GOJE Book 1 Hausa Novels By Binta Umar Abbale.pdf

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Taskar Novels

Chapter   12 / 16

33K to 36K   out of 47.4K words

ya biye musu to su ba zasu gaji dayi masa tambayoyi ba.

Tsit!! dajin babu alamun akwai wani dan adam dake rayuwa a gurin, kukan tsintsaye yafi yawa
sai dai jefi-jefi suna jin kukan dabbobin dake can nesa!............binkice! suke sosai a gurin, sai
dai kuma dukkaninsu a shirye suke domin Babu wanda ya saki jikinsa a cikinsu motsi kad'an
zasu zabura! su juya gami da saita bindiga.
Gurin da yake tsammanin faruwar badakalar! tasu ya nufa, ya jima yana duba gurin kafin yayi
tunanin cire wu'kar dake rataye a jikinshi ya fara tona 'kasar gurin da tsinin wuk'ar.

Cak! ya cire wu'kar ya ajiye a gefe ya tsuguna, hannu yasa yana tutture 'kasar data turbud'e
abinda yake hasashen samunsa a gurin, lokacin da ya fito da sassan hannun yayi dai-dai da
isowar Asp gurin!

Ya tsuguna kusa dashi gabad'aya idanuwansa ya zuba kan dungulmin hannun! yana jimanta
al'amarin! babu shakka! wannan shine hannun mutumin da ya sanya aka zana masa hotonsa
shekaru biyar da suka wuce! abinda ya sanya ya gazgata hakan, zabban zinare da azurfan
dake jikin wannan zane sune jere a jikin yatsun dake gabanshi a halin yanzu.
Ya kalleshi da fadin." Yanzu na 'kara gazgata maganar ka, binkice ya k'are a kanka tunda ga
sheda nan a hannunka wannan kad'ai ya isa a jinjina maka."!!!

Bece komai ba, ya ajiye sassan hannun daya riga yayi wani irin kumburi! kwanaki biyu kacal!

gefe ya matsa yana ya mutse fuskarsa, hannun har ya fara fitar da wari!

Asp ya tattara ma'aikatan gabad'aya ya nuna musu sheda! gabad'ayansu mamaki ya rufesu,
dukkaninsu zuwa sukeyi har inda da yake tsaye suna 'kamewa da sarawa!! alamun jinijina!!

Asp abin ya burge shi, shima hularsa ya cire ya 'kame tare da sara masa! al'amarin ya bashi
mamaki mutuka! Asp din yace." Wannan ba abun mamaki bane Cancanta ce ta janyo hakan.

A takaice dai basu bar dajin ba sai da suka tabbatar da cewa babu wani mahaluki da yake
rayuwa a gurin, iya binkicensu ya nuna musu cewa d'an ta'addan! ya canza she'ka, hakan be
basu mamaki! ba domin dama gabad'aya sunyi hasashen cewa babu yanda za'ayi ya cigaba da
rayuwa a gurin domin ya tsira da rayuwarsa, to har yanzu dai suna nan akan bakansu zasu
cigaba da gudanar da binkice a kansa, ba zasu fasa ba har sai bukatarsu ta biya a kansa.

Maigirma governor da kansa ya 'bukacin san ganin *GOJE!!* gani da ido domin tattauna wasu
muhimman abubuwa.

Asp ne ya jagoranci tafiyar........shigarsu government house din keda wuya Maigirma governor
ya mike daga kan kujerarsa, Asp yayi mamakin hakan sosai! koda yake yaron ya kai kuma ya
cancanta da girmamawa! Governor be zauna ba har sai da suka zauna sannan ya koma ya

zauna kan kujerarsa.

Cikin mutumci da girmama juna suka gaisa kafin su shiga tattauna abinda ya tarasu a gurin.

Ya jima kanshi a sunkuye yana nazari da tunanin maganganun governor a kansa. ya sauke
ajiyar zuciya, cikin nutsuwa ya kalleshi da fadin." Wannan shine burina a duniya cewar na
tabbatu gurin hidimtawa addinin Allah da kuma hidimtawa k'asata Najeria da al'ummar dake
cikinta, amma ranka ya dad'e ya za'ayi nayi gogayya da manya-manyan ma'aikatan tsaro!
bayan bani da cikkaken ilimi a kan hakan, ba zan boye maka cewa iyakaci na secondary skull
ba shin dama hakan tana iya faruwa."?

