ne fa?,ya zaki lullubemin abun rufar da babu kamarsa a duniya da wata suturar da bata kama qafarsa daraja ba?" Ya fada cikin wani irin shauqi da baisan gana bayyana ba,ya kuma juye mata dukka nauyin maganganun hade da nauyin qwayar idanuwansa,gaba daya jikinta sai ya saki,ta runtse idanuwanta,tana sauraren yadda