Nihaad Complete Hausa Novel

Author :  Khalisat Haidar Category :  Complete Novels

Chapter   45 / 96

132K to 135K   out of 286.3K words

muna fitowa ta kama kuka wai ai wannan cin mutunci ne, ni kuma kasan halina bana daukar nonsense shine yasa ma na zo na sameka yanzu, yaron da a haife na haifesa? Sau nawa nake saka ka a gaba ina cewa kayi hakuri ka bar sa ya dawo gidan nan, shine zai dawo ya saka min da haka?" Abba dai yayi shiru yana safa da marwa a babban parlon nasa, Khalil ya jefa mata wani kallo ta gefen ido, Can Abba ya juyo yana kallonsa da kyau yace "Bata hakuri, sannan duk ka bi su bangarensu ka gaishesu kace masu ka dawo" Khalil ya kalleta a takaice yace "Yi hakuri" Daga haka ya mike ya fice daga parlon, Da ido Abba ya bi sa, Anty Hassana ta saki baki ita ma ta bi sa da kallo, Can ta kalli yayan nata xata yi magana yace "Tashi ki je Hassana, xan nemesa anjima idan na dawo" Aunty Hassana ta dinga kallonsa da mamaki, sai ma taga ya nufi wajen takalmansa ya zauna yana kokarin sa wa, tashi tayi daga karshe ta fice daga parlon kamar xata tashi sama, Khalil na fita ya koma bangaren Maminsa, Mami na tsaye tana kallon Nihad dake sa mayafin Mimi da ta amso mata, Mami ta fesa mata turaren hannunta tana kallonta tace "Baki taho da dankunne ba?" Nihad ta girgiza mata kai kawai, Gaba daya in ka kalleta sai ta baka tausayi, duk ta fita hayyacinta, Khalil dake tsaye bakin kofa kallon Mami kawai yake ya ma rasa abinda xai ce mata, lokaci daya jikinsa yayi sanyi don bai san what she is up to ba, Mami ta dauko ma Nihad wani dankunnen gwal mara nauyi ta mika mata tace "Sa wannan" Nihad ta kai hannu a hankali ta amsa tace "Nagode" sannan ta saka dankunnen, Mami ta dau nata mayafin ta yafa a shoulder tana kallon Nihad tace "Mu je" Nihad ta nufi kofar ta bi gefen Khalil ta fita, Mami na isa bakin kofar ya matsa a hankali ya bata hanya, makullin motarta ta mika masa tace "Mu je" Yayi karfin halin cewa "Where Mami?" Mami tace "Amshi makullin a hannuna ko?" A hankali ya kai hannu ya amsa, Mami ta fita Nihad na biye da ita. Har suka fito compound din gidan babu wanda suka hadu da a hanya kamar dai babu kowa gidan, Nihad ta dinga bin compound din da kallo, it's soo beautiful and big, Khalil ya nufi Ride din Maminsa yana tafiya a hankali, gaba daya ya rasa tunanin da xai yi, Mami ta dinga amsan gaisuwan da securities din cikin gidan ke mata, Nihad dai sai binta take tana satan kallonsu, back seat Mami ta bude tana kallon Nihad tace "Shiga" Nihad ta shiga motar a hankali, Mami ma ta shiga sannan ta kulle motar, bayan few minutes Khalil ya ja motar ya fita compound din bayan an bude masa wagegen gate din gidan, slowly khalil ke driving din har suka fita anguwan, sai a sannan yana kallon Maminsa ta madubi cikin sanyin murya yace "Where are we going Mami?" Mami tace "Take me to Maryam's house" Ya d'an sauke boyayyen ajiyar zuciya sannan ya nufi gidan Aunt dinsa, Nihad sai kallon anguwanni masu kyau take, amma kana mata kallo daya zaka san she is worried, suna shiga estate din su Aunty Maryam basu dade suna tafiya ba suka isa gidan, Khalil yayi horn bayan an bude gate din ya shiga yayi parking, Mami ta sauka tana kallon Nihad tace "Sauko" Nihad ta sauko, ta bi bayan Mami zuwa gidan, Aunty Maryam ta rungume Khalil tana welcoming dinsa cike da farin ciki tace "Idon son dina kenan nake gani haka?? Alhamdulillah ya Allah, Alhamdulillah" Murmushi kawai yayi ya gaisheta, ta amsa tana kallonsa daga sama har