KAWAR ZUCIYA PART-2 BY TAKORI KABARA .pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 17

27K to 30K   out of 48.7K words

arha, su Hatoon ki siyo Swiss
laces masu tsada, shin akwai bambamci
tsakaninsu ne a gurina? Ban ji dadin
abinnan da kika yi ba ko kadan, baki
kyauta min ba”. Sai ta soma bashi hakuri, tace “ba
haka bane Habiby, kudin ne sunyi kasa
sosai, sai naga cewa su Zahra yafi dacewa
da wannan, su din kannenka ne da kuke
ciki daya, hakkinka ne ka yi musu komai
yanzu, musamman da hakkinsu kamar a
wuyanka yake, su Sabah kuwa Ihsani ne
tsakaninku wanda bai zame maka dole
ba”.
Cikin takaicin kalamanta yace
“sannu Mrs. Right, Gwanin na iya sarkin
iyawa, toh canjin da kika dawo mun dashi
me zanyi dashi? Idan har na isa dake ki
koma kasuwar nan, abinda kikayi wa su
Hatoon, shi nake so inga anyi wa su
Sabah…”.
161

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
​ Dolenta suka koma kasuwa
washegari aka sake siyo kayansu Sabah,
don ransa ya baci sosai a ranar, ya dauke
mata wuta da wannan abinda tayi, har
saida ta gyara kuskurenta, ta kawo ta
nuna masa ta bashi hakuri. Sannan ya
sauko, ta hadawa kowa nashi aka aika
kayan Katsina. Infact duk kannensa da
aka kai musu kayan sun yaba, kowa yayi
murna ana ta bugo waya ana yima Yaya
Baffa godiya don sun dauka shi da kansa
yaje ya sayo masu.
Mama kam kuka ta saka, tace wai
yau Baffa ya tuna mata Baba Bello, komai
Baba zai saya mata sai ya zabo na kerewa
sa’a, don ya san ta da son special abu da
basu cika gari ba, Mama tun asalinta
mace ce mai son gayu da kashe kala, tana
matukar son kayan ado na yayi, tana
harka ta jiki sosai da manyan matan ‘yan
bokon Katsina, saboda farin jinin Baba
Bello. 162

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Da sallah tazo, Zayyan da Safiyyah
dasu Sabah suka yi shiri suka wuce
Katsina don halartar shagalin bikin sallah
kamar yadda mafi akasarin mazauna
birnin tarayyah ke yin sallah a
garuruwansu na haihuwa. Gidan marigayi Prof. Bello
Rafindadi gida ne da ake yin hidimar
abinci ta alfarma duk ranar sallah, gate
dinsu a bude yake. Wannan ya shiga
wannan ya fita. Ana dafa abinci kala-kala
ana bayarwa ga baki da makwabta. Haka
ake yi duk sallah tun Baba Bello yana
raye. To yau ma hakan ce ta kasance a
gidan.
Ya kasance a kowanne washegarin
sallah Mama Fatu tana gayyatar matan
abokan Baba da kawayenta, suzo gidanta
a ci a sha da cimaka ta alfarma da snacks,
su wuni sur har yamma suna hira, zaki
gansu duka hamshakan mata ne kusan su
163

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
goma a falon Mama, ana hira ana nishadi,
to ko bayan rasuwarshi Haj. Fatu ta
cigaba da al’adar tata, ta gayyato
mutanenta ranar sallah.
Wannan shekarar ma kamar ko
wacce, kawayen Mama sun zo harda
matar VC mai ci a yanzu na jami’ar
Umaru Musa ‘Yar adua, Safiyyah tazo
falon ita da kannenta zasu yiwa mutanen
Mama gaisuwar sallah, Sophie ta sha
‘swiss lace’ dinta ‘purple’ me kyau,
kannenta Sabah da Rayyah dake biye
bayanta sun sako kayan da Zayyan ya
siya musu na sallah iri daya sak da na
yaran Mama wato su Hatoon, su Sabah
sun yi kwalliyar sallah da kayan ne
saboda Uncle Zayyan yana gidan, suna so
su nuna mishi godiyarsu, ta hanyar saka
kayan.
Don yace dasu da yamma in sha
Allah idan ya dawo daga cikin gari za’a yi
164

