Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
cika da soyayya ta… na gani, na ji. Zuciyata ta ce haka. Amma me ya sa yake ƙoƙarin nuna babu ni a ransa?”
Ta hura iska mai zafi, idonta ya ɗan kaɗa da hawaye.
“Wannan sabon ma'aikacin fa?, Zayd… yana ƙirana da pretty kamar yana wasa... Bai san darajar sunan pretty a zuciyar Maleekh ba. Sunan da nake adanawa cikin zuciyata a matsayin sirri na soyayya. Amma yanzu? Zai zama abin dariya ne? Maleekh ya ji? Ya ji ana ƙirana da pretty? Ya ji, na san ya ji… amma bai ce komai ba. Shiru ya fi komai ciwo.”
Ta girgiza kanta da sauri tana ƙoƙarin daurewa...zuciyarta ne ya fara magana da cewa:
“Amal, ki nutsu. Wannan company aikin ki ne, ba wurin soyayya ba. Ki bar komai ga Allah.”
Sai ta ɗaga idonta, ta share hawayen da ya fito.
Sai dai duk da haka, zuciyarta na ci gaba da bugawa da irin ƙarfi da ta fi jurewa… saboda har yanzu Maleekh ne kaɗai burinta da farin cikinta...
Suna shigowa bakin ƙofar falo Farha ta nufo su da murmushi a fuskarta. Tana sanye cikin doguwar riga mai walƙiya, ta riƙe jakarta kamar wacce ta fito daga party. Da zarar ta hango Maleekh, ta miƙe da sauri ta tareshi, tana gyara gaban rigarsa tana cewa:
"Sannu da dawowa Ya Maleekh, Allah ya ƙara lafiya."
Maleekh ya ɗan ja gefe yana ƙoƙarin kaucewa hannunta, cikin dannewar takaicin da ke cinsa. Duk da haka, ya daure fuskarsa saboda yana jin nauyin yayanta Zayd, wanda ke tsaye a gefensa yana kallon komai.
Zayd ya zaro ido tare da dariya ya ce:
"Uhmm, soyayya kenan fa ta tashi. To Yaya Maleekh, kai dai ka ce zaka jira fiancé ɗinka?.."
Sai ya ɗan buga kafaɗar Maleekh cikin zolaya.
Farha ta yi wani irin kallo, idonta ya ƙanƙance kamar za ta cinye shi. Ta ce cikin tsawa:
"Haba Yaya! Wace fiancé kuma? Karka yi wasa da irin wannan magana a gabana fa!"
Zayd ya yi dariya ya ɗaga hannunsa:
"Ooops, sorry sorry sorry my sweet sis. Na manta baki son irin wannan zolayar… Amma albishirinki.."
Farha ta ɗan sassauta fuska, tana jinjina kai cikin jin daɗi:
"Goro fari tasss, albishir ɗin me?"
Zayd ya zaro idanu tare da murmushi mai ɗauke da annashuwa:
"Nayi gamo da wata pretty, Farha! Wallahi in kin ganta kamar aljana tsabar kyau. Kin san irin kyawun ‘yan India? To, ta wuce su gaba ɗaya."
Ya yi ƙaramar shiru kamar yana sake jin yadda Amal ta tsaya a gabansa a reception.
Maleekh kuwa ya tsaya daga gefe yana kallonsa da idon da ke iya fashewa da wuta, amma ya danne komai, ya wuce da sauri ya haura sama part ɗinsa bayan ya yi gaisuwa da Ammy.
Ƙannensa suka taru da murmushi suna yi masa sannu da zuwa, amma zuciyar Maleekh babu inda take sai a wajen Amal da kalaman Zayd.
Ammy kuwa, jin daɗin hirar ya ɓace mata, zuciyarta ta tsinke da sauri. Ta kalli Islam da ke gefenta, tana murmushi amma a zuciyarta tana tunanin:
"Wayyo Allah, wannan labarin 'pretty' bai yi min daɗi ba. Ni dai burina Islam ta zauna da Zayd, amma idan aka ce ya kama wata daban fa?.. Hmm…"
A gefe kuma, Farha ta tattara baƙin cikin rashin jin daɗi, ta kalli Zayd da harara:
"Yaya, wai ka haɗu da wata kuma?.."
