*RAYUWAR MACE*      _Hafsat Rano_              Free Page  (1) *******      Sanye take da hijabi ruwan toka dogo har kafarta, kanta a k'asa sanda zata wuce ta daidai majalisar mazan wadda kullum sai ta bi ta wajen idan zata je islamiyya tana kuma jin yadda suke maganar ta a kullum idan tazo wucewa, tun abin na damun ta har ta iiik ya dake makale a kafadarta ta jingine ta a wajen ta nufi dakin nasa kirjin ta n I'm aw dukan uku-uku.     Shi kadai ne a dakin daga gani ya gama shiryawa fita zai kasuwa, tun bayan da manyan yayanta maza suka taso sai ya zama ba kasafai Abban yake fita ba sai ya dau kwanaki yana gida yana hutawa.    "Sannu da hutawa Abba.". Tace tana neman waje ta rabe dan ta riga ta san kwanan zancen, ya kwana biyu be mata maganar ba shiyasa ta dan samu nutsuwa a kwanakin "Yawwa Asma'u, an dawo!?" "Eh Abba." "Toh Madallah, sannu da dawowa." "Yawwa." Ta amsa a ciki tana sake lankwasa kafarta "Kina jina ko,akwai wani da yazo ko kuwa har yanzu dai?" "Babu kowa Abba." Tace a sanyaye dan tuni har yar karamar kwalla ta soma taruwa a idon ta.    Shiru Abban yayi be tanka ba, tamkar me tunanin abinda zai ce, bayan wasu yan dakiku ya kalle ta sannan yace "Ko dai kina korar su ne Ma'u?" Da sauri ta girgiza kai hawayen da take kokarin rikewa suka sakko. Kura mata ido yayi sosai sannan ya soma magana a nutse cikin son kwantar mata da hankali    Kanta a kasa tana jin Abban har ya kai karshe, cikin nutsuwa tayi masa godiya sannan ta mike ta baro dakin zuciyar ta na sake tsinkewa. Idan tace bata damuwa da rashin aure tayi karya. Tafi kowa son ganin tayi auren kamar yadda yake burin duk wasu iyaye da zarar yar su ta kai munzalin aure! Tabbas tasan duk wasu iyaye da yar su ke gaban su basu da kwanciyar hankali har sai sun ga sun aurar da ita gudun magana da abinda ka iya zuwa ya dawo. Amma kuma abu guda da mutane suka kasa ganewa shine, aure, haihuwa da mutuwa duk lokaci ne mutum be isa ya bawa kansa ba idan ba har lokacin ne yayi ba.    Da yan yatsun hannun ta, take kokarin kirga adadin kannenta da akayi wa aure kamar yadda ta saba a kowanne lokaci, ta riga ta san adadin su sai dai kirgawar na sake tabbatar mata da dole ne mahaifin ta ya dinga tunasar da ita a kowanne lokaci. Duk da shekarun ta ba wai sun ja sosai bane dududu a yanzu ne ta cika shekara ashirin da biyar sai dai yanayin yadda ake musu aure da kananun shekaru ya saka ake ganin ta tsofe a gida. Kannenta biyu da akayi wa aure karshe ,shekarar su sha bakwai dan haka idan zaa hada su da me shekara ashirin da biyar toh fa tabbas dole a dinga yi mata kallon taki aure.    Bata san kalar matsalar ta ba, dan ba zata iya tuna lokacin da wani ya tare ta ko a hanya bane. Ta kan zauna tayi ta tunanin ko dai ba zata taba aure ba a rayuwar ta? Kila bata da rabo shiyasa hakan ta kasance dan bata zargin kowa balle tace ko wani abu akayi mata. Ta bar hakan a matsayin wata jarrabawa ce a gareta wanda take fatan cinye wa.    Daga labulen dakin Ummah tayi, ta leko da kanta tana karantar yanayin ta kafin tace “Ya kamata a dora girkin rana lokaci yana tafiya kafin yan makaranta su dawo." Da toh ta amsa ta mike, ta chanja kayanta zuwa karamar riga da skirt ta saka hula a kanta ta nufi kitchen rik'e da wayar ta a hannu, tana zuwa ta ajiye a saman cabinet ta dora ruwa a babbar tukunya sannan ta fito da kayan miya daga cikin ledar su ta soma gyarawa.     Maganar Abba taji a tsakar gidan nasu yana yiwa Umma magana akan dalilin dawowar sa bayan fitar sa kenan bata jin ma ya bar layin nasu "H pollo upar fa mun hau titi sai ga kiran Yaya Asabe wai gasu nan zuwa gidan da wata muhimmiyar magana, dole nace ya juyo my dawo dan bansan wacce magana ce ba." " Gaskiya kam, toh Allah yasa muji alkhair" Umma tace tana bin bayan sa suka shiga falo. Daina aikin gabanta tayi ranta na sake jagulewa jin Hajiya Mama zata zo, Itace mutum ta farko da abban su yake jin maganarta fiye da ta kowa a duniya, duk wani abu da tace masa toh fa an gama shi, ko da kuwa baya so zai amsa mata. Su biyu iyayen su suka haifa itace kuma take masa role din uwa dan tun yana karami iyayensu suka rasu suka barsu su biyu.    Turo gate din gidan yayi daidai da tsayawar bugun zuciyar ta, ta window din kitchen din da hange su suna shigowa ita da shi yana rik'e da handbag dinta ya makala ta a kafadar sa kamar wani mace. Daf da zasu karaso wajen kitchen din tayi saurin dukawa saboda kar su ganta, tana jin sanda Umma ta fito tana musu sannu da zuwa Abba na tsaye daga bakin falon sa fuskar sa na nuna jin dadin ganin Yayar tashi. "Sannun ku da zuwa." Abba da Umma suka dinga jera musu har suka dangana da falon sannan ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta cigaba da aikin ta a nutse.     Tana cikin aikin wayar ta dake sama tayi kara, ta dauraye hannun ta a sink ta jawota tana kallon wayar, kawarta ce Safiyya take kiranta, ta daga tana saka wayar a handsfree ta ajiye ta suka koma magana.    Maganar da yaji ya sakashi dawowa da baya zuwa kitchen din, ya tsaya daga kofar yana kare wa halittar ta kallo wadda take sanye da dogon skirt da riga. Motsi taji, ta waigo sai kawai taga mutum tsaye a bayan ta har ya iso daf da ita yana kokarin taba ta. "Lafiya!?" Tace tana matsawa da sauri har tana neman gogar tukunyar miyar dake saman gas din. "Fine Baby, kin hadu." Yace cikin muryar sa ta yan duniya, kallon sa tayi daga sama har kasa, zuwa kunnensa dake sanye da dankunne sai wani jibgegen takalmi da yake jibge a kafar sa, wandon sa irin wanda yake a yagen nan ne ta tsakiya sai askin kansa da ya kara nuna mata ainihin shi din waye.    Yaya Adam ne, tilon namiji a yaran Hajiya Mama kuma shalelenta, tun suna yara Allah be hada jinin ta da nasa ba dan ko haduwa akayi sai yaci zalinta, ya zage ta yace mata shegiya baka saboda duk yan uwanta sun fita hasken fata. Hannun sa taji a saman fuskar ta yana shafawa, tayi saurin bige shi tana watsa masa mugun kallo. "Menene haka Malam!?" "Comman sai kace wadda bata waye ba, kin ganki kuwa!? Haka kika chanja kamar bake ba." Hararar sa tayi tana sake matsawa baya, dan bata masa kallon me cikakken hankali ko a da ma, balle yanzu da yaje yayi rayuwar turai idon sa ya kara budewa. Hayaniyar dawowar yaran daga school ya bata damar zamewa ta bar kitchen din tayi saurin zuwa daki ta dauko hijab din ta, ta saka sannan ta koma kitchen din, amma sai daga baya nan, tayi kwafa ta cigaba da aikin ta da sauri sauri karma ya dawo ya sake samunta dan ta lura bashi da kunya sam.    Fasa fita yayi wajen ya koma falon da ya baro su Abba yana zuwa zai shiga yaji Hajiya Mama na tambayar Abba akan maganar Asma'u ko har yanzu shiru, amsar da Abban ya bayar ya sakashi saurin fadawa dakin "Uncle ni zan aureta." Duk suka bishi da kallo, "Boy me kace?" Hajiya Mama tace fuskar ta kamar gonar auduga "Yess Mom..." Kallon Abba tayi, wanda shima yake kallon ta a daidai lokacin "Kaji wani abun almara, Ashe Adam ne mijin shiyasa aka ta fama, kai Alhamdulillah nayi farin ciki sosai." Saurin sakin fuskar sa abba yayi duk da be san yadda zai misalta abinda yake ji a lokacin ba, farin ciki ko akasin sa? A zahiri babu abinda yafi so da ji kamar ace Ma'un sa ta samu miji, sai dai kuma be zaci haka ba, sannan be taba kawo mutum kamar Adam din a irin mijin da yake mata shaawa ba, amma kuma ta Yaya zai ki jinin Yaya Asabe!? Matar da ta so shi tamkar yadda uwa ke son dan ta? "Alhamdulillah!." Ya samu kansa da furtawa yana gida kansa duk da be ji abinda Yaya Asaben tace ba. Umma da ta kusan sakin abinda yake hannun ta sanda taji maganar ce ta karaso ta zauna tana kallon Abban amma sam yaki yarda su hada ido ma balle ya gane abinda take so ta nusar dashi. "Allah ya tabbatar mana da alkhairi Yaya." "Amin Ahmadu, sai a saka lokacin kad'an tunda dama abinda muke jira kenan, kaji al'amarin Allah, babu yadda banyi da shi ba akan ya fitar da matar aure tunda ya dawo yaki ashe ashe dai matar sa na nan tana jiran sa." "Haka dama al'amarin Allah yake." Abban ya amsa cikin yak'e, sai ta waiga wajen da Umma ke zaune tace "Sai a fara shirye shirye kawai bilkisu, bari mu wuce dan tun a yau zan fara shiri auren yara biyu." "Haka ne. " Tace itama tana yak'en wanda sarai Hajiya Maman ta ga yadda dukkn su maganar ta dake su amma ya zatayi? Dole ta so abinda danta yake so duk kuwa da bashi ta nagartar da za'a bashi mace amma ai hannun ka baya rubewa ka yanke ka yar dole sune zasu rufa mata asiri.    Duk abinda ake Adam na zaune a wajen sai da Hajiya Maman tace ya tashi su tafi sannan ya mike ransa fes yana haskilo irin hutuwar da zai da yarinyar dan ba k'aramar mace bace.   A harabar tsakar gidan ya tsaya yana sosa keya umma da ta rakosu ta kalle shi tana karewa shigar sa kallo cikin takaici "Mah please bari na dan sake ganin ta, zan same ku a mota." Dariya ta saka ta kai masa duka ya goce, "Mara kunya, tana ina ne bata zo ta gaishe mu ba ma ko bata ji shigowar mu bane?" Katse Maman yayi yace "Ke da zata zo gidan ki gaba daya mah!" "Auw kareta kake kenan, toh ai shikenan." Tace tana cigaba da tafiya "Muna jiran ka a mota." Tace sanda sukayi sallama da Umma ta fita ita kuma ta shigo, ta tarar dashi a tsaye a inda suka barshi. "Bari a kirawo ta." Tace sannan tayi gaba, yayi saurin bin bayanta ganin ta nufi daki, tana shiga shima yana shiga Asma'u dake kwance ta mike da sauri, kafin tayi magana ta hangi mutum a bayan umman yana zuro kansa yana kokarin shigowa dakin da dukkan karfin sa. "Kar a shigo!" Tace da karaji ya tsaya cikin jin tsoro, sai a sannan umma ta san ya biyo ta, ta juya da sauri mamakin rashin kunyar sa na neman kai ta kasa "Kaje falo zata zo." Kawai tace masa cikin takaici, ya juya ba dan ya so ba, ya fita yana taku dai-dai. Girgiza kai Umma tayi cikin tsananin bacin rai tace "Ki je wajen sa a falo bari na samu Abban ku, jinkirin aure ai ba hauka bane da za'a dauki wannan mara tarbiyar a baki, ba zan yarda ba." Sam bata fuskanci in da maganganun  Umman suka dosa ba. "Umma!" "Kiyi abinda nace kawai ba sai ya sake dawowa ba, ki rik'e Areef ku je tare karki je ke kadai." Daga haka ta juya da sauri ta nufi wajen Abban dan a san wacce za'a yi, ta dade da sanin Hajiya Maman bata santa,amma bata san rashin son ya kai haka ba! Rayuwar mace cike take da kalubale mabanbanta! Kaddara ce tsanin duk wata nasarar ta! Ba zata ce ita din rayuwa bata mata adalci ba, sai dai akwai tarin kalubale cike da rayuwar tata, wanda a karshe zata kirasu da matakin dukkan nasarar ta! _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* *RAYUWAR MACE*      _Hafsat Rano_              Free Page  (2) *** A kofar dakin Umma ta tarar dashi, ta nuna masa falon da hannu sannan ta wuce falon Abban. Yana tsaye yana kai kawo a tsakiyar dakin tana shigowa ya bi ta da ido dan yasan abinda ya kawo ta. "Alhaji.." Da sauri ya dakatar da "Maganar ba zata chanja komai ba, muyi mata addu'a kawai bamu san me Allah ya tsara ba." "Amma dai hakkin mu ne mu nema mata miji na gari, wanda muka yarda da addininsa da nagartar sa, amma Adam fa? Ya cika wannan sharadin?" Zama yayi a nutse bayan ya cire babbar rigar jikin sa da hula sannan yace " Mu bar wa Allah komai, ya fimu sanin komai akai, ba zan taba iya hana Yaya Asabe abinda take so ba, ba kuma zan taba kin danta wai don munin halin sa, ni ma ban fi karfin Allah ya jarraba ni da irin sa ba." " Yanzu shikenan muna ji muna gani saboda kawai muna so yar mu tayi aure za muyi mata zabin tumun dare!?" " Idan da rabo sai kiga ta dalilin ta Allah ya shirye shi, sai tayi kokari ta sauya masa DABI'AR sa tunda mace tana da matukar tasiri a rayuwar namiji." Wani abu ne yazo ya tokare wuyan Umman, bata tare da masu ganin cewa mace zata iya gyara wa namiji Hali bayan ta same shi da girman sa, kawai idan kaji an ce haka toh fa lallai an shirya zalintar macen. Tana tsaye ya zo zai fita daga falon, ya kalle ta yana gyara hular kansa sannan yace " Karki nuna mata wani abu da zai sa taki auren, muyi mata addu'a kawai dan babu abinda zai sa a fasa sai dai idan Yaya Asaben da kanta tace sun fasa, amma muddin bata ce ba, toh babu makawa sai anyi." Kasa tanka masa tayi har ya fice, ta zauna dabas a wajen tana jin da gaske an cuce ta, ta kuma tabbatar da biyu Hajiya Maman tayi dan ta nuna mata ta isa da Abban da ma duk wani abu da ya dangance shi.   Da k'yar ta mike daga wajen ta fito bayan ta jawo masa falon, ta isa dakin Asma'un ta tarar da ita tana sallar azahar, sai kawai ta wuce dakin ta domin ta gabatar da tata sallar.    Tana idarwa Asma'un na shigowa, bata ce komai ba ta hau gadon umman ta kwanta rigingine tayi shiru tana tuna abinda ya faru bayan taje wajen sa. Kadan ya rage be rungume ta ba da ta shigo, ya hau surutan da ta kasa gane komai akai, haka ya karaci babatunsa ya tafi bayan yace mata zai dawo da daddare. "Umma wai me ya faru?" "Aina da?" "Ya Adam, ban gane ba wallahi. " " Kinsan kowanne bawa da yadda Allah yake kaddaro masa rayuwar sa, sannan duk dan ta yayi ma iyayen sa biyayya toh fa ba zai taba tabewa ba, mahaifin ki ya yanke shawarar aura miki dan uwanki Adam... " A yadda ta mike daga kwancen sai da ta bawa umman tausayi, " Umma Adam kuma? " Kai ta daga mata " Innalillah wa inna ilaihi rajiun, umma wallahi tallahi bana son shi, bashi da hali me kyau wallahi Umma, wallahi Allah bana son shi dan Allah Abba yayi hakuri. " Duk ta gigice ta rikice, hawayen da Umman take ta rikewa ne suka soma saukowa tayi saurin maida su tana karfafar kanta. " Menene haka? Me kike haka? Ashe ba zaki iya yiwa mahaifin ki biyayya ba?" " Umma Adam fa? Umma dan Allah kice yayi hakuri wallahi ba zan iya ba. " Wani kallo umma ta watsa mata " Ki nutsu ki saurare ni, kinsan waye mahaifin ku, kin kuma san wacece Hajiya Mama a wajen sa, kukan ki da magiyar ki ba zasu taba sauya masa abinda yayi niyya ba sai dai idan su suka ce sun fasa, dan haka ba ruwana wallahi, ba zan bari ki hadu da fushin mahaifin ki ba, kiyi masa biyayya ku rabu lafiya nima na rabu da nawa lafiya, kuma in sha Allah zaki ga ribar biyayya. " Daga haka bata kuma cewa komai ba, ta fice ta bar ta a dakin tana jin yadda take kuka wiwi, wayar ta ta dauka ta kira babbar 'yarta hadiza ta sanar da ita komai sannan ta kira sauran yan uwan Asma'un da sukayi aure, kafin kace me sai gasu a gidan gaba dayan su, duk kansu kowa be ji dadin labarin ba, amma kuma sai Umma ta hana su fuskar da zasu kushe abun dan ta riga tasan halin Abban su sarai zai iya saba musu akan maganar, sannan tunda tasan babu fashi gwara kawai tayi kokarin ganin basu bawa Asma'un kofar da zata bijire wa mahaifin nasu ba.   Lallashi da ban baki suka dinga yi mata har suka samu ta dan nutsu amma bata bar kuka ba. A haka Abban da yan mazan suka dawo suka tarar dasu, Abban ya danyi fadan dalilin zuwan su haka sai suka ce ai zuwa sukayi su gaishe su, ya ji su ne kawai amma ya riga ya san umma ce ta kira su akan maganar.    Bayan sallar magriba Yaya hadiza ta samu Abban da maganar, ya nuna mata babu fashi su dai kawai su tayata da addu'a, haka ta baro dakin jikin ta a sanyaye bayan ta roke shi ya barta su tafi da Asma'un ya amince amma iya sati daya kawai dan sati uku ya saka bikin tunda babu wani shiri da za'a yi dan kowanne bangare a shirye suke dama.    Mijinta ne yazo ya dauke su wajen tara, a hanya take bashi labarin abinda ya faru, ya dan juyo yana sake bawa Asma'un baki yana tsokanar ta, ta dan yi murmushi kawai amma ita kadai ta san yadda take ji a ranta.    ***Washegari bayan an makaranta sun tafi umma ta shirya Abbati ya kaita chan Mandawari gidan su ta samu Hajiyar su da maganar auren Asma'un da lokacin da Abban ya saka, duk basu ji dadin hukuncin Abban ba, da kuma rashin bawa Asma'un dama ta fadi ra'ayin ta dan kawai ana ganin kamar ko an barta ma ba wani ne zaizo neman auren nata ba. "Toh yanzu dai ya riga ya gama yanke hukunci, namu kawai shine mu bi ta da addu'a, Allah ya basu zaman lafiya ya kade fitina." Hajiyan tace bayan sun gama magana da Umman. "Amin, ni na rasa ta ina zan fara ba, sai a aika su miko su sanar da su umman Asiya da su Aunty Falila da gidajen su kawo muntari." "Eh yana shigowa zan aika shi, sati uku kamar yau ne ai, duk sai a sanar da dangi, Allah ya basu zaman lafiya." "Amin." Tace a sanyaye. ***Bangaren gidan Hajiya Mama shiri take na ban mamaki, tuni zancen ya karade dangin su bangaren Abban da kuma bangaren Baban su Adam din, mutane da yawa suna tausayawa Asma'un saboda dai sam babu hali na nagarta da zai saka ka dauki yar ka, ka bawa Adam din, ciki kuwa har da yan uwa makusantan su Abban dan wani kawun su sai da yayi wa Abban magana kasancewar kowa ya riga ya san nutsuwa da kamala irin ta Asma'un dan kaf yan uwanta babu kamarta, duk da su ma basu da matsala amma kuma ita din daban ce, magana da koman ta a nutse take yin sa, bata da rawar kan yan mata dan ba zaka taba tunanin ta je jami'a ba ma, bata dauki duniyar da zafi ba haka kuma bata da son kyale kyalen duniya. Haka ya saka mutane suke ganin kamar akwai zalunci a dauke ta a hada ta da Adam wanda ake tunani hatta giya yana sha bayan mugun halin sa na neman mata da yayi shura akai, amma yadda Abban yayi biris da duk wannan ya saka kowa ya shafa ma kansa lafiya aka shiga bin su da addu'ar fatan alkhairi.   Zuwan Adam din uku tare da zugar abokai baya samun ta karshe dai ranar da yazo ya tarar da Abban nan yake gayawa Abba ai yazo baya samun ta, nan fa Abban ya shiga dakin Umma yayi ta mata fad'a sannan ya dauki waya ya kira Yaya hadizan yace ya fasa sati dayan gobe gobe ta dawo gida. Jiki a sanyaye ta amsa masa da toh, bayan ya kashe sai kuma yaga kamar ya zafafa da yawa, sai ya sake kiranta yace ta kyale ta zuwa satin amma zatayi bako gashi nan zaizo yanzo. Nan ma dai toh din tace ya kashe ya koma ya samu Adam din ya yi masa kwantancen gidan Yaya Hadizan sannan ya bashi number wayar Asma'un da ta Yaya Hadizan yace idan yaje ya kira. Bakin sa tamkar gonar auduga ya karba suka dauki hanyar gidan Yaya Hadizan baka jin komai a motar sa ife ifen su irin ma gogaggun yan duniya, burin sa kawai ya nuna musu kalar matar da zai aura ya san ba karamin taya shi farin ciki zasuyi ba, hutu kam zai huta a wajen sosai, yadda yake ji ma kamar sati ukun yayi masa mugun yawa amma haka zai hakura ya lallaba ya cigaba da maneji da su Fido kafin ranar da zai gwangwaje.   Gidan bashi da wahala suna zuwa suka gane, ya dauko wayar sa zai yi kira sai kuma ya fasa ya fito da kafar sa ya karasa gate din gidan ya kwankwasa da dan karfi saboda karar Gen, be jima yana bugun ba mijin Ya Hadizan yazo ya bud'e masa, ya bashi hannu suka gaisa sannan yace ya shigo ciki "Owk tare muke da guys suna mota bari nayi musu magana." "Owk." Yace ya wuce ciki ya bar musu kofar a bude, ya samu falon ba kowa an gama jera ruwa da lemo akan dan centre table din, ya dauki remote ya rage volume din tv daidai lokacin da suke shigowa, su hudu ne dukkan su sanye da kananan kaya daya ma daga ciki wandon sa da kad'an yafi guiwar sa, askin kansu kuwa kai kace gobara akayi a wani gefen kan nasu babu kyaun gani, hannu ya basu suka gaisa sannan ya wuce ciki cike da al'ajabin dalilin da zai sa Abba amincewa bayan ya san waye Abban da nagartar sa.   Da k'yar da ban baki Ya Hadiza ta sakata fita dan bata son fushin Abba akanta zai iya hadasu daga ita har Asma'un yayi musu tatas. Hijabi ne burmeme a jikinta har kasa, ta dauko facemasks ta dora akan fuskar ta sannan ta tura kofar falon kanta a k'asa ta shiga. Wata iriyar kunya ce ta kama Adam din da ya ganta da shigar, shi da yaso suga kalar matar da zai aura amma shine zata je ta burma uban hijabi kamar wadda zata zaman makoki.   Dariyar shakiyanci suka fara yi suna kallon sa, ya hade rai sosai yaki kallon ta, a k'asa chan ta rakube ta gaishe su suka amsa cikin dariya dan su basu ga  abinda yake ta musu kozozoto akai ba. "Our wife kina lafiya?" Daya daga ciki yace yana kunshe dariyar sa. "Lafiya lou." Ta amsa a takaice kanta still a k'asa ba zata iya cewa ga adadin su bama balle kamar su, uban gayyar kawai ta gani sanda ta shigo taga ya wani diririce kamar wanda yayi karya aka gano shi, bata kuma kallon sa ba ta zauna. Tana jin su suna ta shakiyan ci suna tsokanarshi amma ko uffan be ce musu ba, sai da suka gama suka fita, ya taso yazo daidai kanta, ya saka hannu ya fuzge facemask din, ta kalle shi da sauri "Wannan wane irin wulakanci ne na kawo guys dina su ga matar da zan aura shine zaki sako wannan buhun sannan ki wani toshe fuskar ki dan tsabar iskanci." "Kamar ya? Me yasa zasu ganni ko su din muharramaina ne?" "Shit! A 21th century dama akwai mata villagers irin ki? Ke baki san civilization ba? Ko baki ga alamar mijin da zaki aura wayayye bane?" "Ban san duk wannan ba, abu daya na sani shine abinda addinin musulunci ya koyar dani." Ta murguda masa baki tana jan facemask din zata mayar ya fuzge da karfi sannan ya buge mata baki "Karki yarda kice zaki min rashin kunya wallahi, dan zan taimaka miki na aure ki, naga ma ai neman kai ake dake na taimaka nace zan aura, so watch your mouth wallahi, kuma na sake zuwa kika zumbulo min irin wannan Hijab din sai na cire shi ta karfi wallahi. Nonsense!" Ya juya da sauri ya bar falon har da buga kofa, kasa ko da kwakkwaran motsi tayi, bakin ta da ya buge na mata zafi sosai, sai kuma maganganun sa da suka yi mata mugun ciwo, da gaske taimaka mata yayi? Kuma neman kai ake da ita shine ya tausaya mata zai aure ta. Wani kuka ne yazo mata, ta gwammace ta mutu ba aure akan ta auri mutum irin Adam, jinkirin aure ai ba shine zai saka mutum yayi wrong choice ba, gwara ma ace ka aura baka sani ba, amma wannan kowa ya san halin sa.   Ta jima a wajen tana kuka sosai, kafin ta tashi da k'yar bayan ta goge hawayen ta shiga ciki. RAYUWAR MACE COMMENT GROUP LINK. Meson comment group sai ya shiga link din nan https://chat.whatsapp.com/EcH31iWkbGnD9DWC8SsuL _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* *RAYUWAR MACE* _Hafsat Rano_ Free Page (3) *** Tun da suka dauki hanya suke masa shakiyance be ce dasu uffan ba, ya riga ya san dole suyi yadda ya dinga kuranta musu ita, ba karamin bata masa rai tayi ba ta kuma maida level dinsa baya a cikin abokan sa, ba dan ya kwallafa rai akanta ba babu abinda zai sa ya aureta dan shi baya son mace me duhun kai. Tsaki ya dinga ja har suka zo in da zasu rabu, ya sauke su ya fizgi motar kamar zai tashi sama sai gida.    A falo ya tarar da Hajiyar da tarin akwatunan lefe tare da sisters dinsa su uku da suka je hado kayan, suna zaune suna dubawa ya shigo ransa a bace zai wuce Nadiya ta dakatar dashi "Boy baka gammu bane?" "Na ganku mana." Yace yayi wucewar sa ya haye sama ya barsu da wagaggen baki. "Ina ga dai an batawa boy rai, yadda yake zumudin auren nan ai ya tsaya ya ga komai." " Gaskiya dai, abun ya motsa." Fadila tace tana dariya " Bari naje naji ko menene ya faru." Nabeela ta mike Hajiya ta dakatar da ita "Ku rabu dashi kila shi da abokan sa ne, zai sauko anjima kadan idan ya watsa ruwa." Komawa tayi ta zauna suka cigaba da maganar auren suna hada kayan da lissafin abubuwan da za'a siya kuma, Hajiyar na jin su tana amsa waya akai-akai Adam din ya sauko ya zauna a kusa da Nadeeya ya tankwashe kafar sa yana kallon kayan. "Have a look, kayan wife din ka ne." Dan wara idon sa yayi akan kayan sai kuma ya dauke kai yana kallon Hajiyar "Mah ba zai yiwu a dawo da bikin nan next week ba?" "Next week kuma? Ai kamar yau ne upper week din Adam, hakuri zakayi a samu ayi shirye shiryen komai a nutse." Shiru yayi be sake cewa komai ba, ya ja baya ya jingina da kujera ya ciro wayar sa ya shiga chatting da yan matan sa, hakan ya saka shi manta abinda ya faru, har ya sake suka shiga hira da su kafin su tattara su tafi akan zasu dawo gobe saboda wasu kayan da basu gama siya ba. ***Tsaye Ya Hadiza take a kanta tunda ta shigo take kuka ta ki fad'a mata abinda ya faru, ita kanta ji take kamar tayi kukan dan ta san yanayin da Asma'un take ciki wanda ta taba shiga kusan irin sa Allah ya kiyaye Abba ya sakko aka daidaita, shiyasa take matukar tausayin ta dan mutum irin Adam ace shine mijinka ba karamin tashin hankali bane. "Ki fad'a min abinda ya faru dan Allah, hankali na ba zai kwanta ba kuma wannan kukan sai ya saka miki ciwo." Bayan hannun ta, tasa ta share hawayen sannan ta hau ciro hijab din jikinta saboda zafi da hucin da jikin ta ke fitarwa. Duk Ya Hadizan na tsaye akanta har ta cire ta ninke sannan ta hau kokarin kakalo murmushi ta dora a saman jar fuskar ta. " Wani abu yace miki?" Da ka ta amsa mata tana jin wasu hawayen na neman zubowa. " Karki yarda ki biye wa maganganun sa dan irin Adam xasu iya karar miki da hawayen ki tas babu abinda ya dame su. He's not worth your tears, ki nutsu ki shiga kai wa Allah kukan ki, sai kiga komai yazo da sauki ta inda bamu zata ba." " In sha Allah." Tace tana kwanciya.      Fita Ya Hadizan tayi bayan ta kara bata baki, ta barta tana sakawa da warwarewa, ta riga ta san rayuwar ta tazo karshe, dan tana jin komai zai iya faruwa a zaman ta da mutum kamar Adam, bata san yadda zata kasance ba amma tana da yakinin zaman ba zai taba dadi ba.     Shirye shirye ya kankama sosai a baangarorin biyu, ita Umma dai tana yin komai ne domin ya zama dole amma ba wai don son auren ba, sai dai bata da damar nunawa saboda Asma'un da Abba dan ba zata yarda ta bata kofar da zata bijire wa mahaifin ta ba. Satin ta guda ta dawo gida a lokacin ne aka shiga yi mata yan gyararrakin mata na al'adah duk da ba wani zafafawa akayi ba amma kuma dole dai zaka yi auren 'yarka ka dan tabuka wani abu ko yaya.     Komai baya mata dadi duk abinda ake mata kawai tana bi ne don babu yadda zata yi, saukin ta ma tun da yazo gidan Ya Hadiza be sake dawowa ba, sai magana da yayi mata a whatspp akan abinda take bukata tace babu, sai missed video calls dinsa da ta gani sau biyu bata bi ba, shikenan shima be sake bin kanta ba dama Nadeeya ce tace masa ana tambaya shiyasa ma ya tambaye ta, abinda tayi masa ranar yayi masifar bata masa rai shiyasa ya tattara ya watsar da ita ya cigaba da shirye shiryen sa dan babu fashi a auren dan yadda yake ji idan be aure ta ba akwai matsala.   Saura sati daya bikin suka kawo lefe, akwatuna goma cif masu kyau da tsada, tun daga nan hankalin ta ya kara tashi sosai, ta yarda da gaske dai auren babu fashi, babu abu daya da ya burgeta a kayan dan bata son duk wani abu da ya danganci Adam din, sosai take jin tsanar sa. Bayan an karbi lefen kowa ya watse su Ya Hadiza suka zauna zaman yi mata nasiha dan idan aka shiga satin bikin babu me sukunin zama yayi mata, jin su kawai take dan duk abinda suke fad'a bata jin zata iya yin guda daya, ita dai kawai ta riga ta san zatayi aure ne dan biyayya ga mahaifin ta.     Da daddare kafin duk su watse sai gashi ya zo, gabanta ne ya fadi da taji Areef yace yazo, duk suka zuba mata ido tayi saurin zamewa daga zaunen da take ta kwanta kuka na taso mata. "Tashi zakiyi kije, kiyi hakuri." Ya Hadiza tayi maganar tana mikewa, tashi tayi daga kwanciyar, ta ja hijab dinta dage gefe zata saka ta girgiza mata kai " Musulunci ma ya halatta mishi ganin wani abu sashe na daga gareki, ki saka mayafi dan Allah, sai ki dauki Hibba kuje." Bata yi mata musu ba, ta ajiye Hijab din ta karbi mayafin dake jikin kanwarta Rauda ta yafa, ta rik'e hannun hibba din suka fita, already ya shigo yana falon Abba shi da Abbaty da Yaya Ibrahim. Da sallama ta shigo duk suka juyo suna kallon ta, sannan suka amsa, murmushi yayi mata tayi kamar bata gani ba, ta samu gefe chan ta zauna sai suka tashi suka fita ya zama daga ita sai shi sai Hibba da ta makale a kusa da ita dan tana da kiwa. Tsam ya taso daga wajen zaman sa ya dawo kusa da ita, har tana jin kanshin turaren sa sosai, bata dago ba ta gaishe shi ya amsa yana bin ta da mayen kallon sa, riga da skirt ne a jikinta simple dinki amma tayi kyau sosai, fuskar ta fayau babu hoda sai yar rama da tayi akan ranar da ya ganta a kitchen. "Fine baby, ya sunan ki?" Ya mika ma Hibba hannu ta noke yayi murmushi "Madam ya gida?" "Madam?" Tace a ranta "Lafiya lou." Ta amsa tana mummuraza yan yatsun hannun ta. Kallon hannun yayi, ya kai nasa hannun ya kama tayi saurin janye wa a tsorace ta kalle shi, a lokacin ta lura da shaddar dake jikin sa an masa karamin dinki iya guiwa kansa babu hula ya rage gashin sa sosai. "Menene haka? Kamar kin ga wani dodo." Ya tambaya cike da mamakin ta "Ka daina taba ni." Tace kai tsaye tana kokarin tashi daga kujerar yayi saurin fizgo mayafinta yana zaro mata idon sa. "Me kike nufi? Aure fa zamuyi? Me yasa kike behaving kamar baki san yadda rayuwar ta zama bane, bana fa son kauyanci." Kallon sa tayi cike da mamakin sa, ta lura akan rayuwar da yake so yake ganin daidai ce nan da nan zaka ga fushin sa, ita kuwa ta gwammace duk abinda zai fad'a ya fad'a fushin sa ba komai bane akan fushin ubangiji. Tana jin sa ya cigba da gaggasa mata magana san ransa, tayi biris kamar ba da ita yake ba, tana da yakinin zafin zuciya ce dashi, kuma bakin sa bashi da control wejan gasa magana. Sai da ya gaji don kansa yayi shiru yana jan tsaki. Ya zaro wayar sa ya hau kira yana cigaba da huci akan kawai ta hanashi taba jikinta. "Babe where are you?" Yace bayan an daga wayar "Ok I'm on my way." Ya kashe kiran ya mike yana kallon ta "Ba zan yi tolerating kina hana min abinda yake nawa ba, ba zan sake dawowa ba idan an kawo ki gidan zaki ga yadda zanyi dake." Daga haka ya juya yana taku dai-dai yayi ficewar sa, be ko yi sallama da kowa ba ya kama gabansa sai gidan Fido, daga chan ya wuce wajen abokin sa ya karbi wasu kaya sannan ya wuce gida. Tun ranar da ya tafi bata sake jin duriyar sa ba, Hajiya Mama dai tazo sau daya da maganar yadda bikin zai kasance tunda duk abu daya ne bangaren ta da na Abba, umma dai bata ce komai ba, duk abinda suka tsara suka yanke ita bata da ta cewa dan ko da tace din ma ba lallai suyi amfani dashi ba. Daga haka aka shiga satin bikin. Ranar laraba aka je akayi kafi, gidan yayi kyau sosai sama da k'asa sai parking space, a jikin gidan Hajiya Maman yake dan katangar su daya, dama tace ko Adam zai yi aure yana tare da ita bata so yayi nisa ko kad'an, balle kuma da zai auri Asma'un sai take ganin ai shikenan ma dama Asma'un ikon ta ce itama. Alhamis aka shiga bikin gadangadan, gidajen biyu ko ina biki ya kankama Hajiya Mama dai saboda yawan mutanen wasu sai dan karamin hotel hotel din dake bayan gidan aka kama musu musamman abokan Adam din da sukayi karatu a turai tare suka zo daga wasu states din. It's better to marry late than to marry wrong! (Kamar haka dai bature yace, na manta dai. Don't marry out of desperation dan aure ya wuce duk tunanin me tunani! _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* https://arewabooks.com/chapter?id=628b84d5aed642354ddce302 RAYUWAR MACE* _Hafsat Rano_ Free Page (4) ***Zazzaune suke da kawayenta su biyar wanda sai da Umma tayi mata fad'a sannan ta sanar da su da maganar bikin,sai gasu kuwa washegari da aka yi kafi. Lefe suka kalla suke cin abincin da Umma ta saka aka kawo musu sannan suka me kushin da Nadeeya ta turo ta shiga aikin yi musu kunshin wanda ita dai asma'u kawai bin su take da kallo ta sallama komai musamman da taga an soma yi mata lallen sai ta fad'a kogin tunanin yadda rayuwar ta zata kasance idan ta auri Adam. Duk hayaniyar da suke da tsokanar ta, bata kula sh ba, dan ba ma gane musu take ba. Ana gama mata jan lallen sai kawai ta zame a wajen ta kwanta ta rufe idon ta, tana fatan ace tayi bacci ta farka taga an ce ai mafarki ne babu maganar auren ta da Adam din. Sai dai sam baccin yaki daukar ta, duk abinda suke fad'a na shakiyanci tana jin su.    Sai bayan magriba sannan aka gama musu,  suka tafi anan ta samu ta shige daki ganin gidan ya cika sosai da yan uwa, gobe za'a yi kamu dan haka makusantan umman duk sun zo da su Yaya Hadiza da yaran su, dangin Abba kuwa kusan rabin su suna gidan Hajiya Mama, sai gobe zasu taho nan din daga nan kuma sai su raba kansu gida biyu wasu su zauna anan wasu a gidan Hajiya Maman.    Tana kwance Rauda da Hidaya suka shigo, suka zauna suka shiga yi mata hira, sai ta mike ta dan ware a cikin su har tana kyalkyala dariya tamkar bata da sauran damuwa, su kansu sun yi mamaki sai suka ki yarda su bar ta ko na dan lokaci ne suka raba dare suna hira irin ta yan uwa, da tuna rayuwar baya da yarintar su. Sai chan dare suka kwanta suka tashi da asubah daga nan kuma aka shiga shirye shiryen kamu da za'a yi a kangon Abban dake jikin gidan nasu ta baya.    Bata fito ba ta sake gyara kwanciyar ta dan dama ba sallah take ba, ta dai kama ruwa ta wanke jikinta sannan ta sauya kayanta ta koma ta kwanta dan bata san idan ta tashin me zatayi ba, kayan da zata saka a kamun da komai duk su Rauda sun hada mata waje daya, dama tun farko tace musu ba zatayi make-up ba, wanda dama shine yake cinye dukka lokacin shiyasa kawai ta cigaba da mikewa tana jin hayaniyar na tashi ana dora tukunya ana saukewa alamun dai da gaske bikin ake, babu kuma wani abu da zai hana sai dai mutuwa.    Ji tayi ta nemi guntun hawayen da take dashi ta rasa, tana tunanin ma ko sun kafe ne tun yanzu dan ta san akwai sauran kuka a gabanta. Sai kawai ta dinga sauke ajiyar zuciya a hankali tana karanto duk addu'ar da tazo bakin ta.    Breakfast su Rauda suka shigo dashi, kosai ne da kunu sai farfesu da akayi mata daban sai ruwan tea game bukata, bata shan kunu da dangogin sa tun da chan, shiyasa sai Rauda ta hada mata tea ta dinga hadawa da kosan da bread kuma sai taci sosai dan kwana biyu bata samun isasshen cin abinci saboda zulumi. Umma ce ta shigo rik'e da wata Leda a hannun ta, ta ajiye a dakin ta kalle ta, tace "Ku koma chan gidan Safiyya sai ku shirya a chan nayi mata magana, za'a aiko muku da abincin rana idan an gama nan dakin ma wasu bakin ne zasuyi amfani dashi." "Dama yanzu muke shirin tafiya." Cewar Rauda tana tattare kayan wajen. " Kizo daki na." Tace wa Asma'un tayi gaba, tashi tayi tabi bayanta tana fita akayi mata cha, amarya amarya, ta dinga yake kawai tana gaishe su har suka dangana da dakin Umman inda duk kannen umman suke cike. Gefen gadon ta zauna tana gaishe su, suna amsawa wasu suna tsokanar ta, Aunty hauwa ce ta tabo ta, tace ta dawo ciki sosai, ta matsa wajensu, ta soma mata magana a hankali yadda ba kowa zai ji ba, sai ita da take fadawan, har ta gama bata ce komai ba, tayi godiya idon ta na cikowa da kwalla dan maganganun sun shige ta sosai kasancewar Aunty Hauwan babbar malama ce ta san addini kwarai, duk abinda ta fad'a mata gaskiya ne sai dai bata san ta Ina zata fara ba, ta Ina zatayi yiwa Adam irin biyayyar da Aunty Hauwan take fad'a. Ta dan jima a dakin har sai da su Rauda suka leko sannan ta tashi suka dunguma zuwa gidan Safiyya, amarya ce bata jima sosai a unguwar tasu ba, suna da alaka ta bangaren Umma shiyasa ma umman ta zabi su je chan su zauna saboda gidan zai cika da mutane sosai.    Wajen karfe hudu ta gama shiryawa da taimakon su Rauda da wasu kawayen ta da suka zo tun dazu, kuma suka tursasata dole aka dan mata makeup duk da light ne amma tayi kyau, ta dinga hararar su suna mata dariya dan ita har ga Allah bata son duk abinda ya shafi kwalliya irin wannan ita dai barta da yar powder da kwalli sai lipstick shikenan.    Abbati ne yazo daukar su a motar Abba duk da ba wani nisa bane duk cikin layi daya ne amma ita kunyar fita take a haka shiyasa kawai ta kirashi yazo ya dauke ta da kawarta daya su kuma sauran suka yi gaba wajen kamun suka jira a wajen dan su shiga da ita.    Wajen ya cika sosai, an tsara komai yadda ya kamata, Hajiya Mama da Jama'arta suna bangare daya sun sha kwalliya, su Nadeeya ma sun iso sun sha kwalliya sun yi kyau sosai, kallo daya zaka musu kaga banbancin wayewa fiye da mutane da yawa a wajen, idon su a bude yake sosai sai suka zama daban a wajen.   Amarya na zuwa aka soma abinda ya tara mutane a wajen, nan fa su Hajiya Mama da mukarrabanta suka bud'e bakin aljihu suka dinga zazzaga kudi, baka jin komai sai sunan su da MC ke ambata saboda ya ga ruwan kudi, ita kanta Ummaa uwar bikin gefe ta koma ta zubawa sarautar Allah ido, sun kankane komai hatta wajen Amaryar su Nadeeya ne suna ta aikin daukar hoto, sauki daya da umma take hangowa Asma'un shine ta wajen su Nadeeya din da Hajiya Maman, kamar suna son ta, kamar zata samu sauki a wajen su, ko dan alaka me karfi da take tsakanin su, sai dai kash!    