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
(family picture) harda su kafin ya
maidasu Dandume gobe kamar yadda ya
alqawartawa Malam. Idan su Zahra da
Zaitoon sun iso daga gidajensu. Shiyasa
suka saka kayan ba tareda sun kawo
tunanin komai a ran su ba. Suna shiga falon Mama tayi arba dasu, ta
kalli kayan dake jikinsu, nan da nan
annurin fuskarta ya dauke kaman an aiko
mata da saqon mutuwa. Tana tozali da
kayan jikinsu Sabah ta danna ashar a
zuciyarta, tace a ranta lallai ma Safiyyah
da take rainawa ta bari tayi kauri da
yawa, ta samu Baffa da yawa, me
Safiyyah ke nufi na sakawa kauyawan
kannenta kaya irin nasu Hatoon?
​Haka suka karaso suka gaishe da
Mama da kawayenta Mama na zabga
musu harara daga su har Safiyyah din.
Hajiya Yabi kawar Mama ta lura da irin
165

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
kallon da Mama ke musu sai kawai ta
bude baki tace.
“Wai ni kam Haj. Fatu, Safiyyah
har yanzu bata haihu ba ko?”
A gaban kawayenta Mama tace
“tayani tambaya, shiru, har yanzu,
tamkar Malam yaci shirwa”. Haj. Yabi ta
ce “kuma kuke zaune haka baku tashi
tsaye akai ba? A can kan tudu layin gidan
iyaye na akwai wani mai bada maganin
haihuwa, maganinshi kaifiyyan, in kunaso
zan karbo mata”.
Sai ta kalli Safiyyah wadda
hankalinta ya soma tashi ranta kuma ya
soma baci da jin zancen da suke yi a
kanta, ai har abada ba ita ba sake neman
haihuwa tawata hanyar balle ta hanyar
malaman tsubbu, ta riga ta tuba wa Allah
da Habibiy dinta, tace bazata sake ba.
Haj. Yabi tace.
166

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
​“Diyata Safiyyah ina fatan zaki sha
maganin in an amso, don magani ne me
tsada. Kar na karba kizo baki sha ba”.
Safiyya ta gyada kai kawai amma
ko motsi da bakinta ta kasa. Mama ta
zucciya da banzan data yi musu, ta daka
mata tsawa a cikin mutane tace “baki ji
ne ana miki magana kinyi shiru, kar ta
kashe kudinta a banza a wofi ta karbo
miki maganin baki sha ba.
Ni ban ma cika son harkar maganin
gargajiya ba Haj. Yabi, nafi yarda da
asibiti, amma tunda na matsu na ga diyan
Baffa gara a jarraba can din, ba’a san
inda za’a dace ba, tunda anyi na asibitin
duk ba nasara”. Duk sauran matan suka ce “exactly,
gara a jarraba na gargajiya”.
​Baki daya falon sai ya karade da
zancen rashin haihuwar Safiyyah har
167

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
tsayin shekara goma da aure, kannen sa
daga mai biyu sai mai uku, kowacce na
tofa abinda take tunanin shi ya hana
Safiyyah haihuwa, har da masu cewa ko
PCOS gareta, don mafi akasari shi yake
hana mata haihuwa yanzu. Safiyyah da kannenta duk sai
sukayi jigum-jigum a zaune, suka rasa
abinda ke musu dadi, ba zaginta ake ba
amma hakan fallasa ne da gori a fakaice,
suka rasa abunda zasu ce, duk Safiyya ta
tsargu da kanta, taji kamar tayi wani
gagarumin laifi ko abun kunya, wanda
al’umma ta kasa yi mata uzurinsa, wani
irin kuka na takaici ya taso mata.
Sabah ta fahimci hakan, tayi maza
ta kama hannunta suka mike suka bar
falon, uffan basu ce ba.
Suna fita Hajiya Yabi ta dubi Mama
cikin damuwa tace,
168

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
“ina fatan dai ba maganar da nayi
bace ta bata ran surukar tamu?”
Mama tace “oho mata, ita ta sani,
daga abun kirki? Yarinya sai kafirin
zurfin ciki da nuku-nuku, gata da
sumumu-kasau irin nasu na ‘ya’yan
Alarammomi da ka kan rasa gane
zuciyarsu”. ​Fitarsu harabar gidan suka ci karo
da shi yana kokarin shigowa da hancin
motarsa bakar ‘Ford Mustang,’ Arch.
Zayyan ya sha adon sallah masha Allah
dashi cikin farar shaddah bugaggiyar
Wagambari babbar, bugun hannu, ba
karamin kyau da kwarjini da kamala
shigar yau ta kara masa ba. ta kuma kara
fiddo zahirin kuruciyarsa ainun.
Da annuri sosai ya shigo gidan,
amma yana ganin fuskarta ya gano akwai
abunda ya faru da ya canza mood dinta.
Suna tsaye a kofar shiga babban falon
169