Zayd ya ɗan yi dariya mai sauti yana ɗaga hannunsa sama kamar mai rantsuwa:
"Eh mana, ba wasa nake ba. In kin ganta kin ga kamar aljanar gaske ce ta bayyana.. Wallahi pretty ce, Farha."
Farha ta ce tana haɗa rai:
"Kai dai kawai, zan ga yadda wannan maganar ka zata ƙare."...
Farha ta juyo tana kallon Ammy domin suna son haɗa soyayyar Zayd da Islam.
Duk da Islam bata jin wani soyayya a ranta kuma bata san ana wannan haɗin ba...
(To pah Farha, kema yaushe soyayyarki ta settling balle ku seta soyayyar wasu 🤣🤣, Su Hajiya Ammy da duk kan alamu fa Zayd ya fiki bariki..😅😅..)..
To masu karatu sai NEXTTT...
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 47 to 48
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Maleekh ne ya rufe ƙofar ɗakinsa a hankali, ya jingina bayansa da ƙofar yana riƙe da kirjinsa da hannayensa biyu. Numfashinsa ya ɗauki nauyi, zuciyarsa na bugawa kamar ƙarar gangar yaƙi.
Ya taka a hankali zuwa jikin gilasan window, ya zuba ido waje yana kallon sararin sama. Fitilun gari suna walƙiya amma idanunsa sun rufe da hazo na baƙin ciki.
A zuciyarsa ya ce:
"Zayd… pretty… Amal. Wannan sunan har yanzu ba ya barin kunnena. Ashe ita ce wacce ya haɗu da ita? Ita ce yake cewa kamar aljana tsabar kyau?.."
Ya girgiza kai da ƙarfi, yana ƙoƙarin danne hawayen da suka cika idanuwansa.
"Ni na furta mata bana sonta, na koreta daga rayuwata… Amma yau zuciyata ta tabbatar min ban taɓa son kowa irin ta ba. Duk da na yi ƙoƙari in kore ta daga zuciyata, amma ganin Zayd yana kiranta da pretty… Ya Allah, yaushe wannan ciwon zai daina cin raina?.."
Ya tafi ya zauna a gefen gado, ya jingina kansa da tafukan hannunsa, yana ƙoƙarin hana hawayen sauƙa. Amma hawayen ya ƙi tsayawa, ya gangaro yana shigar masa da zafi kamar wuta.
A wancan lokacin, ƙarar dariyar Zayd daga ƙasa ta sake taso masa a kunne, kamar an kunna masa kaset. Wannan dariyar ta cika masa zuciya da kishi da ɓacin rai.
Sai kawai ya daki tebur da ƙarfi, ya furta a hankali cikin rawar murya:
"Amal… pretty ɗin Zayd… wallahi wannan abu ba zai yiwu ba."
Washe gari tun safe, babban harabar CashTalk Empire Holdings ta cika da ɗaukakar jama’a. An kawata wurin da flowers masu kyau, ana kunna kiɗa mai laushi a gefe. Fitilun gilasa na haskawa suna ba da hoton kamfani mai ƙima da daraja.
Manyan baƙi daga ƙasashen waje sun iso cikin manyan motoci masu sheƙi. Ana tare su da farin cikin manyan jami’an company.
Maleekh ya fito cikin suit baƙi da red tie da ya kara masa ƙwarin girmamawa. Fuskarshi cike take da kalar nutsuwa, ko da zuciyarsa na tafasa, bai bari kowa ya hango hakan ba.
A gefe kuwa Amal ce ta biyo shi, sanye da skirt suit navy blue mai matuƙar kyau. A daidai wannan rana dukkan ma’aikata sun tabbatar da cewa ta cancanci matsayinta na assistant CEO. Duk da kalar gajiya a idanunta, kwarjini da kyan tafiyarta ya zame musu abin sha’awa.
Zayd kuma cikin farin ciki yake ta shawagi a wajen, yana ɗan tsokanar Amal cikin sirrin murya:
“Pretty, idan kika tsaya gefe, to kowa zai ce kina ɗauke da kyakkyawar kwalliya fiye da CEO ɗin kansa. Kar ki barni na rikice.”
Amal ta dube shi da idanu masu sanyi, ta ɗan harare shi a hankali, sannan ta matsa gefe. Amma duk wanda ya kalla ya fahimci ba ta ɗaukar abin da yake cewa da muhimmanci.
