Zuciyar Mace Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 41

3K to 6K   out of 121.6K words

kunna data, sai ta ga Ramla ba ta online, ta sauke ajiyar zuciya, amma har lokacin tana fargaba, ta rasa ya za ta yi ya daina janyo mata abun kunya irin haka, ana fara sallar isha'i ya tashi zai fice, yana cewa Salim"Sai na dawo".

Salim ya ce"Daddy ina za ka tafi? Don Allah ka zauna yau kar ka fita".

Ya yi dariya yana Waga Amir sama ya ce"Ai dole na fita, idan na zauna a gidan me zan yi Salim? Zuwa zan yi na gyara wasu abubuwa".

Salim kuwa da surutu ya ce"Wani abu?"

Ya ce"Kai yaro ne Salim, ina zuwa kar ka yi bacci ka ji?"

Ya gyaWa masa kai, Nura ya fice yana kiran waya, idan ya yi irin wannan fitar sai ya kai sha biyu har ?arfe Waya, kullum sai ta yi bacci yake dawowa.

Zuwa takwas da rabi yaran sun yi bacci, ta yi musu shimfiWa a falo, ta yi musu addu'a, sannan ta rufe falon ta shige Waki, ?ofar gidan dama kodayaushe a rufe take, sai dai idan ya dawo ya saka mukulli ya buWe, dayake tana da nauyin bacci ba kullum ba take jin dawowar tasa ba.

Ta sauke Aiman daga bayanta ta kwantar, ta yi masa addu'a, sannan ita ma ta yi, babu jimawa bacci ya Wauke ta, haka take yi kafin ?arfe tara ta yi bacci, saboda babu Wan fira.

Yayin da Hasana ta saki baki take sharara bacci, shi kuwa Nura yana fita masallaci ya tafi sallar isha'i, bayan an idar ya hau babur Winsa ya tafi gidan su wata Hafsa, wacce ya karSi lambarta tun shekaran jiya da ta zo shagonsa siyan kayan kwalliya, tun a ranar ya so zuwa, amma yana da wasu al?awuran, sai yau layi ya zo kanta, Ramla ma ya je ganin gidansu ne kawai amma sai zuwa jibi zai koma. Fira sosai suka yi da Hafsa, wacce bai Soye mata yana da mata da ?a?a uku ba, sai dai ya faWa mata sam bai yi dacen mace ba, Hafsa ta ce"Ikon Allah, amma dai auren wuri ka yi, wallahi ban yi zaton kana da aure ba".

Ya yi wani murmushin ?asaita ya ce"Wallahi da aurena, kawai dai tsabar tsafta ne da kula da kai, sannan kin san idan mutum yana cin guminsa yadda ya kamata ya ci mai kyau ya sha mai kyau, dole za a gan shi tsaf".

Hafsa ta ce"Hakane" Don ita ta tsani kishiya, ba za ta iya auren mai mata ba, ta yi soyayya da masu mata wajen su uku, duk mamma?o gare su, ba sa Sarin kuWi saboda hidimar gidansu ma ta ishe su, sai dai shi wannan ta ji yana zancen yana cin mai kyau.

Nura ya ce"Wallahi Hafsa a hakan ma da kika ganni don ma dai ina da matsala ne a gidana, ban yi dace da mace ba, kin san ita rayuwa idan ka yi dacen mace ta gari wacce ta haWa komai kamar dai ke Win nan, to fa har wata ?iba kake yi".

Hafsa ta ce"Kuna samun matsala da ita kenan".

Ya ce"Idan kin ji matsala Waya kenan, matsaloli ne da yarinyar nan birjik wallahi, kin ga dai irin kayan kwalliyar da nake siyarwa, amma wallahi sai na yi wata ban ga hoda a fuskarta ba, kuma duk order da na yi sai na dara kai mata ta zaSi kaya kafin na kasa a kasuwa, Winki duk wata sai na yi mata ita da yara, amma indai kin ga ta saka sabon kaya to fita za ta yi, nama a firji sai dai wani ya tarar da wani, amma idan ta kwaSa girkin kare ma ba zai ci ba, gaskiya mata kuna da matsala, yawanci ku ne kuke saka mazanku ?ara aure".

