Author : Sumayya Abdulkadir Category : Taskar Novels
cewa (is not by force, is so gentle, so soothing and so romantic), domin
yana yi ne yana hadawa da lallashin ta a kowanne dakika, ta hanyar kwantar da gashin kan ta
da hannun daman sa, kuma baya rushing, yana yin komai a sannu, sannan yana bari ta huta na
wasu awanni yana bata labarin rayuwar sa a Paris da irin wahalhalun da ya sha wajen neman
na kai da neman ilmi, to amma fa ita a wurin ta akwai mugunta da son ladabtar da ita duk da
haka.
A wurin Maina Mukhtar yadda ka tafiyar da matar ka a daren farko a haka zata mike, don
haka Mukhtar bai yi da sauki ba, sosai ya baiwa Amani irin darussan soyayyar da yake so ta
tashi dasu. Ta mika da su har karshen rayuwar su. In fact, sai da ya fanshe duka kwanakin
auren nan nasu da aka kwange masa a daren jiya da wunin jiya kadai, ko yace ya sauke
wahalar duka samartaka data tuzurancin sa within 24 hours only.
Da asubahin ranar Amani ta kafa sabon kuka, musamman data ga bazata samu yadda ta ke
so daga gare shi ba, wato so take Mukhtar ya lalace yayi ta lallashi da tarairayar ta, kamar
Romeo kada ya je ko’ina, amma tuni shi ya tashi ma yayi wankan sa ya zuba farar shaddah
Wagambari, kyale ta yayi tana ta yi riii-riiii-riii, wai don ya ce ta taka da kanta zuwa toilet, bazai
iya barin lokacin sallah ya shige shi ba, shi baya son rakin nan nata, ya hau shirin tafiya
masallaci, ta tabbatar fita zai yi, sai ta kara rushewa da kuka.
Da ya rasa yadda zai yi da kukan nata don baya son jin sa ko kadan, zuciyar sa tabuwa take,
tsinkewa take, sai ya yi wa Baba Sahura waya, yana tsoron kada yau ma Amani ta sa yayi
missing jamI kamar yadda ta sa shi sallah a daki jiya, da wannan kukan nata mai bukatar ya
lalace a lallashin ta. Sahura na shan barcin bayan asubahi wayar Maina ta tashe ta, da sauri ta tashi zaune ta
amsa, sai ta ji gyaran muryar Mukhy yana cewa, yi hakuri Baba Safoorah, na tashe ki daga
barci, Im so sorry.
Nan da nan Sahura ta wartsake ta ce Babu komai Maina, Allah ya sa dai lafiya kuke, ran ka
ya dade? Gabana ya fadi.
Sai da ya kai zuciya nesa sannan ya iya cewa Yar ki ce bata ji dadi ba, ni kuma ban san
taimakon da ya dace in bata ba, sannan inaso in samu sallah. Ya fada cikin dakewa, don ya
gwammace ya kira ta akan dai ya kira Ummami, duk da itama Baba Sahuran yana jin kunyar ta,
amma ya san gara wata kunyar a kan wata. Baba Sahura nan da nan ta je gano, ta soma
murmushi ta ce ranka ya dade ai ba abun damuwa bane, ba sai na zo ba, hada mata ruwan zafi
cikin abin wankannan ka saka ta a ciki kamar minti talatin, ka bata panadal ta sha tayi barci mai
kyau shikenan zata samu karfin jikin ta in sha Allahu. Har ya je ya yi sallah ya dawo tana nan yadda ya bar ta amma barci na fizgar ta.
Bayan sun aje wayar itada Mukhy Baba Sahura kasa rike wannan labarin ita kadai ta yi a ran
ta, bakinta har kaikayi yake, ta kira Ummami ta sheka mata labari, Ummami ta ji kunya amma
sai ta hau ta da fada tana fadin ita fa Uwa ce ta dinga kama kan ta, ta daina shiga shaanin su,
ta kuma hau murmushi ita kadai, a lokacin tana tare da Mai a turakar sa, amma ya fita sallah bai
dawo ba, tana ta murmushin ta na farin cikin yau Mukhy ya zama magidanci, sai ga Mai ya
shigo, tana rike da wayar a hannun ta.
