Author : SIS NERJA'ART Category : KDP NOVELS
tunani bacci 'barawo yasace shi.
Wajen k'arfe bakwai kiran da yashigo wayarshi ne yatashe shi dakyar yabud'e idanunshi da sukayi mashi nauyi saboda rashin samun isashen bacci, d'auko wayar yayi yaduba yana ganin me kiranshi sai ma yamaida ta silent sannan yamik'e yashiga wanka.
Bayan ya fito ya shirya cikin shirinshi na tafiya aiki jikkar laptop d'inshi da wayoyinshi yad'auko yafito parlor daidai da Momcy ta shigo parlorn d'auke da plask tsayawa tayi tana kallonshi.
Murmishi Faruk yasakar mata tare da gaisheta.
Amsawa tayi sannan tace Son ka dai san babu inda zakaje sai ka yi breakfast ko?
'Bata fuska yayi yace Momcy bana jin yunwa.
Batace mashi komai ba tawuce dining area.
Ajiye kayan da suke hannunshi yayi yabi bayanta yana zuwa yaja kujera yazauna, fara serving d'inshi tayi sannan tace d'azu Nasiba ta kirani a waya ta ce tana ta kiran wayarka baka d'auka ba.
Yi yayi kamar baiji ba yafara breakfast d'inshi.
Kallonshi Momcy tayi tace Faruk magana fa nake maka ka min shuru.
'Dagowa yayi yakalleta yasakar mata murmushi sannan yace momcy time d'in bacci nake kuma ko da natashi ban bi ta kan wayarba saboda naga zanyi late ban tafi aiki ba.
Momcy kallonshi kawai tayi tawuce tatafi cikin ranta tana mamakin halin d'an nata.
Sama sama yayi breakfast d'in yamik'e yad'auki kayanshi yaficce yabar gidan.
Yana cikin mota yana tuk'inshi a nutse nan wayarshi tafara ringing kallon wayar yayi ganin sunan da yabayyana a jikin screen d'in wayar yasa yai saurin yin picking tare da yin sallama,,, yanayin yadda yake maganar kawai zaka gani kagane cewa akan wajen aiki ne suke tattaunawa sun dad'e suna wayar kafin daga bisani suyi sallama.
Suna gama wayar d'an guntun tsaki yaja tare da canza hanya yanufi wajen aikinsu.
Yana isa yai parking a daidai inda yasaba yin parking yad'auko bakin space d'inshi yadad'e fuskarshi sannan yafito daga cikin motar yazagaya yabud'e mazaunin me zaman banza yad'auko jakkar laptop d'inshi.
Tafiya yake cikin takunshi me burgewa duk inda yagifta sai mutane sun mashi barka da safiya saidai kawai yad'aga masu hannu, wad'anda suka yi mashi farin sani ne kawai zasuce daman haka yake dan Barr Faruk ba mutum bane me yawan son hayani.
Yana zaune a office d'inshi akayi mashi knocking izini yabada ashigo nan aka turo k'ofa.
'Daga kai yayi yakalli me shigowa sai kuma yamaida kallonshi ga system d'in shi.
Sacratery takowa yayi ya iso wajen Barr Faruk daga gaban table d'inshi yatsaya yace Barrister barka da aiki.
Batare da ya d'agoba yace yauwa barka.
File d'in da yake hannunshi yamik'a mashi yace gashi oga yace akawo maka.
Ohk ajiye nan.
Ajiyewa yayi saman table d'in yace atashi lafiya sannan yajuya yafita.
Barr Faruk d'auko file d'in yayi yabud'e yafara dubawa chan sai yamik'e tare da d'aukar file d'in da key d'in motarshi yafita.
Saida yafara biyawa a office d'in ogansu suka tattauna sannan yatafi.
Yana barin nan direct gidan yari yawuce yana isa kamar yadda yasaba office d'in abokin nashi yafara safka bayan sun gaisa ne yanuna yanaso yaje yagana da jawahir.
Alhaji Nasibi yanuna ba matsala nan yakira wani ma'aikacin gidan kamar yadda yasaba yahad'a shi da Barr Faruk suka je.
Suna zuwa suka sameta zaune ta had'e kai da gwiwa, daga bakin k'ofa ma'aikacin yatsaya inda shi kuma Barr Faruk yashiga ciki ko kad'an bata motsa ba daga inda take da alama kamar bata ma san da shigowarshi ba.
Barr Faruk matsawa yayi yatsugunna a gabanta tare da kiran sunanta ahankali.
