Rainon Soja Book 2 Hausa Novel By Maman Teddy .pdf

Author :  Aisha Maman Teddy Category :  Taskar Novels

Chapter   7 / 10

18K to 21K   out of 29.9K words


nace fiye , don haka ku kama kan ku babu ruwan ku da yarinya ta. Aiki kuma daga yau na cire
maku kusa mun ita bare har tayi ɓarna kuce tace maku ita yarinya yanzu kowa ya samata ido .
Nafi san haka kawai .

Kai kuma Ali kar ka ƙara saka mun yarinya knee down har ƙafafunta su kumbura irin haka!
Fatan ka jini da kyau?. Gyaɗa kai yayi tare da cewa “ Yess mami ”. Juyawa tayi tana dafa

Ma'eesha tare da cewa “ Lets go baby”. Fuska a narke don har a lokacin kuka take yi sosai don
ƙafarta zugi yake mata zugin da bata taɓa jin irin sa ba .

Mami anya babu kuskure anan? Muryar jidder ya katse su tana kwantar da murya a makirce
kana ta cigaba da cewa “ Common thing indomie Ma'eesha Bata iya girkawa ba ,aƙwai matsala
fa a ƙasa ”. Aure zan mata! Nace Aure zan yi mata da zan damu ta iya indomie ko bata iya ba .
Bare yanzu fa take ɗagawa wannan duk mai sauƙine nasan zata iya nan gaba .
Muryar Haidar ne ya katse su yana saƙo da maganar sa cikin hikima da dabara “ eh zata iya
don datayi na farkon baiyi dadi amma na biyu yayi daɗi sosai kamar kar ya ƙare. Shiyasa ma
nake so gobe mu tafi Lagos tare tayi hutun ta Acan.

Buɗe baki Mami tayi tana waro manyan idanun ta wanda Aliyu ya ɗebo su waje kana tace“
Wannan dai yarinyar tawa Ma'eesha ce zan baka ita Ali ka tafi da ita kake nufi? ”. Kallon Mami
yayi yana gyaɗa mata kai Alamun eh jikin sa yana dan sanyi don dama yasan za'a kai ruwa
rana wurin Amincewar Wannan tafiyar nasa da Ma'eesha ”...To baka isa ba, Ba zan yarda da
Wannan tafiyar ba . Mami ita ce take so , Ma'eesha bakya so mu tafi tare ? Yayi maganan yana
sauke Muryar sa tamkar ba shine mai bata horon nan ba ”.

Ɗago da ido Ma'eesha tayi tana kallon Mami kana ta kalle shi tsoron gargaɗin da yayi mata ne
ya dawo mata ka....Wannan yasa ta gyaɗa kai hawaye na kwanciya a idanun ta kana tace “
Mami ina so zan bi Uncle ”. Nasan zai kula dani sosai ’. Hummmmmmmm ..... Numfasawa
Mami tayi kana ta rungume Ma'eesha tsammm tana furta “ Allah sarki Aiiiii na . A'isha na
Ma'eesha . Yau zamu fara shiri ,amma yanzu zan fara gasa ƙafarki ne ya saki sai kiyi barci gobe
sai ayi shirin tafiya da Uncle . Aliyu.....!!! Mami ta kira sunan sa har sau uku kana tace “ Ka kula
da Ma'eesha tana budadden zuciya tana jin ka sosai a ranta da zuciyar ta . Ma'eesha ƙanwa ce
a gare ka .


“Ohhh Mami ” ki daina faɗin haka , Ma'eesha ba ƙanwata Bace mami nine fa Aliyu , Ai Ma'eesha
ƴa ce a gare Ni . Wanda na ɗauke ta da hannu na kuma na Raine ta . Mashaallh Uban san
girma , na baka Ma'eesha a yanzu ma .... Ma'eesha na! Ta kira sunan ma'eesha da ta zuba
mata lumsassun idanun ta kamin tace “ Na'ma Mami”.
Kin shirya Uncle Haidar ya ƙara Miki RAINON SOJA a karo na biyu?. Zai kula dake sosai ina da
yarda dashi da amincewa da zai kula mun dake . Cike da Yarinta ta saki Murmushi tana
gyaɗa kan ta tace da cewa “ Eh mami nasan Uncle zai kula dani sosai . Muje fara shirin tafiya
nidai kam sai da ɗan hawaye ya tsillo daga ido na don na tausaya ma Ma'eesha a
hannun Ali haidar a wannan karon ”.


