Author : Mansur Usman Sufi Category : Taskar Novels
Barde Shabbaru mahaifin Hibairu
SARKIN SADAUKAI,
Domin yayi amfani da mahaifin na sa wajen mallakar sa,
To masu saurare sai muje zuwa Littafin na gaba domin muji yadda zata kaya tsakanin
sarakunan duniya
Lokacin da tawagar sarki Baddadul-ulkas suka dauki hanyar da zata kai su izuwa dajin
Baitul-shamshan,domin da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI.
Sai suka wanzu suna tsala Azababban gudu a bisa dawakansu,
Daya ke tafiyar ta manyan sarakai ce da suka yi shura a halarar tsafi sai ya zamana cewa,
Tafiyar da za'a yi ta a cikin kwanaki shida sai ayi a kwana biyu,
Kasancewar masu iya magana na cewa sarkin yawa yafi Sarkin Karfi dai yazamana cewa komai
yawan abokan gaba da dakarun sumame,
Cikin abin da bai huce dakika ashirin ba ake hallaka su,
Wadansu ma cika wandonsu ke da iska domin tsira da rayukan su domin sun san cewa ko ba'a
gwada ba linzami yafi karfin bakin kaza.
Haka dai wannan tawagar ta wanzu tana ratsa duwatsu koramu haɗe kwazazzabai gami
sarkakiyar bishiyoyi,
Wannan shi ne abinda ya faru da sarki Baddadul-ulkas ya birnin Rum.
Gaskiyar masu iya Magana da suka ce sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba.a je
ba.
Akwana a tashi sai gashi jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI ya cika kwanaki ɗari uku da
sittin da biyu,
Ma'ana saura kwanaki ɗaya kacal ya kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN
SHIRI,
A daren wannan rana ne aljani Marhutul-Azab ya sauke su saurayi Hizmal a bakin kofar
shiga dajin Baitul-shamshan,
Bayan ya sauka a turba ne sai kowa ya yunkura ya sauko ƙasa,
A sannan ne kowa yasha jinin jikin sa bisa yin arba da yadda farkon shiga dajin
Baitul-shamshan yakasance,
Duk da kasancewar a wannan lokaci dare ya tsala babu abinda kunne keji face kukan
tsuntsaye da kananan dabbobi,
Jaruma Husnaila ta katse shirun da wanzu ta hanyar buɗar baki tayi gyaran murya a karo na
farko tace"ya abokanan tafiya ta ahalin yanzu gashi mun iso dajin Baitul-shamshan domin
saduwa da jarumi Hibairu,
Kuma na ji a jikina cewa muna halitta ta farko da muka riga kowa zuwa wannan waje,
Shin yanzu mene ne abin yi?
Koda jin wannan batu daga bakin sunaila sai kowa yayi shiru aka rasa wanda zai ce kala'.
Sai daga bisani aljani Marhutul-Azab yayi''''' gyaran murya yace "yaku abokan tafiya kuyi sani
cewa wannan waje da muka iso shine waje mafi haɗari fiye da ko ina ,
Domin kuwa duka burikan sarakunan duniya, bokaye,da jarumai ya dogara da dajin
Baitul-shamshan,
Ku sani cewa a subahin gobe ne nan da Sa'a uku Hibairu SARKIN SADAUKAI zai fito daga
wannan daji na Baitul-shamshan,
Shawarar da zan ba mu ita ce mu dole mu kasance a cikin shirin ko ta kwana domin kowa ne
lokaci sauran abokan gaba na iya iso nan,
Idan bamu mai da hankali ba zai zamo abin nan da masu iya magana ke cewa
Kura da shan bugu gardi da kwace kuɗi,
Koda jin wannan batu daga bakin aljani Marhutul-Azab sai kowa yayi na'am da shawarar.
