Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
tare da sanin kowa a cikinsu ba,satin gaba kuma da zasuje bauchi hutu,zuwansu na farko bayan tahowarsu dukka gaba daya kaduna.
Daren da suka isa da qyar widad takai safiya cikin gidan,saboda wani birkicewa da tayi,an dasa ma zuciyarta wani mummunan tsoron gidan,kwanan zaune tayi tana rusa kuka,tana jin kamar ta fita da gudu tanar cikin gidan,wani irin qunci ne ya cika mata qirji,tana jinta kamar wadda aka jefa cikin dokar daji ita daya.
Sosai hankalin abbas ya tashi lokacin da ya biyo da asuba dubata ya sameta firgai firgai,tana ganinsa ta fada jikinsa ta saki kuka,tambayar duniya me yake faruwa ta gaza yi masa bayani,abu daya dai take fada
"Banason gidan nan uncle don Allah,ka kaini wajen hajiya ko gidansu nujood" ko fita a part din ta hanashi,bata wani damu da jarabar hafsat da zata iya biyo baya ba saboda zamansa a part din nata ranar kwananta,haka shima abbas din,ba wannan bane damuwarsa,abinda ya sauya widad din yasa ta firgice haka ke bashi mamaki,bayan yasan lafiya qalau suka baro kaduna.
Ko part din bai bari ba ya sanyata ta shiga toilet tayi wanka,wankan ma da da tace tayi idan sunje gidansu nujood yace aah,kafin ta fito ya shirya mata jakarta da kansa,ta fito ta shirya agurguje kamar wadda ake jira suka fito ya kulle mata sashen da kansa,yanata binta da kallo cike da mamakin abinda yake damunta.
Sai data shiga motar sannan yace mata yana zuwa,ya juya zuwa sashen hafsat.
Da sauri ta bar bakin window din,ta koma saman dining tana ci gaba da gyara kwanukan data zuba akai,duk da ba wani abun kirki ta dafa ba,a cewarta ta gaji,ba zata iya wani dogon aikin abincin safe ba.
Amsa sallamarsa tayi kamar bataga komai ba,ta daga kai tana dubansa,shima ita yake kallo, already ya saba ba kasafai yake gaidashi da safe ba,wani lokacin yayi mata gyara wani lokacin ya watsar da ita
"Zan kai widad gidan muhsin kada ki jini shuru"
"A dawo lafiya" ta amsa masa ba tare data dubeshi ba hankali kuma kwance,tana jin wani dadi yana ratsata,sai ya shafa kan yusra dake kwance cikin kujera sannan ya juya ya fice.
Yana fita taja wani mugun tsaki sannan ta saki dariya
"Habaaaaa yarinya,ki hanani sakewa a can a nan ma ki hanani?,Allah ya raka taki gona,da ikon Allah ma kin fita kenan ba zaki sake dawowa ba" ta sake rufe zancan nata da tsaki,tabar aikin da takeyi din ta koma saman kujerar tana karkada qafa,a duniya ita daya tasan yadda yarinyar tayi mata karen tsaye a rayuwa,duk yadda takai ga zuba iskancinta bata taba fuskantar matsala irin wannan daga wajen abbas ba sai yanzu,ta sake jan wani tsakin
"In sha Allahu sai nayi maganinki,bazan gaji ba wallahi" ta fadi a fili kamar ita da wani suke magana.
Kamar cirar qaya haka taji bayan fitarsu daga gidan,sai taji komai yana raguwa cikin kanta, nutsuwarta tana dawo mata a hankali a hankali.
Sanda suka isa gidan ta shiga ciki mamaki ne ya kama hajjaa,koda ta tambayeta lafiya?,ce mata tayi ba komai,kawai ta gaji da zaman gidanne.
Cikin mintuna qalilan ta sake sosai kamar ba ita ba,zuwanta ya yiwa yaran gidan duka dadi,ta ware sosai abinta,har zuwa sanda abbas dake setting room sunata hira da uncle muhsin,irin hirar da suka jima basuyi irinta ba ya tashi tafiya,ta miqe ta yafa mayafin abayarta ta fice don suyi sallama.