Bud'e rinannun idanuwanta tayi tare da d'ago kanta tasafke idanunta a fuskarshi inda fuskarta take a d'aure.
Cike da jin tausayinta yake binta da kallo inda itama take kallonshi babu ko k'yaftawa.
Ajiyar zuciya yasafke yace jawahir insha Allahu zan taimaka maki zan wanke ki daga zargin da akeyi maki.
Lokaci guda tamik'e tsaye tare da sakar mashi murmushi sannan tawuce tafara taku d'aya biyu sai taja tatsaya batare da ta juyo ta kalleshi ba cikin dashewar murya tace zargi kuma? Wanene yafad'a maka zargina akeyi? Duk abinda kaji ance na aikata to dagaske ne.
Mik'ewa yayi daga inda yake yatsaya yace idan har abinda kika rubuta a kan labarinki gaskiya ne toh tabbas zanyi k'ok'ari wajen wanke ki.
Murmushi tayi a karo na biyu tare da sake jefa mashi tambaya tace labarina kuma?
'Dan matsowa yayi kad'an yace Eh saidai inaso insan k'arshen shi dan samun cikakkar hujja.
Shuru tayi kamar bataji abinda yaceba ganin haka yasa Barr Faruk yace shin ina Umar?
Lokaci guda tajuyo takalleshi cikin sauri tatako ta iso wajen da yake tsaye tare da cacimo wuyar rigarshi muryarta tana rawa tace wanene yafad'a maka shi? Ina kasan yaya umar d'ina?,, tafad'a tare da fashewa da kuka.
K'wacewa yayi daga rik'on da tayi mashi yad'an ja baya kad'an yace ban san umar ba saidai na karanta acikin labarin da kika rubuta.
Hannu tamik'a mashi muryarta tana rawa tace ina diary na.
Cikin nuna rashin damuwa yace yana wajena zanyi wani aiki ne akanshi ammah jawahir ya kamata kisanar da ni ina umar da su Abba shin suna raye?
Sulalewa tayi a lokaci guda tazauna k'asa tare da rushewa da kuka tace nima ban saniba bansan me yasa babu wani wanda yazo gareniba meyasa zasuyi min haka?
Takowa yayi yamatso wajen da take yace kenan suna a raye jawahir?
Wani irin kallo tayi mashi har ta bud'e baki zatayi magana sai kuma tafasa.
Ganin haka yasa yacigaba da cewa jawahir dole sai kin daure kin sanar da ni komai domin ta haka ne zamu samu mafita wad'annan mutanen da suka kashe maki iyaye, sannan ita wannan aljanar ta wace hanya takebi tana d'aukar maki fansa akansu, kuma idan har itace take yin kisan ai inaga bai dace ace ankama ki akan laifin da bake kika aikata ba ammah me yasa tun lokacin da akayi abun baki sanar da hukuma ba? Inaga da ace kin sanar da......wata irin k'ara jawahir tayi tare da toshe kunnuwanta cikin d'aga murya tace ya isa haka barrister! ya isaaa!!!
Hawaye ne suka cigaba da fita daga idanunta tace taya kake tunanin hukuma zata taimaka min bayan Ammina ita kanta ta je ma hukuma ammah babu wanda yakulata bare har yataimaka mata, wannan dalilin ne yasa nad'auki fansa dakaina ban damu da abinda zai faru da niba bana buk'atar cigaba da rayuwata ina so akasheni saidai kafin nan nafiso incika burina a rayuwa sai na ida kashe wad'anda suke da hannu a mutuwar iyayena daga nan nima zanyi farin ciki sosai idan na mutu dan daman mutuwar itace nafi buk'ata,,,,, juyawa tayi takalli gefe guda sannan tace rayuwata batada sauran amfani ban ta'ba bak'in ciki ba akan zaman da nayi a nan na tsawon wata goma zanyi farin ciki ace daga nan gidan sai k'abarina zan shiga.....
Katseta Barr Faruk yayi yace jawahir wannan wace irin magana ce kikeyi kidaina cewa haka insha Allahu zaki rayu ni zan taimaka maki kifita daga gidan nan saidai ta ina zan fara bi, shin ya za'ayi in iya sanar da kotu cewa aljanah ce take wannan kisan?
"Wannan ba gaskiya bane nice nan nayi kisan Barrister kar kasaka kanka acikin lamurra na domin gudun kar kajefa rayuwarka acikin had'ari, duk wanda yanemi yajawo jikinshi agareni yana shiga matsala yakamata kafahimci hakan.
