Gurbin Ido Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   48 / 67

141K to 144K   out of 200.8K words

ta karanta abinda yake rubutawa a fuskar system din

"Daddy ka ajjiye don Allah muci abinci" sosai yaji dadin tayin data masa,don yunwa yakeji,ya kuma yo takeaway amma ya gaza ji,sai tattarashi yayi ya ajjiye,saboda kwata kwata taste din bai masa dadi ba,har yanzu taste din breakfast din safe yana jinsa akan harshensa,wannan yasa ya kasa jin dadin kome,amma kuma baison yarinyar ta fahimta haka,bayason raini,saidai kafin ya sake kowanne tunani amna tayi caraf da hannunsa,ta kuma riqeshi gam,babu damar ci gaba da aiki,dole yabar komai ya miqe yabi bayanta tana gaba janye da hannunsa.

Yankewa tayi kawai ta fara karatun bayan shigarta daki kada bacci ya dauketa bata karanta komai ba,har ta zauna sai kuma taji sha:awan shan gwanda,don haka ta miqe tayo kitchen,ta dudduba freezern gaba daya babu ita,da alama ta qare kenan,dama kuma last hisham ne ya siya ya bayar a kawo mata,ranta babu dadi ta rufe freezer din ta dawo daki,sai ta yanke kawai ta kirashi ta roqeshi ko zata samu wata,tana matuqar sonta.

A bakin qofar dakin amna ta sake masa hannu

"Daddy ka kirawo anty moon,yau tayi aiki sosai,zan dauko mana spoons da plates kafin ku qaraso,na iya zaka gani,anty moon ta koyamin" sai ta juya da hanzari ta bar wajen cikin zumudi ba tare data tsaya sauraren me zaice ba.

Da kallo ya bita har ta bacema ganinsa,baisan wanne irin qauna bace tsakaninta da ita ba,yana ganin zumudi sosai a fuskarta da farinciki duk sanda zasuci abinci tare,kansa ya girgiza yana sakin qaramin murmushi a fuskarsa sannan ya maida kansa ga qofar dakin.

Gaba ya matsa kadan ya dora hannunsa akan handle,sai a sannan ya tuna da abinda tayi masa dazun,hakan yasa ya qara hade fuskarsa,sannan ya murza qofar a hankali ya tura qofar dakin.

Tsaye take a gaban gadonta inda litattafanta suke ajjye,ta bawa qofa baya,sanye da farin high waisted skinny leggings da baqar armless robber shirt,gashinta data daure da siririn band mara fadi yana ta reto a bayanta,kanta babu dankwali,hannunta riqe a qugunta,ta kara wayar tata a kunnenta

"Ya hisham don Allah,Allah yasa ban takura ka ba" ta fada cikin karyar da murya,saboda batason matsanta masa da gasken,don dai batasan wanda zata kira din bane sai shi

"Kada ki damu matar yaaya,za'a kawo in sha Allah"

"Na gode sosai ya hisham,you are such a kind person" fusgar wayar da akayi da wani irin zafin nama yasa bata samu daman jin me hisham ya fada ba,sosai ta tsorata ta kuma juyo a razane,don ko kusa ko alama bataji shigowar mutum ba.

Dab da bayanta yake a tsaye,abinda yasanya ta kusa fadawa jikinsa kenan sanda ta juyo din,cikin sauri ta zare idanunta daga nasa,saboda wani kallo da yake mata,wani irin abu ne ke gilmawa cikin idanuwansa,yayin da qirjinsa ya cika da wani irin qunci fushi da kuma bacin rai,abinda ya sanya launin qwayar idanunsa canzawa kenan cikin qanqanin lokaci.

Taku biyu ya qara ya kawar da dukka tazarar dake tsakaninsu,fuskarta ta sauka tsakiyar qirjinsa saboda yadda ya bata tazara wajen tsaho,yayin da shi kuma habarsa ta sauka a tsakiyar sassalkan gashinta,da sauri tayi taku biyu baya saboda sake bata ratar daya hade a tsakaninsu,bata sauke diddigenta a qasa ba ya maara mata baya,sake jaa tayi da baya ya sake maida qafarshi inda ta sauke,bata gushe ba tana matsawa yana binta har ta qure da bangon dakin.

