SANADIN KENAN 1 HAUSA NOVELS BY TAKORI.doc

Author :  sumayya Abdulkadir Takori Category :  Romance

Chapter   9 / 10

24K to 27K   out of 27.7K words

a kafofin yada sadarwa masu matsalolin can da ya ambata a baya.
Matasan Bauchi da iyayen yara talakawa suka amsa kiransa da gaggawa, ya dora ma aikata masu amana, aka soma yi wa matasan maganin matsalolinsu daga cibiyar MA AROUF FOUNDATION. Ya gina katuwar makarantar firamare ta kyauta, wadda gwamnati ta san da zamanta.
Allah kadai ya san adadin matasan da suka samu kwalin digiri daga aljihun Ma arouf a jihar Bauchi. Su gama ya yi musu hanyar samun aiki daga gwamnati ko (private sectors), ilmin firamare mai kyau (free) ga kananan yara, masu zaman banza an sanya su (6-week orientation) sun koyi sana o i ana ba su wadataccen jari. Sai a hankali sunan Ji-qas ya fita a Bauchi har ake masa kallon wani babban dan siyasa ne. Har zuwa yanzu (foundation) din na ci gaba da gudana.
Wannan ne ya janyo ra ayin matasan Bauchi na son ya tsaya musu takarar gwamna na kara yaduwa. Sun yi gangami sun bayyana masa ra ayinsu na son ya shiga siyasar ya taimaka wa jiharsa, su kuma za su tsaya wajen yi masa kamfen babu ko sisinsa. A lokutta da dama hakan ta faru babu wanda ya samu gamsasshiyar amsa daga bakinsa.
Daga baya jama ar suka bi ta kan surukinsa wanda an san ba ya ketare shawarwarinsa a gare shi. Sun zauna ya yi masa nasiha, cewa ya rungumi alherin da mutane suke so da shi, ya tsaya takarar ya barsu da kokarin komai na Allah ne. Mahaifinsa kuwa addu ar da ba ya fasa yi masa kullum ita ya yi masa, yana fadin,  Allah ya yi jagora, Allah ya zaba mafi alkhairi .
Hajiyan Ji-kas, kusan ra ayinsu daya da Baba, cewa ta yi idan siyasar alkhairi ce Allah ya yi riko da hannunka .
Aisha ce kadai ba ta son zancen siyasar nan. A cewarta yanzu haka sai in dau lokaci ban sa ka a idanuna ba, kana nan kana can, ina kuma ga ka shiga siyasa? Ina kuma ga ka zama gwamna?
Ita ma ba ya ba ta amsa, murmushi kawai yake yi.
Yau da gobe ba ta bar komai ba, kwadaita masa siyasar da kowa ke yi da goyon bayan da ya samu daga sama da kasa ya sa ya amince, ya shiga siyasa karkashin jam iyyar (NPC) wato  Northern People Congress . Bai tsaya takarar gwamna ba, ta dan majalisa ya tsaya mai wakiltar Bauchi ta Kudu don ya kara bude ido da yadda al amuran siyasa ke tafiya.
Ai kuwa da gudu ya haye, suka koma Abuja shi da iyalinsa. Su Baba kan je, Hajiyan Ji-kas kan je ta yi hutu duk sanda ta so, su ma kuma suna zuwa ganinsu akai-akai.
Ashe da kafar dama suka fada siyasar, domin a shekarar ne ciki ya billo a jikin Aisha. Murna da godiyar Allah gurin ma auratan da iyayensu da duk wani mai kaunarsu abin ba a cewa komai. Sai shukrah ga Lillahi.

