Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
ya kusanceta baya iya jurewa sai ya raba jikinshi da nata, domin ya
samu nasa kason na ni’imar kamshin fatar jikinta da kamshin bakinta, ya haska idonshi da
hasken hakoranta.
Ya fahimci Rayhanah tana amfani da fararen kayan ciki ne (inner wears) kuma kulawar da
take basu kullum ba ta bari su canja launi, domin ba sai sun nuna datti take wanke su ba, in har
ta san ta saka, ta wuni ta kwana dasu, to lokacin wankanta da safe za ta wanke su da omo da
bleach ta shanyasu. Inda duk Ibrahim ya sa kai a jikinta baya iya mai da numfashinsa dai-dai ba tare da ya rabi
ni’imar da Allah ya zuba a jikinta ba.
Ba ta ciye-ciyen kayan mata na shirme da lakatawa da mannawa da turawa, sai dai ta ci
wadanda za su kara mata lafiya. Wadanda addini ya yarda su, kimiyyar lafiya ta yi amanna
dasu.
A fannin sittiru ba irin atamfar da ba ta daurawa in dai kalarta za ta amshi bakar fatarta ta
haskakata, ba sai ta dubunnan nairori ba. Ta nairorin ma sau dubu sai ta zabi mai rangwamen
kudi ta barta, in dai kalarta ta amshi fatar jikin ta, saboda sanin sirrin atamfa ajikin matar
bahaushe, atamfa ko wacce iri ce kyau take indai a jikin Rahane ne. Kuma ita ce favourite
regular attire dinta.
Wannan ita ce, RAYHANAH MATAR IBRAHEEM!!!
Wadda ba kyale-kyale ne ke fizgar hankalin mijinta a kanta ba. Tsafta ce, da gyara. Don ko
jambaki, bai taba gani a lebban Rayhanah ba, sai Avon lip Gloss.
A tsayin mintunan da Ibrahim ya diba yana bambance kamanni, halaye da dabi’un matar
tasa, sai ya yardarwa kansa cewa wannan ita ce MATAR DA YA KE MAFARKI; mai kyakkyawa
kuma sassaukan gayu na hankali da tunani, kuma ‘yar bokon data yiwa boko kyakkyawar
fassara, though she's not wealthy but she has a great mind! Ba kamar yadda mata da yawa
suka jahilci kalmomin guda biyu ba.
Turawa da larabawa da yawa kudinsu suke sanyawa suna sayen (Zaitun) don su rage
hasken fatarsu. Black is beauty! And there's nothing worth respecting like naturalism!!! Fari ba
shine kadai kyau ba, balle wanda akasa kudi aka sayo.
Mata da yawa sun gama amincewa cewa yin shampoo (kona gashi) da karin gashi, sanya
tsadaddar suttura ta almubazzaranci ko mai zahirantar da tsiraici a wuce ana barbadawa duniya
kamshi. A sanya dankwala-dankwalan ‘yan kunnaye, a lambata jambaki shine kwalliya ta
wayewa da burgewa…. To ba shi bane a ra’ayin RAYHANAH RASHID TAKAI. ******
Da wannan Ibrahim ya sauke idonshi a kan Rayhanah, sai ya ga ta yi barci tana numfashi
cikin nutsuwa, baccin da ba na komai bane face na wahala da azabar da ya gana mata. Shima
da ya duba aika-aikar da ya yi mata sai ya ji kwalla ta ciko idanunsa.
Ya kasa sakinta, ya kasa aikata komai a kanshi ko a kanta, yana jarumtakar maida
hawayensa amma sun ki hakan, sai da suka mirgina cikin gashin Rayhanah. Ya kankameta
sosai.
Sauran abubuwan da yake tattaunawa cikin zuciyarsa na auratayyar da yayi a yau da
Rayhanah, kuma al’amari na farko a tsayin rayuwarsa, da matsayin da hakan ya karamata a
zuciyar sa, daga shi sai Ubangijinsa suka sani.
Shi da kansa ya fiddo kayan aiki da baka rasa likita da su a gida, don ya tabbata sai ya yi
mata stitches, ya ji mata rauni sosai da hakan ya sa shi challenging (kalubalantar) kansa da
selfishness (son kai) da rashin tausayi.
Bai san kuma ya zai yi ya yi mata ba tareda ta tashi daga barcin hutun da baya son ya rabata
da shi ba. Sai ya maida ta kan sofa dake gefe ya yi mata allurar da ta karawa barcinta nauyi,
sannan ne ya yi, ya gyara komai ya canza shimfidar gadon.
