Author : Sumayya Abdulkadir Category : Taskar Novels
shiryawa su
Inna don kowa dake Kofar Naisa ya san sun dawo, inda aka gayyato dukkan makwabtansu na
kusa dana nesa. Baka jin komai a Badalar Kofar Naisa ranar walimar nan sai labarin Malam
Bilyaminu, batansa da abinda Zakari yayi masa, da labarin Innar Hauwa da Hauwa data
makance Allah yayi mata ludufin rayuwa tayi a aure a Saudiyyah da makanta da komai ta haifi
yan biyu son kowa. Ai an ance ma gawurtaccen likitan ido take aure acan din.
Wai wacce Hauwar kuke nufi? Ba dai yarinyar nan mai ciwon ido na apolo Hauwar Inna ta
lokonsu Malam Isa ba? Ita fa, wadda Salele yake yiwa jagora”.
Ai kuwa wqadanda aka gayyata dama wadanda baa gayyata ba a kofar Naisa duk sun taho
walima da gulmar gani da ido gidan Malam Bilyaminu dan kofar Naisa. Mama da wasu daga
cikin yan uwanta dana Abba da ke Shanono da Mardiyya sun samu halarta. Mardiyya da Salele
sune masu rabon abinci da abin sha natake away ga mahalarta taron. An ci an sha anyi hanian
an yi hotuna da vedio na tarihi yan biyu kowa ya gansu ya daukesu ya musu addua.
Sunje wa Mama zasuyi sati a wurinta nan Mama ta koma gyaran haihuwa, wanan karon
wane gyaran amarci don Maman Farida guda ta yiwa waya tace tayiwa Hauwa gyaran haihuwa
ko nawa ne zata biya.
yan biyu kuwa kusan tsakiyarMama da Abba Prof.suke kwana suna lelensu da shafesu da
addua. Ana I gobe zasu koma Jiddah Abbah ya sa Sarham a gaba yace sai ya gaya masa ina
zancen karatun Hauwa ya kwana, da yanzu ta gama year two dinta a wanda ta jingine. Sarham
yace ya samar mata makarantar da suke Inclusive Education wato jamiar DAAR EL-HIKMAH
UNIVERSITY da sun koma zata fara don haka wanna karon Sarham da kansa ya bukaci tafiya
tareda Mardhiyyah don ta taimakawa Hauwa da rainon yan biyu da sauransu.
Dakin Sumayyah aka baiwa Mardiyyah take hidimar ta da yan biyun ta, tana taimakawa
Hauwa su in zata shayar dasu ta rike mata daya. In kaga yadda Hauwa ke hidimar yayanta
wajen saka musu diaper da yi musu tsarkin kashi da goge tumbidi da bada madarar jarirai abun
zai matukar baka mamaki, haka duk kuka idan dayansu tayi ta san me take bukata. Sarham in
yana gida tareda shi ake komai duka da yanata shirye-shiryen makarantar Hauwa a lokacin
amma kuma tunda ya kyalla yaga ta fara sallah a wani dare abubuwa suka canza. Baiwar Allah
tayi kokarin nuna masa cewa yan biyunta basu yi kwari ba Sarham yace Allah yasa jiya aka
haife su, nima tun haihuwarsu banida kwari, Allah shine mai rayawa kuma shine mai kashewa
kin ji ko? In kuma wannan yarinyar ce ta kara yi miki huduba sai in bar ki da ita in karo ta uku.
Ya fada yana saita alamuran yadda yake son su Hauwa na kwallah har da tsane hawaye tana
fushin da Sarham bai san tana yi ba a lokacin sabida ya tafi da yawa, bai nutsu ba sai da ya
kwashe gyaran Mama tsaf a daren yau. Da aikin tukudin Inna. Ya bar Mardhiyya da yan biyu
tana ta fama, duk sun rikice mata da kuka sun ki kama madarar da take basu a feeder.