kasa, Lokaci daya er fara'ar fuskarta ya bace tace "Welcome son, Allah Ubangiji ya saka maka abinda aka maka" Murmushi kawai shi dai yake, Aunty Maryam na rike da hannunsa ta nufi parlor tana gaida Mami da ladabi, murmushi dauke fuskarta tace "Har kinyi Kumari yar uwa, Allah Ubangiji ya raba mu da mugun ji da mugun ganin" Murmushi kawai Mami tayi, Nihad dai sai kallon Aunty Maryam take don ita ma kana kallonta kasan halfcast ce, fara ce kal kamar Mamin khalil, sannan ita ma ga gashinta da tayi packing har kusan gadon baya, Aunty Maryam ta kalli Nihad don sai sannan ta lura da ita tace "Sannu da zuwa yan mata, shigo ki zauna" Nihad ta sauke kanta ta zauna kasa a hankali ta gaisheta, Aunty Maryam ta amsa tana Zaunawa gefen yayarta, tuni mai aikin Aunty Maryam ta cika gabansu da ruwa da lemo da kayan maqulashe, Aunty Maryam ta kasa daina kallon Khalil tana murmushi, she is so happy seeing him, can dai ta kalli Mami tace "Ya gida Aunty?" Mami tace "Alhamdulillah, kira mai aikinki ta shiga da bakuwar nan ciki ta bata breakfast naga bata wani yi a can gida ba" Aunty Maryam ta kalli Nihad tace "Ayya, to bari in kirata ta zo" Aunty Maryam ta kira mai aikinta a waya sai gata ta taho tace "Gani Hajiya" Aunty Maryam tace "Ki shiga da bakuwar nan guess room ki hada mata breakfast yanzu" Yarinyar tace "Toh Hajiya" Aunty Maryam ta kalli Nihad tace "Tashi ku je yan mata" Nihad ta mike a hankali ta bi bayan mai aikin da tayi wani bangaren daban da ita. Mami na kallon Khalil tace "Ko da za ayi sati admission letter din bai fito ba xata zauna nan har ta karba sannan ta koma gidansu" Khalil ya dinga kallonta ya kasa cewa komai, Aunty Maryam tace "Who is she Aunty?" Mami tace "Tare ya zo da ita" Aunty Maryam ta kallesa tace "Wacece ita din" yayi kasa da murya yace "Yarinyar mai gidan da na zauna a kano" Aunty Maryam tace "Allah sarki, Admission take nema nan din?" Ya gyada kai kawai, Aunty Maryam tace "Lallai ya yarda da kai tunda har ya bar ka da yar sa har ku ka taho tare, Allah Ubangiji ya saka masa da alkhairi" Khalil dai bai ce komai ba, Mami tace "Ameen" Mami ta kalli Aunty Maryam tace "Yaushe tafiyar naku, naji shiru baki ce komai ba" Tace "Ohh wllh yace sai yayi settling a can kafin mu bi sa, may be nan da sati biyu in sha Allah" Mami tace "Toh Allah ya kai mu" Aunty Maryam tace "Ameen" Khalil yayi kasa da murya cike da karfin yace "Mami about that video.... yan dakinsu ne a makaranta suka mata bata sani ba, sannan suka saki a social media... the Case is silently in court now, mahaifin nata yayi sueing dinsu gaba daya, so that's why zai canza mata makaranta yanzu, since the incident yake processing admission dinta a nan garin so coincidentally xan taho sai yace mu taho tare da ita" shiru yayi cause he him self knows he sounds so stupid, there is nothing making sense in what he is saying, Mami tace "Toh ni ka ji nace wani abu Khalil? Allah dai ya tsare mana zuri'a gaba daya, kawai ta zauna nan har sanda xa ta amshi abinda ta zo amsa sai ta koma gida, ae shikenan ko...." Aunty Maryam dake ta kallonsu tace "Wai me ke faruwa?" Mami ta sauke ajiyar zuciya briefly tayi mata bayanin abinda ya faru daxu da safe da yara suka shigo, Aunty Maryam ta saki baki da mamaki looking speechless, can ta kalli Khalil tayi kasa da murya tace "Wai kana nufin wancan ita ce yarinyar da video dinta yayi trending weeks ago?" Khalil bai iya yace komai ba, Aunty Maryam ta girgiza kai hankali tashe tace "Amma ta bata wayonta, tayi