Tana Rungume a jikin mami suka nufi bedroom din ta suna barin falon . Jidder taso hana
wannan tafiyar amma kuma bata da yanda zatayi saboda Tafi son taga ta raba Mami da

Ma'eesha kamin ta dawo ta ɓanɓareta ta da Haidar,amma ita har a yau so take taga Ta bude
ido Ma'eesha ta bar cikin gidan .
**
7:00pm.
Zaune suke duka a falon Daddy kowa da Abin da yake yi. Ma'eesha na gani daga ƙasa inda
Ƙafar Daddy yake tana rungume da yar teddy din ta Pink mai kyau tana murmushi alamun
Daddy wani maganan yake faɗa mata . Ɗagowa tayi tana kallon Khalil da shima ita yake kallo .
Sosai yake tsintar kansa cikin yanayin jin daɗi a duk lokacin da yaga murmushi a tare da
Ma'eesha ”. Ya Khalil i will miss you ”. Ta furta tana kallon sa . Murmushi yayi yana danne abun
dake taso mata kamin yace “ i will miss you too Ma'eesha na”...Da Sauri Ma'eesha ta miƙe tana
nufar inda Khalil yake tare da rungume shi.... Rungume ta yayi yana murmushi tare da cewa
"nan kusa zaki dawo ai . Wani irin zafi Aliyu................!





*Ban yarda ki karanta mun baki biyani ba . Wanda ya karanta shi da Allah . Masu ɓukatar
regular group ₦500 vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha
keystone bank*
[1/6, 4:25 PM] Real~Mamanteddy: *️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*


23


Barkan mu da dawowa wannan tafiya da muka ɗan jinkirta wurin kawo maku shi ,hakan ya faru
ne Sakamakon ɗan rashin lafiya da nayi ,amma yanzu jiki alhmdlh komai normal ina
sauraren sharhin ku tare da fatan Alheri ina kuma godiya sosai . Taku Ayshatu Mrs
Usm...(Maman-teddy).

*Don girman Allah kar ki karanta indai baki biya kudin littafin ba . Masu buƙatar payment regular
group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha
keystone bank shaidar biya ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 yan Niger katin
Artel zaku tura na 500f*

Wani irin zafi Zuciyar Aliyu keyi ganin yanda Khalil yasa hannayen sa biyu yana rungume
Ma'eesha cike da kulawa . A hankali Zuciyar sa ta fara tambayar sa da “ Me yasa kake jin zafi a
duk lokacin da kaga Ma'eesha da Wani ɗa namiji bayan kai koda kuwa jinin ka ne? . Ɗan
lumshe dulu-dulun idanun sa yayi yana ba kansa amsa da cewa “ Saboda ina son kare

mutuncinta ne ,don babu wanda yasan darajarta da ya wuce Ni . Su duka sauran ganin ta suke
kamar kowacce ƴa , Ni kuma a jinin jiki na ke jin ta . Wannan shine banbancina da su . Shi
kuma yasa nake jin zafi a duk lokacin da na ganta tare da Wasu maza . Saboda maza basu da
tabbas.

Ma'eesha ya kamata kiyi barci yau da Wuri kar gobe kiyi mun barcin mota . Don NDA zamu fara
zuwa daga can mu wuce Aviation .

Muryar Aliyu ya katse su , yana mai zuba idanun sa zuwa inda Ma'eesha take zaune a jikin
Khalil suna magana ƙasa ƙasa wanda babu mai jiyo su . Wato yarinyar nan har Tasan ta rinƙa
irin wannan maganan amma bata iya girki ba? Zata sani ne? Duk wani kalan girki sai kin iya shi
haka Aikin cikin gida , don ko Bedroom baki iya gyaran shi ba . Wannan ɗabi'un naki duka basu
yi mun ba dole na sauyaki zuwa yanda nake SO .