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
gidan itada Sabah. Ya adana motar a
parking lot na gidansu a nitse, bai fito ba
ya sauke glass na barin da yake zaune, sai
ya yafitota da hannunsa, yace.
​“Sabah, ku ara min Yaya Safiyyah
mana, ku shiga gida zan ganta, gata nan
zuwa yanzu”.
Sabah da Rayyah har suna hada
baki wajen cewa “Toh! Uncle Zayyan”.
Suka juya zuwa cikin gida.
Ganin Safiyyah taki motsawa daga
inda take tsaye bayan wucewar su Sabah
ciki, sai ya fito ya kama hannunta, dole ta
bishi kamar rakumi da akala zuwa motar,
ya bude suka shiga gidan gaban motar ya
rufe, dama glassanta duka masu duhu ne
(tinted), motar tana kunne, don haka AC
na aiki. Ga kamshin ‘Car fresh’ din motar
mai dadin kamshi da ya hade da kamshin
turaren jikin Zayyan na mazan da suka
amsa sunansu (Ultraviolet), su suka hadu 170

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
suka dawo da nutsuwa da salama a
zuciyar matarsa Safiyyah, ta jingina
kanta a jikin kujerar bayanta, ta hau
sauke ajiyar zuciya a jejjere, ba tareda ta
ko san tana yi ba. A hankali Zayyan ya mika
hannayenshi biyu ya rungomota jikinsa,
bakinshi a kasan wuyanta ya sumbaceta
lightly, yace.
​“Sophie yaya akayi ne? Wani abu
ya faru da bana nan ne? Na ganki
moody”.
​Safiyyah tayi shiru, haka kawai taji
kwalla na kara ciko mata, tace “Habiby,
ina so in haihu ne, kuma da wuri!” Yace
“Yaa Subhanallah! Ita haihuwar nan ba’a
hutawa da yin ta? Tukunnama yaushe aka
gama jegonta? Kuma shin me ya kawo
zancenta?”
171

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Daga Safiyyah babu amsa, sai ma
idonta daya karasa cikowa taf! Da
hawaye. Kiris suke jira su sauka kan
kuncinta.
Zayyan yayi-yayi ta gaya masa
abinda ya kawo zancen haihuwa amma
Safiyyah ta ki. Kada ya zama cewa ko ta
kai karar Mama da kawayenta wajensa
ne. ​A karshema da ya dameta da
tambaya sai ta kifa kai a kirjinsa ta fashe
da kuka mai cin rai.
​Bai iya yin komai ba ko hanata
kukan a wannan lokacin, banda ya
rungumeta cikin kirjinsa tsam-tsam, yana
shafa bayanta a hankali cikin lallashi. Ya
kuma barta tayi kukanta ma’ishi, yana
magana cikin lallashi, kauna da soyayyah
masu yawan gaske, wadda ta bayyana
kanta a zuciya da tone din furucinsa,
Zayyan yace.
172

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
​“Ki kara hakuri kinji Safiyyah,
haihuwa da samun ‘ya’ya duka lokaci ne,
in kuma Allah bai ga damar bamu ba….
inaso ki sawa ranki WANI HANIN GA
ALLAH BAIWA ne”. Ya fahimci an mata gorin haihuwa
ne as usual. Amma kowanene bai kyauta
masa ba suna cikin farin cikin ranar
sallah, ranar celebration din musulmi. Sai
ya kira Sabah a waya yace “ta robar, me
ya faru ne da Sophie da bana nan? Kunje
wani wuri ne an bata mata rai?”
Yasan Rayyah ko kusa bazata fada
masa ba, don zurfin cikinta irinna
Safiyyah ne, kuma bata da yawan
magana, amma Sabah tsaf zai ji komai,
har abinda bai tambaya ba, don tasu tazo
daya sosai. Sabah tace, “kawai-kawai, daga
munzo falon Mama mun sameta da
kawayenta mukayi musu gaisuwar sallah,
173

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
shine wata mata tayi mata zancen
haihuwa, nan aka fara zancen rashin
haihuwarta, hadda cewa za’a karbo mata
maganin gargajiya wajen mai bada
maganin haihuwa”. ​Baki daya Zayyan ya rikice, ransa
kuma ya baci, don ya tsani a kuma zancen
zuwa gun malamai karbo maganin
haihuwa, yace “wanene da wannan
maganar?” Sabah tace “oho bansanta ba,
amma tana zaune a gefen Mama, wata
fara mai jiki haka”. Yace “Maman, me
tace toh?”
Da yake Sabah bata da tsoro sai
tace “ba abunda Mama tace, illa ma cewa
tayi ta tabbata ta sha maganin da matar
zata karbo mata don kudi me yawa za’a
saka a karbo. Tace kuma itama bata
yarda da maganin gargajiya ba, kawai
don ta matsu taga diyoyinka ne”.
174