Ya yi wanka ya fita dining don ganin abin da Benjamin ya girka. Ya kai hannu ya bubbude
dishes din yana gani; Lemon Ricotta, Pancakes with syrup, Quinoa, Poached-eggs, Sliced
bacon, Sliced bread with jam. Abinda Benjamin ya shirya musu a dining kenan matsayin karin
kumallo. Yasa murya ya ce,
“Benjamin!”
Daga can kicin Benjamin ya amsa ya fito da hanzarinsa hannunsa rike da wuka da farar
albasa katuwa. Ya ce,
“Jeka maza ka yo min farfesun salmon (kifi) easy chicken recipe da omelets ya isa, ina son
su in ten minutes”.
Benjamin ya amsa cike da girmamawa ya koma ya fara aikin.
Minti uku ya kara akai daga mintunan da ubangidansa ya ba shi, ya jero a tray cikin ‘yan
kananan bowls din karau (tangaran) zai soma jerawa a dining bayan ya kwashe wadancan
maigidan nasa ya fito daga corridor din da zai sadaka da dakinsa yana sanye da farar shirt
DKNY an rubuta DKNY din da ruwan kasar zare da dogon (brown jeans) ya debi wanka ya
sharce gashin nan nasa da kumfar Arganavita. Shaidar sujjadarsa ta fito sosai a karshen
goshinsa.
Ga mamakin Benjamin isowa ya yi gareshi da kansa ya karbi katon tray din ya sallame shi.
Har sanda ya shiga bedroom din nata da abincin ba ta tashi daga nannauyan barcin da ya
tsikara mata allura don ta yi ta yin shi ba.
Shima bai bi ta kan abincin ba computer ya kunna yana ci gaba da hidimar da ta kawo shi ta
yanar gizo.
Ba wani abu ne ya kawo shi ba face tattara ajiyarsa da ke manyan bankunan Amurka
daban-daban irin su J.P Morgan Chase, HSBC, U.S Bancorp, Morgan Stenly, Wells Fargo Don
komawa gida kwata-kwata.
Gidan da yake ciki wanda mallakinsa ne kadai zai bari a Amurka ba zai sayar ba.
Jefi-jefi ya kan daga kai ya kallo Rayhanah wadda ta soma gyara kwanciya, sai ya sunkuya
ya ci gaba da abin da yake yi. Yau jin kansa yake sakayau, kamar an sake haifo shi duniyar ne,
new IBRHEEM! Babu nauyin komai cikin jikinsa da kwakwalwarsa har ma da zuciyarsa, sai
abubuwan da zai loda musu yanzu. Duk wasu tensions sun fita. Wanda ya tabbatarwa kansa ba komai ne ya haifar masa da wannan nutsuwar ba face
rahamar dake cikin aure, da tarin lada da gafarar da Ubangiji ya sanya a cikinsa.
Daga lokacin da ka daura hannu a jikin matarka ta sunnah dukkan alhakin da ka dauka a
rayuwarka na zina ko makamancin hakan Ubangiji ya juya shi zuwa abundant reward wanda shi
kadai ya san adadinsa.
Juyi ta yi cikin gyara kwanciya kafin ta soma magana cikin gigin barci ne ko na allurar barci
ne bai sani ba…..
“Ya Himu….. Ya Himu .... don Allah ka yi hakuri, na tuba na bi Allah na bika….Baba Dacta ka
ceceni zai kasheni....!”.
Kalaman da take furtawa kenan wadanda a jiya ya hanata furtawa, sai yanzu suka samu
sarari suke sakin kansu cikin magagin barci. Wadanda suka sa Ibrahim Takai, cikin wani hali
mai kama da nadama, bai so al’amarin ya zo masa all of a sudden haka ba, amma ba regretting
yake yi ba, tunda in a wajen Ubangiji ne baida wani laifi. Shi Ya ce ku zowa matanku a duk lokacin da kuka so ko da suna a halin nakuda. Matanku
gonakinku ne, ku zo musu a duk lokacin da kuka ga dama idan ba haila, ko nifasi suke yi ba.
Yadda bai yi tunanin cutuwarta ba sai na shi biyan bukatar shine abinda yake regretting, to
shi kansa bai san yadda zai yi da kansa ba, samartakar, tashen balagar da tuzurancin ya hada
duka ya saukewa Rayhanah a lokaci daya. Adadin kaunarka ga matarka, adadin karfin
sha’awarka a kanta. Sai dai ya yarda ya yi laifi, dole ya yi lallashi harma da banbadanci, in ma bai iya ba yanzun
nan zai shiga makarantar soyayyah ya koyo. Ture laptop din ya yi, ya mike ya shige cikin
bargon nata, ya mika hannu ya janyota gareshi.