Me ya faru ne Mowar Sarki? Irin wannan murmushi da sassafe ban yarda kalau ba. ke da wa
kike waya da asubahin Allah?. Ta yi yar dariya ta ce labari Sahura ke bani wai yau Maina ya
zama magidanci, shine nake mata fada na ce ta daina shiga shaanin su. Farin cikin Mai Diffa ya
kasa boyuwa, Ummami ta kara da cewa kuma ta ce diya ta ta kawo mutunci fal, kamar yadda
dai aka san gidan mu. Alhamdulillah.
Mai Diffa ya daga hannu ya yi wa Allah godiya, yace ki shirya kyauta ta musamman ki bata in
ji ni, amma kada ki gaya mata dalili, ko ta san mun sani, to ya maganar sadakokin da Sultan ya
bashi? Tunda sai yanzu ya angwance ma?
Anya basu yi wuri ba Ummami?
Ummami ta ce gaskiya dai, a dan dakata kadan, a tsahirta ko zuwa ta yi haihuwar fari ne, su
fahimci juna sosai tukunna, da koyon rayuwa tare a gidan sarauta, wanda basu tashi sun girma
cikin sa ba. Don na lura akwai kuruciya har yanzu a tare da su su duka musamman ita.
Mai Diffa ya yarda da shawarar Ummami.
**** **** ****
Ka ce wai nauyi, nauyi ne da ni, don haka bazaka iya daga ni ka kai ni toilet da kan ka ba Ya
Mukhy?
Amani ta fada cikin marairaicewa, kafin ya amsa ta sake cewa “to shin wa ya dauko ni ya
kawo ni dakin nan? In ji dai na san ba da kafafuna na shigo ba?
Amani ta bashi dariya sosai da wannan maganar, amma da yake ba gwanin yin ta bane
murmushi yayi, haka ta cigaba da nacin sai ya dauketa ya kaita toilet yadda Romeo yake yi wa
Juliet, dariyar ta subuce masa wannan karon, sannan ya ciccibeta ya dauka duk da nauyin nata
da yake korafi ya nufi toilet da ita. Ke dai ki rufe min bakin tsiwar nan, kafin ki zaburo ni na kara dinke shi. An ce na hada ruwan
zafi a Jacuzzi in saka ki a ciki na rabin awa, kada ki tashi. Amani ta fiddo ido Wane irin ruwan
zafi kuma Ya Mukhy? Haihuwa nayi? Mukhtar ya ce To me marabar ki da mai haihuwar tunda
na bude hanyar haihuwar? Mace sai tambayar tsaya tana fama da kan ta, amma ba ta tsayawa
ta ci ribar zance.
Mukhtar ya dire ta a toilet ya hada ruwan yasa hannu yaji shi da zafi cau, kamar na wankan
jego, sai ya dauka haka Baba Sahura ke nufi, ya dauki Amani ya tsumbula ta a ciki, da ta yi
wani zillo sai ga ta ta koma jikin sa ta shako shi, sai gashi shima tsudum ya biyo ta sun fada
cikin ruwan tare, shima ya ji zafin yace, wash! Muguwa! Ta ce ai gara mu sha zafin tare Mukhy ya ce of course, tunda tare muka sha dadin ma! Amani
ta rufe ido tana jin kunya, in wani ya gaya mata wannan Mukhyn Alhaji ne mai wannan daure
fuskar da rashin walwala kamar malaikan daukar rai zata musa, tabbas (mace mai canza namiji
a aure komai zafin sa).
Amani ta boye kan ta a kirjin Mukhy cikin murya mai ban tausayi ta ce ni kam ban gane
komai ba sai azabar da ka bani Ya Mukhy, muryar ta abin tausayi ta saka Mukhtar ya rungume
ta sosai a cikin ruwan, ya sumbaci lips din ta affectionately sannan ya ce, kada ki damu kin ji ko
Sweetheart, don na farko ne shi yasa, you will soon come begging for more! Amani ta rasa inda zata sa kan ta don kunyar da Mukhy ke bata yau, amma ta lura Mukhy ko
a jikin sa. Yau cikin nishadin sa yake komai.
Don haka tare aka yi wankan jinyar, Mukhtar da Amani.
Aka zo maganar wankin zanin gado, yace ni kam bazaki saka ni aikin wahala ba bayan
wanda na kwana yi, ki dauki abin ki ki wanke. Amani ta yi narai-narai da ido, ta ce ai ka san ko a
gida ban taba yin wanki ba, balle na zanin gado, ni fa ko bras dina Rakiya ke wanke mun da
azama ya bada amsa nan kuma ba gida bane wajen neman lahira ne, wallahi in bazaki wanke
ba, Baba Sahura zan kaiwa ta wanke. Amani ta bare baki zata yi kukan nata na gado, Mukhy ya
ce cikin kwafa,
kina farawa ina karawa.