Kallonta yake gabad'aya ta hargitse yace ban damu da wannan ba jawahir kawai dai akwai wasu tambayoyi da nakeso inyi maki shin ina lauyan mahaifinki wanene shi? Sannan dagaske kina da hannu acikin mutuwar Alhaji....
Bata bari yak'arasaba takatseshi tace ya isa haka barrister na fad'a maka babu abinda zaka samu daga gareni wannan duk ba gaskiya bane,,,, tana fad'in haka tamik'e taje chan wajen 'yar k'aramar tagar nan da tasaba tsayawa wajenta tatsaya tajuya mashi baya ahankali tace wannan duk shirina ne ya kamata katashi katafi.
Idanu Faruk yazuba mata yana kallonta har ya bud'e baki zaiyi magana tatari numfashinshi tace banason jin komai daga gareka dan Allah kabarni haka bansan ya zanyi ba tambayoyinka sun min yawa!.
Mik'ewa Barr Faruk yayi yace shikenan jawahir zan tafi ammah inaso kisani zan dawo agareki bamuda isashen lokaci ya kamata kisan haka sai anjima,,,, yana fad'in haka yajuya zai tafi sai jin muryarta yayi ta ce katabbatar ka maido min diary d'ina.
'Dan guntun murmushi yayi yajuya yafita.
yana fita yajiyota ta fashe da kuka d'an ja yayi yatsaya sai kuma chan yawuce yatafi.
Saida yabiya ta office d'in Alhaji Mahadi sukayi sallama sannan yawuce yatafi yana a mota DPO yakira shi a waya yace suna son ganinshi yanzu, amsa masu yayi da toh gashinan zuwa sannan yakashe wayar.
Lokacin da ya isa station d'in direct office d'in DPO yawuce lokacin yana ciki suna ganawa da wani dan haka yajira sugama.
Kusan minti shidda sai ga mutumin ya fito juyowar da Barr Faruk zaiyi nan sukayi ido hud'u da Alhaji Mansur wani shu'umin murmushi Alhaji Mansur yasakar mashi tare da cewa Barr Faruk barka da rana.
Kallo d'aya Barr Faruk yayi mashi batare da ya tanka shi ba yawuce zai shige sai jiyo muryarshi yayi daga baya yana cewa har yanzu kana da damar da zaka mallaki Nasiba but in kana da buk'atar hakan.
Ja yayi yatsaya har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa yawuce yashige.
Dariya Alhaji Mansur yayi yace nasan dai zaka amince da hakan.
Yana shiga hannu yamik'a ma DPO suka gaisa nan yanuna mashi kujera yazauna, tambayarshi yayi ya aiki ya amsa da Alhamdulillah.
DPO jujjuyawa yayi a kujerar da yake zaune sannan yace Barrister Faruk ba komai yasa na kiraka ba sai akan case d'in jawahir akan kisan Alhaji Sa'idu wanda a yanzu mun k'ara samun k'wak'k'warar hujjar da tanuna mana tana da hannu a cikin kisan shi zamu mik'a case d'in a kotu dan ya kamata kotu tayi gaugawar d'aukar mataki saboda abu sai k'ara cigaba yake.
Shuru Faruk yayi yazuba mashi idanu yana kallonshi har yakai aya sannan yace DPO na ji bayaninka saidai inaso kasan cewa wannan zancen duk ba gaskiya bane jawahir bata da hannu acikin mutuwar Alhaji Sa'idu Nepa yakamata kudaina zarginta saboda kun duba CCTV Camera a daidai lokacin da akayi kisan muna a hotel kaga babu hujjar da zatasa ace itace takasheshi.
'Dan guntun murmushi DPO yayi yace Eh munga haka ammah wannan bai isa yazama k'wak'warar shaida ba, inaso kasan wani abu duk mutuwar wad'anda ake zarginta akansu kusan haka yafaru kuma muna tunani tana amfani da layar zana ne tana 'bacewa taje takashesu sannan su kansu lauyoyinta bata barsu ba tana acikin gidan yari takashesu.
Na ji wannan saidai ban gamsu da hujjarka ba.
Cikin d'aga murya DPO yace Barrister nasan aikina sannan ina k'ok'ari wajen ganin na kawo cikakkun hujjoji da dole za'a yadda cewa itace takashesu kamar yadda tun yanzu na fara samu dan mun samu hoto kamar yadda muka samu an aje a mutuwar sauran mutanen shin wannan ba hujja bane?