Maigirma governor yayi dariya irin ta manya kafin yace." Malam bahaushe yace ta yaro kyau
take bata k'arko! UMARU! ai bai cancata ka kira kanka da jahili ba, koda iyakacinka primary ka
cancanta daka zauna a kujera irin ta Asp saboda jarumtarka, kayi abinda shi Asp din ya kasa
dashi da wa'inda suke 'karkashinsa, sun buga! sun buga! sunyi-sunyi! Allah bai basu nasara
ba, wannan dalilin ya sanya na d'auko hayar sojoji daga libiya domin su taimaka musu, sai
gashi kai d'aya 'kwal kayi aikin mutum dubu! koda baka san (A) ba to ni na d'auke 'ka aiki
a'kar'kashin mulki na, kuma zan biya ka albashi mai kyau! sannan kuma na baka kyautar gida
da motar hawa, domin ka zauna da iyalinka a ciki."

Sai ya rasa bakin magana kawai ya zubawa Asp ido yana jimanta al'amarin, ganin ya rasa bakin
magana ne yasa Asp din ya ari bakinsa domin yaci masa albasa.

Governor ya kalleshi da fadin." Asp babu batun godiya UMARU ya cancanci abinda yafi haka,
godiyar ta isa haka, kai dashi duk kuna aiki kan gaskiya gami da kishin 'kasar ku, duka kun
cancanci a baku lambar yabo."

Asp ya mika masa sannu cike da farin ciki yace." Mungode sosai da wannan karamci ranka ya
dade Allah yasa ayi a gama lafiya." Ya amsa da "ameen ya Allah, kuma Allah ya taimake ku
akan aikinku." gabadaya suka amsa da "ameen."

Hotona sukayi sosai suka sanya shi a tsakiya, sai kuma wasu da maigirman governor ya
rungumeshi bayan ya bashi lambar yabo da girmamawa!! sosai ya samu kyaututtuka na
mussaman daga gurin manya manyan 'yan siyasan dake gidan gwamnatin, su kansu sun
jinjinawa kokarinsa,
Cike da tsantsar farin ciki da annushuwa suka fita daga gidan gwamnatin.


******
A daran ranar da al'amarin ya faru ZINATU da kyar ta iya runtsawa saboda 'bakin ciki da
takaicin ganin yanda lokaci guda Allah ya daukakashi, ganin hotonsa da governor a lokacin da
ya bashi lambar yabo da girmamawa ya mugun daga mata hankali, haka kawai take so ta

ganshi a tagaiyare! a wulakance! amma hakan bata samu ba, babban bakin cikinta yanda taga
manya mutane na girmamshi tare da kambaba! darajarsa, bata damu da kyaututtukan da ya
samu ba kamar yanda ta damu da taga ya k'askanta!

Washe gari da 'kyar ta fito daga dakin domin breakfast, Asp din ya gidan be fita ba, ta
gaisheshi kamar bata so, ya amsa yana nazarinta shi kansa d'abi'un yarinyar gabadaya basu
bashi sha'awa, shiyasa yake so su shirya ranar da zasu kaita gaban mahaifinta kamar yanda
yayi alkawari.
Ya kalleta sai kumbure-kumbure take alhalin babu abunda akai mata, da kulawa a maganarsa
yace."ZINATU Ina fatan dai kina jin dadin zama damu ko."

Da 'kyar tace." Um ina jin dadin karamcinku a gareni nagode amma yaushe ne za'a sallame ni
haka, tunda dai duk bukatunku sun biya."

Ya kalleta da mamakin maganarta yace." Kamar akwai abunda yake cikin ranki duba da yanayin
maganarki."

Murmushi takaici tayi da fadin." Ranka shi dad'e wannan mutumin fa da kuka d'auki son duniya
kuka d'ora masa bai da kirki ko kad'an! mugu! ne azzalimi! ni har yanzu ban yarda da
gaskiyarsa ba."