Wajen takwas aka gama, shima da an daka ta tasu ba za'a tashi ba, basu shiga gidan Abban ba, suka hau motocin su suka tafi. Sauri take ta isa daki ta cire kayan dake jikinta dan ba karamin takura mata sukayi ba, tana zuwa dakin su taga mutane ne tsofaffi a cike duk sun kwakkwanta,juyawa tayi zuwa dakin su Abbati, tasan babu kowa kuma basu dawo ba, tana shiga ta sauke ajiyar zuciya ta hau kokarin zuge zip din rigar da ta kamata sosai dan ma ta saka wadataccen mayafi amma da babu abinda zai sakata, jin hannu tayi a gadon bayanta, ta juyo a razane suka yi ido biyu dashi, ta daddage zata kwalla kara ya rufe mata bakin da karfin sa. Kici-kicin fuzge kanta take ya saka dayan hannu ya rike mata kan sosai, sai kawai ta fashe da kuka me cin rai. Sakin ta yayi da sauri yana mata wani irin kallo. Da sauri ta juya ta fice daga dakin jikin ta sai rawa yake kamar mazari, dakin Umma ta shiga ta wuce da sauri wardrobe din Umman ta dauki hijab ta saka sannan ta fito da sauri, a tsakar gida sukayi kicibis da Abbaty,ya tare ta da sauri "Dama ke nake nema, Adam yana dakin mu tun dazu yana jiranki." " Dan Allah kace ya tafi, ni ba zan iya zuwa ba." Zaro ido yayi " Abba ne fa yace na zo na gaya miki, babu ruwana wallahi." "Abba!? Ya dawo ne?" " Tun dazu ai yana nan, shima Adam din tun kuna wajen kamun yazo Abba yace ya jira shine yayi magana aka tashi ai daga kamun. " Wani abu ne ya tokare mata a wuya, bata masa magana ba kawai ta bi hanyar dakin nasu, ta tura ta shiga, yana tsaye yana kai kawo a tsakiyar dakin. Gefe ta samu ta makale ya matso yana kallon hannun ta da kafarta da akayi mata lalle. "Menene wannan haka?" Ya fad'a muryar sa a dan tunzure, ta masa banza kamar bata ji ba, ta gwammace ya kashe ta idan ma kashe ta zai amma ba zata tanka masa ba, sake magana yayi da dan karfi, ta dago a tsorace taga yana wa hannun ta da kafarta kallon tsana. "Bana son wannan abun da kika je akayi miki, karki kuskura kizo min gida dashi wallahi, ki san yadda za'a yi ki goge shi." A wani irin yanayi take kallon sa, mamaki na neman kashe ta, lallen yake nufin be sani ba, ko kuma me? Bata gama dawowa daga tunani ba, taji ya wurgo mata leda akan fuskar ta, tsinin takalmin dake cikin ledar ya buge ta, sosai taji zafi. "Kayan da zaki saka ne a dinner din da friends dina suka shirya gobe, saura ki zubar min da girma na da aji na da kauyancin ki, ki tabbatar kuma kinje an goge wannan bakin abun na hannun ki, ina laifin ma ki saka nail polish ko kiyi fixing nail din ma , amma kiyi wannan abun irin na yan kauye, bana son shi bana son ganin shi kuma." Saroro tayi tana kallon sa mamakin sa na neman kashe ta, tashi tayi daga zaman da tayi, ta dire masa kayan a gabansa tace "Bana bukatar kayan nan saboda ba zan je wajen ba, sai ka dauka ka kaiwa wadda take da wayewa daidai da taka, wadda ba zata baka kunya da kauyancin ta ba. Lalle kuma ba zan goge ba, tunda ba dan kai nayi ba, kuma hannu na ne da kafata ba ta wani ba, abinda naga dama shi zanyi.". Ta murguda masa baki ta juya da sauri ta fice dan tasan tsaf zai iya gaura mata mari yadda taga yana huci. Kasa motsawa yayi daga wajen kamar wanda aka bigewa kafa, ya kalli kayan da ya kashe kudi masu yawa wajen siyansu amma ta watsar masa a wajen, sannan ya gaggaya masa magana yana tsaya har ta fita be fisgota ya nuna mata shi ba sa'an ta bane. Ransa ya kai kololuwa a baci, huci ya dinga yi kamar wani dan karamin zaki, sai ga Abbati ya shigo da yaga fitar Asma'un, kallon kayan dake kasa yayi ya kuma kalli fuskar Adam din, sai ya juya zai fita. "Tsaya pls, wannan kayan ta manta su ka kai mata, ni zan wuce." "Owk." Yace ya dawo ya dauki ledar suka fito a tare ya tafi shi kuma ya shiga ciki ya samu Rauda tana waya a tsakar gidan ya bata ya tafi. ***Daren gaba daya bata iya runtsawa ba, bata kara tabbatar da banzar al'adar Adam din ba sai a jiya, hakan ya tsaya mata a rai matuka har ta rasa irin tunanin da zatayi akai, tana jin yar hayaniyar wadanda basuyi bacci ba a tsakar gida suna aikin abinci har ta daina jin su kwata kwata, sai daf da asubah sannan bacci ya dauke ta cikin yanayin da ba zata iya misaltawa ba. Wajejen bakwai aka hau tashin ta kasancewar ranar ce daurin aure, ta tashi idon ta duk sun kumbura saboda rashin isasshen bacci. Shiryawa ya Hadiza tasa ta ta hau yi, babu um babu a'a ta hau shirya war, tana jin sanda su Abba da jama'ar da zasu tafj daurin auren suka tafi saboda a garin su Abban za'a daura Sumaila, ji tayi jikinta ya kara sanyi sosai. Ta zauna rik'e da kanta dake sara mata sosai, ko da aka kawo breakfast din sai ta kasa shi, jiya ma ashe dan ba taga anzo tafiya daurin auren bane har ta samu sukunin ci sosai. Babu yadda su Rauda basuyi da ita ba amma bata da nutsuwar da zata iya saka wani abu a cikin ta, lokaci kad'an sai ta duba agogon wayarta har sha daya tayi, jikinta ya kara saki sosai ta saddakar shikenan, shikenan ta shiga rayuwar da bata da yakinin samun kwanciyar hankalin ta.    Wajen karfe daya da rabi suka soma shigowa, kowanne su cike da farin ciki, farin cikin da yake daidai da bakin cikin ta, tana jin sanda wani kawun ta kanin umma yake fadawa matan tsakar gidan an daura, wata daga cikin su ta saki guda me karfi. A take taji kanta na wani irin juyawa, taga dakin na neman fado mata akai, bata san sanda ta fashe da wani irin kuka ba, su Rauda dake gefenta suka hau tayata dan dama karfin Hali kawai suke da kuma bin umarnin umma! _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* RAYUWAR MACE*       _Hafsat Rano_          Last Free Page (5) ***Babu wanda yake da niyyar rarrashin wani a cikin su har saida Ya Hadiza ta shigo, ta harari Rauda da Hidaya cikin bacin rai tace "Menene haka? Ku da zaku karfafa mata guiwa sai kuma ko zauna kuna tayata kuka, kukan menene? Akwai wanda ya isa ya kujema kaddarar sa ne? Kowanne bawa fa da yadda Allah ya tsara masa, ku tashi dan Allah kafin hankali ya dawo kanku. " Shiru duk sukayi har ita Asma'un sai dai ba zata iya fasalta yadda take ji a kirjin ta ba, abu ne dankare me girman gaske, wanda ko hadiyar yawu sai tayi da gaske take iyawa saboda yadda ya tokare mata ko ina.   A hankali gidan ya sake cika sosai bayan dawowar yan daurin aure, suka dinga jerin gwanon shigowa wajen yin Allah sanya alkhair, daga nan kuma aka dinga fitar musu da abincicika kala kala. Sakon gidan Hajiya Mama ne ya iso, katinan dinner ne ta aiko dashi sannan ta aiko da kuloli manya dankare da sinasir da waina, sai a lokacin su Ya Hadiza suka san da maganar dinner din dan babu wanda ta fadawa. Tunanin yadda za'a yi da zuwan suka shiga yi, dan a kalla ya kamata ace an shirya sosai, basu ji dadin short notice din ba amma kuma babu yadda za'a yi haka za'a je din dan be kamata a bar ta ita kadai ba babu yan gidan su.    Kamar yadda yake a al'adar Malam bahaushe bayan daurin aure ana zuwa angwaye su gaida iyayen amarya suyi musu godiya, bangaren Adam kuwa da abokan sa suna chan hotel din da aka sauke su, Adam na tare da Fido, dan ko daurin auren be je ba, dan dama yace in dai a Sumailan za'a daura ba zashi ba, sai abokan sa uku kawai ne suka je dama suma duk target dinsu na ga dinner din ba wai daurin auren ba, musamman da aka kaishi har Sumaila ba zasu iya bin hanyar ba balle su sha wahala shiyasa sukayi zaman su har aka dauro aka dawo, aka aiko musu da abinci suka ci sukayi nak sannan suka soma shirin shiryawa dan su shiga gidan su Adam din sannan su rakashi wajen Amaryar tasa bayan ya samu da k'yar ya lallaba Fido ta tafi, jin sa yake yau babu ya shi dan zai gwangwaje sosai, sai kuma yi maganin tsiwa da rainin ta, dan bata kai matsayin da zata gaggasa mata magana anyhow kuma ya zuba ido ya kyale ta, dole sai koya mata hankalin da ba zata sake ba.     Suna shiga cikin gidan nasu aka yi musu cha ga ango ga ango, yan uwa sai faman tsokanar sa ake, yana washer baki tamkar gonar auduga, da sun san dalilin da yasa yayi auren nan da basu taru haka ba, so yake da gaske ya dauke hankalin kowa daga kansa, ya sheke ayarsa babu me saka masa ido, ya kuma rabu da mitar Maman na kullum yaki aure, shiyasa ma be yi wani dogon tunani akan hukuncin sa ba, dan dai shi yasan ba son ta yake ba, tana dai da abin da yake so a tattare da mace, amma batun kyawun fuska yafi son fara sosai, ita kuma tana da duhu musamman da take cikin fararen tas dan duk yan uwanta sun fita haske hakan ya saka ake ganin har kyau din ma sun fita. Jingina dogon tunanin da ba zai amfane shi ba yayi, suka shiga dakin Mama in da take tare da manyan kawayenta, ai sai kawai ta rungume shi cikin farin ciki, baka jin tashin komai sai gud'a da sambarka, ita kadai tasan yadda take ji da auren nan nasa, a kalla idon mutane zai bar kanshi, kuma tana fatan Asma'u ta shirya mata shi, ya bar duk wata banzar al'adar sa, dan ita a ganin ta ma, idan har mace ta kasa daidaita dabi'u da al'adun mijinta, zuwa nata da take so to tabbas bata kai mace ha, ko tace ma kawai ta rako mata duniya ne. Sun dan jima a dakin sannan suka fito suka rankaya gidan Abban.    Sanye yake da riga jamfa da wando babu batun babbar riga dan babu ita a tsarin sa, musamman lokacin zafi ne ko da Mama tayi masa magana sai yace mata ai tana mota zai saka idan sun fita, nan kuwa ko dinka ta be ba, hula ma dan dai kawai babu yadda zai ne, amma tabbas yana dawowa zai cire kayan dan ba zai iya ba, saukinta ma a dinner din suit zasu saka da ace manyan kayan zai sake maimaitawa toh da an samu matsala dan shi a rayuwar sa baya son abinda zai zo ya takura masa.    Sanda suka isa gidan sauran yan daurin auren basu gama watsewa ba, da yawan su ma suna zazzaune ne a kofar gidan an saka rumfa suna shan iska ana hira cike da Raha, yawanci su yan Sumailan ne sai yan tsirari da suke abokan Abba. Shi kansa Abban yana wajen tashi yayi ya amsa waya ya dawo.     Labarin isowar angwayen ya riski cikin gidan, aka shiga shisshiryawa shigowar tasu, asma'u da taji abun daga sama sai da taji wani ras a kirjinta, tayi saurin dafe shi ta mike tana kokarin neman hanyar ficewa daga gidan, tun dazu umma take sababin su koma gidan Safiyya a aiko musu da abinci amma ya makale a dakin Umman taki fita, sai gashi yanzu tana son fitar amma bata san yadda zatayi ba, dan dole idan tace zata fita sai sun ganta, abinda ita kuma bata so kenan. Ganin take taken ta na son guduwa ya saka Aunty Hauwa ta dakatar da ita, ala dole ta dawo ta zauna tana kudundunewa a cikin mayafin ta.     Hargowar su ta fara jiyowa alamun sun shigo ciki, tana jin wasu mata da bsta gane su waya ba suna ta tsokanar su,su kuma suna biye musu, irin dai wasan jika da kakan nan, shine a gaba wajen zakewa da amsawa tamkar bashi ba, kamar ba ango ba ma dan babu wata alama da zata nuna a jikinsa da zaka gane ango ne, tana jin sanda suka dungumo suka shigo falon umman, lokacin su Aunty Hauwa duk sun fita falon, nan dai akayi addu'a wanda aunty hauwan ce ta assasa da babu me wannan tunanin a cikin su, sannan suka yi waje suna cigaba da hayaniyar su. Wani ne cikin abokan ya tabo shi, yace "Ina amarya ne?" " Ba za'a hadu wajen dinner ba, kyale ta kawai pls." " Ok." " Ku jirani a waje ina zuwa." Yayi hanyar dakin su Abbati, suka sheke da dariya, wato ba zasu ga Amaryar ba amma shi zai ganta, ba komai ai akwai anjima. Waje sukayi shi kuma ya shiga dakin ya tarar dasu da abokan su, Abbati yayi saurin tashi suka gaisa sannan yace ya taimaka ya kira masa ita, fita yayi sauran abokan ma suka fita ya zama sai shi kadai a ciki, a tsaye yake be zauna ba, da ba dan ace yana so ya kara jaddada mata maganar dinner din ba , da babu abinda zai saka shi nemanta, tunda dai an daura ai shikenan, duk ma abinda take tunani ko ji dashi zasu gauraya ne, daga shi sai ita yadda zai nuna mata shi din gogaggen dan duniya ne, idan aka ce ta sake gaya masa magana ma ba zata sake ba.    Sanda kiran ya isketa kusan shidewa tayi, bata hango rangwame wajen Adam ba, shiyasa bata son duk abinda zai hada su waje daya daga shi sai ita, narai narai tayi da fuska, kamar zatayi kuka dan har kwalla ta cika mata ido, ganin yadda ido ya dawo kanta ya sakata tashi ta bi bayansa, duk taku daya da take ji take kamar ta saki fitsari a wando saboda zulumi. A hankali ta tura kofar sai kuma ta tsaya ta kasa shiga, yana kallon inuwar ta, ya ja tsaki ganin zata bata masa lokaci, ya fizgota da hannun sa ta dawo cikin dakin,durkushewa tayi da sauri jikinta na rawa tamkar mazari. Kallon ta yake yana kokarin ganin ko tayi abinda ya sakata, yana nan zanen kamar jiyan babu abinda ya chanja. Dogon tsaki ya ja, sai yayi maganin ta kuwa, yanzu ba wannan ne ya kawo shi ba tukunna "Ina kayan da na bawa Abbati ya kawo miki?" Shiru tayi, ya sake maimaitawa bata amsa ba, sai da ya daka mata tsawa me karfi sannan tace a kidime. "Suna wajen Hidaya." "Ok." Yace yana matsowa daf da ita, ya daga ta gami da fizge mayafin da tayi lullubi dashi, ya rage daga ita sai tsuran kayan jikinta, riga ce fitted da skirt da yayi daidai da jikinta, bin ta ya dinga yi da wani shu'umin kallo, ya lashe lips dinsa na k'asa yana kallon saman kirjinta, hannu ta sa da nufin karewa ya sa karfi ya murde hannun har sai da tayi kara. "Baki isa ki hanani abinda na saka kudi na siya ba, karki sake idan ba haka ba, zaki fuskanci hukunci me tsananin." Yawo maganar ta shiga yi mata akai, siya? Kenan ba auren ta yayi ba ma, siyan ta yayi, da lefen kenan ya siye ta ko da sadaki? Bata gama tunani ba sai jin hannun mutum tayi a jikinta, ta firgice tana kokarin guduwa, hannu daya ya saka ya matse ta kam, ya shiga taba ta duk in da yaga dama, kuka take sosai ta rasa yadda zatayi dan ya hana mata ko da kwakkwaran motsi ne, sai da ya ga dama dan kansa, sannan ya ture ta da karfi tayi baya saura kad'an ta fadi Allah ya taimaka ta tsaya a kafarta, be ko kalleta ba ya juya ya fice yana maida numfashi, ba zai iya resisting ba idan ya tsaya, komai zai iya faruwa.     Durkushewa tayi a wajen ta saki kuka me cin rai, bata taba ganin aure irin nata ba, duk wata amarya a wannan ranar tana cikin farin ciki mara misaltuwa saboda auren wanda take so yake son ta. Sai dai ita akasin haka ne a gareta, babu digon soyayyar ta a tattare da adam, tun tana yarinya Adam be tana kaunar ta ba, be taba tausayin ta ba, illa ma duk sanda suka hadu ko a gida ko a wani waje sai yayi dwewrieiririwroieoei e pie I i a little more Ta yaya zata iya? Me yasa babu wanda yake hango mata abinda take hangowa a gaba, me yasa? Ko kuma dai suna hango matan kawai babu yadda zasu yi ne, musamman Umma da tafi kowa saninta, ita ya kamata tafi kowa tausaya mata, amma sai taga kamar itama bata damu ba. Cigaba da zama tayi a dakin har sai da yamma tayi likis, sai da Abbati yazo sannan aka san tana dakin, dan har hankali ya fara tashi abna tunanin in da taje, idonta ya yi luhu luhu saboda tsabagen kuka, haka dai aka babbata baki sannan ta wuce dakin Abba, kasancewar daga wajen dinner din za'a wuce da ita ba zata dawo ba, nasiha sosai yayi mata wadda ta sake kashe mata jiki, ta kara volume din kukan ta dan kukan ne kadai yake rage mata radadin da take ji a ranta. Shi kansa Abban duk dauriyar da yake sai da yaji ya karaya, hawayen da ita suka tsaya masa a rai, ya nemi dan guntun farin cikin da yayi saura ya rasa, ya dinga ganin baiken sa, da ya barta zuwa lokacin ta, da be yi gaggawa ba. Shi da kansa ya dinga bata hakuri, tayi shiru tana sauraren sa cikin yanayin karaya, umma kuwa kasa cewa komai tayi, har Ya Hadiza ta shigo ta taimaka mata zuwa dakin ta, sannan ta sakata shiryawa saboda dinner din, bata musa ba, dan musun bashi da amfani tunda aikin gama ya riga ya gama, sai dai tana wanka tana kuka sosai, hakan ya jawo mata dadewa sosai a ciki, sai da Rauda ta kwankwasa mata sannan ta fito, suka taimaka mata ta shirya a cikin gown din da ya kawo, gown din da bata da maraba da ta arna sai dogon hannun net da ke jiki, mayafi fari ta dora akai da ya rufe mata duk wajen da yake a bude a rigar, kirjinta da sangalalin hannun ta, takalmin ne dai ba zata iya sak'awa ba saboda ya mata tsayi da yawa, bata ma iya tafiya dashi ba.    Duk abubuwan bukatuwar ta sun yi gaba kafin ta iso, hatta kayan sawarta da komai rankatataf an kai mata su, yadda ana gamawa zasu wuce chan gidan, dama duk wanda suke da bukatar ganin gidan Amarya sun gani tuni, shiyasa kawai aka yanke shawarar musamman ganin dare zai yi kuma shi kansa Adam din ya fadawa Mama yau yake so a kawota, har su Nadeeya na tsokanar da yayi rashin kunya, yayi kuwa mirsisi yana jin su yayi gaba abin sa. Ita kuwa Mama farin cikin da take ciki ba zai fadu ba, ta hasaso shiryuwar danta, tunda duk alamun sa sun nuna yana son Asma'un, a kalla zatayi galaba a kansa a wasu abubuwan da yawa.    Tuni wajen ya cika da jama'ar Adam da kawayen Mama sai su Nadeeya kowa da jama'ar ta, sai bangaren su Asma'un suka tashi yan kad'an, duk suka koma suka darare dan babu ma wanda ya nuna jin dadin ganin su, dama basu da yawa dududu su goma ne kawai, sai Asma'un da Rauda da Hidaya, sai kawarta guda daya, zuwan su ne ma wajen ya saka su Nadeeya nuna sun gansu, aka raka amarya wajenta duk kunya ta isheta, kamar ta tsaga kasa ta shige dan ita ire-iren abubuwan nan tun da ma ba zuwa take ba. Tana zama suna isowa cikin zugar su guda, sun sa suit bakake sai uban gayyar da ya saka fara tayi masifar karbar sa kasancewar shi fari sosai. Nan da nan wajen ya kachame. Baka jin komai sai tashin kida me masifar kara da ya saka haifar mata da matsanancin ciwon kai. Zama yayi a gefenta, daf da ita har tana jin jikinsa a gefen nata, kafarta ya take mata bayan ya zauna, ta kalle shi da sauri ya watsa mata harara, tayi saurin tun k'asa da kanta. Tana jin shi ya lalubo hannun ta, ya matse shi sosai har sai da tayi kwalla, ya sakar mata murmushi yana matsowa daf da ita kamar zai fad'a mata wani abu, ta runtse idon ta da sauri, tana jin sanda ya furta. "Kinyi kyau matar Adam!" Ya saki murmushin gefen nan, wanda shi kadai yasan manufarsa sai ita da take hasashe! Rayuwar Mace labari ne daya tamkar da dubu, akwai kalubale a rayuwar asma'u, a rayuwar da yawa yawan mata! Amma sai dai me? Me zai faru? Wanne irin zama ne zai kasance tsakanin ta da shi? Mata da yawa suna zaune da mazaje masu halin Adam ko fiye, amma kullum magana daya ce, muyi hakuri!   Akwai haske tattare da RAYUWAR ta a gaba, hasken da zai yaye mata dukkan damuwar ta!    Soyayya me tsafta, soyayya me tsayawa a kalbi! Ku biyo zafafa biyar dan ganin yadda zata kasance a RAYUWAR Mace! Rayuwar Asma'u _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_*      *RM*           6 *_ZAFAFA 5 NA MIKA GAISUWAR TA'AZIYYA ZUWA GA MARUBUCIYA UMMY AISHA, TA KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION, BISA GA RASHI NA MAHAIFIYAR TA DA TAYI. MUNA FATAN ALLAH YA JIKANTA DA RAHAMA, YA GAFARTA MATA, YA KUMA BASU HAKURIN WANNAN BABBAN RASHI AMIN._* __________________________________ _SAKINA VENDIBLES_ _SAKINA VENDIBLES_ _SAKINA VENDIBLES_ _(INDE HARKAR TURARUKA NE MASU KAMA JIKI DA GIDAH KAI HARDA TSUGUNNO. SAKINA VENDIBLES ITACE KAN GABA)_ _SUNA DA KAYA INGANTATTU MASU MATUKAR KYAU AKAN FARASHI MAI RAHUSA.)_ _KINASON ASAN KIN ISA MACE? WADDA ZAKUYI GOGAYYA DA MASU SAKA DESIGNER TURARE AMMA KI FUSU KAMSHI? DUK INDA KIKA GIFTA ASAN EH. KEDIN TABANCE , KIN ZARCE SAURAN MATA)_ _AKWAI KHUMRAH WHITE AND BLACK_ _KULACCAM BLACK (FOR HAIR( AND WHITE FOR BODY_ _WASU DAGA CIKIN KAYAYYAKIN MU SUN KUNSHI👇_ Turaren wuta list* Queens special Kajiji mix Kajiji whole Gabgab Brown Hawiii Special Halut Sandal balls Sandal strips Sandal flakes Dubai oud White Hawii Classy Dufr Black bange Black bange Musky Dorrot(Na tsuguno) Cous cous *_DA SAURAN SU DA YAWA_* *_Handles_* *Instagram* @sakina_vendibles *Facebook* @Sakina vendible *Tiktok* @Sakina vendibles_ ****Zuwan angwayen ya saka aka shiga gabatar da bikin gadan-gadan. Babu abinda take ji sai faduwar gaba a duk sanda ta tuna abinda yake tunkaro ta, suna nan zaune aka fara kiran amarya da ango su fito fili. Murmushi ya sakar mata ya miko mata hannu, ta kalle shi a tsorace, ya sake sakar mata murmushin sannan ya kama hannun nata ya mikar da ita, suka shiga takawa zuwa filin tamkar tsofaffin masoyan da suka jima da kaunar junan su.    Sun jima a filin shi da abokan sa na ta tikar rawa, taji jiri kamar zai debe ta, ta daure kanta na k'asa amma tayi matukar gajiya, yana ankare da ita yana sane kuma suka cigaaba da abinda suke, sai da ta gama gajiya likis sannan suka koma suka zauna, ta  kalle bangaren da su Hidaya suke, suka hada ido ta marairace fuska, tasowa suka da Rauda suka zo wajen ta, suka zauna a side dinta sai taji kamar an yaye mata dukkan damuwar ta, hira suke mata k'asa k'asa, hakan ya sakata warewa har tana murmushi, nan fa su ya Hadiza ma suka taso suka hawo wajen, daukar hoto. Tasowar yan gidan su ya sakata mantawa da shi da existence din sa a wajen, ta sake sosai har sai da mc yace ya isa haka su koma sannan suka koma amma ban da Rauda da ta rikewa hannu kam ta hanata tashi, sai kawai ta cigaba da zama a gefenta da yake akwai spare kujera a wajen.    An dau lokaci sosai har su Ya Hadiza suka fara deciding kawai su tafi, basa son barin ta ita kadai amma dare yana yi musu sosai hakan kuma ba sabon su bane, bayan haka dukkan su da mazajen su, gashi duk ba gidan umma zasu koma ba sai gobe zasu koma. Waya Hidaya ta kira Rauda daga wajen zaman su, ta daga amma bata jin ta, sai ta mata text tace zasu tafi, suna kallo ta radawa Asma'un, nan da nan idon ta ya ciko da kwalla zatayi kuka, "Dan Allah karku tafi." Ta rada mata tana sake riketa "Dare yayi sosai, zamu dawo amma in sha Allah da wuri." Sakin hannun tayi ta sunkuyar da kanta, tana jin tana mata sallama ta daga mata kai kawai.    Bayan tafiyar su sai da aka kara almost an hour sannan aka tashi, wajen karfe daya na dare, Nadeeya ce ta rik'e ta suka fito harabar wajen bikin, ya karaso wajen su yace "Kuje kawai zan zo." "Ok, gidan Mama ko gidan ka?" Ta tanbaye shi ta sigar zolaya. Shafa kansa yayi yana kallon Asma'un da take kallon gefe yace "Gidanta mana, me zakuyi wa Mama a tsohon daren nan, kawai sun hadu da safe." Dariya Nadeeya ta saka, ta budewa Asma'un mota ta shiga, ya rankwafo kanta yace "Get ready for me." Yayi mata shu'umin murmushi sannan ya juya zuwa wajen da friends dinsa ke tsaye suna jiran sa, da kallo ta bi bayan sa, tana kisisiisma iya abinda yake tanadawa a ransa,tasan babu batun sassauci a tattare dashi, ita kuma tayi alkawarin rik'e mutuncin ta har sai ta tabbatar da wanne irin aure akayi mata.    Tafiya motar ta soma yi, tana cigaba da hangen sa tsaye suna ta magana da shewa, baka jiyo me suke cewa amma tabbas ko ma menene suna cikin nishadin sa, sanda motar ta fita daga harabar event centre din a lokacin ta lunshe idon ta, wasu zafafan hawaye masu dumi suka zubo mata, sai kawai ta kwantar da kanta ta rufe idon ruf tana jin duk hirar da suke a tsakanin su, wanda duk maganar yadda dinner ta kasance musu ne.     Tafiyar da sukayi ba me yawa bace kasancewar dare ne babu cinkoson ababen hawa, tana jin motar ta tsaya tayi saurin bud'e idon ta, ta kalli gidan da yake amsa sunan gidan ta, gidan da zata zauna a ciki tayi rayuwa wadda bata san iya adadin ta ba,watakila ma sai dai a fidda gawar ta, ji tayi kamar an sake bubbuge mata kafafunta, taji kamar ta juya ta shiga gari watakila ta samu wadanda zasu fuskanci halin da take ciki, sai dai bata duk wannan damar, tana jin kuma saboda kasantuwar ta mace ce, watakila da itan namiji ce da hakan ba zata taba faruwa ba.    Bin su ta dinga yi tamkar rakumi da akala har zuwa tsakiyar falon gidan, wanda yake fidda shihirtaccen kamshi, amma halin da take ciki ya hanata fahimtar haka, hasalima baki take ganin gidan, basu tsaya da ita ba sai da suka dangana da bedroom din ta, suka zaunar da ita a gefen gadon sannan suka zauna suma suna dan bata baki, hakan ya sakata sakin kuka wanda a da tayi alkawarin ba zatayi ba, sai a sannan ta karyata duk dauriyar ta, domin ba karamin abu bane rabuwa da iyaye ko da kuwa auren soyayya ne balle ita nata da bata ma san a wanne bigire zata ajiye shi ba. Tana jin su suka cigaba da bata baki, suna kokarin ganin ta kwantar da hankalin ta, bata daina kukan ba amma tayi k'asa da muryar ta har suka yi zaton ta riga ta daina, sukayi mata sallama suka tafi. Daga nan gidan yayi tsit babu motsin komai, tsoro ne ya soma shigar ta, ta duba wayar ta taga daya da rabi ta wuce, da sauri ta zame a wajen dan dama bata sallah, ta kudundune jikinta waje daya.  Bayan kamar minti talatin da tafiyar su, taji motsi kad'an kad'an alamun tafiya, sai kuma magana da ta kasa tantance ta waye sai da aka matso kusa sannan ta fuskanci shine yake waya, diri-diri tayi ta rasa me zatayi kuma, ta kalli kanta sai kuma ta kalli kofar, ta tashi da azama zata rufe sai dai kafin ta kai ga rufewar ya danno ya shigo, yana sakale da wayar a kunnensa cikin shigar boxer da wata riga armless, saurin ja da baya tayi ya kalle ta yayi murmushi yace "Baby kina da matsala, na fad'a miki I'm all yours, babu ruwan aurena da alakar mu, you can see me whenever you want,kamar dai ko yaushe." Dariya yayi yana sake makale wayar, ya shiga ciki sosai ya zauna akan bedside yana cigaba da wayar, komawa tayi ta zauna a gefe a k'asa, har ya gama sannan taji ya taso ya nufo ta, kafin ya karaso ta mike da sauri, ya tsaya a gabanta yana kallon ta. "Wannan kayan baki chanja su ba, nifa bana son kazanta fa." Ya fad'a a wulakance ya kai hannu gefen wuyanta ya shafo ya kalli hannun "Duk kin yi gumi baki san miji zai zo wajenki ki dan watsa ruwa ki saka sexy night wears ba, bansan duhun kai fa." Shiru tayi masa shi kansa dama ya san shirun zata masa, kuma dama ya san a hakan zai tarar da ita dan abokin sa yace haka matan hausawa suke, wai kunya sai a kawo amarya da wasu kaya masu uban nauyi ta yi ta wani nuku-nuku a ciki, shi sam baya son ire-iren wadannan al'adun malam bahaushen wanda suke cike da kauyanci da gidadanci.    Cigaba da bin ta da kallo yayi, zai sake magana aka kuma kiran sa, ya kalli wayar kamar zai daga sai kawai ya fasa ya kashe ta gaba daya ya cillar da ita a saman gadon, sannan ya fizgota zuwa jikinsa ya matse ta. "Me kika zo dashi?" Ya rada mata a kunne yana zame dankwalin kanta. "Ina fatan dai sun shirya ki sosai da sosai, bana son matsala ko kad'an, kin gane me nake nufi." Bata gane abinda yake nufi ba dan duk a kidime take, yana ta jujjuya hannun sa a jikinta ya na zagaye da ita, har ya kai bakin gadon, ya hankada ta baya sannan ya bita yayi mata rumfa, da sauri tace "Bana sallah." Kamar be ji ba, sai kuma ya tsaya chak yana kallon ta, kallon neman karin bayani, da girgiza masa kai alamar eh da gaske take, wani irin mikewa yayi da sauri yana ja baya, kamar yaga abun kyankyami, ya fice daga dakin, mikewa tayi ta dauki mayafin ta, ta yafa a tsorace kamar wadda tayi gudu saboda yadda ta rude.    Be jima da fita ba sai gashi ya dawo, rik'e da wasu kaya masu yawa, ya watsa mata a fuskar sa sannan yace "Ki goge min kayan nan tas kafin naje na dawo, tunda baki da amfani kika kuma karya min lissafi baki isa ki kwana haka ba wallahi." Kaya ne masu yawa nasa jeans jeans da tshirts, su yake so ta goge da wannan uban daren, "Ba zakiyi ba?" Yace yana zare mata ido, bata amsa ba. Ya matso sai jin saukar mari tayi da ya kusan sakata sakin fitsari a wajen. "Wayyo Allah na!" Tace a karon farko tun shigowar ta gidan,sake matsowa ta ga yayi, da sauri ta hau kwasar kayan tana kuka "Stupid, tunda baki da amfani sai dai kiyi min aiki." Ya juya yana tsaki, ya shiga dialing number Fido dan ba zai iya asarar daren ba! _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* *RM*          7 ****Kayan ta hau tattarewa tana kuka sosai, duk da dama ta san akwai kalubale a gabanta amma bata taba hasashe ko tunanin rashin mutuncin Adam din ya kai haka ba, ranar da aka kawo ta? Ai ko jaka aka kawo masa a wannan ranar dai ya kamata yayi treating dinta da sauki.    Bata san in da zata fara neman iron ba, haka ta dinga dubawa guri guri har lokacin tana kuka, sai da k'yar ta gano shi a dakin da take da yakinin nasa ne don yadda yake dauke da tarkacen kayan sa, zama tayi dirshan tana cigaba da kukan ta hau goge kayan daya bayan daya wanda duk da gugar su ya hargitsa su kawai dan ya wahalar da ita , bakar gajiya da  yunwa su suka fi damun ta, batun bacci kuwa babu shi dan ko jin sa batayi. Tana cikin gugar aka dauke wutar, duhu ya mamaye ko ina, tsoro ya kamata ta yunkura da sauri zata tashi, ta manta shaf da iron din sai ji tayi kafarta a jikin iron din,tayi kara da karfi zafin na shigar ta sosai. Jan kafar tayi ta dinga laluben hanya da k'yar ta fad'a dakin, ta hau laluben wayar ta amma bata samu ba, durkushewa tayi a wajen ta dinga kuka tamkar ranta zai fita,da dade sosai a wajen sai da taji kafar ta rage zugi ta sake lalubawa ta samu gadon ta haye ta kwanta cikin jin tausayin kanta da rayuwar da ta samu kanta a ciki.   Bata san karfe nawa ba, bata san adadin dadewar da tayi a kwance ba tana kuka, ta nemi bacci ta rasa amma kuma idon ta kamar zai cire tsabar zafin da yake mata, haske ne ya gauraye dakin, a daidai lokacin ya turo kofar ya shigo. Tsayawa yayi yana kallon ta kwance a kan gadon sa, itama shi take kallo ya sauya kayan jikin sa zuwa gajeren wandon 3quater, da wata rigar daban da ta dazun, tashi tayi zaune ta hau kokarin sakkowa daga gadon, ya rigata ya hawo ya dora mata karfin sa gaba daya, ya danne ta ya hanata motsi, kafarta da ya kama mata ta dinga kokarin nuna masa tana kukan amma ko gezau be ba, kamar ma baya cikin hankalin sa. Kayan jikinta ya hau kokarin raba ta dasu, yana fincike su da karfin gaske! Bata da karfin da zata hana shi, sai dai kuma tana tsoron abinda zai je ya dawo, tana tsoron kar yayi kokarin take dokar Allah, dan taga alamun so yake da gaske sai ya raba da  martabar ta,wanda ko da babu period ba zata taba bari ya kusance ta a yanayin da yake ba, bata san matsayar ta ba, taba san wanne irin aure yayi da ita ba. Gadan-gadan taga yana neman wuce gona da iri, bata san sanda ta samu hannun sa ta go gantsara masa cizo ba, hakan ya saka shi sakin ta da sauri gami da sakin gara, da sauri sauri ta tashi ta fice daga dakin, ta fad'a dayan dakin ta sakawa kofar key, sannan ta zame a wajen ta fashe da kuka. Wannan wacce iriyar masifa ce? Tsawon daren bata runtsa ba, ya dade yana buga kofar ta kamar zai balla saboda bacin rai, ya gaji dan kansa ya tafi amma ta san dole haduwar su ba zatayi kyau ba, zatayi iyakar kokarin ta wajen ganin ta gujewa haduwa dashi din ko da zata mutu tayi mushe a dakin. Da k'yar ta tashi lokacin da hasken rana ya hudo dakin sosai,ta shiga toilet ta gyara jikinta ta fito, ta chanja kayan jikinta ta hau gado ta kwanta tana fatan ta samu ta runtsa ko yaya ne. Cikin baccin taji kamar ana taba kofa, ta tashi zumbur tana kallon kofar a tsorace. Sake bugawa akayi sai dai bugun na hankali ne, "Waye?" Tace cikin muryar ta da ta dashe saboda kuka "Nadeeya ce." Sakkowa tayi ta bud'e kofar tana kallon bayan ta ko tare suke, dan kallon ta tayi ganin yadda ta fige kamar wadda tayi rashin lafiya me tsawo, "Ina kwana?" Ta gaishe ta ganin yadda take kallon ta. "Lafiya lou, breakfast ne Mama tace a kawo muku, yarinyar tayi ta sallama shiru shine Mama tace nazo na gani." "Wallahi bacci ne ya dauke ni." "Ba damuwa, ki koma ki kwanta ai akwai gajiya,ga breakfast din nan a kitchen." "Mun gode." Tace ta juya ita kuma ta sauka k'asa tana ayyana ramar da Asma'un tayi a dare daya kachal. Kasa komawa baccin tayi kuma ta dinga juyi tana jin duk motsin sa tsakanin daki da falon saman, baya minti biyar sai ya amsa waya wanda yawancin mata ne sai tsirarin abokan sa. Bata dai jiyo me yake cewa amma tana jin sautin muryar sa, tayi tunanin zai zo ya buga mata sai kuma taji shiru, daga baya ma sai taji fitar motar sa daga gidan. Da sauri ta sauko, ta bud'e kofar ta sauka k'asa zuwa kitchen din da ta nemo shi da sauri sauri, ta dauraye plate ta zuba abincin da sauri ta sake hayewa saman ta saka key cike da tsoron kar ya dawo. Har ta gama ci bata ji ya dawo ba, ta tabbatar ya yi nisa ko kuma yana gidan Hajiya Maman, wanda tayi tunanin yi dan dazu bata iya wankan ba tana tunanin zai iya balla kofar ya shigo, a gurguje tayi wankan ta shirya ta dan gyara dakin sannan ta fito wajen da ta bar kayan sa na jiya, babu ko daya duk an kwashe sai ta koma ta rufe dakin ta kwanta ta fad'a kogin tunanin da ya zame mata aboki a yanzu. Karar bud'e gate din gidan taji, ta leka ta window ta hango su Hidaya da Abbati da Rauda sai yaran gidan da jikoki na shigowa bayan me gadin ya bud'e musu, da sauri ta tashi farin ciki na mamaye ta, ta bud'e kofar ta sauka k'asa a dai-dai lokacin sun karaso balcony din, ta bud'e musu gami da rungume Rauda da take a gaba, dariya suka saka dukka Abbati na tsokanar su, suka shiga ciki suka zauna. Zuwan su ya saka ta manta tashin hankalin da take ciki, ta sake sosai suka dinga hira suna bata labari tana jin su, ta kwaso musu kayan abincin dazun suka cinye tas, sannan sukayi mata wanke wanke da dan gyaran gidan. Bayan nan sai ga yan biki daga gidan Hajiya Mama na ta shigowa ganin gidan amarya, hakan ya sakata sake shagala da abinda yake gabanta dan ko tuno shi batayi, sai yamma likis sannan suka tafi, su Ya Hadiza zasu zo gobe su kuma su kawo gara dangin su alkaki da su dublan, banda garar abincin saboda Hajiya Mama tace wa Abba ba sai anyi komai ba, duk daya ne shiyasa tun kafin bikin ma an dankare komai na abinci a gidan babu ce kawai babu. Bayan tafiyar su sai gidan ya koma kamar yadda yake kafin su zo, saurin kau da komai take na falon ta koma daki chan sama kar yazo ya tarar da ita sai ga aiken Hajiya Mama tana kiran ta, wasu yan mata ne su biyu aka aiko, su tafi da ita, sama ta koma ta chanja kaya ta fesa turare sannan ta sakko suka tafi, bayan ta cire key din da ke jikin kofar ta rik'e a hannun ta. Gidan na nan kamar ba'a gama bikin ba, dankare da mutane duk sai kunya ta kamata ta dinga sunnewa tana gaishe su har suka dangana da falon Hajiya Maman in da suke dukkan su a zaune, shi ta fara cin karo dashi yana kallon kofa, ya mike kafafun sa a tsakiyar falon suna hira da Maman yana ta dariya tamkar ba shi ba, tsoro taji ganin irin kallon da yayi mata, ta sauke kanta k'asa ta karasa da k'yar tana harharde kafafu kamar zata fadi. Sai da ta zauna sannan ta gaida Maman ta amsa a sake tana nuna mata gefenta. "Dawo nan Asma'u." Da jan jiki ta matsa ba dan ta so ba, suka sa Maman a tsakiya shi da ita, ta shiga yi musu nasiha cikin sigar lallashi, wanda gaba daya a kaikaice da Asma'un take, duk nasihar akan yadda zata kula da adam din ne, da dukkan al'amuran sa, tana jin ta har ta gama sannan tace ta taso su je daki akwai sirrin da zasuyi, su Nadeeya suka fashe da dariya suna tsokanar Maman ta ja hannun Asma'un suka shiga ciki,suna shiga ta kalle ta tace "Alfarma nake nema asma'u, ga yayanki nan Adam, dan Allah asma'u ki taimaka min, Adam ya dawo cikin nutsuwar sa, kiyi kokari wajen jawo Adam jikin ki, dan Allah ki yi kokari wajen ganin ya bar dukkan abubuwan da suke mara kyau, Adam yana son ki zaki iya amfani da soyayyar da yake miki ki dawo dashi kan gaskiya, babu me iya yi min wannan alfarmar sai ki, kiyi hakuri ki danne duk abinda zai biyo baya, a karshe zamu ci riba, kinji? Dan Allah. A duk maganganun Mama babu daya da ya tsaya mata a rai wanda dama bata sani ba face wai Adam yana son ta, wai Adam yana son ta. Ta tabbata a kaf duniyar nan babu wacca Adam ya tsana sama da ita, da za'a bashi bindiga ace ya harbe mutum daya ta tabbata ita ce, haka take itama a wajenta, tana jin tsanar sa sosai a zuciyar ta, tsanar da bata taba yiwa wani mahaluki ba, bata son ganin ko da fuskar sa ce, dan ta gama tabbatar da rashin imanin sa, bashi da kirki lamba daya, ta yaya ake tunanin zata iya gyara shi, bayan shi a ganin sa babu wani abu da yake mara kyau? Bayan ba dauke ta a matsayin mutum me daraja ba? Tana ji Maman ta cigaba da magiya, ta amsa mata da kai dan bata san kuma me zata ce mata ba, ba zata taba fahimtar ta ba, tunda ta riga ta saka son kai a cikin al'amarin auren masu, wanda ta tabbata tayi hakan ne saboda personal interest dinta, ba wai dan alakar ta da abban su ba, ba kuma wai dan soyayyar da take ikirarin Adam din nayi mata ba. Fitowa sukayi in da suka bar su, ta koma kusa da su Nadeeya ta rabe tana jin hirar da suke, kiran sallar magriba ya tashe su daga wajen, ta bi bayan su Nadeeya zuwa daki, sukayi sallah tana zaune a gefen gado suka idar, sai suka cigaba da zama a dakin suna hirar karatu. Mama ce ta aiko ta zo, ta fito ta ganshi a tsaye ya jingina da bangon falon. "Bishi kuje asma'u, zaa aiko muku da abinci wai Ashe tun da ya fita be koma gidan ba." Murmushin yake tayi, gabanta ya hau dukan uku uku, yayi mata alamar su je yana nuna mata hanya, ta shiga gaban sa ya take mata baya yana murmushin mugunta. _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* *RM*        8 _SAKINA VENDIBLES_ _SAKINA VENDIBLES_ _SAKINA VENDIBLES_ _(INDE HARKAR TURARUKA NE MASU KAMA JIKI DA GIDAH KAI HARDA TSUGUNNO. SAKINA VENDIBLES ITACE KAN GABA)_ _SUNA DA KAYA INGANTATTU MASU MATUKAR KYAU AKAN FARASHI MAI RAHUSA.)