Nan take kowa ya zare takobin domin shirin ko ta kwana,
Aljani Marhutul-Azab ya zare wani zabgegen Gatari a gadon bayan sa,Hizmal goye da yaro
Humair makaho,sunaila da budurwar Nihla suka zare waɗansu takubba a damtsen su,
Kuma aljani Marhutul-Azab ya dunga rangadi yana kai komo a harabar wajen domin tabbatar
da cikekken tsaro,
Ana cikin wannan hali ne sunaila ta dubi budurwa Nihla tayi gyaran murya tace da ita"yake
wannan jaruma shin mene ne labarin rayuwar ki kuma mene ne dalilin daya sanya wannan
azzalumar sarauniya ke farautar rayuwar ki? .
Ko da jin wannan tambaya daga bakin sunaila sai idanun Nihla suka suka ciko da kwalla,
Har ta buɗe baki da nufin ta ba wa sunaila amsar tambayar sai kawai a ka ji wani gurnani
daga sararin samaniya,
Cikin hanzari kowa ya ɗaga kan sa izuwa sama domin ganin abin da zai wakana,
Nan take akayi arba da waɗansu halitta na sauka daga sararin samaniya,
Sannu a hankali halittun suka dunga sauko ƙasa,
Lokacin da suka sauka a turba sai aka fara kallon- kallo tsakanin su da su saurayi Hizmal,
Ba wasu ba ne halittun ba face aljani Haulatul-infal dauke da gimbiya Hushriba,sarki
shazwan,sarkin bokaye Dargas,da tawagar matsafa biyar,
Halitta ta biyu kuwa ba wata ba ce aljani Darmanu ibn kauƙas dauke da sa sarki uslaim da
boka ƙarzum da tawagar su
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin jaruma sunaila da yar uwar ta Hushriba,
Sarki sarki shazwan kuwa da saurayi Hizmal,
Sarki uslaim da boka ƙarzum kuwa sa aljani Marhutul-Azab,
Gimbiya Hushriba ta taka da kafafun ta ta durfafi inda Sunaila ke tsaye yazmana tazarar dake
tsakanin su bata huce taku goma sannan taja ta tsaya,
Kana ta buɗi baki cikin matukar ƙiyayya tace"yake yar uwa ta kuma babbar abokiyar gaba ta
har abada kiyi sani cewa nayi matuƙar baƙin ciki da na gano cewa mahaifin mu ya sanar da ke
maganin da zai warkar dashi daga shirin da muka yi masa domin ki samu nasarar hawa Bisa
karagar mulkin kasar mu,
Gashi Ni da dan uwana yarima zufair har kin riga mu mallakar yaro Humair makaho wanda
shine kaɗai iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI,
Kuma kina tare da aljani Marhutul-Azab dake ɗauke da taswirar fadar Sarkin bokaye inda anan
ne za'a ɗauko tsumin tsafi da mahaifan mu zai sha ya warke,
Duk da waɗannan nasarorin da kika samu Ina mai tabbatar miki dacewa sun tashi a banza
domin a yanzu batare da ɓata lokaci ba zan hallaka ki kuma na mallaki yaro Humair makaho da
taswirar fadar Sarkin bokaye,
Koda jin wannan batu daga bakin Hushriba sai jaruma sunaila tayi guntun murmushi mai tattare
da takaici yace"kaicon ki yake yar uwa ta haƙiƙa kin tafka babban kuskure da kike tunanin cewa
zaki samu nasara akai na kwatar yaro Humair tare mallakar taswirar fadar Sarkin bokaye,
Ki sani cewa har abada ƘARYA DA GASKIYA basa taɓa haɗuwa a waje guda, Domin kuwa
keda ɗan uwan ki kuna kwaɗayin mulki ne domin ku zalunci talakawa,
Wanda akan dalilin hakan ku kayi yunkurin hallaka mahaifin mu, Ni kuwa ina so na warkar da