Idanuwanta dake cike fal da tsoro ta daga ta kalleshi,sai taji tsoronta ya ninka na baya,fushin data hanga saman fuskarsa da yadda idanuwansa suka sauya ya sake tsoratata,ci gaba yayi da aza mata kallonsa yana kuma sake hade gap din dake tsakaninsu,dab da ita ya tsaya ya daga hannunsa, abinda ya sanya maimunatu qanqamshe hannayenta tana jiran jin saukar duka ko mari,duk da batasan ainihin laifin data masa ba,amma wani sashe zuciyarta na gaya mata kashe masa wayan da kikayi daxu,ba abinda zuciyarta ke hasaso mata sai irin marin data taba karba daga wajensa shekarun baya da suka shude,da qyar idan yau ba za'a maimaita ba.

A hankali ya sauke hannuwan nasa yana morewa kallon fuskarta dake cike da tsoro,duk da idanuwanta a kulle suke amma hakan bai hana kyanta fita ba, siraran jajayen lips dinta nata motsi,koda ba'a gaya maka ba kasan kuka take shirin saki,bai gama wannan tunanin ba kuwa hawaye suka ratso rufaffen idanunta,bin hawayen yayi da kallo,sai yaja baya a hankali,ta gama karya lagonsa,baisan dalili ba bai kuma san me yasa ta shiga sahun mutanen da hawayensu ke saurin karya shi ba,ba abinda wannan ya tuna masa sai shekarun baya sanda ya mari marainiyar fuskarta,abinda ya tsaye masa a rai tun a wancan lokacin fiye da komai,zuciyarsa yaji tayi laushi,amma kuma bacin ran dake can qasan ransa har yanzu yana motsawa.

Daga hannunsa yayi yana kallon wayar da ya qwace din,number hisham din ce,sai ya danneta ya shiga wajen block yayi blocking nasa sannan yayi deleting number kwata kwata daga kan wayar,bai tsaya a nan ba ya sake shiga contact nata,numbers din dake kai ba masu yawa bane,duka duka na 'yan gidansu ne sai na wasu mutum hudu afrah besty teema ummu,numbers dinsa ya saka ya shiga wajen kira,number batayi appearing ba,alamu dake nuna cewa kenan bata da number dinsa?,yaja qaramin tsaki can tsakiyan ransa,sai ya samu kansa da yi mata saving number,ya kuma sanya mata full name dinsa

_*ja'afar marwan akko*_,ya daga kansa a nutse ya sauke a kanta,tana tsaye manne da bango kamar zai tsage ta shige,fuskarta duk danshin hawaye,sauka idanunsa sukayi saman qirjinta wanda shape dinsa ya fita sosai saboda robbern da rigar ke dashi,komai a zaune das sun kuma cika rigar,sai sama da qasa qirjinta yake alamun tsoro da kuma bugawar zuciya.

Yana son ya tsaida ganinsa a nan amma ya kasa,sai ya samu kansa da zarto da kallonsa zuwa faffadan qugunta,cinyoyinta sun fita sosai kamar babu ma wando a jikinta sai fatar jikin nata kawai kasancewar leggins din skinny ne ya zauna mata yadda ya kamata,zaka tsammaci ciko tayi musu don sun fita yadda ya kamata,kai kace zana mata qugun zuwa cinyoyinta akai

"Allah...." Ya fada can qasan ransa tsigar jikinsa tana tashi,wani irin mahaukacin kishinta karo na farko ya sauko ya lullubeshi,karon farko da tunanin yaya uniform din makarantarsu yake ya taso masa?,wando ne?,ko kuwa doguwar riga ce?,wanne irin kaya take sanyawa a matsayin house wear?,hannunsa ya dunqule ya kuma yarfar,ya cije lips nasa na qasa ransa na masa suya,shi kansa ya yadda dari bisa dari yana da tsananin kishi,bashi da sassuci ta bagarori da dama,amma tasha yi masa fada ya dinga sassautawa

"Open your eyes" ya fada da wata tattausar murya da maimunatu bata taba tsammani ba,cikin kokwanto ta soma bude idanun nata a hankali,tana gama budesun sabbin hawaye suna sake wanke mata fuska