tarnishing image dinta a idon duniya, ta kuma yi ma kanta ta6on da goguwansa sae wani ikon Allah, duk yanda aka yi bata ji, banda bata ji meye zaki zauna daga ke sai skimpy inner wears a daki har maki video kina dariya, kai ai abun nan bai min dadi ba wallahi, Allah Ubangiji ya tsare mana zuri'a, amma wannan ta6on ai baxai gogu ba har tsawon rayuwarta sai ma ta tashi aure zata gane hakan barin idan tana da mahassada" Kallonta kawai Khalil yake baya cewa komai, Aunty Maryam ta rike ha6a cike da jimami tace "Kaii, sai kawai naji bata burgeni ba don bana son yaro mara kamun kai, don da tana da kamun kai da babu yanda xa ayi tayi abinda tayi, babu yanda xa ayi hakan ya faru da ita, wallahi ranan da naga videon ta sai da nayi tashin dare nayi addu'a Allah ya kare mana xuri'a da al'ummar Musulmi baki daya, abun sam babu dadi, gashi babu inda wannan videon bai je ba, kuma kun ga wllh ban ganeta ba ni banda kun yi magana, to ma banda abun uban nata ai aurar da ita kawai ya kamata yayi a yanzu ba wai ya sake biya mata makaranta a wani wajen ba, tana kanon ma a gabansu tana shakiyanci ina ga ta hadu da yan matan garin nan ai kuma sai abinda hali yayi, gata wata sumu sumu kamar bata magana... To kai garin yaya kasan mahaifin nata?" Khalil ya sauke idonsa kasa, Mami dai sai kallonsa take, Aunty Maryam tace "Kayi shiru" Ya dago ya kalleta a hankali yace "A sanda na sauka a kano bani da kowa bawan Allahn ya rike ni tamkar dan sa, yayi accomodating dina, yayi feeding dina without knowing who i am, mahaifiyarta mace ce mai kirki warce saboda ita nayi dadewar da nayi a tare da su, ina jin ta kamar ke da Mamina a gidan, yayyinta maza kuwa zaman mutunci da girmama juna muka yi da su, basu ta6a nuna min ni ba dan gidan bane, haka sauran yan uwanta mata dake gidan, abinda nake so ku gane, ba wai na je masu da real identity dina bane, i went der as a nobody, babu wanda yasan wanene ni har yanzu da nake maku magana banda ita yarinyar yanzu, amma suka min karamci a irin wannan zamanin da muke ciki, i know i can never repay them their good deeds, kuma yace in taho tare da yarinyarsa ta amshi admission letter saboda wani mistake nata sai in ki?" Aunty Maryam ta sauke ajiyar xuciya tace "Baxa ka ki ba kam, amma surutun yan gidan nan naku ake gudu" Mami ta kalli Aunty Maryam tace "That is it dear, abinda na guda kenan na kawota nan gidan har ta gama abinda ya kawota ta koma, banda mu da muka san wannan labarin da ka fada a kan gidansu yarinyar waye ya sani? Nobody, kai ko sun ji cewa xa su yi karya kake, don haka duk abun magana gudunsa nake nan da ka gan ni, daxun ma da suka shigo ba saboda Allah bane, gulma ce ta kawosu, yarinyar kawai suka zo gani, ita kuma wannan yarinya ta bata wayonta don waje daddaya ne xata je aki ganeta, Allah dai ya kiyaye ya tsare mana zuri'a, ya bata mijin da xai aureta yayi overlooking mistakes dinta ya rufa mata asiri duniya da lahira, da da mijin ma da auren kawai yayi mata ta ci gaba da karatun nata a dakin mijinta don hakan zai fi mutunci, Allah dai ya takaita mata gori a duk inda xata kasance" Khalil dai kallonsu kawai yake, Aunty Maryam tace "Ameen, da ganin wannan lamari kasan influence na bad friends ne hade da rawan kai irin na yaran yau, saboda haka ne ya kamata mu kara sa ma yaranmu ido sosai" Wayar Mami ya fara ring ta daga ta kai kunne, bayan sun gaisa tace "Lahh ai gani a gidan Maryam, kin fito ne?" Mami tace "Yauwa to, kawai ki taho nan din idan kin fito, shima