AJIYA A DUHU BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   62 / 77

183K to 186K   out of 230.9K words

  “Wai shi wannan tagumin na miye Baby? Ba komai ya wuce ba”. Fawzan ya faɗa yana kallon Nibras. A hankali ta janye tagumin da tayi, tare da sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ta matsa ta kwanta a jikinsa kanta a saman ƙirjinsa. Ji take inama a jikin AA take haka.
    “Jaan”.
Ta kira Fawzan ɗin da sunan da take kiransa. Amsa mata yay idanunsa a lumshe yana shafa bayanta.
        “Dan ALLAH ka kira Yaya AA a waya mana na ƙara bashi haƙuri. Kar yay barci da fushina”.
     Ɗan jimm Fawzan yayi kafin ya buɗe idanunsa a kanta. Duk da maganar tata tayi masa wani banbarakwai sai ya daure ya ce, “Nibras na faɗa miki zai huce. Kema kin san halin Auta ai. Yana da zafi amma baida riƙo. Zuwa safe normal zaki ganshi kamar komai bai faru ba. Amma duk kinbi kin damu kanki. Please ajiye batun wani Auta a gefe zo kiga na nuna miki wani abu”. Bai bata damar magana ba ya haɗe lips ɗinsu waje guda. Kicin-kicin turesa ta shiga yi, sai dai bai mata da wasa ba. Dan in dai wannan wahalar ce ya saba sha a wajen Nibras a duk lokacin da yake buƙatar hakkinsa. Kuma a farkon aurensu ba haka take masa ba. Daga baya ne dai matsalar tasu ta fara. Sai sun sha uban daru wani lokacin ma ya nuna mata ƙarfi sannan. Amma bai taɓa faɗama kowa hakan ba saboda Fawzan akwai haƙuri. Ta ɓangaren zurfin ciki kuwa shi da AA suna kamancece niya..
      Koda suka gama dai-daita tashi tai ta bar masa ɗakin. Da kallo kawai ya bita, zuciyarsa dai sai son kawo masa wani tunani take yana turewa. Daga ƙarshe ya miƙe ya shiga bathroom domin tsarkake kansa.....

________★

      Washe gari suna breakfast a sashin Oum kowanne cikin shirin tafiya office RK ya sanar ma Oum batun zuwa Kano da yake son yi da kuma abinda zai kaisan. Har ga ALLAH sai da gaban Oum ya faɗi ta ɗan dubi sashen da AA yake har tana neman ƙwarewa da shayi. AA ɗin ne cike da dakewa ya miƙa mata ruwa yana mai tsatstsareta da idanunsa da suka ɗan juye..
      (Magana ta ALLAH Uncle RK kana saka Oum da ɗanta a cakwakiya fa🥱 ka kiyaye mu😂🤣🏃🏃.)
Murmushi Oum ta ɗan sakarma AA na yaƙe, tare da sanya masa albarka bayan tasha ruwan. Sai kuma ta maida dubanta ga RK da shima ke mata sannu. Amsa masa tayi tana jinjina kanta. Sai kuma ta maida hankalinta ga abincin tana juya abinda ta ke son faɗa a cikin ranta. Fin mintuna biyu sannan ta ce, “Ita Maanal ɗin ce ta baka dama Rafeeq?”.
       “Eh Aunty, tun kwana biyar ma daya wuce. Jiya kuma muka sake maganar da ita dan nace miki yaje kd. Sai kawai naga nima ya kamata naje su Abbu su san da zancen shi da Baba Sardauna ayi a wuce wajen ko ya kika gani”.
      “Hakan yayi, ALLAH ya zaɓa abinda tafi alkairi.”
     “Amin ya rabbi”.
RK ya faɗa fuska washe da murmushi. Miƙewa AA yay tsam, tare da ɗaukar wayoyinsa. Ɗagowa Oum da RK sukai suna kallonsa. Batare da shi ya yarda ya kallesu ba ya ce, “Oum na wuce office bye”. Sai kuma ya ɗan duƙo ya kama hannunta ya sumbata. Kafin ta samu damar yin magana har ya fice. Murmushi RK yayi da faɗin, “Uhmm Aunty wannan ɗan naki dai sai ke. Ko har yanzu fushin jiyan ne oho masa. Nace ya shirya muje Kanon wai shi Chaina zaije, haka ya balbaleni da bala'i daren jiya laifin matar Fawzan ya koma kaina”.
      Murmushi kawai Oum tayi, “Ya dai faɗa ne kawai. Duka yaushe ya dawo ƙasar ma, balle a yanzu da suke kan project babba a Company.”
        “Nima abinda na gani kenan, amma nasan sa kamar ɗan sama jannati yake ba wahala gantalin ke masa ba. Bara nima naje anata kirana daga asibiti. Komi kenan zan dawo mu sake tattaunawa dai”.
    Kai ta jinjina masa tare da addu'ar fatan alkairi. Ya amsa da jin daɗi yana mai ficewa. Dan bayan uwa da uba a duniya ƴar uwar tasa da mijinta sune na biyu da yake matuƙar so da girmamawa. Yana musu kallon iyaye na biyu a rayuwarsa ne duk da suna amsa sunan yayu ne......

