Author : Nimcyluv sarauta Category : KDP NOVELS
ciganvi ɗinkin doguwar
riga. Tausayin Halisa ya kamata amma ta share ta ce "Sai yanzu ki ka gama?" Kallon
mother kawai tayi ta kasa cewa komai, ta ɗaga ƙafa da ƙyar ta nufi bedroom ɗinta.
ko hijabin Jikinta bata cire ba ta kwanta kan gado tare da jan pillow ta rungome,
ta rufe idanu sai suffar Yaa Sheikh ta dinga zama kamar magic a Idanunta, ta tuna
rungumar da ya yi mata ta ƙarshe sai ta matse ƙafa da ƙyar barci ya ɗauke ta.
Wajan azahar barcinta ya yi nisa taji kamar ana motsi a ɗakinta, ta kasa buɗe ido
sama-sama kuma wani ƙamshi ke ratsa hancinta yana sauka har ƙasan zuciyarta,
ƙamshin da ba zata taɓa manta irin shi ba, idan tai kamar zata farka sai a hura
mata iska taji an rungometa tsam a ƙirji, ɗumi na rasata. Ta saki jiki cikin
magagin barci ta ce
"Abbana" aka shafa kanta ana manna mata baki a wuyanta tare da sakar mata wasu
lafiyayyun kisses cikin wata murya mai rauni da shauƙi aka ce
"Madadin Abbanki ne" baki ya kai da niyyar kissing nata ta buɗe ido da sauri tana
cewa
"Modibbo!" Ɓat! Kamar gilmawar walƙiyya ya ɓaci daga cikin bedroom ɗin sai ƙamshin
turaren Roja daya bari, cike da zullumi ta miƙe tana kunna hasken ɗakin, abin
mamakin bai huce yadda ta ganta naked babu kaya ta juya zuwa kan bed taga kayanta
ya she zube a ƙasa.
Ta shiga tattaɓa Jikinta da sauri ta ɗauki hijabi ta saka har ƙasa ta saka wani
skert tai waje da gudu tana sakin ajjiyar zuciya,sam bata lura da tarin mutanan da
suke parlourn ba, kai tsaye tai wajan mother ta ce.
"Abbana ya zo?" Mother tai mata kallon baki da hankali ta ce "Waye kuma Abba?"
Halisa tai shiru. "Oh! Tsohun mijinki Yaa Sheikh wai?" Ta ɗaga kai da sauri ita
burinta ta ji ya zo ɗin.
Mother ta ce "Ikon Allah ko shirman naki har kwakwalwarki ya taɓa ne Halisa? Banda
haka ina za muga Yaa Sheikh yanzu bayan ya yi tafiya kuma ha yanzu zai dawo ba"
Halisa ta ce.
"Na ganshi yanzu a bedroom ɗina, na tabbatar shi ne, naji ƙamshin turaren shi har
na ce masa Abbana sai kuma ya gudu"
Mother ta ce "Ah, ta tabbata kin zauce tsanar shi ce tasa ki ka fara mafarki da
shi?" Ta tura baki ta ce "Koma mene ai Abbana ne, ko ya sakeni ai baby zan haifa
masa" Umma A'isha ta ce
"Haka ne, kuma babyn mai sunan Ummul da Mother" Halisa ta taɓa rai ta ce "Ai na
rasa Mother farin ciki take da Abba ya sakeni" Mother ta ƙara sawa ranta cewa
Halisa akwai wauta da ƙuruciya a kanta tana son mijinta sosai abu ne kawai ke yawo
a kanta.