Murmushi Barr Faruk yayi yace kusan haka saidai inaso kasani nima zanyi bakin k'ok'arina a matsayina na lauyanta.
Jinjina kai DPO yayi yace dakyau Barr Faruk.
Mik'ewa yayi tare da mik'a mashi hannu sukayi musabaha sannan yace na barka lafiya.
Ta'be baki DPO yayi yace ba damuwa a duk lokacin da buk'atar nemanka yataso zakaji kirana.
Ohk ba damuwa inspector sai na ji ka.
Tunda yakama hanya ba abinda yatsaya mashi a rai sai maganganun da jawahir tafad'a mashi kenan har hukuma sun sanar da su akan kisan da akayi ma mahaifinta ammah ba'a d'au wani mataki ba? Indai hakane to da wannan damar sukayi amfani wajen d'aukar fansar kisan da akayi ma iyayenta saidai taya zan samu cikakkun hujjojin da zan iya kareta da su? taya zan wanketa gaban kotu? A fili yace ya zama dole jawahir kiyi min magana indai har kinason barin gidan kason nan ammah ita fa wannan aljanar...bai rufe bakiba sai gani yayi ta mirrir d'in motarshi kamar wannan tsohuwar ce zaune tana kallonshi da k'walak'walan idanunta saurin jan burki yayi yatsaya tare da waiwayawa baya ammah baiga kowa ba, ajiyar zuciya yasafke tare da jingine kanshi a jikin kujera kusan minti ukku sannan yatada motarshi yanufi gida.
Yana isa wanka yayi yashirya sannan yafito parlor yasamu iyayenshi Momcy tazubo mashi lunch yazauna yayi suka d'an ta'ba hira yatashi yakoma d'akinshi wayoyinshi gabad'aya yakashe dan kar atakura mashi yad'auko laptop d'inshi tare da diary d'in jawahir yazauna yana aiki saida yaji k'walwarshi ta d'auki caji tana buk'atar hutu sannan ya ajiye tare da kwantawa saman gadonshi bai dad'e da kwanciya ba bacci yai awon gaba da shi daman abu ga wanda bai samu yaruntsa ba.
Ba shine yafarka daga baccin da yake ba sai wajen biyar a gurguje yai wanka sannan yad'auro alwallah.
Bayan ya gama duk shirinshi yad'auki laptop d'inshi da key d'in motarshi yafita dan yaje chan gidanshi da yake gani zaifi samun kwanciyar hankali yayi aikinshi yana fita daidai lokacin motar nasiba ta cinno kai cikin gate d'in gidan.....
_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:09 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]
_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_
_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_
PART TWO
_~GORON SALLAH~_
*PAGE 2*
Kallon motarta yayi yad'auke kai sannan yawuce yanufi parking space wajen motarshi, wani irin parking tayi yana ji lokacin da taja burki dak'arfi, tabud'e motar tafito cikin sauri tanufi wajen da yake tafiya tare da kiran sunan shi.
Ja yayi yatsaya batare da ya juyoba har ta iso, gabanshi tatsaya tana kallonshi damuwa k'arara ta bayyana a fuskarta cikin karyayyar zuciya tace haba Faruk yanzu har ni zaka gani na zo ammah kashareni baka ma da lokacina.
Faruk sai a lokacin yakalleta yace ba haka bane Nasiba taya kike tunanin zan shareki.
Ba ga shinan ba ka yi, bansan menayi maka ba har zaka yanke hukunci irin haka faruk, wane irin laifi nayi maka da har zaka k'i amincewa da aurena, ko sona ne kadaina yi,,,, tafad'a hawaye suna fita daga idanunta.
Hankalin faruk ya tashi sosai ammah bai nuna mataba yace ko d'aya Nasiba ba haka bane ke kanki shaida ce ina sonki kuma ba wai na fasa aurenki bane mahaifinki ne kawai yakeso yabada matsala a cikin maganar aurenmu.
Katseshi tayi tace koma dai minene faruk bai dace saboda aikinka kak'ini ba, meyasa kake son fifita aikinka akaina? Kana nuna min kamar aikinka ya fini matsayi a wajenka.
'Dan guntun murmushi yayi yace Nasiba kidaina cewa haka ko d'aya ba haka bane huruminki daban na aikina daban banaji zan iya had'a soyayyarki da komai saidai me bazan ta'ba bari sonki yashafi aikina ba bansan dalilin da yasa mahaifinki yakeso yashiga cikin aikina ba idan har baiyi niyar bani aurenki ba kawai sai yafito yafad'a min ba wai sai ya sa min dokar da bata shafi aurenmu ba.
