A BARI YA HUCE BOOK Complete by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Taskar Novels

Chapter   18 / 27

51K to 54K   out of 79.7K words

haka Dina da wasu daga cikin kannen Amiru suka shigo, don haka dakin ya yi albarka, ba
masaka tsinke, wanda ke nuni da lallai Amiru dan dangi ne. Kowa na fadin albarkacin bakinshi.
Akan yanayin jikin Amirun. Ba su bar asibitin ba sai dare, aka barshi da Habibu wanda shi yake
kwana da shi. ***
8/5/21, 3:11 PM - Kawata: D

Awashegarin daurin aure, wato lahadi, tun safe motocin daukar amarya zuwa garin Gaya suka
iso. Dina ta shirya amarya cikin fararen liffaya na Larabawan Mouritania, ta fesheta da turarukan
'gibenchy' su Habiba da Hajara suka sanyata a tsakiya, Dina na gidan gaba suka nufi garin
Gaya. Anyi musu tarba ta GIRMA, a gidan sarkin Gaya na lokacin, wanda ya kasance kaka ga Amiru,
tunda kuwa shi ya haifi Alhaji Abdurrahman, dangin Mairo sun tabbatar Mairo ta yi aure da dan
dangi, wanda ake so, ake kauna kwarai, ake kuma son abin da yake so, sannan aka san
mutumcin dan Adam. Kwanansu uku ana shagalin biki irin nasu na masarautar Gaya, kuma fulanin usli. Mai martaba
Sarki Abdulkarim Sarkin Gaya III ya yi wa amarya kyautar bajimai uku da sabuwar mota.
Washegari suka nufo Abuja inda aka shiryawa amarya gidanta cikin gidan surukanta, bangare
guda, wanda dama tun sanda za a gina gidan an gina shi ne musamman sabida Amirun.
Duk da dai gidan ba ya bukatar komi, wannan bai hana Habibu da Alh. Abbas yi wa Mairon su
gata ba. Dakuna uku manya-manya aka ba su suka shakewa Mairo da dukiya.
Sai dai fa ba wai rambatsau ba, a'ah, komi ya dace da muhallinshi. Cikin tsari mai burgewa da
ban sha'awa, sannan sun kawota da gararta (trailer) guda. Lokacin da suka shigo wajen Hajiya
Aisha aka fara kai Mairo, inda dukkan dangin ango suke tare da Hajiyar a babban falonta.
Duk kannen Amiru guda goma sha biyu na ciki da na waje sun hallara, suka karbi amaryarsu
cikin mutuntawa da kamala. Daga nan sai sassan Daddy wanda ya dade yana yi musu addu'a

ta neman dacewa a duniya da lahira.
Daga nan aka taho da amarya bangarenta banda kuka da shessheka ba abin da ta ke yi. Ta
kama Dina ta rike tamau, ta rantse ba zata tafi ta barta ba, sai dai su koma tare.
Dina na dariya ta ce
"Ina kika taba jin anyi haka Mairo? Ai auren ke nan, YAKIN MATA…… Ko ba ki ganin nima
namu gidan na baro na ke zaune da Yayan ki, a inda ba ni da kowa? Ke kuwa fa? Ga ki ga su
Hajiya, ga su Amina, ko su kadai sun isheki debe kewa. Duk lokacin da kike son zuwa Kano za
ki je". Cikin kuka ta ce
"Yanzu Aunty Dina ni da ku shi ke nan? Ni da su Little Mairo shi ke nan? Sannan ba zan koma
makaranta ba?"
Dina ta ce
"Idan na ce za ki koma makaranta, ko ba zaki koma ba na yi karya, sabida a halin yanzu ba mu
da iko da ke, sai abin da mijinki ya hukunta a gare ki. Yara kuwa na yi miki alkawarin da zarar
sun samu hutu zan kawo miki su. Ki kwantar da hankalinki ki zauna da mijinki Amiru is a nice
person". Sabah ta yi murmushi, ta ce
"Sai ma kin zauna da shi for a little while..."
Dina ta ce
"To kinji ba, kannenshi ma sun shaida".