      Wani irin gajiyayyen numfashi Oum ta sauke bayan fitar RK, sai kuma ta ajiye cokalin hannunta ta dafe kanta da taji yana mata nauyi. A hankali Abah dake kallonta ya kai hannu ya taɓata, firgigit ta dawo hanyyacinta, sai kuma ta zuba masa ido kamar yau ne ta fara ganinsa. Zaune ya kai a kusa da ita, tare da jimƙe hannunta cikin nashi sosai, cike da kulawa ya ce, “Fatima na mike damunki haka da irin wannan zurfin tunani? Ko akan Fawzan ɗin ne dai? Dan ALLAH ki kwantar da hankalinki,  jiya fa ina lura dake bakiyi wani barcin kirki ba sam, shin haihuwa bata ALLAH bace ba. Kuma lokaci ne”.
      A hankali hawayen da suka cika mata ido suka shiga silalowa. Sai ta kauda kanta da sauri tana ƙoƙarin sharewa. Fuskar tata ya kamo cikin duka hannayensa, idanunsa cikin nata ya ce, “Zarah na kin san fa damuwar ki na tayar min da hankali, hakama yaranki da zarar sun ganki a damuwa hankalinsu tashi yake yi. Ki duba har na fita na sake dawowa saboda ban gamsu da yanayin dana fita na barki ba”.
           “Kayi haƙuri Zaki na, in sha ALLAHU zan kiyaye. Zan kuma cigaba da musu addu'a su dukansu”.
     “Yauwa haka shine dai-dai, ALLAH yay miki albarka kinji.”.
    “Amin tare da kai kaima da yarana duka”.
    Murmushi ya saki tare da jan hancinta kaɗan ya kashe mata ido ɗaya, ta saki dariya tana mai saka kanta a ƙirjinsa. Shima dariyar yayi yana rungumota. Sun jima a haka kafin ya ɗagota ya fara bata abincin a baki cike da kulawa.
          “Gadanga!”.
      “Uhmyim Fateeman Gadanga minene?”.
     “Ajwaad da Rafeeq”.
“Miya samu Ajwaad da Rafeeq ɗin?”.
Sai da taja numfashi mai nauyi sannan ta ce, “Rafeeq ne yake cigaba da damuna akan aurensa da Maanal.”
         Ɗan tsai Abah yay yana kallonta, sai kuma ya sauke numfashi shima yana mai furzar da iska. “To ni Fateema mi kike so nayi? Yaron kin nan ya cika murɗi. Tunda shi taurin kai ne aikinsa basai a bar Rafeeq ɗin ya aureta ba. Ni zanyi farin ciki da hakan, dan har cikin raina ina ƙaunar Yarinyar nan, har gobe tana a raina wlhy, zan so ta kasance a cikin zuri'ar nan tamu”.........✍️