Ai sai ta soma kokarin kwacewa tana rokonsa tana magiya cikin kuka, gabadaya ta gama
tsorata da shi. Ko ganinsa bata son yi. Karfi yasa sosai ya riketa. Har tasoma gajiya da kokawar
ta, jikinta yayi sanyi lakwas.
“Ka taba kashe abin da ka fi so a duniya RAYHANAH???”
Yadda ya yi maganar cikin sanyi, tarin so da kauna da kulawa, sai ta daina kokawar kwatar
kan nata.
“Rayhanah idan ka kashe shi kai da wa za ka zauna? Wajen wa za ka je ka sauke son nashi
da ya yi maka babakare a zuciya?
Ina rokon Allah ya kasheni ya barki, ki yiwa ‘ya’yana tarbiyya irin taki.
Madallah….. da shigowarki cikin rayuwata….. Maadallah... da Uba irin Babanki Dr. MANSUR.
Mai so na da ALHERI..... da dimbin kauna mai yawa agareni. INA SONKI RAYHANAH! INA
SONKI RAYHAH!! RAYHANAH I so much love you!!!.”
[12/29/2019, 19:10] Takori: Sai ta daga kai a hankali don ganin daga bakin da wadannan
zakakan kalmomin ke fitowa, da babu wanda ya taba gaya mata kwatankwacinsu a zaki da
gardi? Tana tababar ya zamo cewa daga bakin Ya Himu ne…. wanda in ya ganta bai iya cin
abinci. Fuskar da ta gani cikin hasken safiyar da ya keto fararen curtains din dakin barcin, ya fi
gaban a kirashi Ya Himu.
Cikakken likitan Koda ne Dr. Ibrahim Mansur Balarabe Sardauna, mai matsayin (Nephrology
Consultant) a babban asibitin Illinois, ba dan matashin dalibin nan mai girman kai da kwalisa a
AKTH da gidan Dacta Mansur ba.
Wannan fuskarsa cike take da gargasa lallausa, da tarin hankalin da shekaru suka taimaka
wajen karuwarsa. Idan aka kira shi Dr. Ibrahim Mansur Takai, zai fi dacewa da shi fiye da a kira
shi Ya Himu.
Duk da cewa halayen basu canza ba, zuciyarshi ta yi laushin da bata da shi a baya, mijin da
ko kyakkyawar surar jikinsa ta kalla kullum, ya ishi zuciyarta ta kasance cike da wadatar zuci, da
godiyar Ubangiji. Ta kuma yi alfahari da zamantowarsa barin rayuwarta, kuma uban ‘ya’yanta.
Wadda ta fi kowacce mace a duniya samun alfarmarsa, har kuwa da uwar da ta haife shi sai
dai a ba ta matsayinta na UWA a bar neman albarka, amma ba za ta taka wannan matsayin ba.
In haka ne bai kamata ta ji haushi, tsoro ko nuna gazawa a kan hakkinsa da Allah ya rataya a
wuyanta ba. Har ta yi sake da wannan damar da Allah ya bata, wasu ‘yan iska a waje su kwace.
Masu iya magana suka ce, wai tsalle daya shi ke jefa mutum rijiya, abin nufi a nan, tun a
lokaci na farko ta nuna gazawa wanda hakan zai sa ya yi baya-baya da ita don gudun bacin
ranta ko bacin zuciyarta.
Ya soma tunanin hanyar da zai bi ya dinke barakar ta, wadda ba komai ba ce illa ya nemo
wata, wadda za ta jurewa jarumtakarsa a auratayya.
Wannan tunanin da Rayhanah ta yi, ba wani ne ya koya mata ba, ba karantawa ta yi ba.
Tsinkayen hankali ne kawai (foresight ).
An ce wai idan baka iya kuka ba, to iyayenka ne ba su mutu ba. Baki iya goyo ba saboda
yana da wahala kuma zubewar aji ne, to baki haihu bane. Ko kece ‘yar Karuna in dai
Bahaushiya ce ke, kuma cikakkiyar ‘yar kasar Nigeria.
Shirun da Rayhanah ta yi, da kukan da ta daina lokaci daya kamar daukewar ruwan sama,
shi ya ba Doctor Takai, damar kara mamayarta (Needing for more…....).