Duka maganan yake a zuciyar sa , yana yi yana ɗaura yatsunsa bisa pillows din dake Daga
saman Cushine ɗin da yake zaune ,yana matsasu ji yake tamkar bakin Ma'eesha yake matsawa
da ƙarfi haka don ya ɗau Aniyar ganin ya saita ta yanda yake So, don a ganin sa Sangarta ta
Mami tayi ba tarbiyya ta bata ba . Muryar Mami ne ya katse su inda take cewa “ my baby A
tashi haka nan , nasan ki da son barci kinji tun yanzu sharuɗan da ya fara yi Miki . Nifa Ali indai
wannan tafiyar taka da Ma'eesha da takura wahalar mun da ƴarinya zaka yi Tom a haƙura ,
Nima ba SO nake nayi nisa da ita ba ” . Mami ta ƙare maganan tare da Watsa ma Haidar kallon
uku saura ƙwata .

Cike da Ƙwantar da kai da murya Ya furta “ Mami please ki daina tunanin komai fa , Ma'eesha
tawace! ....gigif Khalil yayi yana miƙewa daga kishingiɗen da yake bisa ga jin Furucin Ali Haidar
...Muryar Aliyu ne ya cigaba da cewa “ Ba zan Wahalar Miki da ita ba , cool your mind please ” .
Hummmm ... Mami ta sauke wani gauron numfashi kana tace “ Alright ga Amanata nann” .
Uhmm Mami kenan . Nifa mamaki kike bani wallahi ...Haidar ne zaki ba Ma'eesha wai kuma
kike tunanin ba zai wahalar da ita ba? Ai kima bar wannan tunanin Allah dai ya bata ikon cinye
jarabawa ”.

Dariyar Mugunta ne ya kusa kama Jidder don ita a rayuwar ta bata da Burin da ya wuce Taga
Ma'eesha cikin mawuyacin hali . Amma sai ta dake tana cigaba da latsa Wayar ta tare da
karƙaɗa ƙafa ɗaya .

Buɗe baki Mami tayi tana shirin magana Muryar General Saleh Yelwa ya katsesu da cewa “ Ya
kamata yanzu fa kusan kun girma haka nan. Khalil Haidar , wai yaushe saɓani ya fara shiga
tsakanin ku? Ƙwata² babu jituwa kaman ba kaine Ali haidar mai tausayin Yayan ka ba . Mai
kuma haƙuri da masa biyayya....Kai kuma Khalil kamar ba kaine babban Yaya ba , Wanda koda
ya ɓata maka kake dannewa Bama kason mu sani . Please ku cigaba da yanda kuke a da baya
. Abun naku yana neman zama sakarci kuma na rasa gane menene ya kawo maku wannan
rikicin haka!

Tsit...!!
Falourn yayi har Daddy yayi maganan sa ya gama , sai Muryar Mami da ta furta “ Suma dai yi ,
Ni nawa ido , zasu daina ,abin da basuyi farkon shi ba ai baxasu yi ƙarshen sa ba. Ma'eesha na
taho muje kiyi barci .


“Da sauri Ma'eesha ta miƙe tana kallon Mami kana ta saki Murmushin nan nata tana cewa “ No
mami zan ƙwanta ba sai kinzo ba . Wankan kuma fa? .

Muryar mami ya katse ta , wanda jin haka yasa ta saurin juyawa tana kallon inda Ali Haidar
yake , gabanta na bugun uku² , a Zuciyar ta tana cewa “ Na shiga uku kar Fa Uncle yace Har
Wankan ma ban iya ba naja ma kaina ”. Shagwaɓe fuska Ma'eesha tayi tana cuno ɗan mitsulun
bakin ta tare da cewa “ Mami nifa ba kya mun wanka tuntuni Ni nake yin abu na ”. Dariya Daddy
da mami suka saka harda Khalil .....Wannan yasa Ma'eesha juyawa tana barin falourn , Don sun
fahimci Ma'eesha ba son zancen wanka take yi ba a gaban su Khalil da Haidar .