Asp ransa ya baci da jin maganarta sai kawai ya rufeta da fad'a ta inda yake shiga ba tanan
yake fita ba, yace." Ban san wace irin kiyayya kike wa Umaru ba, shin me kike so muyi masa
bayan wanda yafi haka? mutumin nan ya taimakeki a lokacin da kike bukatar taimako amma
duk sanda za kiyi magana a kansa ba mai kyau bace! shin wai me yayi miki da zafi da kika
tsaneshi haka."!

Cikin 'Kunci da takaici tace." Ranka ya dade mu bar maganar kawai domin duk abinda zan fada
maka a kansa ba zaka yarda ba duba da ganin yanda zuciyarka ta hasala! kawai saboda na
kiraye shi da macuci alhalin sunan daya cancanta dashi kenan."

Yace."Kin san Allah ba zan matsa daga gurin nan ba har sai kin sheda min irin cutar da yayi
miki da har kike kiran sa da wannan sunan."

Ganin yanda ya kafe ta da idanuwansa yasa jikinta mutuwa, me zata ce yayi mata bayan alkairi,
ta san ya taka muhimmiyar rawa a kanta amma haka kawai take jin haushinsa! a yanzu duk
abinda zata fada a kansa sharri ne!

Ya katse tunaninta da fadin." Ke nake sauraro na fada miki ba zan bar gurin nan ba har sai naji
dalilin da yasa kike tsaneshi."

Bakinta ya sub'ce gurin fadin"Saboda ya keta min haddi sakamakon kad'aicewar mu a dajin."

Ya zuba mata ido da so ya tabbatar da maganarta......."Ya keta miki haddi kamar yaya."?

Ko kunya ta sake lailayo wani sharrin......"Fyad'e yayi min." Tafad'a babu nadama a cikin
maganarta.

Ya jima yana kallonta da mamakin furucinta kafin ya girgiza kai da fadin." Wannan shaci fad'i ne
ban yarda zai aikata hakan ba."

Murmushin takaici tayi da fadin." Ai dama ba zaka yarda ba saboda jarumtarsa tana burgeka a
matsayinka na babban mutumin mai rik'e da mu'kamin Asp bai kamata ace kana mubaya ga
wannan k'azamin mutumin ba."

Maganarta sai ta bashi dariya, ya tsaya ya dara kafin ya mike yana duba agogon dake daure a
hannunsa yace." Lallai yarinyar nan da gaske kike amma babu damuwa, wannan maganar
kuma ba zan barta ba sai mun tattaunata da mutumin naki." Shuru tayi ba tace komai ba, har
ya bar gurin, tana zaune a gurin suka fito tare da madam d'inshi dirarriyar mace kyakykawa da
kyawun jiki sam ba za kace ta haifi 'yar shekara ashirin ba, hannunta rike da 'yar jakarshi ta
rakashi bakin mota ta nayi masa fatan alkairi.
Koda ta dawo a falon ta zauna suna hira jefi-jefi ta d'an saki jikinta sakamakon mutunci da
karamcin matar wanda ya janyo mata 'kima da mutunci a idonta......Sai dai kwata-kwata jininta
bai had'u da Nabila ba, haka kawai ta tsani yarinyar alhalin babu wani abu da tayi mata na
laifi........daidai gwargwado tana bata girma tunda ta fahimci cewa ta d'an girme mata sai take
kiranta da Auntyna. hakan yana sake sanyawa kanta ya kara girma domin akwai ta da son
girma, gata dai a gidan ubanta amma mulkar yarinyar take, da yake ita din mai saukin kai ce
bata damuwa, domin bata mance ingantaccen hadisin nan da yake cewa "ka girmama bakon
ka, wannan dalilin yasa take mata duk abinda take so, wanda ita kuma anata 'bangaran take
ganin kamar ta isa ne! shiyasa take mata biyayya.....!