Idanunsa qur bisa qofar,kamar daman jiran isowarta yakeyi,ta yaye labulen ta shigo a hankali,saiya miqa mata hannunsa,ta kama a hankali ya jawota a tausashe yayi mata masauki saman cinyarsa.
Hannusa guda daya ya dora saman cikinta,kamar yasan me akayi yayi wani zillo,tadan motsa da sauri tana zare ido,don har yau ta kasa sabawa da irin wannan motsin,abbas da yaga irin yadda ta motsa sai ya saki murmushi
"Kin gani ko?,shi kansa yana cewa zaiyi kewar babansa,amma mamansa kamar bata damu ba" ya qarashe maganar yana langabe mata kai kamar wani maraya me neman agaji.
Yadda yayi din ya bata dariya,tadan saki siririyar dariyar data bayyanar da fararen haqoranta dake burge abbas sosai,ta saka hanuwanta duka biyu ta riqe kansa cikin tafukan nata tana dubansa
"Mamansa zatayi kewarka fiye da yadda shi zaiyi......"
"Amma me yasa kika zabi kibar gidan?,kinsan yadda nakeji duk lokacin da na juya cikin gidan naga babu ke a cikinsa?,widad.....duk gidan da babu ke a cikinsa shida kango daya suke a wajena.
,inji a zuciyata kina gidana wata babbar rahama ce a wajena,kallonki yana bani dukkan nutsuwa da zuciya da ruhi suke buqata.....ban taba kasancewa tare dake ba.....koda wata mu'amala bata shiga tsakanina dake baba tare dana samu nutsuwa ba" yadda yake tsara mata kalaman da yadda yake karanta mata su cikin kunnuwanta sai suka kashe mata jiki,ta matsa a hankali ta kwantar da kanta saman kafadarsa tana rufe idanunta gami da jin yadda bugun zuciyarta ya bugawa a nutse,irin bugun da bata samu irinsa ba daren jiya.
Ita kadai tasan irin yadda take fighting da wani mugun tsoro..... tsoro irin wanda bata taba jin irinsa ba..... qunci da damuwa da wata irin qaguwa na tabar gidan,ta matsa a wajen,tana jin kamar tana taka qayoyi a qafafunta duk sanda take taka kowanne sashe na gidanta,amma batasan ya zata gaya masa ba,ya zatayi masa bayani,tunda ita daya takejin hakan,ta sani tana addu'a kuma tana samun sauqi lokaci lokaci.
Sun jima a haka suna shan dumin jikin juna,kafin ya dagata yana duban fuskarta
"Gobe ne kwananki,zanzo na daukeki,babu cin bashi" narke masa tayi,ya dora yatsantsa saman labbansa
"I will bring you back,right?" Murmushi ta sakar masa sannan ta gyada kanta,tashin hankalinta dama yace zata ci gaba da zama har zuwa sanda zasu koma Kaduna.
Kwana daya tak tayi yazo ya dauki abarsa,hajja nata tsokanarsa ko surukuta babu?,bai amsa ta ba illa binta da yayi da miskilin murmushinsa.
Hafsat ta sake sosai ganin widad bata gidan,hankalinta kwancw tana ganin zata ci gaba da riqe abbas muddin suna bauchi saidai idan sun koma kaduna,a can dinma tunaninta ya fara karkata.....me zai hana tayi wani abu a kaine kwatankwacin abinda ke wakana yanzu?.
Sosai shawarar ta zauna mata cikin kai,don a yanzun da take zaune ita daya cikin gidan sai takejin kamar bata da sauran matsala a duniya.
Ba qaramin kaduwa tayi ba lokacin da ta fara jiyo qamshi na fita daga part din widad din,qamshin turaren wuta da na abinci duka lokaci guda,sam sam batasan sun shigo gidan ba,daga ita har abbas din,zuciyarta tayi wani irin nauyi,mamaki ya kusan kasheta
"Wannan wacce irin musiba ce" ta furta a fili kamar zata zunduma ihu,duk ta inda take hangen nasara sai alamun nasarar sun fara bayyana kansu sai komai ya rushe.