Kaman mintuna biyu Khalil ji yake tamkar ana tsingulunsa , Abubuwa da yawa na cunkushe a
cikin Zuciyar sa . A hankali yakai hannun sa yana dafe ɓarayi guda na Zuciyar sa kana ya rintse
idanun sa .... lokaci guda Idanun sa sun sauya kala sunyi jah....miƙewa yayi yana kallon Su
mami kana yace “ Ammmm Bara na duba Ma'eesha ta ƙwanta kuwa! . Uhmmmm aifa duba mun
ita , don kwana biyu bata barci sai Game a laptop ɗinta tun da suka samu Hutu itama take
Hutawa abinta. Mami tayi maganan tana bin bayan Khalil da kallo don tuni ya nufi hanyar da zai
kaishi zuwa Bedroom ɗin Ma'eesha ”.

Ɓangaren Aliyu kuwa tun da Khalil ya miƙe yaji jikin sa bai basa ba , wannan yasa shi Oga ne
bai tsaya yi ma kowa magana ba yayi gaba yana nufar Bedroom ɗin kansa tsaye.

Hannun sa yasa a Handle Door din yana ƙoƙarin murɗawa yaji furucin Khalil daga ciki wanda
sai da Ƙirjin sa ya buga da ƙarfi . Wannan yasa shi dakatawa yana Sauraren kalaman Ma'eesha
”.

Ya Khalil Menene? Meke faruwa ya Khalil? Tana maganan Muryar ta na rawa alamun kuka
....Muryar ta ne ya cigaba da Amon cewa “ Ya Khalil ƙwallah ne fa nagani ko nace hawaye a
ƙwance a idanunka . Hummmmmmmm Jan Ajiyar zuciya yayi yana saukewa kana yace “
Yessss Ma'eesha hawaye ne wannan sannan kar kiyi mamakin ganin su” .
Ya Khalil menene ya saka ka kuka? Mene ya faru? Kukan......Shiiiii ɗaura yatsarsa yayi bisa
laɓɓanta yana katse zancen nata kana yace “ Sorry dear Kece kike saka zuciyata wannan
kukan tuntuni wanda a yanzu ta kasa daurewa da jurewa har idanuna sun fara zubda Ƙwallah ”
.
Jikin ma'eesha ne ya hau Rawa , ƙwallah na ciko idanun ta . Cikin kuka ta fara furta “ Ya Khalil

me nayi maka Ni? Ka faɗa mun na baka haƙuri ”.


Numfasawa yayi kana cikin wani irin sarƙaƙƙiyar murya ya furta “ I love You Ma'eesha.... Nasani
ya Khalil nasan kana so na , nima ina Sonka. No! Ba Wannan soyayyar ba. Son ki nake Don
Allah Ki Aure Ni mu rayu tare A matsayin miji da mata� yayi maganan yana zubewa Gwiwowin
sa ƙasa a gaban ta . Wani irin bugawa ƙirjin ma'eesha keyi ....cikin Muryar kuka ta
furta.........................!