"Ya salam" ya fada a boye yana jin yadda zuciyarsa ta wani irin harbawa ganin yadda ta narke gaba daya tana sauke sabon kuka,rarrabuwa hankalinsa yayi,baya son kukan,amma kuma baisan ta yadda zai rarrasheta ko ya tsaidata ba

"Keep quiet" yafada da kakkausar murya,tsai da kukan tayi cak tana qanqame jikinta waje guda,sosai ya hade fuskarsa

"Waya baki izinin yin waya da wani?" A mamakance ta dago kai ta kalleshi,duk da taso tsirashi da ido yadda yake mata amma sai ta gaza,tadan kauda idanun nata dake cike da lema,hisham dinne wani?,ta tsammaci ya duba yaga waye tunda ya karba wayar a hannunsa ai

"Don't let me repeat my question....." Ya fada yana jin siqewa a ransa,wani sashe na zuciyarsa kuma najin damuwa da zubar da hawayenta keyi amma kuna yana danne hakan,sai data kauda kanta gefe,cikin muryar kuka tace

"Yaa hisham ne"
"who is hisham?" Ya fada yana goye hannayensa a bayansa,har yanzu bai rabu da kallon baby face dinta ba,dan daburcewa tayi,saboda bata fahimci inda tambayar tasa ta dosa ba,duk da haka tayi dauriyar cewa

"Yaa Hisham dai....."
"Ba hisham qanina ba,koda ciki daya kuka fito dashi na sake ganin kuna waya sai nayi matuqar saaba miki?,kin fahimta?" Kai ta daga masa sabbin hawaye na fito mata,shuru yayi yaci gaba da kallon ta,haka kawai yaji baiso tsaiwar tasu ta yanke,kallon fuskarta kuma kamar yana qarawa lokaci gudu ne,tare da sanya wucewarsa nan da nan

"Me yasa kika kashemin waya dazu?,ni sa'anki ne?" Kamar zata kalleshi sai ta fasa,saboda yadda gaba daya ya dafa mata jiki da kallonsa,takejin kamar ba zata iya ci gaba da tsaiwa ba,zuciyarta kuma tayi raunin da bazata iya ci gaba da amsa tuhume tuhumensa ba,sai kawai ta soma sulalewa a wajen tana sakar masa kuka.

Baisan ya isa inda take ba sai da ya ganshi tsaye a kanta,ya duqa a hankali sai kuma amna ta turo qofan dakin da murnarta,turus tayi jin kamar sautin kuka,sauri ta qaro ta iso gaban maimunatu dake duqe a wajen ja'afar na tsaye

"Daddy kuka?,kaine ka sata kuka" Amna ta fada tana durqusawa a gaban maimunatu itama kamae zata fashe masa da kukan,rasa wacce amsa zai bawa yarinyar,ta fara qoqarin son dago kan maimunatu abinda yakeson yi kenan tun dazun,tambayarta take

"Anty moon,daddy ne?" Kai ta girgiza mata alamar a'ah,sai ta sake dagowa tana dubansa

"Daddy ka bata haquri.....ko zatayi shuru" wannan fa shi ake kira qaqa qara qaqa,sai ya debe hannuwansa zuwa aljihun rigarsa ya boyesu a ciki kamar baison wani ya gansu,a hankali labbansa suka motsa

"Am sorry" maganar ta fita da wani irin taushi da kuma qaramin sauti,sai ya juya a hankali yana barin dakin,amma kunnuwansa na ciki har sai daya fice.

62

Har suka gama cin abincin bata sake ba,tana ta juya cokali cikin abincin,har yanzu fuskarta babu cikakkiyat walwala,hakan yasa amna ta kasa sakewa.

Yatsun hannayensa ya hade guri guda yana duban amnan,ya tabbatar albishir din da zaiyi mata a yanzun zai sanyata ta ware

"Are you ready?" Kusan tare suka daga kai,saidai ita maimunatu ta basar kamar hankalinta bai wajen

"For what daddy?" Ta tambaya with full excitement tana kallonsa kamar wata babba yadda ta tambaya din,hannunsa ya sanya a aljihun rigarsa ya fidda ticket ya nuna mata

"Trip to Lagos" ihun murna ta saki harda miqewa tsaye,yadda ya zata din kuwa haka ne,nan da nan ta sake,ta fara zayyano masa ina da ina zasuje,yana zaune yana kallonta kawai,duk sai data gama murnar sannan ta zauna tana fadin

"Daddy,ins ticket din anty moon" shuru yayi, yarinyar ta iya tambayar qure,baisan me zaice mata ba,a hankali ya saci kallon maimunatu wadda har yanzu bata bar jagula abincin ba,kamar ma bata wajen,don fuskanta baiyi kama da wadda taji abinda amna ta fada ba,tunda ta taya amna murna ta kame kanta.