Wayarta ta hau ruri ta yi murmushi
"Ni ma nawa tsohon angon kirana yake yi in mishi tausar gajiyar da kujuba-kujubar aurenki ya
sanya shi. Don haka amarya sai ince, asubah ta gari".
Tana ji tana gani Dina ta fice, ji ta ke kamar ta dora hannuwa aka ta ce "Wayyo Allah". Ko ta
sami sa'idah.
Ya rage daga ita sai su Amina, don su Hafsat kannen Dina duk sun tafi tun dazun. Nabilah
dama ba ta taho Abuja ba, daga Gaya suka nufi gida ita da Isma'il.
Suna so ta yarda su yi hira, amma amaryar tasu ta ki sakin jikinta. Ganin abin ta ke kamar a
mafarki, wai yau ita ce a gidan wani mijin ba Uncle Junaidu ba.
Ta yi saurin yin istigfari da wannan mummunan tunanin ta amince, ta yarda da kaddararta. Ta
amince haka Allah Ya rubuta musu dukkaninsu. Zata koyawa zuciyarta juriya da karbar rayuwa
a duk yadda ta zo mata.
Hajiya ta yi kiran wayar Amina, ta ce duk abin da suke yi su bari su taho gida haka dare ya yi.
Dukkansu suka mike suna yi mata sai da safe Hajiya na kiransu. Ta rike mayafin Sabah tana
kuka sosai har ta karyawa Sabah zuciya, ta ce su tafi zata taho.
Ta koma ta zauna ta ce "Haba Antinmu? Ya ya kike abu kamar karamar yarinya ne? Amare
yanzu ba sa kuka, sakin jiki suke a sha soyayya. Kuma ni kinga idan ban tafi ba zan yi laifi wurin
Hajiyarmu, don haka ki yi hakuri na tafi na yi miki alkawarin gobe da safe zan dawo idan Allah
Ya kaimu". Haka ta kalallameta da dadin baki ta samu ta gudu. Ya rage sai Mairo kadai cikin katafaren
gidanta, daga ita sai halinta. Ji ta ke kamar an kawo ta kabarinta. Don haka ta ce bari kawai ta
yi ibada ko ta samu sanyin zuciyarta.

Ta mike a hankali, ba tare da ta ajiye nadin laffayar da ke jikinta ba. Ta nufi kofar da jikinta ya ba
ta bandaki ne, ba don ta saba da ire-iren wadannan wuraren ba, da hakika ta tsaya kauyanci.
Komi na bandakin wanda ya kasance (Jacuzzi) kalar ruwan hoda ne, watau 'pink' kamar yadda
makeken bed room din shi ma ruwan hodar ne da ratsin fari. Ta dauro cikakkiyar alwala ta fito. Ba tare da ta tsaya neman darduma ba ta nemi wani gefe a
can wani korido na dakin ta tada ikama. Sallolin neman biyan bukatar duniya da na lahira da
neman dacewa a rayuwar aurenta ne ta ke yi. Cikin sujudunta tana mai yi wa Babanta da
Innarta addu'ar samun rahma da gafarar Ubangiji. Cikin tahiyarta ta ji alamun ana taba kofa, kafin cikin nutsuwa ta ji an murda kofar an shigo.
Angon ya bayyana a dakin cikin fararen kayan barci.
Dai-dai lokacin da ta yi sallah ta mike ta kara tada sallah, ya aje kwali da tambulan din da ke
hannunshi, shi ma ya shiga ya dauro alwalar ya cimmata suka ci gaba da sallar tare. Agogon
bango ya buga karfe biyu dai-dai na sulusin dare lokacin da kowane mai rai yake neman hutu,
amma ga wadannan ma'auratan abin ba haka yake ba. Sun fada wata duniyar tunani ta daban, ba wannan tamun wadda muke ciki ba. Abin nufi,
kowanne da tunanin da ke cin ranshi. Ba auren sha'awa ya yi ba, auren so da kauna ya yi. Don
haka babu sha'awar Mairo ko yaya a tare da shi a daren yau.
Ya dauko kwalin 'fresh milk’ na madarar 'oldenburger' da ya shigo da shi ya tsiyaya a kofin ya
mika mata. Ba tare da ta tashi daga inda ta yi sallar ba, ta mika hannu ta amsa. Ya sauko daga
gefen gadon ya yi zaman rakuma a gabanta. Ya dauki dukkan hannuwanta ya rike cikin nashi.
Wannan ya haifar da tashin tsigogin jikinta duka a lokaci daya. Ta samu kanta cikin matsananciyar sha’awar mijinta Amiru, wanda sassanyan kamshinsa na
turaren 'Miyaki' ke kara dagula mata al'amura, dama yaya lafiyar kura, balle an tsokaneta,
amma ga shi Amirun, abin ba haka yake ba.