Fashewa da matsanancin kuka tayi tace Faruk ban ta'ba tunanin haka daga gareka ba koma menene na d'auka zaka iya sadaukar da shi akan soyayyarmu, me zai hana kahak'ura da koma menene muyi aure.
Zuba mata idanu yayi yana kallon yadda take kuka bilhak'i duk sai yaji tausayinta ammah yana tunowa da yadda sukayi da mahaifinta sai yagirgiza kai yace bazan iya haka ba, kamar yadda wani uzuri na aikina bazai hanani aurenki ba toh haka shima aurenki bazai shiga hurumin aikina ba duk son da nake maki zan iya hak'ura har zuwa lokacin da mahaifinki zai amince muyi aure dan haka kar kiga laifina a ciki kiyi hak'uri,,,
Yana fad'in haka yawuce yanufi wajen motarshi yabud'e,, cikin kuka Nasiba tafara k'wala mashi kira ammah yashareta yashiga yamaida yarufe yatada motar yabar gidan, ta window yana kallon yadda take kuka tana bin motar da kallo, duk sai yaji babu dad'i wani irin abu ya tsaya mashi a rai, yana fita daga gate d'in gidan taka burki yayi yatsaya tare da kife kanshi a jikin steering yana jin wani irin tausayinta da soyayyarta sun mamaye mashi zuciya, shi kanshi ya san yayi k'ok'ari sosai wajen danne sonta, girgiza kai yayi ahankali yace Nasiba mahaifinki ne yasaka mu cikin wannan halin ammah ni ina sonki.
Ya dad'e a wajen sannan yaja motarshi yatafi, tuk'i kawai yake ammah yana jin babu dad'i a ranshi har ya isa gidanshi da yaci buri sutare shi da amaryarshi Nasiba.
Nasiba ganin yadda yaficce bai ko tsaya saurarentaba yasa tacigaba da kukanta tare da juyawa cikin sauri tashiga cikin gidan, Momcy da shigowarta parlor kenan sai ganin Nasiba tayi kamar anjefota.
Cike da mamaki tamatso wajen tana cewa lafiya Nasiba me yake faruwa?
Kasa yi ma Mom bayani tayi sai ma cigaba da kukan da take nan hankalin Mom ya ida tashi taruk'ota sukaje saman kujera suka zauna sannan tace dan Allah Nasiba kidaina kukan haka kiyi min bayani me yake faruwa?
Cikin sheshek'ar kuka tace Mom Faruk ne.
Ajiyar zuciya Mom tasafke tace me yafaru da Faruk d'in wani abu yayi maki?
Cigaba da kukanta tayi dan batasan abinda zatace ma Mom ba.
Ganin haka yasa Mom tace shikenan kidaina kukan kibarni da shi zai zo yasameni.
Tsagaitawa tayi daga kukan tace baimin komai ba cewa yayi bazai aureniba.
Zaro idanu Mom tayi tace shi Faruk d'in da kanshi yace haka?
Sadda kanta tayi k'asa tace ba wai hakaba ya ce min aikinshi ya fiye mashi ni.
Jinjina kai tayi cikin ranta tace watau kenan k'arya yayi masu da yace yayi magana da Daddyn Nasiba akan kar ayi baikonsu sai ta gama karatunta, to me yake nufi da hakan, koma menene zaya dawo gidan yasameni,,, dafa Nasiba tayi tace kinga kidaina 'bata hawayenki insha Allahu babu abinda zai hana aurenku da Faruk kibarni da shi.
Wata irin kunya ce takama Nasiba tace Mom ba wai haka ba kawai dai....sai kuma tayi shuru.
Murmushi Mom tayi tace koma menene kar kidamu kinji?
'Daga kai tayi alamun toh sannan tamik'e tace Mom bari intafi gida.
A'a Nasiba tun yanzu? Ko ruwa fa baki sha ba.
Kanta sadde k'asa tace Allah Mom nagode daman sauri nake Hajiya ta aikeni.
Toh shikenan Nasiba kikwantar da hankalinki babu abinda zai hana aurenku da Faruk kibarshi zai dawo gidan yasameni, kigaishe da Hajiyarku kinji.
Cikin jin dad'i tace toh Mom zataji sosai.
Tunda tashiga mota inba goge hawaye ba babu abinda take maganganun Faruk sun tsaya mata a rai