yana nan ai" Daga haka ta katse wayar, Aunty Maryam na kallonta tace "Wacece?" Mami tace "Hajiya Safeenah ce" Aunty Maryam tace "Allah sarki, taji sauki kenan" Mami tace "Aa da sauki sosai, 3 days ago ma ai taje can gida wajena" Aunty Maryam ta mike tace "Bari inje in sanar ma mai aikin can tayi mata wani abun kafin ta iso" Daga haka ta bar parlon, Mami na kallon Khalil tace "Wai fasa tafiyar kayi yau Khalil?" khalil na danna wayarsa yace "Sai na shirya Mami" Aunty Maryam ta Wan tsaya kitchen din tayi assisting mai aikinta bayan da ta gama hada komai ta bar mata ta fito parlor, duk bata tarar da su a parlon ba, har zata wuce sama sai kuma tayi bangaren guess ta kara ganin Nihad, don kawai abun ya tsaya mata a rai tun daxu, bude kofar dakin tayi ta shiga ta ganta zaune kasa ta jinginar da kanta da gado, Aunty Maryam na kallon abincin dake ajiye tace "Baki yi breakfast din ba?" A hankali Nihad tace "Na koshi" Aunty Maryam tace "Toh fito parlor kiyi kallo, yara sun jogane kayan kallon nan din sai an gyara" Nihad dai bata ce komai ba ganin Aunty Maryam ta juya ta mike a hankali ta bi bayanta, har suka fito parlor tare, nan din ma a kasa ta zauna, Aunty Maryam ta tafi ta kulle kofa sannan ta wuce sama wajen Mami, Khalil na kwance saman kujera Mami na basa labarin abubuwan da suka faru baya nan, Aunty Maryam ta zauna kenan aka kira Mami, Mami ta daga tace "Kin iso ne?" Sai kuma Mami tace "To bari a bude" Katse wayar tayi tace "Kin kulle kofar parlon ne Maryam?" Aunty Maryam ta kalli Khalil da sauri tace "Dr ka bude mata kofa, yanzu kuma na kulle kafin in hauro" Ya mike ya fita daga parlon ya sauka downstairs, Nihad na zaune ta k'ura ma Tv ido duk da ba fahimtar abinda ake yi a ciki take ba, kallo daya yayi mata ya nufi kofar parlon ya bude, Da ladabi ya gaisheta yayi mata sannu da zuwa, da fara'a tace "Maa sha Allah, ka dawo lafiya Khalil?" Yace "Alhmdlh mum" Tace "Toh Alhamdulillah, sannu, Allah Ubangiji yayi maka albarka" Yana murmushi yace "Ameen" Sannan ya koma gefe ta shigo parlon, ya juya ya nufi inda remote yake ya dauka don rage volume din Tvn, a hankali Nihad ta gaisheta ta amsa da fara'a, Khalil Yace "Suna sama Mumy" Upstairs ta nufa, Kamar ance ya juya ya ganta ta jingina da kofar parlon tana kallonsa tana murmushinta me kyau, wara ido yayi kafin yace komai ta taho da sauri ta rungumesa ta lumshe ido a hankali tace "I have missed you so much" Daga kai Nihad tayi ta kalleta, shi kam yayi stiff a wajen da yake duk ya daburce cause she took him unaware, Lokaci daya ta lura da Nihad dake wajen da sauri ta sakesa ta koma baya tana mata murmushi tace "Sannu, sorry i just badged in, Assalamu alaikum" Nihad dake kallonta daga sama har kasa ta dauke kai kawai, Khalil ya bude palm dinsa with surprise yace "But you didn't say u are coming with Mum" Ta langwabar da kai smiling at him tace "Surprise" Kallonta kawai yake, a hankali hawaye na taruwa idonta tace "I missed u so much..." Ya mata wani kallo yace "Come off it dear" Lokaci daya Nihad ta mike ta fice daga parlon zuwa guess room da take ciki daxu, Nadeeyah ta bi ta da kallo, sai kuma ta kallesa tace "Dear Wacece ita? Ko dai taji haushin yanda na shigo ko? Wallahi i was just overwhelmed" Khalil ya daga kafada yace "No, kece dai kika ga haka...." Tace "Ohk, tayi hakuri in ma taji haushina ne, where is Mami?" Ya nuna mata sama tace "Let me go and greet her" yace "Ohk dear" Tana barin wajen ya bi ta da kallo har ta haura sama.....







Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah





Ur evidence via 07087865788





Assalamu alaikum manyan mata!!



For your Egyptian Abaya's, mad gowns, laces and handbags and all sort of jewelries... Give me the privilege to be ur plug plss, and u will never regret it>ØpÝ





Join my WhatsApp group for beautiful samples.



Contact https://wa.me/c/2349090591769





39



Bayan Azahar Aunty Maryam ta sakko downstairs tana kallon mai aikinta dake parlor tace "Kin kai ma bakuwar can abinci kuwa?" Mai aikin ta tashi da sauri tace "Wallahi na manta Hajiya" Aunty Maryam ta saki baki tana kallonta tace "Amma ai baki mance naki cikin ba" Da sauri mai aikin tayi hanyar kitchen, Aunty Maryam ta nufi guess room, bude kofar dakin tayi taga Nihad zaune saman darduma, Aunty Maryam ta shiga dakin, Nihad ta daga kai tana kallonta, Aunty Maryam tace "Kiyi hakuri ashe wancan gantalalliyar bata kawo maki abinci ba ni ina can sama ban sani ba" Nihad dai tayi murmushi kawai bata ce komai ba, Aunty Maryam tace "Me yasa kika ki zama parlon kiyi kallo?" A hankali Nihad tace "Ba komai" Aunty Maryam bata kuma cewa komai ba, Sai ga Murja ta shigo da abinci dakin ta ajiye ma Nihad, Aunty Maryam na kallonta tace "Ki karo lemun" Da sauri Nihad tace "Aa ya isa Aunty" Aunty Maryam tace "Toh zuba abincin ki ci" Daga haka ta juya ta fita daga dakin, All through Khalil na compound wajen shan iska tare da Nadeeyah, kana ganinsu kasan they really missed each other, abincin ma waje aka kai masu suka ci tare, bayan Nadeeyah ta zuba masa drink din kwalin gabansa yana kallonta yace "Thank you" Tayi murmushi tace "Continue... ina jin ka" Ya Wan buda ido yace "Me xan ce kuma,?" Tace "Ba labarin stay dinka a kano kake bani ba, ai baka gama ba" Yayi murmushi yana shafa kansa yace "Shikenan, all the household are very nyc, i think that's the most important of all" Tace "To ita wannan yarinyar da na ganku tare, yar gidan ce?" Yayi shiru, sai kuma yace "Nihal!! Of course yarinyar mai gidan ce..." Nadeeyah tace "Allah sarki, wani school take?" Yace "Ahmadu Bello" Nadeeyah tace "Ohk, but kasan har yau yan gidanku basu san inda kake ba all those while, a lot of time Farhana da Sajida suna yawan tambayata about u, irin dai suna

45 / 96