Zuciyarshi ta kasa amincewa Mairo na sonshi, a ganinshi Habibu ne ya takurata ta aure shi, don
haka akan me zai sallama mata soyayyarshi? Yana son ya koyar da ita sonshi da kaunarshi, ba
wai sha'awarshi ba kamar yadda ya karanto karara cikin fararen kwayar idanunta.
Haka suka yi ta zama dungur-gur bisa kafet har aka yi kiran assalatu, kowanne na ji da
miskilanci. An rasa wanda zai fara keta billensa, ya kwantar da kai ga dan uwansa. Ya rausayar
da kai, ya ce
"Mu je mu sake alwala".
Ba musu ta mike domin dama ta tsauwala da wannan zaman na babu gaira babu dalili.
Don haka koda suka idar da sallar Mairo gefen gado ta koma ta takure. Shi kuma ya ja filo ya
jefa bisa kilishi ya kwanta. Ta leka ta hango idonshi a rufe ta dauka barci ne ya dauke shi, don
haka ta mike ta warware laffayarta, yadda zata ji dadin yin barci, ta nade a gado ta ja bargo ta
rufa. Wani irin fitinannen barci na fizgarta, hakan yasa ba da dadewa ba sarkin barayin ya yi
awon gaba da ita.

Mairo ba ita ta farka ba sai wajejen karfe goma na safe. Shi ma din sakamakon feshin ruwan da
ta ji akan fuskarta ne. Ta juya a hankali saitin da feshin ruwan ya ke, Amiru ne ke taje sumarshi.
Ya yi shiri cikin bakaken 'suit' masu ban sha'awa.
Ta zuba mishi ido kurr kamar mayya, har yawun bakinta na tsinkewa, sakamakon wata

matsananciyar sha'awarshi da ta kara saukar mata. Wannan mutum kamar Romeo ya ke,
kamar an ce da shi 'juya' ya juyo suka yi ido hudu da ita, ya daure fuska sosai, ya ce
"Lafiya kike kallona? Ko na yi kama da tsohon saurayinki ne mai sunan aljanu? Haka kawai
yarinya kin zama kurma, in dai ni ne to mu zuba, shege ka fasa".
Ya kuta, ya sake cewa
"Halan Dina ko gayar da mutane ba ta koya miki ba?"
Ta dauke kai ba ta ba shi amsa ba, sannan ta yunkura ta mike ta fada bandaki ta yi wanka tare
da wanke baki ta fito. Yana tsaye jikin sif dinta yana amsa waya, ga dukkan alamu da Harrit
yake wayar, wani kululun bakin ciki ya taso ya tokare ta. Ta yi saurin komawa bandakin don ta
dauka ya fita ta aje tawul din ta maida kayan jikinta. Ta sake fitowa wannan karon ya gama
wayar yana sanyata a aljihun wandonshi.
Ya bi-ta da wani irin kallo kasa-kasa ya girgiza kai, ya fita yana cewa
"Abinci za mu ci, ko yau ma ba za a ci da ni ba?"
Ko ta tafas ba ta ce masa ba, don ta lura neman baki yake yi da ita.
Ta shirya cikin shadda 'orange' babbar riga 'senegalese', ba ta yin kwalliya rankacau don haka
kullum fatarta ta ke danya shar (fresh). Ba kankanuwar yunwa ta ke ji ba, don haka ta nufo falon
ta cimmashi a 'dinning area' na falon. Kallo daya ya yi mata ya dauke kanshi, zuciyarshi na
bugawa. Wannan yarinya kamar Juliet ta ke.
Ta ja kujera mai fuskantarshi ta zauna, sannan ta fara bude ma'adanan abincin, sinasir ne da
waina, sai hadaddiyar miyar agushi wadda ta ji naman rago, a gefe farfesun hanta da Koda ne
sai Shawarmah da snacks dangin su meat-pie, samosa, spring rolls da sauransu.
Cikin sassanyar murya ta ce "Can I serve you?"
Hakika ya ji wannan muryar har cikin kokon ransa. Bai iya ya amsa ba, illa kai da ya gyada
mata, don haka ta fara da hada mishi ruwan 'lipton' mai zafi da ganyen 'Hemorrhoid tea',
sannan ta zuba mishi Sinasir din da farfesun a faranti daban-daban.
Ya yi mata wani sassanyan kallo ba tare da ta sani ba, sannan ya soma ci. Ta hada 'lipton' ta
sha, amma ta yi-tayi ta ci abinci a gabansa ta kasa. Ta mike ta ce
"Zan shiga wajen Hajiya".
Ya ce
"A'a, sai kin ci abinci na gani tukunna".
Ta koma ta zauna, ta dauki sinasir guda daya, ta sanya a faranti ta soma ci cike da kunya. Ya
tura mata farfesun gabanshi ya ce, "Cinye shi".
Ba musu ta karba don ba zata iya yin jayayya da shi ba. Sai da ya tabbatar ta cinye, sannan shi
ma ya mike yana cewa
"Mu je na rakaki wurin Hajiyar".