Shiyasa ake cewa Uwa tafi tausayi yayan ta, sai da ya koma Sarhamun sa sannan ya koma
lallashi. Yace Maijidda abun alfaharinki ne ace mijin ki cannot do without you. Ni kadai nasan
manejin danayi har kwanakinnan arbain, kiyi hakuri ni bana gudun kaddarar yaya karewa ma
son su nake yi, so nake ki cika min gida dasu son samu duk shekara ki juye min yan biyu. Bari
in gaya miki abinda bai kamata in gaya miki ba nafi samun duk wani contentment da duk
nutsuwar aure idan ina tare da ke. Soyayya daban, sexual satisfaction shima daban. Madinah
ina mata soyayya ke ina miki so da kauna wanda yafi gaban ina ganin ki in iya kauda
kwadayina sai dai in bakida lafiya to wannan kuwa zanjure har ki samu lafiya. Ni likita ne na san
yadda zan kula da lafiyar yaya na kin ji ko?
Ta gyada kai cikin sanyin jiki, yana daura mata tawul a jikin ta yace karbo su ki basu nono
kukan su ya dame ni.
Anan ne tayi magan cikin hararar sa.
wallahi bai dameka ba, da ya dameka da ka hakura sai sun yi shiru. Yace to sai me? Ba da
hakan ba da an same su? Yanzunma kannen su nake hari shiyasa ban sauraresu ba ta zuba
jallabiyya a jikin ta zata fita bata saurare shi ba yace dakata, tsofaffi sun ce sai kin yi wanka zaki
taba su kada ki shafa masu datti, kodayake ni na san jiki na ba datti sai albarka ta dan dakata
jimmm a bakin kofa, ai kuwa Innama ta gaya mata haka wai in taje dakin miji kada gta yarda ta
taba su sai tayi tsarki, sai kawai ta juya ta nufi toilet. Ya ce ai kya tsaya in gama hada miki
ruwan mai zafi sosai ance baki gama jegon ba har gobe. Tace don Allah don annabi kaje ka
basu madara zan kula da kaina ka cika ni da magana ga kukan su yana ruda ni. Tausayi ta
bashi sosai yace to ai nima ban yi wankan ba ko inzo muyi tare? Kin ga daga nan in cuda miki
baya da dogon wuyanki. Hauwa takaicinsa ya isheta ta shige toilet dinta harda saka key.
Sarham yayi jifa da filo ya mike yana saka jallabiyyarsa yana rero baitukan sa na ;
-Addua nake Allah ya taimakeki HAUWA-HAUWA!.
Daga cikin toilet Hauwa tana zuba ruwa mai zafi cikin gashin kanta, take jin sa tana sakin
murmushi daga zuciya zuwa ruhi. Ta ce a hankali;
Nima Adduaa nake Allah ya ja da ran maigidana Lelen Abba a dade ana aikin lada.. shi da
HAUWA!.
Ya gama dukkan shirye-shiryensa na yiwa Hauwa aiki ranar Litinin amma sai me?
Ya dawo gida yau a bit late kuma ranar girkin Hauwa ne, suna girki a kitchen ita da Mardiyya
shinkafar Basmati ta tafaso Mardiyya ta bude tukunyar, Hauwa ta shaka sosai kawai sai taji
wani mugun amai ya yunkuro mata.
Ta tsugunne a wurin tana kakari amma aman yaki fita kamar zuciyarta zata fito ta bakinta ga
goyon Safiyya a bayanta. Da sauri Sarham ya bar maganar da suke yi da Madinah a falo ya
karso kitchen din, kai kakarin me nake ji haka? Dai dai lokacin ta samu aman kore fatau dashi
ya biyo makogaronta don azumi take na alhamis bata ci komai ba shirin buda baki suke yi. Da
sauri ya sauri ya ida gareta ya daga bayan ta yana shafawa har ta samu ta amayar da komai
dake cikin hanjinta. Madina ta gifta zata wuce dakin ta kallo daya ta yi mata tasan ciki ne da ita
ana mata amai a kitchen ta wuce daki cikin gigicewa.