*#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number....
22796074090....Dala dari katin airtal ko mov*
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!!🏹*
🐕â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶º
_(SADAUKI OMAR RETURN💫👑)_

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*MANAZARTA WRITER'S*

*ASSOCIATION📚🖊ï¸*
_______________



*35&36*
Cikin 'kananun kayan data ajiye masa ya shirya jikinsa tsaf, ya fesa turaranshi mai sanyi da
sanyayya rai, ya kimtsa tsaf dashi, kai tsaye b'angaran nasu ya nufa cikin yanayin tafiyarsa ta
gwarazan maza!

Uwale kawai ya samu a falon ta zubawa tv ido tana kallo, ya shiga da sallama a bakinsa tayi
saurin kallon bakin kofar ganinsa yasa ta sauke ajiyar zuciya ta amsa sallamar tare da maida
hankalinta kansa har ya k'araso inda take zaune.

Tibin ya d'an kalla kafin ya zauna kusa da ita da fadin." Kallo kike ne."? Ta gyara zama da
fadin." Gashinan dai Ina kallonsu da ido amma bana fahintar komai, yanzu nake cewa
Hamra'u ta kai min tashar Arewa 24 nafi fahimtarsu duk da cewa su din ma wani sa'in suna da
abun haushi."
Ba tare da yace komai ba ya dauki romot ya canza tasha sunnah tv ya kai dai-dai lokacin da
marigayi malam Ahmadu B.u.k yake tambihi akan hadisan Annabi Muhammad (SAW) tace."
Allah ya jikan wannan malami yayi wa addinin Allah hidima." Yace."K'warai kuwa ba iyalinsa ne
kadai sukayi rashi ba duk duniya ne muna rokon Allah ya jadadda rahama a gareshi." Cikin
alhini ta amsa da ''ameen ya Allah."

Gurin yayi shuru gabadaya hankalinsu na gurin sauraran malamin, har Hamrau ta 'karaso gurin
kafin tace."Yayana na kawo maka abinci nan ne."?

Hankalinsa na gurin malamin yace." Eh ki kawo min nan." Da sauri taje ta shiryo masa abincin a
tire ta ajiye masa a gabansa, kasan kafet ya sauka ya tankwashe kafafunsa, yana kokarin bude
kwanakun abincin tayi saurin zuwa ta bude cikin nutsuwa ta zuba masa towon farar shinkafa
tas dashi lailaye a leda da miyar zogale wacce taji kayan hadi tayi kyau sosai sai kamshi ne
yake tashi, ya kalleta da murmushi a fuskarsa yace."My dear wannan miyar wace kala ce.''?

Tana kokarin magana Uwale tace."Miyar zogale ce, ni nayi sha'awarta nace a maimakon
taushe tayi mana ko baka so ne."?

Girgiza kai yayi da fadin." Ai ko bana so tilas naci domin farin cikin ku, na san kuma miyar za
tayi min dadi kamar yanda nake bukata."

Hamra'u farin ciki ya lullubeta, murmushi tayi ta tashi daga gurin taje ta samu kujera ta zauna.

A nutse yake cin abincin yana yaba nutsuwa da nagartar yarinyar, duk inda ake tunanin mace ta

kai, komai Allah yayi mata nutsuwa tarbiya uwa uba iya girki na zamani dana gargajiya, tunda
yake cin abincinta bai taba cin karo da kuskure ba, komai yana masa dai-dai wannan dalilin
yasa yake zagewa ya cika cikinsa ba tare da wata fargaba ba, ya cinye wanda tasa masa tas
ya 'kara wani yaji dadin miyar sosai da sosai.
Koda ya kammala cin abincin, sai ta kwashe kayan ta nufi kicin dasu domin wankewa........Ajiyar
zuciya ya sauke bayan barin ta gurin, ya janye idonsa daga hanyar da tabi, Uwale ta kalleshi
da fadin." UMARU ni kuwa ina labarin wannan yarinyar."?

"Wace yarinya kenan."? Yafada idonshi a tsaye a kanta.

Tace." Yarinyar da ka taimaka mata wacce ake maganar 'yar sarkin kano ce."

'Bata fuska yayi da fadin'' Tana nan Lafiya." daga haka sai yayi shuru da bakinsa.