Tare suka jera har gidan Hajiya. Tana sallar walha sanda suka shiga a karamin falonta. Sai da
ta idar ta shafa addu'o'inta sannan ta juyo gare su, cikin matsananciyar kauna ta mikawa Mairo
hannu
"Zo dawo nan kusa da ni diyata".
Sai ga su Sabah su ma sun fito, suka gaida Yayansu wanda ya maida hankali ga amsa kiran da
ke shigowa cikin wayarshi.

Daga karshe ma fita ya yi ya barsu, bayan ya fadawa Hajiya zai je ya raka bakinshi airport. Su
Amina kamar su hadiye Mairo. Nan ta wuni sur tare da su.
Bai dawo ba sai bayan la'asar, lokacin da ya shigo tana kicin ita da su Sabah suna hada abincin
dare. Hajiya na falo ta ce
"Sai yanzu?"
Ya ce
"Wallahi kuwa, ai bakin nawa ne suna da yawa, kuma jirage daban-daban za su shiga, amma
dai alhamdulillah duk sun tafi sai fatan Allah Ya sauke su lafiya".
Hajiya ta kwalawa Mairo kira, ta fito ba tare da ta iya hada ido da Amirun ba. Wanda ya bita da
kallo kamar bai santa ba. Ta russuna gaban Hajiya cike da girmamawa, Hajiya ta ce, "Shi miji
idan ya dawo yana bukatar kulawar matar sa, ta hanyar yi mishi sannu da zuwa, da ba shi abu
mai dan sanyi ya sha kafin a gabatar mishi da abinci. Don haka bi shi ku tafi, su Amina za su
shigo muku da abincin idan an karasa".
Cikin jin nauyi ta ce
"to Hajiya".
Shi abin ma dariya ya ba shi, wai wannan katuwar ake koyawa kula da miji, Hajiya ba ta san
yaran zamani da wayonsu ake haifarsu ba, balle Mairo rainon Dina, kula da miji sai dai ta
koyawa wasu, sai dai in ba ta sa kanta ba.
A 'bedroom' dinta ya cimmata, tana kokarin sauya kayan jikinta. Duk dauriyarshi da
jarumtakarshi ya kasa sarrafa kanshi, don haka ya yi hanzarin komawa da baya ya ja mata
kofar. Ta yi saurin juyowa amma ba ta ga kowa ba, sai karar rufe kofa.
Ta ci gaba da abin da ta ke yi kamin ta jiyo sallamar Amina da Rayyah a falo. Ta fita suka aje
abincin a 'dinning. Suka yi 'yar hira ba su jima ba suka fita. Ba ta san dakin da ya shiga ba, ko ta
sani ma ba zata shiga ba, don haka ta zauna nan falon tana jiran shi sai zuba kamshi ta ke.
Zamanta da wajen mintuna ashirin sannan ya fito, da alama wanka ya fito. Wannan karon cikin
shigar kananan kaya, farar shirt din (Tommy Hilfiger) da bakin wando Tokyo. Sai ‘miyaki’ ke
tashi. Mairo ta daga kai a hankali tana kallonshi. Wani irin abu na tsirgawa cikin jikinta yana tada
tsigogin jikinta. Kallo daya ya yi mata ya karanto halin da zuciyarta da ma gangar jikinta ke ciki. Ya murmusa ya daga gira ta kara rikicewa, a ranshi ya ce "munafuka! Idan dai wannan Amirun
ne yarinya, to kwalelenki har sai kin so shi, kin kaunace shi don Allah, tunda kiri-kiri kin fada
mishi cewa ba kya sonshi, akwai wanda kike so, don haka wannan jikin ma da kike wa marmari
ba zaki same shi ba". Abincin da Mairo ba ta iya ta ci ba ke nan, sabida gani ta ke kamar Amirun yana karanto
zuciyarta. To da gaske hakan ne, tunda yake shi din ba yaro ba ne. Ya fita ilmi da hankali nesa
ba kusa ba. A kwayar idanunta ya gama gane ta tsaf.
Yana kallonta sai caccaka cokali ta ke cikin abinci ta kasa kai ko loma guda. Shi kuwa cin
abincinshi yake cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yana kallonta a kaikaice. Wani zubin ya yi
murmushi, wani zubin ya girgiza kai. Wannan karon bai takurata da lallai sai ta ci ba, don ya
tabbata ba zata ci din ba. Dan Abdurrahman Gaya, kadai ta ke so a jikinta. Kararrawar kofar shigowarsu ta yi kara, wannan ne ya ceci Mairo daga kaifafan idon Amiru. Da
azamarta ta mike ta nufi kofar ta bude. Ta sha mamakin ganin Daddy da kansa. Cike da
girmamawa ta ba shi hanya ya wuce.
Sai da ya zauna a 'seater' ta zube a kasa tana gayas da shi. Ya ce