*** *** ***
Aisha ta sauka lafiya a  National Hospital ta samu  yarta mace, santaleliya mai kama da ubanta a komai. Ranar suna Baba ya sanya mata suna Amina. A cewarsa babu sunan da ya kai wannan albarka (Aminatu mamar Manzo) haka yake kiranta.
Amina ta taso cikin gata da soyayyar iyaye da kakanni. Hajiyar Ji-qas Abuja ta dawo kacokam tana musu jego, yanzu kam Aisha ta dade da zama tauraruwa a cikin  yan uwanta, kowa nan-nan yake da ita saboda ita Allah ya rufa wa asiri fiye da su. Ba ta ki su ba, kuma ba ta hana su rabar arzikin da Allah ya yi mata ba. Dogon hannu gare ta, kullum cikin mikawa kowa abin alheri ta ke. Don albashi gare ta mai zaman kansa cikin (account) dinta, duk wata Ma arouf ke zuba mata, ba ruwansa da me za ta yi da shi.
Yanzu shekarun Amina hudu ke nan a duniya, ta dade da shiga makaranta. Ma arouf (tenure) dinsu ta kusa cika, sun yi nisa da yawon kamfen da shirye-shiryen zabe mai zuwa ba da jimawa ba. Shi ne dan takarar da jam iyyarsu ke tinkaho da shi, kuma dan takara mafi rinjayen magoya baya.

*** *** ***
Jirgin gab yake da sauka a filin jirgin zaman Abuja, idanunsa a lumshe, fuskarsa rufe cikin hular kansa, kan nan sumul ya sha saisaye irin na su na masu madafun iko. Za ka yi tsammanin tunda ya zauna cikin jirgin bacci yake yi, sai yanzu da aka ce ya yi fasten belt jirgi zai sauka. Ba bacci yake ba (flash back) ne na gwagwarmayar rayuwarsa ya gilma masa.
Ya ja dogon numfashi ya sauke. A hankali ya bude idonsa, ya cire hular daga fuskarsa ya mayar da ita mazauninta. Ya mike ya fito daga cikin jirgin inda dumbin jama arsa ke jiran fitowarsa.
Daya bayan daya yake mika wa jama arsa hannu suna musabaha, kamin su dunguma su shiga motocin da suka zo a cikinsu. Motar sakatarensa Idris ya shiga suka shiga cikin birnin Abuja, sai da suka kai shi har gida sannan suka juya. Gidansa na Abuja a  Apo ne. Tuni kukun gidan ya kammala komai na abincin rana a tebirin cin abincin falon ya gaida ogan ya fita.
Sallah ya fara yi, sannan ya ciro wayarsa daga cajin da ya sanya ta. Cike da mamakin me ya sa Aisha ba ta kira shi ba, in shi jama a da rashin cajin waya sun hana shi kiranta.
Kunna wayar ke da wuya ya tadda  missed calls har ba adadi, sai (text messege) na Aisha guda uku, su ya fara budewa.
 Mun kusa isowa, da fatan ka sauka lafiya, I ll miss you beyond expression Baban Amina& 
Murmushi ya yi, Aisha ke nan, me ya kawo maganar  missing kuma (kewa) bayan waje daya za mu kwana? Ya bude  text na biyu.
 Ka taya ni kula da Ameena, ba don na raina kulawarka gare ta ba. She will need extra more& 
Na uku, kuma na karshe, mafi gajarta, ga abinda Aisha ta rubuta;

 Lots of love, Aisha Mansur .

Lumshe ido ya yi. Ya zauna a dandaryar  tiles yana dan nazarin kalaman nata. Kafin ya danna mata kira.
Ya yi-ya yi iya kokarinsa layin ya ki shiga, sai ya danna ta direban Aisha wanda ya dauko su daga Bauchi.
Iya kokarinsa ya yi, Malam Bukar bai daga waya ba, alhalin kuma ga ta nan tana ta ringin. Kamin ya yi wani yunkurin kiran bakuwar lambar da ya gani ba adadi da ya kunna wayarsa ya sake shigowa.
A ka idarsa ba ya amsa kiran lambar da bai sani ba, amma sai ya ji gabansa ya yanke ya fadi, zuciyarsa ta tsinke daidai shigowar wannan kira, don haka a sanyaye ya latsa (accept button).
Abin da aka gaya masa shi ne abu mafi tashin hankali a kafatanin rayuwarsa, kuma tun daga lokacin rayuwarsa ba ta kara komawa yadda ta ke ba.
 Sun yi accident, matar da direban sun rasu, yarinyar na ICU na ABUTH .
Rasa abin da zai ce ya yi. Ban da zama a dandaryar  carpet , wata irin zufa ta shiga keto masa har daga dan yatsansa na kafa. Daga bisani kamar wanda aka yi wa wahayi, ya soma ambaton,  Innalillahi wa inna ilaihi raji un .
Duk wata basira ta bace masa. Idanunsa sun yi jajawur, amma hawaye ko digo daya ya kasa fitowa balle ya ji dan sanyi. Ji yake kamar an gumbuda masa barkono a idanunsa. A haka ya shafe awa daya a zaune.
Ma arouf Ji-qas bai dauki Aisha da soyayyarta nan kusa ba. Har dai da ta haifa masa sanyin idaniya AMEENAH. Tunda ya aure ta bai kaara kallon mata da sunan so ba. Ta kankane ta toshe duk wata kafa da zai bukaci karin mace. Da gaske dan sandan nan yake? Aisha ta bar duniya bari na har abada?
Da sauri ya rarrafa ya isa ga wayarsa, ya budo  texts dinta da ya gama karantawa yanzun nan.
 I will miss you beyond expression Baban Amina.
Ka taya ni kula da Ameenah ba don na raina kulawarka gare ta ba, she will need extra more&