Da idanu ya yima yarinyar sign na ta tambayeta hadi da dauke kansa ya azasu bisa wayarsa,amma kunnuwansa suna saurarensu

"Anty moon.....zaki bimu nida daddy ko?,zai kaimu yawo sosai,zamuje har kifs beach garden,qawata tana ban labari suna zuwa ita da dad dinta duk sanda suka je".

Qaramin murmushi mara sauti tayi,tadan dafa kan amna

"A'ah amna......saura kwanaki mu koma school,banason nayi missing komawata makaranta" haka kawai yaji amsar tata wani iri,bai zaci zata ce hakan ba,amma sai ya basar yana miqewa daga wajen sanda amna ta soma magiyar ta bisun,da taga kuma ya tashi sai tayo wajensa,wai wayowa yayi,ya dora hannunsa saman kanta ya tofa mata addu'a sannan yace

"Ki kwanta anan amnee,ina da aiki da yawa da nakeso na gama kafin mu wuce" da yake cikin murna take sai batayi wani rigima ba ta yaddan,ya juya yana barin falon,yayi hakanne don baison ya sake shiga dakinta kada wani abun ya sake giftawa da zai hanashi cikakken bacci,don jiyan da qyar ya qwaci kansa.

Yana fita ta miqe tana gyara gurin,tayi mamaki sosai da yawan abincin da taga yaci,don kusan rabinsa shi ya cinye,tana aikin amna na sake mata magiya,sai data bar komai ta kama hannunta ta sanya cikin nata

"Kinaso a kori antynki daga school?" Kai ta girgiza da sauri

"Good girl,to kinga indai bakison hakan,dole na koma makaranta da wuri,next time sai muje tare"

"U promised?" Kai ta gyada,duk da bata da tabbaci tasan ta amsa ne kawai,amma kuma bata da mafitar data wuce ta amsa din.

Washegari gaba daya bai zauna a gida ba,ita kanta amna din bata ganshi ba kwata kwata,su biyu suka wuni,wannan ya sanya koda dare bata yi wani wahalar abinci ba,sai tayi musu jallop na taliya kawai wadda aka wadata da veggies,bayan sallar isha'i kadan amnan tayi bacci saman qafafun maimunatu suna tsaka da kallon wani film,sai falon yayi shuru saura ita kadai.

Shirye shiryen tafiyar shine ya tsaidashi yau a waje,bai dawo cikin gidan ba sai qarfe tara da mintina ashirin har da doriya na dare,har ya gota sassan unaisa sai ya dawo da baya,yayi knocking qofar,minti kusan daya sannan aka bude qofar.

Cikin matuqar girmamawa ta xube a qas tana gaidashi,daya daga cikin masu aikinta ne,masu aikin da ba'a nema izninsa ba kafin zuwansu gidan,abinda yasa ua dauke wuta kaman baisan da xamansu ba,ita kanta unaisan ba wani tunawa yake da lamarinta sosai ba bare wadanda ta ajjiye,komawa baya tayi ta lafe sanda yake shigowa,yana gama shigowa tayi wuf ta fita a sashen.

Zaune take saman three sitter dinta,tana sanye da doguwar rigar atamfa,sai dankwalin kayan dake aje a gefe,kanta dake cike da gashin doki da aka yiwa kitso tamkar nata yana a bude,ta miqe qafafuwanta tana kadasu,hannunta dafe da wayarta da alama chart takeyi,gefanta teburin glasa ne dake hargitse da ragoyin abinci gorar ruwa data lemo dukka da tasha.