Maleekh da kansa ya gabatar da su a gaban baƙi:
“Wannan ita ce Assistant CEO, Amal Abdulsamaad, tana kula da aikace-aikacen da ke hannun shugabanci... Wannan kuwa shine younger brother ɗina, Zayd, wanda ya dawo domin cigaba da aiki tare da mu a nan company. .”
Baƙin suka yi mamaki da yabawa. Wani daga cikin su ya ce:
“Wannan company tana da hazikan matasa. It’s a pride to invest here.”
Ana haka aka shiga babban hall ɗin taro. Tables sun jera, projectors suna nuna hotuna da bayanan nasarorin company. Maleekh ya tsaya yana gabatar da jawabi cikin harshen Turanci, yana nuna sabbin shirye-shiryen da zasu ƙara bunƙasa hannun jari.
A yayin da yake magana, idanunsa na kai ga Amal a gefe ba tare da kowa ya lura ba. Sai dai kowane lokaci idan ya hango Zayd yana yi mata magana ko murmushi, zuciyarsa ta sake yi masa raɗaɗin kishi.
A ƙarshe bayan an gama taro, baƙin sun tsaya suna tattaunawa da ma’aikata daban-daban. Wani babban baƙo ya matso ya kalli Amal da murmushi sannan ya ce:
“Young lady, you really impressed me. You have a bright future in this industry.”
Amal ta yi murmushi cikin ladabi ta ce:
“Thank you, sir.”
Zayd kuwa yana tsaye a gefenta yana faɗin:
“Of course sir, she is more than just impressive… she is my pretty.”
Baƙon ya yi dariya, ya ɗauki abin a wasa. Amma Maleekh da ke gefe sai ya matse yatsunsa da ƙarfi, yana ɓoye zafin zuciya cikin annashuwa.
An jera baƙi a babban hall, manyan keken Turawa da wasu manyan ‘yan kasuwa daga ƙasar waje suna zaune cikin nutsuwa. An yi musu hidima sosai aka jera musu juice da snacks a kan teburori masu sheƙi.
Sai ga Farha ta shigo. Ta sha kwalliya fiye da yadda aka saba ganin ta, fuska ta cika da powder, jan baki ya ƙara mata ɗaukar ido, riga da siket masu sheƙi sun matse jikinta kamar yadda ta saba. Da sallama ta gaisa da baƙin, ta yi murmushin ƙarfin hali.
Bata tsaya ko ina ba sai ta nufi wurin Maleekh kai tsaye ta zauna a gefensa, har ta riƙe hannunsa a gaban kowa, tana faɗin:
“Na zo duba angona… Ashe kunyi manyan baƙi.”
Maleekh ransa ya yi wani irin mummunan ɓaci.. Fuskarshi ta ɗan canza amma sai ya daure saboda girman taron da kuma irin mutanen da ke wajen. Ya ƙanƙance idanu yana tambayarta da ƙarfi cikin nutsuwa:
“Me yasa zaki zauna kusa da ni a gaban mutane?…”
Farha ta ƙyalƙyale da dariya ta ce:
“Oh… kana so mu zauna kusa da juna a bayan fage ne? Don mutane kada su ganmu?”
Sai ya yi mata duba mai cike da haushi, ya ce cikin jin zafi:
“Wannan wani irin rashin hankali ne?”
Sai wani ɗan kasuwa Bature ya dube su, ya ce da farin ciki cikin Turanci:
“Wow! This must be your wife-to-be. Congratulations, Mr. Maleekh!”
Farha ta yi murmushi tana washe haƙora, ta ce cikin harshen Turanci da ɗan izza:
“Yes… yes, I am his wife-to-be. Don’t we look perfect together?”
Kowa ya ɗan yi dariyar siyasa kawai, amma Amal da ke gefe zuciyarta kamar za ta fashe saboda kishi. Ta ji kamar ta miƙe ta gudu, amma ta daure ta cigaba da zama da kyan halinta.
Sai ga Farha ta juya tana nuna Amal da yatsa a gaban baƙi:
“Please… kawo mana coffee ni da mijina.”
Maleekh ya dubeta da tsananin takaici. Sai ya ce:
“Farha, wannan fa assistant ɗina ce, ba ‘yar aiki ba.”
Farha ta kankance ido ta ce cikin raini:
“Assistant ɗinka ce to… ai mai yi maka aiki ce. Don haka ita taje ta haɗa.”
Baƙin suka kalli juna cikin ɗan mamaki.