09032345899





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖8️⃣3️⃣


______________


........“Humm amma Gadanga kasan Auta na matuƙar son Maanal. Ka duba al'amarin nan, kada mu biye ta nashi zurfin ciki ne kawai ke damunsa. Ka duba yanda bayan samun lafiyarsa ya shiryo yazo ƙasar nan yayta wahalar nemanta, duk da bai fito ya faɗa mana ba ai munji a majiya mai ƙarfi akan ƙoƙarin sa.”
       “Amma yanzu daya gantan wane mataki ya ɗauka?. Tunda kika bani labarin komai ai na sanya ido a kansa, amma ban taɓa ganin wani yunƙurinsa ba, ko gidan Shahidah bai taɓa zuwa ba sai dai su haɗu a wajen aiki. Ni kuma ba zanje nema a bashi auren yarinyata dole ba. Itama sai ta zaɓa ta darje. Idan kuma har Rafeeq ya mata zan tsaya tsayin daga na mata auren gata, shiyyasa ma ranar juma'a ɗin nan zamuje Kaduna ɗin. Mijin Asiyan na aurar da ɗa kuma ya gayyaceni, sai muyi amfani da wannan damar muje gareta duk da ina jin matuƙar kunya wlhy”.
      Fuska sosai Oum ta ɓata tana kallon Abah. Idonta cike da ƙwalla ta ce, “Amma ya kamata ku mana uziri, ku fahimci Ajwaad, sannan ita kanta Maanal tana son shi ai, ka zauna da shi kuma zakaji ta bakinsa. Zuwa Kaduna kuma ALLAH nima kunyar sake haɗuwa da Asiya nake yi, shiyyasa naketa tufka da warwarar tunkararta. Dama Majdiya ta faɗa min zancen bikin. Amma dan ALLAH ka duba al'amarin nan na Ajwaad a sassauta masa”.
         “Ai in dai bashi ne ya kawo min zancen ba bai isa na masa ba. Kema kuma ban yarda ki saka shi ya min ba. Ki barsa ya mangantu a karan kansa ni naga ƙarshem miskilanci.”
    “Amma Gadanga.......”
  Kai ya girgiza mata tare da ɗaura yatsarsa akan lips ɗinta. Idanunsa a cikin nata ya ce, “Please Fateema ki fahimceni, in dai maganar Ajwaad ce na gama ta a gidan nan. Zuwa Kaduna kuma ku shirya ku duka zamu je”.
       “Na fahimceka, amma hukuncin ya mana nauyi a sassauta mana”.
    “Sassaucin a hannunku yake ai. Sai dai ina sake gargaɗi bana buƙatar fargarwa daga gareki a kansa.”
    Rasama abin cewa Oum tayi, sai kawai ta zubama Abah daya miƙe ido. Sallama ya mata ya fice yana sanar mata ya koma wajen aiki...

