Nihaad Complete Hausa Novel

Author :  Khalisat Haidar Category :  Complete Novels

Chapter   49 / 96

144K to 147K   out of 286.3K words

kitchen take bata wannan boring labarin, wannan yasa ta tuna nasu mai aikin a can gida, warce ko magana bata son ya hadasu da ita ba kuma ta zama inda take saboda tana ganin ta fi karfin hakan kamar yanda Umma ta ke yawan sanar mata, and for the first time Nihad felt bad at the way she treated Hafsah back then, yau dai ga ta ita ma a gidan mutane ba gidansu ba tana cin arziki.... Khalil ya sauko downstairs yana danna wayarsa, yayi dialing number Usman, yana fara ring Usman ya daga, ya nufeta ya mika mata wayar, tuni Murja ta gaishesa ta bar parlon da sauri, Nihad ta amshi wayar ba tare da ta kallesa ba tana kallon screen din amma bata gane number waye ba, ta kai kunne, jin muryarsa a hankali tace "Ya Usman" Yace "Ya kike Nihad?" Tace "Lafiya lau, ina yini" yace "Alhamdulillah, hope you are doing fine, babu matsala dai ko?" Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace "Eh" yace "Ohk are you still using ur account?" Tace "Bani da atm card ne" yace "Toh ya kaiki banki ki amsa wani" Tace "Toh" Yace "Xan maki transfer a ciki yanzu" a sanyaye tace "To yaya Nagode" Katse wayar yayi, hawaye ya cika idonta ta rufe fuskarta jikin kujera hawayen na zubo mata, bata son taji tana jin haushinsu a rai sbda Umma because she love all of them, basu ta6a nuna mata ubansu ne kawai daya ba, shi dai Khalil na tsaye don bata basa wayarsa ba, bayan few minutes ta dago tana goge idonta ta mika masa wayar ba tare da ta kallesa ba, kallonta yake, zata ajiye masa kan kujera ganin yaki amsa yace "Kee" Sai a sannan ta kallesa babu yabo babu fallasa, yace "Da xan baki wayar saman kujera na ajiye maki?" Ita dai bata ce masa komai ba, ya amshi wayar ta mike ta bar wajen, ya bi ta da kallo har ta bace sannan ya fita daga parlon, washegari kuma ya bar Nigeria for Zanzibar in the morning. Ranan Talata Mami ta kira Aunty Maryam, bayan sun gaisa Mami tace "Maryam bakuwar nan ta tafi kuwa?" Aunty Maryam tace "Ehh ta tafi jiya" Mami tace "Toh maa sha Allah, banda dai yace a gidansu ya zauna ai yarinyar nan bai kamata a gansu tare ba balle har ya kawota nan gidan" Aunty Maryam dake sauraronta tace "Saboda me Mami?" Mami tace "Kika ce saboda me?" Aunty Maryam tace "Au... Toh Allah dai ya kyauta, Allah ya tsare mana zuri'a" Mami tace "Ameen" Aunty Maryam tace "Ai ko yan gidansu suna ta godiya" Mami tace "Allah sarki, yanzu hostel din zasu kama mata ta zauna kenan?" Aunty Maryam tace "Toh ban dai sani ba" Mami tace "Toh idan ba nan din ba suna da yan uwa a Abuja ne? In basu da kowa ai sai dai hostel din dama" Aunty Maryam tace "Haka ne" sallama Mami tayi ma Aunty Maryam ta katse wayar, Aunty Maryam ta fara tunanin ta ina za a fara convincing Mami?? Tun bayan tafiyar Khalil Zanzibar duk sanda Mami taje gidan Aunty Maryam a daki Aunty Maryam ke sa Nihad ta zauna har sai Mami ta bar gidan, idan kuma ita ke son xuwa gidan yayartata ita kadai take xuwa da Mus'ab ta bar Nihad da mai aikinta a gida, unlike before da har da mai aikinta take zuwa gidan, a cikin wannan kwanakin kuma mijinta ya sanar mata nan da kwana biyar xa su taho kasar da yake, ta rasa ta inda xata billo ma yar uwarta a kan Nihad. Ranan friday ta shirya taje can gidan, bayan sun gaisa da Mami a bedroom dinta, it took her like five minutes kafin ta samu kwarin gwiwan yi ma yayartata magana, Mami tace "Wani magana kuma ke tafe da ke? To Allah ya sa lafiya, ina jin ki" Aunty Maryam tace "Mami dama iyayen yarinyar nan ne suka kira jiya, suna neman alfarman ta zauna wajenmu don basu son xamanta a hostel, and i think lectures will be commencing in 2 weeks