Maleekh ya yi shiru, zuciyarsa cike da tsawa amma saboda girman taron sai ya ce a hankali:
“Ki je, tana son coffee.”
Amal ta yi masa kallon da ya haɗa da zafi da kishi, ta ɗan harare shi kafin ta miƙe.
Tana fita can kitchen na company ɗin, sai ga Zayd ya biyo bayanta da murmushi, yana ƙara tsokanar ta:
“Pretty… ke za ki haɗa coffee? Wani kamfani na duniya zai yi sa’a idan ya samu irin assistant kamar ki. Bari na taimaka miki…”
Duk da ta ƙi kula shi, sai ya rinƙa ɗan taya ta surutun ban dariya har suka haɗa coffee ɗin...
Bayan Amal ta dawo, tana riƙe da tray ɗin tana tafiya a hankali ta miƙa kofin farko ga Maleekh. Shi kansa sai ya yi shiru yana kallonta kafin ya ɗauka. Sai ta miƙa na biyu ga Farha.
Cikin mugunta Farha ta ɗauki kofin da zafi sosai da ta girgiza shi, sannan ta watsa tafasasshen ruwan coffee a kan hannun Amal!
Amal ta saki wani irin ƙara mai tsuma rai, ta jefar da tray ɗin a ƙasi..
A zabure Maleekh ya miƙe daga kujera kamar wanda aka cusa masa wuta. Zuciyarsa ta tsaya cak. Yana faɗin:
“Amallll!”
Ya riƙo hannunta da sauri, ya shiga hura mata iska daga bakinsa, yana shasshafa hannun cikin firgici kamar shi aka zuba wa ruwan zafi.
Gaba ɗaya ya manta wurin cike yake da mutane! Amal ma ta tsaya kallonsa, zuciyarta na bugu kamar za ta fito daga kirjinta.
Sai bayan ya dawo cikin hankalinsa ya ga irin kallon da kowa ya yi musu, ya ja dogon numfashi. Nan take ya kalli Farha da fuska a haɗe, ya ce cikin tsawa:
“Tashi ki koma gida… PLEASE, ki tafi!”
Farha ta yi wani ɗan murmushi mai cike da raini, ta ɗan harare Amal, amma ganin fushin Maleekh sai ta turo baki ta miƙe.
Sai wani daga cikin manyan baƙi ya tashi ya ce cikin Turanci:
“This is a big mistake… An assistant CEO is not a servant. She should never be humiliated like this. She is equally important in this company.”
Wani Bature ma ya ƙara da cewa:
“If this company respects professionalism, then treat her with dignity. That’s how we trust our investment.”
Gaba ɗaya hall ɗin ya yi shiru. Kowa ya san a ranar Farha ta kunyata kanta, amma Amal ta ƙara girma a idon jama’a.
Maleekh ya dafe kansa da hannunsa ɗaya, yana jin tsantsar kunya da haushi. Amma zuciyarsa na yi masa magana ɗaya:
“Ba zan taɓa bari a ci zarafinki ba, Amal…”
Bayan taron company
Ana waje suna yi wa baƙi bankwana. Zayd yana gefe da Amal, sai ya rinƙa ƙoƙarin jan hirarta.
Zayd yana dariya ya ce:
“Kin ga yau dai kin tabbatar da ni cewa ke pretty ce. Ko mai kika yi, kina da wani irin shine da mutane ke gani. Koda bak’i daga ƙasar waje, sun ga darajar ki. Kin ga kuwa? CEO ma bai iya kare kansa ba, sai dai ya kare ki.”
Amal ta ɗan yi murmushi, ta sunkuyar da kanta cikin kunya sannan ta ce:
“Zayd, don Allah ka daina irin wannan magana. Ai aikinmu ne kawai. Bana son a yi min wata fassara daban.”
Sai Zayd ya girgiza kai da nishadi ya ce:
“Toh ai ni gaskiya nake faɗa miki, kinga CEO Maleekh ya yi break-up da wata, shi ya faɗa min da kansa... "
Amal ta ji maganar kamar an caka mata wuƙa a zuciya. Sai ta yi shiru, ta ƙara ɗauke kai gefe...
Zayd ya ƙara da cewa:
“Kin ga ke kuwa, ke assistant ɗinsa ce kawai, ba komai a tsakaninku, kuma hakan ya fi kyau. Amma gaskiya, wallahi ina son ki san… bana jin zan iya daurewa ba tare da na nuna miki yadda nake ji a raina.”