_ _KINASON ASAN KIN ISA MACE? WADDA ZAKUYI GOGAYYA DA MASU SAKA DESIGNER TURARE AMMA KI FUSU KAMSHI? DUK INDA KIKA GIFTA ASAN EH. KEDIN TABANCE , KIN ZARCE SAURAN MATA)_ _AKWAI KHUMRAH WHITE AND BLACK_ _KULACCAM BLACK (FOR HAIR( AND WHITE FOR BODY_ _WASU DAGA CIKIN KAYAYYAKIN MU SUN KUNSHI👇_ Turaren wuta list*  Queens special Kajiji mix Kajiji whole Gabgab Brown Hawiii Special Halut Sandal balls Sandal strips Sandal flakes Dubai oud White Hawii Classy Dufr Black bange Black bange Musky Dorrot(Na tsuguno) Cous cous *_DA SAURAN SU DA YAWA_* *_Handles_* *Instagram* @sakina_vendibles *Facebook* @Sakina vendible *Tiktok* @Sakina vendibles_ ***Tafiya take ba tare da ta san ina take wurga kafarta ba, kasancewar shi a bayan ta, ya hana mata dukkan nutsuwar ta, har suka isa gate din gidan ta ja ta tsaya, ya karaso yana wuceta ya kwankwasa kofar, mai gadi ne yazo ya bud'e da sauri, ya wuce ciki ta bi bayan sa a darare, be kula taba har suka shiga ciki, yayi hanyar bedroom din sa hakan ya saka ta tunanin ko ya rabu da ita ne, tayi saurin yin hanyar dakin ta, ji tayi an fizgo ta da karfi, har sai da ta bugu da gefen bangon da yake tsaye. "Dan Allah kayi hakuri!" Tace cikin muryar ta gwanin ban tausayi. "Ni kika ciza? Ni!?" Ya nuna kansa still yana rik'e da ita gam. Girgiza kai tayi da sauri alamar a ah, murmushi yayi ya shiga janta zuwa cikin dakin, yana zuwa ya wurgar da ita a tsakiyar dakin ta durkushe da sauri. "Kwashe kayan nan dukka ki wanke su a toilet din nan, kuma minti goma kawai na baki, idan kika wuce haka sai na yi k'asa k'asa dake!" Kallon tarin boxers da singlets dinsa tayi da yace ta wanke a minti goma, ta hau tattare kayan da azama, komawa yayi ya zauna akan couch yana duba agogon wayar sa, " Kuma su fita sosai wallahi, useless!" Da sauri take komai, ta tara ruwan ta shiga wanke su da sauri tana kuma saka karfi wajen dirza su sosai. Wayar da ya saba ya shiga amsawa hakan ya mantar dashi duba lokacin da yake har ta gama tas ta fito dasu a cikin bucket. Hada ido sukayi ya harare ta ya cigaba da wayar, ta fita ta zagaya chan baya wajen abun shanya ta shanya su dukks sannan ta gudu dakin ta. Bayan ya gama wayar ya zo ya murda kofar yayi tsaki ya fice daga gidan. Washegari su Ya Hadiza suka kawo gara suka tafi ba su wani dade ba, tun daga nan da ta ga kafa ta dauke ta daina yarda su hadu, kafin ya dawo ta dauki abinda zata dauka ta shige daki, har ta samu tsarki ta soma sallah ta shiga kaiwa Allah kukan ta, dan shi kadai ne zai yaye mata damuwar ta. Watarana bayan magriba haka tayi sallah ta idar, ta koma ta zauna ta dauki wayar ta, tana dannawa rabin hankalin ta yana kan chatting din da suke da Rauda har bata ji motsin komai ba, sai ji tayi an bud'e kofar, ta saki wayar ta fadi garin mikewa tsaye. Fuskar sa a hade tamau babu alamun tausayi ko sassauci, wajen da take yayo gadan gadan, tayi yinkurin guduwa ya tarde ta, tayi kamar zata fadi, ya tare ta da hannun sa ta fado jikin sa, ya daga ta chak ya fice da ita daga dakin duk ihun da take da magiya ko gezau be ba, sai da ya kaita dakin sa sannan ya jefa ta a saman gadon, ya koma ya sakawa kofar key ya rufe ya dawo in da ya barta tana kuka ya daka mata tsawa "Dan rashin mutunci na biya kudi nayi komai amma kice ba zaki bani ba, abun da gashi nan kamar banza kyauta ma ake raba mana shi bama so, ko dan kinga na damu? Taimaka miki nayi kar sha'awa ta kashe ki a gida ba aure, shine zaki dinga wahalar dani a banza." Yace yana huci, ya hawo gadon ya sake fizgota, ya murde mata hannu zuwa bayan ta sannan ya zuge zip din rigar ta har kasa ya yi wurgi da ita, idon ta, ta runtse tana cigaba da kuka. Kare mata kallo ya tsaya yanayi, kafin ya shiga sarrafa ta yadda yake so, ya kuma yana mata motsi ko kad'an, ya danne ta ko ta ina, yaci karfin ta, saddakarwa kawai tayi ta dinga jan kuka saboda yadda yake mata, babu digon tausayin ta, hannun ta da yake baya ya sage sosai yayi tsami saboda yadda ya danne su, numfashin ta taji yana sama-sama, ta dinga jin tamkar ranta zai fita daga jikinta saboda azaba. A hankali a hankali komai na jikinta ya saki, ta sume ba tare da ya sani ba! Afwan! normal posting zai fara in Sha Allah weekends. Nagode _SAKINA VENDIBLES_ _SAKINA VENDIBLES_ _SAKINA VENDIBLES_ _(INDE HARKAR TURARUKA NE MASU KAMA JIKI DA GIDAH KAI HARDA TSUGUNNO. SAKINA VENDIBLES ITACE KAN GABA)_ _SUNA DA KAYA INGANTATTU MASU MATUKAR KYAU AKAN FARASHI MAI RAHUSA.)_ _KINASON ASAN KIN ISA MACE? WADDA ZAKUYI GOGAYYA DA MASU SAKA DESIGNER TURARE AMMA KI FUSU KAMSHI? DUK INDA KIKA GIFTA ASAN EH. KEDIN TABANCE , KIN ZARCE SAURAN MATA)_ _AKWAI KHUMRAH WHITE AND BLACK_ _KULACCAM BLACK (FOR HAIR( AND WHITE FOR BODY_ _WASU DAGA CIKIN KAYAYYAKIN MU SUN KUNSHI👇_ Turaren wuta list*  Queens special Kajiji mix Kajiji whole Gabgab Brown Hawiii Special Halut Sandal balls Sandal strips Sandal flakes Dubai oud White Hawii Classy Dufr Black bange Black bange Musky Dorrot(Na tsuguno) Cous cous *_DA SAURAN SU DA YAWA_* *_Handles_* *Instagram* @sakina_vendibles *Facebook* @Sakina vendible *Tiktok* @Sakina vendibles_ RM*        9 *** Tsawon lokaci ya dauka kafin ya kyaleta ya fice daga dakin zuwa na kusa dashi, be tsaya duba halin da take ciki ba, sai da yaje ya watsa ruwa sannan ya dawo dakin ya tarar a halin da ya barta, ya dan tsorata ya dinga girgiza ta, ganin da gaske bata motsi ya sashi saurin samo ruwa ya zuba mata, aka yi sa'a ta dawo ta hanyar jan dogon numfashi, kallon sa tayi ganin shi durkushe a kanta ya sakata sake kidemewa har tana yinkurin tashi ta hau masa magiyar dan Allah yayi hakuri a cikin yanayin da duk rashin tausayin mutum sai ya tausaya mata, shi ko gogan ko oho, ganin ta farfado ya saka shi sake tsallake ta yayi ficewar sa bayan ya dalle mata baki na mugunta! Kasa tashi tayi a wajen, ta dinga jan jikinta da yake mata mugun ciwo zuwa dakin da kayan ta suke, da k'yar ta kai kanta a daidai lokacin taji karar fitar motar sa daga gidan. Toilet ta rarrafa da k'yar bayan ta shiga dakin ta hau gyara kanta tana yi tana kuka wiwi, kukan da sautin sa baya fitowa sai hawaye da yake ta ambiliya a fuskarta, yadda Adam yayi mata ya tabbata har da mugunta a ciki, be lallaba ta balle yayi mata a hankali, tana kuma kyautata zaton yayi mata babbar illa, ta dade aciki tana kuka sosai sannan ta sake rarrafowa ta fito zuwa bakin gadon ta nade a kasan carpet ta cigaba da gurzar kukan ta Ji tayi an shigo, sai dai ta kasa dagowa balle ta kalle shi, ajiye mata leda yayi a gabanta daga tsaye yace "Ki sha idan kin gama kukan, bana son raki wallahi. Mtsw!" Ya juya da nufin barin dakin "Kaji tsoron Allah, duk abinda kayi min Allah sai yayi mana sakayya." Tsayawa yayi chak ya fasa fitar, ya dawo ciki yana mata kallon mamaki "Hakkin nawa da kika hanani tsawon kwanaki shine kike ganin na cutar dake akai!? Dariya yayi sosai cike da mamakin ta " You are not serious malama , kadan ma kika gani idan dai nine wallahi, sai kin gwammace baki ja dani ba. " Ya juya yana sake jan tsakin da yafi na dazu, yayi ficewar sa, yana jin ta tana jaddada masa taji ciwo amma yayi biris, farin ciki na sake mamaye shi, be taba mu'amula da irin ta ba, sai yaji ta daban da duk sauran matan da ya taba Hulda dasu daga fararen fatar har namu na gida bakaken, sai dai a yadda ya dauki aure, da yadda yake ganin mace baa bakin komai ba, ya hanashi ya saukar da kanshi ya nuna mata kulawa, yana ganin bata isa ba! Bata kai wannan matsayin ba, be taba tausayin mace ba, balle har wata aba soyayya ta shiga tsakanin su, abu daya ya sani kawai shine, idan tayi masa sai ya dandana ko ta halin kaka, amma fa daga daya baya karawa wasu ma, idan ba irin Fido da ita kadai ta san logon sa ba, amma kuma Asma'u, ta musamman ce a wannan bangaren, amma baya jin zai iya sauko da kansa har ya nuna mata tausayi ballantana raini ya shiga tsakanin su. Kuka ta cigaba da yi a wajen ba tare da tasan madafa ba, sai wajejen sha biyu na dare sannan ta sake tashi ta koma toilet, ta fito daure da alwala amma ba zata iya sallah a tsaye ba, sai kawai tayi a zaune tana idarwa ta sake kwanciya a wajen zazzabi na sake rufe ta sosai. Washegari ta tashi da mugun zazzabi, ita kadai a gidan dan ko motsin sa bata ji ba, bata iya ko mikewa bare tayi ma kanta wani abu, haka ta cigaba da kwanciya a wajen kamar zata mutu, tun tana kuka da hawaye har ta daina idon ta ya soye. Chan wajen azahar taji ana buga kofa da dan karfi, kofar shigowa falon su, sai kuma taji maigadi na sake tabbatar mata tana nan dan be ga fitar ta ba,tana jin su har zuwa lokacin da taji ana bud'e kofar da key, sai muryoyin su yana mata bayanin ya dan fita ne, Nadeeya ce kila kiran sa tayi a waya, dakin kasan da Asma'un take ciki ta shigo, tayi saurin yin kanta ganin ta a kudundune cikin rawar sanyi. "Boy!" Ta kwala masa kira tana dagota zafin jikin nata ya bata tsoro, "Kaji jikin ta kuwa? Baka san bata da lafiya bane? Ko ya akayi?" "Ban sani ba fa, bata fad'a min ba kuma har dazu da mukayi sallama na fita, zazzabi ne?" Yace kamar be san komai ba "Bana son haka Adam, ya zaka fita ka bar matar ka a wannan halin kace sai ta fad'a maka, ya kamata ace ka sani ai, sannu asma'u, zo ka taimaka mata ta kwanta a saman gadon nan na duba ta sosai." Kamar ba zai zo ba, sai kuma ya saki kofar da ya toge da ita da ya shigo ya dagata chak ya dora a gadon, zafin kasan ta ya sakata runtse idon ta, tayi yar kara, karar da ta ankarar da Nadeeya din ta kalle shi da sauri ta kalle ta. "Boy!" Ta kalle shi da sauri a tsorace, sai kuma tace ya fita, ya juya yana bouncing ya fice gami da ja musu kofa cikin nuna halin ko in kula, daga ta tayi ta dora mata kanta a saman pillow, sannan ta dauko ruwa ta bata a hankali tasha cikin tausayin ta tace "Ya ji miki ciwo ne?" Kasancewar ta nurse ta fahimci komai, da ka Asma'un ta amsa mata hawaye na bin kuncin ta. "Kiyi hakuri, bari na duba ki.". Tace tana gyara wa, ta taimaka mata ta gyara sannan ta duba ta, a tsorace tace "Naa shiga uku!" "Amma Adam bashi da hankali wallahi, sai kace mahaukaci." Zama tayi dabas a wajen cikin tausayin Asma'un, sai kuma ta dauki wayarta ta kira shi, ya shigo ya tsaya a kofar ta harare shi kamar ta rufe shi da duka tace "Me kasha? Kana hauka ne ko me?" "Sis!" "Ba wani sis, ba zan taba goyon bayan cutarwa ba, Asma'u yar uwarka ce makusanciya, why will you do this to her, wannan pure wickedness ne ban yarda da wani silly excuse ba." "Ita ta fad'a miki!? Matsala aka samu fa, ita ta jawo komai." Sake hade fuska tayi cikin fad'a tace "Baka ma yadda kayi laifi ba kake sake bata laifin, lallai." Sosa kansa yayi yana dariya kasa k'asa, hakan ya sake kular da Nadeeya ta kuma sake tabbatar da rashin mutuncin kanin nata. Hanya ta nuna masa alamun ya fita ya bata wuri.fita tayi itama ta dauko wayar ta, ta kira wata abokiyar aikinta tace zata zo da patient a duba ta, sannan ta dawo ciki ta taimaka mata suka fito zuwa wajen motar ta, yana kallon su yana tsaye suka fita be ce musu uffan ba, asibitin su ta kaita, aka duba ta sannan tace a bata gado tana bukatar Hutu, aka saka mata drip har yamma suna asibitin sai da ta dan samu karfin jiki ta bata abinci ta dan ci kad'an sannan suka dawo gida, bayan sun dawo ma bata tafi ba sai da ta sake taimaka mata tayi wanka ta bata magunguna sannan ta tafi a zuwa zata dawo da safe ta sake dubata, ta bata shawarwari sosai ta kuma gargade ta akan sake yarda dashi, dan komai zai iya faruwa ta bari ta fara healing shi ma zata masa magana kuma ta sake masa fad'a akan abinda yayi. Ba karamin dadi taji da abinda Nadeeya tayi mata ba, bata taba tunanin tana da kirki haka ba, babba ce kusan sa'ar Ya Hadiza, tayi aure ta fito bata sake ba tun daga lokacin har kawo yanzu. Dakin ta sake rufewa dan ta tabbatar da bashi da ishashen hankali zai iya dawowa a kowanne lokaci wanda ta san idan hakan ta kasance zata iya rasa ranta ma ba suma ba saboda ita kadai ta san azabar da tasha. Satin ta guda tana jinya bata sakashi a idon ta ba, tana jin motsin sa da wayar sa amma be yi ko attempt din zuwa in da take ba, bata sani ba ko fad'an Nadeeya din yaji, ko kuma yana tama ta ne kamar wanchan lokacin oho. Nadeeya kullum sai ta shigo ta taimaka mata ta kuma bata magungunan ta, hakan ya taimaka mata sosai wajen samun sauki da wuri, bata fadawa kowa ba dan wannan ba maganar da zaka fad'a bace, sun yi waya da yan gidan su har da umma amma ta kasa ce musu komai akan irin zaman da take a gidan Adam din, ta dauki hakan a matsayin jarrabawar ta dan kaf gidan su babu wanda yake auren miji irin nata, kowa daidai gwargado suna zaman su cikin mutunci da kaunar juna. Kwana wajen uku ta daina jin motsin sa, Ashe tafiya yayi bata sani ba, daga fuskanci baya nan sai ta fito ta sake sosai tana harkar ta, gidan yayi mata dadi sosai kamar ta dawwama a haka babu shi. Ranar tana zaune a falon kasan bayan Hajiya Mama ta aiko me aikin ta, ta kawo mata sinasir da miyar taushe ta gama ci kenan ta dawo falon ta zauna sai taji ana saka key a kofar, dama dare ne wajen takwas ma tayi, mikewa tayi dan bata ko ji karar bud'e gate ba bare shigowar sa, shine a gaba tana biye dashi kanta babu rufi ya sha uban attachment har gadon bayan ta, zuba mata ido yayi yana takowa cikin falon, tayi saurin yin hanyar sama ya rigata cikin sassarfa ya riko ta, Fido dake biye dashi ta tamule baki cikin jin haushin shi, kwace hannun ta tayi, ta haye da sauri ya tsaya yana bin bayanta da kallo har ta gama hawa, sannan ya dawo da ganin sa kan Fido da ta hade rai "Menene haka Lion?" "Me kika gani?" Yace yana zama a inda Asma'un ta tashi. " "Baka ga me kayi ba?" Tace cike da kulewa " Me nayi?" Ya dage mata gira yana baje hannayen sa a saman kujerar "Menene na wani riko ta kamar irin kayi missing din nan nata." "Missing? Ni nace miki haka? Warning kawai nake so nayi mata, baki tsaya kin ga komai ba amma har kin yanke hukunci." ", Shikenan." Tace tana zama a kusa dashi, ta kwantar da kanta a kan kirjin sa, ya juyar da fuskar sa dayan side din sabon tunani na bijiro masa. Dafe kirjin ta, tayi bayan ta shigo daki tayi gaggawr sakala key ta kulle sannan ta zauna tana maida numfashi, macen da ya shigo da ita ta dinga hasasowa a idon ta, lallai Adam ya shahara, tunda har zai iya kawo mace gidan auren sa, ba tare da fargaba ko dar ba. Bata damu ba, idan ma dari zai kawo matsalar sa ce, ba zata dai yadda kuma ta sake hada jiki dashi ba. Saman taji sun hawo, suna kyalkyala dariya cikin yanayin da ta hasaso a ranta, dakin sa suka shiga gami da murzawa kofar key, shiru bata sake jin motsin su ba.. ishirwa taji tana ji, ta manta bata hawo da ruwan ba na saman ya kare, tashi tayi ta sallalaba ta fita xuwa kitchen din kasan, ta dauko ruwan kenan yana shigowa kitchen din, yi tayi kamar bata ganshi ta, tayi kokarin rab'awa ta gefe zata fita ya tare hanyar yana bin ta da kallo. "Zan wuce!" Tace a dake "Ba zaki wuce ba!" Yace yana matsowa "Sauri nake please ka matsa." "Anki a matsa din, saboda Sis ta hure miki kunne shine har kike da bakin fad'a min magana, wai tsaya ma, baki san nayi tafiya ba? Baki san ki duba mutum yana nan ko baya nan ba, kin fiso ma idan bana nan ko?" Wani banbarakwai taji maganar tasa, ta kalle shi a kaikace ta sake kokarin rabawa zata wuce ya kamata ya hada jikin sa da nata, ta fizge da karfin gaske, ruwan ya fadi kasa tayi ficewar ta, ta barshi tsaye cike da takaicin abinda tayi masa, lallai ma yarinyar nan, sai kuwa ya koya mata hankali dan yaga kamar ta manta waye Adam, ko dan taga kamar ya sakko yana mata magana a nutse, tsaki ya ja mayen kamshin turaren ta da ya cika kitchen din ya shigar masa har makoshi, sink ya nufa ya kuskure bakin sa sannan ya dau ruwan ya fito. _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* RM*        10 ***Da asubah Fido ta bar gidan bayan ya sauke ta a gidanta da take zaune wanda shine ya kama mata shi yake biyan kudin hayar gidan tsawon lokacin da suka sauka a tare. Gida ya dawo direct ya wuce daki ya kwanta babu batun sallar asubah a lokacin burin sa kawai yayi bacci dan ba wani isashen bacci suka samu a tafiyar da sukayi ba ta bikin abokin sa Chairman shiyasa yake jin tamkar idonsa zasu rufe saboda bacci. Sallar asuba ta idar ta zauna a wajen tana karatun al'qur'an har gari yayi sha sannan ta tashi ta gyara dakin ta koma ta dan kwanta zuwa takwas ta mike, so take ta shiga gidan Hajiya Mama shiyasa ta ki bari ta koma baccin safen. Wajen goma ta gama abinda take ta bud'e kofar ta dan leka ta tabbatar baya nan sannan ta fito ta rufe kofar a hankali ta fita. A harabar gidan suka hadu da Nadeeya zata fita, tsayawa tayi suka gaisa ta sake tambayar ta jikin ta, a kunyace ta amsa mata tayi godiya ta fice ita kuma ta shiga ciki. Hajiya Mama na zaune a falo tana breakfast, ta saki fuskarta sosai ta hau yi mata sannu da zuwa "Dama ina shirin yi wa Adam korafi, idan ya fita kiyi tahowar ki nan kiyi zaman ki, chan ai sai kadaita ta dameki." "Ina kwana?" Tace tana durkusawa k'asa "Lafiya lou wallahi, zauna mana." A kunyace ta tashi daga tsugunan ta zauna daga gefe, Hajiyan ya turo mata tray din dake gabanta "Maza ci abinci, bari na watso ruwa nazo." "Naci abinci Mama." "Gidanku, maza dauki ki zuba kici wani abincin kirki kake iya ci ne, Nadeeya ma tace min baki ji dadi ba, ban sani ba wallahi sai yau take fad'a min, ni dai nace Allah yasa addu'a tace Allah ya amsa min." "Uhumm..." Tace cike da kunyar Hajiyar, fuskar ta cike da farin ciki ta shiga ciki, ta bar Asma'un da tunann maganganun ta, bata jima ba ta dawo ta zauna, ta shiga jan Asma'un da hira cikin sigar son bugun cikin ta ko taji wani abu dangane da zaman nasu, dazu take maganar Asma'un anan Nadeeya take ce mata ai bata ji dadi ba ma, daga haka kuma bata sake ce mata komai ba, shiyasa tayi tunanin ko cike ne da Asma'un, tayi niyyar dama anjima ta shiga gidan nasu sai kuma ga Asma'un ta hutashsheta ta shigo, bata samu amsar dukkan bayanan da ta nema wajen Asma'un ba dan kamar kunyar Hajiyan take ji sosai hakan ya sake tabbatr wa da Hajiyan Asma'un cikin ne. Har sha biyun rana suna zaune a falon in da Hajiyan ta saka aka ajiye mata abubuwa masu yawa a gabanta duk wani abu da tayi tunanin zata ci sai ta saka an ajiye mata, ita abin ma sai ya dinga bata dariya da mamaki, bata dai nuna komai ba, ta dai jinjinawa kokarin Hajiyan da kuma irin soyayyar da take wa Adam din nata. Cikin shigar dakakkiyar shadda coffee colour ya shigo falon, sosai shigar ta karbe shi ko dan be saba irin ta ba? Kallo daya Asma'un tayi masa ta kauda kai dan ita sam bata ga abun kallo a wajen mutum irin Adam ba, wanda yake da kyawun dan miciji. "Shine kika taho kika barni ko? Bayan nace ki jirani mu zo tare." Kallon baya asma'u tayi a tunanin ta da wata yake, sai kuma taga ya nufo ta, yana sake son tabbatar mata da itan yake, yak'e ta hau yi ganin idon Hajiyar na kansu tana ta murnushin jin dadi, dungure mata kai yayi yace "Punishment dinki kenan na tahowa ki barni, gobe ma kin kara." "Gidanku Adam, karka kara dungure mata kai, wani ya hanaka tashi da wuri?" "Toh ai laifin ta ne fa, ita ta hanani baccin jiya, shine kuma ta taho ta barni." Mutuwar zaune tayi, bata taba sanin akwai maza makirai ba sai yau, kallon sa take shima kuma ita yake kalla idon sa fes a kanta, ya harare ta, ga gefe ba tare da Hajiyan ta gani ba, tayi saurin sauke kanta k'asa mamakin sa na sake girmama a ranta, ya wuce duk in da take tunanin sa. Be sake bata mamaki ba sai da taga ya zo ya zauna daf da ita yana cigaba da tsokanar ta, wanda ta lura ba karamin dadi hakan yayi wa Hajiyar ba. Anan suka ci abincin rana, ko da tace zata tafi sai Hajiyan ta hanata, ganin su a tare a hakan yayi mata dadi ainun, ta dinga hasaso yadda komai zai daidaita a rayuwar Adam din ta. Sai da akayi la'asar ta barta ta tafi lokacin shi ya ma riga ya fice wai zai raka wani abokin sa neman aure. ***Gidan su take son zuwa, gashi bata san ta ina zata fara sanar dashi ba, tasan haramun ne ta fita bata tambaye shi ba, amma kuma bata san ta ina zata fara tambayar ba, ita kadai take sakawa da warwarewa har tara na dare be shigo ba, ba jiran sa take ba dama, amma kuma tana ankare da duk motsin sa. Bacci ne ya soma daukar ta, ta mike daga zaman chatting din da tayi da su Hidaya ta je ta dauro alwala tayi shafa'i da wutri tazo ta kwanta bayan ta rage kayan jikin ta, ta daga curtains din dakin yadda iska zata shigo sosai. Bata san yaushe ya shigo ba, cikin bacci bacci taji ana taba ta, ta tashi a firgice, ya rik'e ta gam yana toshe mata baki. "Hakki na nazo karba, kikayi gardama na sake miki kacha-kacha." Gumi ne ya shiga karyo mata, tana tuna bakar wahalar da tasha a wajen sa waccar ranar, magiya ta soma masa da hada shi da Allah amma babu alamun zai ji ta balle ya tausaya mata, tunanin yadda zata kwaci kanta ta hau yi dan kuwa idan bar ta amince masa akwai matsala bata gama warkewa ba har yanzu dan kusan kullum sai ta shiga ruwan dumi take jin dadi, dukkan karfin ta, ta tattaro ta hankade shi, ta mike tayi hanyar barin dakin duk da duhun da ya mamaye ilahirin dakin, shaf ta manta gaba daya da kafar benen dake wajen, burin ta kawai ta tsira da ranta, ji tayi kamar ta taka abu me tsantsi, sai kuma taji ta zame ta kwalla kara gami da zamewa ta fadi a wajen, kanta ya bugu da karfin stairs din ya fasa mata saman goshin ta! *mg's skincare* Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩 Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️ Shin kinafama da Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata? Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫 Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind Bridal kit:18k Beauty kit:11k Student package:7k Herbal whitening soap:3k Chat 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Facebook: mg's skincare Instagram:glow_with_mgs Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝 Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩 Then @mgs skincare gat you covered 💯 Now is time to glow😍 Pamper ur skin🦵 Shine like bride👰🏻‍♀ Glow🧖‍♀️ 💯 tested nd trusted🤝 Guarantee Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166 RM    11 Akan hannun ta ta fadi, tayi kara me karfi, be fito ba, ya tabe baki cike da haushin ta. Kokarin tashi tayj amma sam ta kasa motsa hannu, wani irin zugi yake mata ga goshin ta da yake fidda jini sosai. Kuka take sosai ta shiga kiran sunan sa  "Ya Adam! Ya Adam! Zan mutu dan Allah ka taimaka min!" Yi yayi kamar ba zai zo ba, sai kuma wani abu ya darsu a ransa ,ya mike da sauri yayo wajen, a yanayin da ya ganta ne ya saka shi karasowa a guje "Tashi! Tashi!" Ya hau ce mata a kideme dan be yi tunanin hakan ba, ganin ta soma zama unconscious ya saka shi dagata chak ya sauka da ita da gudu gudu, ya shiga kwala wa me gadi kira,sosai kanta yake zubda jini ga hannun nata da ya tabbatar da ya samu matsala. Direct asibiti ya wuce da ita, bayan ya kira Nadeeya da wayar sa daya da ya bari a mota, a kidime ta amsa masa tace gata nan sannan ta kashe ta kira Hajiya Mama tace mata Asma'u babu lafiya sun tafi asibiti, itama Hajiyan ta tsorata sosai, ta dinga kaiwa da komowa har sai da driver ta da ta aika ya dawo, sannan suka dauki hanyar asibiti .    Taimakon gaggawa aka shiga bata, aka samu aka tsaida jinin goshin mata amma sai da akayi mata dinki a wajen, sannan aka tabbatar masa da ta samu karaya a hannun da ta fadi a kansa, ji yayi kamar almara, ya dinga kallon ta a karon farko yaji burburshin tausayin ta ya wanzu a zuciyar sa, dakin da aka kwantar da ita ya tura ya shiga, ya tarar tana kwance tana fitar da numfashi daidai na azaba, wayar sa ya daga da Nadeeya ta kirashi, ya juya ya bar dakin yana amsa wayar da kwantancen dakin da suke, kusan a tare suka iso da Hajiya mama dan ita Nadeeya din daga nesa take, dukkan su a rude suke, suka isa dakin Nadeeya ta riga mama isa gaban Asma'un tana kallon hannun ta "Karaya?" Tace cike da tashin hankali "Innalillah wa inna ilaihi rajiun!" Hajiya mama ta fad'a tana kallon Adam din cikin son karin bayani "Faduwa tayi wallahi mah, a wajen sauka daga stairs bansan dame ta zame ba, wallahi ban sani ba." Wani kallo Nadeeya ta masa, ta kalli Maman ta fita zuwa wajen Drs din. "Garin yaya haka ta faru Adam? Garin yaya?" Girgiza mata kai yayi, yana jin wani iri, abun da be taba ji ba. "Fad'a kukayi? Ko dama chan har yanzu akwai matsala ne?" Girgiza kai ya sake yi, ta matsa ta taba jikin Asma'un da ya rure da zazzabi me zafin gaske "Me zance wa mahaifanta? Waye kake ganin zai yarda da cewa faduwa tayi? Bayan kowa ya san yadda akayi auren nan, sannan kowa ya san halin ka." Bashi da bakin magana, domin shi kansa be san bakin da zai yi amfani dashi wajen kare kansa ba, adah idan aka ce zai russuna haka har yaji tausayi irin haka zai karyata, amma kuma ya rasa dalili, sosai yake jin tausayin ta musamman ganin irin bakar wahalar da tasha a yanzun, karaya ba abu bane me sauki musamman a wajen wanda ya soma girma ba kamar yara kanana ba, ya taba samun dislocation sanda yana tashen ball ya san wahalar da yasha a lokacin ballanta na ita, yana jin Maman tana ta maganganu be ce komai ba, be kuma bar dakin ba, har zuwa sanda Nadeeya ta dawo da ya lura tana fushi dahsi sosai, har zuwa lokacin da Maman ta kira Abba a waya ta sanar masa.    A tunanin sa zasu zo a take a lokacin, amma babu wanda yazo, da Hajiya Maman ta sake kiran Abban sai yace mata babu komai su ma sun isa zasu shigo da safe, hakan ya sake karyar wa da Hajiyan guiwa, taji da gaske bata kyauta ba, bata yiwa Asma'un adalci ba kuma ba ta yiwa mahaifin yarinyar hallaci ba, ya dauke ta ne tamkar uwa mahaifiya ya kuma amince mata yana bata dukkan girman ta, son kai ya kwashe ta da aikata abinda ba zata taba yafewa kanta ba.    Kwanan zaune sukayi saboda yadda hannun ya matsa mata, sun tausaya mata dukkan su, har shi uban gayyar da ya zama so silent kamar bashi ba, sai gabannin asubah sannan ta samu wahalallen bacci ya dauke ta.    Toilet mama ta shiga tayi alwala Nadeeya ta tsaida shi ganin zai fita, ta tsare shi da ido cikin tuhumar sa tace "Me kayi mata?" "Naam?" "Tsorata kawai tayi ba, shine ta fito da gudu ta fadi, wallahi ban mata komai ba." Ranta ne ya sake baci sosai, ta nuna masa kofa jin Maman zata fito, ya fice da sauri yana sake rejecting kiran Fido da take ta jera masa shi tun daren. ***Abbati ne yazo tare da Abba wajen takwas lokacin Adam din ya bar asibitin yaje dauko mata kaya, nan fa Hajiya Mama ta saka wa Abban kuka, ya dinga bata baki yaki yarda ya nuna damuwar su ko wani abu, ya kuma sake jaddada mata hakan kaddarar Asma'un ce, babu wani da ya isa ya hanata faruwa. Be jima ba yayi mata addu'a ya tafi, ya bar Abbati saboda ko za'a nemi wani abin tun da Adam din baya kusa.    ***Waya umma suke da Ya Hadiza ta fad'a mata abinda ya faru, kuma Abba yace ta kyale Hajiya Maman suyi jinyar kar ma tace zata je ta zauna, hakan ba karamin bata mata rai yayi ba, a kalla dai a barka ka zauna da danka dan yafi bukatar ka akan kowa, hakuri Ya Hadizan ta bata tace gatanan zuwa gidan zata kuma kira Abban a waya, ajiye wayar sukayi umma ta cigaba da shirin tafiya asibitin dan ma yace ta jira Abbati ya dawo ya kaita da tuni ta tsufa a chan dan ba zata iya jurewa ba, dama ta san za'a rina ai tunda aka hada Asma'un da mahaukacin miji.    Har Yaya Hadizan tazo Abbatin be dawo ba, sai kawai umman ta fito suka tafi, a hanya take fad'a mata yadda sukayi da Abban, yana nan akan bakansa be yarda Umman taje ta zauna ba, ya dai amince taje kullum amma ba wai da zuwan zaman jinya ba, ran Umman ya sake sosowa ainun, bata taba yi wa Abban bore ba, tun auren su take masa biyayya daidai gwargado, ba zata bijire masa ba a yanzu musamman da girma yazo, amma bata ji dadi ba, kuma shima ya san be kyauta mata ba. "Allah Umma kina da hakuri sosai, anya akwai wadda tayi hakurin ki kuwa a cikin mu?" Murmushin umman tayi, sak Asma'un itace, baki daya halayen ta irin na Umman ne shiyasa take tausaya mata, bata da zafi ko kad'an hakan ya saka tun da ma kowa taka ta yake, ballantana kuma ta hadu da miji irin Adam. Har suka isa asibitin ran Umman be saki ba, ta daure dai kawai suka shiga ciki. Adaidai lokacin Asma'un ta farka, zafin ciwon ne ya farkar da ita, babu wanda be tausaya mata ba, dan ma tana da masifar dauriya, gefe umma ta koma ta dinga share hawaye, zata sake lallaba Abba ita dai ya barta tayi jinyar yar ta, ko ta koma gidan ba zata taba samun nutsuwa ba, ba wai kuma dan tana ganin ba za'a yi Asma'un abinda ya dace ba, sai dan kawai dai wani abun dole sai uwa mahaifi.    Ganin su umman ya sakata sake jin ciwon na dawo mata sabo, tun bayan auren bata ga umma ba, dama jiyan take so ta tambaye shi taje ta wuni dan tayi kewar gida sosai, sai ga tsautsayin da ta gamu dashi.    Allura akayi mata da zata rage mata zafin ciwon, hakan ya saka ta dan samun nutsuwa. Kin motsawa nan da chan Hajiya Mama tayi dan tana tsoron ta bar su Asma'un ta fad'a musu abinda ya faru duk Adam din ya rantse mata be mata komai ba amma bata yarda ba, tana kyautata zaton yana da alaka me karfi da abinda ya farun.    Har yamma likis su umma na asibitin duk su Hidaya sun zo da yan uwan umman, Adam ma ya dawo amma be sake shigowa dakin ba tsakanin sa dai wajen zuwa wajen Drs sai idan abu ya taso haka suje da Abbati. Su kansu su Ya Hadiza sai da sukayi mamakin sa, sun ga sauyawar sa sosai har suka yi tunanin ko dama ya chanja bayan auren dan aure na  chanja mutane da dama.     Bayan sun yi sallar magriba sun dawo da yaga an ragu sosai a dakin sai ya shigo, da sauri Asma'u ta rufe idon ta Hajiya mama ma ankare da ita, a dan baya ya tsaya ya gaida umman da rabon su dashi tun bikin, ta tambaye shi me jiki ya amsa kansa a k'asa tamkar ma kirki. "Ya jikin?" Yace yana kallon gadon da take kwance, bata amsa ba ta sake rufe idon ta sosai, umma dake zaune daga gefe ta dan leko ta "Inaga ta samu bacci." Juyawa yayi ya fice duk suka bishi da kallo hatta Maman na cike da mamakin Adam din, kamar wanda aka chanjo mata shi da wani daban, shiyasa ta sake tabbatar da sanin sa, fatan ta daya Allah yasa ba turo yar mutane yayi daga benen ba ma, dan babu wanda ya san ainihin me ya faru ya dai ce zamewa tayi ta fadi.     Tana jin ya fita ta saki kuka me cin rai, bata son sa bata kaunar sa ko kad'an, bashi da tausayi bare imani ko na digo, kanta sukayi dukka kowa na tambayar ta menene, bata ce komai ba, ta dinga kukan ta a hankali wanda kusan duk sun dauki hasken dalilin kukan nata, yana da nasaba da shigowar Adam did, kunya duk ta kama Hajiya Mama, ta dinga borin kunya tana so ta dauke hankalin su daga kan Asma'un amma kuma sun riga sun gane komai.     Sanda su umma suka zo tafiya tayi bacci, dan haka bata san sun tafi ba sai chan wajejen sha biyu na dare da ta farka ta ganshi zaune akan kujera yana danna waya, kansa a kasa yana ta murmushi, wurga idon ta tayi zuwa sauran sassan dakin, babu kowa sai shi kadai ya bada dukkan attention dinsa akan wayar. "Zan sha ruwa." Ta furta tana kallon gefe, dagowa yayi ya kalle ta, ya dauke kansa ya cigaba da danna wayar sa, ta sake maimaitawa a karo na biyu nan ma yayi biris.   Jujjuya hannun ta, ta dinga yi mara ciwon cikin jin ishirwa sosai, ta yi kokarin daukar na ajiye akan bedside drawer din asibitin amma ta kasa, yayi kamar be san me yake faruwa ba, sai da ya gama abinda yake tas, sannan ya tashi ya dauki ruwan ya mika mata. Kautar da kanta tayi alamun bata so, ya dire mata a wajen ya fice gami da jawo mata dakin! _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* RM    12 ***Tun da ya fita be sake dawowa dakin ba, har drip din da yake hannun ta ya kare, jini ya soma biyo hannun. Tsoro taji, ta shiga kiran nurses din amma babu wanda ya shigo,akwai yar tazara tsakanin nurses lounge din dakin da aka kwantar da ita, gashi ba zata iys kashewa ba saboda dayan hannun ko motsa shi bata isa tayi ba, cigaba da kallon robar da drip din ke sauka tayi, wani guntun hawaye ya ziraro zuwa saman kuncin ta, ta gaji sosai da zubar da hawayen ta, zuciyar ta zafi kawai take mata, bata san dalilin da ya saka aka barta daga shi sai ita ba, ya kamata ace mace ta zauna ko da kuwa Yaya Hadiza ce idan Umma tana jin nauyin Hajiya Mama, ji tayi duk ta soma jin haushin su, tunda ita bata san abinda ya faru ba, Hajiya Mama ce ya kamata ta zauna amma sai ya nuna mata shi zai zauna, ya dinga mata magiya ganin cewa ai mijin ta ne ya saka kawai ta kyale shi, tana fatan dalilin hakan su gyaro matsalar su kafin wayewar garin.    Wucewa wata nurse tazo yi zuwa wani dakin sai ta duba ta ganta, tayi saurin karasowa dakin ta kashe drip din cike da mamakin ganin babu kowa a dakin sai ita kadai "Babu wanda zai kiramu? Ke kadai kika zaune?" Girgiza mata kai tayi "Fita yayi." "Ok, idan ya dawo kice ya daina nisa gaskiya ko a samo wata babba ta zauna dake aikin na mace ne ba namiji ba, ko ba a garin nan kuke ba? " Tayi mata tambayar cike da mamakin idan har yar gari ce ai be kamata a barta da namiji ba, bata amsa ba sai kawai tayi shiru tana motsa yan yatsun hannun da suka gaji sosai, juyawa nurse din tayi ta fita tana mamakin dalilin da zai saka a barta ita kadai bayan dazu cike wajen yake da yan uwanta gal     Baki daya ma baya cikin asibitin dan sai da akayi asubah sannan ya dawo, bata runtsa ba saboda azabar ciwo haka ta dinga kuka me cin rai ita kadai kwal a daki kamar bata da galihu, Fido ce ta matsa masa da kira gashi ya rasa dalilin da ya saka baya iya kana kansa zuwa wajenta idan har ta kira din, sai yaje ya dawo yake jin haushin kansa, ya sha tama yi mata wulakanci amma sam ya kasa, ita kadai take juya shi son ranta duk kuwa da ita din ma wataran yana mata bore idan yan abun suna kusa dashi.    Ganin dawowar sa ya saka nurse din nan dawowa dakin, ta tarar dashi yana kokarin kwanciya akan couch din dake dakin, dakatawa yayi ganin ta shigo a tunanin sa ko magani zata bawa Asma'un "Be kamata ka dinga nisa ba gaskiya, dan dazu Allah ya kiyaye nazo da wuri, baa so a bar mara lafiya shi kadai ko Yaya ne, idan akwai uzuri babba sai a nemo mace dattijuwa ta zauna da ita." Wani kallo yayi mata irin na wacece ke, kafin yace a kufule "Ina ruwan ki? Bana son gulma da munafurci malama." Tsaye tayi tana duban sa baki bud'e, ya ja tsaki ya kwanta yana rufe kansa har sama da abinda aka kawo wa Asma'un saboda rufa, kallon gadon da Asma'un take tayi, taji tausayin ta ya kamata, ta kuma dau alkawarin in dai ta gane iyayenta sai ta sanar musu da su zauna da yar su gaskiya, yanzu take da bukatar kulawa fiye da kowanne lokaci.    Ana idar da sallah Hajiya Mama ta taho asibitin, ta tarar duk suna bacci shi a kujera ita a gado, murnushin jin dadi tayi , ta saka sallaya a gefe itama ta dan kishingida a wajen.    Duk abin nan a tunanin Nadeeya a asibitin Maman ta kwana, shiyasa daga asibitin su tayo nan din wajen bakwai da rabi dan night duty tayi dama da tabbas ita zata zauna da Asma'un.    Zuwan ta ya tashi Adam din, sai a lokacin ya ga Hajiyar ma, ya mike suka gaisa, Nadeeya ta tambaye shi me jiki ya amsa da sauki tamkar wanda ya san halin da take ciki da gaske. Tare suka tafi gida suka bar Hajiyan yaje yayi wanka ya huta. Wajen tara Umma tazo tare da Abbati da breakfast, jiya bata iya bacci ba saboda tunanin halin da Asma'un ke ciki, ta kuma sake rokon Abban akan ya barta amma sai ya nuna fushin sa sosai, sai kawai ta kyale shi duk a tunanin umman ai Hajiya Maman anan ta kwana, a yadda ta sameta ma da yadda ta amsa dubiyar zaka rantse a wajen ta kwana. Babban likita ne yazo, suka shigo tare da nurses ya duba Asma'un da hannun nata, hakan ya farkar da ita, suka gama suka fita daga nan yace ayi masa hoton hannun sannan sai aga me yakamata ayi.    Matsawa Umma tayi gaban gadon tace "Ya jikin naki?" Maimakon ta amsa sai kawai ta saka kuka. "Kuka kuma? Menene kuma na kuka eh? Hakuri zakiyi kowanne bawa da kaddarar sa." "Dan Allah karki tafi umma, ki zauna." "Ai dama ba yanzu zan tafi ba, sai anjima." " A'ah, karki tafi gaba daya, bana son ya Adam ya zauna mugu ne, bashi da kirki." Da sauri umman ta kalli Hajiya Mama da itama umman take kallo a gigice, sam Asma'u bata san Maman na dakin ba tunda a k'asa take daga jikin bango baa gano ta. "Karki sake cewa mijinki mugu, bana so kar na sake ji." Umma ta fad'a ranta na sosuwa sosai. Cigaba Asma'un tayi "Jiya ficewar sa fa yayi ya barni, drip din ya kare babu kowa, so yake na mutu wallahi." Ta karashe tana sake fashewa.   Shiru umman tayi bata ce komai ba, sai zuwa chan tace mata tayi shiru kar ta karawa kanta wani ciwon ko ta sakawa kanta hawan jini wanda bata ma san ko ta riga ta kamu dashi ba.    Kasa hada ido mama tayi da Umma, ita kuma umman tayi kamar bata san me Asma'un ke nufi ba, har zuwa sanda Abba yazo duba Asma'un, tana ganin shi ta sake fashewa da kuka, sosai yaji tausayin yar tasa, ya kuma san tabbas baa kyauta mata ba. Hakuri ya dinga bata da zai tafi Hajiya Mama ta tashi ta bishi waje, umma ta tabe baki tana ayyana yau ko da auren ta zai mutu ba zata bar asibitin nan ba, kawaici da kara daidai gwargado tayi, kuma babu wanda baya son dansa bare ace ta nuna son yaya, ta shiryawa Abba bore duk abinda zai ce ba zai hanata zama ta kula da Asma'un ba.    Dawowa ciki Mama tayi, suka cigaba da zaman kurame har zuwa sanda yan gidan su Asma'un su Rauda suka zo, da kuma kannen Adam din, hakan ya saka wajen sakewa ba kamar dazu da ko uffan babu me cewa wani a cikin su ba, ita Hajiya Mama nauyi da kunya ta hanata katabus, ita kuwa Umma tana sane ta mata banza dan ta lura bata san kawaici ba, shiyasa zata nuna mata ita ma tana da iko akan yayanta da kuma mijinta, ba dole sai abinda taga dama take so shi za'a yi ba, ko da hakan na nufin cutar da yayan ne.    La'asar likis Hajiya Maman tayi musu sallama ta tafi a zuwan sai gobe da safe, umma bata yi mamakin tafiyar ta ba dan kunya take ji sosai musamman da Umman ta gano ba ita ta zauna da Asma'un ba, kuma taga duk take taken Umman na son nuna ikon ta a wannan karon shiyasa ma ta ce Abban ya bar umman ta zauna ta kula da Asma'un ita sai ta dinga zuwa da safe, be yi musu ba tunda dama ita yake karawa amma dama har ga Allah yafi son umman ta zauna sai dai ba zai iya ce mata ta zauna din ba kar Hajiya Maman taga rashin kyautawar sa. Hakan kuwa da akayi sai yaji dadi, ya tafi kasuwa da yakinin daga umman har Asma'un zasu fi jin dadin hakan. Da yamma sai gashi ya sake dawowa ya sake duba jikin nata yaje ya samu likitan yaji duk bayanan da ya kamata ya sani akan hannun nata.    