Hafsa ta ce"Wasu matan dai, amma ni yaushe zan samu mijin da zai yi mini komai na ?i faranta masa?"

Ya ce"To Allah Ya sa kakata ce ta yanke sa?a".

Ta ce"Hmm! Idan da gaske kake ba".

Ya ce"Kamar ya?"

Ta ce"To ai na ga haka kuke masu matar nan, yawancinku kuna zuwa wajen zance ne don ku rage dare ba don aure ba, sai an ce ku fito sai ka ga wani matarsa ta fi ?arfinsa, wani kuma gidan nasa ma da ?yar ake cin abinci sau uku a rana, ba shi da halin ?ara auren, ni fa shiyasa ban fiya sauraron mai mata ba".

Nura ya yi wata dariya ya ce"Baby Hafsa kenan, kin sanfa akwai maza, akwai muna maza, wallahi ni kam namiji ne a gidana, na fi ?arfin gidana, sannan idan da yunwa a gidana a jikina za ki gani".

Hafsa ta ce"A jikin matarka dai, ko tana da matsalar gyara jikinta na san tana cin abinci ta ci ko ba daWi".

Ya ce"To ni dai ki gwada ni ki gani, na tabbata ba za ki yi nadamar Sata lokacinki ba".

Ta ce"Zan yi bincike dai".

Haka suka dinga fira, yana ta kushe Hasana, da ?arairayi, don rabon davya Wauki hoda ya ba ta kyauta har ta manta, ita yanzu sam babu kwalliyar ma a gabanta tun da ko ta yi ba ya ganin ?o?arinta ballantana ya yaba, sai dai idan ta yi wanka ta shafa hodar da man leSe, don kanta ba dai don miji ba.

Sai ?arfe goma ya bar wajen Hafsa, ya zarce majalisarsu ta bakin titi, ana ta fita sai sha biyu ya koma gida, ya buWe ya shiga, ya saka sakata, ya tura ?ofar falon ya shiga, yana haska yaransa, ya gyara musu kwanciya, don Waya ya Worawa Waya ?afa, sannan ya shiga Wakin, ya canza kaya ya hau gadon, ya haska Hasana da take ta sharar bacci, Aiman a kusa da ita, ya taSe baki ya kwanta, a yanzu ba shi da burin da ya wuce ya ?ara aure, yana bu?atar ?ar sawalwala wacce dare yana yi zai ji yana Wokin dawowa gida su sha soyayya, babu ciki babu goyo babu yaran da za a jira su yi bacci.


*******
?arfe takwas da rabi wayar Nuratu ta fara ?ara, ta duba ta ga lambar ce daga Saudiya, ta san Abdul ne mai kira, don yana aron wayar mutane ya kira ta idan ba ta hau online ba, saboda ba kasafai yake saka kati ba, Abdulmalik mutum Waya da take gani a matsayin sanyin idaniyarta bayan mahaifiyarta, ta san bai ji rasuwar da wuri ba shiyasa bai kira ta ba, ta Wauki wayar da sallama, ya amsa, sannan ya Wora da faWin"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!".

Nan ta ji wani sabon rauni ya taso a zuciyarta, ta fara kuka, ya ce"Ashe Mama lokaci ya yi" Sai ta kasa magana.

Ya ce"Ki yi ha?uri Nuratu, duk mai rai mamaci ne dama, Allah da Ya Wauke ta ya fi mu son ta..."

Cikin kuka ta ce"Yaya Abdul ina bu?atar Mama a rayuwata, ina bu?atar uwa, yanzu da wa zan zauna a wannan bahagon gidan namu mai cike da takaici kala-kala?"

Ya girgiza kai kamar tana ganinsa ya ce"A'a kar ki sake faWar haka, Mama ba ta yi gaggawa ba, mu ma wata?il yau ko gobe ne, duk mai rai gawa ne shi a tafe. Sannan Allah Yana sane da yanayin gidanku Ya Wauke ta Win ya bar ki, sai mu bar hakan a matsayin wata jarabawar rayuwa Allah Ya ba mu ikon cinyewa".