Ita kuma Hauwa haka take da Haihuwa cikin lalura Allah mai girma!
Ya kamo Hauwa zuwa dakinta yace Mardhiyya ta gyara wurin. Suna shiga ya soma checking
dinta har fitsari tayi ya saka masa PT strip. Wata wawuyar runguma da Sarham yayiwa Hauwa
saida ya kayar da ita a saman gadon aurensu. Tana tambayarsa cikin tsoro da fargaba ko meye
yakewa murna haka? Kuma me sakamako PT strip ya nuna? Amma bai saurareta ba sai
sukuwa yake cikin rawa da waka yana narkewa cikin jikin Hauwa;
“Gimbiyar mata kike a zuciyata HAUWA.
Da zaa bani biro na baki maki HAUWA
To zaki haura lambar da zaa baki HAUWA.
In zaa tara mata wa zata fi ki HAUWA.
To addua nake... Allah ya taimakeki HAUWA.
**** ***** *****
Aikin da baa yiwa Hauwa ba enan a wannan shekarar amma dai tayi borin zuwa makaranta
duk da haka. Bayan ta ci kukanta ta gode Allah na gwarne da take ganin wahala ne. Shima
kuma da yake lallabata yake ya yarda ta fara zuwa DAAR AL HEKMAH UNIVERSITY a wannan
shekarar duk da yaron cikin, ya kuma dauki alhakin kaita lacca da daukota da kansa kullum. Haka Hauwa-Kulu ta soma karatunta karkashin BLaw (Bachelor of Law) wanda zai dauketa
tsayin shekaru hudu a jamiar Daar Al Hekmah, Jeddah, KSA.
Cikin Hauwa wata takwas ta haifi yarta ta uku a duniya wadda ta rokiSarham Allah da Annabi
ya saka mata sunan aminiyarta Sumayyah.
Sumayyah wadda har lokacin ake ake kai ruwa rana akan maganar aurenta, don Hajja
Ramlah ma tabi bayan su Madinah tace ya nemo wata, bata ga dalilin sai wadda ke kin yar
uwarsa zaice zai aura ba. Baban su kuwa wato Ahaji Attahiru tun karin auren Sarham dama
basa ga maciji shi da Sarham don yaji ciwon abinda yace masa a asibiti lokacin da zaa yiwa
Madina tiyata. Don haka ma da yaji wai kanwar Sarham ce Usman yake so bai saka baki ba
kuma bai yi adawa ba ya dai ce sai abinda suka shawarta shi da yar uwarsa.
Shikuma Usman ya dage baiga dalilin da zaa ce Madinah ce zata yi masa deciding matar da
zai aura ba tunda gaba yake da ita. Don haka ya kai karar Madinah gun Kakar su Haj Laila kan
tana bata masa zancen aure ta karkashin kasa a gurin iyayensu. Haj Laila sai kawai ta tada
waliyyai suka tafi gun Abba suka kai kudin aure, Abba bai karba ba yace sai yayi magana da
Sarham tukunnah tunda shi yasan Usman fiyeda kowa.
A karshe dai Kakar saida ta tafi har Jeddah ta samu Alh. Attahiru ta gyara komai tsakaninsa
da Sarham, tace ita bata ga dalili ba da don suna son autar su Madinah zasu ce bazaa yiwa
Madina kishiya ba tunda ba alkawari sukayi a rubuce ba na cewa daga kanta Sarham ba zai
kara aure ba, kuma wulakantata yake yi ba sannan polygamy aladar mutanen Kano ce. Itama
da suk ganin baayi mata ba harsuke reference da ita to bari ta gaya musu gaskiya Alkalin
Alkalai ya so yi ita ke lalata zancen duk inda yaje neman aure har ya gaji bari, tace tayi nadama
lokacin da yayanta mata biyu suka ki auruwa har bayan digiri na uku suna gabanta. Don haka
su bar Usman ya auri wadda yake so yar gidan mutunci wato gidansu Sarham su bi su da
addua. su daina biyewa kishin Madinah sauda dama tana gyara gidanta ne shi Usman ta saka
shi a matsala don ta san suna matukar sonta.