Adam be dawo asibitin ba sai dare, gida yayi tafiyar sa ya kwanta ya huta ya fito da yamma ya je chan majalisar su sannan ya wuce ya siyo nama da lemuna ya wuto asibitin. Babu wanda ya kulashi a cikin su Rauda shima be kula su ba, umma kawai ya gaida sai Ya Hadiza da ta fito daga toilet bayan ya zubar da ruwan da ta goge wa Asma'un jiki dashi. Kadaran kadahan ta amsa ya dan yi tsaye jim sai kuma ya ajiye ledar hannun sa ya fice. "Adam baya kyautawa sam, na rasa dalilin da yasa ya amince da auren nan idan har baya son Asma'u." Umma tace cike da takaici "Hmm, duk wanda yayi na gari ai kansa ko? Ni dai fatana Allah yasa ba shine dalilin karayar nan tata ba, dan idan har aka tabbatar toh babu amfanin zaman su fa." "Ni kaina abinda nake zargi kenan, dan dai kinga ba zaka fara tambayar yaro yana cikin wannan halin ba, jira nake ya sake samun karfin jikinta sai mu bi baasi, idan har akwai cutar wa babu amfanin auren." "Gaskiya dai, ya kamata a bincike ta aji." " Allah ya kyauta. " Umma tace tana mikewa ta fita wajen Abba suyi magana,  ta tarar da Abba ya dawo zai shigo dakin, ta hade rai a tunanin ta zai mata maganar tafiya amma sai taji yace " Yaran nan ya kamata su tafi haka saboda dare, idan kuma mazajen nasu ne zasu zo daukar su toh." " Eh sune zasu zo. " " Toh Madallah, ya jikin nata? " " Da sauki. " " Allah ya kara sauki, bari na wuce ni, zan shigo da safe saboda ance babban likitan da safe yake zuwa sai kuma yamma wajen biyar. " " Ok, Allah ya kaimu. Allah ya bamu alkhairi. " " Amin summa Amin, sai da safe. " Ya juya ita kuma ta koma ciki, anan take fad'a ma su ya Hadiza yadda sukayi da Abban. Sukayi dariya Rauda har da kwaikwayon yadda Umman ta fita da nufin ita da Abban ko shi ko ita idan yayi mata maganar tafiya. Dariya suka saka gaba daya har Asma'u da take kwance sai data murmusa. Daya bayan daya suka yaye ya zama daga ita sai Umman, ta sake sosai tana jin kamar bata da saurin ciwo, hira umman ta dinga janta tana son gano irin zaman da take a gidan Adam din duk da dama duk sun yi hasashen irin rayuwar da zata tarar din. Kasa fadawa Umman dalilin da ya sakata faduwa tayi, dan da nauyi sosai, tace mata me? sai kawai tace mata zamewa tayi a wajen sauka daga benen bata fadi ainihin abinda ya faru ba, kamar dai Umman bata yarda ba, amma kuma sai ta kyale ta kurum, ta bita da addu'ar samun lafiya.***      _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* *RM* 13 ***Washegari da wuri Hajiya ta aiko masu aikin ta da abinci, tace zata shigo anjima. Karba umma tayi ta zuba ma Asma'un da tace kadan da k'yar, itama da dan ci sannan ta taimaka mata ta gyara jikin ta kafin likitan yazo, tun bayan fitar Adam be sake dawowa ba, gida ma ya wuce daga nan yana kokarin shigar da motar sa ciki Hajiya Mama ta kirashi tana son ganin sa, fasa shiga yayi ya ajiye motar a waje ya shiga gidan nasu in da ya tarar da ita zaune ita kadai a falo tana sakawa da warwarewa, tana ganin shi ta mike daga kishingidar da tayi, ya zauna kusa da ita daf ya dan matsa mata kafar ta, janye kafar tayi alamun tayi fushi ta tsare shi da ido cikin bacin rai irin wanda be taba gani ba tace "Ka kyauta kwarai da watsa min k'asa a ido." "Mah! Me kuma akace nayi?" "Yanzu ka kyauta ka bar matar ka ita kadai ta kwana, bayan magiyar da kayi ta min akan na kyale ka, dama kawai ka shirya wulakanta ni shiyasa kayi haka ko?" " Comman, yanzu mah kin yarda da maganar ta? Wallahi sharri tayi min, baki zo kin same ni a dakin ba? Bafa muyi bacci ba sai wajen asubah fa, ina zaton dai zafin ciwo me ko kuma kiyayyar da take min ce har yanzu bata hakura ba." " Kiyayya?" Tace tana kallon sa Juyar da fuskar sa yayi kamar wanda yake cikin yanayi yace " Kwata-kwata bata kauna ta wallahi, babu yadda ban yi da ita ba amma tun auren taki sakewa dani, haka nake hakuri dan ko hakki na bata bani, wannan tsautsayin ma wai dan kawai nazo dakin ta shine ta tashi ta fita garin sauri ta zame a kafar bene ta fadi, amma kinga yan uwanta da kowa kallon ni ne me laifi, saboda ni aka sani me matsala." " Haka take dama Asma'un? Ikon Allah!" "Saboda ni ne me matsala shiyasa kowa laifi na yake gani, amma itama bata san ya kamata ba. " " Bansan haka take ba, kallon mutuniyar kirki nake mata, ashe itama kwalla kanta ce, ai shikenan, duk da na zata laifin ka ne, ko wahalar musu da ya kake. " " Ko daya, ni me ma zan mata na wahalar da ita? Ko fa gaishe ni batayi balle tayi min magana, dan dai ma Ina da hakuri ne wallahi. " " Ah gaskiya bansan bata da hankali ba sai yau, amma babu komai zamuyi magana." " Shikenan, amma dan Allah kar ayi mata fad'a, ni ba dan kin matsa ba da ba zan ma fad'a ba. " " Sai ka zauna a haka? Bayan anayin aure ne saboda a samu nutsuwa da kwanciyar hankali. " " Zata daina ne. " Yace yana mikewa " Har sai yaushe? Zan same su ita da mahaifiyar ta ta dana lura itama haushi na take ji, zan fada mata komai sai ta fad'a min idan haka ake zaman aure a garin su. " Kada kansa yayi, ya fice ransa fes, yayi shigewar sa gida yayi kwanciya sa sai wajen tara ya sake shiryawa ya fice abun sa. Da kwarin guiwar ta, ta isa asibitin dan tayi alkawarin yi wa umman magana ko ita da ita ne idan yaso sai ta nuna wa yarta gaskiya dan idan ba irin Adam ta samu ba babu me hakuri da hakan da tuni anji kansu. A yadda ta shigo dakin kadai ya saka Umma tunanin akwai wata a k'asa, ba kamar jiya da ta kasa sakewa ba, daga tsaye ta duba Asma'un ta fita wajen ta samu kujera ta zauna tana kallon masu shige da fice a asibitin, ta dade a wajen har aka soma zuwa, umman ta fito wajenta ta saka musu carpet babba tace Maman ta dawo, ba musu ta dawo ta zauna ta dubi umman da take hade kan kwanukan abincin jiya waje daya tace "Magana nake so muyi dake ta fahimta." Barin abinda take tayi, ta zauna kana tace "Ina ji, Allah yasa dai ba wata matsala bace." "Kusan hakan, amma dai ko kin tambayi Asma'u yadda akayi ta fadi?" "Tsautsayi ne ai da yake kan kowa, ban tambaye ta ba gaskiya dan ban ga dalilin tambayar ba." "Aikuwa akwai dalili, ya kamata ace kin bincika kinji, nidai na binciki Adam, kuma dai har ga Allah maganganun babu dadin ji, ban tsammaci hakan daga wajen asma'u ba. " " Me ya faru? " " Eh toh, Adam dai yace min zaman nasu babu dadi dan ko magana bata masa, gashi bata bashi hakkin sa na aure, wannan tsautsayin ma ya faru ne sanadiyyar yazo wajenta tayi niyyar barin dakin sai ta gamu da tsautsayi! " " Kinga ai ba'a haka, miji daraja ce dashi duk kuwa da halin sa, ki hango ace da ba Adam din bane, da tuni ba zancen da ake kenan ba." A tunanin ta umma zata ce wani abu, ko ta nuna rashin kyautawar Asma'un amma sai tayi kamar bata gane ba ma, tace kawai " Allah ya rufa asiri." Hakan ya kular da Hajiyar, ganin Umman na niyyar mikewa tace " Iyakar abinda zaki ce kenan?" " Toh me zance Yaya? Yaran yanzu ka haife su ne baka haifi halin su ba, kuma dai kinga halin da Asma'un take ciki ya kamata a daga mata kafa har ta samu sauki kafin a tuhume ta, a gani na hakan ya dace." Shiru ya biyo bayan maganar Umman, Hajiyan ta rasa me zata ce,da n ta gane sarai magana Umman ta gasa mata me zafi, ganin bata ce komai ba ya saka ita kuma Umman tashi ta bar ta a wajen. Kwafa tayi cikin jin haushin ta bar asibitin, ba zata lamunci sakarci ba dole ta takawa abun birki. Sosai umma taga son zuciyar Hajiyan fiye da ada ma akan batun auren, ko makaho ya shafa Asma'un ya shafa Adam din zai gane komai, amma saboda tsabagen son zuciya har mutum na kwance a gadon asibiti amma kazo da irin wannan maganar. Tun ranar da hakan ta faru, Hajiyan bata sake lekowa ba, tana dai aiko da abinci kullum sau biyu a rana, Nadeeya ce kawai take zuwa kullum ba fashi amma shi kansa gogan sai ya ga dama yake dan lekowa fisha yayi gaba abin sa yana sake rura wuta a wajen Hajiyar tana jin zafin umma sosai tana ganin da saka hannun ta Asma'un tayi duk abinda tayi ma. Satin ta uku a asibitin aka cire cast din da aka saka mata a hannun sannan aka sake mata x-ray aka tabbatar da yana healing sosai kuma very fast, gentle hand therapy aka cigaba da yi mata wanda aka fara tun kafin a cire cast din, hakan ya sake taimaka mata wajen samun karfin hannun har tana iya motsa shi sosai. Sallamar su akayi sannan aka basu appointment, Hajiya na jin an sallame su ta kira Abba ta sanar dashi gidan ta za'a kawo ta ba gida za'a wuce da ita ba, Abba yace toh ya kira umma ya fad'a mata a wuce da Asma'un gidan ta ko mijinta ya dauke ta kawai su tafi ba sai sun je ba, shiru umman tayi masa ya gama ya kashe. Dama ita bata ce zata tafi da ita gida ba tun da dai da mijinta. Gidanta suka fara kaita wanda Maman ta saka aka gyara shi kafin su dawo, shine zuwan umman na farko suka dan zauna zuwa azahar sannan suka tafi gida ita da Ya Hadiza da Abbati. Suna tafiya ta tashi ta lallaba ta hau saman tayi wanka ta shirya, tana kokarin shinfida sallaya ne taji alamun an shigo kasan saboda babu motsin komai shiru gidan, ajiye sallayar tayi ta fito sai ta tarar da Hajiyar da kanta zaune a falon tana dan kallon gidan. "Sannu da zuwa." Tace tana kasowa falon, ta tsuguna ta gaishe ta amma yadda ta amsa ya saka ta jin wani iri, "Lafiya." Tace a yangace tana kalle kalle a falon, tayi zaton ko duba jikin ta, ta sake yi tunda ta jima bata zo ba sai aike amma sai taga akasin haka. "Fad'a nazo yi miki tunda ita umman taku ta kasa ba zata iya ba, ni da kaina zan miki kuwa, kinsan hakkin miji akan matar sa kuwa?" " Naam!? " " Kin jini sarai, daidai gwargado ai kunyi karatu both na addinin da na bokon, kuma dai ke ba yarinya bace gasu Hidaya nan ai gaba kike dasu, amma ace ba zaki iya yiwa mijinki abinda yake so ba? Har sai yana binki kina butsarewa, duk da irin rokon da nayi miki na ajiye girma na? Ban zaci haka daga gareki ba. " " Hajiya wani laifin yace nayi? " " Laifi ? Laifufuka dai, babban laifi wanda ko a wajen ubangiji kin yi babban laifi, dan gayun nan dan tarairayar nan ace duk baki iya ba, kamar wadda ta fito daga kauye, kauyen ma kayau, lallai ki gyara kanki, ba zan lamunci shashanci ba. " Sai ta mike tsaye "Dole kiyi wa mijinki biyayya kiyi masa kuma duk abinda yake so, batun hakkin sa kuma ke da Allah wannan idan kika ki bashi. " Daga haka tayi hanyar fita tana sababi, kan Asma'un gaba daya ya kulle, ta gaza fahimtar in da Hajiyar ta dosa kai tsaye, hawaye taji na neman zubo mata, ta maida su da sauri tana girgiza kanta, ta mike ta haye saman ta rufe kanta ta shinfida sallayar da sauri ta tada sallah tana kokarin hana wa kanta tunanin maganganun Hajiyan balle har suyi tasiri a ranta. Bayan ta idar ne maganganun suka dinga mata amsa kuwwa a cikin kunnenta, ta danne kanta a saman gadon tana runtse idon ta. Har dare yayi wajen goma na dare be dawo ba, ta shirya ta kwanta tana karfafar kanta da zuciyar ta, tana shiryawa zama da Adam da selfish mahaifiyar sa, tunda har Hajiyar ta soma irin wannan zantukan toh tabbas ta shirya kuntata mata a zaman su, zata kuma goyi bayan Adam din a komai, bata san me yaje ya fad'a mata ba, sanin ma bashi da amfani tunda ba damar kare kanta za'a bata ba, ita mace a kullum itace a k'asa, ita ake bawa laifi a komai babu kuma wanda yake sauraron korafin ta, idan ta bud'e baki zata fadi damuwar ta sai a dakatar da ita, ace mata rayuwar aure yar hakuri ce, tayi hakuri kawai. Ta kuwa shiryawa hakurin da ko kashe ta Adam da Hajiya zasuyi ba zata taba ce musu dan me ba, zata kare rayuwar ta a haka har zuwa lokacin da Allah zai yanke mata. Da safe ta tashi da kwarin jikin ta, ta dan sake gyara gidan da abinda take bukatar ya kasance a wajen da take bukatar sa, sannan ta hada break fast me sauki ta ajiye a dining din da ba wanda ya taba zama akai. Ta dauki nata ta koma daki taci ta dauko al'qur'an me girma ta shiga tilawar sa. Be kwana a gidan ba, da safen ya dawo ya wuce daki ya hau ramakon baccin da yake kansa, kasancewar weekend ce babu in da zashi, sai wajen sha daya ya farka ya fito falon idon sa ya sauka akan dining din, ya isa wajen ya bud'e yayi murmushi wanda shi kansa be san dalilin sa ba, komawa yayi ya fara wanka sannan yazo yaci abincin ya koshi sannan ya nufi dakin nata. A tunanin sa zai tarar dashi a rufe amma sai yaga akasarin hakan, tana zaune kyem ya shigo ta dan dube shi ta cigaba da karatun ta, rabon shi da ya karanta alkur'ani me girma yayi mugun jimawa, ganin ta tana karantawa ya tuna masa, ya k'asa karasawa ciki ya tsaya yana sauraron ta, tayi kamar bata san da zaman sa a wajen ba har ta kai karshen shafin, ta rufe ta ajiye a bedside ta mike tace "Ina kwana?" Bata jira amsar sa ba tayi gaba zuwa hanyar toilet, tayi shigewarta ta barshi a wajen, abinda yayi niyyar yi mata sam sai yaji bashi da karsashi, yaji tayi masa kwarjini dalilin karatun da yaji tanayi, juyawa yayi ya bar dakin, ya bar gidan baki daya ma. _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* RM    14 ***Tun daga ranar kullum zatayi duk ayyukan da tasan son zama wajibi akanta na sauke hakkin sa sannan zatayi girki kuma yana zama yaci wani zubin ma har ya cinye tas musamman na safe da na dare dan baya zama da rana a gidan daren ma sai late yake dawowa dan sai da safe take jin motsin sa mafi yawancin lokuta, babu wanda hajiya ta sake aikowa gidan tun bayan ranar da ta shigo din, Nadeeya ce dai duk sanda ta samu dama ta kan leko su gaisa ta sake dubata sannan ta tafi. Ranar da ta shigo ne take ce mata ya kamata ta dan dinga lekawa tana gaida Hajiya, ta amsa da toh a ranar kuwa bayan ta gama komai ta shiga gidan sai dai tarbar da ta samu wajen Hajiyar yayi masifar daure mata kai, tamkar ba jinin ta ba, a wulakance ta amsa gaisuwar ta, ta kuma share ta, ta ma yi shigewar ta daki daga karshe ta fito ta bar gidan ba tare da ko magana ba, haka ta karaci zaman ta daga ita sai masu aiki ta koma gida. Washegari sai ga kiran Hajiyar, hijab kawai ta rufa tabi bayan yarinyar, ta same ta a tsaye a tsakar gidan an jibge kayan miya masu uban yawa da su kabewa da alaiyahu. Masu aikin ta ne da wasu mata su biyu akan kayan. Gaishe ta tayi ta amsa sama sama, ta nuna mata kayan miyar da hannu "Aiki ne gashi nan, a gyara a dora kafin na dawo, baya za'a je akwai murhu da itace, sauran aikin sai na dawo za'a fara." "Toh!" Tace a sanyaye ta ja kujerar tsugunnun dake gabanta, ta zauna ita kuma Hajiyan ta koma ciki. Aikin suka shiga yi ka'in da na'in har wajen azahar kafin su ga raguwar sa, ta gaji sosai ga wani ciwon kai da ya matsa mata kwana biyu, babba daga cikin masu aikin ce taga yanayin ta, tace ta koma baranda ta zauna zaasu karasa, ki tayi dan bata son abin magana, suka hada baki wajen rokon ta da ta huta amma taki, ana haka sai ga Nadeeya da Adam din sun shigo a tare, wani irin kallo yayi mata na cikin ido, ta dauke kanta tana maida shi wajen Nadeeya da mamaki ya cikata "Asma'u har dake a aikin!? Ke da ba ishashiyar lafiya ba?" Yake tayi, suka gaisa tace ta taso, ba musu ta tashi ta bita ciki shi kuma ya take musu baya, suka yada zango a falo. "Daga kin shigo kin ga ana aiki sai ki hau yi, duk dauko su akayi biyan su Hajiya zatayi, wannan aikin yafi karfin ki ai." Murmushi kawai tayi, dama ta san da biyu Hajiyan ta saka ta aikin bayan ga masu aiki nan bajaja, har da hayar wasu ma, duk da bata san taron menene ba amma kuma bata ji komai ba a aikin da ta saka ta, a rayuwar ta aikin gida da duk abinda ya shafi girki baya mata wahala sam, dan ma bata dan jin dadi ne, da ba zasu ma fahimci gazawar ta ba. A kusa da ita daf yazo ya zauna, ya dan bige ta a kafadar ta ya harare ta "Ba zaki min magana ba?" Tabe baki Nadeeya tayi ta sungumi jakar hannun ta, tayi hanyar bedroom dinta "Na lura kunya ta maka karanci Boy." Dariya ya saka tamkar bashi ba, tana shigewa ciki ya juyo yana matsawa daga kusa da ita, "Baki san waye Adam ba har yanzu." "Bani kuma da bukatar sani." Tace tana matsawa itama, murmushi ya saki ya janyo hannun ta, tayi kara kad'an ya saka hannu ya dalle mata baki "Sai kin gane baki da wayau, amfanin ki ya kusa karewa a waje na, daga nan zaki gane waya Adam!" Tsam ta mike, yafi mata kwarai ta koma wajen masu aikin ko aikin zai kasheta da ta zauna inuwa daya da Adam, tana kokarin fita Mama na shigowa, dan saura kadan suyi karo ta matsa baya da sauri "Amma ina miki magana shine zaki tafi? Magana ta bata da muhimmanci ko?" Muryar sa ta daki kunnenta ta hanata daga kafarta da take shirin yi ta bar falon, da sauri ya juyo, ita yake kallo irin kallon cikin idon nan " Mijin ki yana miki magana amma shine zaki kada kanki Asma'u, anya?" " Hajiya wallahi ba haka bane. " Tace cikin son kare kanta dan bata san makircin Adam din ya kai haka ba " Kin karyata mijinki kenan?" Girgiza kai tayi da sauri " Yayi kyau. " Hajiyan tace tana wucewa ciki, ya tashi ya karbi Jakarta " Welcome Mah, ai ban ga shigowar ki ba sai maganar ki kawai naji. " " Ka cigaba da hakuri kaji, da kaina zanyi maganin abun." Sosa kansa yayi " Ki kyale kawai Mah, babu komai fa, zata daina ne wallahi. " Tsaki taja ta shige tana ganin kamar Adam din ma tsoron Asma'un yake ji, duk tsaurin sa da zafin sa akanta baya iya komai. Sai da ya tabbatar Hajiyan ta shige ya kanne ma Asma'un ido daya ya sa dariya. Jiki a sanyaye ta koma wajen masu aikin ta cigaba da aikin amma rabin hankalin ta na ga abinda ya faru, tana jin ana cewa makircin mata bata san a mazan ma akwai makirai ba, marasa tsoron Allah masu dabi'ar da bata san me ma zata kira su ba. Dare sosai ta kai a gidan sannan ta koma gida a gajiya tikis, kamar ta dora hannu aka tayi ta ihu haka take ji, zafi goma da ashirin, ta taba jin labarin makirin namiji wanda zai nuna a gaban yan uwansa shi din na kirki ne, ya kuma musguna miki a gida daga ke sai shi, irin Adam kenan shi abin nasa ma har yayi yawa dan ko ita da take mace ma ba zata iya abinda yayi ba wallahi. Duk da uwar gajiyar da ta sha haka ta dora abincin dare me sauki ta ajiye masa ranta duk babu dadi, tana ajiyewa yazo ya haye yaci yayi kyatsa ya bar mata komai a wajen tazo ta tattare ta kai kitchen dan ba zata iya kuma wanke su a daren ba, burin ta kawai ta ajiye hakarkarin ta a kasa ko zata ji dadi. Kwanciyar ta kenan bacci ma ya soma daukar ta, taji ana tabata, ta yinkurin tashi amma ya danne ta, sai da yayi abinda ya kawo shi sannan ya tsallake yayi ficewar sa, ya barta da kuka me cin rai, ta tsani Adam ta tsani ko da jin sunan sa ne, haka ta tashi ta tsaftace jikin ta, sannan ta dawo ta kwanta amma sai ta nemi baccin da take ji ta rasa, tayi tayi amma sam yaki zuwa, tunani ta hau yi, ta saka wannan ta kwance wannan, ganin kwanciyar haka babu amfani sai kawai ta tashi ta dauro alwala ta raya daren, tana idarwa nan da nan bacci ya kwashe ta. Da asubah ta farka kasan mararta na dan mata ciwo kad'an kad'an, har ta idar da sallah be daina ba, komawa tayi ta kwanta dan bata jin zata iya yin wani abu, kasala take ji sosai shiyasa har gari yayi sosai bata mike ba. Fitowa yayi ya nufi dinning din kamar yadda ya saba sai yaga wayam, haushi ne ya turnike shi dan yana sane jiya ya shigo da doya dan ita yake sha'awar ci yasan kuma in dai ta gani zata soya musu ita, yana matukar jin dadin abincin ta sosai shiyasa duk abinda yake baya taba yarda ya wuce shi, ji yayi ransa na sake baci, ya koma saman ya tura dakin sai ya tarar da ita a kwance a gado ya lulluba har kanta, yaye abun da ta rufar yayi, suka kalli juna "Ina breakfast?" Yace yana tsaye kanta "Babu." Tace kanta tsaye ta juya dayan side din, bankaro ta yayi ya juyo da ita "Ya ina miki magana zaki juya min baya, uban wa ya saka ki fara abinda ba zaki iya dorewa ba, ko kinyi tunanin zaki sace zuciya ta da girkin ki ne?" "Dan Allah Ya Adam ka rabu dani, ni na saka kaina nayi girkin kuma yau ban ba, ka kyale ni naji da abinda yake damuna dan Allah." Tace cike da kosawa da halin sa "Tashi zakiyi ki soya min doya kiyi min sauce, ina jiranki fita zanyi." Tana jin sa ya juya ya fice, ta cigaba da kwanciya a wajen ciwon marar na karuwa sosai. Chan wajen minti talatin ya dawo dakin, ya tarar da ita a yarda ya barta, ransa idan yayi dubu ya baci, ya fizgota da karfi ta fado daga gadon, ya shiga kokarin neman abun da zai saka ya daketa. Tunawa yayi da belt din dake jikin wandon sa, ya hau kokarin ballo ta, tayi saurin rik'e hannun shi tuni har ta soma kuka sosai "Dan Allah kayi hakuri wallahi bani da lafiya ne." Be ji ta ba, bakar zuciyar shi ta riga ta ingiza shi, ya daddage ya zabga mata da karfin gaske, ta gantsare tana kwala karar azaba, idon sa ya rufe ruf, burin sa kawai yayi mata lilis yadda gobe ba zata sake ja dashi ba, baya son raini da wulakanci ba kuma zai dauka a wajenta ba, ita din da bata da maraba da takalmin sawar sa, wanda yake takawa ya wuce. Sau uku yana zabga mata, ta rarrafa da k'yar ta shige bayan gadon, biyo ta yayi ya sake dagawa yaji an rik'e belt din, daga nan yaji saukar mahaukacin mari a kuncin sa, kafin ya dawo hayyacin shi aka sake sauke masa wani me zafin gaske. Umar ne a tsaye yana huci sosai, sai Umma dake gefe tana kuka sosai, sakin belt din yayi ya fadi kasa, umar din ya shaki wuyan sa ya gwara kansa da bangon dakin. "Kasheta zakayi? Kasheta zakayi? Wallahi kafin ka kasheta ni zan fara kasheka, shege dan iska mara mutunci." Ya sake kaiwa bakin sa naushi "Umar zo ka daga ta, mu kaita asibiti kamar tayi bari." Umma tace tana kuka ta tallafo Asma'un jikin ta, sakin sa umar din yayi, babban yayan su Asma'un kenan, yana da masifar zuciya shi yasa baya shiga sabgar kowa, yanzu ma umma ce tazo gidan Hajiyan bayan ta aika da cingam din gayyatar bikin yar kanwar Baban su Adam din wadda ta taba rik'e ta kafin ta koma hannun iyayenta saboda Adam din, duk da Hajiyar bata sani ba, bikin ake shine aikin da su Asma'un suka yi jiya, tayin aikin umman tazo shine tace bari ta fara shigowa gidan Asma'un, sai kuma suka ji ihunta a sama, shine suka hawo da sauri suka tarar da bakin azzalumin yana dukan ta tamkar ya samu jaka. Bari tayi kamar yadda Umman tayi tunani ganin jini, a asibitin aka kara tabbatar musu sannan aka ce suje suyi scanning a tabbatar ko ya gama fita duka. Daga nan kuma aka bata maganunguna suka wuce gida, gefen idon ta shatin duka ne inda Allah ne ya kiyaye be same ta a ido ba, ajiyar zuciya kawai take babu wanda yayi magana a cikin su, ran umma yayi masifar baci suna isa gida ta kira Abba a waya tace yazo gida babu lafiya, sai gashi nan da nan kuwa, ya tarar da Asma'un a kwance, fuskar ta da ta dan daga ya kalla a tsorace sai kuma ya kalli Umman, "Gata nan, zuwa mukayi muka tarar da ita yana jibga kamar ya samu jaka, kalli idon ta, bayan ta ma shatin dukan sa ne." "Duka?" "Gashi nan ka duba ka gani ai idan baka yarda ba, ko ka kira Baba ai a gabansa akayi." "Asma'u?" Ya kira sunan ta, ficewa umma tayi daga dakin dan hatta Abban haushin sa take ji sosai. " Dukan ki adamu yayi wai? " " Eh. " Ta gida kanta tana goge kwallar takaici Shiru Abban yayi tamkar ruwa ya cinye shi, jiri jiri yaji yana neman kayar dashi, ya zauna da sauri yana dafe jikin kujerar " Innalillah wa inna ilaihi rajiun. " Yayi ta maimaitawa, har ya samu nutsuwa, ya dinga kallon ta tausayin ta na shigar sa sosai. Idan har namiji zai daga hannu ya daki mace, toh lallai ya kai makura a jahilci, be san abun na Adam din ya kai haka ba, be san mahaukaci bane na ajin karshe, waya ya dauka ya kira Ya Asabe, lokacin tana gidan Adam din an kira likita yana goge masa wajen da Umar ya fasa masa, tana ganin kiran Abban ta daga a zafafe " Yanzu Karami har Umar yayi girman da zai shigo har gidan Adam ya dake shi haka, wacce irin tarbiyya ka bawa yaran nan ne,? Har cikin gidan kazo ka daki mutum saboda kana tunanin wani abu daban? " " Adamu ya aiko wa Asma'u da takardar sakin ta, yau ba sai gobe ba, idan kuma yaki sai hukuma ta raba mu dashi!" Yana kaiwa nan ya kashe wayar sa, saroro tayi da wayar a hannu, ta kalli Adam din ta kalli wayar, tana son sake tabbatar da Abban ne dai ya kirata ba wani ya bawa wayar ba, shi din ne dai yayi mata magana babu gaisuwa bare girmamawa! RM    15 ***Ajiye wayar yayi a kusa dashi ya karasa wajen Asma'un yana dubata, "Tashi kinji." Yace cikin tsananin tausayin ta, mikewa tayi zaune da k'yar har lokacin kanta na mata masifar ciwo, gefen idon ya dame ta sosai dan ya daga wajen. "Ina hijab dinki? Zaki iya tafiya!?" Girgiza wa Abban kai tayi saboda yadda take jin ta very weak, kamar zata fadi haka take ji. "Ina zuwa." Ya fita yana kwala wa umma kira, ta taso tazo tana kin kallon sa "Taimaka mata, ta saka Hijab dinta ku sameni a mota." "Ba dai maida ita zakayi ya karasa kashe ta ba ko?" Wani kallo yayi wa umman, yayi tsaki yace "Kuyi sauri nace, ina jiranku." Kada kai Umman tayi zuwa ciki shi kuma ya fita waje, taimaka mata tayi ta rik'e ta suka fito suka tarar dashi a mota Umar na zaune a mazaunin driver suna magana da Abban. "Da ka sani ka karairaya shi ka zubar tunda be san mutunci ba." Abban yace a maimakon tunanin da Umman tayi na zaiyi wa har Umar din fad'a, shiru umar din yayi bayan sun shigo, ya tada motar bayan ya kalli bayan cikin tausayin Asma'un. "Asibiti zaka fara kaimu, kafin ka kaimu chan gidan tsoho." " Ok." Yace yana juya motar zuwa hanyar teaching hospital din garin. Tun da suka dauki hanya Abba yake waya, wanda umma ta fuskanci ransa yayi kololuwa a baci, dan duk a fusace yake maganar karshe ya kirawo Ya Hadiza ya sanar da ita umman naji, dan ita ko kiran kowa a cikin su batayi ba saboda bakin cikin da take ciki.    Asibitin Abba ya saka aka sake duba masa Asma'un sosai aka kuma tabbatar masa da babu cikin ya fice idan kuma taji wani abu daga baya sai ta dawo a sake dubawa, magungunan ta da aka bata likitan ta gani ta chanja mata wasu sannan ta ce zasu iya tafiya.   Har sun mike tsaye, sai Abban ya tsaya yace wa likitan yana bukatar ayi wa Asma'un gwajin jini, ta rubuta musu tace aje lab, akaje aka biya komai aka dauki jinin nata akayi mata dukkan tests din da suka shafi HIV, Hepatitis da sauran su, duk suna cikin zulumi har sai da result din ya fito babu matsalar komai, ajiyar zuciya Abba ya sauke da karfin gaske, duk suka kalle shi, yace su tafi bayan an tsaya an sai ma Asma'un abinda zata dan ci duk da sam bata da taste a bakin ta.    Gidan tsoho suka wuce, dama tuni Abba ya sanar dashi zuwan su ya kuma saka shi kiran Hajiya Mama itama yace tazo tare da Adam, toh tace amma zuciyar ta fal take da mamakin yadda Abban ya dau zafi dan tun dazu take kiran sa amma yaki dagawa, tasan yana da hakuri matuka tun yana yaro musamman a abinda ya shafe ta, baya hada ta da komai amma kuma a wannan karon, yana son nuna mata yar sa ta fi masa akan ta, bayan kuma abubuwan da Asma'un tayi wanda shi be sani ba. Mayafi kawai ta yafa tace Adam din ya taso, da farko yace ba zai je ba,amma tace dole ne dan bata isa ta tsallake maganar tsoho ba, ba asan ransa ya shiga motar ba, suna kokarin barin gidan Nadeeya na shigowa a tata motar, ta tsaya tana bin baasin in da zasu, sai kuma ta hango fuskar Adam din da tayi suntum, ya kuma hade rai tamau hakan ya sake taimakawa wajen hayewar fuskar. Dariya ce taso kwace mata, ta daure ta kanne cikin nuna kulawar ta tace "Boy me ya same ka!?" Banza yayi mata, Mama tayi kwafa tana sake kallon fuskar tasa "Wai Umar ne ya shigo dan rashin mutunci har gida ya dake shi, akan wai dan ya tarar dashi yana yiwa asma'u fad'an taki yi masa breakfast, ni wannan masifar da na san haka auren nan zai zama da ba'a yi ba wallahi, daga taimako da zumunci sai kuma abu duk ya lalace." "Daga kawai ya same shi yana mata fad'a sai ya hau dukan sa? Anya kuwa boy?" Tace tana kallon shi, juyar da kanshi yayi gefe yana jan karamin tsaki "Ina ita Asma'un toh, tana gidan ne ko yaya?" "Sun tafi dai da ita, yanzu haka tsoho ne ya kira ni akan na same shi a gida na san kuma akan maganar ne." "Gaskiya Mama akwai boyayyen abu da baki sani ba game da zaman Adam da Asma'u, ya fad'a miki gaskiyar komai kafin kuje kar azo ana jin kunya." "Toh, dama na dade da ganin take taken ki, yanzu maimakon ki goyi bayan kanin ki, sai ki goyi bayan ta? Toh dai idan ma wani abun yayi mata ina ruwan Umar din? Ba mijin ta bane da zai shiga?" "Idan kuma samun sa yayi yana kokarin kashe musu ya fa?" "Driver wuce mu tafi dan Allah, sai mun dawo." Maman tace a kufule, dan ma dai Nadeeya din ce har ta tsaya tana gaggasa musu wannan maganar da wani ne da ba zancen da ake kenan ba. Girgiza kai Nadeeya tayi, ta matsa suka fice tana jin rashin kyautawar maman, da na kowa ne kuma Asma'u da Adam duk na ta ne, duk daya suke a wajenta ya kamata ace tayi mata adalci kamar yadda take kokarin kare Adam din, ita fa duniyar nan kaso naka ne, duniya taki shi, kaki shi kuma duniya ta so shi, shi da da dukiya baa musu mugunta dan baka san wanda zaka mora ba.    Har ga Allah bata ji dadin abinda yake faruwa tsakanin Maman da Abban su Asma'un ba da tun da suka taso suka san yadda Abban yake daukar Maman da yadda itama yake a wajen ta, wanda suka san shine dalilin da har ya iya daukar Asma'u da tafi kowacce yar sa hakuri da saukin kai ya bawa mutum kamar kanin nasu Adam da su kansu watarana basu tsira daga rashin mutuncin sa ba.      ***Ganin motar Abba a kofar gidan tsohon ya saka mama tabe bakin ta, tana jin ta shirya wanke Abban har an kawo matsayin da ba zai tsaya shi da ita su fahimci juna ba sai ya kawo maganar wajen tsoho. Kamar Adam ba zai fito daga mota ba, dan ya dan dau sakanni a ciki kafin ya fito tamkar bijimin sa, yabi bayan Maman yana sake tamke fuskar sa.     A tsakar gidan suka tarar da su Abban a zazzaune an shinfida tabarmi guda biyu Umma da Asma'un ba kai daya sai su kuma mazan na daya, wajen su umman Maman ta nufa ta zauna daga gefe sosai shi kuma Adam din ya tsaya a tsaye yaki karasowa har sai da tsoho ya buga matsa tsawa "Zo ka samu waje ka zauna ka yi mana tsaye aka!" Sai da ya maula yana daga tsayen suna kallon sa sannan ya dosana duwawun sa a gefen tabarmar ya zauna.    Sai alokacin Mama ta gaida tsohon ya amsa a sake yana tambayar ta bayan saduwa, sai kuma umma ta gaishe ta, ta amsa a gadarance, idon ta na kan Abba da yayi kamar be san da shigowar ta wajen ba, abinda yafi bata mata rai fiye da komai ta dinga satar kallon wajen su sai taga yayi mata kwarjini sosai kamar ba shine kaninta me kaunar ta da kaunar duk abinda ya zama mallakin ta ba. "Toh Alhamdulillah, abinda ya tara mu anan ba wai boyayyen abu bane, magana ce akan Adamu da matar sa Asma'u, wanda muke so kowanne a cikin su ya dubi girman Allah, ya fadi gaskiyar abinda ya hada su. " Da sauri Abba ya tare shi, " Allah ya baka hakuri Baba, ban tari numfashin ka ba, amma Adam ya bawa Asma'u takardar ta kawai, shine dalilin zuwan mu nan ba maida magana ba, maganar abinda ya hada su kuwa duk wanda ya zalunci wani a cikin su, toh Allah yayi masa sakayya tun a duniya." " A ah karami, ba'a shishigi a cikin al'amarin ubangiji, bari mubi komai a sannu, bamu san abinda Allah ya boye ba." " Babu abinda Allah ya boye, kuma dai kamar yadda Karami yace ne, babu bukatar a zauna ana maida magana, kai Adam, saki Asma'u anan ba sai an bar nan ba, ka tashi mu tafi." Ran tsoho ne ya baci, ya kalle su, duk su biyun yace " Idan har zaku iya yanke hukunci haka menene amfanin zuwa gareni? " " Allah ya baka hakuri Baba, duk abinda kayi daidai ne. " Abba yace yana jan bakin sa yayi shiru, itama Maman bata sake cewa komai ba, ya kada kansa yana duban Adam " Adamu kaine gaba da Asma'u ba a shekaru ba kawai hatta a wajen Allah saboda kai din shugaban ta ne, kuma mijinta, inaso ka dubi girman Allah, ka sanar damu abinda Asma'u take maka a zaman ku da ita." " Menene ma bata yi min ba, gata nan ai, tasan koma a tambaye ta." " Bana son sakarci, tambayar ka nayi kuma kai nake son ka amsa min, ai na ganta din kai nake so ka fada min. " Shiru yayi dan bashi da abin fad'a, kallon sa Hajiya ta dinga yi tana masa signal yayi magana, ya kasa cewa komai har sai da tsoho ya sake maimaita maganar sa sannan yace " Ta raina ni ne, bata bani girma na a matsayin na, na mijin ta. " " Muna sauraron ka, kamar wanne irin raini? " " Raini dai kawai, idan nace tayi abu sai ta ga dama zatayi, ko gaishe ni bata yi bare na samu kuautatawa irin ta mata da miji. " " Toh Adam, bayan wannan fa? " " Naam. " " Bayan wannan fa sai me take maka, karka ji komai ka fada mana. " Shiru yayi yana kokarin tuna abinda zai ce, " Shikenan abinda take maka ko? " Shiru ya sake yi nan ma, " Toh Madallah, ko zaka iya fad'a mana abinda ya faru har ka daga hannu ka dake ta." " Duka? " Yace sai kuma ya kalli Umar ya dauke kansa da sauri " Eh duka, mahaifiyar ta da dan uwanta sun tarar da kai kana dukan ta, shine muke son sanin dalilin hakan. " " Ita ta tunzura ni, na dake ta ai, magana nayi mata ta tashi ta hada min breakfast tace ba zatayi ba, ta hau zazzagi na, shine ni kuma na sake ta." " Zagi? Wanne irin zagi kenan? " Kafin ya bud'e baki Mama tayi karaf tace " Zagi dai kowanne iri ai sunan sa zagi, ni kaina na san abinda ku baku sani ba, akan faduwar da tayi wanchan karon, duk a dalilin yana bin ta akan hakkin sa ne ya saka ta wannan faduwar saboda ta tsani ta hada inuwa waje daya dashi. " Maido da hankalin sa yayi kan Mama, yayi murmushi yace " Asabe ban tambaye ki ba, amma naga alamar kamar kin fi Adam sanin matsalar gidan sa, sai ki sanar damu abubuwan da kika sani. " " Ga Asma'un nan a tambaye ta ai, idan ba hakan ne ya faru ba, dan har Umman tasu nayi wa maganar amma ta nuna ko in kula akai, kuma da kaina na tambayi Asma'un ko Adam din ne ya sakata faduwa amma tace min a ah, duk wannan abun Adam yayi hakuri ya zauna a haka da ita, amma shine har Umar yana da damar da zai shiga har gidan sa ya dake shi, saboda ya taba yar gwal. " " Ko akwai hukuncin duka a musulunci? Irin wanda Adam din yayi wa Asma'u?" Juya zancen tayi zuwa wani daban, Abba ya girgiza kai yana cike da mamakin Maman. " Toh duk ba wannan ba Asabe, kinsan a sanadiyyar dukan da Adam yayi wa Asma'u har da barin ciki da tayi? " " Ciki? " Tace tana zaro ido, sai a lokacin ta kalli Asma'un, sai tsoro ya kamata ganin yadda fuskar Asma'un tayi, tana masifar son jikoki dan bata da su, musamman ta bangaren Adam din, amma shine har akayi cikin har ya zube bata san dashi ba, da ta san dashi ko kuda ba zata taba bari ya hau kan Asma'un ba, bare har wani abu ya sameta. Tayi nisa a tunanin ta, duk basuyi aune ba, sai tsinkayar muryar Adam din sukayi a tsakar kansu, muryar sa cike da izza da rashin mutunci yake furtawa "Na saki Asma'u saki uku!" Wani irin zillo Hajiyar tayi ta rafka salati tana kwala kiran sunan sa, tuni har ya suri takalmin sa yayi hanyar barin gidan, duk suka bishi da kallo Abba ransa fes, fuskar Umma tamkar gonar auduga, ita kuma Asma'u hawaye ne ya gangaro mata a saman kuncin ta, ba wai hawayen bakin ciki bane, hawaye ne kawai da ba zata iya tantance na menene ba, ta dai ji sun zubo mata kawai. "Alhamdulillah." Abba yace daga zaune, "Allah ya ga niyyata ta son karfafa zumuncin mu Yaya duk da sanin waye Adam da irin halin sa, amma na dauka cewa Adam da Umar duk nawa ne, kuma hannun ka baya rubewa ka yanke shi ka yar, ki gafarce ni idan nayi miki ba daidai ba, itama Asma'u tana da hakki akaina a matsayin ta na yata, na bi mata hakkin ta kar Allah ya kamani da hakkin ta ranar gobe kiyama. " Wani abu ne ya daki Maman, ta kasa motsa ko da yan yatsun ta ne daga wajen, tana ji tana gani suka tashi dukkan su, sukayi wa tsohon sallama suka fice. Da k'yar ta mike ta fito sai ta tarar babu motar da suka zo, Adam tafiya yayi ya bar ta kenan, Nadeeya ta kira a waya bata daga ba tana wanka, sai ta shiga takawa a hankali zuwa titi, ta tsaida napep ta hau zuwa gida! _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* *RM*      16 ***Suna isa gida suka tarar da Ya Hadiza tazo, yanayin da ta gansu ya sakata rage damuwar da ta tawo da ita, falon Abba suka wuce gaba daya, Asma'un ta kwanta su kuma duk suka zauna. Ajiyar zuciya Abba ya sauke bayan ya nutsu yace "Toh dai kunga yadda Allah yake al'amarin sa, tun farko ba wai na aurawa Asma'u Adam bane dan bana son ta, babu iyayen da basa son yayansu kuma ba zan taba cutar da Asma'u ba, ina so ki saki jikinki, ki cire komai a ranki ki dauka hakan shine kaddarar ki, in sha Allah Allah zai kawo miki miji na gari ko dan hakurin da kikayi." "Haka ne." Ya Hadiza tace tana kallon umma da taki saka baki "Wai har yanzu fishin ne hajjaju?" Abban yace wa umma yana son tabo ta "Toh ga yayanki nan dai suna kallon ki, ku tayani bawa gimbiya hakuri Umar." Dariya suka saka dukkan su har Asma'u, suka mike daya bayan daya suka fice Ya Hadiza ta tallafa mata zuwa dakin ta, tsohon dakin ta da ta tafi ta barshi ba tare da ta shirya ba.   