Kasa jurewa tayi ta aika yaran su gano mata abbansu yana nan,baya nan din don tunda ya ajjiyeta ya fita yace zaije ya dawo,saidai sun dawo mata da tsarabar lafiyayyen samosa da yaji nama carrot dankali da wadatacciyar albasa.
Samosan yana daya daga cikin abinda take mugun so,qyuya son jiki da rashin maida hankali a koyi girki yasa bata iya ba,duk da suna da komai na amfani a gidan da zata iya yi da kanta,sa'annan son kudi da son abun duniya kuma baya barinta ta siya a wani waje,saidai idan anci sa'a ta fita wani gurin sha'ani ta samu a can taci.
Duk sonta dashi yau din quncin zuciya da kuma tsanar widad din ya hanata ci,duk da yawan wanda ta bawa yaran,suka sanya abinsu a gaba suka cinyeshi tas suka sha ruwa,duk sai suka hau bacci.
*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*UCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 14
Tun daga ranar sai ya zamana duk sanda sukazo kadunan gidan hajja take sauka abinta,don a yanzun ta yiwa gidan hajiya qaura,mugun kunyarta takeji saboda cikin da yake jikinta,ranar da hajiyan tayi mata addu'ar Allah ya raba lafiya kamar zata mace a wajen saboda kunya,taso qwarai ma ya dinga barinta kaduna,amma yaqi,saboda hajiyan nayin fada duk sanda yazo babu ita,bugu da qari shi kansa bazai iya wadan nan kwanakin tana wani gari yana wani ba,a haka rayuwar taci gaba da juyawa,har suka share watanni uku,mugun nufin hafsat din bai cimma gaci ba yadda takeso take kuma tsarama ranta,saidai a wasu abubuwan da dama ubangiji kan yiwa bawansa talala ya barshi da zabinsa.
*_B A Y A N W A T A U K U_*
Sanye take da wata farar gown ta wani cotton material dake da wani irin ado mai qyalli na golden din zare,ta bude sosai daga qasan rigar,hade take da mayafinta mai dan yalwa,tana tsaye gaba madubin dakin nujood tana shafawa fuskarta farar powder,nujood din na saman gadonta daga bayan widad din,hannunta dauke da littafin da widad din ke karantawa,tana tsaka da karatun abbas yayi kiranta kan cewa zai shigo.
Yadda widad din keta qalqale jikinta yasa nujood ta kasa yin shuru
"Ni banga amfanin wannan qaqale qaqalen da kiketa yi ba,just yaushe kikayi wanka ma?,wannan skin din naki da baya riqe dauda kwata kwata?,a wannan kyan da cikinki ya sakaki kikayi indai baso kike ki matso muninki ba don Allah kibar face dinki haka" murmushi ya qwacewa widad din ta juyo tana kallonta
"Uncle abbas ne fa zaizo,ke waya gaya miki ana wasa da lokuttan da za'a kebe da miji,kin mance kishiya gareni?" Dariya sosai nujood ta kece da ita sai itama widad din ta saki dariyar,ta tashi ta zauna sosai saman gadon
"Ni wanna kishiyar taki ita da zero duk daya,kinsan Allah tun bankai haka wayo ba nake tunanin uncle abbas me aji,dan gayu wanda bai rasa komai ba.....me ya gani a tattare da wannan wai?,wai kinsan tun asalinta qazama ce?,da sallah abba yayi yayi muje gidan uncle abbas muqi,ya rasa dalili in gaya miki,baisan idan munje wuni muke da yunwa ba,bata iya dafa mana abinci saidai ta hadamu da kayan tarkace,ci banza ci wofi,ga uban wanke wanke da wankin undies da zata hadaka dashi" sauke hannuwanta data goya widad tayi tana jinjina kai,qazantar hafsat din ita kanta tana matuqar daure mata kai,harta kama jikinta,don ko kumbarta ka kalla kasan akwai burbushin qazanta a tattare da ita