Sai ta maida bakin ta ta rufe har da toshe shi da hannun ta, shi kuma ya yaye zanin gadon
ya aje shi gefe ya ce ta shimfida sabo.
Bata kula da sanda ya dauka ya jefa shi a kwandon kayan wankin su ba, ta shimfida sabon
bedsheet ta lallaba ta koma ta kwanta, sai Mukhy ya baro magani ya kawo mata da kofin ruwa.
Amani ta ce narka min shi a kan cokali, ban iya hadiyar kwayar magani ba Mukhtar ya ce
Amani kina wahalar da ni ina wahalar da kai ko ka wahalar da ni? Ko dai mun wahalar da juna?
Kema fa yarinyar nan na lura a matse kike, Allah ne yayi cewa ni din nine da kin hana sadakoki
na masu shigowa samun sauran komai a tare da ni. Tun da ya fadi haka Amani bata sake kula shi ba, ta juya ta kwanta ba tare da ta karbi
maganin ba. Mukhy ya ce.
Gara ma ki karba ki sha, don ki warke kafin dare, this is your daily duty as a house wife,
tunda ke kadai ce for now, gara ma ki sani tun yanzu ban fasa karbar sadakoki na ba, sai ranar
dana karbi ta goma! Zan rufe kofa. Amma har a Aljannah ina fatan ki zamo shugabar mataye
na. Amani ta tashi zaune, idon ta fal hawaye, duk da cewa ya karramata cikin maganar sa ta
karshe amma ko kadan bata son zancen sadaka kamar yadda bata son mutuwar ta, ta ce a
sanyaye.
Yaya Mukhy, wanda ya sake cutar da wani tsakanin mu daga yau, koda da zazzafar magana
ne, ko maganar da dayan mu ya nuna baya so, bayan mutual understanding din da muka samu
yau, and forgiveness to each other, ina rokon Allah ya bi masa hakkin sa a kan dan uwan sa!.
Sai kuka. Juyawa yayi bayan ya ajiye mata maganin akan bed-side din, jikin sa ya dan yi sanyi da jin
kalaman ta, ya yarda da gaske Amani bata son maganar sadaka. Ai kuwa shi maganar yanzu
ma ya fara domin ya samu makamin yakin sanya Amani ta yi masa abinda yake so a duk
lokacin da ya ga dama da barazanar Sadaka, ba don wai ya yanke a ran sa zai karba ko ba zai
karba ba.
Ganin kukan da take bilhaqqi take yin sa, sai ya koma lallashi To shikenan, ki yi hakuri
Sweetheart, idan na daina maganar Sa-daka, kullum sau nawa zaa yi mun alfarmar?
Kafin in fita fada, da bayan na dawo? Kin ga ke din Sweetheart dina ce bana gajiya da rabar
niimar da Allah ya yi miki, ga ki Sweet 16 Amanin Mukhy, Allah da ya halicce ki ba da kyawun
sura kadai ya bar ki ba, daga sama har kasa har ciki Amani Tafisu ce, Tafisu ba dai abunnan ba.
Ya karasa da rungumeta sosai yana kissing idon ta da suka yi narai narai da hawaye, ta ce ko
sau nawa kake so Ya Mukhy, ko zan mutu zan amince, in dai zaka bar maganar sadaka.
Sai Mukhtar yaji wani dadi a ran sa, ya riko hannayen Amani cikin tafukan sa, ya kai su ga
fuskarsa suka tallafi lallausar sajen dake kwance a kowanne gefe na fuskar sa.
Balle ma bazaki mutu ba, sai dai hakan ya kara min son ki, sannan ki yi ta suburbudo min
yaya ina kara son ki da kaunar ki, ina kara kula da ke Tafisu.
Ke din wata mutum ce mai daraja a waje na saboda ALHAJI! Wadda komai tsayin lokaci da
canjin da zamani zai kawo, ko tsufa, ko canzawar halitta saboda shekaru ko girma da ya same
mu, ko wani abu makamancin hakan, bazan taba iya wulakantawa ba.