Da waannan Haj Laila ta gyara zancen auren Sumayya da Usman. A wata asabar, a
masallacin jumaa na tsohuwar jamiar Bayero aka daura auren SUMAYYAH SHANONO da
USMAN SORONDINKI. Kasancewar duk suna birnin Jeddah daga angon har amaryar kuma
Sumayyah na tsakiyar karatu dole iyayen da kakannin ne sukayi yinin bikinsu sukadai.
Sumayyah ta koma gidan Bhaiya dakin Hauwa acan aka shafa mata lalle dole Madinah ma ta
saki ranta albarkarkacin Sarham da Usman da yae ta mata hidima don ta sa hannu a aurensa.
Ita taje ta shirya musu kasaitaccen gidansu a Jeddah ta tsara komai dama dai Madinah ba daga
nan ba. yayinda Hauwa ke kula da yaranta da danyen jegonta da kawayen Sumayyah da ke
cike a gidan kowa nata shaawar yaran Hauwa da yadda take sabgar kula dasu musamman
wajen breast- feeding. Sarham dole ya daga kafa a gidansa sabida hidimar da akeyi kuma shi
Abba Prof. ya turowa kudi ya hada da abinda ya tara musamman don auren Sumayyah ya
baiwa Madinah ta zabar mata kayan daki daidai karfinsu. Duk da cewa Usman yace baya
bukatar komai amma saida suka yi wanda zasu iya kasancewar Usman yana ISDB ne tareda
Babansu.
Watan Hauwa uku kenan da haihuwar Sumayyah yarinyar tayi bul-bul gwanin shaawa haka
kamanninta da Sumayyah yayi yawa, a lokacin Hauwa na shekararta ta biyu a (BLaw) Sarham
ya gama duk wasu shirye-shiryensa na yiwa Hauwa aikin ido. Ya saka ranar Litinin 5/5 a
matayin ranar da zai shiga da Hauwa tiyata, ya kuma kira waya ya gayawa gida, nasa iyayen
dana Hauwa, sannan ya gaya musu itada Madinah.
Ya roki Madinah wata alfarma data sanyaya mata jiki.
Na san a policy dinki Munawwarah, babu taimakawa kishiya, amma ina rokon ki ki taya
Mardhiyyah kularmin da yaya na, har Allah yasa ayi aikinnan na mahaifiyarsu lafiya a gama,
kuma idan Waheedah ta shiga wajen su ki daina cewa Mardiyyah ta daina goya mata su bazata
iya daukar su ba sabida girman jikinsu, in ma ta tika su da kasa babu ruwanki yan uwanta ne,
kinji ni ko?.
Mama dama tayi shirin zuwa Umrah a wannan shekarar kasancewar watan Ramadhan ya
kama. Don haka ta hau shiri don tuni ta samu visar Umrah. So take ta isa Jeddah kafin ranar da
zaa yiwa Hauwa aikin.
Dr. Madinah ta kai gwauro ta kai mari ana I gobe zaa yiwa Hauwa aikin idanunta, tana
fafatawa da zuciyarta da kuma shaidan, a karshe ta rinjayi shaidan din, da taimakon Ubangiji.
Ta fuskanci maigidanta Dr. Sarham da ke fitowa daga toilet cikin fararen kayan barci, ya yi
wanka ruwa na yarari daga kansa yana yarfewa da santala-satalan hannayensa.