"Allah ya kawo mata sauqi"
"Ai wannan ba zata daina ba har ta mutu"
"Banason wulaqanci,mamar yaran masoyina ne fa" widad ta fada tana jifan nujood da hararar wasa,saita fidda ido
"Wai yaushe kika zama rasa kunya ne?,komai naki uncle abbas,baki da aiki sai maganarsa?" Fararen idanunta ta juya kafin ta saukesu akan nujood
"Kin manta shine rayuwata?,a kansa na fara sanin soyayya qauna kulawa da tattali,a kansa na fara sanin rayuwa, ga kuma d'a ko 'yarsa a jikina" baki sosai nujood ta kama tana gwalalo ido
"Na shigesu,widad yanzu kinfi qarfina,Allah yasa dai nima gab nake da auren nan bare ki sani a uku" dariya suka sake qyalqyalewa da ita
"Wai nikam......mamar mimi tasan da cikin nan?,banji har yanzu ta nuna kowanne reaction ba" baki widad ta tabe,har zuciyarta bata qaunar zancan matar,ita a yanzun ta mijinta kawai takeyi
"Idan nace miki muna iya sati daya bamu hadu ba zaki yarda?"
"Haba dai?" Juyawa widad tayi tana zizarawa idonta kwalli
"Bata da aji gaba daya matar,da farko kallon mamata ma nakeyi mata,bana iya.musu ko qanqani da ita,ta cutar dani taso gurgunta rayuwata ta hanyar yin amfani da quruciyata,to a yanzun kuma meye yayi saura tsakanina da ita,ina kishin uncle sosai,shi yasa bana hada inuwa daya da ita,har muzo bauchi mu gama zamanmu bama sake haduwa sai a mota idan zamu koma,to me zai hada ni d........" Maganarta ta katse sanda kira ya shigo wayarta,ta duba fuskar wayar tana murmushi
"Uncle dina ya iso....."kafin ta daga wayar kiran ya katse,dai dai nan hajjaaa ta turo qofa tana gaya mata tayi ta fito ga uncle abbas dincan a setting room
"Saina dawo" ta fada rana zira wani plate white shoes na fata daya dace da qafarta
"Allah ya kiyaye hanya Juliet matar romeo"
"Babanki ne dai" ta amsawa nujood ta fice tana dariya,itama dariyar ta saki tana bin widad din da kallo,gaba daya rayuwarta da uncle abbas din burge nujood take,wata qauna da soyayya yake bata irin wadda bata iya boyuwa,duk inda kayi musu kallon farko zuwa.na biyu zaka fahimci hakan
"Ashe dama uncle din nan dan duniya ne" ta fada qasa qasa a fili tana dariya, saboda ta tuna sanda yake zuwa gidansu,tsakaninsu dashi gaisuwa,sai qarancin fara'a da kuma tsare gida da yake dashi,amma fa duk da haka dama can din shi mai kirki ne da yawan kyauta.
A nutse tayi masa sallama da sassanyar muryarta wadda ta tanadeta musamman sabodashi,kasa amsa sallamar yayi,saima ya miqe tsaye cak yana jiran isowarta.
Hannuwansa ya bata duka biyun,ya kuma jawota zuwa jikinsa yayi mata kyakkyawan masauki,ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi yana tura kansa cikin mayafinta da kyau,tare da shaqar daddadan qamshin da take fiddawa.
Ya jima a haka shi da ita suna jin dumin jikin junansu,kwana biyu tal amma yana jin kamar ya shekara ba tare da ita bane
"Ka zauna uncle" tayi qarfin halin fada,saiya dago fuskarsa ya hade da tata
"I missed you har bansan yadda zan kwatanta miki ba"
"I missed you too uncle" ta fada tana qanqameshi sosai,sai ya saki murmushi tare da ajiyar Zuciya gaba daya,yana jin dadin yadda kullum widad din ke sake zama cikakkiyar mace data karanci abinda yafiso da wanda bayaso,tamkar yana mata sharinga wani part na qwaqwalwarsa ne.