time" Mami dai kallon Aunty Maryam kawai take, Aunty Maryam tace "Toh ni kuma gashi nan da kwana biyar xa mu yi tafiya" Mami tace "Ikon Allah, to Maryam ke ko da ba tafiya xa kiyi ba ina ke ina rike yarinyar nan dama? Kuma ma da suka gaya maki haka ai sai kice barin kasar ma xa ki yi, sannan ni kuma da kika zo nan kika gaya min me kike son ince maki? Meye nawa a ciki?" Aunty Maryam tace "Amma Mami ke kam ba me mance alkhairi bace, bansan ki da manta alkhairi ba komin kankantarsa, ko albarkacin xama da suka yarda Khalil yayi a gidansu har na shekara daya ai bakya ce haka ba" Mami tace "Yanzu ya kike son ayi Maryam, ni dai kinsan baxai ta6a yiwuwa ince yarinyar nan ta zo gidan nan ta zauna ba, tsangwama da hantaran yan gidan ma kadai ya isheta balle aje ga shi matsalar da Khalil din xai shiga in har Abbansa ya samu labarin shi ya kawota gidan nan, a ina ya santa da har xai kawota gidansa, ku na lura yin abu ku ke kanku tsaye duk wani abun magana bakwa gudunsa, ke kinga da sararin zamanta nan gidan, kwana daya kadai da tayi kina ganin abinda ya faru" Aunty Maryam tace "Ni wallahi idan kina nuna shakkan matsiyatan gidan nan a fili abun kona min rai yake yaya, ita tsinanniyar Hasanar kike tsoro ko kuma Aminar? Haba Mami ko sau daya ke baxa ki kwatar ma kanki yanci ba, ke kenan baki son fitina ke kenan gudun abun magana, A haka rayuwar xai ci gaba? Yo Abun magana na nawa? Dubi tuggun da suka hada ma danki suka sa ya bar gidan nan kina ji kina gani baki iya buda baki kin tsaya kinyi defending dinsa ba shi da gidan ubansa, nima kika hanani magana a sannan, wannan wace irin rayuwace? Toh wallahi mu ba butulu bane, kuma ba mu mance alkhairi komin kankantarsa, in sha Allahu yarinyar nan bata da wajen zama tayi karatunta da ya wuce nan gidan, kuma wajenki tunda har iyayenta suka nuna mu ma sun yarda damu, sannan da iyayen nata basu rike shi khalil din ba Allah kadai yasan depression din da xai fada a lokacin, kana ji kana gani a kwace duk wani abu naka da ka mallaka, a amshe takardunka akan laifin da baka aikata ba, a toshe duk wani hanyar samun kudinka, sannan ace ka bar gidanku ba a son ganinka, infact garin ma gaba daya kada a samu information din kana ciki, ka tafi duk inda xaka tafi, me kike tunanin zai samu mutumin da aka ma hakan idan bai fada hannun na gari ba? Ni nasan zamansa gidansu really contributed wajen rage masa damuwarsa banda haka da baki gansa a yanda kika gansa ba yanzu, ai Allah ya tsine ma Hasana da Amina, ya walakanta su dai dai gwargwado, wato tunda ta kashe aurenta yau shekara kusan ashirin to bari naki ma ta kashe maki, ga agololinta ta cika gida da su suna ta baza mulki son ransu, wani abun ma sae ayi masu ba ayi ma naki yaran ba, to ai ni da xata burgeni ta auri Janar din kawai mana mu ga, for 20 good years kina daukan cin kashin matan nan kin kasa ta6uka komai, don dai kawai ni xamana ba steady bane a Nigeria amma wani abun da ba ayi ba wallahi, to gaskiya it's high time kema ki kwaci kanki ki daina shirun nan Mami, yarinya kuma duk shegiyar da tace Khalil ne ya kawota gidan nan kice karya take, bai santa ba bai ma ta6a ganinta ba, babu sa hannunsa a zuwanta gidan, dama ai kowa ya sanki da taimako to wannan ma duk cikin taimakon da kika saba yi ne, amma babu ta inda khalil ya santa, kawai haka za ki ce masu, sannan hantara da tsangwama da kika ce baxa ma su ganta ba balle su yi mata, dakin baki na nan bangaren xata zauna, da safe ta tashi ta tafi makarantar ta, ta dawo da yamma to a ina za su ganta? Duk sanda na shigo Nigeria yin wani abu ta dawo wajena har sanda xan koma, ba shikenan ba?" Mami dai kallon Aunty Maryam kawai take ta kasa cewa komai, sallama aka yi a parlon duk suka daga kai.