"To ai ni ke nake tayawa murna, farin cikin ki shi ne nawa fa" ta juya kan Umma
A'isha ta ce
"Ke kaɗai zaki faɗa mini gasky, amma wallahi Modibbo na gani" Ummul dake zaune ita
da hajja da Dada da kuma Fulani Atine, da Fulani Balaraba sai Dr A'isha da Yaya
Halima da Maimoon da Zeefa. Ummul ta kalli Halisa ta ce "Arɗo ki ka gani, anya ta
ya ya?" Ta faɗa tana son tabbatar da abin da take zargi ta ce "Da gaske Ummul naji
ƙamshin shi" Ummul a ranta ta ce "Wato ya tuna da layyar zanar shi kenan? Yanzu
mata a suffa mai wahalar ganewa" a fili ta ce.
"Ki nutsu, gizau ne da saka abu a rai"
"Ba kiga kayan lefen Zahrah ba ne?" Sai a lokacin Halisa ta lura da wasu mayan set
ɗin akwatuna har set biyar different colours ta dinga kallon kayan, abin ka da
wacce ke shirin kaɗan ga damuwa da tai mata yawa, kowa ya juya mata baya, ga rashin
cin abinci. Ta runtse idanu bata fahimci baya tayi zata faɗi ba sai taji an kamata
an zaunar tare da bata ruwa ta gane cewa suman wani lokacin tayi, kanta a ƙasa ta
dinga goge hawaye a takaice. Daga ƙarshe ta miƙe tare da barin wajan.
Tana barin wajan Ummul ta ce "Mai ya sa kuke son wahalar da ita, why not a faɗa
mata Gasky she's still his wife, look at her condition ba ita ɗaya bace, don't
think wani abu zai iya affecting health ɗinsu?"
Mother ta ce "Wannan kada ki ji tausayinta ko kaɗan, barta kawai ba abin da zai
sameta"
Fulani Atine ta ce
"Allah sarki akwai ƙuruciya fa, na lura bata kula da Dadarta ba, balle mu" Dada tai
murmushi kawai amma yadda taga Danejo ta koma sai duk Jikinta ya yi sanyi.
"Sannu da ƙoƙari Ummul, kaya sun yi ma sha Allah Halisa anyi ƙoshi" Yaya Halima ta
ce "Wallahi sai son barka, hadda key ɗin mota, ki duba gold necklace ɗin da suke
ciki da rings, an narka dukiya" Dr A'isha ta ce "Yanzu an fasa haɗa na wajan
Barrister?" Yaya Halima ta ce "Lefen da Barrister ta haɗawa Halisa daban, wannan
kuma daga mijinta Aliyu ne kamar yadda Abba Hakimi ya buƙata" Dr A'isha ta jinjina
tana son fahimtar mai ya sa Abba Hakimi ya nuna mata an saki Halisa?...
08119237616
IDAN BA KE
₦500
[1/25, 7:24 AM] Abk: "Excuse me?" Ummul ta faɗa tana miƙewa tsaye tare da nufar
bedroom ɗin da Halisa ta shiga, Dr A'isha ta bita da kallo tana son fahimtar abin
da Ummul take son yi.
Ummul na shiga ta samu Halisa zaune bakin gado Idanunta ya yi jajir hannunta ɗaya
riƙe da mararta dake mata mahaukacin ciwo,ganin Ummul ya sanya ta saki yanayin
fuskar domin Allah ya gani tana son Ummul sosai har cikin ranta.
"Ummul da gaske kayan lefen Zahrah ne?" Ummul ta ɓalle murfin gorar data shigo da
shi mai ɗan sanyi ta bata ta ce.
"Drink" ba tai mata musu ba, domin tana buƙatar ruwan sbd bushewar da maƙoshinta ya
yi. Sai da ta shanye fiye da rabi kafin ta ajjiye, ta tura mata plate ɗin wainar
fulawa wanda tasa Maimoon ta soya mata, aka saka Attahiru ciki sbd yajin da take
so, with egg aka soya da manja.
"Eat" Ummul ta furta cikin kulawa sai a lokacin ta ce "Bana jin yunwa Ummul, komai
a ƙirji yake tsaya mini"
"See you, you can do it maza cinye kiji wani abu" badan ranta ya so ba, ta fara cin
wainar fulawar ranta cinye tas ta ƙara shan watermelon juice.
