Chapter 11 Reading Gidan Rina Auren Tilas by Jidda Aliyu HN Novels

Gidan Rina Auren Tilas by Jidda Aliyu

Author :  Jidda Aliyu Category :  KDP NOVELS

Chapter   11 / 26

30K to 33K   out of 76.6K words

ya kwanta akan kujera, ya minmik'e k'afafu, yana lumsashe idanu ga alama
bacci yake so yi.
"Yalla6ai ba dai bacci bayan la'ssar za ka yi ba?"
Ya bude idonshi d'aya yayin da d'ayan yake arufe, ya kalleta yana murmushi sosai
yana yin da yake kallonta ya haddasa mata fad'uwar gaba, ba shiri ta dauke kanta da
bari kallonshi.

Shima ya dauke idanuwanshi daga kallon nata yana fad'i "Ke dai ki ce kin Kagara ki
je gida ki ga Abba.
'Yar siririya dariya tayi mai ban sha'awa tsayawa ya yi yana kallon bakinta yanda
sauti dariya yake fita daga cikin.

"Ta tsagaita da dariyar ta ta, ta ce banida laifi Yalla6ai kaine ka saka min
ra'ayin son zuwa gida, don haka bacci bai ganoka ba ka zo mu tafi tun kafin na fara
tsandara maka kukan ido d'aya.
Sosai furucinta na k'arshe ya bashi dariya da yake shi ba gwanin dariya bane,
sai kawai ya yi murmushi mai sautin gaske kafin ahankali ya ce "oh.....haka ne?
Ai kuwa kin d'ebo ruwan dafa kanki don sai kiyi min kukan ido d'aya, za ki ga Abba.

"Dauke kanta tayi tare da rufe bakinta da tafi hannunta.
Da gaske fa sai kin yi kukan ido d'aya.
ya k'arasa magana yana turo baki kamar k'aramin yaro.
"Ba shiri ta taso ta durk'usa gabanshi ta had'e hannayenta wuri d'aya ta ce "don
Allah Yalla6ai ka rufa min asiri da wasa nake.
"Murmusawa ya sake yi kafin ya mik'e batare da yasake magana ba, ya ra6ata ya haura
upstairs ya sauya kayan jikinshi zuwa shadda as usual fara tass......har da saka
hula zanna bukar.
k'afarshi sanye da loafers shi ma white in colour.
Yana fitowa ta ragu da d'an gudunta ta dauka handbag, sai murna take za ta gida.
Parking lot suka nufa suna tafiya side by side kallo d'aya za ka yi musu kagano
sunyi bala'in dacewa da juna.
"Tun kafin Isah ya gama parking ta balle k'ofa za ta fita, karaf ya rik'o palm
d'inta yana mata shegen kallon nan nashi na k'asan ido.
Batasan lokaci da ta rausayar da kanta tana kallon k'ofar shiga apartment d'insu,
wannan shi ake kira ga k'oshi ga kwanan yunwa.

"Hey.....barrister stop act like small girl, kina gudu kamar wata 'yar baby.
"Dauke kanta tayi ta ji wani irin mugun kunya ya lullu6eta, ya saki hannunta
tak'arasa fita.
Tana fitowa khalil da Khalid da ke fitowa daga cikin gida suka hangota, da gudu
suka rungumeta sai ihun murna ganinta suke, Khalid ya d'agata kamar 'yar baby sai
juye yake da ita yana sauke ta Khalil ma ya d'agata, k'arshe ya direta ya kar6i
handbag d'inta suka nufi cikin gida.

"Aliyu da ke tsaye a jikin mota ya yi folding hannayenshi a k'irji, sai kallonsu
yake yana murmushi, har sun yi kusan shigewa cikin gida sai ya ga twins d'in sun
juyo yayin da barrister ta shige ciki.

Wurinshi suka nufo suna murmushi, khalil ne yafara mik'a masa hannu yana fad'i
"sannu da zuwa Yalla6ai!
Uhmm......sannunku twins ina kallonku za ku karya min mata.
Dariya suka yi shima yana taya su ta hanyar murmushi, shoulder Khalid ya dafa ya ce
twins ya karatu?"
Alhamdulillah!
Suka had'a baki.
Mu shiga daga ciki Yalla6ai kada matarka ta tuhume mu mu bar ka a tsaye.
"Shiru Aliyu ya yi yana shafa geminshi, jerewa suka yi zuwa cikin gida.
A babban falo suka tararda ummi barrister A tana kwance a jikinta, duk ta
makalk'aleta.
Shigowar Aliyu yasa ta tashi a kunya ce sai faman gyara veil d'in kanta take yi,
gaida Ummi ya yi ta amsa cikin fara'a barrister A ta mik'e ta shiga kitchen da
kanta ta kawo mishi ruwa da lemo duk tasan ba sha zai yi ba.
sallama ya yi da Ummi akan sai k'arfe 8:00pm zai dawo picking d'inta, sosai hakan
ya yi mata dad'i har k'ofar fita daga falo ta rakashi.
*****"""*****""""****