Suna fita umman ta mike itama tabi bayan su, Abba yayi murmushi kawai dan yasan halin kayarsa, fushi take dashi sosai amma yasan zata sakko ne. Fita suka sakeyi da Umar suka biya aka siyo wa Asma'un nama me yawan gaske, Abban yace ayi mata farfesu ta ci sosai sannan a sarrafa mata wani, Ya Hadiza ce tayi aikin kafin ta gama ma sai gasu Hidaya da Rauda kusan a tare, dukkan su da tsohon cikin su, tare suka zauna da ita har dare sannan suka tafi, suna tafiya bacci ya dauke ta dan dama ta gaji sosai ga ciwon kan da yaki barin ta. ***Sau biyu me napep na nanatawa Hajiya Mama an zo, kafin taji dan tayi nisa a kogin tunani, sauka tayi ta bashi kudin sa ta wuce zuwa cikin gidan, ta ja kafarta zuwa cikin falon da tunanin ganin Adam din a falon, baya nan babu kuma alamar ma ya shigo gidan, fasa zama tayi ta juya zuwa gidan nasa, ta kwankwasa kofar megadin sa ya bud'e, ya matsa da sauri ganin ta, ta wuce ciki ba tare da ta iya amsa gaisuwar sa ba. A kwance a falon ta tarar dashi yana waya sama-sama, cikin bacin rai yake maganar ta riski karshen in da yake cewa "To hell with her." Yaja tsaki ya kashe wayar, sai a sannan yaga Maman, ya kawar da kansa gefe a dole yayi fushi, bata zauna ba, daga tsayen ta kira sunan sa sai dai yadda sautin muryar ta, ya fita ya saka shi tashi dan ya ji fushi sosai a muryar tata "Adam!" Da ido ya amsa mata, ta nuna shi da da dan yatsa tace "Ni ka watsawa k'asa a ido, a bainar jama'a? " " Mah wallahi ba zan iya cigaba da zama a wajen nan ba, dan rainin hankali kina ganin yadda tsohon nan yake min wasu banzayen tambayoyi kamar dan jarida, Asma'un gwal ce? Da za'a dinga raina min hankali haka. " Sakar baki tayi tana jin sa, ya cigaba " Idan ma banda dai kaddara ni me zan da ita, taimaka mata fa nayi, kwantai tayi a gida na taimaka mata, shikenan sai ace za'a daga min hankali akai, babu dole ai dan ni dama ba wai ina son ta bane. " " Adam! " " Yanzu Adam ni kake kallo kake faffadawa wadannan maganganun? Duk abinda nayi maka a rayuwa? Yanzu har ni zaka iya wulakantawa a gaban mutane kayi saki irin sakin da yake mafi muni sannan ka taho ka barni. " " Raina ne ya baci, su je su jika yar tasu su sha, idan ta rube musu a gida su suka jiyo, mtsw! " Dauke shi tayi da mari, mari me karfin gaske, rik'e wajen yayi cikn tsananin mamaki, Mama ce yau ta mare shi, abinda bai taba faruwa ba a kaf rayuwar sa, akan wata banza, akan wadda be taba dauka a cikin jerin mutanen da suke da muhimmanci ba. "Bansan baka da mutunci ba wallahi sai yau, nayi dana sanin barin ka da nayi haka sakaka, dama duk abinda ka fada min akan Asma'u karya kayi mata, ka saka na musgunawa yar mutane saboda farin cikin ka, karshe ka dake ta, dukan da yayi sanadiyyar zubewar gudan jininka, amma ko gezau baka ji ba!? Baka ji komai ba?" "Ni tun chan dama bana bukatar haihuwa, it's too early ni ban shirya hayaniya ba, yara stress ne kawai, da damuwa su ishi mutum. " Saura kiris ta fadi daga tsaiwar da tayi, ta rik'e gefen kujerar da take kusa da ita, bakin ta ya kasa sake furta komai saboda kaduwa, haka tayi sakaci? Haka tayi sakaci da rayuwar Adam har ta lalace haka? Ashe shima namiji kamar mace kana bukatar jajircewa wajen tarbiyyar sa, kamar yadda zaka kula da mace a tsare mata mutuncin ta haka da namiji ma ya kamata kayi masa? A tunanin ta babu wani abu da yake tsakanin iyaye da yaran su maza, musamman iyaye mata basa iya tsawatarwa yayan su maza da zarar sun kai wani lokaci, sai a sake su da tunanin duk abinda namiji yayi ado ne, hakan shine silar gurbacewar al'umar mu, domin namijin shi ne zai dawo ya fara bata rayuwar yara matan da aka tsare aka kare!        Zagaye kujerar da take kai yayi ya fice daga gidan yana kunkuni, zuciyar ta, ta dinga bugawa da sauri, jinin ta nan da nan ya hau saboda bacin rai, ji tayi ba zata iya tashi ba, sai kawai ta zauna a wajen tana kokarin ganin ta samu daidaituwar zuciyar ta.    Wayar ta dake cikin jakar hannun ta, da ta dire a falon ta wuto gidan Adam din Nadeeya ta kira, sai taji ringing din a falo, ta taso tazo ta duba sai taga jakar, a tunanin ta Maman na daki ko ta shiga toilet, amma kuma shiru har lokacin yaja sosai bata fito ba, zuwa tayi ta kwankwasa jin shiru shiru ya sakata turawa ta gani,babu kowa a ciki, nan da nan sai hankalin ta, ya tashi ta shiga duba Maman lungu da sako a cikin gidan, ganin dai da gaske maman bata nan, duk kuma masu aikin babu wanda yaga shigowarta, kiran Adam ta yi, har ta karaci ringing dinta be daga ba, tana kokarin kiran Asma'u taji ko har lokacin basu gama bane, sai ga Maman ta shigo a cikin yanayin da ya tsorata su, duk sun yi cirko cirko tazo ta wuce ciki Nadeeya tabi bayan ta da sauri tana tambayar abinda ya faru. "Nadeeya na cuci kaina, na cuci Karami na kuma cuci Asma'u da zumunci, ashe Adam shine bashi da gaskiya, kinga dukan da yayi wa yarinyar nan, ya kuma zubar da cikin da yake jikinta, cikin da na kwallafa rai nake dakon zuwan sa, ashe wai har yana da bakin magana, hmm." "Subhallahi, gaskiya boy be kyauta ba, be yi adalci ba sam, daman ni nayi tunanin haka, saboda kusan abinda ya faru kenan lokacin da tayi rashin lafiyar nan, ban sanar dake bane amma Adam sai da ya kusan yi mata illa, dan kusan fyade yayi mata." "Na shiga uku na, amma shine baki fad'a min ba? " "Toh gani nayi ba wai abun fad'a bane, da kunya kuma tunda hakan sirrin su ne, babu ma kyau fadar, amma nayi masa fad'a sosai wallahi, yayi min alkawarin ya daina kuskure ne ma, shi yasa na kyale maganar ma." Dafe kanta tayi da hannu bibiyu, " Adam yayi asarar mace, yayi asarar mace daya tamkar da dubu, ya cuci kansa kuma sai yayi dana sani." " Ya rabu da ita ne? " " Saki uku yayi mata, sakin wulakanci,. " " Ya Salam, ya Salam! " ***Wuni Maman tayi a daki, dan sai da Nadeeya ta dubata tayi mata bp dan jinin ta ya hau sosai, shi kuwa gogan ko sake waiwayo gidan be ba, a dole fushi yake da Maman akan ta mare shi, gidan Fido yayi tafiyar sa ya kwanta yayi bacci, yana farkawa ya ganta a zaune a gefen sa cikin yanayin damuwa. " Lafiya?" Yace dan har ga Allah ya bashi tsoro da farko. Takardar hannun ta, ta mika masa tana tabe bakin ta, "Duba ka gani." Karba yayi ya hau dubawa, be gane komai ba , ya mika mata cikin son jin ta mecece yace "Ban gane komai ba, takardar menene?" "Takardar ciki ce, I'm pregnant with your baby." Wani yimm yaji akansa, ya daga ido yana kallon ta, kallon karki rainawa kanki hankali mana, itama kallon nasa take a dake, dan ta riga ta shirya komai ba zata taba jin tsoron hargagin sa ba. "Ciki kuma, kamar ya?" "Ciki dai ciki dai." Mikewa yayi ya zabure "You must be kidding, ciki ana zaune kalau, ta yaya kika samu ciki?" "Ka fini sani ai." "Kin ga... Bana son wasa please" "Allah ba wasa bane, ciki ne dani kuma cikin ka!" Chakumar wuyan rigarta yayi "Ni zaki raina wa hankali? Wallahi karya kike kije tun wuri ki nemo ubansa, tun dare be miki ba. " "Akwai ubansa da ya wuce kai ne, saki ne malam!  Tayi masa nuni da hannu, kin sakin ta yayi, ta fincike tana mikewa "Ko kaki ko kaso wallahi kaine uban cikin nan, idan ma baka yarda ba toh, kanka, zan je in da za'a saka ka karba ta karfin gaske." Kiranta ya dinga yi amma tayi masa banza tayi ficewar ta ta bar gidan ma, tsaki yaja ya mike shima ya fito, sai ya koya mata hankali sannan zata gane shi ba sa'anta bane, kuma ciki ba zai karba ba, dan be shirya daukar dawainiyar kowanne yaro ba bare ya takura masa ya hanashi more rayuwar sa, da zarar ka haihu shikenan sai duk tsufa ya kamaka, ina ba zai iya ba, idan ma tun wuri zata nemi uban yaronta ta nema ba sai dare yayi mata ba. Mota ya shiga a fusace ya tada kura, ko gefen sa baya dubawa gudu kawai yake yi a cikin layin, duk wajen da yazo sai an kalle shi an kara kalla, masu Allah wadai nayi masu matsawa da sauri nayi dan har wani tsoho ya kusan zubarwa akan keken sa, kwana yazo zai sha wanda yayi daidai da fitowar su, suma zasu sha kwanar, yadda ya shigo da mugun guda babu horn ba komai ya sakasu kusan hadewa Allah ya takaita amma dai sai da suka taba juna. Fitowa yayi a fusace, a dole an masa laifi yayi wajen motar yana zage zage, a dole an masa laifi, babu wanda ya motsa a cikin su, suna zaune daga motar suna kallon sa har ya karaso ya daki glass din gefen driver din, tint ne a motar shiyasa be iya ganin na ciki ba, hakan ya taimaka wajen sake kular dashi sosai, zuge glass din akayi, yayi masa kallon raini yace "Malam haka ake tuki a garinku?" "Ban sani ba." Adam yace a fusace "Idan ka iya koyawa ai sai kazo ka koya min yadda ake yi din." "MD let him be please, kasan bana son hayaniya, menene damage din da akayi masa, ya fad'a sai a biya shi." A dage Adam ya kalli na gefen da yayi magana, ya watsa masa banzan kallo "Kai waye da har zaka iya biyana,ko an gaya maka ni matsiyaci ne." Wanda aka kira da MD ne yace "Kai fa na lura kamar baka da aikin yi, mu bamu da lokacin batawa, idan zaka fadi abinda za'a baka ka fada, idan baka fad'a mu wuce." "MD... " Ya kira shi yana saka masa ido " Abuya, please ka bari mu kyale guy din nan, kasan sauri muke, yaci kansa kawai." Daga haka ya daga glass din sama, ya take motar suka bar Adam a wajen tsaye yana zage zage, da kyar ya tattara ya koma wajen motar sa cike da haushin na gefen dan shi yafi bata masa rai dan yadda yake magana kawai ya lura dashi, hakan ya sake kular dashi, ya rike number din motar watarana zasu gauraya ko ba yau ba,sai ya nuna musu shi din gogaggen dan duniya ne na ajin farko! Gida ya wuce kai tsaye, tun be karasa kofar gidan ba, ya hangi motar Fido a fake a kofar gidan su, wani irin wrong parking yayi ya fito da sauri, ya fad'a cikin gidan nasu jikin sa har rawa yake yi! *RM*         *17* ***A durkushe ya samu Fido din a tsakiyar falon su tana kuka wiwi, daga gani bayani ta gama yi, wajen da Hajiya take zaune ya kalla sai yaga tana hawaye. Kan Fido din yayi gadangadan, ta mike da sauri tayi tsalle zuwa bakin Nadeeya da take tsaye cike da mamakin Adam din. "Karka kuskura ka taba ta." "Me tazo tace muku, wacce karyar tazo ta sanar daku?" "Ka santa kenan ashe." Hajiya Maman cike da takaici, sai a sannan ya tuna tabargazar da yayi, da ya sani ya nuna be gane ta ba, a kada a raya yace shi sam be gane ta ba. " Kina ina fiddausi." " Gani Mama." Tace kamar ta kirki " Kiyi hakuri dan Allah dan darajar annabi ki bar maganar nan, idan ta fito ba Adam ba, ni kaina na shiga uku, ki fadi ko nawa kike so zan baki amma ki tafi kiyi nisa sosai da nan, dan Allah na roke ki." " Gaskiya ba zan iya ba, saboda ni ba yarki bace? Bayan shi ya bata min rayuwa ya raba ni da nawa iyayen sannan kice na hakura na tafi, ina zanje da ciki?" " Toh a zubar, dan Allah ki taimaka min." " Mah ya zaki tsaya kina bawa wannan yar iskar hakuri." " Idan ka sake magana sai naci mutuncin ka wallahi, duk ba kai ka jawo min ba." " Atoh, ni dai wallahi bansan yadda zan da cikin nan ba, ba zan kuma iya zubarwa ba, ko Adam ya karbi cikin sa ta cikin lumana ya yarda ya aure ni, ko na kaishi kotu wallahi." Sai ta mike, " Zan dawo gobe, kafin nan sai ku yanke abinda zai fi muku." Ta harari Adam din, ya kai mata duka ta goce, kunya kamar zata kashe mama, ga takaici ga baccin ran abinda ya faru ga kuma wannan masifar, yanzu ya zatayi da wannan yarinyar? Daga ganin ta, tatacciyar yar bariki ce, ba abinda ya dame ta, bata ki ayi duk abinda za'a yi ba, dan babu kunya ko digo a al'amarin ta. Tana fita ya dawo kan Maman zai yi magana ta daga masa hannu " Bana son naji komai, kaje yadda ka ja ra'ayin ta babu wanda ya sani kaje ka roke ta, tayi hakuri ta zubar ko a bata kudi." " Allah ya kiyaye walalhi, ita din banza, babu abinda ta isa tayi wallahi, karya take ni ban mata komai ba, ta san in da dare yayi mata dan babu shegen da zai sakani na karbi abinda ban yi niyya ba." " Har ni!?" Maman tace Kunkuni yayi, ya wuce ta rafka tagumi zafi goma da ashirin kenan, ina zata saka kanta ne taji dadi. Sakayyr da Adam din zai nuna mata kenan bayan duk irin gatan da ta nuna masa. ****Har suka karbi sakon suka bar unguwar MD be daina tsaki ba, gayen yayi masifar bata masa rai, dan dai Abuya yaki barin sa ne da sai ya gane cewa su ba sa'annin sa bane. " Still dai baka hakura ba MD?" Ya tambaye shi yana dora kansa saman kujerar motar daidai lokacin da suka shigo layin su " Kana ganin fa yadda yake daga mana kai, shiyasa ni fa yanzu ban fiya son fita tare da kai ba, ka fiya hakuri wallahi, dani kadai ne da ya gane shayi na ruwa me." " Menene amfanin rashin hakurin? Beside ba wai yayi mana wani abu bane me muni, ko da ace yayi din ai be kamata mu biye masa ba ko?" Dukan sitiyarin motar yayi, " Kullum haka kake cewa, ai kai kam kana da heart of gold, matar ka ta huta wallahi." Dariya ya saka yana maida ganin sa zuwa cikin katafaren gidan nasu sanda gate din gidan yake budewa, sai da suka shiga ciki motar ta daidaita sannan ya bashi amsa " Kai kuma matar ka ta shiga uku da mitar ka." Balle murfin motar yayi ya fita, ya zagayo ta bangaren MD din yace " Mika musu sakon ka same ni a masallaci,." "Okh Ya sheik!" Murmushi kawai yayi, ya nufi masallacin cikin gidan yana nannade hannun rigar sa. Ciki MD din ya shiga dauke da sakon Baba Alhaji, ya tura kofar falon ya ajiye saboda babu kowa, ya fito ya nufi masallacin dan yasan duk suna chan. Sallah sukayi tare da ma'aikatan gidan da makwafta na kusa da suke shigowa ta kofar waje, ana idarwa suka zauna karatun bayan magriba har zuwa lokacin isha, sannan suka yi sallar kowa ya fito, tare suka jero da Baba Alhajin suka saka shi a tsakiya suna maganar aiken da yayi musu, MD ne yake bashi amsar duk tambayar da yayi dan shi gogan dama mafi yawancin lokuta MD din ne ke aron bakin sa yaci masa albasa, sai ayi abu sau tari sai dai yayi murmushi kawai, baya dogowar hira idan ba da MD din ba, shi kadai yake sakewa suyi hira sosai, mutane har tambaya suke anya Abdallah yana magana kuwa, dan sai ka wuni dashi baka ji yace komai ba. Sai da suka rakashi har ciki, ya zauna sannan suma suka zaune cike da girmamawa, ya kalle su dukka, yace "Abuya, miko kayan nan na gani." Tashi yayi ya dauko ya kawo masa gabansa ya ajiye, "Kai kuma Mudassir, tashi ka bud'e mu gani, Allah dai yasa an yi abinda ya dace." "Amin, suka amsa MD ya bud'e kayan suka dudduba, komai yayi yadda ya kamata, maida su gefe akayi, suka dan taba hira kad'an kafin su tashi su wuce zuwa shashen su. Suna shiga MD ya fad'a saman kujera ya sauke numfashi, " Mitar ce?" Yace yana kokarin shiga chan ciki " Kana da matsala wallahi." " Toh ai naga abu baya wucewa wajen ka ne fa." " Wannan din ma be wuce ba, har sai na hadu dashi na koya masa hankali." " Allah ya bada sa'a." Ya wuce ciki, ya sauya kayan jikin sa sannan ya dawo falon nasu, ya tarar da MD din yana waya, yana kashe murya tamkar bashi ba, girgiza kai yayi ya jawo laptop dinsa ya jona ya shiga rage ayyukan dake kansa. ***Bangaren Asma'u kuwa, sosai ta kwantar da hankalin ta, dan dama ba wai ta damu bane, kawai dai tana bukatar healing daga abubuwan da suka faru, gata babu irin wanda Abba ya nuna mata, yana dawowa gjda zai saka a kira masa ita su zauna yayi ta hilatarta da hira, tun tana nokewa har ta saki jikinta, tana jin ya dawo idan ta daidaici ya huta take zuwa, hakan ya taimaka kwarai wajen samun nutsuwar ta, bata tuna Adam bare shirgin sa, ranar suna zaune Hajiya Mama ta kira Abba, tunda abin ya faru bata kira shi ba, dan bata da bakin da zata masa magana, yanzu ma maganar Fido ce ta hana ta sakat dan yarinyar babu alamun zata hakura, ita kuma a yanzu duk yadda zatayi ta kare mutunci da martabar gidan ta zatayi. Tashi yayi ya saka Abbati ya kaishi, sai yayi mamakin ganin ramar da Hajiya Maman tayi, kana gani zaka gane bata da lafiya sosai,ji yayi duk babu dadi, ya zauna ya gajshe ta, ta amsa masa a kunyace ta saka aka kawo musu ruwa, fita waje Abbati yayi ya barsu su kadai, ta shiga sansr dashi matsalar da take fuskanta tun bayan rabuwar Adam din da Asma'u, shiru Abban yayi yana nazarin maganar a zahiri, a badini kuwa girman Allah yake sake gani, ko babu komai Asma'u ta wanko, kuma tayi biyayya irin wadda ba kowa ne zai yi ba, ganin yaki cewa komai a tunanin ta ba zai taimaka mata ba, sai ta fashe masa da kuka tana bashi hakuri, da sauri yace "Dan Allah Yaya kiyi hakuri, komai ya wuce a waje na, yanzu kokarin yadda zamu kauwar da matsalar da take gaban mu ce kawai, abu daya za'a yi, shine tirsasa Adam auren yarinyar nan, idan ba haka ba, matsalar da zata jawo gaba sai tafi haka, kuma kince dalilin sa take zaune a garin nan." "Haka ne." "Toh shawara daya, ya aureta,tunda sun fahimci juna sun san junan su, zaman zai musu sauki, sai ta haihu a dakin ta cikin rufin asiri." "Na shiga uku, yanzu Karami ina rufin asiri a haihuwar tit." " Toh ya za'a yi Yaya? Ko kina da wata shawarar." Girgiza masa kai tayi, " Kin gani, hakan shine rufin asirin mu dukka." Shiru tayi kamar ruwa ya cinye ta, ta dinga jan maganar ta gaza furta abinda zata ce, bata san da wacce fuskar Abban zai kalle ta ba, kila ya kirata da wadda tafi kowa son kai a duniyar baki daya, har tsawon mintuna ta gaza cewa komai, yana lura da yanayin ta, magana take son yi ta kasa, mikewa yayi yana gyara babbar rigar sa " Zan koma Yaya, idan akwai wani abu sai a sanar dani." " Toh toh, nace ba... Dan Allah ba zakayi hakuri Asma'u ta dawo dakin ta ba?" Chak ya tsaya da abinda yake, ya kalli Maman, tayi saurin dauke kanta, shiru ya biyo bayan maganar ta ta, dan be san me zai ce mata ba, kunya ce ita kanta ta kamata, tayi saurin cewa "Bansan na furta ba, kayi hakuri." "Allah ya kyauta." Yace kawai yayi mata sallama ya tafi, yana fita ta dafe kanta tana jin kamar zai tarwatse mata, sakamakon makauniyar soyayyar da ta nuna wa Adam din kenan, karshe ita zai saka a masifa dan ta lura shi be damu ba da duk abinda yake faruwa ba, kwana biyu ma bata saka shi a idon ta ba, an dai tabbatar mata a gidan sa yake kwana amma baya shigowa nan din, hankalin ta duk yana kanshi tana tsoron kar yaje yayi wani abun. Ranar da wuri ya shigo gidan, ya kalli dinning area din yaga wayam, tsawon kwanaki uku kenan duk sanda ya shigo gidan sai idon sa ya jashi zuwa dining din, daga nan sai zuciyar sa ta tunzura shi ya kawar da tunanin da yake neman hanashi sukuni, shiyasa baya zama a gidan kwata kwata, da ya shigo sai yaga tamkar ita din zai gani, yau ma dalilin dawowar sa gidan da wuri saboda kansa da yake masa ciwo, neman Fido yake ido rufe amma sam ko a waya baya samun ta saboda ta shirya ci masa mutunci, sosai ya shiga matsala sanadiyyar hakan da shi bashi da burin auren mace irin Fido din gashi kuma tana neman sakashi dole, duk da yana ganin babu uban da ya isa ya sakashi auren da be niyya ba. Kai tsaye sama ya hau, ya nufi dakin ta, inda koman ta yake a yadda ta barshi sai kayan sawarta kawai da Ya Hadiza tazo ta kwasar mata tun ranar da ta tafi, babu wanda yazo yace zai dauki wani abu kuma bayan nan, saman gadon ya fad'a mayen turaren ta da yake jin yana shigar masa hanci yana nan manne da zanin gadon da blanket din da ta rufa dashi a ranar da ya dake ta, kwanciya yayi, ya rufe kansa da blanket din kamshin na ratsa shi, ya jima sosai a hakan har sai da abun ya dawo kansa, ya tuna a inda yake, ya kuma tuna abinda yake, ya mike zumbur yana yin jifa da bargon ya sakko yana jan tsaki, cikin son karfafa kansa akan abinda yake ganin ba me yiwuwa bane, amsa kuwwa muryar ta, ta shiga yi masa a kunne tana ratsa shi, sanda take masa magiya akan ya daina dukan ta, muryar ta tar cikin yanayin wahaltuwa, kama kansa yayi da hannayen sa biyu ya damke, ya toshe kunne yana girgiza kansa, yana magana da sauri yana barin dakin "Na tsane ta, bana son ta bana kaunar ta, na tsane ta, na tsane ta!" Ji yayi zuciyar sa ta karyata shi, ta maida masa da martanin karya yake, da sauri ya suri key din motar sa, ya shiga ya bar gidan gaba daya, sai dai maimakon hakan ya taimaka masa wajen samun saukin abinda yake bijiro masa, sai ma abinda ya karu, yawo ya dinga yi a titi, ya shiga nan ya sauka nan ya rasa in da zai kai kansa, a ganin sa yana da damar da zai iya yin fatali da banzan tunanin da banzar zuciyar sa take saka masa ba, be san cewa, addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi da Allah, kai tsaye Allah yake amsata. Wasa-wasa sai gashi ya kusan kure duk titinan, gangarawa yayi wata babbar unguwa dake kusa da in da yake, ya shiga wani layi yayi parking motar ya kashe kawai ya kwanta a ciki. Ya dan dade a cikin motar dan layin babu mutane babu hayaniyar kowa duk suna cikin gidajen su, ji yayi an masa knocking a window din sa, ya dago ya kalli mutumin dake tsaye. "Malam lafiya?" "Kamar ya?" "Eh naga kazo nan ka zauna ne tsawon lokaci, idan wata matsalace sai ka fada ko?" "Ina ruwan ka? Ko tsabar shishigi!? Ku me yasa sam mutane bakwa minding business dinku ne, da kunga mutum sai kuzo ki ishe shi da tambayoyi, mtsw bana son irin haka." "Daga tambaya? Naga ka dade ne a wajen, kuma a ka'idar unguwar nan matsayin mu na masu kula da tsaron wajen bama barin bare ko wanda bamu sanshi ba, ya zauna haka babu wani abu, ka dauke motar ka kayi gaba, ko kuma ka fuskanci hukunci. " " In naki fa? " "Jikinka ne zai gaya maka. " "Babu in da zani, tunda dai nan din ba gadon gidanku bane ai, idan kuma gadon ku ne sai naji." "Owk, tunda haka kake so, fine! " Sai ya kalli bayan sa " Kuna ina!? " "Gamu sir." "Ku dauke shi daga nan, ku dan sassamamin shi ko zai koyi manner's." "An gama sir, Adam na zaune wai shi uban taurin kai, sai gani yayi sun karaso, suka bud'e motar suka fizgoshi, suka shiga lallasa shi tamkar yadda ogan nasu yace. Gate ne ya bud'e mota ta fito daga gidan Baba Alhaji, Abuya ne, shi kadai babu MD shima zai je ya siyo perfumes ne saboda nasa sun kare, ganin kamar suna dukan wani ya sakashi danne horn, suka dakata ya fito da sauri " Lafiya kuke dukan sa? " " Barawo ne! " " Barawo? " Yace yana leka fuskar Adam din, nan da nan ya shaida shi, dan yana da saurin gane mutum " Satar me yayi? " " Tun dazu yake zaune kamar bashi da gaskiya, shine oga yace bari yayi masa magana amma sai ya hau oga da cin mutunci, shine muke dan koya masa hankali." "Ku kyale shi, tashi." Ya mika masa hannu. Adam da yaci bugu sosai a wajen yan sandan majiya karfi ya kasa mikewar, bakin sa ya mutu murus dan har ya soma basu hakuri, be taba dakuwa irin ta yau ba tun da uwar sa ta haife shi, sai gashi a banza masu warin kashi sun daddaka shi saboda shegen bakin sa. Taimaka masa Abuya yayi, ya tashi sannan ya rakashi wajen motar sa,. Ya bud'e masa gefen me zaman banza ya shiga, sannan yace dan sandan guda yazo ya kaishi chemist sannan ya kaishi gida, ba musu yazo ya shiga, ya kalli Adam din da yaki yarda ya kalli bangaren sa yace "Kayi hakuri aikin su kenan, da ka basu hadin kai duk hakan ba zata faru ba." Kin magana yayi, ya juyar da kansa dan iyakar muzanta ya muzanta, har baya son ganin mutumin gashi ya tsaya yana bata masa lokaci da wasu maganganun sa na banza, kila ma su suka saka aka sake shi akan abinda ya faru ranar, amma koma menene, ai ba zasu dawwama a cikin unguwar tasu ba, idan kere na yawo, zabo na yawo toh dole zzsu hadu, kuma sai ya rama wulakanci da akayi masa. *RM*      18 ***Har kofar gida ya kaishi ya ajiye ya wurga masa mukullin sa ya tafi, gidan su ya shiga a maimakon nasa gidan da ji yake ya tsani duk abinda ya danganci gidan nasa, yana shiga Hajiya Mama ta dauke kanta kamar bata ga shigowar sa ba, sai dai yanayin yadda yake tafiya ya saka ta kallon sa, ya wuce zuwa tsohon dakin sa ya shiga, akwai matsala, ta lura abin ka da uwa mahaifiya sai ta kasa jurewa har sai da ta tashi ta bishi zuwa dakin, ta tarar ya cire rigar sa yana kallon bayansa a mudubin dakin, zaro ido tayi ganin layin bayan sa, yayi kamar be ga ta shigo ba, ya hau maida rigar sa "Me ya same ka?" "Ba komai." Yace yana to maida rigar jikin sa, "Karka fad'a min din, jikinka ne ai ba nawa ba, mun yanke shawarar aura maka fiddausi saboda rufin asirin mu." " Wa zai aure ta? Ni wai? Karya ma fa take bata da cikin komai, idan ma dashi ai baa aure da ciki ko? " Ya kyalkyale da dariya, shiru Hajiyar tayi, tunanin hakan sam be zo mata ba, tabbas musulunci yayi hani da aure da ciki, duk da akwai masu yi saboda son zuciyar su, itama sam bata tuna hakan ba saboda idon ta ya rufe, amma me yasa Abba ya bata wannan shawarar toh? Shima ya manta ne ko kuwa dai yana daukar ta a yanzu xata iya komai ma don biyan bukatar ta, shiyasa ma be tsaya nuna mata ba yayi komai a dunkule, nufin sa duk abinda zatayi kawai tayi ko da hakan ya saba wa addini, girgiza kai tayi ta juya ta bar dakin, jirin da take ji yana kara karuwa, kwanciya tayi ko zata samu sa'idah amma sai taji a kwancen ma jirin take yi, kiran Nadeeya tayi da ta tafi chan gidan kanin baban su da rikicin nan be bar Hajiyar ta samu halartar komai na bikin ba, saukin ta dama ba a gidan ake taron ba girki dai ne akayi anan da sauran abinda ba za'a rasa ba, shiyasa yau tace Nadeeya din taje ta kara basu hakuri, jin jikin nata ya kara rinchabewa ne ya sakata kiran Nadeeya din, tace ta dawo bata jin dadi, bata dade ba sai gata, ta tarar da Hajiyar zazzabi ya rafke ta, ga jirin da ya dameta a kwance ma yin shi takeyi, auna bp dinta tayi, taga yayi high sosai, ta shiga bata taimakon gaggawa, zuwa dare jikin ya sake rikicewa, dole ta dauke ta, ta tafi da ita asibiti, nan da nan akayi admitting dinta, aka daura mata drip, nabeela ta kirawo sannan ta kira fadeela ta fad'a musu an kwantar da Maman dan duk abinda ake su ba wani sani sukayi ba, nan da nan sai gasu, lokacin Maman ta samu bacci , ta rame sosai kamar ba ita ba.    Tare duk su ukun suka kwana da ita, dan dama duk babu me wani nauyi akansa, nauyin miji ne kawai babu wacce ta haihu cikin su, basu kira Adam ba, dan haushin sa suke ji sosai, duk shine yayi sanadiyyar shigar Maman halin da take ciki, kuma kamar be damu ba, kansa kawai ya sani.    Da safe ya shiga cikin gidan ya tarar basa nan, ya tambayi mai aiki suna ina, sai anan yake jin an tafi da Maman asibiti, ya ciro wayar sa ya kira Nadeeya amma bata daga ba, ya dinga jera mata kira har ya gaji, ya dauki mota dan yana da yakinin asibitin su zata kaita.    Yana zuwa ya samesu a chan dan a barander suka hadu da fadeela ta fito siyan abu, ta share shi yana mata magana tayi tafiyar ta, sai ya bin bayanta har ta siya abinda zata siya ta juya sannan yaga dakin da Maman take. Babu wanda ya kulashi a cikin su, ya shigo ya zauna kusa da Maman yana rik'e hannun ta a cikin nasa, baya so wani abu ya samu Maman dan bashi da tamkar ta kaf duniyar nan, ji yayi yana nadamar wasu abubuwan da ya aikata, wanda ya tabbata su suka janyo shigar matsalar Maman, ba zai kyale Fido ba, duk ranar da ya kamata wallahi sai yayi mata rashin mutuncin da bata taba zato ba, dan yasan ita ce ta sake assasa matsalar da Maman take ciki.    Ko da maman ta farka bata nuna ta ganshi ba, suka dinga maganar su, su kadai babu wanda ya saka shi a ciki, haka ya cigaba da zaman sa ba tare da ya damu ba, dan yasan babu wadda a cikin su zata hanashi zama a dakin.  Waje azahar Abba yazo dan sai a sannan ya samu labarin, ya dubata ya wuce da daddare suka sake dawowa da Umma itama ta duba ta, umma ta lura duk kunya ta hana Maman sakewa dasu, har suka tafi bata iya yin magana sosai ba, da safe Abban ya sake dawowa tare da Abbati da breakfast yace da rana umman zata zo ta sake dubata.    Asma'u na kwance umma tace ta tashi ta shirya zata rakata dubiya, tun da ta dawo gidan fitar ta biyu ce shima asibiti kuma tare da Umma suka je da Abbati, Hijab kawai ta saka me hannu maroon ta saka flat shoe ta rik'e wayar ta a hannu ta fito, ta samu umman tana karasa shiryawa. Titi suka fita kasancewar a napep zasu Abbati baya nan Umar ma haka, babu me mika su, shiyasa umma ta bar abincin sai da daddare wani a cikin su sai ya mika musu idan sun dawo.    Sai da suka shiga napep din sannan take tambayar umma in da zasu "Waye ba lafiya!?" "Hajiya Mama ce, kwananta biyu a asibiti kamar." "Allah ya kara sauki." Tace ta ja bakin ta ta tsuke har suka isa, suka nufi dakin kai tsaye tunda already Abba ya riga ya fad'a ma umma room number din.    Dakin a cike yake da mutane yawanci kawayen Maman ne sai su nabeela da fadeela sai sirakar fadeelan da tazo da kannen mijin nata, a waje suka dan tsaya na ciki suka fito sannan suka shiga, Hajiya na ganin su ta washe baki tana kafe Asma'un da ido, daga bayan umman Asma'un ta gaishe ta, ta dubata amma sai ta yafito ta da hannu, ta matsa gaban gadon a darare. "Ina wuni?" "Lafiya lou Asma'u, kina lafiya." "Lafiya lou." Ta amsa tana sunkuyar da kanta k'asa, "Zauna mana." Ta nuna mata kujerar gefen gadon, ta zauna ba musu tana zama Nadiya ya shigo, ta gaida umma cikin girmamawa sannan ta isa wajen Asma'u fuskar ta na bayysna farin cikin ganin ta, ita kanta Asma'u taji dadin ganin ta ko babu komai Nadiya ta nuna mata soyayya irin ta Yaya da kanwar ta, kuma ta sota da gaske ba kamar Hajiya da dan lelen nata ba, su dama Fadeela da Nabeela ba wani haduwa suka cika yi ba, amma duk da haka ta san ba kamar Nadiya da ta nuna mata soyayya fiye da Adam din da suka fito ciki daya ba.    Ita dai umma nata ido ne ganin yadda suke nan nan da Asma'un, wato baka gane muhimmancin abu sai ka rasa shi, wajen la'asar umman tace Asma'un ta tashi su tafi, fuskar Maman ce ta sauya zuwa bacin rai, tace "Har yanzu fushin ne umman su?" "Fushi? Akan me yaya?" "Akan abinda ya faru." "Ai da mun dauki fushi ko zuwa nan ba zamuyi ba, ko kuma nazo ni kadai na barta a gida, mu babu komai a zuciyar mu wallahi, ai ya wuce." "Toh idan da gaske ne, dan Allah ki bar Asma'u ta zauna zuwa anjima sai ta dawo." Girgiza kai Umma tayi " Kiyi hakuri." Sai ta kalli Asma'un da ta riga ta mike amma kuma bata taho ba " Muje, Allah ya kara sauki Hajiya." Daga haka ta tisa yar ta a gaba suka tafi, dan ko tasha giyar wake ba zata bar ta ba, akan me? Sai yanzu za'a nuna ana son ta bayan abu ya kwabe musu, hakan ma da suka zo ya wadatar ba sai kuma an nemi wani abun ba. Ita kanta Asma'un ba son zaman take ba, dan dai kawai ba zata saka baki a maganar su Umman ba, shiyasa umman na cewa su tafi tayi saurin bin ta.     Suna kokarin barin cikin asibitin Adam na sako kansa, su suna kasa shi yana mota basu ko lura dashi ba, shi dai ya gansu dan har wani burki ya taka da ya kusan janyowa na bayan shi ya taba shi, allah dai ya kiyaye, gefe ya ja ya matsa masa yazo ya wuce shi kuma ya juya motar yabi bayan su, be san dalilin bin nasu ba, kawai ya samu kansa da zuciyar sa da bukatar hakan, har sun tare napep zasu shiga ya karaso wajen, Asma'u ce ta fara ganin sa gaban ta yayi mummunar faduwa, tayi saurin fadawa napep din kafin ma umma ta gama yi masa kwantancen in da zai kaisu. "Ai kin tsaya a gama daidaitawa ko Asma'u!?" Umma tace tana shigowa itama, sai a lokacin ta ga Adam din, yana tsaye a gefen su zaune cikin motar sa, be fito ba kuma be tafi ba, dauke kai Umman tayi tamkar bata san shi ba, tacewa me napep din "Muje." Bari wajen su kayi ba tare da sun nuna sun ganshi ba, ya daki sitiyarin motar yana jan tsaki, me ya hau kansa ne da har ya aikata haka? Juya motar yayi zuwa cikin asibitin yana me jin haushin kansa. Duk yadda yaso ya yakice tunanin ta ya gaza, duk in da ya juya ita yake gani sanda ta kalle shi da zata shiga napep din, hirar ta yaji su Mama nayi da Nadeeya, ya kasa kunne yana saurara har da murmushin sa, sai bayan yayi ya kuma hade rai yana me jin haushin kansa, tashi yayi ya bar dakin ya fito waje ko zai daina jin abinda yake ji a ransa.    Yana fita Fido na zuwa ita da kawarta, reception ta tsaya sai da ta gano dakin da Maman take tazo dubuta, ita kanta Maman da ta ganta sai da ta ji gaban ta ya fadi, wani irin kwarjini da tsoron yarinyar take ji wanda ta rasa na menene, kamar mutuniyar arziki take gaida Hajiyan, shiru ne ya biyo bayan gaisuwar, har sai da Faiza ta dan zungure ta sannan tace "Mama dama batun ciki ne." "Naam?" Mama tace a kideme Nadeeya da ranta ya baci tace "Wai baku ga halin da take ciki bane, haba mana." "Abun da zai sakata warkewa ne ai, dan nasan shine dalilin kwanciyar tata, ciki dai na zubar dashi..." "Kin zubar?" "Eh, an ma da sharadi, dole Adam ya aure ni, magana tuni tana hannun hukuma idan ya amince sai na janye idan be amince ba shikenan." "Ya ma amince, ya amince ma." Murmushi tayi, suka kalli juna ita da Faiza, sai suka mike a tare suka ajiye ledar hannun su "Ga kayan dubiya, Allah ya kara sauki." "Angode, ku gaida gida." Suna fita Nadeeya ta dubi Maman "Mama tsoron ta kike?" "Sosai nadeeya, wallahi ko kallon fuskar ta bana son yi, idan Adam be aure ta ba zan taba samun nutsuwa ba. " " Innalillah wa inna ilaihi rajiun, Anya mama haka yarinyar nan ta barki? Karuwa ce fa, kalli zubin ta amma a haka zaki sa Adam ya aureta? " " Shi din menene Nadiya? Sanda yake kula ta duk be san hakan zata faru ba, ko kina ganin shi tunda namiji ne yaci banza, abinda ake nuna musu kenan, baka san da wadda zaka hadu ba, ba kuma kasan sharrin ta ba, tunda har ya kasa zama da mutuniyar kirki irin Asma'u bani da zabi, sai ya auri daidai dashi su karata, dama ai mazinaci sai mazinaciya irin sa. " Shiru Nadeeya tayi cike da tausayin Maman da Adam din, dan tasan Maman na fadar haka ne dan bata da hanyar da zata hana yarinyar, amma babu wanda zai so auren irin Fido duk lalacewar nasa dan! ***Duk yadda yaso abun ya bar kansa,ya kasa tsawon sati biyu kenan tunda ya ganta ya gaza sukuni,duk abinda yake yi ita yake gani. Gaba daya ya fita hayyacin sa, shiyasa ma ki maganar Fido baya tunawa, tun bayan dawowar mama daga asibiti da tayi masa maganar auren Fido din yaki amincewa, ta nuna bacin ranta sosai akai kawai yace suyi duk abinda suke ganin daidai, be sake sanin abinda ake ciki ba, dan ko yar fitar nan ya daina, yana gida a ko da yaushe tamkar bashi ba. Ba zai iya jurewa ba, duk yadda yaso ya yakice tunanin ya gaza har ya soma fita hayyacin sa, shiryawa yayi ya nufi gidan Abban kawai duk ma abinda zai faru ya faru.    Umma na tsakar gida da yake yamma ce su Abeed sun zo sai dare Baban su zai zo ya dauke su, fitowa Asma'u tayi ta zauna a gefen Umman tana jawo Abeed din jikin ta "Abba zai barni naje gidan su Abeed umma?" "Zai iya barin ki, kinsan yanzu lallaba ki yake, ki kirashi dan yace yau zai yi dare, ko ki bari idan ya dawo gobe sai ki shirya kije." "Ai ban ma hada kayan ba, idan ya dawo din sai na tambaye shi." "Hakan ma yayi, kwana nawa zaki?" "Sati daya." "Kai Asma'u har sati?" Dariya ta saka "Umma ai ba yawa satin fa, dan ma Abba ba zai bari ba da nayi ko sati biyu ma." "Lallai, satin ma ki yi addu'a ya barki, kinsan baya son ki matsa nan da chan, da ya shigo yake fara neman ki." "Tausayi na yake ji ai, ni kuma fa komai ya wuce na manta ma ni wallahi." "Shi ai yaki mantawa." Zatayi magana akayi sallama a dan corridor din da yake kafin ka shigo gidan, gaban ta ne yayi mummunar faduwa, ko a mafarki taji muryar shi sai ta firgita bare har taji shi a tsakiyar cikin gidan su, duk da tsoratar da tayi amma bata nuna ba, tana zaune kyem tana cigaba da wasa da hannun Abeed, umma ce ta amsa tana dan leka kanta, dan bata dau muryar sa, jin an amsa ya saka shi shigowa kai tsaye, ta mike ta kama hannun Abeed din suka shige ciki. "Adamu ne, shigo mana." Umma tace ba tare da ta nuna masa komai ba, babu kunya ya zo ya zauna a gefen tabarmar da Asma'un ta tashi, ya gaida Umman ta amsa ba yabo babu fallasa. Shiru ya biyo baya har sai da Umman tace "Hajiya ce ta aiko ka?" "A ah, wajen Asma'u nazo." Kallon ashe baka da hankali Umma tayi masa tace " Wajen Asma'u kuma!? Ko dai kayi batan kai ne? " " A'ah, tambayar ta nazo yi ne. " " Lallai Adam, yanzu kai dan Allah har kana da bakin yiwa Asma'u magana? Toh wai ba ma wannan ba, baka ji kunyar zuwa kace wajen ta kazo ba? Ban ce kwata kwata ba zaka zo gidan nan ba, amma ba wai wajen Asma'u ba, ko dan kaga mun kyale ka bamu kaika wajen hukuma ba. " Ransa ne ya baci, sai a lokacin yaga wautar sa ta zuwa, umma kuwa ta wanke shi tas dan dama rashin samun dama ne, yana ranta dan da wani ne bare wallahi sai sun yi shari'a dashi, kasa mikewa yayi har sai da ta gama yi masa tatas, tace kuma kar ya sake zuwa da sunan wajen Asma'u dan aure ma zatayi ta samu miji, wannan maganar ta karshe ita tafi firgita shi, har ya dauki hanyar gida baya gane abinda yake masa dadi. _RM_    *19/20* _Hafsat Rano_ ***Dariya abun ya bawa umma, ita kadai ta dinga janjana maganar Asma'u na jinta taki fitowa, bata san Adam din ma bashi da kunya ba sai yau, ko kuma dai tsabar rainin wayo ne zai wanko kafafu yace wajen Asma'un yazo oho, aikuwa ta wanke shi tsaf dan dama ta jima tana jiran ranar duk da bata saka ran zuwan ta nan kusa ba. Wayar ta dake gefen ta, ta jawo ta kira Ya Hadiza ta bata labarin abinda ya faru, dan ta rasa wanda zasu zanta Asma'u tayi mata kirmisisi kamar bata ma san anayi ba, ita kanta Ya Hadizan sai da ta yaba kokarin Adam din ko tace tsantsar rashin ta ido da har zai iya zuwa kuma kai tsaye yace yana son magana da ita, duk da basu san maganar mece ba amma zuwan nasa kadai ya isa ka gane komai,sun jima suna magana kafin a kira sallar magriba sannan suka hakura.    Duk abinda ya faru Asma'un na ji amma bata da ta cewa, bata kawo zuwan nasa na da wani muhimmanci ba kamar yadda su umman suka zata dan ta riga ta san Adam baya da bukatar wani abu wajen ta dan bata cikin sahun mutanen da yake ganin su da kima da muhimmanci da har zai iya tako kafar sa yazo dan kawai yayi magana da ita, tafi tunanin dai ko yazo na ya kara jaddada mata tsanar da yayi mata ne, wanda idan ta samu damar haka tabbas sai ta sanar dashi yadda itama ta tsane shi, dan kaf duni babu mutumin da ta tsana kamar Adam din ba.    