Bayan ta dawo nutsuwarta Ummul ta kama hannunta ta ce
"Meke damunki Halisa? Mene a ranki share all your feelings with me kinji
daughterna"
Halisa ta kasa magana sai haɗiyar zuciya, idanunta suka ƙara rikicewa Ummul ta ƙara
yarda mugun mugun zafin zuciya ne da Halisa, taurin kai, tare da kafiya da naci.
"Talk" hawaye ya shiga silalowa Ummul ta ce "Ok don't cry my dear, take a deep
breath".
A hankali yaja numfashi kamar yadda Ummul ta ce "breathing down"
nan ma ta ƙara saukewa, kamar ƴa da uwa haka Ummul ta jata Jikinta ta rungome, ta
fashe da wani matsanancin kuka wanda bata taɓa irinsa ba, ta ƙanƙame Ummul tana
shassheƙa Jikinta na rawa, tausayinta ya kama Ummul ta rungometa very tight a
Jikinta, ta fahimci Halisa ba soyayyar miji ta rasa ba, hadda ta uwa, da wanda zai
zauna da ita yaji ainahin damuwarta, ta rasa soyayyar miji, ta rasa kulawar uwa, ga
batun kishiya, ga cikin dake Jikinta ga abubuwan da suke yawo a kanta tare da
gurɓata tunaninta.
"Ya isa daina kuka haka"
Ta ɗagota tana share mata hawayen ta ce
"Ya akai?" Cikin rawar murya ta ce "No one's love me, no one's care about me duka
sun tsaneni Ummul, ban san meke damuna ba, am a bad gril Ummul"
Ummul ta kama hannunta ta ce
"Listen, Halisa." Ta nisa kaɗan ta ce "If someone hate you tunani zaki dan me ya sa
ya tsaneki? Mene laifinki mai ki ka aikata har ya tsaneki? Idan ki ka fahimta, sai
ki fara ta yaya zaki Correcting mistakes naki? By apologies? Or by thinking your
future, idan yafiya zaki nema, at anytime zaki iya making mistakes na rayuwa wanda
kowa na yi, idan kuma zaki kalli rayuwarki ta gaba dake jiranki, to zaki fara
tunanin tayaya zaki kare kanki daga ƙara aikata wannan lafin da ki kai a baya? faɗa
mini wanne option ki ka ɗauka?"
Halisa was speechless da ƙyar ta ce "Zan yi tunanin gaba" Ummul ta ce "That's my
daughter, amma faɗa mini ke ki ka aikata har aka tsaneki ake Publishing naki haka?"
Ta marairaice ta ce "Nace bana son Abbana ya sakeni" Ummul ta girgiza kai, tana
kallon zallar ƙuruciya duk mai kunya a gaban uwa mahaifiyya ai ba zai ce baya son
ɗan data haifa ba, amma ita ko a Jikinta.
"Saboda me bakya son Abbanki?" Ta ce
"Ummul duk laifin shi ne fa, ya hanani zuwa wajan dangina, kuma ya furta kalmar
rabuwa dani ba tare da sanin yadda kalmar zatai tasiri a zuciyata, na yanke
shawarar na rama gwargwadon zafin da naji a zuciyata a kan shi, shi ne nace kawai
ya sakeni bana son shi, ban san meke damuna ba a lokacin amma komai ƙanƙantar abu
zafin shi nake ji a raina, cikin ƙaramin lokaci zuciyata take fusata, amma duk da
haka ya sakeni yaje zai auri wata to don Allah Ummul ba dole naji haushi na daina
cin abinci ba, na daina dariya da fara'a kuma kullum bana iya barci"
Ta jinjina kai irin abin ya ɓata mata ɗin nan ta ce "Duk dare abin ya yi ta yi mini
yawo a jiki, marata ta kumbura naji kamar akwai abin da nake so, naji ƙirjina yana
ta ƙaiƙayi, sai nayi kuka nake jin daɗin"
Ummul understand!