    Da sauri Saheeba tabar kitchen ɗin Oum ɗin ta baya, da alama duk tattaunawar Abah da Oum a kunnenta ne. Kai tun zaman RK da AA ma tana a sashen. Ta shigo ne wai zata amsarwa su Naufal abinci dan ita yau ta makara da girki, masu aikin sashen Mamy kuwa ba wani iya abinci sukai ba, ita ko Oum da kanta take girki bata saka masu aiki. Shine taci karo da hirar RK da Oum. Mai aikin Oum ta bama abincin su Anum tace ta kai musu, idan kuma takai kada ta dawo kitchen ɗin sai ta kirata. Shine ta laɓe tana saurare. Bayan fitar RK harta fito sai ta hangi Abah daya dawo, shine itama ta dawo da sauri ta sake laɓewa taji komai nan ma.
      Da sassarfa ta isa sashen Mamy, masu aiki ne keta faman gyara, ganin bata a ƙasa ta haye sama nemanta. Acan kuwa ta sameta zaune a dining zata karya. Zama tayi itama a saman dining ɗin ta gaisheta. Mamyn ta amsa tana kallonta, dan yanayinta ya nuna da zance tazo. Saheeba kuwa ta cigaba da faɗin, “Humm Mamy da ga sashen matar can nake. Yau dai mun sami tabbacin itace ta dawo da yarinyar nan rayuwar Ajwaad. Tana can tana tsara Abah akan Ajwaad ya auri yarinyar shi kuma yana botsare mata. Wai ashe kin san bayan samun lafiyar Ajwaad tafiyar da yace zai yi ɗin nan ya barmu a can Nigeria yazo neman yarinyar nan”.
“Nigeria?”.
“Wlhy kuwa Mamy nan yazo ya dinga nemanta lungu da saƙo. Ni wlhy yanzu ma wani tunani yazo min, wai minene ma'anar sunan kamfaninsa na agogo?”.
Tsai Mamy tai tana kallon Saheeba zuciyarta na wani kalar tsaitsinkewa. Sai kuma a hankali ta girgiza kanta. “Ban sani ba Saheeba. Ban kuma taɓa maida hankali akan na sani ba. Wani abu su Fateeman sukace akan sunan kamfanin?”.
“A'a, basu ce komai ba. Nice dai nayi tunanin yanzu.”
Ture plate ɗin abincin Mamy tai gefe, batare data sake cema Saheeba komai ba ta miƙe. Bedroom ta nufa, hakan yasa Saheeba rakata da idanu tana wani ƙyaƙyƙyafta su. Sai kuma ta miƙe tana murmushi. Sashenta ta nufa. Tana zuwa tai kiran uwarta a waya ta zayyane mata komai. Daga can mamanta tai ƴar dariya da faɗin, “Kai Saheeba ALLAH ya shirya min ke. Yanzu to mi tace?”.
“Tashi tai ta shige ɗaki Umma. Wlhy na fahimci idan ba wuta-wuta mukai mataba yanzu zata canja ra'ayinta ne akan auren Nuratu da Ajwaad maƙiya sumana dariya. Kin dai ji abinda malam ya faɗa ai yarinyar can Huznah take komi shegiya ita da uwarta ba zaune suke ba. Ga kuma wannan maƙallaiyar mayyar Maanal ɗin da danginta, munafukar can kuma ta ɗaure musu ƙugu, idan ba munafunci ba ta bari ƙanin nata ya auri yarinyar mana ba sai suje suyi zumuncin ba da ƙyau”
“Ke ko tayi haka tunda tasan burin yarinyar da iyayenta cin dukiya ne, ai gara aci wadda ba tasu ba. Ta ƙaninta kuwa aita ubansu ce akwai gadonta a ciki. Ai Yaya Kamila ta tafka babban kuskure a rayuwarta wlhy da gyarashi sai dai ALLAH kawai. Yoni ina zan iya mallakama kishiya ƴaƴana dan neman wata soyayyar mijin banza can. Gashi nan har yanzu bata sami yanda take so a mijin ba ƴaƴa kuma sun nuna basu santa ba”.
“Ai Umma sai ma kina gidan nan zakiga ikon ALLAH. Jiya dai mai aikina ke faɗa min rigima Fawzan yasha da wacan sakaran. Ban dai gane kan zancen ba sai na bincika dan wai har ga haɗa kaya zata bar gidan ita Mamyn ta hanata, a sashen uwar tasu akai shari'ar, taga kuma Ajwaad ɗin ya fito a fusace”.
“Hummm ita wannan gaɓuwar ai ban san irinta ita da uwarta ba. Kamila ce bata jin shawara, amma sai da aka faɗa mana yarinyar sakarai ce gata da boko sun maidata shashasha amma tace zata bari ai. ALLAH ya ƙara suyita yi mu ƴan kallo ne”.
“Wlhy kuwa Umma. Bara naje anjima zan kiraki”.
“To shike nan sai na jiki”......