Kamar yadda ya yi alk'awali 8:00pm a gidan tayi mishi, yana tsaye jikin mota sai ga
khalil ya fito daga cikin gida za shi parking lot Abba ya aike shi ya dauko mishi
wasu documents a mota.
Shaking hands suka yi kafin ya dauko aike da aka yi mishi ya jagorance shi suka
shigo cikin gida.
"Gaba d'aya ahalin gidan suna zaune, ya durk'usa har k'asa ya gaida Abba, cike
da fara'a Abba ya mik'e masa hannu cikin jin kunya Aliyu ya yi musabaha da shi.

Nasiha Abba ya shiga yi musu akan zamantakewar aure, sai kuma dadd'a k'ara bashi
amanar barrister A.
"Hakan yasa Aliyu ya ji jikinshi ya yi sanyi.
Gaba d'aya har Abba suka rako su wurin motasai kuka take, Abba ya rik'e hannunta
kamar ba zai saki ba, ta gefen ido Aliyu yake kallonsu "the thing looks very funny
musanmman yadda Abba ya yi da idanu kamar shi ma zai yi kuka.
Saida suka ga fitar su daga gidan, sannan suka juya cikin gida.
Suna tafiya tana share 'yan hawayenta ji take kamar ta ce ba za ta bi shi Abuja ba
yabarta Yola, ta dinga gani parents da siblings d'inta.
"Ya waigo suka had'a ido ya daure fuska tamau....kaman ba shi bane yanzu nan ya
gama murmushi ba, ya fito da handkerchief daga aljihunshi ya mik'a mata yana cewa
common wipes that tears before I loosing my control na bige miki baki, kanki aka
fara aure da za ki cikawa mutane kunnen I hate cry in my whole life" musanmman irin
naki na rashin dalili.

"Hannunta na rawa ta kar6i handkerchief ta goge fuskarta, har da fayyace su
majina ya yatsina fuska ya d'an buge shoulder ta ya ce k'azamar banza wannan
handkerchief yana zamanki, don ni ba abinda zan yi da shi.
Kunya ya lullu6eta har suka iso gida ko kwakwaran motsi takasa.

Har ta juya za ta shiga d'akinta ya tsaida ta ya ce "ki shirya luggage dinki sai ki
zo ki shirya min nawa, banaso mu yi latti morning flight za mu bi.
"Ta gyad'a kanta sai kusan 10:18pm ta gama shirya kanyata, ta gaji sosai dole ta
wuce bathroom ta watsa ruwa masu zafi ko za ta wartsake daga gajiya.
"Cotton night gown tasaka mai spaghetti hands pink colour, ta sauka iya gwiwarta
ta zura hijab mai hannu yana ja da k'asa ta nufi d'akinshi.
Tana tura k'ofa yana tsaye jikin window daga shi sai wando sleeping dress bai saka
riga ba, har ta juyo za ta fita ya ce "ke....banaso shirme zo ki yi aikinki nida
gidana ba za ki hanani shan iska ba.
A kunyace tadawo ta bud'e closet tana fitowa da suits dinshi tana sakawa a trolley,
ahankali take satar kallon jikinshi cikinshi a shafe ga six packs dinshi a jera,
muscles d'inshi a murd'e Aliyu giants man ne yana cikin maza masu inverted triangle
body, ta Kalle yadda wandon ya zauna a waist dinshi kamar wani modeling.
"Yasaki curtain ya zauna akan resting chair ya dauki system d'inshi, yana dan-
dannawa ita kuma tana aikin had'a mishi luggage.
"Gyagyad'i tafara bata ankara ba bacci ya yi wuf....da ita hannunta rik'e da
boxer dinshi
Hankalinshi ya dauku sosai ga aikin da yake shiyasa bai lura da ita ba, tsawon
lokaci ya dauka yana sarrafa laptop atunaninshi ta gama had'a kayan ta fice sai da
safe ne kawai bata yi mishi ba.
Doguwar hamma ya yi had'e da mik'a waigowar da zai yi ya ganta zaune a k'asa ta
kifa kanta a gefen gado, ga boxer d'inshi akan fuskarta dad'in bacci yasa ta ya6a
boxer akan fuskarta.