*Not too okay, ayi manage pls*

wa enda suka yi payment ban masu reply ba har yanzu su yi hakuri xan yi kokari inyi pls, those that checked on me i do really appreciate, Allah ya bar zumunci.





Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah



Ur evidence via

07087865788



42



*This pages is dedicated to Safiyya Usuman uwar Sultan, sauran kuma duk su ci kansu kandas ba mai ba yaji* >ØÝ







Umma tace "Ayya inna ai suna can garinsu da ita" a tsorace Inna tace "Garinsu? Ina ne garin nasu? Buzu ne fa, ba shi da wani gari da ya wuce Nijar, Nijar din ya kinkimi jikata ya kai kuna gani baku hanasa ba? ta ina zata fara da zafin saharar su, ga shi ance mana ana ta juye juyen mulki a can yau kwana da kwanaki, ni da Abubakar muna ta jimami" Umma tace "Aa Inna, garin zaria ya tafi da ita" Inna ta saki baki, can tace "Kan uba, ku ka bar sa ya tafi da ita wannan garin, ai duk Wan kano yafi karfin zama a can, Sannan da xai kai ta can din wani shegen ya bi su a cikinku??" Umma tace "Haba Inna, ai sun je sun dawo ya fi a kirga, Nihad fa ta sake fiye da yanda kike tunani Inna" Inna tace "Kai nima dai wallahi da na tsaya nake biye maki kamar wata er wiwi, maganina ma kenan, matsa ki ban waje wajen Ibrahim na zo ba wajenki ba, kai kuma Ibrahim wajenka na zo ba wajen Sumayya ba" Abba yace "Toh ya kike son ince Hajiya? Dama ana zuwa cigiyar wanda kulawarsa da komai nasa ya fita daga hannun iyayensa? Ai ni tuni na mikata garesa, alaqarsa da ita ya fi namu yanzu, don haka duk inda ma ya kai ta dai dai ne, ba ruwana, ba ruwanki, ba ruwan kowa" Inna da ta saki baki tana kallonsa tace "Yau ba lafiya, kace ba ruwanka Ibrahim?" Yace "Toh hanasa tafiya da ita xan yi?" Umma na murmushi tace "Banda abunki Inna mata da mijinta ki zo cigiyarta a gidansu, ita da gidan nan kuma ai sai dai ta kawo mana ziyara, idan aka ganta gidan nan yanzu ai ba lafiya kenan, kuma wallahi ko sati ba ayi ba sun zo gidan nan da shi sun mana sallama kafin su tafi Zarian wai garin mamarsa ce, kawai dai ba ku da rabon ganawa ne, amma yace ba jimawa xa su yi ba za su dawo, suna dawowa kuma da kaina xan je can gidan in dauke ki in kaiki gidan nasu" Inna tace "Toh wai ni shikenan nuna masa ku ka yi bani da matsayi ne da tun da aka aura masa ita daga shi har itan babu wanda ya taka yaje inda nake yace min ci kanki? duk da dai naje Bauchi kwanan nan na dawo" Umma tace "Au ashe dai kinyi tafiyar dai, to ki dai yi hakuri Inna, sun je ne baki nan, ki tambayi yan gidan kilan basu gaya maki bane da kika dawo" Inna tace "Kai Ibrahim fito za mu yi magana" Daga haka ta juya ta nufi kofa tace "Don ban ga xan iya magana gaban kwaSeSiyar nan ba" Abba ya mike ya bi bayanta suka fita, Umma ta bi ta da harara, can ta ja tsaki tace "A haka dai"

