A Rubucetake Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   33 / 33

96K to 97K   out of 97K words

qoqarin maida qwallar data cika masa ido,ya waiwaya gasu sajjad, identical twins masu kama daya

"Ku kuma mage da bera.......kun gama cakar da ita sai yau kukasan yaaya mimin taku ce?, nawwara harda ke?,ranar fa ina jinki kina cewa gwara ta tafi ta barki ki shaqata,ba wanda zanwa jaje ma sai hadizatu" yusra ta yunquro


"Daddy nifa..."kafin ya bata amsa al'ameen ma yace

"Nima daddy" duk sai suka bawa kowa dariya,kowa so yake ya nuna mimin tashi ce,shi kansa IG a sannan qarfin hali da dauriya kawai yakeyi.

Kusan duka motocin gidan aka dauka yiwa mimi rakiya airport,duk titin da suka ratsa sai ansan 'yar IG ce zata wuce,don qarqashin security suke har suka isa.

Sai da suka isa din IG abbas ya juya ya juya baiga widad ba,ya saki murmushi qasan ransa,yasan tana can tana kukan data ci masa alwashin ba zatayi ba,basu bar airport din ba sai da jirginsu mimi ya tashi sannan kuma sukayo gida.

Sanda ya dawo ya dinga bulayin nemanta cikin gidan amma bai ganta ba,daga qarshe acan part dinsa cikin qawataccen bedroom dinsa ya cimmata,ta gama kukan nata ta wanke fuskarta,tana tsaye gaban madubinsa tana laluben powder da takan ajjiye zata shafa.

Sunan hada ido tayi saurin janye idanun nata,ta wani hade rai tasha mur,ita lallai kada yace ta karaya sai da tayi kukan,dariya ta qwace masa ba tare da ya shirya ba,dariyar tasa ta qara raunata zuciyarta,yazo bayanta ta tsaya yana duban qwayar idanunta,sai kawai ta sakar masa kukan shagwaba tana fadawa jikinsa,shagwabar nan da har yau ba abinda ta rage masa a cikinta,bata ganin girmanta idan tana tare dashi,kamar yadda bata ganin girma da shekarun abbas din,har yau tana ganin kamar jiya jiya suka hadu,kamar jiya jiya aka daura musu aure,shi dinma kullum kallonta yake a mitsitsiyar widad din nan,shagwababbiyar ummu,mai yawan tsoro wauta da sakalci.

Ya zare babbar rigarsa ya ajjiye gefan gado yana murmushi,ya sanya hannuwansa duka ya ya lullubeta cikin jikinsa,ya sani daman,ba zata iya jura ba,kuma duk duniya a yanzu shi yafi kowa iya lallashinta,yadan hura mata iska a fuska kadan yana cewa

"Ai dama na sani,you can't take it......ke kuma da son yara,ai dama na shirya aikin lallashi" sai da yaga kamar kukan bazai tsaya ba sanann suka zauna,ya kama dukka hannayenta yana bata baki,daga qarshe ta buge da murmushi cikin jin kunya tana boye fuskarta saboda wata kalma da ya gaya mata,ya miqe shima yana dariya

"Nifa madam aiki yayi kira,ina tunanin nima yau da dare zanbi jirgi na koma abuja,ki taimakeni ki sallami baqinki kiyi qoqari ki biyoni,bana jin dadin gidan sam idan baki kusa" ta riga data saba,duk inda abbas din zashi sai ya ganta a gefansa hankalinsa yake kwanciya,duk inda zashi a nan nigeria ko a waje sai ya tafi da ita,tun tana zolayarsa harta gane haka tsarinsa yake,a jininsa qaunarta take,hafsat ta kasa fuskantar sa tun farko akan irin wannan tsarin nasa abinda ya fara kawo musu matsaloli kenan tun yana qaramin dan sandansa ana yawan masa musayar garuruwan aiki,shi mutum ne dakeson ko yaushe yaga yana tare da iyalinsa,bawai kasancewa ta auratayya ba, a'ah, at least ya dawo daga duk inda yake ya shigo gida ko masauki ya tarar dake,ita data fuskanci hakan sai ta bashi dukka rayuwa da lokacinta,shi kuma ya sakar mata ragamarsa.