Zaro idanuwanshi ya yi cike da mamaki ya tashi ya nufi wurinta, ahankali ya ciro
boxer ya k'ura mata ido baccinta take yi hankali kwance.
Bai san lokaci da ya tintare da dariya ba abinda bai cika yi ba.




Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:01 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*


*22*

Ya shiga bubbuga hannunta yana kiran sunanta ahankali, ko motsawa ba tayi ba.
Cigaba da tashe ta ya yi hey.....barrister wake up go to your
room...hey....hey...wake up!
Barrister nace ki tashi ki tafi d'akinki nace ki tashi mana don't tested my
patience.
Ya k'arasa magana cikin shouting firgigit tayi tana kallonshi, sai kawai ta sulale
akan tiles ta cigaba da bacci abinta.
Omg!
Yafad'a dafe da goshi duk yadda yaso ya tashe ta abin yaci turu dama barrister
akwai nauyin bacci.
"Tilass....ya dauketa cak ya aza akan gado ahankali ya cire mata hijabin
jikinta, gashinta yarufe mata fuska, ya tattare shi ya mayar mata da shi baya ya yi
tsaye yana kallon yadda numfashinta ke sauka k'irjinta na up and down, boobs d'inta
na wani d'agowa ga shatin two nipples d'inta da ke cikin night gown kamar su
tsokane mishi ido.