Tas ta gane me Halisa ke ji, ba Abin da take buƙata da kewa kamar mijinta ta kuma
kasa gane shi kan shi feelings ɗin.
Ta gyara zama domin Mentoring nata take son yi da kyau ta ce.
"Ki manta ni na haifi Yaa Sheikh, kiyi tunanin ni ce Dadarki shawara zan baki irin
ta ƴar da uwa"
Ta ɗaga kanta a hankali Ummul ta ce
"Kina son Aliyu ko baki son shi da gaske?" Halisa ta sunkuyar da kanta ƙasa kunya
ta kamata, tayi abubuwa da yawa wanda Idanunta ya rufe har bata san ta aikata ba,
yanzu kuma da wahala ta iya sarrafa kanta akan soyayyar tsohon mijin nata.
"Faɗi abin da yake ranki, kada kiyi wasa da damarki daughter" tai ƙasa da kanta
taƙi magana, Ummul ta miƙe tsaye ta ce "Ok fine bari naje kada muyi late zuwa Yola"
ta faɗa tana yin waje. "To ai ya sakani ko da ina son shi" ta faɗa a sanyaye
Idanunta na zubar da hawaye.
Ummul ta juya ta kalli Halisa sai ta dawo ta zauna, kafin suyi magana Dr A'isha ta
shigo ta nemi waje ta zauna, ba tare da Ummul ta kalli Dr A'isha ba ta ce "The you
need something?"
Dr A'isha ta girgiza kai ta ce "just to rest"
"Ok, am sorry zaki iya bamu waje, You can using the other room"
Rai ɓace ta miƙe ta fita, Ummul ta kalli Halisa ta ce "Ba ruwanki daya sake ki,
amsa zaki bani"
"Ina son shi, yadda nake son Abbana ko Mai martaba bana jinsa haka a raina, yanzu
ya manta dani" Ummul tai murmushi ta ce "Your father is your father, matsayin kowa
da ban, idan ki kai mini al'ƙawarin zaki sauya na miki al'ƙawarin zan saka Aliyu ya
ƙara aurenki ina nufin ya dawo dake"
"Ai wallahi nama sauya, ina son Abbana ina son zama da shi fa, da yana nan zai ta
rarrashina har nayi barci, kuma ya goya...," Ummul ta katse ta da faɗin.
"Enough, sirrine haka zaki zauna da Zahrah kina faɗa mata anything daya ke faruwa
matar malam?" Ta ɓata fuska jin sunan Zahrah ta ce
"To na daina, amma dai ai mijina ne" ba wasa a fuskar Ummul ta ce
"Haka ne, amma aure sirri ne! Ki nemi yafiyar Yaa Sheikh domin bashi kaɗai ba Allah
da mala'ikunsa suna fushi dake, kije ki zauna da abokiyar zamanki babu tashin
hankali ki nuna kema kina son mijinki duk abin da zai faruwa kada ki yarda tasan
faɗa kuke, ko kuna fushi, yanzu kije ki kira shi"
Ta marairaice ta ce
"Ai bani da number shi, ban san inda yake ba"
Ummul pretend! Ta zaro ido ta ce "Au kema? Ai babu wanda ya san duniyar da Yaa
Sheikh yake babu wanda yake da number shi, Innalillahi Allah ya sa ba wani abune ya
faru ba"
Halisa ta gigice ta miƙe zatai waje Ummul ta riƙeta sosai ta ce
"Ki bari Abba Hakimi ya dawo, nasan zaki samu wajan shi, da ga yau kada ki kuskura
ki ƙara faɗawa wani abin da yake faruwa" ta ce
"Adda A'isha kawai nake faɗawa ita take so na, take bani shawarar kada na sake bari
Abbana ya taɓa ni" murmushi kawai Ummul tayi tana ganin criminal take ganewa balle
ita da take police banda ma zata bada takardar barin aiki.