mahaifin mu ne daga sihirin da kuka yi masa domin na samu nasarar hawa Bisa karagar mulki
domin na gaji mulkin adalci irin na mahaifin mu,
Sannan da kike iƙirarin cewa za ki samu nasara akai na shin kin manta ne cewa a halin yanzu
ina ɗauke da dukkan sirrikan tsafin mahaifin mu,
Koda jin wannan batu daga bakin sunaila sai Hushriba ta cika da matukar baƙin ciki zuciyar ta
kama tafarfasa tamkar zata kone,
Abangaren sarki shazwan kuwa bayan ya kammala karewa saurayi Hizmal dake goye da yaro
Humair makaho kallo sai ya dube sa cikin matukar fushi yace "yakai Hizmal kayi sani cewa
haƙiƙa ka aikata mini laifi mafi munin gaske sanadiyyar tseratar da rayuwar yaro Humair
makaho da kayi wanda sanadin hakan ya jefa al'umma ta cikin gagarumar tashin hankali
sakamakon GOBARAR DAJI,
Ina mai tabbatar maka da cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne,
Cikin ruwan sanyi ka damƙa mini yaro Humair domin na yanke maka hukunci cikin lumana ta
hanyar daddatsa sassan jikin ka,
Koda jin wannan batu daga bakin sarki shazwan sai saurayi Hizmal ya bushe da dariyar ƙarfin
hali sannan daga bisani ya murtuke fuska yace"kaicon ka yakai wannan azzalumin sarki da bai
damu da darajar ran ɗan adam ba face buƙatar kansa,
Ai a halin yanzu yaro Humair yayi maka nisa, domin bazaka taɓa samun nasarar hallaka sa ba
matsawar ruhina yana tare da gangar jiki,
Da jin wannan batu sai takaici ya turnuƙe sarki Shazwan jikin sa ya kama tsuma,
Har ya sake buɗar baki da nufin ya furta wani abu sai aka ga wani haske na ratsowa daga
sararin samaniya
Koda kowa ya mayar da duban sa zuwa ga wajen take aka yi ido biyu da wata tsaleliyar
kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance tare da wani dattijo mai karin shekaru zaune abisa kan
wata dardumar sihiri.
Mu haɗu a GOGA SHA FAMA 2
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
MANSUR USMAN SUFI
08137237071
BABI NA ƊAYA
Al'amarin su sarki uslaim kuwa lokacin da suka kammala fafata yaƙi da wadannan ayarin
gwaggwan birrai,
Sai sarki uslaim yayi umarni aka kafa tantuna domin ya da zango, nan fa kuyangi suka shiga
aikin dafa abinci domin yin kalaci,
Sarki uslaim ya shiga izuwa nasa tantin domin ya ɗan samu nutsuwa,
A lokacin boka ƙarzum ya kebance ana sa tantin domin shiga cikin halarar tsafin sa domin
gudanar da bincike na musamman,
Lokacin da ya baje alƙalumman sihirin yafara gudanar da binciken,
Abinda yafaru tsakanin sarauniya Nuwairat da boka Jadwar gami da su saurayi Hizmal ne
yafara bayyana a madubin tsafin,
Tun daga lokacin da waɗannan miyagun halittun ke biye da wannan kyakkyawar budurwa, har
izuwa lokacin da su Hizmal ɗin suka samu nasarar ceton rayuwar ta,
Sa'adda boka Jadwar yaga wannan al'amari sai kawai ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu
wanda ya firgita duk wata halitta dake filin sansanin kuma ya yi sanadiyar farkawar sarki uslaim
daga gyangyaɗin daya ɗauke sa,ya mike tsaye zumbur daga kan gadon sa,
Ya zare takobin sa ya ruga izuwa waje bisa tunanin cewa koda dakarun sumame ne suka kawo
farmaki