Ita ya fara zaunarwa sannan ya zauna a gabanta,ya dauko dukka qafafunta ya dora saman cinyoyinsa yana matsawa a hankali hadi da sauke mata wani narkakken kallo kamar zai cinyeta.
Kusan ta saba da irin wannan yanayin,duk da yana azama zuciyarta wani sabon naiyi ne,amma ko tace ya koma saman kujera ya zauna bazai zauna ba,yakance yana matuqar jin dadin hakan,duk da tana zaune sai data rusuna da dukkan girmamawa tace
"Barka da yamma yallabai"
"Barka kadai yallabiya maman biyu" saita zaro ido
"Uncle.....kanason na mutu ko?" Kai ya girgiza da sauri
"No.....idan kika mutu babynuncle......na tabbatar a ranar nima zan biki,just kawai ina sha'awar twince dinne,amma tunda bakiso shikenan" ya fada yana dariya cikin ransa,ta wani bata fuska kamar shine mai bayarwa ko kuma yace lallai twince din zata haifa.
"Ya bakaso dasu mimi ba?" Ta sake tambayarsa
"Ban qarasa gida ba,daga sokoto direct nan nayo.....ba zama ma zanyi ba,ki koma ki dauko abinda zaki dauko mu wuce gida" fuska ta narke masa sosai tana kallonsa
"But uncle.....a wajen mummyn mimi ya kamata ka sauka,kuma ma ka manta.....gobe fa na gaya maka zasu wuce kano anty madeena ta haihu,inason na bisu,i missed ummu alort,nayi missing kowa,abba na....su Aarifa da kowa"
"I know.....i know,bance kuma ba zakije ba,amma ina buqatar ki cike ragowar kwananki,kwana daya nayi miki aka kirani sokoto,kin tuna?" Baki ta turo masa gaba,a kwanakin gaba daya ciwon mara ne yake damunta,abunka da rashin kan gado fa rashin sanin makama irin na masu haihuwar fari saitake ganin duka takurarsa ne ya jawo mata,don kamar wanda aka qarawa qaimi a kanta,baya iya daga mata qafa a dukka kwanaki biyun da zaiyi a wajenta,shi kansa yasan tabbas tana qoqari,wannan ya qara mata matuqar kima da martaba mai tarin yawa a idanunsa,abinda wadda ta linka shekarunta ta gaza qanqanuwa da ita tana iyayi,kai bama ita ba,hatta da muhsin yanzun ganin girmansa yake qwarai da gaske
"Uncle a daina tuna baya fa"
"Wannan tuna bayan ya zama dole ai" ya fada yana lumshe ido,yana zagaye lips dinta da suka dan qara tudu kadan da yatsun hannunsa
"Nidai nidai"
"Baki zuwa?,sai naje na kaima mummyn mimi kwanan naki" ya dauka zatace bata yarda ba,don ya gama sallamawa kan yadda take kishinsa,saidai kishi ne irin na hankali da sanin ya kamata,wanda zakayi zaton wasu shekaru gareta masu yawa,amma sai yaji yace ta yarda.
Kicin kicin kuwa yayi,ya kasa ya tsare yace ta shiga ta fito yana jiranta,cikin sa'a Allah ya jefo da uncle muhsin,ya goya masa baya ya tayashi koro qaryarta,harda guzurin
"Kada ka yarda gobenma ta wahalar dakai,zasu biyo ta nan gidan su dauketa basai tazo ba".
A mota ta dinga masa fishi,bai damu ba ya biye mata kawai,ya yita yawo da ita ya cikata da qwalaman kayan toshiyar baki,bakin kuw aya tosu,ta tasa kayanta a gaba ta dinga ci,saidai a yau din bata wani ci da yawa ba taji ta qoshi.
Yau dinma bayan widad din kawai hafsat din ta gani sanda shiga sashenta,mugun kishin da takeji a ranta ba kasafai ma yake barinta take iya mata wani kallo mai tsaho ba,don duk sanda tace zata zurafafa kallonta