 Lots of love, Aisha Mansur .

A wannan karon ne wasu zafafan hawaye suka zubo wadanda sun fito ne tun daga karkashin zuciyarsa.
 Ashe Aisha bankwana ki ke mini? You are bading a farewell?
Sai kuka mai tsanani.

Wayarsa ta ci gaba da ruri har ba adadi, dole ya daga, dan sandan dazu ne yake masa tuni su yi gaggawar zuwa ABUTH su tafi da gawarwakin, sannan yarinyar na bukatar kulawa ta musamman.
Cikin hawaye mai tsananin yawa ya latso lambar Baba.
 Baba wai Aisha sun rasu, suna ABUTH, mu je mu dauki gawarsu. Ba zan iya kiran Baba Mansur& .....
Baba ya kidime,  Me ka ke fada ne? Ba na fahimtarka sosai& 
 Su Aisha sun yi  accident sun rasu Baba .
 Innalillahi wa inna ilaihi raji un . Baba ya ambata, kamin dif! Ya kashe wayar.
Mikewa tsaye Ma arouf ya yi da wayar a hannunsa, ya latso lambar Hajiyan Ji-qas.
 Sun rasu Hajiya! Abinda ya fara furta mata ke nan, yana mai share ambaliyar hawayensa.
 Su wa? Hajiya ta tambaya cikin tashin hankali.
 Su Aisha! .
Hajiya ta debo salati ta dire,  Ma arouf saurare ni, kada ka yi tuki da kanka, nemo direba. Bauchi za ku wuce da su .
Kamar wani karamin yaro ya ce da Hajiya,  Toh .
Wayar Anas direbansa ya kira, da ma yana harabar gidan. Nan da nan ya fiddo mota suka kama hanyar Zaria.
An basu gawar Aisha da direbansa na Bauchi malam Bukar, da Amina wadda ta jikkata sosai a (ambula???? 
  
