Chapter 46 Reading WATA KISHIYAR Alkhairi Ko Sharri By Maryamah Mrs AM HN Novels

WATA KISHIYAR Alkhairi Ko Sharri By Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  KDP NOVELS

Chapter   46 / 46

135K to 135.5K   out of 135.5K words

datti da yayi saboda qurar qasan gado da suka watso masa palour dazu. Haka ya shiga dakinsa yayi wanka gaba daya gurin ya hargitse masa ya rasa ta yanda ze fara mayar da kayansa cikin wardrobe tunda ya saba da an kawo masa guga Ma'u ce take jera komai a inda ya dace.

Haka ya zura jallabiyya ya dawo palour ya kade kujera ya zauna ya bude abincin, loma uku yayi ya ture gaba daya abincin ya fice masa daga rai dan bakinsa ya saba dame dadi, dukda wannan din ma me dadin ne amma dandanok girkin Ma'unsa ya banbanta dana kowa shikadai ne abincin da ko iya qamshinsa yana rage masa yunwa dan shi fa abinci indai ba nata ba ko yaci baya jin ya qoshi sedai kawai cikinsa ya cika maganin yunwa amma ba wai dan ya gamsu da cewa abinci yaci ba.

Yana zaune yana dannan waya su Ahmad suka shiga gidan da gudunsu, Ganin sune ya debe masa kewa har aka kira sallah suka tafi masallaci tare, yana kallon Aliyu ko inda yaje yaron be kalla ba yayi murmushi kawai da suka dawo zaau tafi ya dakko Chocolate ya basu harda ta sauran kafin ya raka su har qofar gidan suka shiga, yana jiyo qamshin abinci da alama girki sukeyi.

Badan kar mutunchinsa ya zube ba babu abinda ze hana ya shiga yaci amma ya qudurce a ransa dole ya koyawa Ma'u hankali ta yanda da kanta zata bishi ta bashi haquri, a qalla se tayi kusan kwana dari da wani abu kafin cikar Iddarta dan watan ta me kwana talatin da shida ne kafin sannan kuwa ta biyu liqis ta yanda ko kara ya ajiye bazata sake tsallakawa ba. Haka yaja jiki ya wucw yana hadiyar yawu, qarshe se se shayi yasha da wani guntun cake da Allah yasa basu dauke ba ya hada da dambun nama shima a irin wanda take masa ne ya ajiye a office ya tuna yana mota ya dakko shi.

Seda yaje kwanciya idonsa ya kai kan farar takardar da tun jiya ya ganta amma be duba ba, daga kwancan ya janyota ya bude yana mamakin ko tasa ce ma ya manta sedai tambarin Asibiti da sunan Ma'u daya gani yasa ya qara hasken fitila dan ya gani da kyau.

"Kai Allah na gode maka, Wallahi Allah yana sona" ya fada a fili cikin farin ciki, wannan wata dama ya samu ya tabbatar se Asma'u ta kawo kanta da kanta musamman da yawancin cikinta suna qara mata buqata yana zaune zata zo har inda yake ta bashi haquri kai wannan abu ya masa dadi.

Hotonsu dashi da ita da yake akan bedside drawer ya dakko yana shafa fuskar ta, ranar Anniversary dinsu na shekara Goma suka duke shi daga shi har ita suna dariya ya manta dariyar me sukeyi a lokacin.

Sumbatar fuskarta yayi kafin yace
"Kiyi haquri Ma'una, nasan sena fiki azabtuwa da rashin ki a kusa dani amma ke kika jawo mana, taurin kanki da kafiya ya saka komai ya faru amma yanzu ga dalilin da ze dawo mun dake cikin ruwan sanyi na samu, Ina son ki Ma'una".

46 / 46