Suna cikin cin tuwon dare ne mijin Ya Hadiza yayi sallama, ita ta amsa masa ya shigo bayan umma ta yafa mayafin ta duk da babu wani haske sosai a tsakar gidan, gaisawa sukayi a mutunce dan shi mutum ne na gari ga kirki sosai sun saba da yan gidan kamar gidan su haka ya dauki su umma tamkar iyayen sa, su Abeed yazo dauka, umma tace ya tsaya a kawo masa tuwon, ba musu kuwa ya gyara zama Asma'u ta kawo masa, umma ta koma cikin falo ya kuwa ci tuwon sa sosai sannan ya kwashe su suka tafi. Suna tafiya Abba ya dawo tare da su Abbati da Umar da suka rakashi zariya daga nan suka tsaya kasuwa sukayi siyayyar kayan amfanin gidan. Dakin sa ya wuce kai tsaye Umar yaje ya kunna gen da Abba baya jure zafi ko kad'an. Bayan ya zauna ya nutsu ya huta sosai ne Asma'u ta shigo tambayar sa zuwa gidan Ya Hadizan da take son yi wanda Ya Hadizan ce da kanta ta roketa tazo ta kwana biyu dan idan ta itace tafi son zaman ta a gida akan ko ina, fuskar sa ce ta fad'ad'a da farin cikin ganin ta, ya amsa sallamar ta yana tsokanar ta "Ma'u ce?" "Nice Abba, sannu da hutawa." "Yauwa sannu Asma'ul Husna." "Yawwa." "Akwai labari ne?" Yace yana matsar da plate din da yaci tuwo, tashi tayi da sauri ta kwashe ta matsar gefe ta saka tissue ta goge har miyar da ta zube sannan tace "Abba dama so nake naje gidan su Abeed." "Toh, wuni ko kwana?" "Kwana Abba." "Kin ganki ko? Har kwana nawa?" Sai da ta boye fuskar ta a jikin kujerar da take kusa da ita sannan tace "Sati daya." "Umma kina jinta ko?" "Wannan maganar ku ce, ba ruwana." Tace daga cikin daki, dariya kawai Abba yayi "Shikenan, Allah ya bada sa'a, amma kar a wuce satin." "In Sha Allah, nagode Abba." "Allah yayi miki albarka." " Amin ya Allah." Tashi tayi ta fita, Abba ya bita da kallon tausayawa, shi dai kawai yana tausayin ta sosai, tayi masa biyayya hakan ya kara masa son ta sosai.   Sai a lokacin ya tuna ya ga missed call din Hajiya Mama, ya kirata a lokacin saboda suna hanya bata shiga ba, duba lokaci yayi yaga tara tayi har da yan mintuna, kiranta yayi bata dauka ba, sai ya ajiye wayar ya mike kafarsa ya chanja channel tv ya shiga kallon labarai.    Daki ta koma ta hada kayan da zata tafi dasu waje daya, ta gama ta kwanta ta dan danna wayarta kad'an zuwa goma ta kashe ta kwanta gaba daya. Da safe ta tashi da shirin tafiya, har umma na tsokanar ta akan ta matsu, dariya kawai tayi, ta gama duk ayyukan da take taya umman zuwa sha biyu bayan Abbati ya kai Abba kasuwa ya dawo ya dauke ta, Abba be yarda da fitar ta ita kadai ba shiyasa ma yasa Abbati din ya dawo ya kai ta, lokacin Ya Hadiza na kitchen suka zo, ta fito da sauri ta rungume Asma'un tana musu sannu da zuwa. Daki ta kai kayanta ta dawo suka baje a falon sai hira, tafi sakewa da ita akan kowa yanzu dan sosai take jan ta a jiki take kulawa da ita, shiyasa tasu tazo daya, tare suka gama abincin ranar Abbati yaci sannan ya koma kasuwa wajen Abba. Yaran basu dawo ba sai yamma likis tare suke hadawa harda islamiyya, da murna suka dane ta dan duk miskilancin ta, tana sakewa sosai da yara, ta iya tafi dasu shiyasa suke nanike mata. ***Tun da Oga Adam ya koma gida sai ya kasa aiwatar da komai, ya dinga jin kamar ana hadeshi waje daya ana daddaure shi, be san me yake ji ba kai tsaye, amma yasan ko menene yana da nasaba da Asma'u, dakin ta ya shiga, wanda yake kamar yadda ta barshi, kayan sawar ta da sauran tarkacen ta kawai suka dauka sauran kayan da Hajiya Maman ce ta zuba basu dau komai ba, gadon ya hau ya kwanta yana tuna wasu abubuwa dangane da ita, runtse idon sa yayi ya bud'e su, yana mikewa a kasalance ya sakko k'asa zuwa kitchen ya dauki ruwa ya sha har lokacin tana sake masa gizo a idon sa, wayarsa dake aljihun sa ce tayi kara, ya ciro ta yana kallon screen din "Kana ina?" "Ina gida." "Ka shigo gidan ina son ganin ka." " Owk. " Yace ya kashe ya maida aljihun, maimakon ya je a lokcin sai ya sake komawa saman, ya watsa ruwa ya sauya kayan jikinsa sañnan ya shiga gidan nasu ya samu Maman tana waya, zama yayi ta gama sannan ta dube shi "Za'a je garin su fiddausi neman aurenta." Kirjinsa ne ya buga da karfi, sai a sannan ya tuna da wani maganar aure, ya rasa dalilin da ya saka Hajiyar damuwa da maganar, yadda tadage akan maganar auren ne zai baka mamaki, kamar bata san wace yarinya bace Fido din,yasan ba tuban gaskiya tayi ba, kawai dai akwai dalilin ta na kafewa sai ta aure shi, wanda shi akaran kansa be san dalilin menene ba. "Nifa ba zan auri yarinyar nan ba." "Aikuwa baka isa ba, aure kamar anyi an gama ne." "Wai Mah kin fi son ta ne akaina? Ko ni yanzu bani da wani amfani." "Oho, ban sani ba nima, aure ne dai babu fashi, ba zaka sake sani a wata masifar ba, karfin hali kawai nake ba wai Ina jin dadi bane, dan haka kar ma ka fara wata magana wallahi sai ka aureta sai dai idan mutuwa nayi." Mikewa tayi ta bar shi a wajen a zaune tamkar wanda aka dasa, be san yaushe Hajiyan ta chanja masa haka ba, wanda a baya ita da kanta take bashi zabin duk abinda yake so, ta kuma mara masa baya dari bisa dari, amma be san dalilin da yasa yanzu ta kafe akan lallai sai ya auri Fido din ba, bayan ita da kanta ta san abinda ya hadu ba wai abu bane me kyau. Ita kanta Hajiyar sau tari tana mamakin yadda take jin sam ba zata taba iya nutsuwa ba har sai an daura auren, tamkar ana hura mata wuta haka take ji, shiyasa ta dage kai da fata ko da hakan na nufin shigar Adam din hali na daban ne.      *** Waya Faizan ta gama suka kwashe da dariya a tare suka tafa, Faiza tace "Kin ga abinda nake fad'a miki ko!? Ai ba'a bori da sanyin jiki, maganin uwar kawai shine magana yanzu ba gashi nan ba komai na tafiya daidai, amma da ke kin dauki wata shawarar da ba zata bulle miki ba, hakan kuwa shine kawai maganin irin su, idan suka ki bi sai a biyad dasu, shima Adam din ki kyale shi zai gane bashi da wayo, sai ku zauna su gama daku sannan su ajiye ku su dauko masu kamun kai, ba zata sabu ba." " Wallahi ni sam hankali na be dawo jiki na ba, sai da na samu labarin yarinyar da yaga min ihun baya so har da barin ciki tayi, ina rashin so anan?" "Ke ya mayar gaula ai, ki zauna ki kare rayuwar ki a haka babu me kwasar ki, ko shi ba zai kwasa ba, bare wani." "Haka ne wallahi, toh ba zata sabu ba wallahi." " Ai da kin tsaya kallon ruwa." " Ai na dawo hayyaci na wallahi, ko nawa zan kashe, akan na same shi, idan yaso duk abinda zai biyo baya wannan daga baya ne." " Yawwa yar gari." Suka sake tafawa cike da jin dadin yadda abubuwan suke tafiya. ***Tunda tazo gidan Ya Hadiza ake kiranta da unknown number, da bata dagawa har ta fara dagawa amma sai ayi shiru tayi ta magana ita kadai, daga baya sai ta daina dagawa kawai ko sau nawa za'a kira, gashi na kiran wasa bane sai a jera kira yana katsewa guda goma, data gane idan aka kira ko sau daya ne ta daga ba za'a sake kira ba kuma sai bayan wasu awoyin sai ta cigaba da dagawa amma itama sai tayi shiru idan kuma Abeed na kusa da ita sai ta daga ta bashi yayi ta shirmen sa, har a gaji a kashe. Ranar juma'a bayan yaran sun dawo daga makaranta sun hutakasancewar da wuri suke dawowa ranar Abban su yace su shirya zai kaisu shopping, suka hau murna da shiryawa, daki Ya Hadiza ta sameta tace ta shirya zasu fita ana idar da sallah, tashi tayi bayan ta ajiye littafin da take karantawa ta shiga toilet din dakin tayo alwala ta fito, ta chanja kayan jikinta zuwa abaya ash colour me kyau, ta yane kanta da mayafin abayarw, very simple and unique, tayi kyau babu komai a fuskarta sai powder da wetlips. Ana idar da sallah Ya Hadiza tace ta fito, ta fito dauke da Abeed a kafadarta. "Kinyi kyau kanwata." "Kai Ya Hadiza." "Wallahi baki ganki ba, son kowa kin wanda ya rasa." Murmushi tayi kawai tabi bayan ya Hadizan zuwa mota, mamaki duk sukayi ganin motar Adam a kusa da ta Abban su Abeed din, suna tsaye tare kamar magana suke, dauke kai sukayi suka shige mota sai da Abban ya kara wajen minti biyar sannan ya shigo motar yana murmushi "Mutuminki ne fa, wai yazo wajen Asma'u." Gaban Asma'un ne ya fadi ta dafe da sauri, dariya taji Ya Hadizan tayi "Bashi da hankali amma ko?" "A ah, na raba ki da shiga tsakanin mata da miji fa, sai su shirya su barki da babatu. " "Ko Asma'u? " Yace yana juyo da kansa baya, bata ce komai ba, har suka bar unguwar kanta na k'asa kuma shi Adam din be tafi ba, sai ma biyo bayan su da yayi. Wani babban supermarket suka tsaya, yana kallon Adam ya parker daga bayan su Asma'u da ya Hadiza basu ganshi ba sam, ciki suka shiga, Abeed na hannun Asma'u ya Hadiza da mijinta suka hau sama suka bar ta da yaran a k'asa suna daukar tarkacen kayan school dinsu. Fitowar sa kenan daga office a gajiye ya tsaya ya duba wa Baba Alhaji madarar sa da yake sha Ensure, kullum sai ya manta ya koma gida yau dai yace bari ya shiga kawai ya huta dan kwana biyu be sha ba, suit ce a jikinsa ya cire ta saman, kafarsa sanye cikin bakin takalmi sau ciki, sai siririn glass fari da ya dora akan kyakyyawar fuskar sa, tun da ya doshi kofar shiga supermarket din securities din wajen suke gaishe shi, amsawa yake a sake ba tare da takure kansa ba. Kansa tsaye ya wuce wajen da ya saba dauka, ya dauki iya adadin da yasan Baban zai kwana biyu yana sha be sake nema ba. Wayar sa ce tayi kara, ya zaro ta yana dagawa, yana tafiya yana amsa wayar daidai lokacin da Asma'u ta biyo Abeed da yake ta gudun sa tsakanin wajen, be ganta ba, ita ma kuma bata lura dashi ba, sai ji yayi ya bigi mutum, da sauri ya furta "Subhallah." Saura kadan ta kai kasa Allah ya kiyaye, cike da kulawa yake tambayar ta "Baki ji ciwo ko wani abu ba? Sannu I'm very sorry ban ganki ba, fault dina ne ina waya ban duba ba sosai." Kallon sa ta danyi, yadda yake faman bata hakura kamar shi kadai ne yayi laifin, girgiza masa kanta tayi a hankali tace "Ba komai, kayi hakuri kai ma." "Are you sure you are okay?" Da kai ta amsa masa, "Masha Allah." Yace ya cigaba da tsayawa a wajen maimakon ya wuce, kunya taji, tana son barin wajen amma kuma ya tsaya yaki tafiya, kamar wanda aka dasa a wajen haka ya tsaya shi be ce komai ba, be kuma tafi ba " Sai anjima." Tayi karfin halin ce masa tana jan hannun Abeed din, bata ji me yace ba, dan taga kamar he's lost in his thoughts, tayi gaba abinta ba tare da ta sake waiwayo wa ba, sai dai kamshin turaren sa da ya cika baki daya wajen ya cigaba da biyo ta har saman wajen su Ya hadiza. Payment Abban su Abeed ya tsaya yi yace su je mota, suka bar shi a ciki suka je mota suka shiga, ya gama payment din kenan ya fito ana saka masa kayan a baya yaji an masa sallama, ya juyo yana amsawa sannan ya bashi hannu suka gaisa " Sunana Abdallah." " Sannu Abdallah, ya gida ya aiki?" "Alhamdulillah wallahi, dama naga wata ne bansan ko matar aure bace, ta shiga motar nan tana sanye da abaya "Ash ko? Ba matar aure bace, sister din matatace." "Owk Masha Allah, dan Allah idan babu damuwa inaso ka bani dama na ganta, ba yanzu ba cox yanzu dare yayi kar na tsaida ku, may be kuma sai ka fara neman permission from her Dad, kamar yadda yake, I can wait." " Ba damuwa in sha Allah, lets exchange number zan kiraka duk yadda ake ciki." " Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi." " Amin." Yace ya bashi number sa shima ya bashi nasa, yayi gaba zuwa wajen motar sa Abban su Abeed din na kallon sa har ya fita daga cikin harabar wajen, dadi ne ya kamashi, dan idan Allah ya amsa addu'ar su toh tabbas Asma'u ta yi miji, miji irin na nuna sa'a, ABDALLAH IBRAHIM K'AREFA. Duk abinda ya faru Adam na makale yana kallon su, duk da be ga fuskar mutumin ba, be kuma ji me suka tattauna ba, amma sai yaji sam hankali sa be nutsu ba. *RM*     *21* ***Shigowa motar yayi fuskar sa na bayyana yanayin da yake ciki, Ya hadiza ta dan kalle shi zatayi magana ya rigata "In Sha Allah Asma'u tayi miji." Kasa k'asa yayi maganar saboda haka Asma'un dake baya bata ji ba, ga yaran dake faman mata surutu, fuskar Ya Hadizan ce ta fad'ad'a zuwa tsantsar farin ciki tace "Dan Allah? Waye?" "Kina jin wani family K'AREFA?" "Sosai." Ta fad'a cike da zakuwa "Toh baban dan gidan ne, mallakin K'AREFA MOTORS, shi kika ga muna magana, kuma maganar akan Asma'un ce, very responsible guy ni na sanshi amma shi be sanni ba, nasan har cikin gidan su saboda wani aiki da ya hada office dinmu da Mahaifin sa, mutanen kirki ne wallahi sosai, sai kin ga yadda yazo min, kai Alhamdulillah." "Alhamdulillah!" Ya Hadiza ta furta tana waigawa baya, ta kalli Asma'un dake kokarin budewa Abeed chocolate, tayi murmushi tana jin zakuwar kiran umma ta fesa mata daddadan labari, ta tabbata Allah ne ya dubi Asma'un yayi mata chanji mafi alkhairi, ko dan hakurin da tayi. Sama sama suka karasa abinda ya fito dasu sukayi takeaway suka yi gida, shi kansa Abban su Abeed din ya matsu ya sanar da Abba maganar, ita kuma Ya Hadiza Umma, suna shiga gidan kuwa kowa yayi dakin sa domin kiran wayar. Umma na tare da Abba a lokacin suna maganar Asma'un, sai ga kira a kusan lokaci daya, umma ce ta fara dagawa sai shima Abba ya daga cike da girmamawa suka gaisa da sirikin nasa sannan ya sanar dashi abinda ya faru da uzinin da Abdallan yake nema, bayan ya gama Abban yace "Ai kai ma uban Asma'u ne Ali, na baka wuka da nama kayi duk abinda ya dace, abu daya na sani, shine Asma'u ce take da damar zabarwa kanta abokin rayuwa a yanzu, idan har ta amince dashi kuma ka gamsu dashi, shikenan babu damuwa. " "Nagode Abba Allah ya kara girma. " " Amin ya Allah, a gaida yaran da matar gidan. " " Zasuji. " Jinjina kai Abba ya dinga yi har Umman ta gama amsa wayar Ya Hadizan cikin farin ciki, tana ajiye wayar yace. "Uwata ce ko?" "Eh, akan maganar Asma'u ne." "Alin ya sanar dani komai, Allah ya wuce mana gaba yayi mana zabin alkhairi." "Amin ya Allah." Ta amsa tana jero addu'ar dacewa a ranta. ***Asma'u na daki Ya Hadiza ta biyo ta da abubuwan da aka siyo nata, a gefen gadon ta ajiye ta tsaya ta idar da sallar isha, ta juyo tana duban ta "Ga kayanki nan, ga abincin nan a ciki, kici akwai labari me dadi." "Ai ba zan iya cin abincin ba idan ban ji labarin ba.". Tace tana mikewa daga sallayar "Ai na zaci shafa'i da wutri zakiyi." "Idan nazo kwanciya zanyi, dan Allah fad'a min, labarin." "Kema fa wasa wasa akwai son jin gulma, toh ai labarin akanki ne." "Ni kuma?" "Eh wallahi,Allah ya amshi addu'ar mu, kin samo gallelen miji in Sha Allah, wannan da suke magana daxu da Abban su, kin ganshi?" Girgiza kai tayi a sanyaye "Toh dai zaki ganshi ai, dan zaizo gobe." "Waje na?" "Emana." "Wallahi ni dai tsoro nake ji. " " Babu abinda zai faru sai alkhairi, kiyi istikhara kafin ki kwanta, mu nemi zabin Allah, Abban su dai ya gamsu dashi dari bisa dari kinsan kuma halin shi. " Shiru tayi jikinta duk yayi sanyi, bata da tunanin hakan nan kusa, tana so ta huta sosai dan ita gaba daya auren ya fita daga kanta, duk da akwai mazaje na kirki na gari amma an ce ruwan da ya dake ka shine ruwa, amma duk da haka zata nemi zabin Allah, ta barwa Allah komai.    Chachakalar abincin kawai tayi dan duk sai taji bata ma da appetite, ta kwanta bayan tayi nafilar tayi lamo akan gado, bata jin bacci ko na digo, rayuwar ta ce ta shiga dawowa mata tiryan tiryan, tun sanda ta bud'e idon ta, ta ganta a gidan su kawo zuwa lokacin da ta mallaki hankalin kanta zuwa rayuwar gidan Adam da bayan ta, ta tsinci abubuwa da yawa cike da rayuwar tare da kalubale da suke tattare da rayuwar baki daya. Ta jima tana sake-sake kafin barci barowa yayi awon gaba da ita. ***Tunda Adam ya koma gida ya kasa zaune ya kasa tsaye, abin duniya yayi masa mugun yawa gashi ya gama saddakarwa da gaske son ta yake, irin soyayyar nan me zafin gaske, irin wadda mutum yake jin zai iya komai akai, sanda ya shiga gidan su sai da Mama ta dube shi ta sake dan ya rame sosai tamkar bashi ba, abinci tasa aka kawo masa amma sam yaji bashi da taste ko kad'an, a tunanin ta ko akan maganar auren sa ne da ta matso sosai, ba zata fasa ba dan haka ma ba zata bashi fuskar da zai zo da wata magana ba, idan ma akan auren ne duk zai sauke idan akayi auren, su Nadeeya ma sun mata mitar sun hakura sun zuba mata ido dan da gaske abin yafi karfin su kuma ba fasawa zatayi ba dan ta kafe. Gidan sa ya koma ya tarar an kwashe kusan komai na gidan da yake a mazaunin na Asma'un, kamar ya ari hauka haka ya koma gidan su ya samu Maman yake tambayar ta kayan gidan "Na aikawa Asma'u kayanta tunda da sunanta akayi su, ita kuma fiddausi sai tazo da nata." "Innalillah, amma Mah da baki aika ba, ina so wallahi." "Me zakayi dasu? Kai da za'a kawo maka sababbi." Idan ma yace zai tsaya mata bayani ba zata yarda ba, juyawa kawai ya koma ya shige dakin sa ya rufo, ya dauko album din da Nadeeya tasa akayi musu na bikin ya bud'e ya hau kallo tamkar gaula, idan yazo kan nata sai ya dau dogon lokaci yana kallo yana murmushin, sai yanzu ya kara tabbatarwa da kansa ya kamu sosai, kamu me wahalar gaske. Be san ta ina zai fara gyara kuskuren da yayi ba, ya riga ya bata komai wanda gyaruwar sa zatayi matukar wahala. Da hoton ta ya kwanta rungume a kirjinsa, yayi mafarkin tana zaune a dinning tana zuba masa daddadan abincinta ya sauko yazo ya zauna, ta shiga bashi a baki tana masa kallon da yake sake narkar dashi, juyi yayi be san yazo karshen gado ba, sai ji yayi ya fado tim, ya mike a zubure yana zazzaro ido, ya sake daukar hoton ya koma tsakiyar gadon ya kwanta, mafarkin da yayi na dawo masa, tsaki yaja da ya gane da gaske mafarki yake, ya dinga juye-juye kafin ya samu barcin ya sake dauke shi.     ***Tun da suka tashi da safe, suka hau shirye shiryen tarbar bako, ya sanar da Abban su Abeed zaizo da yamma wajen hudu da rabi bayan sallar la'asar, seat room din da yake saukar baki ya gyara da kansa har da daga kujeru da su sharar yana ko ina yayi fes, snacks Ya Hadiza ta saka Asma'u tayi me dadi, sannan ta sakata gyara jikinta tayi wanka wajen uku da rabi, tasan ba gwanar kwalliya bace itama kuma tafi son mace ta fito a natural dinta shiyasa bata ce tayi ba, zuwa hudu komai ya zama ready, sukayi sallar la'asar wajen hudu da rabin kuwa sai gashi yazo, da Abban su Abeed suke waya har ya karaso kofar gidan, ya fito ya taro shi zuwa ciki, ya kaishi har falon bayan ya kunna gen kasancewar babu wuta a garin. Ciki ya shiga bayan sun gaisa yace wa Ya Hadiza ta turo Asma'u, tare suka dawo ta riko hannun ta, yana tsaye ya tsokaneta sukayi dariya, a kunyace ta shiga seat room din bakin da dauke da sallama tana kokarin daidaita kanta da yanayin faduwar gaban da take ciki, ga wani irin bugawa da kirjin ta yake yi zuciyar ta tamkar zata hudo ta fito waje. A bayyane ya amsa sallamar tata muryar sa tar idon sa akanta sai dai ita kasa take kallo har ta samu waje ta zauna sannan ta gaishe shi. "Ba zan amsa ba, haka ake gaisuwa babu kallon mutum?" Dagowa tayi kad'an, ta kalle shi sai mamaki ya kamata ganin na jiyan nan ne a supermarket din nan "Yauwa ko kefa, kina lafiya!?" "Lafiya lou." "Masha Allah, ya gida ya komai." "Alhamdulillah." Daga nan sai sukayi shiru, shi be san yadda ake magana da mace ba gashi dama ba gwanin magana ba, balle ita kuma, yaso MD ya rakoshi amma yaki yace sai dai yaje da kansa idan yaga kamun ludayinsa sai ya rakoshi gaba, baran baran sukayi akan haka, still yaki biyoshi dan har mota ya rakoshi yana tsokanar sa yayi masa banza yayi tahowar sa bayan ya karfafi kansa akan zai iya, sai gashi ya rasa duk kalaman bakin nasa da yayi ta tsarawa a cikin kansa tun jiya, amma ya nemi guda daya sam ya rasa. Kiransa akayi, hakan ya taimaka wajen rage shirun da wajen yayi "Kana da matsala wallahi."  Yace "Ban sani ba, idan abinda ka kira ka tambaya kenan, toh zan kashe." "A ah tsaya, Mr love karka kashe dan Allah, kira nayi dama na tuna maka da ka bar note din da ka rubuta na abinda zaka ce idan kazo, bani address na kawo maka yanzu." MD yayi saurin tsaida shi yana danne dariyar sa. " I have no time to waste, sai anjima malam! " Ya kashe wayar yana murmushi, idon su ne ya hadu lokaci daya, tayi saurin janye nata gabanta na sake bugawa da karfi, shi kansa sai da yaji wani abu me kaifin gaske, ya sake murmusawa yana taba zoben azurfar dake hannun sa. Shigo da tray akayi, Abeeda ce ta ajiye ta gaishe shi ya amsa a sake sannan ta fita, ya jawo tray din ya zuba ruwan yasha hade da Bismillah tana jin shi, sai taji ya burgeta hakan da yayi, ya koma ya zauna yana tattaro dukkan nutsuwar sa "Husna." Ya kirata da sunan da ba wanda ya taba kiran ta dashi idan ta cire Abba da shi ma yawanci Asma'ul Husna yake cewa idan yaso hakan, muryar sa me taushi ta ratsa dukkan sassan jikinta, tayi tsam a zaune wani yanayi na ratsa ta, sake kiranta yayi "Husnaaa, ga Abdallah yazo da kokon barar sa, yana fatan zai samu karbuwa, ba da wasa nazo ba, da gaske nake so mu fahimci juna." " Uhum. " " Pleaseee karki ce a ah, ko kice na miki tsufa, yaro ne daidai dake wallahi. " Sautin dariyar ta yaji, yayi murmushi yana jin kamar ya samu lagon ta tunda har tayi masa dariya " Kin yarda? Zaki bawa wannan bawan Allahn dama? " Shiru tayi dan bata san amsar ba, eh zatace ko a'ah, yasan ta taba aure ko kuwa? Zai karbe ta a haka ko kuwa? Wannan tambayoyin su suka dinga mata yawo aka tun daren jiya, sai da kuma aka zo gabar sannan taji da gaske Adam ya cuce ta, ko ta ina kuwa. "Baki ce komai ba?" "Bansan me zan ce ba." "Kice eh, please kice eh kinji? Ki bani dama kawai, ba zaki danasanin hakan ba." "Na taba aure." Maganar ta fito ba tare da ta shirya ba, bata ga yanayin sa ba, bata kuma san tasirin da maganar tayi masa ba, kafin ya bata amsa aka danno kai ta hanyar banko kofar da take ta bangaren harabar gidan, Adam ne a tsaye tamkar mahaukacin zaki, yana huci fuskarsa a hade " Dama tun ranar da na ganka naji bana son ka, ashe ashe abinda zai faru kenan, Malam wanann din matata ce, ka kwashi tsummokaran kafafunka kafin na saka a babballamaka su ka bar nan wallahi. " Murmushi kawai Abdallah yake daga zaunen da yake ko gezau be yi ba, duk hargagin da Adam din yake be saka ya motsa ba, hakan ya sake hassala Adam din, ya kalli Asma'un ya daka mata tsawa " Dallah tashi ki shiga ciki. " Wani banzan kallo tayi masa, kallon da ya saka shi shiga taitayinsa, ta kuma juya wajen ABDALLAH da yake hakimce yana kallon komai hankalin sa a kwance tace "Na amince Allah ya yi mana zabin alkhairi." "Amin Ya Allah my soon to be wife, nagode sosai da wannan damar, in Sha Allah ba zaki nadama." Kamar basu san dashi a wajen ba, haka suka yi, ba kamar Abdallah da ya nuna kamar Adam din be dame shi ba, nan kuwa haushin sa ne sarke a  ransa, be niyyar tafiya ba a lokacin amma ba zai iya cigaba da zama inuwa daya da Adam din ba, tashi tayi zata raka shi, ya dakatar da ita dan baya so ya tafi ya barta da wannan mahaukacin, rakata yayi har kofar da zata shiga cikin gidan yana take mata baya, cikin wani yanayi kamar na me tsaron lafiyar ta, sai da ta shiga ciki sannan ya juyo, ya fice daga dakin yana kokarin hana kansa jin kalaman da ke fitowa daga bakin Adam din, a daidai lokacin Abban su Abeed ya dawo daga bayan da ya zagaya, ya hango motar Adam din shiyasa yake ta sauri be san already ya riga ma ya shiga gidan ba. "Har zaka tafi?" Yace masa yana waige waige ko zai ga Adam din "Eh wallahi, amma zan dawo, kamar kayi bako ma,." "Bako? Yana ina? " " Yana ciki. " " Adam! Kayi hakuri dan Allah, babu wanda ya san da zuwan sa, kamar yadda na sanar da kai ne, babu wata alaka yanzu tsakanin su illa ta yan uwantaka, ba dan wannan ba ma na tabbata da yanzu shari'a ake, dan ba zamu kyale ba, dalilin da ya saka na sanar maka kenan, saboda ba'a boye maganar aure a nema. " " Babu komai, da gaske nazo zan auri Asma'u ko da aure dari tayi ta fito, kuma shi Adam din zan yi maganin abun, so karka damu. " *RM*     *22* ***Ciki ya shiga bayan Abdallan ya tafi, ya tarar da Adam din yana kai komo a compound din gidan, yana ganin shi yayo wajen shi da sauri "Adam kana cikin nutsuwar ka kuwa?" Ya fad'a ganin yadda kirjin sa je bugawa da karfi, dafa shi yayi jin You know what I don't remember the number Now kamar zai zube a wajen, ya taro shi yana furta "Subhallah;" Cikin seat room din ya kai shi,ya taimaka masa ya zauna ya zuba masa ruwa ya mika masa, karba yayi ya kafa kai, be ajiye ba sai da ya shanye tas, ya mika masa cup din ya mike, yana kiran sa be amsa ba, ya fice da sauri ya fad'a motar sa, ya tada ita a guje ya bar layin!      Unguwar ya nufa yana jin duk abinda za'a yi sai dai ayi, amma sai ya je, yana isa ya tarar da gate din a rufe yan sandan suna zaune daga gefe, horn ya danne yana daga cikin motar suka kallo shi, tasawo sukayi, ya sauke glass din yana zura kansa "Wajen wa kazo?" Kafin ya amsa dayan yace "Baka gane shi bane? Gayen nan ne da yayi mana rashin kunya ranar har Oga Abdallah yace a kaishi gida." "Oh na tuna, kai me ya kawo ka nan?" " Wajen uban gidan naku nazo,idan har ya cika shi din jarumi ne, ya fito ya fuskance ni, ni kadai ba tare da ku ba." " Gayen nan fa kamar yana da matsalar brain, ku wuce muga iya kar haukan sa." Barin wajen sukayi suka koma suka zauna, ya dinga horn yana kumfan baki, sukayi masa banza hakan ya sake kona masa rai, ya juya ya bar layin. Allah ne kawai ya kaishi gida lafiya dan mahaukacin gudu ya dinga yi, ko parking din be daidaita ba, ya shiga gidan su, Mama na zaune taga ya fado "Lafiya Adam? Na shiga uku." Zube mata yayi cikin wani irin yanayi yace "Mah Asma'u." "Me ya same ta?" "Wani, tare da wani na ganta, Mah zan mutu, wallahi zuciya ta ba zata iya dauka ba." "Me zan gani? Macen kake wa wannan abun, macen ma Asma'u da kace baka son ta?" "Karya nake wallahi, I'm a very big liar, ban san me nake aikatawa ba a lokacin. " " Ka manta babu aure a tsakanin ku toh? " " Nayi laifi dan Allah mAh karki bari a hukuntani da shirmen da na aikata, a nemi wasu malaman ai ance saki uku a kalma daya, daya ne." " Saboda irin ku ai masu yin saki ukun na ganganci daga baya ku dawo kuce ba haka ba, aka hana, ka riga ka saki Asma'u saki uku cif ko a kalma daya ko a kalma daban daban ta saku." Da sauri ya hau rarrafawa zuwa wajen Nadeeya da ta fito daga daki ta bashi amsar nan, ya kama kafarta cikin tashin hankali yace "Dan Allah sister karki ce haka, sabanin malamai, dan Allah karki haramta min Asma'u wallahi ba zan iya rayuwa babu ita ba." "Tirkashi, wannan shine abun da na guje maka Adam." Hajiya Mama tace tausayin dan nata na kama ta, janye kafarta Nadeeya tayi tana zama a kujera tace "Bama tare a wannan lokacin boy, the earlier you realize the better for you, kayi wasa da damar ka Asma'u tayi maka nisa." "Na shiga uku!" Yace yana dafe kansa, kallon sa mama take ganin kamar ba adam dinta ba, sai a yanzu taga muguwar ramar da yayi, yayi baki ya wani shiririce, babu tsaftar nan da gayun nan kwata-kwata, girgiza kai kawai ta dinga yi dan al'amarin ya sha kanta yafi karfin ta, bata san ta ina zata bullowa al'amarin ba, shi kadai ya dinga mirgina kansa yana rik'e shi kamar wanda ya samu matsala, suka taso kansa suna tambayar sa me yake ji amma ya kasa magana, wannan wacce iriyar soyayya ce haka ta kama Adam, lallai Allah na azzalumin Sarki bane, duk abinda kayi Yana kallon ka, dole akwai ranar sakayya ko a kusa ko a gaba. Da k'yar Maman ta samu ta lallaba shi ya kwanta a saman kujerar falon, Nadeeya ta samo allurar bacci tayi masa ganin yana ta surutai, kafin allurar ta dauke shi sai da yayi ta nanata sunan Asma'u, har idon sa ya rufe ruf. Tagumi Hajiya Mama ta zabga a gabansa tana kallon sa, ji tayi hawaye na sakkowa a saman fuskarta, ta saka hannu ta share tana komawa dayar kujerar ta zauna abun duniya ya taru yayi mata yawa.     Shirye shiryen biki Fido take yi ita kadai bata damu da Adam din yana so ko baya so ba, ta riga tayi wa kanta alkawarin auren sa ko yana so ko baya so kuwa, duk abun da ya kamata tayi Faiza ce ke tsaya mata, ita ke sakata a hanyar komai, dama da kudin ta, kashe su kawai take tana shiryawa kanta da auren da zatayi, wanda da yawa kawayenta suke mata bakin ciki akai, ita dai ko a jikin ta, burin ta kawai ta shiga gidan Adam din, ta kuma juyashi a tafin hannun ta tamkar yadda ya dade yana gara rayuwar ta tamkar yar gare-gare.  Dawowar su kenan daga kasuwa tare da Faiza aka kirata a waya, kafin ta ciro wayar ta katse, ta duba taga Hajiya Mama ce, tayi dariya tana nunawa Faiza "Mutuniyar ki ce." "Sirikarki wai?" "Ita." "Auw wai har kiranki take kenan." "Wannan ne na biyu, ta matsu watan nan ya kare ayi bikin nan." "Lallai Malam Ya'u yasan ta kan tsiya , ya bi da ita wallahi. " " Bari na kira naji me ya faru kuma? " " Owk kira muji." Kira tayi Nadeeya ta daga, lokacin Maman ma kan Adam tana tofa masa addu'a, dan duk farkawa tun da allurar ta soma sakin sa yake surutai, da sumbatu, gashi da kunya ta kira Abban su Asma'u ta fad'a masa, bata san me kuma zatayi ba, gaba daya komai ya tsayaa mata chak, " Bata kusa zata kira idan ta dawo. " Nadeeya tace ta katse kiran tana jan siririn tsaki, " Kinga fa da gaske Adam yake fa, yanzu ya zamuyi? " " Ya zamuyi Mama, ba zai yiwu ba wallahi. " " Kunyar kiran karami nake, bansan me zan gaya masa ba. " " Karma ki kirashi Allah, ai da kunya. " " Shikenan sai na bar Adam a haka, tun yanzu ji yadda ya fara komawa inaga nan gaba. " "Toh ai duk laifin sa ne ma, shi mutum daraja ce dashi, sanda yake wulakanta ta, be tuna irin wannan ranar ba. " " Yanzu Nadeeya wannan maganganun naki me zasu sauya? " Bayan aikin gama ya gama ai sai ki goyi bayan shi ko sau daya ne, ba wai kiyi ta nuna kamar ma dadi kikeji da hakan ta faru ba, duk tsiya Adam jinin ki ne." "Toh Mama na yi shiru." "Yafi dai, bani wayar na kira Karami." "Mama?" "Bani nace, Kanina na ne ba naki ba." Mika mata tayi "Kira min shi ki bani, ai naka sai naka, ba zan iya jurar ganin Adam a wannan halin ba, hannun ka baya rubewa ka yanke ka yar, ballantana nasan karami yana kauna ta da duk abinda nake so." "Gashi an daga." Ta mika mata tana matsawa gefe "Lafiya lou, ya matar gidan?" "Alhamdulillah, Adam ne bashi da lafiya wallahi." Sai ta fashe da kuka, "Dan girman ALLAH ka taimake ni kar na rasa shi, kayi hakuri ka dawo masa da matar sa. " " Yaya? " Ya katse ta da sauri cikin tsananin mamaki " Dan Allah ka taimaka min, wallahi yayi nadama sosai ba zai sake ba. " "Yaya kin manta babu aure tsakanin Adam da Asma'u ne? " Cikin kuka tace " Aje wajen malamai, akwai wadanda suke ganin tunda a kalma daya ne, za'a iya komawa. " " Tirkashi! " Ya ma rasa bakin magana, magiya ta cigaba da yi masa tana kuka wiwi " Ka taimaka min dan Allah, ka dubi girman zumunci dan Allah. " " Zanzo gidan Yaya, wannan maganar ba ta waya ba. " Be jira ta sake magana ba, ya kashe wayar yana murmushi " Yaya Asabe ce. " Yace wa Umar da yake suna tare " Wai so take Asma'u ta koma? " "Eh wai. " " Allah ya rufa asiri. " " Toh Amin Babana. " Har suka zo gida maganar na yawo akan Abba, ya bawa Umma labari tayi dariya kawai, dan bata so tace wani abu ne kawai saboda girman da Hajiya Maman take dashi a wajen Abba, amma da ba haka ba, da anji maganganu manya manya. Missed calls wajen biyar tayi masa, ya daga daga karshe ta cigaba da masa magiyar dan Allah ya daure yazo, yace zaizo zuwa da safe, ba dan taso ba tace toh, amma gani take safiyar tayi mata mugun nisa. _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* *RM*      23 ***Hannun sa rik'e a cikin na Baba Alhaji suka karaso wajen motar, ya bud'e masa ya shiga yana jaddada masa abinda suka tattauna, murmushi ne kwance a fuskar sa har zuwa lokacin da motar ta fita daga cikin gidan, juyowa yayi yana kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa, ya burza shi yana taba airdrop din dake sakale da kunnen sa,  kiran ta yake so yayi tun dazu, yaji zazzakar muryar ta me sanyi da taushi, sai dai Baba Alhaji be bashi damar hakan ba, dan be bar shi ba tun bayan da ya dawo sai da ya tabbatar da ya sake jaddada masa abubuwan da yake so a aiwatar kafin dawowar sa. Tafiya yake a nutse irin ta jaruman maza masu cike da nutsuwa da haiba, ta daga kiran nasa hade da sallama, bata san shi bane dan be karbi number a wajen ta ba, sai bayan ya tafi ne ya tuna ya kira Abban su Abeed ya tura masa, a time din yaso ya kirata amma kuma shi mutum ne me bin komai a kaida da tsari, baya so ya takura ta musamman da rabuwar su kenan be san ko ta shiga wani uzurin ba, sai kuma yazo ya samu Baba Alhaji ya rike shi gam be barshi ba sai da ya tafi, zai je Abuja yayi kwana biyu akan wasu estates din sa guda biyu da yake son saidawa.   Sallamar ya amsa cikin bawa kowanne harafi hakkin sa, murmushin tayi me sauti, ta gaida shi ya amsa yana karasawa wata yar kujera ta zauna, sannan ya tambaye ta gida da kowa da kowa, ta amsa masa muryar ta tar babu nuku nuku, kwarin guiwar yaji ya samu sosai, ya gyara zaman sa ya shiga yi mata yan tambayoyi a game da abubuwan da yake son sani a tattare da ita, yadda take bashi amsar yafi masa komai, dan a cikin amsar ya fuskanci nutsuwar ta, wadda ya hanga tun jiya a supermarket din, shagala sosai yayi da hirar, dan sosai yake jin dadin hirar har be san an dau lokaci haka ba. MD ne ya dawo yake ta neman sa ya rasa shi, yaje part dinsa yaje masallaci amma duk baya nan, kuma a gate baa ce masa ya fita ba, motocin sa duk suna nan har wadda ya hau yaje zancen dazu, ya matsu su hadu ya tsokane shi, tunawa da yayi da hanyar garden din dake bayan gidan yayi, ya nufi chan da dan saurin sa yana ayyana samun sa a wajen. Ta baya ya hango shi, shi kadai amma da dukkan alamu waya yake, da sanda ya karaso wajen ya labe daga baya yana jin wayar da yake muryar sa tar kamar bashi ba, sai yaji kamar ma har wani makale muryar yayi, ya ji yana cewa pleaseeee, hadda marairace murya, rik'e bakin sa yayi da yake neman tona masa asiri yayi, ya zaro wayar sa ya danna record, ya kara matsawa kad'an daidai lokacin da yayi mata sallama, bayan ta kashe ya furta "I love you my asmy, love at first sight!" Sai ya jingina da kujerar yana lumshe ido, ihun dariyar MD din ta sakashi juyowa da sauri, ya dinga tafa hannu yana zuwa wajen nasa, mur yasha sosai yana mikewa "Dan sa ido, menene na biyo ni nan din?" "Ai kai ma kasan wallahi dole na saka maka ido, Abuya ne yau yake waya da mace, who's this lucky girl, gaskiya yau za'a yi ruwa da soyayyen kifi, wai." "Allah MD bana son abinda kake min, me ka maida ni ne!? " Agogo mana, ko nace dutse dan ni wallahi Allah na dauka ma baka da lafiya ne, ashe ashe kana ankare. " "Mtss, kana da matsala wallahi. " Ya juya zai barshi a wajen "I love you my Asmy... " MD ya kwaikwaye shi yana buga kafa, juyowa yayi a kunyace zai kai masa duka ya goce " Haba ango Ma'u, wuce nan na tsaya, kuma wallahi yau zan fasa maganar nan a babban falo, kowa sai yaji musamman ma Mum, bari kaga." " Tsaya Dan Allah, kar muyi haka da kai, dan Allah karka min haka. " Kin tsayawa yayi, ya biyo shi da sauri yana kwala masa kira, sai da suka zo Balcony din da zai shigar dasu main part din sannan ya tsaya, ya karaso da sassarfa " Zan fasa fad'a amma under one condition. " " Menene? " " Sabuwar motar da kayi order inason daya, I ll pay half ka cika min ragowar. " " Kai! " " Shikenan bari naje na siyar da jaridar, bari kaga. " " Na yarda." " Yes! Thank you big bro, Allah ya kara arziki me albarka, ya raba ka da iyayenmu lafiya ya baka My Asmy dinka. " Duka ya kai masa ya same shi kuwa, dariya suka saka a tare, ya rike masa kunne ya ja " Baka ji sam, ka raina ni. " " Abuya! " Ya fad'a da sigar tsokana "Ka bata min suna tun daga yarintar, gashi nan hatta Baba ma haka yake fad'a." "Amma kasan me? Ina son sunan sosai, ina jin dadin duk sanda ka kirani da sunan, yana tuna min old memories din mu na yarinta." "Abdallah-Abuya." Suka sake yin dariya, ya rik'e masa hannu suka fasa shiga ciki suka juya zuwa nasu bangaren suna cigaba da tattaunawa kamar kowanne lokaci. Da gudu Ihsan ta koma ciki tana kwalawa Mami kira, tare suka fito da Mum ta sakasu a tsakiya ta ratayo kafadar su "Albishirin ku?" "Goro." Suka ce a tare "Ya Abuya yayi budurwa." "Da gaske?" "Wallahi, yanzu naji suna maganar da Ya Mudan, yana tsokanar sa." "Wannan maganar danki ce babu ni a ciki." Mum tace tana zama, Mami kuma ta cigaba da tambayar Ihsan din abinda taji, ta kwashe komai ta fad'a, murna ta hau yi, tace ta dauko mata Jakarta a daki, ta kawo ta ciro ATM din ta, "Goron albishir, ki je ki siya abayar da kika ce min kina so." Ihu ta saka ta dane ta, "Thank you thank Mami na, you are the best, nagode Allah ya kara girma." "Amin Mamana." "Kinji abun farin cikin da ya sameni ko?" Tace wa Mum bayan Ihsan din ta fita "Dan naki ne sha'anin sa sai shi, Allah sa da gaske ne." "In Sha Allah ma gaske ne, bari nazo na fara shirin shan biki, grand biki da baa taba irin sa ba." "Allah yasa kar ya baki kunya." "Bama zai bayar ba." " Shikenan zamu gani." Tace cikin nuna halin ko in kula amma a kasan ranta wani dadi ne ya lullube ta, Abdallan ta ya samu matar aure. _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* *RM*     *24* *** Daren ranar Hajiya Mama bata runtsa ba, tana kan Adam da ya farka ya kuma nemi barcin ya rasa, sai magiya yake mata akan ta taimaka masa, tayi wa Abba magana. Ta rasa abinda yake mata dadi Abban ma da yace zai zo be zo din ba, tasan ba abu bane me sauki a wajen sa ba, musamman shi da aka batawa, amma ya zatayi? Bata da kamar sa kaf duniyar nan, dole dai shine sai sake rufa mata asiri a san abinda za'a yi kafin Adam din ya karasa zaucewa dan taga abun ba na wasa bane. Da safe ya tashi kamar bashi ba, kamar kazar da aka tsoma a cikin ruwan zafi, yayi laushi sosai, sallah Mama ta sakashi ya rama wadda ya rasa ya zauna aka kawo masa tea yasha tace yaje yayi wanka, maimakon ya tafi gidan sa sai ya nufi dakin sa na cikin gidan ya sake kwanciya yana dasa sabon tunani, ya dade be fito ba har Maman ta biyo sahun sa, ta ganshi kwance kamar ruwa, tashi ta saka shi yayi ya shiga wankan, sannan ta fito ta jawo masa kofar, yana wankan tunanin ganin da yayi wa Asma'u da gayen jiyan nan na bijiro masa, ya dinga huci shi kadai da k'yar ya karasa wankan ya fito ya shirya, ya bar gidan ba tare da Maman ta sani ba, ya nufi gidan Ya Hadiza, be duba karfe nawa ba, ya isa gidan ya fito ya hau kwankwasa gate din, weekend din saboda haka babu wanda ma ya tashi a gidan sai yara da su dama sabon tashin makaranta baya barin su baccin safen nan, Abeeda ce taji ana bugu da dan karfi, ta shiga dakin da Asma'u take ta hau tashin ta "Anty Asma'u ana knocking a gate." "Waye?" "Nima ban sani ba, tun dazu ake yi, su Momy kuma basu tashi ba." "Owk, Ina zuwa. Kar wanda yaje ya bude zanzo." "Owk tam." Tace ta juya ita kuma ta tashi, ta sakko daga gadon ta shiga bayi ta kuskure bakin ta, ta wanko fuskarta, ta fito dama tayi sallah tun asuba, sai kawai ta zura hijab ta fito, biyo ta Abeedan tayi, suka je tace waye.? Jin muryarta, ya saka shi jin wani sanyi a ransa, ya tabbata idan yace shine toh ba zata bud'e ba, sake maimaita waye tayi, yayi kokari sosai wajen saita muryar sa, yace Abbati ne. Ji tayi kamar muryar abbatin kamar kuma ba tashi ba, kai tsaye ta zare lock din ba tare da tunanin komai ba, cike da hanzari ya tamki hannun ta, ta turje idon ta na fitowa waje " Menene haka?" Da sauri Abeeda ta juya ciki tana kwala kiran Mummy, ya sa karfi ya jata zuwa motar tana kwacewa, sai dai karfin su ba daya ba, tura ta yayi ciki ya rufe da key sannan ya zagaya ya bud'e bangaren sa ya shiga ya bar layin.  