"Ki nutsu kada ki bawa kowa damar shigowa rayuwarki sai wanda ya cancanta, idan
naga kina saka damuwa bakya cin abinci to ba ruwana dake" a sanyaye ta ce
"Na gode Allah ya saka da alheri" Ummul ta fita tana fita, ta samu sauran a parlour
suna ƙara yaba kyan kayan lafen na Halisa, maƙowa da ƴan uwana da sauran abokan
arziƙi duk sun shigo.
Kaya aka zuba na gani na faɗa duk wanda kayan yasan an narka dukiya. Aka bada
tukuici Ummul taƙi amsa sam, Hajja ta amsa ta ce "Ai hakƙine" suka bar gidan.
Yaa Sheikh na zaune a babban gidan shi dake ƙasar Makka cikin garin Madina, a
hankali ya sauke numfashi idanunsa rufe, tunda yabar gida babu ranar data zama ta
banza a gare shi, kullum cikin hukunta kanshi yake da azumi ya ɗauki laifin ya
azawa kan shi, so hana ganin laifi, baya layin mazan da so yake rufe musu ido komai
girman so zai iya hukunta Matarshi akan laifinta, amma wannan laifin shi da kan shi
ya bada ƙofar yi, ya kuma san halin abar shi tun tana ƙarama da zuciya.
Ya sauke numfashi yana juya Apple ɗin dake hannunsa bai jimawa da shigowa daga
sallar Issha ba. Umar-khan ya shigo bakinsa ɗauke da sallama ya zauna yana faɗin.
"Abba ya kira"
Ya jinjina kai tare da yin baya ya ɗora ƙafar shi saman table.
Ƙamshin turaren Roja wanda ya zauna a jikinsa da kyau yana fita tare da mamaye
makaken parlourn na shi, ya faɗaɗa Jallabiyar jikinsa tare da ɗora ƙafarsa saman
cinya. Umar-khan kallon Yaa Sheikh ɗin yake yana mamakin abin da yake ɓoyewa.
Ringing ɗin waya ya katse shirun Umar-khan ya ce "Ummul ce"
Nan ma Yaa Sheikh bai magana ba sai tsare Umar-khan ɗin da ya yi da narkakkun
idanunsa, Umar ya bashi wayar ya kara a kunne.
"Aliyuna" Ummul ta kira shi a taushashe, ya sauke ajjiyar zuciya yaƙi cewa komai,
Umar-khan ya a miƙe tare da barin wajan ganin kamar zamansa ya takura Yaa Sheikh
ɗin. Yana fita Yaa Sheikh ya ɗan marairaice ya ce.
"Ummul" ta ce "Halisa ko?" Ya lumshe idanu ya buɗe a nutse ya ce "Ya take?" Ta ce
"Tana cikin damuwa, na rashinka na lura wani abu na faruwa" ya numfasa da kyau ya
ce "Dr A'isha" da mmki Ummul ta ce "Ya akai ka sani?" Ya jima bai ce komai ba sai
can ya ce
"Na ɗauka ba zaki mamaki ba, ki ɗaukeni matsayin halitta biyu, Mutum da Aljan"
tsoro ya kama Ummul ta ce "Mutum da Aljan Aliyu anya wannan rayuwa?" Ya ce "Kada ki
mamaki kowa da ƙaddarar shi, ina iya faɗa miki me kike yanzu, tayi yiwu tsari ne
daga Ubangiji naji ina son zama haka"
"Kenan da gaske Halisa kai ta gani jiya? Layar zana?" Ya yi murmushi mai taushi
hannunsa akan dogwan gemunsa yana ja ya ce
"Babu ko tantama, ni ne na kasa jurewa" kamar zatai kuka ta ce "Nayi maka magana
akan layar zana Arɗo ashe baka ji ba, bayan kasan babu kyau?" Cikin kulawa kamar
tana gabansa ya ce "Ummul ko wanne ɗan tara yake bai cika goma ba, ina da ilimi
both side, ina arziƙi, ina da kyau ki ɗauka layar zana shi ne dalilin daya sanya
ban cika goma ba, na zama tara, amma ni nama manta da ita wannan zuwan bayi na
bane, kici gaba da addu'a"
Ko ba a faɗa ba yasan kuka take ta kasa cewa komai daga ƙarshe ta kashe wayar.