Gogan naku baisan lokaci da ya hadiye yawu ba, wannan shine karo na farko da yata6a
k'arewa mace kallo.
Da sauri ya runtse idanunshi ya shiga waresu ahankali, he was still staring at her
ya durk'usa gefen fuskarta wearing a killer smile, wanda shi kanshi ba zai ce na
menene ba.
Ahankali yasa two soft hands d'inshi ya d'an gyara mata kwanciyarta.
"Ya zagaya gefenta ya kwanta ya dauki three pillows ya yi musu tsakani, kamar
jira take ya rufe idanunshi tafara wani shegen snoring a firgice Aliyu ya bud'e
idanuwanshi, don tabbatar ita ce take snoring ya lek'a fuskarta duk da d'akin diff
light ne bai hanashi, hango yadda snoring d'in ke fita daga bakinta ba.
A tsoro ce ya janye yana dafe goshi mik'ewa ya yi ya nemo auduga ya toshe
kunnayenshi, ya ja duvet ya rufe jikinshi can cikin bacci ya ji ta fincike duvet
d'in ta rufawa nata jiki, hakan ba k'aramin k'ona mishi rai ya yi ba.
Afusace ya fizge duvet ya girgiza shoulders ta ya ce ke tashi maza ki barmin
d'akin.
Ba zai yu ki hanani bacci ba nida d'akina.
wani juyi ta yi ta cigaba da baccinta.
"Mtsss....ya ja tsaki yana hararata ya kwanta can tsakiyar dare har baccinshi
yafara d'adi yaji wani shegen kick a d'uwawunshi, ya tashi atsoroce cikin angry
face yake kallonta.
"Ya rabbi help me this girl gonna kill me, yafad'a dafe da goshi ya sauka daga
gado ya jefa mata bargon yana fad'i gashinan ki cinye duvet d'in mayya kawai.
Kan resting chair ya koma ya kwanta sannan ya sami bacci saidai ba mai dad'i ba
Kiran sallar asuba ne ya tashe shi, ya tashi yana dafe goshi, sakamakon rashin samu
wadattace bacci ya jawo mishi headache ya juya ya kalli kan gado sai sharar
baccinta take yi.
Ta rungume pillow a k'irjinta.
Dauke idanuwanshi ya yi daga kallonta, ya mik'e tsaye da kyar yana rangaji ya
shiga bathroom.
Ya dauro alwala canza kayan jikinshi zuwa farar jallabiya, da farko har ya yi niyar
ya yi tafiyarshi masjid ba zai tashe ta ba, sai kuma ya ga rashin dacewar hakan.
"Cike da mugunta ya zuba mata wani shegen duka a gadon baya, saida ta gantsare
kafin tayi nasarar kwalla jahilin ihu mai barazanar doshen dodon kunne Aliyu.
"Da sauri ya fice daga d'akin yana murmushin mugunta.
Fitarshi yasa tadawo da natsuwarta ta fahimci idan take, sosai mamaki ya rufeta da
ta tuna abinda ya kawota d'akinshi har bacci ya dauketa.
"K'ayattace murmushi ta yi ta d'an bige bayan k'eyarta, sai kawai take ji wani irin
nishad'i ta jima sosai tana blushing kamar wacce aka yi wa albishir da mallakar
zuciyar Aliyu....lol.
Jin footsteps dinshi ya nufo d'akin yasa ta mik'e da gudu ta shiga bathroom, koda
tafito har ya shigo yana zaune akan resting chair closing his two eye's ta kalle
shi asanyayye kafin ta dauki hijab da praymat ta yi sallah, tana gama sallah ta ce
"Ina kwana Yalla6ai?"
Ya bud'e idanuwanshi masu cike da bacci, saida ya yatsine fuska kafin ya ce
banganshi ba.
Zaro manyan idanuwanta tayi masu kamar da an diga mata zaiba, tana kallonshi ba ki
bud'e.
Kafin tayi magana ya katseta ta hanyar cewa tashi ki je had'a mana breakfast, idan
kin kammala ki zo ki tasheni.
Ta mik'e tana murmushi ta nufi k'ofar fita ya bi ta da kallo, tana ficewa ya sauke
k'atuwar ajiyar zuciya.
Ya haye bed had'e da switch off d'in bulb.
Ga mamankinshi a maimakon ya yi bacci sai ya tsince kanshi da tunaninta, tsawon
lokaci ya dauka kafin ya samu bacci ya dauke shi.
Tana bari d'akin ta shiga nata ta canza kayan jikinta, ta shiga kitchen a gaggauce
ta had'a breakfast, ta shirya table, sannan ta koma d'akinta tayi wanka ta shirya
tsaf.....cikin atamfar super exclusive d'ikin skirt and blouse kayan sun kar6i
jikinta sosai tayi kyau na ban mamaki tayi dauri d'an kwali Zarah buhari, ta
kammala komai sannan ta nufi d'akinshi, ta samu ya tashi har ya shiga wanka, ta isa
ga gadonshi ta shiga gyarawa, tana cikin gyara gadon ya fito daga bathroom sanye da
bathrobe ta dauke kanta daga gefen da yake tsaye, tana gama gyarawa ta fice daga
d'akin.
misalin k'arfe 11:00 na safe suka bar gidansu zuwa Airports, Isah direba na sauke
su ya yi sallama da Aliyu saboda zai shi yi driving motar barrister A zuwa Abuja.
"Lokaci da flight d'insu ya yi landing direban Daddy ne ya dauko su.
Tun da suka fito daga Airports take kallon hanyoyin da direban yake bi, har suka
iso Ardo mansion.
Da gudu gateman da security d'in gidan suka iso wajensu, suna gaida su ta amsa
fuska sake har ma da wani d'an siririn murmushi.
Ta fito daga mota tabi bayan Aliyu sun iso flat dinshi ya ciro keys ya bud'e k'ofa
suka shiga daga ciki.
Gate man ya shigo musu da kayansu, cikin mintuna k'alilan ta d'anyi nazarin falon
k'asa duk abinda ke ciki kama daga cushion har zuwa painting falon white colour ne,
kamar dai yadda gidansu na Yola yake saidai wannan yafi na Yola had'uwa.

"Ki hau sama mana"