Ai kuwa koda fitar sa ya ruga izuwa kofar tantin da yaga dakaru na yin tururuwar shig,
Da isar sa izuwa wajen ya tusa kai izuwa cikin tantin
Nan take yayi arba da boka Jadwar zaune a bisa buzun tsafi fuskar sa a murtuke babu annuri,
Sarki uslaim ya dube sa cikin fushi yace yakai ƙarzum shin ina dalilin wannan kururuwa taka,
Koda jin wannan tambaya sai boka ƙarzum ya dubi Sarki uslaim cikin ladabi yace "Ka gafarce ni
ya shugaba na kayi sani cewa bakomai bane ya sanya wannan ihu ba sai bisa Abin da na gani
a cikin madubin tsafi na,
Abinda na gani ɗin kuwa shine abinda muka fito farauta wato yaro Humair makaho sun samu
nasarar ceton rayuwar wata jaruma da ake kira da suna Nihla,
Ya shugaba na kayi sani cewa a halin yanzu bincike ya tabbatar dacewa wannan budurwa itace
mace ta farko da SARKIN SADAUKAI Hibairu zai fara gani a rayuwar sa,
Kuma tabbas da zarar yagan ta zai kamu da matukar soyayyar ta
Haƙiƙa jaruma Nihla ita ce zata zamo tana sarrafa Hibairu tamkar yadda ake sarrafa masa akan
kasko saboda tasirin soyayyar ta a zuciyar sa
Wani abu daya kara dugunzuma hankali na shine al'ajanin dake ɗauke da su saurayi Hizmal
shine ke ɗauke da taswirar fadar Sarkin bokaye,
Babu wani mahaluki da ya isa yaje fadar Sarkin bokaye face ya mallaki wannan taswira,
Kaga kenan koda ace mun samu nasarar saduwa da Hibairu kuma ya amince zai ceto gimbiya
zarifa to fa tilas ne yazo muna ɗauke da taswirar fadar Sarkin bokaye,
Sa'adda sarki uslaim yaji wannan batu daga bakin boka ƙarzum sai hankalinsa ya dugunzuma
ainun fiye da ko yaushe,
Ya dubi ƙarzum cikin alamun tsananin damuwa yace yanzu mene ne abin yi ya masanin ilimin
tsafi,
Boka ƙarzum yace "Mafita ɗaya ce tabbas dole mu yi kokari mu riski su saurayi Hizmal,
Domin a halin yanzu kwanaki ƙadan ne suka rage su isa dajin Baitul-shamshan,
Kuma yanzu haka sarauniyar kyawawan duniya Nuwairat tare da boka Jadwar na biye da su,
Baya ga su ɗin ma akwai sarki shazwan tare da tawagar matsafan sun bazama farautar yaro
Humair tare wata hatsabibiyar jaruma mai Hushriba
Wacce takasance yar uwa ga jaruma Husnaila da ke tare da saurayi Hizmal domin tserar da
yaro Humair makaho
Tabbas masu iya magana na cewa A bari ya huce shine ke kawo rabon Wani
Kuma tabbas da zafi zafi akan daki ƙarfe domin a sarrafa shi yadda ake buƙata,
Tabbas wanda ya daɗe zai ga daɗau,
Sa'adda boka ƙarzum yazo dai dai nan zancen sa sai sarki uslaim yace "Haƙiƙa zancen ka
dutse ne ya dodon bokaye,
Yanzu dazarar mun yi kalaci za'a cigaba da tafiya ba zamu yada zango ba,
Koda gama faɗin hakan sai sarki uslaim ya juya ya fice da ga masaukin boka ƙarzum,
Wannan shi ne abinda ya faru da sarki uslaim da tawagar sa a lokacin da suka kammala artabu
da gwaggwan birrai,
A ranar da tafiya dajin Baitul-shamshan tazo tun sa'adda alfijir ya keto SARAUNIYA
ABIDATUL-AULIYA ta kammala shiri tsaf
Ta zauna tana jiran matsafi shubairu, tsawon daƙiƙa hamsin tana zaune a cikin wannan hali ne
kwatsam bazato babu tsammani sai matsafi shubairu ya bayyana a gare ta a cikin siffar wannan