 !"#$%&'(*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?nce) suka kama hanyar Bauchi.
Suna isa Bauchi aka wuce da Amina ATBU Teaching Hospital, su kuma suka isa unguwar Yalwa, ainahin gidan iyayensu. Inda aka yi wa mamatan suttura zuwa gidansu na gaskiya.
Idan Ma arouf ya zauna yana tuna yadda da hannayen nan nasa ya sanya Aisha cikin kabarinta, sai hawaye su tsattsafo mishi. Ya kara yarda rayuwa ba komai ba ce. Kamar matafiyi ne ya tsaya don ya huta ya ci gaba da tafiya. Sai ikhlasi ya kara cika zuciyarsa.  Memories na rayuwarsa da Aisha ya dawo masa sabo fil.
Ya ki zama wajen karbar gaisuwa koyaushe yana asibiti gurin Amina, wadda ba ta farfado ba ma balle a san hakikanin  injuries dinta. Likitoci dai sun tabbatar tana numfashi da taimakon (oxygen), ta kuma karye a dukkan kafafunta.
Aisha tamkar ruhi ce a gare shi. Ya tabbata ya yi babban rashin da ba zai taba maidawa ba. So zama ana mishi gaisuwa ba abin da zai rage na daga radadi da zugin da zuciyarsa ke yi na rasa ta, sai dai ya kara. Don haka ya zabi da ya yi nisa daga amsar gaisuwar.
Kwanan Aisha bakwai da rasuwa wanda ya yi daidai da kwanan Amina bakwai a asibiti, cikin matsananciyar kulawar likitoci numfashinta ya daidaita. Aka cire (oxygen) aka ci gaba da bincike ta. Daga baya likitocin suka kira Ma arouf don gaya masa halin da diyarsa ke ciki.
Ma arouf wanda komai na duniya ya fice masa a rai, burinsa a yanzu tashin kafadar gudan jininsa, ya yarda Aisha ta tafi, inda ba za ta taba dawowa ba. Ya karbi wannan kaddarar da hannu bibbiyu, fatansa Allah ya tashi kafadar Ameena ya samu mai taya shi yi mata addu a.
Likitan ya kalli kyakkyawar fuskar wadda ta karade talabijin da sauran hanyoyin yada Campaign irin su  posters a garin na Bauchi, ya mika masa hannu cike da kauna. A fili ya ce,
 I solute, Ma arouf Habibu Ji-qas, sai ka yi. Insha Allahu!!!
Ba kamar da ba da in an fadi hakan yake murmushi. Yau bai yi ba, cike yake da son jin matsalolin diyarsa. Hannu kawai ya mika wa likitan, wanda a jikin aljihun farar rigarsa aka rubuta  Umar Bolori suka koma suka zauna a tare. Gani yake likitan wanda aka kira Umar Bolori, bai damu da damuwarsa ba sam, ta siyasa yake, wadda a halin yanzu shi ba ta gabansa.
Ganin kallon da Ma arouf ke masa na zakuwa kamar zai matse bakinsa ya fada masa makomar lafiyar diyarsa, ya sanya Dr. Bolori kintsa kansa. Ya zauna yana fuskantarsa kana cikin nutsuwa ya soma yi masa bayani yana karantowa daga takardun gabansa.
 Yarinyarka Ameena Ma arouf ta samu karaya guda biyu, a dukkan kafafunta.
Babbar matsalar ita ce gefen jikin Amina ya mutu, abin da muke kira  paralysis (shanyewar barin jiki). Wadannan sune matsalolin Ameena, sai ciwuwwuka haka ba a rasa ba, da kukkujewa a wurare da dama .
Zufa ce ta kara keto mishi, (she is the only hope he had in this life), ban da ita jinsa yake ba shi da komai. Wane taimako ko kokari zai yi don ceto lafiyarta shi ne bai sani ba.
Idanuwansa sun kada sun sanja launi zuwa (brown), wannan shekara ya yi (marking) dinta matsayin shekarar bakaken kaddarorinsa. Bayan shekarun da ya shafe cikin fararen kaddarori, da farin cikin rayuwa mara yankewa. A matsayinsa na cikakken musulmi wanda ya yarda karbar kaddara mai dadi ko mara dadi na cikin rukunin cikar imani, dole ya mika hannu ya amshi kaddarorinsa da hannu bibbiyu, ya fuskance su a duk yadda suka zo masa.
Numfashi ya zuka ya fitar, ya dago ido jazur ya dubi likitan, shi kansa likitan ya karanto matsananciyar kaunar yarinya Amina daga wadannan idanun. Ya kuma tausaya a zuciyarsa. An dauki mintuna kafin Ma arouf ya bude baki ya yi magana, shi kuma bai nuna kosawa ba, kullawa yake a zuciyarsa yadda zai kula da yarinyar nan ba don kobon ubanta ba, sai don kaunarsa da yake yi ba, tun yau ba, in bai manta ba, kannensa matasa uku ne suka yi digiri daga tallafin  Ma arouf Foundation .