Daidai lokacin Ya Hadiza da Abban su Abeed suka fito da mugun gudu ya Hadiza ko dankwali babu akanta, amma kafin suzo har ya bar layin, rik'e Abeeda tayi tana fashewa da kuka "Waye ya tafi da ita? Waye?" "Uncle Adam ne." "Na shiga uku, me zan cewa Abba, Adam dama bashi da hankalin ban sani ba?" "Calm down, tunda ma shine ai da sauki, muje ciki ki shirya bari na kira Abba, dole ya dawo da ita tunda mu ai ba mahaukata bane kamar sa, idan yaki sai a saka shari'ah a ciki, tunda be san addini ba."   Hankali a tashe ta koma ciki ta chanja shigarta dan ba ma zata iya wanka ba, tana jin shi suna magana da Abban, a nutse suke maganar da dukkan alamu ba kamar ita da ta rude ba. Wayar Asma'un ta dauko a daki da handbag dinta suka tafi gidan su, suna zuwa suka tarar da Umma hankalin ta  a tashe, ranta yayi masifar baci, shi kansa Abban dan dai namiji ne amma kana kallon fuskar sa zaka ga yanayin sa ya chanja, be kira Hajiya Mama ba, tunda ya fuskanci kamar har yanzu tana goye da bayan dan ta, kuma ma dai baya bukatar wata magana kawai Adam ya dawo masa da yar sa. Dama mijin Ya Hadizan yake jira yana zuwa suka fita a mota tare, sai police station dan shine kawai mafita yanzu a garesu, sai da suka je kofar shigar kuma sai Abban ya kasa sauka daga motar, ya dinga jin kamar hakan tona asirin family din su ne, kamar kuma be kyautawa Yayar sa ba, tunda duk tsiya dai Adam din ma nasa ne, cewa yayi su juya zuwa gidan Hajiya Maman kawai, Abban su Abeed ya jinjina zumunci irin na Abban wanda baa samun sa a wannan zamanin sai an tona. Shi kadai ya fita ya shiga gidan yace mijn ya Hadizan ya jirashi, ya shiga kansa tsaye ya same ta a zaune a falo ta rafka tagumi "Sannu da zuwa." Tace masa tana mikewa, maimakon ya zauna sai ya tsaya daga kofar shigowar "Adam yaje har gidan Ali ya dauki Asma'u, bansan me yake nufi ba, ban kuma san ina zai kaita ba, amma inaso ya dawo min da 'yata kafin nan da awa daya, idan ba haka ba zan nemi hukuma ta shigo ciki." "Na shiga uku, Adam din? Chan ya tafi dama? Wannan wanne irin abu ne dan Allah, na shiga uku." Ta hau tafa hannu tana salallami, sallama Abba yayi mata ya fita yana jin duk babu dadi yadda abubuwan suka kasance. Wayar ta, ta jawo da sauri ta shiga kiran layin Adam din amma be daga ba, ta dinga jera masa kiran ba kakkautawa. ***Gudu ya dinga shararawa har sai da ya kusa kure titin, be san ina zashi ba,be shiryawa hakan ba, a lokacin da ya ganta kawai tunanin yazo masa. Duk magiya da rokon da take masa yayi kamar be ji ba, shi dai tunda yanzu suna tare burin sa kawai ya samu in da zasu, ya samu wanda zai tabbatar masa akwai aure har yanzu a tsakanin su, sannan ya umarce shi akan ya daura musu aure a take a wajen! Jin kiran da ake masa babu kakkautawa ya saka shi daukar wayar ya kashe ta ma baki daya, ya juya akalar motar zuwa hanyar barin garin baki daya. ***Hankalin Fido yaki kwanciya akan kiran da Hajiyar tayi mata kuma ta kira bata daga ba kuma bata biyo kiran ba, a daren da zata tafi gidan Faiza ta hanata tace ta bari dai da safe, aikuwa wajen goma na safe taga shiryawa, Faizan ko tashi batayi ba, ta dauki hanyar gidan bayan ta tsaya tayi wa Hajiyan siyayyar kayan fruits.   Yanayin Hajiya Mama ya chanja lokacin da ta ganta ta shigo, ta kalli hannun ta kafin ta aro jarumtar yi mata maraba, zama tayi tana gaida hajiyan "Dama naga kira ne jiya, shine nazo naji ko lafiya?" "Eh wallahi, lafiya lou bansan na kira ba ma wallahi, jiyan nan ina neman wata number ashe ke nake kira." "Ayya." Tace tana karewa falon kallo, ta jima bata ga Adam din ba, bata kuma da bukatar ganin sa har sai ranar da ta shigo gidan sa, a yanzu tasan zai iya cewa zai nada mata duka, shiyasa take mugun takatsantsan dashi. "Na tura wa chan kannen Baban Adam din address din da kika bani, nasan yanzu sun je ko zasu je ma, ban dai ji daga gare su ba, yau nake shirin ji." "Allah sarki." Tace tana sinne kai, dadi na cikata saura kiris burin ta ya cika, dan jim ta zauna ganin kamar Hajiyar bata cikin nutsuwar ta, ya sakata mikewa "Zan koma Maama,dama zuwa nayi na duba ko lafiya." "Lafiya lou, nagode sosai ki gaida gida." "Yauwa." Tana fita ta zauna dabas, zafi goma da ishirin, kira ne ya shigo wayarta, tayi saurin wawurar wayar a tunanin ta Adam ne, sai taga wani kawun su Adam din ne, kawu murtala. Dagawa tayi "Barka da safiya Asabe." "Barka dai kawu, ya mutanen gida." "Lafiya lou, dama batun Adamu ne, akan yarinyar da aka ce muje mu nema masa aure, toh Alhamdulillah, an je kuma mun samu iyayenta da maganar sun yi murna da farin ciki, sun kuma amince sun bashi ita dan a take ma akayi komai muka bada sadaki aka daura aure..." "Na'am?" "An daura aure, sai bayan an daura ne ma wani baffanta yake shaida mana ai rabon su da ita yau shekara guda kenan tun wani zuwa da tayi ta gaishe su, tunda har ta turo a nemi auren ta toh su dama haka suke so, shiyasa ma baa bata lokaci ba." "Tirkashi!" Ta furta "Sauran bayanin zanzo gidan anjima, wannan dai na fad'a miki ne saboda girman maganar ba zan iya jira sai nazo din ba, jiya muka je kuma dare yayi mana a hanya ga rashin network me kyau da tun a jiyan ma zan kira." " Shikenan Kawu, sai kazo." " Yawwa,Allah ya sanya alkhair ya basu zaman lafiya." Kasa amsawa tayi da Amin, taji kamar  kalmar bata chanchanci a fadeta a irin wannan auren na Adam ba, jin tayi shiru sai kawai ya kashe, su yanzu sun zama yan kallo a sha'anin Hajiya Maman da yaranta, duk abinda tace dasu suyi shi kawai sukeyi basa wani duba ya dace ko be dace ba.    ***Dukkan su sun hadu a gidan suna zazzaune, Rauda har da kuka da aka gaya mata ta taho a lokacin, Hidaya ma da sauran yan gidan duk sun zo, wayar Asma'un da Ya Hadiza ta dauko aka kira, umma ta kalle ta ita ma ta kalle ta sannan ta kalli wayar, ABDALLAH ta ga anyi saving, ta gane waye amma kuma bata san me zata ce masa ba idan an daga. Katsewa tayi aka kuma sake kira "Ki daga kice bata kusa." "Toh." Tace tana dagawa "Hello, ina kwana." "Lafiya lou." Ya amsa cike da tantamar wadda ta daga "Yayarta ce, Asma'un bata kusa." "Oh... Ina kwana?" Ya gaishe ta "Lafiya lou, zaa fad'a mata idan ta zo." " Owk nagode Aunty." Ya katse yana cike da jin kunya. Tashi yayi daga gadon dan yau ya more baccin sa sosai, yana tashi ita ta fara fado masa a rai, shine ya kirata yaji lafiyar ta, toilet ya nufa yana rage kayan dake jikin sa, ya bud'e drawer a dan corridor din da zai kaika wajen da akayi a farkon toilet din me dauke da wardrobe din kayan sa, laundry basket, mirror , shoe rag da sink a gefe, towel ya ciro ya daura a kugunsa ya tsaya a gaban mirror din yana taba sajen fuskar sa, yana bukatar aski dan ya dan tara gashin sosai, maimakon ya shiga toilet din sai ya jona clipper ya tsaya a gaban mirror din yayi gyaran fuska, ya gama ya mayar da komai wajen sa sannan ya fad'a cikin toilet din in da toilet din da wajen wankan yake. A tsanake yayi wankan ya fito ya gyara jikinsa ya saka kananan kaya riga da wandon, ya zura slippers ya fito falon su, MD ya tarar a saman table yana duba abu a system gefen sa black tea ne, zama yayi a kujerar gefen sa. "Good morning Sir." Ya dan sauke kansa kasa alamun girmamawa Dariya MD ya saka yana ture system din "Waye Sir din? Ai wallahi ban isa ba.". " Sir Mudan mana, MD K'AREFA GROUP OF COMPANIES." " Toh ai kai kuma kai ne kankat din Oga, kai na a k'asa." " Munafuki motar nan na zuwa zaka koma raina ni." Ya buge masa kafada " Ai ban isa ba wallahi, Oga a kawo maka tea din ne?" "Eh a kawo, a hado da wani abun me dan nauyi." " An gama ranka ya dade." Ya mike yayi hanyar barin part din, murmushi kawai Abdallah yayi, yana kara jin kaunar dan uwan nasa, hadin kansu shi yafi masa komai, hakan kuma ya samo asali ne tun a farkon zamantakewar iyayen su, in da har baka iya banbance dan waye wannan a cikin su, shi kansa yasan yafi sabawa da Mami fiye da Mum da ta kasance mahaifiyar sa, haka ma MD yafi sabawa da Mum, tsiran haihuwar sa da ta Mudan shekara daya ce shiyasa suka taso tamkar tagwaye. Koman su daya ne tunda suka tashi har kawo yanzu da suka girma hakan bata chanja ba, banbancin su kawai shine shi Abdallah bashi da hayaniya da magana kamar Mudan din. _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ 2 _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* *RM*      *25* ***Dawowa yayi dauke da tray ya ajiye masa a tsakiyar falon, mikewa yayi bayan ya gama karanta bayanin dake kan screen din system din yazo ya zauna ya tankwashe kafarsa, gefen sa MD ya zauna shima bayan ya dauko system din ya dawo da ita kasan, suka cigaba da hira yana breakfast shi kuma yana shigar da wasu informations. "Kunyi waya da Baba kuwa?" Abdallah yace bayan ya gama ya ture tray din gefe, a ka'idar sa baya taba magana idan yana cin abinci, sai ya kammala. " "Eh munyi." "Owk ya maganar dawowar sa? Ko zaka je ka same shi a chan?" "Anya? Kamar sun ma gama zuwa jibi yace zai dawo." "Owk,. Allah ya dawo dashi lafiya, akwai aikin da ya bani nima, kafin ya tafi duk da dai naci karfin sa, sauran rarrabawa kawai." "Aikin zakkar ne?" "Eh wallahi, shi yake sani kwanciya late kwana biyu,amma an gama fitar da komai kawai yanzu rabawar ne.." "Ah masha ALLAH, gaskiya Baba yana kokarin sauke hakkin Allah, kasan fa yanzu yan kasuwa da masu kudi basu cika fitar da zakka ba, ko a fitar a bada ita ta yadda ba zata taba wani amfanar wanda aka bawa ba." " Sosai, Allah ya bamu ikon sauke nauyin dake wuyan mu." " Amin na Ma'u." " Ka fara kenan ko?" " Daga magana?" " Tashi mu shiga wajen ciki, Allah yasa bakayi barin zance ka fadi maganar nan ba." "Wacce, ta I love you din nan?" "Kana da katuwar matsala, kaga ka sameni a ciki kawai." "Allah ban fad'a ba, na dai ji inason na fad'a da na shiga dazu, na daure dai saboda abinda kayi min alkawari." "Kaji dashi, idan ma ka fada kanka kayi ma ai." "Ba zan ma fad'a ba." Yace yana zura takalmi a kafarsa, tuni har Abdallan ya kai kofa , yayi sauri suka jera har ciki, Ihsan da Amira na zaune kowacce da waya suna dannawa, suna ganin su kowacce ta nutsu, suka gaishe da Abdallah tunda dama shine be shigo ba, ya amsa yana hararar hannun Ihsan da yake ita ke facing dinta, "Baku da aiki sai danne dannen waya ko?" Girgiza kai tayi, ya wuce be sake cewa komai ba, dariya ce ta so kwacewa Ihsan din tuno abinda taji jiya, ta kalli Amira tayi mata signal da ido,dan dama tun a jiyan ta fesa mata labarin, kama bakin ta tayi da hannu tayi mata alamar wallahi babu ruwan ta, "Gulmar me kuke? Munafuki."MD yace yana duban kowaccen su "Wallahi Allah Ya Mudan babu ruwa na." "Nima babu ruwana." "Sai kun fad'a min, kallon me.kike mata? Ke kuma me kike cewa ba ruwanki?" "Dama ihsan ce..." "Amana fa nace miki." "Toh ni ai ba ruwana, ni bance ki fad'a min ba kika fada min,." " Wai me? Me ta fad'a miki." Rage muryarta tayi sosai kasa k'asa tace " Jiya ne kuna magana da Ya Abuya a balcony ashe isy taji shine tazo ta fadawa Mami da Mum nima ta fad'a min." " Shikenan kun ja min, yanzu zai dauka ni na fad'a.". Da sauri yayi hanyar dakin Mami da Abdallan ya shiga, ya tarar da shi a zaune kusa da mamin tana masa magana, wani kallo da yayi masa tun kafin ya karaso ciki ya bashi tabbacin maganar Mami take masa, Ashe neman shi da take tayi tun dazu kenan, ji yayi tana cewa " Naji dadi sosai wallahi, Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya sa ayi damu." Kasa amsawa yayi da Amin saboda kunyar da ta lullube shi, ya dinga jerawa MD aiken harara, da sauri ya karaso ciki yana kama bakin sa "Wallahi Allah bani na fad'a ba, Mami dan Allah ni na fad'a miki?" "Toh idan kaine sai me? Dama ai dole a fad'a mana tunda abin farin ciki ne." "Eh amma.dai ai ba wajena kika ji ba? Waccan me bakin akun ce ta fad'a miki ko?" "Wa?" Tace tana nuna kamar bata san wa yake nufi ba, dan tasan zasu iya takurawa Ihsan akan haka, shiyasa ba ma zata ce ita bace ta fad'a, tsakanin su chan su karata da boye boyen su "Kai ka fada min dazu da ka shigo ko ka manta, anan su ma yaran sukaji." "Mami..." Ya fad'a saman gadon ta yana hade hannayen sa waje guda "Dan Allah ki taimaka min kice bani na fad'a ba." "Waye ya fad'a toh?" Ganin da gaske ba zata fad'a ba, ya saka shi bin bayan Abdallan suka shiga dakin Mum suka sake fitowa a tare, su Ihsan basa falon sun tashi, daga gani Mami ce tace su tashi kafin su fito. Zai kama su ne ko zuwa anjima ne, ya ayyana a ransa. Wayar sa ya dauko kawai daga shashen nasu ya bar gidan ba tare da ya saurari MD din ba, dan so yake ya fara aikin da Baban ya saka shi yau yaga abinda zai iya yi kafin yammacin ranar. ***Wayar sa ya kunna sanda suka isa zariya, ya dubo number wani friend dinsa da sukayi school tare ya yi dialing, yana dagawa yace masa gashi a zariya yana neman masauki shi da madam ne, baya kuma son sauka a hotel, kasancewar yasan yayi aure ya saka be kawo komai ba, ya fad'a masa in da zasu hadu, ya katse wayar yana sauka daga kan main road din, "Ina zaka kai ni?" "Auren mu zan nemi wanda zai gyara mana shi, I can't do without you, nasan kuma kema haka ne, so ki kwantar da hankalin ki, duk abubuwan da nayi miki a baya marasa kyau, zan gyara komai,." "Bana son ka, bana kaunar me son ka, idan kaga dama ka tafi dani daga nan har karshen duniya ba zan taba auren ka ba." "Ai ba ke dama xaki aure ni ba, ni ne zan aure ki, za kuma ki gani, my baby love." Ya kai hannun sa ya shafi gefen fuskarta, ta matsa da sauri tana hararar sa, ji take kamar ta samu wani abu ta daba masa, ta daina ganin shi kwata-kwata saboda tsanar da take masa. In da zasu hadu da abokin nasa suka je, ya zo suka gaisa ya shigo motar, suka tafi, bata ce musu uffan ba, tana jin abokin yana tsokanar ta da amarya, tayi masa banza sai Adam din ne yace ai bata jin dadi ne, abokin yace Allah ya kara sauki. Wani dan madaidaicin gida ya kaisu, ya fito yana basu umarnin su fito "Ina fatan dai ba zaku takura anan ba, part biyu ne,madam dita ce a daya, dayan kuma na brother dina ne da zai yi aure, an gama komai." " Ya isa, just kwana biyu zamuyi, wani aike ne ya kawo ni da na gama zamu wuce." " Owk, muje toh." " Muje." Ya bud'e mata kofar, ta fito tana masa mugun kallo amma ko a jikinsa, ya sakata a gaba har ciki, dan idan ma tace zatayi masa gardama bata kuma san in da zai kai ta ba. _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ 2 _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* RM      26 ***Matar sa na zaune a falon suka shigo, tun a hanya yayi mata text message saboda haka ta san da zuwan su, ta fara'ar ta, ta tari Asma'un, ta dan saki fuskarta kad'an, suka gaisa sannan tace ta taso , ba musu ta bi bayan ta suka shiga dakinta, ta kawo mata ruwan sha da lemo sai abinci, ruwan kawai tasha ta jingina kanta da drawer din da take zaune a kusa da ita. Sake shigowa matar tayi, tace mata zatayi alwala kasancewar wajen karfe daya lokacin na rana, toilet ta nuna mata sannan ta shinfida mata sallaya kafin ta fito, ta koma wajen su Adam din da suke falo tare da mijinta, ta kwashe kayan abincin da suka ci. Fitowa tayi daga toilet idon ta ya sauka akan karamar wayar dake saman mirror, dauka tayi da dan sauri ta saka number Abba tayi dialing. A dai-dai lokacin Abban tare da Abban su Abeed da Umar da wani abokin Abban suna kokarin tafiya police station sai ga kiran, kallon number da be sani ba Abba yayi, wani tunani ya kawo masa, ya daga da sauri yana kiran sunan ta "Asma'u?" "Abba nice." "Kina ina Asma'u? Fad'a min inda kike yanzu gamu nan." "Bansan ina ya kawo ni ba, gidan wani abokin sa ne dai, yanzu haka ina dakin matar zanyi sallah." "Ina adamun?" "Suna falo." "Ki kwantar da hankalinki, ki zauna a gidan kinji? Tunda bashi da hankali nasan ta inda zan bullo masa." "Yawwa, zan kiraki yanzu ki rike wayar." Kallon su yayi da su ma shi suke kallo jin ya ambaci Asma'u "Wai wani gidan abokin sa ya kai ta, da sauki ma tunda ba wani wajen daban bane." "Toh Alhamdulillah, yanzu menene abun yi." "Ba zamu kai maganar wajen yan sanda ba musamman tunda tana hannu na gari, idan mukayi haka kamar mun daba ma cikin mu wuka ne, bamu san yadda mutane zasu juya labarin ba, sai kaga an juya masa maana kuma dai kaga mace ce gidan wani zata nan gaba. " " Gaskiya ne." Abokin Abban yace, sai duk suka yi shiru kowa yana saka yadda za'a bullowa al'amarin. Ajiye wayar tayi ta tada sallah, lokacin matar ta sake shigowa taga tana sallah sai ta juya, ta same su a tsaye zasu fita, dama Adam din ne yace tayi mata magana, " Sallah take." Tace masa, dan jim yayi kamar yana tunani sai kuma yace "Dan Allah ki kula da ita, kar tace miki zata wani wajen babu in da ta sani." " In sha Allah." Fita sukayi ta rufe kofar falon ta koma ciki, ta zauna tana jiran ta idar da sallar, su kuwa dama fitar da sukayi wajen wani malami zai raka shi, zaman da sukayi suka ci abinci ne ya bashi labarin dalilin zuwan su nan din, amma ya boye masa da ainihin abinda ya raba su din, kuma ya nuna masa suna matukar kaunar junan su dashi da ita, shiyasa ma ya yarda zai taimaka masa suje wajen malamin ko Allah zai sa a dace a maida auren nasu kawai, idan yaso sai su koma gidan da auren su.    Murmushi tayi mata ganin ta idar, ta maida mata itama, "Mijinki ya aiko na kiraki, amma sun fita ba dadewa zasuyi ba." "Ok." Tace a gajarce, "Sunana Aisha, kefa." "Asma'u." "Lallai, kamar ma baku dade da auren ba ko? Dan kamar nasan lokacin da dear yaje bikin naku." "Eh... Bamu dadi ba." "Allah sarki, Allah ya sanya alkhair." Maimakon ta amsa sai tace "Garin ku me kyau, na dade ina jin labarin garin wajen wata kawata mijinta dan nan ne, sai yau Allah yayi zanzo." " Kice baki taba zuwa zariya ba, ah lallai kinyi missing, ba laifi kam garin namu." " Gaskiya, ita wannan unguwar taku fa, ya sunan ta." " Anguwar zariya." " Ok su kamar a limancin kona suke." "Owk na san unguwar sosai, akwai wasu yan uwan mu a can ina zuwa." " Lallai." Tace tana jinjina kai, ta lura gwanar hira ce Ayshan, ta sake da ita sosai kamar sun saba, daurewa take tana tayata hirar tun da ta ji in da take, ganin lokaci na tafiya yace tace " Kinga na bar wayata a mota, dan Allah bani aron taki." "Owk ba damuwa, ina na ajiye wayar ne?" " Itace wannan?" Ta dago mata wadda tayi kiran daxu " Yawwa eh, yi amfani da wannan din, bari na dubo dayar ko a kitchen na barta." " Owk." Text message ta turawa Abba " Muna zariya, cikin birnin zariyan." Reply yayi mata da " Gamu nan. " Goge komai tayi ta ajiye wayar tana sauke ajiyar zuciya, rashin wankan da batayi ba yafi komai damun ta, gashi bata da kayan da zata chanja da har wanka sai tayi, hijab din dake jikin ta ne kawai ya rufa mata asiri dan dogo ne har ya kusan rufe mata kafarta. Tana zaune suna hira sama-sama har su Adam din suka dawo, basu samu malamin ba sai anjima zasu koma, dan haka sai suka zauna a falo suka cigaba da hirar su, bata fito ba tun da suka zo, gashi yana son ganin ta, ji yake kamar ya shiga dakin yaga halin da take ciki amma dole yayi taka tsantsan dan ba zai yi wasa da wannan damar ba. Be kawo zata karbi waya ta kira ba, dan shi a tunanin sa itama tana son shi kamar yadda yake son ta, shiyasa ma yaga batayi wani abu da zai nuna damuwar ta ba, tun wanda tayi bayan sun dauko hanya, hakan ya kara bashi tabbacin komai zai zo musu da sauki. La'asar sukayi suka sake fita dan shi a son samun sa ma ace yau komai ya tabbata, daga nan ya koma gida su tattara kayan su, su bar garin gaba daya tunda be san da maganar Fido ba. A daidai lokacin su Abba sun riga sun kamo hanya har sun yi nisa ma, dan ba zasu bari sai gobe ba. Umar ya taba rashin mutuncin da zai wa Adam din idan suka isa, dan ya gama gane mahaukaci ne na gaske tunda har zai iya take abinda yazo a addinance saboda shegen son kansa. ***Kasa zama mama tayi a gidan ta tafi gidan Abban, ta tarar da Umman da yaranta, kadaran kadahan kowa yayi mata har Umman da take bata girma sosai amma sai taga akasin haka, zuwan nata ya taimaka mata wajen samun saukin tashin hankalin da take ciki tunda ta samu labarin an san in da Adam din yake, ta dauka da gaske Abban zai kai karar Adam din, bayan tahowar ta Faiza ta rako masu motar kayan furnitures da kayan kitchen, sun samu labarin an daura auren bayan Fido din ta koma, aikuwa suka hau shiri gadan gadam sauran kawayen Fido din da ta yarda dasu suka bi Faizan su zasuyi jere, ita kuma ta nufi salon daga nan zata wuce kunshi, ita a dole amarya, fadar irin farin cikin da take ciki ma bata baki ne, shi gogan bata san ko labarin auren be sani ba, kamar ma ya manta da maganar wata Fido kwata kwata. Babu izinin kowa suka shiga gidan maigadi ya bud'e musu cike da mamakin yanayin su, kasancewar gidan yana nan a sabon shi babu abinda yayi, sukayi jeren su da uban kaya, har yamma suka yi ganin ba zai gamu a ranar ba yasa suka bari su dawo gobe su karasa, Fido bata so ma, dan ma tayi kiran Hajiya da shi kansa Adam din duk bata shiga, hakura tayi goben amma idan har be kira ko yazo ba zata kai kanta ne, su Faiza sun rakata idan yaso ya dawo ya sameta a chan tunda dai aure ya riga ya dauro hatta sadakin ta yana cikin acc din ta.    Sai wajen magriba sannan su Abba suka isa zariyan, ya kira number da Asma'un ta kirashi, ta dan jima tana ringing kafin a daga, wayar na hannun matar abokin Adam din ita kauma Asma'u tana sallah, jin namiji ne ya kira wayar ya sakata katse kiran cike da mamakin waye, ajiye wayar tayi ta karasa abinda take ta fito, ta samu ta idar, wayar ta mika mata ganin kiran na sake shigowa "Ko number da kika kira ce?" Da sauri ta karba, ta daga tana mikewa tsaye "Eh abba, bari na baka tayi maka kwatance." Sai ta mika mata "Dan Allah kwantancen gidan nan zaki ma abbanmu." Karba tayi ta gajshe shi cikin girmamawa sannan tayi masa kwantancen, ta bawa Asma'un yace gasu nan, kasa zama tayi dan bata so Adam ya dawo, Aysha na lura da ita, ta kasa hakuri tace "Zuwa zai yi?" "Eh, zuwa zai mu tafi." "Owk." Tace ba dan ta gamsu ba, ta shiga sake sake a ranta, ta tabbata akwai wani abu dan yanayin Asma'un ya sa ta gane labarin ba yadda Adam din ya fad'a bane, basu dade da wayar ba suka iso kuwa, Umar ne ya kira a wannan karon,yace mata sun karaso Toh." Tace ta ajiye wayar, sannan tace wa Ayshan " Suna waje, zasu jira Adam din su dawo, dama so nake su zo sai na fad'a miki gaskiya...Mun rabu da Adam bama tare a yanzu, karya yayi wa mijinki, ba da izini na ko na iyaye na ya taho dani nan ba, bayan kuma babu damar da auren mu zai koma saboda saki uku yayi min,. " " Wayyo, amma be kyauta ba, wallahi ni Ina ganin ki naji kin kwanta min a rai na, dan Allah ki bani number ki ma dinga gaisawa. " "Toh. " Ta saka mata number ta, tace ta kira idan ta koma zata gani sai tayi saving, ta kira kuwa a take, sannan ta shiga daki ta hado mata abubuwa a leda ta kawo mata. Shiru su Adam din basu dawo ba, Umar ya sake kiranta yace ta fito kawai, tayi wa Ayshan sallama ta rakota har waje, ta gaida su Abban, motar Asma'u ta shiga, ta sake mata sallama tana tsaye suka bar layin, ta girgiza kanta tana juyawa dan ta koma ciki, ta hango motar su tana shigowa layin amma ba ta in da su Asma'un suka bi ba, ciki ta koma suka shigo, ta fito tana musu sannu da zuwa, wara ido Adam yake ko zai ganta amma ko motsin ta be ji ba, kasa hakuri yayi yace "Please Madam kice ta fito na ganta, tunda muka zo ake punishing dina." "Owk." Tace sannan tace "Dear dan zo kaji." Bin ta yayi ciki, ta fad'a masa komai da komai da Asma'u ta fad'a mata, dama yayi tunanin haka ganin a yadda suka zo garin da kuma yadda Adam din ya damu sosai, gwara da akayi haka ma, komawa yayi wajen Adam din ya tarar dashi yana kaiwa da komowa irin ta wanda yake cikin damuwa sosai, "Ba zata zo ba?" Yace da sauri "A ah, she's gone. " " How? Ta yaya? " Ya fad'a a kidime " Kayi hakuri kawai, kasan dai babu aure bayan saki uku, ina ganin be kamata kayi kokarin halatta abinda yake haramun ba. " " Ba wannan nake son ji ba, ka fada min tana ina, ina taje? " Yayi maganar cikin daga murya da karaji " Tare da kai muka fita, bayan mun fita aka zo aka tafi da ita, she told my wife everything. " " Damn it! " Ya daki bangon falon " Da na sani ban yi trusting naku ba, amma zan dawo..." Ya juya cikin sassarfa ya bar falon, ya rasa ina zai kama, ta ina zai fara, ya samu dama me kyau amma yayi wasa da ita, me yasa ma ya tafi ya barta, bayan yasan tana da damar da zatayi waya ta kira gida. Rasa ina tsoma ransa yaji dadi yayi, ya kasa tuka motar ma, baya tunanin zai iya hawa titin nan balle ya kai kansa kano a daren, dole zai jira gari ya waye saboda lafiyar sa, sai da ya bari kafa ta fara daukewa a garin ya samu wani gidan mai da baya amfani, direbobin mota ne yawanci suke kwana a ciki parking yayi a ciki, ya sauke glass din motar ya kwanta a baya, sauro kuwa yace da wa Allah ya hada mu, ya dinga gasa masa cizo babu tausayawa, abinka da farar fata kafin safiya ya fice daga hayyacin sa, babu wanka babu komai ya dauko hanya. Hafsat Rano -RM            27 ***Lokacin da suka dauko hanya Umma ta kira Abba, ya daga ya sanar mata da gasu nan tare da Asma'un, Alhamdulillah, ta furta sannan ta kashe tana sanar musu da abinda Abban yace, har lokacin Hajiya Mama na gidan, tana jin an ce sun taho ta tashi, tayi musu sallama ta tafi,dan dama zaman jiran da take kenan, Nadeeya ta kirata ta fad'a mata zuwan kawayen Fido gidan, shiyasa take so taje taga me yake faruwa duk da dai an ce sun tafi. Duk suma sai umma tace su tafi gidajen su sun dawo gobe, Ya Hadiza ce kawai ta rage suka zauna da Umman suna dakon zuwan su Abban, sai dare sosai suka dawo, Asma'u ta rungume umman tana fashewa da kuka, ita ma umman kukan ta saka, amma ba kamar Asma'un da duk dauriyar da take jin tana da ita a gaban Adam din ta neme ta a yanzu ta rasa, ta gaji sosai da komai dama rayuwar baki daya, hakuri duk sukayi ta bata, Abba yayi mata nasiha me ratsa jiki, hakan ya sanyaya mata jiki ya sakata yin shiru sai jan ajiyar zuciya take, su kansu sun san tabbas a yanzu ta kai karshe. Da safe ta tashi da missed calls din sa, da text message bayan kiran da yayi mata da ya Hadiza ta fad'a mata da zata bata wayar, ji take kamar bata bukatar sake shigar da kanta wata matsalar a yanzu, amma kuma ba zata iya yi masa wulakanci ba. Wanka ta fara yi, tana shiryawa umma ta shigo dauke da abincin ta, ta ajiye tana kallon ta, shigowar ta uku kenan tana tarar da Asma'un na bacci, tausayin yar tasu suke ji dan sai da Abba yaga da gaske ba a lokacin zata tashi ba ya hskura ya fita, dan da so yayi ya dan kara bata baki kafin ya fitan. "Umma..." "Naam Asma'u, kin tashi kenan." "Eh na tashi, ina kwana!?" "Lafiya lou, Abban yana ta jiranki, yaki fita da yaga baki tashi ba sai ya hakura suka fita da Abbati." " Allah sarki Abba, bacci nayi tayi wallahi." " Ai gwara ki huta sosai, ga abinci nan kici, saura ki tsaya janjani kici sosai." ",Toh umma." Tace tana sauke abincin kasa, ta zauna kenan wayar ta, tayi kara, ta kalli umma kafin ta kalli wayar, shine yake sake kira. " Shine ko? Ki daga kar yayi tunanin wani abu, jiya ya kira ma." "Toh." Tace tana dagawa, sai umman ta fita ta ja mata kofar a ranta tana addu'ar dacewar Asma'un Daga nan tana iya jiyo ajiyar zuciyar da ya sauke, dan shi kadai ya san yanayin da ya shiga na rashin samun ta a waya jiya gaba daya, badan aikin da ya fita ya tsaida shi ba da komai dare sai yazo, shiyasa yau yana tashi ko shiryawa be ba, ya hau kiran ta, be sameta ba yayi mata text message shima shiru shine yanzu har ya zauna a office dinsa yaji sai ya kuma gwada kiran ko zata dauka, "Ina kwana?" Tayi breaking shirun da yayi ta hanyar gaishe shi, shi kansa be san shirun me yayi ba bayan abinda yayi ta fata kenan yaji ta daga, amma kuma ya lura kamar so yake ta sake magana yaji muryarta tar ya sake tabbatr da ita din ce ta daga a yanzu "Me bawan Allah yayi aka wahalar da zuciya da ruhin sa jiya? Umm?" "Babu komai, wayar ce bata wajena." "Baki san yadda na damu ba wallahi, anyways, hope komai lafiya?" "Alhamdulillah." "Ok masha Allah, nazo na ganki?" "Na'am?" "Eh? Are you free nazo yanzu, inason ganinki. " " Owk sai kazo. " Ta samu kanta da hana shi, murmushi yayi wanda har sai da ta jiyo sautin sa, ya ajiye wayar bayan yace mata gashi nan, mikewa yayi ya cire rigar suit dinsa dake rataye a saman kujerar da yake zaune, ya saka yana balle botir din jiki MD ya turo kofar ya shigo rik'e da wasu manyan files, wani kallo yayi masa ganin yana tattare wayoyin sa daga kan table yace " Don't tell me fita zakayi." " Fita zan, akwai wani abu ne? " " Sosai, sai ka duba kayan nan, akwai wajen da zakayi signing kafin su saki kayan. " " Gaskiya sauri nake, ba zan iya ba, ajiye kawai sai na dawo. " Dora files din MD yayi a saman table din yana bin Abdallah da kalllo, hanyar fita yayi ya bishi da sauri yana jerawa dashi "Meeting zaka?" "A ah." "Ina toh?" "Ina ruwan ka? Dole sai kaji duk in da zani?" "Ahhhh! Yau kuma?" "Eh." Ya kauda kansa barin kallon MD din dan zai iya ranfoshi nan da nan, cikin lift suka shiga MD nata kokarin sai ya ji in da zaije amma yaki fad'a masa, ya bishi har parking space yana masa magiya, ganin da gaske ba zai fda masa ba, sai kawai ya bud'e motar ya shiga, ya zauna a gefen sa "Aikuwa sai dai muje tare, nima dama inaso naga Aunt din tamu, taga dan kanin ta itama." "Mudan wai me yasa kake takura min ne?" "Toh ai kaine, sai kayi ta boye-boye, yanzu dai muje kawai ko ina zaka sai naji." " Oya." Ya jefa masa car key din yana balle murfin motar ya fito, sannan ya zuro kansa yana hararar sa " Kasan ni ba driver ka bane ko? Fito toh." Ba musu ya fito, ya zagayo wajen driver ya shiga, shi kuma Abdallah ya koma wajen me zaman banza, yaja motar. Fita tayi ta samu umma a daki, ta dan yi jim kafin ta fad'a ma umma wai zaizo, tashi umman tayi da kanta ta sake tabbatar da falon Abba a gyara yake, sannan tace " Kin fada masa kina gida? Kar ya tafi chan." Girgiza kai tayi, " Kira shi toh, ba dadi sai yaje chan sannan ya taho nan." Wayar ta dauko, ba zata iya kiran sa ba, dan haka ta tura masa text message na address din gidan, lokacin sun dauke hanyar gidan Ya Hadizan yaga text din, ya saka MD juyawa suka dawo baya, yana bashi direction din gidan har suka karasa, a waje MD ya faka yana kallon unguwar, yana kuma son ya tsokani Abdallah amma kuma sai sun fito, wayar ya ciro ya kirata, gabanta ya fadi ganin kiran sa ,ta mike tana daidaita nutsuwar ta sannan ta daga, toh tace kawai ta ajiye wayar ta fito, umma na ganin ta tasan sun zo, tace taje ta shigar dashi ta kofar gaban gidan. Fitowa tayi ta bud'e kofar gidan ta dan leko, yana zaune cikin mota yaga sanda ta leko, be cewa MD komai ba kawai ya fito, ganin haka ya saka shima fitowa yana ware ido yayi gulma, gaba kawai Abdallan yayi ya bishi a baya, tana tsaye jikin gate din kamshin turaren su me dadi ya riga su isowa, ta yi saurin kallon wajen dan ta tunanin ta basu ganta ba, shiyasa ma daga leko ta koma tana tunanin wanda zata saka yayi musu magana sai gasu, a kunyace ta gaishe su, tayi ciki tace su shigo, "Nan ma ya isa, kinji?" Tsayawa tayi, ta dawo duk kunya ta cikata, ta tsaya daga jikin gate din, ya shigo ciki MD na take masa baya "Auntyn mu." MD uban azarbabi yace yana wuce Abdallan ya shigo ciki sosai "Yau dai naga wadda ta sace min zuciyar brother na, Masha Allah." "Kaje mota gani nan" "Ban gama ba, kina lafiya?" "Lafiya lou." "Toh Madallah, sunana Mudassir, amma an fi kirana da MD, kuma ni kanin sa ne, kuma best friend dinsa." "Allah sarki." " Kaje mota." "Zan dawo ni kadai Aunty, tunda yanzu korata yake, bari na je motar bansan me yazo fad'a ba." Ya juya yana dariyar mugunta, ya fice. Kallon cikin ido yayi mata bayan fitar MD, tayi saurin kauda idon ta tana sunne kanta k'asa, " Ina office fa, naji kawai inason ganinki, dole na ajiye komai na taho shi kuma wannan uban surutun yazo zai cika miki kunne." " Ba komai, ai yana da kirki." " Ko?" Kanta a kasa ta amsa, hakan ya bashi damar sake more kallon ta, yana admiring kyawunta, da cute innocent face dinta, calmness dinta yaana kara masa sonta " Pleaseeee...Bari naga fuskarki sosai yadda ko na koma office ba zan kasa aiki ba, sai nayi ta tunawa." Rufe fuskar tayi da tafin hannun ta, tayi dariya, ita da gaske kunya yake bata dan bata taba experiencing irin haka ba, da yaga da gaske dai kunyar sa take ji sai ya hakura, yace mata zai dawo, amma next zuwan da zai sai ya fara ganin Abba, daga nan sai yaga me ya kamata ayi, ita dai kawai jin sa take yi. Komawa tayi ciki bayan yayi mata sallama ya tafi, yaje ya samu MD a mota yana waya, tada motar yayi suka bar unguwar har lokacin yana waya, sai da ya gama sannan yake fad'a masa jirgin su Baba Alhaji ya kusa sauka, dan haka yana sauke shi a office din ya wuce airport dauko shi, dan be yarda wani ya dauko shi ba idan ba MD din ko Abuyan ba. Suna barin unguwar Adam na isowa, duk ya lalata motar sa dan tuki na hauka ya dinga yi baya kaucewa rami ko duk abinda yake hanyar, kafin yazo duk ta kakkarje ga dattin da tayi, Umar yaga sanda ya shigo layin a haukace, ya biyo bayan sa da sauri ya fasa siyan abinda zai siya, kafin ya karaso har ya shiga gidan kasancewar shi a mota yake shi kuma a kafa, a tsakar gidan ya same shi, umma tana tsaye daga kofar dakin ta, Asma'u kuma na cikin daki rufe har da key dan yanzu Adam ya wuce a sashi a layin masu hankali sai dai mahaukata. Sosai umma tayi mamakin yadda ya koma, kamar bashi ba ga uwar kasumba da ya tara na rashin gyara, Umar na shigowa be yi wata wata ba, ya zabga masa mari, ya rik'e shi yana kokarin dukan sa "Menene haka Umar?" Umma ta daka masa tsawa "Abinda ya dace dashi kenan umma, duk abinda yake wallahi iskanci ne, dan yaga ana kyale shi ne." " Cika shi, babu ruwanka dashi duk wanda yayi nagari kansa, ai ko yanzu Adam ya gane cewa ba abu bane me kyau zalunci, idan Allah yaso kamaka sai ya kamaka ta in da baka yi zata ba." " Toh ai Umma be ma kamata a bar shi ya shigo gidan nan ba, dan zai iya cutar da Asma'u." " Babu abinda zai iya yi mata." " Umma dan Girman Allah ayi hakuri, wallahi umma nayi nadama dan Allah Asma'u ta saurare ni, dan Allah magana kawai zan fada mata nasan zata amince." "Wai Adam baka san babu aure tsakanin ka da Asma'u bane ko yaya?" " Za'a iya gyarawa umma, dan Allah ki taimaka min." " Tirkashi! Abun naka babba ne Adam." Tace tana rik'e baki, jingina yayi da bangon tsakar gidan, Asma'u ta leko ta window ta hange shi a tsaye ya rataya hannun sa ta bayan sa, Umar na gefe yana hararar sa kamar ya kai masa bugu, umma kuma na kofar dakin ta, tana jiran Abba da ta kira yace gashi nan, komawa tayi ta haye gado tayi kwanciyar ta, dan bata da bukatar ji ko ganin duk wani abu da ya danganci Adam din. Shiru Abban be karaso ba, umma ta shige ciki aka barshi a wajen, a rana amma kamar be damu ba, ya cigaaba da zaman jiran fitowar Asma'un, a daidai lokacin Fido da kawayenta suke isa gidan, Hajiya Mama na tsakar gida tana bawa masu aikinta sallahu dan Abba yace tazo gidan ayi magana, sai gasu sun shigo sun saka Fido a tsakiya ta sha lullubi a dole amarya, turus Hajiyan tayi, jiki a sanyaye ta jasu cikin falon, suka gaishe ta Faiza tace amarya suke kawo, da kanta ta tashi ta rakasu har gidan Adam din, sannan ta fito jikin ta na kara sanyaya, a halin da Adam din yake ciki yanzu bata san yadda zai karbi batun auren ba, wanda ita kanta bata san me ya sha kanta ta amince ba, dan sai yanzu take jin ta tafka babban kuskure wajen amincewa,amma kuma bata san ya zatayi ba, bata da zabi. _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ 2 _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* RM *28* ***** Yana tsaye a tsakar gidan Hajiya ta shigo, ganin ta be saka shi tashi ba, sai ma sake gyara tsaiwar sa da yayi dan ko sama da k'asa zata hade yau sai yayi magana da Asma'u, yasan zata fahimce shi, yasan zata sake bashi dama, "Adam!" Ta kira sunan sa tana rik'e bakin ta, sai kuma ta kada kanta zuwa ciki tana kwala sallama, jin sallamar ta ya saka Umma fitowa, tayi mata iso zuwa ciki, ta kasa zama ta tsaya daga tsaye jikin ta duk yayi sanyi "Be karaso ba amma nasan daf yake da shigowa." "Assalamu alaikum." Yayi sallama tana shigowa gidan "Yauwa gashi nan ma." Waje sukayo tare, suka tarar dashi a tsaye a gaban Adam din yana masa magana, "Tsaiwar me kake anan Adam?" Maimakon ya bashi amsa sai kawai gani sukayi ya zube guiwowin sa a k'asa "Abba dan Allah kayi min rai." "Tashi maza, tashi." Ya dago shi amma sai ya noke yana cigaba da magiya da hada