*Ban yarda ki karanta mun wannan labarin ba tare da kin biyani ba . Don Allah kar a soma ayi
hakan . Masu buƙatar payment regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via
6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932
ƴan niger katin Artel 500f zaku turo.* [1/7, 3:59 PM] Real~Mamanteddy: *️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*
https://youtube.com/@mamanteddy4123?si=1cwxAAGsGEzYkelS
Subscribe to MAMAN TEDDY channel @youtube.
24.
Ya Khalil nifa ƙaramar yarinyace kai ne fa naji kana yi ma Anti Jidder faɗa kan karta fara
soyayya! “Yesss”Na sani Ma'eesha, amma tawa soyayyar ba shiririta bane irin nasu . I
really......A'a Ya Khalil Anty Maryam fa? Kwanan fa Za'a yi baikon ku . Muryar Ma'eesha ya
kuma katse ta wanda har kyarma jikin ta ke yi . Ma'eesha!!! Ya kira sunan ta cikin wani irin
Murya wanda bata taɓa jin sa da irin ta ba . Hummmm .... Furzar da Huci yayi kana yace “
Ma'eesha Ni SOJA ne , duk Abinda zai saka Soja ya gurfanar da kan sa da Gwiwowin sa ƙasa
ba ƙaramin abu bane ba , babba ne , wanda girmanta ya kai Akira wannan abun da rayuwar sa
. Ma'eesha idan na rasaki numfashi na zai dakata da Aiki . Ina nufin zan zaɓi mutuwa da
Rayuwa ta�”. Dam-dam-dammmm ƙirjin Ta ya buga da ƙarfi ....cikin Muryar matsanancin kuka
ta furta “ Sorry Ya Khalil ina Sonka”. Wani irin baya Aliyu yayi da yake jikin ƙofan yana zame
hannun sa a hankali duhu duhu na gilma ma idanun sa . Ji yayi jikin sa yayi Wani irin mugun
sanyi sam babu ƙarfi a tare dashi bisa ga jin Furucin Ma'eesha na “ Ina Sonka!”. Zazzaƙar
Muryar ta ne ya kuma katse shi tana faɗin “ Kar kayi tunanin bana sonka Ya Khalil kome kace
nayi maka a shirye nake zan maka shi ”.

“ Cikin Sauri cike da jin Daɗi mara iyaka Khalil ya miƙe daga gurfanen da yake , Hannun sa biyu
yasa yana tallabo kuncinta ta tare da saita idanun sa yana Ɗaurawa bisa nata. “Thankyou
Ma'eesha , na gode!

Ya Khalil to Anty Maryam fa? Da.....shii ki manta da Wannan maganan zan Auri Maryam a
wannan shekarar ke kuma zan cigaba da dakon soyayyar ki har ki girma ki kai lokacin da Daddy

zai Aurar dake , A wannan lokacin zamuyi Aure mu gina Rayuwar mu cikin jin daɗi . Kece nake
so ki haifa mun ƴaƴa masu kama dake ....ya ƙare maganan yana Ɗaga mata gira tare da Sakin
mata murmushi kana ya cigaba da cewa “ Zan Auri Maryam ,amma ba zata haihu ba . Kece zan
jira ki zo ki haifa mun masu Albarka ”.
Cike da Yarinta Ma'eesha ta gyaɗa masa kai tare da cewa “ Shikenan Ya Khalil zan yi barci
yanzu ”. Alright sweat dream...ya furta yana kama ta tare da nufar Bed ɗin ta sai da ta kwanta
sannan ya rufa mata bargo yana takawa tare da rage hasken fitilun Bedroom din yana nufar
Ƙofar fita .
Jin takon sa yasa Ali Haidar Saurin barin wurin yana nufa falo .

A wannan dare a taƙaice sam Aliyu ya gaxa rintsawa , zuciyar sa na masa saƙa da Warwara .
Inda ya kasa gasgata wani ɓangare ɗaya na Zuciyar sa . Sai dai kafewa da yayi akan cewa “
Khalil na son lalata Ma'eesha ne . Har ya fara tunanin ɗaukar mataki da fushin Zuciyar sa ,sai
kuma yace “ A'a ba haka zan yi ba , Ni yanzu da zan tafi tare da ita , ganin ta sai yayi masu
duka wuya .bare har ya kawo wani zancen shashanci mtsww .

**
7:35am.
Mami na hango gaban dressing mirror tana gyara gashin kan Ma'eesha da yake fidda
Sanyayyar ƙamshi , ga tsawo da cika sunan ta kama mata shi ne wuri ɗaya amma Tudunshi har
yayi yawa gashi ya sauko har gadon baya . Ka rantse da Allah Jinin mami ce itama wato fulani .
Riga da Wando ne ta jikin ta ,irin suit masu kyau na mata . Sai mami ta ɗaura mata Hijab ƴar
ƙarama wanda bai ƙare sauka kafaɗa ba ”. Turare take sa mata tana murmushi tare da cewa “
Yau sai na

7 / 10