Sosai tayi mamakin ganinsa a sassan nata,karo na farko kenan tsahon zamanta a gidan,duk yadda taso ta danne farinciki da mamakinta amma sun gaza boyuwa,tana daga zaunen tace masa

"Bismillah ga waje....." Ta datsi maganar tare da qwallawa dayan ne aikin nata dake cikin bedroom dinta tana gyaro mata shi kira,sai gata jiki na rawa,ta zube itama tana gaidashi,da hannu kawai ya amsa mata ba tare da ya dubi sashen ta ba

"Ki hado masa abinci da abun sha" ta bata umarni kai tsaye,sai ta miqe da hanzari ta fice,cikin zuciyarsa yake jin qyanqyamin maganarta,yar aiki?,ta kawo masa abinci da abin sha?,definitely batasan shi ba,batasan komai a kansa ba,ta yaya zai fara tsara zama da irin wannan?.

Daga kai tayi ta dubeshi still yana tsaye hannayensa saye a aljihunsa

"Have a seat" ta sake maimaitawa,tana jin wani dadi da izza tana shigarta,ko har ta fara cikin nasara ne ya biyota da kansa?,indai ko hakane lallai zata nutsu ta yanka qa'idojinta da sharudda wanda zasu dace da rayuwarta ba matsi balle takura.

Baice mata komai ba,yafidda hannuwansa daga aljihu tare da daurin kudi sabbi ya matsa gaba kadan ya ajjiye mata su

"I don't have your account digits....zan xanyi tafi....so koda zaki buqaci wani abu" sai ya ciro dan qaramin qawataccen complimentary card dinsa milk da aka yiwa ado da zaiba ya aje mata

"You can contact me" dauke idanunta tayi daga kan card din ta mayar fuskarsa,wani abu na mata yawo a zuciya,wannan tafiyar da yake fadin zaiyi a qa'ida ace da ita zai tafin,amma sai wani girman kai ya taso mata,meye nata na damuwa ko nuna zakwadin tafiya?,bayan sun zagaya duniya da kyau,kudi sosai daddynta ke fitar musu duk sanda suke son su fita wata qasar,kada ma tayi magana ya rainata yaga kamar so take yaje da ita ne, shikenan sai ta amsa tayin da haj Aaya tayi mata na zuwa inda itama kafin sun dawo,don haka ta koma ta jingina da kujerar tana cewa

"Allah ya kiyaye hanya" labbansa kawai ya motsa alamun amsawa,sannan ya juya yana ficewa daga sashen hadi da bar mata qamshin turarensa.

Ajiyar zuciya ta sauke sanda ya ida ficewar,ta lumshe idanu tana zuqar daddadan qamshin nasa,ashe yadda take hangensa da tsada daga nesa yafi haka wuyar samu ma daga kusa?,amma dai ko yaya ne ita ba zata sake bada kanta ba,zata ci gaba da amfani da girma da martabarta,har sai ya fahimta ya kuma kawo kanshi.

*******Tun da ta farka da safen amna ta kasa komawa barci,wai batason tayi barci daddy ya tafi ya barta,tunda yace flight din safe ne zasu bi, maimunatu nata mata dariya tana kuma shirya mata kayanta,dai dai da yadda tace haka daddy yake shirya musu idan zasuyi tafiya,ba wasu kaya masu yawa ba masu.kuhimmanci kawai ake dauka,sauran abinda basu da,yafi ganewa ya siya musu a can.

K'arfe tara da minti ashirin ta kammala komai harda break fast dinsu,ita dince kawai.batayi wanka ba,tun jiya bata ganshi ba,tana daki dai ya shigo sunyi magana da amna,kafin ta fito sun gama ya fita,kamar ta shareshi amma sai taga bai kamata ba,kodon diyarsa dake qaunarta,don haka ta dauki kwando ta shirya komai dai dai da yadda amnan zata iya dauka

"Muje na rakaki ki kaiwa daddy" daman zaman jira take,ta kuwa sauko da saurinta,maimunatu ta dauki kwandon suka fito tana tsokanar amna,kada dai ace daddy ya tafi ya barta,ta qyalqyale da dariya

"Daddy baya fadin alqawari fa ya saba anty" kai ya jinjina tana murmushin yadda yarinyar tasan halin mahaifinta,duk da shekarunta basufi hudu ba.

Daga second matattakala ta

48 / 67