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Zayyan sai ya rasa me zai ce ma.
Amma ransa yafi na Sophie baci. Karshe
ya kashe wayar bayan ya gama sauraron
Sabah, yace “toh Sophie don Allah banda
bakin baki hakuri, bani da kalmar baki
hakuri, amma kiyi hakuri ki kuma kara
akan naki”.
Washegari da wuri ya daukesu
zuwa Dandume, don kada a kara bata
mata rai a gidansu.
Ya kaisu har cikin gida ya shiga ya
gaida Ammi da Malam. Yayi musu
godiyar aron ‘yammatan gidan da aka
basu na lokaci mai tsaho.
​Bai jima sosai ba ya fito yace ma
Safiyyah ta kwana da Ammi, sai gobe zai
dawo ya dauketa su wuce Abuja.
Ammi kam ta san halin yaranta ta
iya karantarsu su duka, da ganinsu kuma
ta san wani abu ya faru a Rafindadi,
175

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
amma dai bata ce komai ba, ta barsu a
hakan. Suma basu tada zancen ba sai
wanda ya shafesu.
Yana komawa gida ya tarar da
Mama tana zaune ita kadai, mai aikinta
Ankudi nata tattare mata falon da
bakinta suka bata.
Ya shigo ya zauna a gajiye, yana ta
kumburi, ya gaisheta, sai ya koma gefe
yayi shiru, Mama tace “a kawo maka
abinci ne?” Ya ce “a koshe nake Mama”.
Mai aikin na fita yace, ​“Please Mama me ya faru tsakanin
Safiyyah da mutanenki a gidannan?”
Mama tayi salati ta sallame tace.
“Koda naji! Ai dama na san za’a
rina wai an saci zanin mahaukaciya.
Toh Sannu ubana, nace sannu
ubana da ya haifi uwata, matse bakina sai
in gaya maka tunda tuhumar abinda ya
176

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
bata ran matarka ne ya kawo ka ba
gaisheni ba.
Sallamamme kawai, kaje kauye an
wanke ka a minjaye an baka ka shanye,
an aikoka ka mun rashin kunya ko, toh ba
zan fadi me ya faru ba duk yadda tace
maka hakan akayi, akwai abunda zakayi
ne? Ko karya ake mata ta haihu dinne? ​Da ta haihu za’a yi mata zancen
amso magani? Ka amsa ni mana, rasa
kunya beran tanka?
Ai wallahi Baffa mu zuba ni da kai,
in dai jimirinka matar ka ta fada maka
abu kazo ka tuhumeni to tayi kadan, ko
uwarta bata isa ba. Baffa anya kuwa
lafiyarka kalau?” Sai Mama ta hau matse ido tana fadin,
“Safiyyah ta kai Babanta Makkah da
kudinka, addu’arsa taci akanka Baffa, an
janye min kai bakidaya”.
177

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Kawai yayi shiru, ranshi na kuna,
yace “Mama haihuwar nan fa Allah ke
bayarwa ba mutum ba, ba dabararshi ba.
Babu wanda ya janye miki ni
Mama, amma Mama ki dinga yi wa
Sophie uzuri akan lamarin haihuwarnan,
tunda dai ba dabararta ce zata bata ba.
Kuma wallahi Mama ta fi ki son ta
haifa miki jika, amma Mama ace bama ke
ba wasu daban suna shiga cikin maganar
haihuwarta saboda kin basu fuska ai bai
dace ba, ina dai ce Safiyyah tayi haihuwar
nan ba jimawa kowa ya shaida tana
haihuwar? Allah ne yayi hukuncinsa a kai
dagabaya?
​Shin Mama wannan bai isa wanke
mata zargin rashin haihuwa da gorin ta
ba?”.
Mama salatinta da sallaminta ya
karu, tace “yau Baffa dani kake sa’insa
178

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
akan matarka, don ance za’a taimaka
mata da maganin haihuwa?
​Ai kuwa baku so zaman lafiya dani
ba. Nabi haihuwar da ta yin da gudu mai
kama da babu na tattake ba takalmi a
kafa ta!”.
Ganin Mama ta taso gabadaya
kamar zata rufe shi da duka sai ya
kwantar da kai ya koma baiwa Mama
hakuri, don yaga ta hassala sosai irin
yadda bai taba gani ba. Da kyar ya samu
ya lallasheta amma tace masa daga yau in
ya kara zuwa ya tuhumeta akan an
batawa matarsa rai, sai ta yi masa bacin
ran da zai dade bai manta ba.
Zayyan yau da kyar ya samu Mama
ta hakura da fadan suka koma hirar
sallama da juna, don gobe in sha Allah da
safe zasu kama hanyar komawa Abuja shi
da Safiyyah, kuma

10 / 17