“Babansu Waheedah, please ina so ka bani dama in shiga cikin ‘team’ din ku, wato likitocin
da za su yi wa Hauwa aiki gobe. Albarkacin musulunci. Ina so a yi wannan aikin ladan da ni. I
mean it.
Hawaye ya digo daga kwayar idonta. Ta tuno tarin rashin kyautawarta garesu shida Hauwa,
da tarin gorinta ga nakasar Hauwa, yau ga HAUWA-KULU-MISKINIYA-MUSAKA ta cikawa
SARHAMU da gayu gida da yaya, don ita ta fahimci abinda su duka hankalinsu ma bai kai ba, a
matsayin ta na mace kuma cikakkar likita cewa Hauwa-Kulu wani cikin ne da ita, tana boyewa
Sarham wannan karon kada ya kara fasa yi mata aiki. Duk abin da zai dawo mata da Sarham
dinta na baya (very jovial) domin ya dan canza mata tun dawowarta gidan, saboda yadda take
ja baya da duk wata harka ta iyalinsa, tana so ta dawo dashi yadda yake a baya kuma mai
yarda da ita, don haka duk abinda tasan zai faranta masa shi ta ke son yi yanzu. Duk da ta san
baa bari a kwashe daidai.
Ya kama hannunta suka zauna tare a bakin gadonta, ya ce,
Ni na dade da sanin Madinah-Munawwarahta mai kirki ce, mai imani ce kuma mai tsoron
Allah ce. KISHI ne mara amfani yake sarrafa min ita a baya.
Ina rokon Allah ya albarkace mu bakidaya ni da ku iyalina, ya hadamin kan yayana ko bayan
raina.
Ni na san ba za ki iya alaka ta jiki da Hauwau ba, sabida kina mata kallon tasgaro ga
soyayyarmu, kuma ‘barrier’ ga cikar farin cikinki, wanda ko daya in kin duba ba haka ba ne.
Ki sa a ranki aurena da Maijiddah rubutaccen alamari ne daga Allah (S.W.T) wanda ni ma
ban taba hasashensa ba, sannan ba gazawarki ce ta wani bangare tasa na yi shi ba.
Haka nake so duk mata irinki su saka a ransu, sai a samu zaman lafiya da fahimtar juna
tsakaninsu da mazajensu.
Komai Ubangiji ya nufeka da yi, ko Ya rubuta yana cikin kaddararka, hakika sai ya same ka.
Addua ba ta canza kaddara amma tana rage tasirinta.
Don haka ban auri Hauwa ba sai da na yi addua da istikhara cewa, idan ba alkhairi bace a
gare mu, ni da ke kada Allah ya ba ni ikon aurenta.
Madinah ki yarda ba ki gaza da ni ta kowanne bangare ba, sannan rashin gazawar taki baya
nufin shikenan bani da hurumin auren kowa kuma. Hudu Allah ya halattamin. Bayan Hauwa ma
Allah Ubangiji ya halatta min wasu biyun sai in ban yi raayi ba, ko ba sa cikin kaddara ta.
Allah Ubangiji ya yi umarnin a kyautata wa MISKINI da MARAYA a cikinAlqurani, wannan
rubutacciyar ayar Ubangiji ce.
Don haka kyautatawarki ga Hauwa ko akasinta yana cikin mizanin ayyukanki na alkhairi da
na sharri. Na gode da kika fara karkata mizanin don ya koma na alkhairi”.
Madina ta yi maza ta rungume shi tana kuka, ta ce, Wallahi daga yau na tuba da duk abin da
nake yi a kanta. Ka bani dama in shiga cikin likitocinta in yi ‘repenting’ kuskurena ko Allah Ya
dube ni ya yafe mini.
Amma ka sani KISHI da kishinka Sarham wani abu ne da har abada ba zan daina ba,
saboda ba ni nake sawa raina ba, halitta ne. Alkawari daya iya yi maka shine; zan koyi rike
linzaminsa… in dinga controlling dinsa ta hanya mai kyau.