Hawaye mai zafi suka fara tunkuWo juna daga idonta, Yaya Abdul Winta ne kaWai mai mai da damuwarta tasu su biyu, sai dai wannan ?addarar da ta afka a dare Waya ta dalilin inganta rayuwarsa, sai dai tana zargin hatta shi Abdul Win ba zai iya karSarta ba, da wane idon za ta kalle shi idan ya gane tana da ciki? Ina zai saka kansa a ranar? Ta fi kowa sanin zafin kishin shi, shiyasa yake tsaye tsayin daka a kan ?ananun bu?atunta wanda ba su gagare shi ba, ko wannan tafiyar da ya yi dominta ne, yana can yana bauta don ya tara kuWin aurensu, kuma ya samu jarin da zai ri?e su, don su yi rayuwa mai inganci.

Suna cikin waya ta ji muryar Baba yana ?walla mata kira, ta yi saurin cewa Abdul"Ina zuwa ka ga Baba yana kira".

Ya ce"To ki yi masa gaisuwa, anjima zan sake kira".

Kafin ta fito Baba har ya bankaWo labulen yana cewa"Wai uwar me kike yi ne da kika share ni?"

Ta fito jiki ba ?wari tana cewa "Gani nan Baba".

Ya ce"Ga Alhaji can a zaune, sai ki je ku tattauna".

Ta ce"To".

Ta bi bayan Baba, ta tarar da Alhaji Hashimu tsaye yana danna waya, ta tsaya tana kallon fuskarsa da wayar ta haska, babban mutum ne zai doshi shekara sittin, sati biyu kenan da haWuwarsu, ya kawow malamin makarantarsu sada?ar da yake kawowa duk wata, ya ganta, a ranar sai ga Malaminsu wato shuganan makarantar ya zo har gida wai an aiko shi, ya zo neman alfarma, ya faWa mata Alhajin yana sonta, kuma matansa uku, nauyi da kunyar Malam Isma'il bai hana ta faWa masa tana da wanda take so ba, don haka Malam ya samu Baba ya faWa masa, a ranar Baba faWa kamar zai ari baki, ya ce dole kuwa ta manta da kowa ta aure shi matu?ar da gaske yake, duk kuwa da kafin Abdulmalik ya bar ?asar nan sai da iyayensa suka zo suka yi magana akan bayan shekara biyu zai dawo sai a yi auren, a lokacin Baba murna ya dinga yi, saboda yana ganin Abdul zai tara arzi?i kafin shekara biyun, amma bayan zuwan Alhaji Baba har yana cewa"Wane shirmen banza ne ki zauna jiran wanda ya tafi Saudiya? Ai sai ya shekara goma bai dawo ba, idan ya dawo ma ya ce kin tsofe ya samu wata ya aura, don haka ba za a yi wannan shashanci da ni ba".

Mama ta yi iya yinta don a bar zancen Alhaji Baba ya kafe, tijarar safe da ban ta dare da ban, har ?arar Mama ya kai wajen yayyunta tana hurewa ?arsa kunne, shi ne ta ce kawai Nuratu ta ha?ura ta aure shi, to a nan ne fa ta sanar mata zancen cikin jikinta, wanda ta same shi silar taimakon Abdul.


08028966015
*ZUCIYAR MACE*



BY
SADIYA ABDULRAZA?


*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)


https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY

PAGE 3


"Barka da fitowa". Muryar Alhaji Hashimu ta dawo da ita nutsuwarta.

Ta ce"Ina wuni".

Ya ce"Lafiya lau, sannu Nuratu ya ha?uri?"

Ta ce"Da godiya".

Ya ce"Allah Ya yi mata rahma Ya sa aljanna makoma, sai ki yi ta ha?uri kin ji ko?"

Ta amsa da amin, suka yi shiru na Wan lokaci, kafin ya ce"Kin ci abinci dai ko?" Ta yi banza da shi, ya sake cewa"Me kike son ci? Kar damuwa ta saka ki zama da yunwa, sai ya haifar miki da wani ciwon, na zo miki da abinci ki daure ki ci".