Ma arouf ya katse tunaninsa da cewa,  To yanzu wane taimako za ku ba wa Amina?
Dr. Umar Bolori ya ce,  Za mu fara bata taimakon farko na wadanda suka gamu da lalurar  paralysis a sakamakon hadarin mota wato  resuscitation , sannan muyi (attacking bleeding) din data ke yi, a samu ta dawo hayyacinta, sannan muyi mata dorin kafafunta guda biyu, sai sun hade za a fara ba ta kulawar masu shanyewar barin jiki (paralysis).
Mu dai fatanmu ka yi hakuri kada ka ce za ka canza mata asibiti ko za ka fidda ta waje, is all a waste, za mu yi iyakar kokarinmu a kanta, sai dai ka san ba abu ne da za a ce yau ga karshensa ba, lalurar (paralysis) tana bukatar hakuri da rashin kosawa har a samu lafiya .
Da wannan suka kawo karshen zaman nasu.
An yi wa kafafun Ameena dori a washegari, duk da cewa ba cikin hayyacinta ta ke ba, ta nuna azabar ciwon da ta ke ciki. Ma arouf da kansa kwanan asibiti yake shi da Hajiyan Ji-qas, gani yake ko ya ya ya yi nisa zai dawo ya ga babu Ameena kamar yadda babu Aisha. Kodayaushe kanta na bisa cinyoyinsa a kan gadon asibiti yana share mata hawayen da suke fita daga idanunta.
Ba ta iya cewa komai, kuma idonta a bude, amma shi tana gane shi, don yana ganin yadda ta ke rike hannunsa da nata mai lafiya. Hajiya ta yi-ta yi ya bar mata jinyar ya fuskanci ayyukan da ke gabansa amma ya ki, suna da yawon kamfen kananan hukumomi na Bauchi guda (20), amma ya daga fitar saboda lafiyar diyarsa wadda yake jin zai iya sadaukar da duk abin da ya mallaka in har za ta sake taka kasa da kafafunta.
Lokacin da kashin ya soma hadewa Ameena ta soma rigima saboda azaba. Wanka da canza sutura ke maida shi gida, sallah kuwa dama a cikin asibitin yake yinta. Har sai da karayar ta hade likitocin suka koma kan babbar matsalarta ta shanyewar barin jiki, sannan ne Ma arouf ya soma dawowa hayyacinsa.
Sun fita (campaign) garuruwan Ganjuwa, Itas, Katagum, Misau, Toro, Ningi, Darazo, Jama are, Warji, Dass, Tafawa Balewa cikin kwana bakwai. Inda duk tawagar Ma arouf ta gifta masoya ne ke kwararowa ta inda shi kansa bai sani ba. Sai dai kuma rade-radi ya soma yawo, ai ba shi da aure, ta ya ya zai zama gwamna babu iyali?
Wannan rade-radi ya zo kunnen Hajiyar Ji-qas domin an ce ita magana tafiya ta ke da kafafunta.
Dawowarsu ke nan daga garin Jama are ya zarto asibiti wajen su Hajiya. Yana tare da Amina har tsayin rabin awa. Kallo daya Hajiya ta yi masa ta karanto matsananciyar yunwa a tare da shi. Ta jawo sundukan abinci na alfarma da ke gefe ta zuba masa masah mai taushi da dadin gani a ido da baki tasa miyar ganye akai ta jawo tebir ta daura masa akai. A gefe lemon tuffah ne na kwali ta aje da kofi,
 Kyale Ameena, sakko ka ci ka gama magana za mu yi .
A duk sanda ya ga Hajiya cikin wannan yanayin maganar da za ta yi mai muhimmanci ce. Ya bi umarninta. Cikin dadin rai ya soma cin abincin don kuwa ya manta rabonsa da abinci mai dandanon gishiri cikin kwanaki biyun nan, sai (caffinated drinks) da (snacks) da yakan ci in ya samu dan lokaci.
Sosai ya ci masar, har da yi wa Hajiya godiya, lemon kwali guda haka ya shanye shi. Ya tattara hankalinsa ya mika wa Hajiya don ya fuskanci hakan ta ke so.
Ita ma nata hankalin ta bashi.
 Kana sane da cewa ka tsaya siyasa ba ka da iyali?
Da sauri ya dago ya dubi Hajiya. Ita kuwa ta tsare shi da idon.
 Ba ka da iyali ta ya ya za ka shugabanci al umma alhalin kai kanka ba ka da abin shugabanta?
Ya bude baki zai yi magana ya kasa, to me zai ce? Ya manta da wannan shaf! Kuma a da bai dauke shi da muhimmanci ba tunda ya san yana da su, Allah ne ya yi hukuncinsa, yanzu ya tuna wannan (decree) ne

9 / 10