     ___________★

        Tun daga gate kowa ke faman bin motar da kallo. Bawai dan basu san motar ba ne. A'a kowa ai yasan ta boss ce. Dan mota ce fitacciya kasancewar irinta a Abujar kaɗan ce ma, ba kuma ko yaushe yake hawanta ba shi kansa. To amma boss kusan mintunansa goma da isowa tuni ma har ya shige office. Mamakin waye kuma ya zo da motar a yanzu ya sakasu binta da kallon ƙurulla. Guri Manaal ta samu tai parking a parking space ɗin da boss ne kawai ke ajiye motarsa. Batai mamakin ganin motarsa a fake ba, dan tasan ya isa shigowa, saboda ita ta ɗan makara yau ɗin. Fitowar ta a motar yasa kallo ya koma sama ga kowa. Tayi ƙyau sosai cikin riga bubu ta lass ruwan toka da ratsin orange, sai ƙaramin veil shima orange data yana a kanta. Fuskarta tayi wani irin fayau saboda ƙitson da tasha jiya. Yanda ɗaurin nata ya ɗan zama baya kamar ta saka hula ya bayyana kitson kaɗan. Ga ƙamshinta mai sanyi na tashi da har sai ka kasance a kusa da ita gab zaka ma iya jinsa. Kamar yanda ta saba duk wanda ta haɗu da shi takan gaisheshi ta wuce abinta, yayinda su kuma suka fara ƙusƙus na gulma akan ganin ta a motar boss. A Maimakon Office ɗinsu kai tsaye sama ta nufa, bayan ta shiga cikin elevator ta gaisa da wanda ta samu ciki kasancewarsu manyan ta.
         Yanda AS ya wani gaisheta kafin ita ta gaisheshi yaso bata mamaki, amma sai ya dake ta amsa masa tare da ajiye key ɗin hannunta a gabansa. A taƙaice ta ce, “Kaba boss”. Kafin ya ce komai ta juya abinta ta fice. Da kallo AS ya bita, tabbas yasha ganin ƴammata ƙyawawa masu ji da kansu suna zarya a companyn nan saboda boss, kuma yasha ji a ransa sun dace da shi, amma magana ta ALLAH shi da kansa ya yarda yarinyar nan ta musamman ce, irin musamman ɗin da komai nata yay dai-dai da boss. Inama ace zai so ta. Hummm ALLAH sai yafi kowa murna. Da wannan tunanin ya miƙe tare da ɗaukar key ɗin ya nufi CEO office ɗin. Sai da yay knocking aka bashi damar shiga sannan. Kamar kullum sarakin na zaune cikin kujerar office. Baƙaƙen suit ɗin jikinsa sun wani sake ƙawata cikar kamalarsa, yanda yay busy sosai zaka san aikin gabansa mai muhimmanci ne matuƙa. Dan ko ɗagowa ya kalla AS bai ba. Kansa a duƙen ya furta, “Lafiya dai Ahmad?”.
      “Eh lafiya Lau sir, dama Sister Maanal ce ta kawo key wai a baka”.
    Cak ya tsaya daga aikin da yake yi, kafin ya ɗago manyan fararen oily idanunsa gently ya saukesu a kan AS. Dole AS ya rissinar da nasa, dan kallon ya masa nauyi da yawa. Shima AA ɗin sai ya janye nasan ya maida ga aikinsa.
                “Ita bata san hanya bane zata aiko ka? Ka maida mata ta kawo da kanta”.
    Murmushi ne ya so kufcema AS, amma ya dannesa da ƙyar. Cike da girmamawa ya ce, “Okay sir, na barka lafiya”. Daga haka ya juya ya fita. Ɗagowa AA yay ya ɗan zubama ƙofar ido, sai kuma ya shafi ƙasumbarsa ka ɗan ya sake maida hankalinsa kan aikinsa....

       _________★

    Zaune take tana aiki ita da Yaqub daya jawo kujerarsa kusa da ita, nuna mata wasu abubuwa yake da take neman ilimi a kansu a cikin computer ɗinta. Yayinda munafukan nasu su Deeni ke faman zinɗensu da baki. Sai da AS yay knocking duk suka ɗago, batare da ya jira umarninsu ba ya turo glass door ɗin ya shigo. Kai tsaye ya wuce inda Maanal ɗin take bayan ya musu gaisuwar gaba ɗaya. Murmushi ya ɗanyi tare da ajiye mata key ɗin a gabanta da ƙaramar takarda daya rubuta abinda boss ɗin ya faɗa, dan haka kawai yaji shi kam bazai iya maimaita mata da bakinsa ba. Kallon key ɗin Maanal dake binsa da kallo tayi, sai kuma ta sake maida idanunta a kansa. Takardar AS ya nuna mata kawai, batare da yace komai ba ya juya ya fita. Suko duk suka rakashi da idanu, sai kuma suka dawo da dubansu ga Maanal ɗin data basar kamar komai ma

62 / 77