Suna gama waya wani message ya shigo wayar sbd gilmawar notifications, har ya shige
sai ya buɗe saƙo ne daga number da bashi da ita ya fara karantawa.
_“Aliyu ashe baka haifo ba? Ashe zuciyar kare ce da kai? Ka bani mamaki dana
samu labarin ba sakina kayi ba, to wallahi ko zaka mutuwa ba zan komawa aurenka ba,
maye wanda ya rako maza duniya ni Halisa Danejo Rome har abada nayi maka nisa kaje
can ka zauna da karuwa dan ba abin mamaki bane idan kai ma ka sance haka...I HATE
YOU YAA SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU”_
Ya saki wani murmushin manya tare da miƙewa a hankali cikin nutsuwa da kamewa haɗi
da tsantsar kamala da addinin daya gama ratsa shi ya turawa number kalma biyu zuwa
uku.
_“IDAN BA KE”_
shi ne kawai abin da ya rubuta tare da turawa. Tunda ya tsaya a wajan kuma bai
motsa ba, sai zufa dake yanko masa all over him hannunsa ɗaya ya dinga rawa, a haka
Umar-khan ya riske shi ya dinga kiran sunan shi amma bai tanka ba, bai juyawa ba,
zufa bata fasa yanko masa ba. Umar-khan ya ɗauki remote ya kunna karatun Alkur'ani
ya nemi waje ya zauna yana kallon sarautar Ubangiji.
Halisa na zaune gaban Abba Hakimi yana rusa masa kuka tana faɗin
"Don Allah Jon wuro ka yafe mini ka taimaka ka bani number Abbana na kira shi ko
sau ɗaya ne" ya numfasa ya ce
"Matar sau nawa zan shaida miki bani da number? Amma zan miki al'ƙawari idan kema
zaki mini" da sauri ta ce
"Wallahi nama yi maka Abbana nake so ka dawo mini dashi" ya ce "Zan saka a lalubo
mini number shi, amma ina son ki mayar da hankali ki ƙarasa haddarki saura izu
biyar ki kammala kin tsaya wasa, na cike miki form ɗin makarantar "Ibadur-rahman a
can zaki ƙarasa za a saka ki ajin hafizan bana zuwa nan da wata uku kin sauke" ta
zare ido ta ce
"Yanzu sai wata uku zanga Modibbo na shiga uku, ni na haƙura da karatun na haƙura
da sokoto bana son kowa bana son komai Abbana nake so" ya ɓata fuska ya ce
"Shikenan jeki neme shi" ta riƙe hannunsa ta ce "Shikenan na amince yaushe zan fara
zuwa makarantar?" Ya ce "Gobe" a hankali kuka na son ƙwace mata ta ce "Allah ya
kaimu" ta miƙe da sauri tayi bedroom ɗinta lokacin Engineer ya faɗo parlourn a
gigice kamar an cillo shi.
Halisa ta buɗe bedroom ɗin tana sakin kuka ganin bedroom ɗin duhu sosai baƙiƙƙirin
ko hannunta bata iya gani yasa taji tsoro ta juya zata fice taji an murza key.
Ta buɗe baki zatai magana akai saurin rufe bakin da tattausan hannu mai sanyin
gaske hannun duk gargasa, aka fincike hijabin Jikinta zatai ihu ta gudu taji ya
haɗata da faffaɗan ƙirjin shi mai cike da suma ta ƙwalla ƙara sbd jin mutum naked
babu komai a jikinsa...
08119237616
Paid book
[1/26,