"Yaya bakunta Maryamu?"
Ta ce
"Alhamdu lillah".
"Babu wata matsala ince ko?"
Ta ce
"Babu Daddy".

Amiru ya baro kujerarshi ya iso inda Daddyn ya ke ya zauna a gefensa suka soma hirarsu. Ta
mike ta je kicin ta kawo mishi ruwan (Eva) mai sanyi da lemun 'shany' sannan ta gabatar mishi
da abinci.
A nan ne ya yi murmushi, ya ce
"Lemun kadai zan sha Maryamu, na Hajiyarku yana can yana jirana, kada inci a wajenki inje in
kasa cin nata".
Ta yi murmushi ta ce
"To Daddy babu komai".
Ta koma daki ta barsu don su gana.

Yau ma irin kwanciyar jiya suka maimaita, wato shi yana bisa kilishi ita tan kan gado. To haka
kwanakin da suka biyo baya. Idan ka gansu a gaban Hajiya da Daddy. ko su Amina, ba zaka
taba zaton cewa zaman 'yan Marina suke ba. Kowanne na ji da miskilancinsa ya kasa kwantar
da kai ga dan uwanshi. Ga ita Mairo, a ganinta shi ne namiji, shi ya kamata ya nuna mata
kulawa irin ta kowadanne ma'aurata amma ba ita ba. Sannan ba haka Dina ta gaya mata ana
yiwa amare a renakun su na farko a gidan aure ba. Ba haka kuma ta ga Yaya Habibu yana yiwa
Dinan ba. Amiru yace yana son ta baka da zuci, amma bayan aurensu ta ga ba haka ba.
Wannan al’amari yana sanya ta cikin wani irin tunani mai zurfi da wuyar fassarawa. Har ta kasa
jin dadin rayuwar gabadaya.
Shi kuma Amirun, a nashi bangaren, ya riga ya saba samun tarairaya ta karshe daga
banasariyar matarshi, kamar ta goya shi. Bai san cewa matar Bahaushe da matar bature akwai
wasu manya-manyan banbance-banbance ba. Hakika mu Allah Ya ba mu wannan darajar ta
kamun kai da alkunya, wanda ya zamo kowanne irin namiji, duk kyau, aji, mukaminsa da
iliminsa dole ya lallame mu idan har yana son ganin yadda ya ke so.
Yau juma'a

18 / 27