Daddyn ki mutum ne da bazan taba manta alkahirin sa a rayuwa ta ba. Don haka zan kula
masa da tilon Tafisun sa, in adana masa ita a daki na ni kadai, in mayar da ita TAFISU TA
GASKIYA, amma ba da komai tawa Tafisun zata fi sauran mata ba sai da nagarta, kyawun hali
da rikon addini, kula da miji da iya soyayya ga mijin auren ta, da kuma iya kula da yayan ta da
iyayen ta.
Kalaman sa sun kashe Amani don dadin su a ran ta, Mukhy ya daina ce mata shashasha, ya
yarda ita din, ba ballagaza bace. Idon ta fal hawaye ta dube shi da dukkan kauna da soyayya a
kasan idanun nata, ta soma magana cikin rauni murya.
Na san bazan ce ina son ka ka yarda ba yanzu Ya Mukhy, na san na makara, bazan ce
maka tuntuni ba kin ka nake ba, kishin yadda Alhaji ya fifita son ka a kaina ne ya sa nake kyarar
ka ka yarda ba, bazan ce maka a kasan raina ina yawan yaba surar ka da a fili nake kushewa
ka yarda ba, don na bar baya da kura mai yawa, bani da say a yanzu da zai yi tasiri a zuciyar ka
a kan SO, tunda baki shi ke yanka wuya, kuma maganganu zarar bunu ne.
Na fadi maganganu cikin jahilci da yawa, wadanda da inada dama a yanzu, da na mayar da
su na hadiye su a ciki na.
Mukhtar ban fara son ka don na ga kai waye bane, ko don nasabar ka, ni dai kawai gani nan
ne, zan iya cewa tun a Saliyo! Ranar nan. Na fara samun sauyi a zuciya ta a kan ka.
Ka yi min rai Ya Mukhy kada ka karba Sadakoki, ba don ni ba!
Ta cigaba da matsar kwallah tana cewa duk abinda kake so zan maka daga yau, ko da ya fi
karfi na, zan aro karfin a duk inda yake, wani irin kishi ne da ni a kan ka, mai barazanar haukata
ni, idan suka shigo.
Mukhtar yama rasa me zai ce don dadi yau. Ya shirya tsaf cikin irin kayan gidan su, amma
bai nada rawani a kan sa ba.
Your actions will prove your words Hajjaju, babu bukatar rantsuwa anan Hajiya Amani, abun
nufi, in gani a kasa kawai, Mukhy sama Mukhy kasa ana kula da ni, wato ki cigaba da yadda
kika fara yau, saboda ke dinnan tsoro kike bani, sakamakon halin ki na hawainiya yau fari gobe
baki, na rantse tuban ki na muzuru ne a yawancin lokuta, ba kya taba tuba don Allah! Sai kin ji
wuya.
Maganar sa ta so ta bata dariya don tasakanin sa da Allah ya fada. Iya karantar da yayi mata
kenan sama da shekaru goma. Halin ta mai wuyar canzuwa ne don an ce hali zanen dutse ne,
sai dai ma iya cewa zata rage wasu in aka cigaba da ankarar da ita a hankali cikin kauna da
soyayya.
Zani gun Mai, daga nan zamu je Dosso nadin sarautar dan sarkin Dosso, probably sai
Maghriba zan dawo.
Ya juya zai fita, Amani daga kwance ta kira sunan sa, muryar ta abun tausayi ta ce.
Ya Mukhy!
Ya dakata ba tare da ya juyo ba. Sai ji yayi Amani ta ce. Baka yi min goodbye kiss ba, you
know I love your kisses!
Mukhtar dai yau duk abubuwan da ke faruwa a mafarkai yake kallon su, amma gara ya zarce
a cikin mafarkin nan da dai ya farka daga niimomin dake cikin sa.
Murmushi yayi ya daga mata gira da kafada a tare, ya ce cikin dariya.
Na ki din! Maana wato ba zai yi goodbye kiss din ba, har da make kafada alamar ya ki,
sannan ya fita yana mata murmushin dake neman narka zuciyar ta.
Idan wadannan canje-canjen da yake gani a tare da Amani cikin dan lokaci na gaskiya ne
kuma zasu dore, baya jin zai yi maraba da wasu kwarori, kowacce mace kazama kuma
dukun-dukun zai gan ta a kan Amanin sa. Sai dai ita din Zuma ce sai da wuta, amma hakika
Amani ta sanya shi cikin madaukakin farin ciki yau, da yake fatan su dawwama a cikin sa har
karshen rayuwar su.
***** **** *****
Fitar sa ba jimawa ta sha maganin da ya aje mata ta cigaba da