Ranan alhamis Aunty Maryam suka fara shirye shiryen barin Nigeria tare da mai aikinta da yaranta mata biyu da ke wani boarding school a nan Abuja, duk sai jikin Nihad yayi sanyi, the present of Aunty Maryam use to make her feel strong, it's making her move on with life, tana kara samun kwarin gwiwa har ta mance duk wata damuwar da take ciki and now she is leaving her, Aunty Maryam na lura da sanyin da Nihad tayi, and she felt really sorry for her, she wish she could do something about it, she wish xata iya tafiya da ita inda xa ta, daren Thursday Aunty Maryam ta idar da sallahn da take a sama ta sauko kasa ta karasa sauran kintse kintsen da bata yi ba a gidan don ranan Asabar za su tafi, har xata koma sama sai kuma ta tafi ta bude dakin Nihad duk da taga jiya bata yi tashin daren ba da ta leka ta, zaune ta ganta kan darduma ta hade kai da gwiwa, ta dago kai jin an bude kofar dakin, Aunty Maryam ta shigo dakin ganin idonta tace "Kukan me kuma kike Nihad?" Wasu sabbin hawayen suka ciko idonta ta kasa cewa komai, Aunty Maryam tace "Talk to me, why are you crying?" cikin rawar murya Nihad tace "Aunty you are leaving me... idan kika tafi kika bar ni i don't have anybody here" tana fadin haka ta fashe da kuka, Lokaci daya jikin Aunty Maryam yayi sanyi ta dagota ta zaunar da ita gefen gado tana kallonta cikin sanyin murya tace "Ke da zaki fara makaranta Nihad, sannan wajen yayata fa za ki zauna, she is also nice, you will like her so much, and Khalil is also there for you always" kuka kawai Nihad take don tasan idan Aunty Maryam ta tafi shikenan she might go back to her former self, there will be no one to encourage her anymore, har ranta bata son gidansu Khalil, she don't think she can cope staying there, ganin yanda take kuka Aunty Maryam ta jawota jikinta cike da tausayinta tace "Kiyi hakuri Nihad, bana son kina wannan kukan, ni ma ina son mu zauna dake kawai bani da yanda xan yi ne, but even with my absence baxa kiyi lacking komai ba" Kai kawai Nihad ta daga mata hawaye na sauka idonta, Aunty Maryam tace "Je ki wanke fuskarki ki zo ki kwanta" Tashi tayi a hankali ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta fito ta hau saman gadon amma wasu hawayen ne ke zuba idonta, mikewa Aunty Maryam tayi jikinta a sanyaye ta fita daga dakin, ita kanta tasan in dai ba khalil na gidan ba zaman gidan ba lallai yayi ma Nihad sauki ba, duk excuses da Mami ta kawo a kan dalilin da baxata riketa ba gaskiya ne, amma saboda babu wani option yasa Aunty Maryam duk tayi shunning excuses din. Washegari friday tana dakinta tayi dialing number Khalil, yana fara ring ya daga bayan sun gaisa tace "Baxa ka dawo weekend ba?" Yace "Ina airport yanzu haka, in sha Allah yau xan dawo" Aunty Maryam tace "Toh kana sauka ka daure ka fara biyowa ta nan gidana" Yace "Ohk, hope all is well?