Ya kalleta da ido. Amal zuciyarta na bugawa, ta ɗauke kai, ta ce cikin rawar murya:
“Zayd, don Allah ka daina irin wannan magana yanzu. Ba lokacin wannan maganar bane, kuma bana son wani abu da zai kawo matsala a wajen aiki.”
Zayd ya yi dariya kaɗan sannan ya ce:
“Shikenan, pretty. Amma ki sani akwai lokacin da zuciyata zata kasa ɓoyewa. Amma a yanzu zan tsaya a gefe, kawai in ta kallonki, in kuma taimakeki. Kin cancanci hakan.”
Ya bar wurin, Amal ta tsaya da wani irin nauyi a ranta, zuciyarta cike da ruɗani.
A gefe kuwa, Maleekh yana tsaye yana kallon su, idonsa cike da wuta, zuciyarsa tana tafarfasa, amma ya ci gaba da riƙe bakinsa..
__________________________________________
Ana zaune a babban parlour na part ɗin Maleekh, Zayd ya zauna a kan kujerar opposite ɗin Maleekh.
Maleekh yana ta duba wasu takardu, yana ƙoƙarin shagala da aiki don kada zuciyarsa ta bayyana.
Zayd yana dariya, hannunsa a kirjinsa ya ce
“Wallahi Bros, kullum idan na ga pretty sai zuciyata ta yi wani irin tsalle. Amma fa akwai ɗan jiji da kai a tare da ita, tana ganin ta fi kowa. Amma ni, Zayd, na san hanyar da zan lallabeta. Just ka tayani jan hankalinta kawai, shege ne ni, ba zata kauce min ba.”
Maleekh ya ɗago kai daga takardunsa, ya kalle shi da ido masu sanyi amma cike da haushi ya ce
“She is my assistant, Zayd. Kaji assistant. Kana so ka nuna mun ban da iko akan assistant ɗina ne? Kana son ta rainani ne a gabanka da kuma a gaban company?”
Zayd ya yi murmushi yana girgiza kai ya ce:
“Oh bros, kai ba ka fahimta ba. Na sanka da son girma. Ni ba wai ina ganin ta raine ka bane, a’a. Ai kai babba ne, CEO ne zata ji maganarka. Amma na rantse maka, pretty zata zama tawa. Ni ba na rasa nasara a rayuwa.”
Ya jingina a kujerar yana nishaɗi.
Maleekh kuwa ya ɗaure fuska, ya jingina da kujerar yana haɗiye zuciyarsa. Idanunsa sun kaɗa sunyi ja saboda ɓacin rai da kishi, amma bai ce komai ba sai kawai ya ce:
“Do whatever you want, Zayd. Amma ka sani… ba kowace hanya ce zata kai ka inda kake son zuwa ba.”
Sai ya miƙe ya nufi ɗaki, ya bar Zayd yana dariya cikin rashin fahimta..
Zayd yana kallon bayansa, yana ɗan ɗaga gira cikin ransa ya ce:
“Hmm… Bross da gaske yana ɗaukar wannan abun da wasa. Amma zan nuna masa cewa pretty ba za ta ƙi Zayd ba.”....
A company, ranar aiki
Amal ta fito daga office ɗinta tana riƙe da takardu, tana tafiya zuwa wajen meeting. Zayd ya hangota daga nesa, da sauri ya taho yana sanye da farin suit, yana riƙe da jakar hannunsa yana murmushi.
Yana ɗan gyara murya ya ce:
“Pretty, ki bari in taimaka miki, kada ki wahalar da kanki da ɗaukar takardu masu nauyi haka.”
Ba tare da ta tsaya ba, Amal ta ce cikin ladabi.
“Thanks, but zan iya kaiwa da kaina.”
Kafin ta ƙarasa maganar, Zayd ya kwace takardun yana cewa:
“Don Allah ki barni, ai wannan aikin ne na wanda yake tare da ke kullum. Kin san ni na rantse sai na sa murmushi a fuskar pretty.”
Ya yi mata wani irin lallausan murmushi, ma’aikatan wurin duk suna kallon su suna jin daɗi, wasu har suna ɗan faɗin:
“Kai wannan sabon ɗan uwan CEO yana da barkwanci.”
Amal ta ɗan yi shiru, tana so ta kaucewa abun, amma ta kasa nuna