Bashi da tsanani ko takura sam,mutum ne mai wani irin sauqin hali kawaici da kuma yawan bada uzuri,shi yasa idan kaga yadda sukeyi da 'ya'yansa da yadda yake mu'amala cikin gidansa abun zai daure maka kai sosai,ba zakace shine wannan namijin zakin IG din ba

"Zaki biyonin please?" Ya tambayeta cikin karya murya, dariya taso kamata

"Habba uncle.......ka girma fa,yau din nan ka aurar da diya ko ka manta?" Mur yadan sha

"Hakane fa,zaki biyonin?" Ya fada yana murtike fuska da murya,dariya ta qwace musu a tare saboda yadda yanayinma sam bai masa kyau ba

"Zan biyoka uncle,kusan zuwa anjima dama kowa zai wuce gida,na nesan ma gobe zasu tafi,amma ayimin alfarma zuwa jibi saina taho,zan sauka na duba jikin ummu daga can saimu siya wani ticket din,banason ma mu wuce jibin saboda yara duka zasu koma school suma,banason faashin makaranta" fuskarta ya kama yayi kissing goshinta

"Na gode,Allah yayi miki albarka,yadda kika kula dani da yarana da sauran dukka dangina,ina roqa miki aljanna madaukakiya tun daga duniya har zuwa lahira" murmushi mai sanyi ya qwace mata,ta kama button din rigarsa tana dan wasa dashi

"Kaine sirrin komai uncle,ka cancani fiye da haka,don ka zamewa rayuwata wani alkhairi,tun bansan meye rayuwa ba har na santa,Allah ya dawwamar da farinciki a rayuwarka yaci gaba da yi maka jagora,ya doraka saman maqiyanka,ya tabbatar da nasara a dukka rayuwarka"

"Ameen summa ameen wuddu na" ya fada yana jifanta da wani sassanyan kallo daya sanyata jin kunyarsa,saita fice tana cewa bari ya hado masa abinci,ta tabbatar jama'a basu barshi yaci ba,daga nan kuma ta duba komai ta samu yana tafiya yadda ya kamata,su amina su nujood Aafiya na'eema da muneera na kula da komai,don haka ta wuce kitchen ta dauki zababbun warmers din IG ta soma shirya masa abincin da kanta.

*Komai yayi farko yana da qarshe!!*


_Alhamdulillah,Alhamdulillah,Alhamdulillah,dukkan godiya ta tabbata ga Alla madaukakin sarki me kowa me komai daya aramin rai da lafiya har na kawo qarshen labarin A RUBUCE TAKE_

_thank you arewabooks followers for being with me all this while from beginning to end_🥰🥰👏🏽

_Godiya ga tarin masoya mabiya daga kowanne lungu da saqo na media,musamman wadanda basa gajiya da kasancewa tare damu da siyan rubututtukan zafafa biyar ta manhajar watsapp,Allah ya qara danqon zumunci da qauna mara yankewa,ubangiji ya kula da lamarinku_

*Abinda muka rubuta dai dai Allah ya bamu lada,wanda muka kuskure kuma ajizanci ne irin na dan adam,muna fatan Allah zai gafarta mana,ya yafe mana kusakurenmu mu daku gaba daya,sai Allah ya sake sadamu a rubutu na gaba da wasu ZAFAFAN LABARAN idan ubangiji ya bamu aron rai da lafiya*

*Na gode na gode na gode*

@team zafafabiyar

_subhanakallahumma wabi hamdika,ashhadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa'atubu ilaika_👏🏽👏🏽


33 / 33