Amma ga mamakinsa wannan karon bata nuna razana ba, shi din ne ya tuna da dinkin da ya
yi mata ya hakura, amma fa ya kasa hakura da abin da ya fi so daga wadannan ‘luscious lips’
na Rayhanah, shi din ya ci gaba da yi cikin wani irin salo da Rahane ta kasa juyawa baya,
lallashi da banbadanci har da hawayen neman afuwa, abinda ya gigita Rayhanah…. Ya Himu
ne? (She is still doubting).
Alkawarirrikan da yake daukar mata ta san ba a hayyacinsa yake fadarsu ba, don haka ba ta
kama ko daya ba.
Ba ta san lokacin da hannuwanta suka yi fitar bazata ba suka rungume Ibraheem, rungumar
da bata taba yiwa wani abu a rayuwarta ba, bayan gawar mahaifinta.
Ga mamakin Ibrahim Rayhanah ta soma taya shi sumbar cikin nata salon mai bin umarnin
zuciya da odar gangar jiki. Ta sakar mishi komai, ta yarda in mutuwa za ta yi ta mutun, in dai a
kan farin cikin Ibrahim ne.
Shi din ne ya yi jarumtakar cewa,
“A’ah…Rayhanah ”
Yana yin baya-baya da ita kada cin zalin ya yi yawa. Ita kuma cikin kara iza shi take da tana
fadin….
“Ba sai a kara dinkewa ba???”
Duk da halin da Ibraheem ke ciki bai fasa yin dariya ba saboda farin cikin da ya lullube shi. A
kalla yau ya tabbatar Rayhanah na son sa, son da ba ta yiwa Khalipha.
Kalami ta yi cikin jin kan mace ga mijinta ba bisa tursasawa ba ko son fita hakkinsa, a’a, don
tana sonsa. Tana son farin cikinsa fiyeda nata. Sai ya kwaikwayi ‘yar muryarta cikin dariya ya
ce,
“A sake dinkewa don kin zama kwarya??????”
*****
Cikin wannan rayuwar da ta fi kowacce dadi da gardi ga kowanne dan Adam, Ibraheem da
Rayhanah suka ci gaba da rayuwa a Chicago. Suna waya da Daddy da Inna Juma a kai a kai,
shima Ibrahim yana gaisawa da mahaifiyarsa da Yaya Khalipha, sai dai bai taba yi mata zancen
aurensa ko zancen Rayhanah ba, don Daddy ya gargade shi da kakkausan harshe da yin
hakan.
An debi watanni biyar, duk abin da ya kawo shi ya kammala shi, ya auna komai da ya
mallaka a Chicago bankunan gida Nigeria, wasu kuma daga ciki shipping dinsu yayi kamar
motoci da furnitures da yake son kawata gidansa dasu.
Gidansa kawai ya bari bai kadar ba. A zuciyarsa ya ajiye shi ne ga first born din da duk Allah
ya ba shi, mace ko namiji. Su zo su zauna ciki suyi karatu, in sunyi aure su zauna da iyalinsu.
Idan asibiti zai shiga, tare suke shiga, idan University of Chicago zai shiga yi lecturing, zama
take cikin daliban ayi laccar da ita.
Ko tsura masa ido wata a cikin daliban ta yi, ta fara auna mata harara kenen. Ta hanashi
motsin kirki ko doguwar hira yake yi a waya sai ta ce zance yake yi. Haka suke yawo cikin
Illinois hannayensu sarke da juna.
Idan theatre za su shiga, Rayhanah na ofishinsa tana jiransa, shi Ibrahim maimakon ya ji
haushi kamar yadda sauran maza ke ji in matansu na musu hakan, shi dadi yake ji. Domin ta
rabashi da karnukan dake farautarsa, ko wata mu’amala ce ta hada shi da matan asibitin ko
dalibansa, tana gefe sarke da hannu a kirji kafafu a sarke, tana dakon mai kawo wargi. Ga Turawa da shegen tsoro basa son tashin hankali, ta fi ganin maita a kan Ibrahim daga
mutanenmu mazauna can.
Mutum daya ta tsaya mata a rai dake yawan yi masa waya kuma su dade suna hira wai ita
Sapna, bai taba ignoring kiranta ba, amma a cewarsa dalibarsa ce.
Kuma duk sanda ta binciki wayarsa babu hoto. Don haka take addu’ar Allah yasa wata rana
idonta ya ga idon wannan Sapnar, sai yau Litinin a wani marece Allah ya amsa addu’arta.
******