Muryarshi ta daki dodon kunnenta, ta juya cikin salon tafiyarta ta bi steps ta hau
saman saidai ta ja ta yi tsaye sakamakon rashin sani wane daga cikin k'ofufin da ta
samu ne, nata.
Bata jima da tsayuwa ba ya shigo ya ra6ata ya nufi wata k'ofa ya bud'e, ta bi
bayanshi.
Nan ma parlour ne ya sha kayan alatu na more rayuwa.
"Ya nuna mata wata k'ofa can k'asan mak'oshi ya ce ga sasshenki anan, yak'arasa
magana had'e da mik'a mata key, ya shige d'akin da take tunanin shine na baccinshi.
"Ta kad'a kanta ta bud'e falon ta shiga ta wuce bedroom, ta ajiye jakkarta da
mayafi ta shiga gyara wurin saida ta gama, tanufi nashi ta gyara taji motsinshi a
bathroom, agaggauce ta shiga gyara d'akin koda yafito har ta kammala ta fice, ta
gyara mishi falo, sannan ta sauka k'asa nan ma ta gyare shi tass....ta shiga
kitchen ta yi nazarinshi nan ma ta tsafta ce shi, gaba d'aya gidan ya dauki k'amshi
na fitar hankali.
Ta koma d'akinta ta yi wanka ta had'o da alwala, da yake lokacin sallar azhar ya yi
ta yi sallah.
Sannan ta tsantsara simple makeup, ta dauko luggage d'inta ta ciro Arabian gown
purple colour, tasaka tayi rolling da white veil.
"Tana cikin fesa perfume ya turo k'ofa ya shigo shima ya sauya kayan jikinshi,
zuwa white chino trouser had'e da mandarin long sleeve, ya nad'e hannayen rigar.
"K'amshinta ya had'e da nashi ya k'ara k'amsasa d'akin.
Kallo d'aya ya yi mata ya dauke kai, tayi mishi kyau ba k'adan musanmman da tayi
rolling da white veil favorite colour d'inshi.
"Mu je flat d'in momma ki gaisa da su ga alama basu san mun iso ba.
Yana k'arasa magana ya juya ta biyo shi abaya tana k'arewa compound d'in gidan
kallo.
A downstairs falo suka iske momma da Zee-Zee momma na waya yayin da zee-zee ke
kallon movie.
"Sallamar Aliyu ya dawo da hankalinsu akansu, zee-zee ta tashi cikin farin cikin
tayi hugging barrister A.
Lokaci da momma tayi arba da barrister ta ji gabanta, ya yi mummunan fad'uwa da
had'ye wasu mushirkai miyau.
"Barrister A ce tafara janye zee-zee daga jikinta, ta durk'usa ta gaida momma
ta amsa cikin fara'a saboda tsabar makirci hadda su rungume barrister tana fad'i
welcome to the family my daughter ya gajiyar hanya?"
Murmushin jin dad'i barrister A tayi duk tasan wannan welcoming da momma tayi
mata bai gansheta ba
Aliyu ya nufi one sitter ya zauna ya yi crossing legs d'inshi, shi ma ya gaida
momma ta amsa tana washe hak'ora.
"Sultan ashe kuna hanya?"
Uhm....!
Yafad'a kamar an mishi dole.
To miyasa jiya da dare da mu kayi waya ba ka fad'amin yau za ku zo ba?"
"Na manta ne!
Ya fad'a yana yatsina.
Kodai ka fad'awa Daddynka, ni ce da ka rena ba ka fad'awa ba?
Omg.....momma please banaso irin tambayoyin nan naki, sosai suke haifa min da ciwon
kai.
Ya k'arasa magana yana turo miki.
"K'atuwar harara momma ta wulga masa afakace, a fili Kuma ta k'ikk'iro murmushin
dole ta ce haba gadangana don nuna damuwa na akanka laifi ne?"

"Wani shegen murmushi Aliyu ya yi kafin ya ce kai....momma na fahimci yau
K'orafi ki ke ji, to Allah ya ba ki hak'uri.

"Zee-zee ta rik'o hannun barrister A zo mu tafi matar Yaya d'akinmu mu yi
fira, wallahi ina cike da farin ciki zuwanki gidanan ba k'adan ba.
"Nasan ko Meenat idan tadawo daga school ta ganki, haukace mana za tayi, saboda
tun lokaci bikinku bakinta bai huta da zance ki ba.
"Teema ma za tayi farin cikin ganinki.

Barrister A tayi murmushi ta sace kallon Aliyu, karaf.....suka had'a idanu ya kashe
mata idonshi d'aya batasan lokaci da ta lumshe golden eyes d'inta, daga bisani ta
bud'e su fesss......akanshi tayi mishi k'ayatattce murmushi, sannan ta bi bayan
Zee-zee har suka shige d'akin idanuwan Aliyu suna kanta.
"A lokaci da za'a auna Bp momma za'a iske ya haura d'ari biyu da tamani, tsabar
kad'uwa gani abinda Aliyu yake yi wa barrister babban tashin hankalinta bai wuce
mayatattace kallon da ya bi ta da shi ba.
"Da kyar ta tattaro 'yar raguwar natsuwarta ta had'a da k'arfin hali ta dube
Aliyu da idanuwanta ba bu komai ciki face tashin hankali.

"Sul....tan....!
Ta kira sunanshi cikin rawar murya.

Na'am!"

Ya amsa yana kallonta.

Da fatar kana zaune lafiya da iyalinka?"

"Lafiya qalau momma ba wani matsala.

Shiru ya biyo baya jikin momma ya yi sanyi tana so ta tambayeshi yana had'a
shinfid'a da barrister, tana jin tsoron amsar da zai bata.
"Sai kawai tayi ta maza ta gyara

11 / 26