kyakkyawan tsuntsun da bayyanar sa sai ya rikiɗa izuwa ainahin siffar sa,
Sa.adda Abidatul-auliya tayi arba dashi sai ta miƙe tsaye cikin matukar farin ciki taje ta tare sa
fuskar ta cike da annuri,
Matsafi shubairu ya dube ta cikin wani murmushi mai ɗimauta zuciyar duk wata ya mace mai
hankali ya buɗi baki cikin tattausar murya yace"Barka da wannan lokaci ya sarauniyar
kyawawan duniya Abidatul-auliya bintu shafwaz,
Abidatul-auliya fuska cike da annuri tace cikin zazzakar murya tace "Barka da zuwa JARUMIN
JARUMAI kuma sadaukin mazaje,
Tun tuni na kammala shirin komai kai kaɗai nake jira domin gudanar da gagarumar tafiyar mu ta
zuwa dajin Baitul-shamshan domin saduwa da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI ko zamu
samu nasarar cika burin mu na mallakar tsumin tsafi dake fadar Sarkin bokaye domin warkar da
lalurar kuturtar tsagin jiki da ta same mu,
Dajin wannan batu daga bakin Abidatul-auliya sai matsafi shubairu yace"Ai bakomai ne yasanya
nayi jinkirin bayyana a gare ki ba sai domin a lokacin da kika fito ba lokacin sa'a a tafiya ba ne,
Bisa hakan ya sanya na jinkirin ta amma yanzu batare da bata lokaci ba zamu fara wannan
tafiya,
Koda gama faɗin hakan sai matsafi shubairu ya buɗe bakin sa ya karanta wadansu dalasiman
tsafi yake wani Dankareran tsuntsun tsafi ya bayyana a wajen,
Shi dai tsuntsun tsafin yakasance yana kama da mikiya sai dai kan sa irin na batoyi ne,
Koda bayyanar tsuntsun sai matsafi shubairu yayi wa sarauniya Abidatul-auliya nuni da ta hau
bisa tsuntsun,
Batare da bata lokaci ba ta hau ta zauna, Shubairu yayi koyi da ita,
Kawai sai tsuntsun tsafin ya kaɗa fuka -fukan sa ya tashi izuwa sararin samaniya ya na mai
keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya,
Wannan shi ne abinda ya faru da sarauniya Abidatul-auliya ta birnin Tehran tare da matsafi
shubairu daya bayyana a agare ta da siffar kyakkyawan tsuntsu.
Lokacin da sarauniya Nuwairat da boka Jadwar suka bi sahun aljani Marhutul-Azab dake ɗauke
da su yaro Humair makaho,
Sai suka wanzu suna tsala gudu a cikin gajimare bisa kan Dardumar sihiri
Tafiyar Sa'a biyu da daƙiƙa hamsin kacal suka yi su na wannan gudu,
Su na cikin wannan tafiya ne sarauniya Nuwairat ta dubi boka Jadwar tayi gyaran murya tace
"yakai Jadwar shin nan da wani lokaci ne za mu iya cimma su saurayi Hizmal?
Da jin wannan tambaya sai boka Jadwar yayi shiru gami da runtse idanun sa,
Daga can sai ya cire kai ya dubi sarauniya Nuwairat yayi gyaran murya yace"ya shugaba ta
haƙiƙa cimmu su a wannan lokaci abu ne mai matukar wahalar gaske domin kuwa aljanin dake
ɗauke dasu shine aljani mafi tsananin karfin gudu a cikin jinsin aljanu,
Sai dai duk da hakan akwai yiwuwar zamu iya cimmu su a lokacin da zasu yada zango,
Koda jin wannan batu daga bakin boka Jadwar sai sarauniya Nuwairat ta cika da matukar farin
ciki
Daga wannan furuci ne kowa yayi shiru babu wanda yakara cewa kala,
Wannan shi ne abinda ya faru da sarauniya Nuwairat da boka Jadwar akan hanyar su