Ya ?arasa yana mi?a mata babbar ledar da take hannunsa, ba ta karSa ba, kuma ba ta ce komai ba, sai hawaye da suke ta gudu a fuskarta. Ana haka sai ga sallamar ba?i gidan, suka wuce su a zauren bayan ta gaishe su, sarai ta gane Umma ce mahaifiyar Abdul, tare da abokiyar zamanta, sai ?anwarsa, su ma kuma sun gane ta, don da fitila a hannunsu suka shigo zauren, gabanta ya dinga faWuwa, saboda tana fargabar Abdul ya ji labarin an ganta da wani, ga shi mutanen da ba ta isa ta ce masa ?arya suke yi mata ba ne suka ganta, duk hankalinta ya yi cikin gidan, ta ce masa"Zan shiga gida".

Ya ce"To Allah Ya ?ara afuwa, ga wannan ki karSa ki ci, da kuWi a ciki ko za ki yi wata bu?atar, sannan duk abin da kike bu?ata don Allah ki sanar mini, babu abin da ba zan ba ki ba, Allah Ya ji ?an Mama Ya sa ta huta".

Ta amsa da amin, ya ba ta ledar ta karSa ta yi cikin gidan, ta samu su Umma a tabarmar da ke tsakar gida tare da su Mama Asabe, suna mai da yadda mutuwar ta kasance. Ta du?a ta sake gaishe su, suka amsa suka yi mata gaisuwa cike da tausayawa, Mama Karime da ta ?yalla idonta a kan ledar ta ce"Kina zaune ke kaWai a Waki, sai mutuwar ta dawo miki sabuwa ai, ki wuce Wakina ki kwanta, bari na aika a samo miki ko kunu ne".

Ta ce"To" Ta shiga Wakin nata.

Sai Zainabu ?anwar Abdul ta tashi ta bi bayanta, Khadija da Hannatu suna kwance a Wakin, ta zauna tana ajiye ledar, Zainabu ma ta zauna ta mi?a mata ledar da ke ?unshe a hijjabinta tana cewa"Yaya Abdul ya ce na kawo miki"

Sai ta Wakko wayarta ta danna ta kunna mata voice, sai ga muryar Abdul Winta ta bayyana, daidai inda yake cewa"Nuratu ga sa?ona nan, jikina ya ba ni ba ki ci komai ba wunin yau, na yi nisan da zan ba ki wata kulawar da ta dace, amma ga ?anwata nan a madadina, idan a baki kike so sai ta ba ki, don Allah ki ci wani abun".

A nan maganar ta ?are, Zainabu ta mi?a mata ledar, bayan ta ciro yougurt ta buWe ta matso ta kai mata baki, Nuratu ta yi guntun murmushi ta ce"Wato Zainabu biye masa za ki yi ko?"

Tana dariya ta ce"To ai ni ?ar aike ce".

Nuratu ta karSa ta fara sha, ta sha kusan rabin jarkar, daidai sanda su Umma suke cewa Zainabu ta fito su tafi, Nuratu ta ji cikina ya fara hautsinawa, yawu ya taru a bakinta, da sauri ta fita tsakar gida ta fara kwarara amai, suna ta yi mata sannu, Zainabu tana cewa daga shan yougurt, Mama Asabe ta ce"?ila don ta jima ba ta ci komai ba ne, sannu Nuratu kin ji" Ta gyaWa kai, ta gyara wajen ta koma Waki, su kuma suka yi musu sallama suka tafi.

Tana shiga ta kwanta, a kan sallayar da take wajen, Mama Asabe ta shigo tana yi mata sannu, ta Wauki yogurt Win tana cewa ke ma ai ba za ki sha abu mai sanyi ba yanzu, tun da ?ila rabonki da abinci tun jiya, ta ce da Kadija"Dije tashi ki siyo mata kunu, ko ruwan bunu a wajen Mati mai shayi".

Nuratu ta ce"Gara ruwan bunun Mama".

Khadija tana fita, Mama ta janyo ledar wajen Zainabu, ta ga wani yougurt Win ne, da lemuka biyu, sai shawarma guda biyu, ta janyo ta wajen Alhajin, ta fara cin karo da ?an Wari biyar biyar a dun?ule, ta faki idonta ta soke su a zani, ta duba sauran kayan, har da kayan shayi, da biredi da manyan biskit ga kuma kaza da lemo babba, ta jinjina kai ta ce"Lallai ana gatale ki Nuratu".