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Yaushe ne tafiyar Aunty?" Tace "Gobe in sha Allah" Yace "Ohk, sai na dawo in sha Allah" Sallama suka yi ta katse wayar, gaba daya ta kasa sauka gun Nihad don har ranta bata son ganin kukanta. Wajen karfe biyu zeenah ta shigo wajenta a daki tace "Ummi why is ur visitor crying since morning?" Aunty Maryam ta kalleta tace "Go and mind ur business please dear" Ta zaro ido tace "No i was only trying to show concern" Aunty Maryam tace "Je ki kira min ita" juyawa tayi ta fita daga dakin, Bayan wani lokaci sai ga Nihad ta shigo parlon Aunty Maryam tana tafiya a sanyaye, bata yarda sun hada ido ba ta zauna kasan Carpet, Aunty Maryam ta dinga kallon idanuwanta da suka kumbura, can ta sauke ajiyar zuciya tayi kasa da murya tace "Wajen yayata ne baki son zama Nihad?" Girgiza mata kai kawai Nihad tayi bata ce komai ba, Aunty Maryam tace "Toh ki gaya min inda kike son zama" cikin sanyin murya Nihad na wasa da gefen gyalen jikinta tace "Bani da inda zan zauna" Aunty Maryam tayi shiru tana kallonta cike da tausayinta, irin wannan yarinya karama haka ace wai an koreta daga gida, why? to yanxu da ba don Khalil din ya taho da ita ba da ya zata yi kenan, sai da ta shiga duniya kenan tunda gashi wai dangin mamarta basa nan, what a cruel world we are in, how comfortable is this her step mum now da tasa aka kori yar teenager haka daga gida saboda selfish interest dinta, lallai duniya abun tsoro, bayan few seconds Aunty Maryam tace "Je ki zuba abinci ki ci" Tashi Nihad tayi ta nufi kofa ta fita daga parlon. Karfe hudu saura Khalil ya shigo gidan ya tarar da Aunty Maryam dake parlonta a zaune, tayi welcoming dinsa ya zauna sannan ya gaisheta tace "Ya hanya?" Yace "Alhamdulillah" Kallonta kawai yake yana jiran ya ji kiran da take masa, Ta sauke ajiyar zuciya tace "Kjay, ina tunanin halin da Nihad xata shiga idan na tafi na bar ta a kasar nan, she's been crying since 2 days ago, i feel really sorry for, she is too young to be passing through all this, tana bukatar tausayawa da soyayya irin ta uwa, ban san yanda xan yi ba...." Kallonta kawai khalil yake, can a hankali yace "Aunty ba wajen Mami za ki bar ta ba?" Aunty Maryam ta girgiza kai tace "Kai ma kasan mun banbanta da Mami ta Sangarori daban-daban, yanda na jawota jiki har ta sake ta buda min cikinta Mami baxata yi haka ba, sanyinta baxai bari tayi hakan ba, ko me xa ayi mata a gidan kuma nasan iyaka Mami tace tayi hakuri, toh da wanda ya dameta zata ji ko da na yan gidanku KJay?" Khalil dake ta sauraronta yace "Toh meye shawararki Aunty?" Aunty Maryam tace "I am thinking of telling Abu Zeenah sai mu tafi tare da ita ™asar da za mu" Khalil was speechless at first, can yayi karfin halin cewa

49 / 96