'Yar dariya tayi irin ta tsaffi ta dauki goro ta gutsira kafin tace."Haka kawai nake maka sha'awar
auranta"

Ya kalleta da mamakin jin furuncinta, da kyar yace."Me yasa kike min sha'awar auranta bayan
duk ga 'yan mata nan masu hankali da tarbiya''

Shuru tayi na minti biyu kafin tace."To UMARU kaine ai kamar mara lafiya duk macan da akayi
magana maganarta sai ka 'bata ranka abinda yasa nayi maka maganar yarinyar domin naji
abinda yake
zuciyarka na d'auka ko akwai alakar soyayya a tsakaninku."

Girgiza kansa yayi da fad'in" Babu kuma ki cire hakan a ranki, halin da ake ciki a yanzu shine
ina binkice akan yarinyar da zan aura."

Fuskarta a sake tace." To masha Allah, nayi farin cikin hakan, amma UMARU ya za kayi da
wannan yarinyar Hamra'u ta jima tana sonka don Allah kada ka watsa mata 'kasa a ido"

Murmushi yayi kafin yace."Ai ita zan aura da ikon Allah." sai ta wangale baki tana kyalkyala
dariyar farin ciki ta dafa kansa da fadin." Kai masha Allah naji dadin wannan al'amari UMARU
Allah ya tabbata da alkairi ya nuna min lokacin da zanga zuriarka, amma ina alfarma a gurina."

Ya kalleta da fadin." Wace alfarma kuma"? tace." Bana so aja dogon lokaci ayi komai a gama a
lokaci k'ankani." Yace."Kada ki damu insha Allahu daga na dawo daga training za'ayi komai a
gama da yardar Allah." tace." to Allah ya tabbatar mana da alkairi" ya amsa da ameen ya Allah."

*****
A daran ranar Asp ya umarce su ita da Nabila yace su shirya zasuje unguwa, ba a son ranta ta
shirya ba, suka fito harabar gidan a tare sai cika take tana batsewa tana ya mutse- ya mutse,

ita kuwa Nabila kamar koda yaushe fuskarta a sake kamar gonar audiga sa'i da lokaci ta kan yi
mata magana, idan ta kama, sai taga dama take amsawa, a bayan motar suka zauna Asp din
ya zauna kusa da direbansa.

Babban super market suka nufa, ya kalleta da fadin." Duk abinda kike da bukata kina iya
dauka." Uffan ba tace masa ba tayi gaba tana zagaye gurin, girgiza kansa kawai yayi ya matsa
can gefe tare da fito da wayarshi.

Abokin nashi ya kira, don yanzu UMARU ya zama abokinsa duk da ya girme masa, amma
abota suke tamkar tare suka taso aiki yasa sun shak'u da junansu,

Cike da girmamawa ya daga wayar suka gaisa kafin Asp din yace." Ka tsammaci zuwana
gurinka yanzu."

Cike da mamakin hakan yace." Ina fatan ba wata matsala bace." Yace." Alkairi ne zamu
tattauna wasu batu masu muhimmanci" Yace." Okey to shikkenan sai ka shigo din" sallama
sukayi kafin kowa ya kashe wayarsa.


Turaruka kawai ta iya dauka sai kayan za'ki data jida sai kace shazumamu! haka take da shan
zaqi kamar me a cikin hakoranta ma akwai wanda suka dan samu matsala duk ta dalilin shan
zaqi.

Tana gama tsintar abunda take bukata ta mi'kawa Nabila kwandon kayan, ita kuwa ta kar'ba ta
had'a na da na hannunta, kai tsaye gurin total ta nufa da kayan, ita kuma ta fita daga
gurin.......Tun kafin ta k'arasa bakin motar direban ya bude mata ta shiga ta zauna har yanzu
babu sassauci a fuskarta.
Ganin fitowarsu yasa tayi saurin dauke kanta babu wanda ya tanka mata, direban ya bude
masa mota ya zauna, kafin ya kar'bi ledojin hannun Nabila ya bude boot ya zuba, ba ta jira ya
bude mata motar ba, ta bude da kanta ta zauna tare da bisimillah a bakinta.

Koda suka shiga barrack din direba na kokarin parking ya umarceshi da cewa ya zarce dasu
gida mai lamba shida(number

12 / 16