Nuratu saman Wakin kawai take kallo, ta yi nisa a duniyar tunani, Mama ta ce"Wai ni kam dama babanki bai raba ki da Abdul Win nan ba?"

Nuratu ta ce"Mama ni fa wannan Alhajin dole sai dai ya ha?ura".

Mama ta ce"Hmmm! Yaro man kaza, lallai kina da ?arancin hankali Nuratu".

Ana kawo shayin Mama ta Wakko kofi ta haWa mata mai kauri, ta sha, sannan ta ci shawarma guda Waya, ta ba su sauran, kayan shayin da biskit kuma ta Wauka ta tafi Wakinsu, Mama tana cewa ta kwana a nan ta ce a'a.

Ta shiga ta zauna, kawai sai ta fara kuka, ga ta yau za ta kwana ita kaWai babu Mama, wayarta ta yi ?ara, ta duba ta ga Abdul ne, ta Waga a sanyaye, ko gaisawa ba su yi ba ya ce"Nuratu wane ne wanda kuke tsaye Wazu?"

Ta sauke numfashi tana lumshe ido, da tunanin ta inda za ta fara yi masa bayani.

Ya ce"Kar ki yi mini ?arya".

Ta ce"Wani ne, sunan shi Alhaji Hashimu, yana sona ne, ya fara zuwa sati biyu da suka wuce..."

Ya katse ta da faWin"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un!" Sai ya kashe kiran ba tare da ya ce komai ba.

Ta bi wayar da kallo, ta so ya tsaya ta ?arasa, ta yadda za su fahimci juna, dama ta sani za a yi hakan, ga shi ba ta da katin kiran wata ?asar, sai ta kunna data, ta kuwa ganshi online, ta yi masa voice ta faWa masa komai tun farkon haWuwarsu, ya duba bai ba ta amsa ba, ta yi ta jira har ta gaji, ta kashe data, ta saka sakata a Wakin ta kwanta, tana jin wani abu mai kama da tsoro tare da kewar mahaifiyarta, sai ta kasa baccin, sai hawaye da suka ?i tsaya mata.

Haka ta yi bacci rabi da rabi, saboda kewar mahaifiyarta. Da asuba bayan ta idar da sallah ta kunna data, duk yawan sa?onnin da suke tururuwar shigowa na Abdul kawai ta kai hannu ta buWe, "Ba zan fahimce ki ba Nuratu sai na kammala bincike a kanku. Fatana dai kar ki manta da al?awarinmu, ke kaWai ce macen da nake ?auna da fatan aurenta duk duniya Nuratu, kar ki butulce mini". Abin da ya rubuto mata kenan, a maimakon ta ji daWi irin yadda ta saba a yau sai zuciyarta ta yi rauni, ta fara hawaye.

Ta koma ta kwanta tana jin yadda gidan nasu ya kaure da hayaniya, da alama har kowa ya cigaba da sana'arsa kenan, kwana Waya bayan mutuwar mahaifiyarta, kodayake idan ba su cigaba da nema ba, waye zai ba su abin da za su ci?

Sai a lokacin ta Wan samu bacci ya Wauke ta sama-sama, Mama Karime ce ta shigo ta tashe ta, ta tashi zaune tana gaishe ta, Mama ta amsa tana cewa"Sannu Nuratu, kin karya?"

Ta girgiza mata kai alamar a'a. Mama ta ce"Fito ki karSi koko da fanke ga shi na rage miki".

Ta ce"Idan da ruwan shayi dai zan karSa". Ta tashi ta bi bayanta, tana jin yadda sanyi yake ratsa ta, saboda zazzaSin da yake jikinta.

?an'uwa da ma?ota WaiWai ana ta shigowa ana yi mata gaisuwa, daidai lokacin Abdul ya kira ta, ta faWa masa zazzaSi take yi, ya ce zai turo abokinsa ya Wauke ta su tafi asibiti, ta ce a'a ya bar shi, ya ce to zai turo Isa ya duba ta, Isa shi ma abokinsa ne, yana da chamest a ?asan layinsu, ta ce kawai ya bar shi za ta sayi maganin

2 / 41