Abban da Allah, jikin Mama ya kara sanyi sosai tana daga gefe bata ce komai ba, duk abinda yake faruwa bata tanka ba, fad'a Abban ya soma yiwa Adam din cikin sigar lallashi, amma sam ya kasa fahimta shi dai kawai ayi hakuri dan Allah, ganin da gaske ba zai gane ba, ya saka Abban yin gaba yana cewa "Umar dauki waya ya kira min Ali." Toh yace yana komawa daki ya dauko wayar sa, ya kira ya taho da wayar ya mikawa Abban, dagawa yayi da sallama ya gaida Abban, "Kana jina Ali, yaron nan da yazo neman auren Asma'u nake so ka tura min shi, idan zai iya zuwa yanzu toh, idan sai yamma ma dai ina jiran sa." "Yawwa." Ya katse kiran yana juyawa wajen Hajiya Mama "Yaya nayi wa Asma'u miji in sha Allah, dalilin sanin cewa babu aure a tsakanin su da Adamu, dan haka nake so gani baki ga mahaifiyar Asma'u, ina so Adam ya kyale Asma'u ya barta tayi facing rayuwar ta, bana son wata matsala ta taso, alakar dake tsakanin mu tafi karfin abinda zai kai mu wajen hukuma, amma tabbas da ba Adam bane ya dauki Asma'u toh sai dai hukuma ta raba mu dashi." "Na sani." Tace " Amma kayi hakuri nasan ko ta ina ba'a kyauta maka ba, zan masa fad'a in sha Allah ba zai sake zamar wa Asma'u matsala ba." "Kai kuma Wuce muje." Kin tafiya yayi, ya cigaba da magiya, ciki Abba ya shige umma ma haka, ganin yaki tashi ya saka Hajiya Mama fita waje, ta kudura a ranta duk ma abinda zasu masa suyi masa kawai ita ta gaji, tana fita Umar ya fito, ganin babu kowa a wajen yazo da sauri yana kama kafadar Adam din "Tashi ka fita, wallahi ko zaka mutu Asma'u ba zata ganka ba." "Dan Allah minti biyu kawai ya isa, dan Allah." "Ko minti rabi ne wallahi ba zaka ganta ba, kaje chan an kai maka mata, karka zo nan ka ishe mu." "Mata?" "Oho idan kaje ai zaka gani." Cikin hanzari ya mike, yayi hanyar waje da mugun sauri, dariyar mugunta Umar ya fashe da, har da tafa hannu, yana cike da jin dadin yadda abubuwan suka sauya wa Adam din a dare daya, dama chan basa shiri haushin sa yake ji saboda shegen girman kansa. Asma'u na jin duk abinda akeyi, ta sake gyara kwanciyar ta kawai tana jin duk babu dadi. ***Abdallah na office ya samu kiran Abban su Abeed, ya mike tsaye da sauri kafin ya daga wayar, sakon kiran Abban da ya sanar masa ya haddasa masa kasala har ya kasa cigaba da aiwatar da aikin dake gaban sa, duk da dama a yau yayi niyyar zuwa ganin nasa amma kuma sakon yazo masa a bazata, ya kuma saka masa shakku da tsoron Allah dai yasa ba wani abun bane, a daddafe ya karasa abinda yake, be bari yamma tayi ba, ya tashi gaba daya, ya rufe office din ya fito, a kofa suka hadu da Fazallah, yace "Yallabai ba dai tafiya zakayi ba?" "Eh akwai wani abu ne?" "Gaskiya, kayan da Alhaji ya aiko dasu sun iso, har an yi cleaning nasu da komai gasu chan ma a k'asa, dole sai ka fara dubawa kafin ayi distributing dinsu." "Ba zasu iya hakuri gobe ba?" "Eh toh..." "Ka basu hakuri kace su koma gida su huta, gobe duk sai su dawo kowa sai ya dauki wanda zai kai, yanzu kam akwai important abu da zanyi wallahi." "Ba matsala, zan sanar dasu." "Yawwa." Yayi gaba yana take masa baya, wayar sa ya zaro ya kira MD yace ya tashi ya zo gida yana so ya raka shi wajen Baba Alhaji zai masa wata magana, toh yace ya kashe yana sake daga kafarsa zuwa wajen mota, ya samu driver companyn nasu ya bashi car keys din yace ya kaishi gida dan ji yake kamar ba zai iya taka motar ba, zama yayi yana karo karfin AC motar, ya runtse idon sa yana hasaso abinda zai faru, ya family dinsa zasu karbi maganar, har aka zo gidan be san an zo ba yayi zurfin a tunanin sa, sai da yaji motar ta tsaya sannan ya dago idanun sa da suka dan daga saboda gajiya ya zura wa harabar gidan kamar ranar ya fara zuwa, a nutse ya turo murfin motar ya fito yana kallon motar MD dake ajiye a gefe alamun ya dawo kenan, maimakon ya wuce part dinsu, kai tsaye na Baba Alhajin ya nufa bayan ya bawa maigadi jakar sa da tarkacen sa ya kai masa chan. A zaune ya hange shi, daga shi sai yar shara da dogon wando, kansa da ya soma tara farin gashi ya zubawa ido yana ayyana yadda rayuwar take tafiya ba tare da mutane sun farga ba. "Bawan Allah!" Ya fad'a sanda Abdallan ya shigo, hakan ya kara masa karsashi ya karaso ciki da dan sassarfa, da kallo yake bin sa har ya zauna a kasan makeken carpet din dake malale a tsakiyar falon, ya tankwashe kafarsa dake sanye da safa wadda ta tsaya masa daidai idon sahu, ya dukar da kansa cike da girmamawa irin ta da da mahaifi yace "Barka da warhaka Baba." "Barka dai Abuya, an taso?" "Eh baba, ya hanya? An dawo lafiya?" "Alhamdulillah wallahi, ya ayyukan? Ina fatan babu matsala." "Babu." Yace a takaice "Toh Madallah, kaci abinci kuwa? Ko duk gajiyar ce na ganka haka haka." "Naci, akwai gajiyar ma ai." "Toh Allah yasa mu dace." Dan jim yayi bayan ya amsa da amin, ya rasa ta ina zai fara fadawa Baban maganar, Baban na ankare dashi, ya kuma san me zai fad'a masa dan tun daga airport Mudan ya fesa masa, "Abuya?" "Na'am." Yayi firgigit ya amsa "Yarinyar yar ina ce?" "Yan Sumaila ne Baba." "Masha Allah, ka aminta da ita da tarbiyyar ta? Saboda babban kuskuren da mace ko namiji zasuyi a rayuwar su shine zabin abokan zama ba na kwarai ba." "Nayi bincike daidai gwargado, amma zaku iya sake yi." "A ah, babu bukatar hakan dan kai da kanka kana da damar da zaka nemawa kanka aure, kuma na gamsu da kai da tarbiyyar ka, nasan ba zaka yi wa kanka zaben tumun dare ba, yaushe kake so aje?" "Ko yaushe ma, yau dai mahaifin ta yake son gani na,bansan akan menene ba dai." "Kaje aji menene toh, ALLAH ya tabbatar da alkhairi." "Amin." Yace a kasan makoshin sa, "Amma baba, ta taba aure amma bata fi watanni ba, auren ya mutu." "Ka san me ya raba su da mijin ta?" "Eh..." Ya kwashe komai ya fadawa Baban, abinda ya sani dan tun a ranar da ya ganta ya yi bincike yasan komai akanta "Allah sarki, wannan shi ake kira da shikan wawa, irin wanda wani wawa yayi wa mahaifiyar ka har na samu damar aurenta, har kuma yanzu da nake tare da ita ban taba samun matsala da ita ba, mutuniyar kirki. " Sam Abdallan be taba sanin wannan labarin ba, ya dinga kallon Baban har ya kai karshe a maganar sa sannan yace " Kaga shikenan tarihi zai sake maimaita kansa. " Murmushi yayi me sauti, a hankali a hankali ya dinga jin nutsuwa na shigar sa, yana jin kamar ya same ta ya gama ne, dama duk zulumin sa akan yadda iyayen sa zasu karbi maganar ne, amma yanzu da ya samu kwarin guiwa sai yake jin zai iya tunkarar ko ma menene don ganin ya mallake ta. Cike da karsashi ya sake wanka bayan ya chachakali abinci, ya shirya cikin shigar manyan kaya, shi da MD suka fita a motar MD din, Abdallan na zaune a gefen me zaman banza kamar ko da yaushe in zasu fita MD ne yake jan motar, unguwar su Asma'un suka nufa, gaban Abdallan na cigaba da faduwa dan ya kasa nutsuwa da kiran Abban gani yake kamar zai hanashi Asma'un ne, ko yace be gamsu dashi ba, a waje suka tsaya ya kira wayarta a kashe, sai suka samu yaro suka aika shi ciki, tare suka dawo da Abbati da yaron yace su shigo ciki, yana ta satar kallon su, yan gayu sosai, ga hutu da jindadi ya nuna a jikinsa, satar kallon kafar su yayi ya ganta kamar basa taka k'asa, luf luf, ciki ya wuce bayan ya kaisu har falon ya je ya sanar wa da Abba sun shigo. A zaune ya same su, yana shigowa suka sakko k'asa suka gaishe shi, ya masa musu a sake yana karantar su, "Abdallah." Ya kira suna ba dan ya san wanne a cikin su ba, dagowa yayi ya amsa kirjinsa na bugawa "Kai ne kake neman auren Asma'u ko?" "Eh Abba." "Toh masha ALLAH, so nake ka turo magabatanka, suzo muyi magana, dan ba zan boye maka ba, akwai dan uwan ta da muka hada su aure, toh dai Allah cikin ikon sa auren be jima ba, suka rabu bayan yayi mata saki har uku, daga baya ya gane kuskuren sa shine ya dawo, bana son sintirin da yake min anan dan nasan hakan zai hana walwalar Asma'un, shi yasa nake so idan da gaske kake ka fito, idan yaso ko auren ne a daura idan har yaji tayi aure zai hakura dole. " " Haka ne. " MD yace yana jinjina kaie " In Sha Allah magabatanmu zasu zo gobe, in sha Allah. " MD yace dan yasan Abdallan ba zai magana ba " Allah ya kawo su, dama shine dalilin kiran. " " Mun gode Allah ya kara girma. " " Amin ya Allah. " Sai ya mike " Bari tazo, Ku gaida gida." "Mun gode." Ta kofar ciki ya koma, ya tarar da Abbati yana bawa umma labarin su, Asma'u na zaune bata sa baki ba, amma deep down tana jin wani irin feelings dangane dashi, shiyasa ko da Abba ya shawarce ta da maganar tace mata ta amince, musamman ganin yadda hankalin umma ya kwanta dashi duk da bata taba ganin sa ba. Abba ne yace taje suna dakin baki, ta tashi a kunyace ta fita tana daukar takalmin Abbati ta saka, bata ma san shi ta saka ba sam, sai da taje kofar, ta cire sannan ta tuna, shiga tayi tana dan rabewa, ta same su dukka a tsaye idon ta ya sauka a cikin nasa, yayi mata murmushi yana jin sabuwar kaunar ta na ratsa shi, a kunyace ta gaida su, MD ya amsa sannan ya fita ya bar su, gabanta yazo ya tsaya, ta sauke kanta tana jin duk ya cika wajen, kunya da kwarjinin sa suka hanata sakat, muryar sa ta tsinta a saman kanta, taji tamkar kafafun ta zasu kayar da ita a wajen saboda yanayin da ta shiga. "Abba ya amince na turo, kin yarda kin amince zaki bani dama?" Da kai ta amsa masa dan ba zata iya magana ba, yana tsaye daf da ita kamar zai maida ta ciki, sai yar tazara da bata wuce kamu biyu dake tsakanin su ba, mayen kamshin shin sa da yafi komai kashe mata jiki ya cigaba da huda ta, "I promise to take very good care of you, in sha Allah together we will meet tomorrow." "Zan wuce, zan je na samu Baba da maganar, bana so aje lokaci, dan bansan abinda zai faru gaba ba." "Sai ka dawo." Ta samu kanta da furtawa, hayaniyar da suka ji a compound din gidan ta katse su, muryar MD yaji, ita kuma ta Adam, gabanta ya fadi, tabi bayansa da sauri lokacin har Adam din ya shaki kwalar MD, kamar ma baya cikin hayyacin sa, daga gani yasha wani abu ne dan yanayin sa ya nuna hakan. *RM*    29-30 **** Umar tare da Abba suka fito da sauri, lokacin har Abdallah ya karasa wajen, fuzgo Adam Umar yayi, ya hankada shi baya da karfi a zafafe, "Subhallah." Abba yace wata mahaukaciyar kunya na rufe shi, MD ransa yayi mugun baci dan baa taba masa irin wannan wulakancin ba, waya yake be yi aune ba kawai yaji ya shaki shi gami da hada shi da bango, rik'e hannun sa Abdallah yayi yana girgiza masa kai, daga Abban har Umar din sun kasa magana sai girgiza kai kawai da Abban yake yi yana kallon Adam din da yake ta juya idonsa daga gani kasan a make yake, "Dan Allah kuyi hakuri." Abba ya fad'a da k'yar ya ki bari su hada ido da su sam, "Babu komai Abba." Abdallah yace yana jan MD din "Ba komai." Ya sake maimaitawa sannan suka fita daga gidan, MD be ce komai ba, har ya bud'e masa motar ya shiga shi kuma ya zagaya ya zauna a wajen MD din zai kunna motar, rik'e hannun sa MD yayi, yana duban sa "Are you ready to marry  da?" Ya tambaye shi yana tsire shi da ido "I'm more than ready ma, anything?" "Ina wayata?" Ya lalubi aljihun sa, sai ya dauke ta a saman kafarsa "Bani two mint ina zuwa." Ya balle murfin motar ya fita "Karka koma ciki pls." "Waya zan yi." Yace masa yana matsawa gefe, Baba Alhaji ya kira lokacin sun fito compound din gidan shi da Alhaji Muktar da kanin sa Alhaji Tukur, dama duk yammaci indai Baba Alhajin na gida anan suke zama har sai bayan sallar isha'i sannan suke tafiya shi kuma ya shiga ciki, kiran MD ya katse musu hirar da suka akan kasuwancin su, "Ya akayi Mudan?" Yace bayan ya daga "Dama akan maganar yarinyar da Abuya yake neman aure ce,idan kayi mana izini a daura auren a yau?" "Saurin me ake Mudan? Akwai matsala ne? Kuma shi mahaifin nata zai yarda ya baku auren ta daga zuwan ku?" "In Sha Allah babu matsala, dama Baban nata yace a turo ayi magana." "Yanzu me kake so ayi kenan Mudan? Ina shi Abuyan? " "Yana mota, amincewar ka muke nema, idan ka amince sai muga abinda ya kamata ayi." "Na amince, ka tura min address din gidan yanzu zamu zo mu samu mahaifin nata, ka jiramu kafin muzo." " Allah ya kara girma, mun gode Allah ya saka da alkhairi." " Amin. Ina jiran ka." " Zama me kama ku ba, danku ya dauko aure, yanzu haka so suke wai nayi musu izini su nemi auren, shine nace zamu zo sai ayi magana da mahaifin ta muje matsayar sa, su kuma muji dalilin gaggawar, bamu san me Allah ya boye ba, harkar aure tana bani mamaki sosai kar ka sauwala rabo ya kashe ka." " Haka ne, idan har yaron ka ko yarinyar ka ya nuna maka aure yake so , toh kayi masa shine mafi aala, balantana Abdallah ba yaro bane, shi da kansa ya isa ya kai ya nema wa kansa aure kuma a bashi, musamman saboda nagartar sa." " Haka ne." Duk suka hada baki wajen fad'a, suka tashi driver Alhaji Muktar ya dauke su suka nufi unguwar su Asma'un. Lekowa MD yayi maimakon ya shigo matar, fuskar sa tar kamar an masa bushara da gidan aljanna, kamar bashi ne cikin bacin rai a dazun ba, hannu Abdallah ya daga masa alamar ya akayi? Ya kwashe da dariya yana jingina da jikin motar, horn ya danna masa da karfi, ya sake lekowa yana mika hannu ya zare key din motar "Mene haka wai? Na tafiya zamuyi ba?" "Eh akwai sakon da zan karba." "Bani key din ka taho toh, ko so kake ya fito ya kara kama ka da rigima shi da baya gudun abin kunya?" "Wuce nan wallahi, dan a cikin gida ne na kyale shi Amma wallahi anan sai na daka shi kuma na sa an rufe min shi wallahi, yanzu ma ai ban hakura ba, zamu gauraya dashi bayan na nuna masa karfin iko na." Tabe baki Abdallah yayi, cike da kosawa da maganar MD din, " Sai kayi tayi ai." " Zan kuwa yi amma sai na fara aurar da kai tukunna." " Silly boy." Ya zaro wayar sa ya hau dannawa yana share MD din da shirmen sa, Waka yaji yana rarewa, ya girgiza kai yana ayyana abinda ya saka shi farin ciki haka nan da nan, yana zaune cikin motar rabin kafarsa na waje ya zuro su yana rik'e da wayarsa kansa a kasa yana dannawa yaji shigowar mota layi, be dago ba ya cigaba da abinda yake sai yaji an faka a daidai saitin sa, hakan ya saka shi dagowa , mamakin ganin wadanda be yi tunanin gani ba ya cika shi, ya kalli MD da yayi wajen su ya dawo da ganin sa kofar gidan su Asma'un, kansa ne ya kulle ya ma kasa tunanin me yake shirin faruwa ko me yake faruwa, har lokacin yana zaune a motar yana bin su da kallo, Abba ne ya fito daga gidan yana saba babbar rigar sa, cike da girmamawa da mutuntawa suka gaisa sannan ya jasu zuwa cikin gidan, wani kallo yayi ma MD da yake kada kai kamar kadangare yana fatan komai ya kasance kamar yadda ya shirya. Motar Adam na nan kuma be fito daga gidan ba, ya tabbata yana ciki kuma hakan ya sake masa dadi, ya dinga zayaye a tsakanin wajen, fitowa Abdallah yayi ya damko shi yana bata fuskarsa "What have you done? Me ka aikata?" "Wait and see, aure zan maka." "Aure? Ban gane ba." "Nima ban gane ba." "Allah sa ka fada min, kai ka kirasu ko? Me kace musu?" "Eh ni na kira, kana tunanin idan ni ne zan iya barin abinda nake so tare da wanchan mahaukacin? Wallahi ko me za'a yi sai na aure ta na nuna masa iyakar sa, tunda shi jaki ne mahaukaci, kuma ko kusa da ita naga yazo walalhi sai na saka an tsinke min kafarsa daya wallahi." " Oh innalillah, yanzu da wanne idon zan kalle su? Kamar fa yadda ka nuna I'm in desperate kenan ko? Na shiga uku. " "Toh gauro irinka dama ai dole a same shi da matsuwa man,. " " Baka da hankali wallahi. " Yace yana juya masa baya, be san ina zai dauki abinda yake ji ya ajiye ba, farin ciki, tarin fargaba da wani abu kamar tsoro tsoro, a zahiri a nutsen sa yake kamar babu wani abu amma kuma a badini shi kadai ya san luguden da ake a girkinsa, kiran sallar magriba ne ya fito dasu, kasancewar akwai masallaci a daidai saitin gidan, nan suka nufa suna hira cike da raha kamar sun jima da sanin junan su, hakan ya dan kwantar masa da hankali har ya samu kwarin guiwar daura alwala suka bi bayan su. Ana idar da sallah Abba dama yayi wa limamin magana tun kafin a tayar, dan haka ana idarwa ya bada sanarwar daurin auren Asma'un, kallon kallon Abdallah ya dinga yi yana bin mutanen cikin masallaci da kallo, fit ya tashi ya fice MD ya bi bayan sa da sauri, akan kunnen su akayi siga da komai, Alhaji Muktar ya bada sadaki naira dubu dari biyu, anan take aka daura auren Abdallah da Asma'u. Rungume shi MD yayi yana furta Alhamdulillah, shi kuwa gogan sai ya rasa in da zai saka kansa, ya dinga jujjuayashi yana mamakin yadda al'amarin ya kasance. Wajen su, su Baba Alhaji suka nufo, ya mika ma Abdallah hannu alamun su gaisa, a kunyace ya mika masa ya rik'e shi cikin nasa yana murmushi "Congratulations my son. In sha Allah kayi sa'ar mata." "Baba..." Ya fad'a yana shiga jikinsa ya rungume shi, bayan sa ya bubbuga cike da zolaya yace "Abuyan MD ya girma." Dariya suka saka a tare su Alhaji Muktar suka karaso, suka bashi hannu suma dukka sannan suka yi masa Allah sanya alkhair, wani iri yake jin sa kamar wanda iska zata dauke tayi sama dashi "Mahaifin ta ya roki a basu sati biyu kafin ta tare, ganin yanayin yadda auren ya kasance." "Ba komai, mutum na gari me cike da karamci, naji dadin yabon da ya samu dashi da yarinyar, shiyasa ma ban yi k'asa a guiwa ba, wajen ganin Abdallah na ya mallake ta, ina fatan ta zamar masa sanyin idaniya kamar yadda mahaifiyar sa ta zamar min." "In sha Allah." Suka amsa a tare, MD sai rawar jiki yake kamar mazari, shine nan shine chan kamar ya taka rawa, har mota suka rasa su Baba Alhajjn Abba yazo suka sake sallama da yiwa juna murna da fatan alkairi, suna tafiya Hajiya Mama na zuwa ita da Nadeeya a gigice, Nadeeya ce take tukin, Hajiyan ta kasa nutsuwa tunda Abban ya kirata yace zai daura ma Asma'u aure, bata san nan Adam din ya taho ba, yake dai gida ya samu Fido ya nada mata mugun duka sannan yayi ficewar sa, Ashe nan ya taho tana ta kiransa a waya sai Nadeeya ce tazo ta duba Fido din ta bata magani, yanzu haka sun baro ta tare da kawarta Faiza dan har targade yayi mata. Duk abinda ake da maganar auren har da daura auren Adam be sani ba sani ba dan bacci yake sosai a dakin Abbati saboda cewa yayi ba zai tafi ba, kuma duk alamu sun nuna baya hayyacin sa shiyasa Abba yace su kaishi dakin Abbatin kafin ya dawo hayyacin nasa, ita kanta uwar gayyar Asma'u bata san wainar da ake toyawa ba, tana kan abun sallah tana tilawar alkur'ani me girma, umma ma Umar ne ya shigo bayan sun zo yace mata manyan baki ne suka zo wajen Abban sai kuma sanarwar da taji daga masallaci duk da loudspeaker din bata da kara sosai kwana biyu matsala take basu dan haka ba kowa ne zai ji ba. A gigice Adam din ya farka kasancewar ba kwanciya bace ta dadi abinda yasha ne yaci karfin sa ya saka shi baccin dole, Hajiya Mama ya gani a kansa tana sharar hawaye tausayin sa sosai takeji musamman da taji cewa an daura auren Asma'un, tasan zai yi hauka sosai, gaba daya ya zama wani iri, "Mah... Zasu barni naga Asma'u? Dan Allah kice tayi hakuri wallahi ba zan sake bata mata rai ba." "Adam me kake so ka maida kanka? Kana da hankali kuwa?" "Baki kawai zaki saka wallahi zasuyi hakuri, kar su bata wannan da yazo, ni nafi shi chanchanta." "Ka tashi mu tafi gida, wannan ba ita ce rayuwar ka ba?" "Idan na tafi zaki kawo ta? Zaki basu hakuri su sake bani aurenta?" Gida mishi kai tayi tana kauda kanta gefe, ya mike da k'yar yana tangadi kamar zai fadi, ta rik'e shi Amma sai ya zame hannun sa yayi gaba ta bishi da sauri, duk su Abba suna tsaye a tsakar gidan suka fito, ya isa gaban Abban ya durkusa "Abba kayi hakuri." "Ba komai Adam, tashi." Tashi yayi, yayi hanyar fita Nadeeya da Mama suka bishi da sauri, kafin su karasa har ya shiga mota ya kwanta a bayan motar, zuciyar sa zafi take masa kamar zata ballo ta fito, ga wani matsanancin ciwon kai da ya addabe shi, har baya iya bud'e idon sa sosai. Abdallah na tsaye jikin mota shi da MD da yake waya suka fito akan idon sa suka tafi, wayar sa ya zaro ya aika mata da text message "I love you." Sai ya kashe wayar ya zura ta a aljihu ya daga kansa sama, yana kirga yawan taurarin da suke sararin samaniya. Umar ne ya dawo yace su shigo ciki, dan dama tafiyar su Adam din suke jira, da hannu MD yayi masa alamar yaje zai zo, yayi gaba yana jin iska na kada shi, Asma'u dake daki umma tace ta fito, ta tashi tana nannade sallayar da take kai, ta bud'e dakin ta fito, hannun ta umma ta kama zuwa dakin ta, ta dauko wani turare me kamshin gaske ta fesa mata sannan tace taje tana da bako , bata ce komai ba ta fita, a ranta tana ayyana waye?. A daf da kofar da zata shigo ya tsaya, ya kura wa kofar ido kamar ba zata fito ba, sanyayyan kamshin turaren ta ya iso masa tun kafin ta karasa shigowa, tana bud'e labulen ta ganshi a tsaye, ya bud'e hannun sa baki daya, yana mata wani irin mayatataccen kallo, bata yi aune ba sai ji tayi ya rungume ta tsam a jikin sa. Page 31 RM Hafsat Rano ***Kokarin kwace kanta tayi, ya sake matse ta sosai kamar za'a kwace masa ita, jikinta ne ya hau rawa kamar mazari, ta saka karfi sosai ta ture shi,dan ita bata san duk abinda yake faruwa ba. "Bana so." Tace masa tana ware masa idonta sosai, bakin ta ya tsuke kalar tsiwa dan babu abinda ta tsana a rayuwar ta kamar irin wannan rayuwar yanzu da samari da yanmta sukeyi. Murmushi ne ya kufce masa ya saka hannun sa ya sake jawota da karfi ya matse ta gagam yadda ba zata iya kwacewa ba, ya zagaye ta da hannayensa masu taushi yana shakar kamshin jikin ta, kuka ta fashe masa dashi dan ganin abun nasa ya wuce gona da iri, ta dinga kokarin kwacewa amma sam ya hanata, be san me ya hau kansa ba, ji yake kamar idan ya cikata zata barshi, ga wani irin bugawa da zuciyar sa take kamar zata fito waje. Sautin kukan ta a hankali na shiga cikin kunnen sa, duk da haka be sake ta ba, sai da bugun zuciyar sa ta daidaita, sannan ya cikata yana matsawa baya, ta juya da sauri zata bar dakin, ya riko ta da hanzari "Karka kara tabani dan ni ba yar iska bace." "I'm so sorry ba zan kara ba." Ya kama kunnen sa ya rik'e yana so ya saka kwayar idon sa a cikin tata, rasa abinda zatayi tayi, kawai tayi shiru tana duban kasa, dan ta fad'a masa ita bazawara ce shine zai rungume ta kenan, mutane da yawa irin kallon da suke ma wadanda sukayi aure suka fito kenan, shiyasa ko mazan sun zo wajen su sai su bisu da maganar banza, bata zaci haka daga gareshi ba, amma kuma idan ta tuna duk mazan halin su daya, ba ka iya gane musu sai kawai ta sallama. Knocking akayi, kafin ya turo ya shigo hade da sallama. "Amaryar mu." "Uhumm." Tace tana sake yin kicin kicin da fuska dan ta lura ma bakin su daya "Kinga yadda abu ya kasance ko? Al'amarin Allah kenan, babu yadda bata kasancewa. " " Allah ya bada zaman lafiya da zuria dayyiba, I can't wait na ga na zama daddy wallahi, woo wa yaga Daddy Mudan. " Harara Abdallah ya watsa masa yana rik'e kansa, surutun MD yayi yawa wallahi, a duhu ya sakata Dan bata fuskanci komai a maganar tasa ba,tunani ta shiga yi, ta tuna dazu wajen magriba Abba ya shigo ya sameta, ya tambaye ta idan har ta amince da Abdallan, tace masa eh, daga nan ya fice da sauri bayan yace wa Umma yana zuwa da bayani. Bata kaao komai ba, ganin basu dade da tafiya ba, daga nan kuma ta shiga sabgar gabanta dan bata ma fito ba saboda Adam yana nan. Muryar MD ta katse mata tunanin ta, ta kuma kara tabbatar mata da abinda take tunani ya faru "Zamu shirya duk events din a satin sama in sha Allah, komai ake bukata ni za'a tambaya, please." "Yayi toh, can you please excuse us?" "Why not? Idan ma cewa kayi na tafi gaba daya anan zaka kwana kaga lafiya lou, idan kuma kayan ka ma zan kwaso maka ayi duk shirye shiryen kana nan shima daidai ne." Kunya maganar ta bashi, yayi masa banza yana masa kallon zaka sani, shi dai MD dariya kawai yake yi , ita kuma Asma'u tsabar shiga ruduni ta gaza cewa komai, idan har maganganun MD din gaske ne, kenan aure aka daura mata da Abdallan, ji tayi kafafun ta sun mata nauyi, taji tana bukatar ta zauna dan har yar rawa jikin ta ya dinga yi, a wajen ta durkushe MD na fita, yayi saurin zuwa ya durkusa akan guiwoyin sa yana rik'e hannun ta "Me yake damun ki!? Baki da lafiya? Wani abun ne?" Girgiza masa kai tayi, ya sauke ajiyar zuciya yana sakin hannun ta da ya tuna tace masa bata so, kasa kallon sa tayi, ta dinga jujjuya maganganun a ranta, ba zata ja da hukuncin Allah ba, ba kuma zata bijire masa a duka abinda ya zaba mata ba, zata karbi duk wani zabi da hannu bibiyu, hzd ehakan ta tabbata yana cikin kaddarar ta, babu wanda ya sake magana a cikin su, tana durkushe a wajen shi kuma yana tsaye kyam a kanta yana nazartar yanayin ta, be san a wanne matsayi ta ajiye shi ba, dan yana ji da ganin kamar ba'a kyauta mata ba, kamar an mata garaje da ba'a barta ta tantance shi sosai ba, duk da yasan hakan ba zai zama matsala ba,kuma hakan zabin Allah ne. Mikewa tayi bayan ta dau lokaci a durkushe sannan tace "Kayi hakuri." Be san hakurin me take bashi ba, amma sai ya samu kansa da jin dadi, ya daga mata gira yana sakar masa tsadadden murmushin sa, maida masa tayi tana sunne kanta k'asa kunyar shi na ratsa ta, "Zo ki zauna." Yace mata yana nuna mata gefen sa bayan ya zauna, ba musu ta karasa a nutse ta zauna da dan tazara kad'an a tsakanin su, matsowa yayi ya jone da jikinta har kafadarta tana gogar tasa, hannun ta ya lalubo ya rik'e cikin nasa yana dan murza su a hankali, yanayin bugawar zuciyar ta ya sauya nan take, ta dinga jin wani irin yanayi da bata taba fuskantar sa ba. Ta zata wata magana xasuyi amma sai taji shiru har ta dago da niyyar ganin abinda yake amma sai taga kawai ita yake kallo kuri, duk sai taji kunya amma shi ko a kwalar rigar sa., Sai ma sake tsattsareta da yayi yana kokarin lallai sai ya saka idon shi cikin nata, sun jima a haka kafin yayi ta maza ya daure ya cikata yana mikewa "Bana so na tafi, but i have to, kar Abba yaga rashin hakuri na." Shafa kansa yayi ya mikar da hannun sa zuwa gareta, ya mikar da ita tsaye suna fuskantar juna "My wife." Ya kawo fuskarsa daidai tata ta hanyar rage tsawon sa, dan tsaf zai sakata a cikin rigar sa ya boye ta, dago idon ta, tayi da niyyar kallon sa, sai yaga kamar tayi masa fari, wani yarrr yaji tun daga kansa zuwa tafin kafarsa, bakin sa ya kai kuncin ta s kasalance ya manna mata kiss, ta duka da sauri tana damke idon ta "Ki kula min da kanki kinji?" Bata iya amsawa ba sai daga kai da tayi alamar toh, cikin sakannin da basu gaza goma ba ya fice fit daga falon dan abinda yake ji zai iya sashi aikata abun kunya. Yana fita ya tarar da driver yana jiran sa, MD ya tafi shine ya kirashi yazo ya dauke shi, babu bata lokaci ya fad'a bayan motar ya ja suka bar layin. Tamkar wadda aka dasa a wajen haka ta kasa ko da daga kafarta ne, wani feeling me matukar dadi ya dinga mata yawo, soyayyar sa me sanyi da tsayawa a rai, bata taba experiencing hakan ba, baa taba nuna mata so irin haka ba, shiyasa take jin ta kamar wata bakuwa, kamar wadda aka chanja ta da wata ta daban. Da k'yar ta ja kafafunta zuwa cikin gidan nasu, kunyar Umma da Abba na sake dabaibaye ta. Idon Umma fes akanta ta shigo, sai taga kamar umman ta kara mata haske akan hasken ta da ta Santa dashi, bata sani ba ko tsantsar farin cikin da ta hanga a cikin idon ta ne ya sakata ganin farin nata ba, zuwa tayi ta zauna a gefen Umman tana jan mayafin jikinta ta sauke shi k'asa. "Umma ina Abba?" "Ya fita sallah, inaga ko ya tsaya wajensu liman." Sai kawai ta fad'a jikin Umma, ta dora kanta a kafar umman ta runtse idon ta, tana tariyo abinda ya faru yanzu. "Nasan ba dan dare ba, babu abinda zai hana yan uwanki zuwa, amma nasan gobe da wuri zaki gansu, dan duk munyi waya kowa murna wallahi." "Umma wai ya akayi haka ta kasance?" "Al'amarin Allah fa, ke dai ki bar sha'anin aure wallahi." Maida idon ta, tayi ta kulle tana jin yadda Umman take yabon abun, tana kuma kwararo addu'ar dacewar Asma'un da fatan nasara a komai ma, a ranta take amsa amin, tana saka ram samun nutsuwa da Abdallan, wanda a yanzu take jin kamar ya karbe rashin ta ya tafi dashi, kamar akwai wani gagarumin abu da take jin tana kewa. Daina jin maganar Umman tayi sai sama-sama, ta fad'a tunanin shi da hoton fuskar sa, sajen sa da quarter million dinsa shi yafi komai tafiya da ita. Samun kanta tayi tana murmusawa, ta mike daga kan kafar Umman ta fad'a daki yadda zata more tunanin shi sosai ba tare da wani abu ya katse ta ba, wayarta ta jawo da nufin kiran Rauda ta tarar da missed calls da yawa sai text message dinsa guda biyu, budewa tayi tana fadawa saman gadon idon ta kyam akan wayar dadin kamalan na ratsa ta _"The first time we met, I can see that you and i are meant to be together... Your eyes were so gentle, your smile so true... You walked lightly into my heart, captivating and lovely to my mind. For you are my heart, my soul and my oneness. With you i know that I will find my completeness,my eternal peace of mind. You are the one I want to spend my life with. Both of our hearts will forever bond into all happiness, falls, pains and sorrows. I promise together we will meet tomorrow. I love you so much my wife."_ # Juyi ta dinga yi a saman gadon ita kadai kalamansa na ratsa ta, wayar da ke saman kirjinta ta yi kara, ta dan zabura kadan dan tayi nisa a tunanin, Rauda ce, dagawa tayi cike da zakuwa tace " Rauda." " Wayyo...Yaa Asma'u." "Wallahi da k'yar zan iya bacci yau, kinji yadda nake ji kuwa? Farin ciki kamar na ganni a gida wallahi,dan ma Umma tace kar muzo ne da tuni nazo " " Yau da goben duk daya ai, idan da rai da lafiya." " Haka ne,ya kika ji? Nasan ya hadu ba karya wallahi, irin wanda ya dace dake ba wanchan ya Adam din ba, fari kamar farin kosai. " " Ke ko? " " Allah kuwa, dan Allah kice ina gaishe shi da kyau da kyau, da wuri zan faso goben nan ba zan tafi ba sai na ganshi. " " Kyaji dashi dai, kije ki kwanta ki huta kinga ba ke kadai bace. " " Tom, sai da safe.* "Yawwa, sai da safe." Tasan da wuri duk zasu zo, shiyasa ma ta katse Raudan sun hadu gobe ayi duk maganar ma da za'a yi, Hidaya ta kira nan ma sukayi magana sannan ta kira Ya Hadiza, ita ce ma suka dan dade suna magana, har ta soma mata maganar gyaran jiki da duk abubuwan da ya kamata, ita dai jin ta kawai take bata ce komai ba, daga karshe sukayi sallama tace sai tazo goben. Page 31 RM Hafsat Rano ***Kokarin kwace kanta tayi, ya sake matse ta sosai kamar za'a kwace masa ita, jikinta ne ya hau rawa kamar mazari, ta saka karfi sosai ta ture shi,dan ita bata san duk abinda yake faruwa ba. "Bana so." Tace masa tana ware masa idonta sosai, bakin ta ya tsuke kalar tsiwa dan babu abinda ta tsana a rayuwar ta kamar irin wannan rayuwar yanzu da samari da yanmta sukeyi. Murmushi ne ya kufce masa ya saka hannun sa ya sake jawota da karfi ya matse ta gagam yadda ba zata iya kwacewa ba, ya zagaye ta da hannayensa masu taushi yana shakar kamshin jikin ta, kuka ta fashe masa dashi dan ganin abun nasa ya wuce gona da iri, ta dinga kokarin kwacewa amma sam ya hanata, be san me ya hau kansa ba, ji yake kamar idan ya cikata zata barshi, ga wani irin bugawa da zuciyar sa take kamar zata fito waje. Sautin kukan ta a hankali na shiga cikin kunnen sa, duk da haka be sake ta ba, sai da bugun zuciyar sa ta daidaita, sannan ya cikata yana matsawa baya, ta juya da sauri zata bar dakin, ya riko ta da hanzari "Karka kara tabani dan ni ba yar iska bace." "I'm so sorry ba zan kara ba." Ya kama kunnen sa ya rik'e yana so ya saka kwayar idon sa a cikin tata, rasa abinda zatayi tayi, kawai tayi shiru tana duban kasa, dan ta fad'a masa ita bazawara ce shine zai rungume ta kenan, mutane da yawa irin kallon da suke ma wadanda sukayi aure suka fito kenan, shiyasa ko mazan sun zo wajen su sai su bisu da maganar banza, bata zaci haka daga gareshi ba, amma kuma idan ta tuna duk mazan halin su daya, ba ka iya gane musu sai kawai ta sallama. Knocking akayi, kafin ya turo ya shigo hade da sallama. "Amaryar mu." "Uhumm." Tace tana sake yin kicin kicin da fuska dan ta lura ma bakin su daya "Kinga yadda abu ya kasance ko? Al'amarin Allah kenan, babu yadda bata kasancewa. " " Allah ya bada zaman lafiya da zuria dayyiba, I can't wait na ga na zama daddy wallahi, woo wa yaga Daddy Mudan. " Harara Abdallah ya watsa masa yana rik'e kansa, surutun MD yayi yawa wallahi, a duhu ya sakata Dan bata fuskanci komai a maganar tasa ba,tunani ta shiga yi, ta tuna dazu wajen magriba Abba ya shigo ya sameta, ya tambaye ta idan har ta amince da Abdallan, tace masa eh, daga nan ya fice da sauri bayan yace wa Umma yana zuwa da bayani. Bata kaao komai ba, ganin basu dade da tafiya ba, daga nan kuma ta shiga sabgar gabanta dan bata ma fito ba saboda Adam yana nan. Muryar MD ta katse mata tunanin ta, ta kuma kara tabbatar mata da abinda take tunani ya faru "Zamu shirya duk events din a satin sama in sha Allah, komai ake bukata ni za'a tambaya, please." "Yayi toh, can you please excuse us?" "Why not? Idan ma cewa kayi na tafi gaba daya anan zaka kwana kaga lafiya lou, idan kuma kayan ka ma zan kwaso maka ayi duk shirye shiryen kana nan shima daidai ne." Kunya maganar ta bashi, yayi masa banza yana masa kallon zaka sani, shi dai MD dariya kawai yake yi , ita kuma Asma'u tsabar shiga ruduni ta gaza cewa komai, idan har maganganun MD din gaske ne, kenan aure aka daura mata da Abdallan, ji tayi kafafun ta sun mata nauyi, taji tana bukatar ta zauna dan har yar rawa jikin ta ya dinga yi, a wajen ta durkushe MD na fita, yayi saurin zuwa ya durkusa akan guiwoyin sa yana rik'e hannun ta "Me yake damun ki!? Baki da lafiya? Wani abun ne?" Girgiza masa kai tayi, ya sauke ajiyar zuciya yana sakin hannun ta da ya tuna tace masa bata so, kasa kallon sa tayi, ta dinga jujjuya maganganun a ranta, ba zata ja da hukuncin Allah ba, ba kuma zata bijire masa a duka abinda ya zaba mata ba, zata karbi duk wani zabi da hannu bibiyu, hzd ehakan ta tabbata yana cikin kaddarar ta, babu wanda ya sake magana a cikin su, tana durkushe a wajen shi kuma yana tsaye kyam a kanta yana nazartar yanayin ta, be san a wanne matsayi ta ajiye shi ba, dan yana ji da ganin kamar ba'a kyauta mata ba, kamar an mata garaje da ba'a barta ta tantance shi sosai ba, duk da yasan hakan ba zai zama matsala ba,kuma hakan zabin Allah ne. Mikewa tayi bayan ta dau lokaci a durkushe sannan tace "Kayi hakuri." Be san hakurin me take bashi ba, amma sai ya samu kansa da jin dadi, ya daga mata gira yana sakar masa tsadadden murmushin sa, maida masa tayi tana sunne kanta k'asa kunyar shi na ratsa ta, "Zo ki zauna." Yace mata yana nuna mata gefen sa bayan ya zauna, ba musu ta karasa a nutse ta zauna da dan tazara kad'an a tsakanin su, matsowa yayi ya jone da jikinta har kafadarta tana gogar tasa, hannun ta ya lalubo ya rik'e cikin nasa yana dan murza su a hankali, yanayin bugawar zuciyar ta ya sauya nan take, ta dinga jin wani irin yanayi da bata taba fuskantar sa ba. Ta zata wata magana xasuyi amma sai taji shiru har ta dago da niyyar ganin abinda yake amma sai taga kawai ita yake kallo kuri, duk sai taji kunya amma shi ko a kwalar rigar sa., Sai ma sake tsattsareta da yayi yana kokarin lallai sai ya saka idon shi cikin nata, sun jima a haka kafin yayi ta maza ya daure ya cikata yana mikewa "Bana so na tafi, but i have to, kar Abba yaga rashin hakuri na." Shafa kansa yayi ya mikar da hannun sa zuwa gareta, ya mikar da ita tsaye suna fuskantar juna "My wife." Ya kawo fuskarsa daidai tata ta hanyar rage tsawon sa, dan tsaf zai sakata a cikin rigar sa ya boye ta, dago idon ta, tayi da niyyar kallon sa, sai yaga kamar tayi masa fari, wani yarrr yaji tun daga kansa zuwa tafin kafarsa, bakin sa ya kai kuncin ta s kasalance ya manna mata kiss, ta duka da sauri tana damke idon ta "Ki kula min da kanki kinji?" Bata iya amsawa ba sai daga kai da tayi alamar toh, cikin sakannin da basu gaza goma ba ya fice fit daga falon dan abinda yake ji zai iya sashi aikata abun kunya. Yana fita ya tarar da driver yana jiran sa, MD ya tafi shine ya kirashi yazo ya dauke shi, babu bata lokaci ya fad'a bayan motar ya ja suka bar layin. Tamkar wadda aka dasa a wajen haka ta kasa ko da daga kafarta ne, wani feeling me matukar dadi ya dinga mata yawo, soyayyar sa me sanyi da tsayawa a rai, bata taba experiencing hakan ba, baa taba nuna mata so irin haka ba, shiyasa take jin ta kamar wata bakuwa, kamar wadda aka chanja ta da wata ta daban. Da k'yar ta ja kafafunta zuwa cikin gidan nasu, kunyar Umma da Abba na sake dabaibaye ta. Idon Umma fes akanta ta shigo, sai taga kamar umman ta kara mata haske akan hasken ta da ta Santa dashi, bata sani ba ko tsantsar farin cikin da ta hanga a cikin idon ta ne ya sakata ganin farin nata ba, zuwa tayi ta zauna a gefen Umman tana jan mayafin jikinta ta sauke shi k'asa. "Umma ina Abba?" "Ya fita sallah, inaga ko ya tsaya wajensu liman." Sai kawai ta fad'a jikin Umma, ta dora kanta a kafar umman ta runtse idon ta, tana tariyo abinda ya faru yanzu. "Nasan ba dan dare ba, babu abinda zai hana yan uwanki zuwa, amma nasan gobe da wuri zaki gansu, dan duk munyi waya kowa murna wallahi." "Umma wai ya akayi haka ta kasance?" "Al'amarin Allah fa, ke dai ki bar sha'anin aure wallahi." Maida idon ta, tayi ta kulle tana jin yadda Umman take yabon abun, tana kuma kwararo addu'ar dacewar Asma'un da fatan nasara a komai ma, a ranta take amsa amin, tana saka ram samun nutsuwa da Abdallan, wanda a yanzu take jin kamar ya karbe rashin ta ya tafi dashi, kamar akwai wani gagarumin abu da take jin tana kewa. Daina jin maganar Umman tayi sai sama-sama, ta fad'a tunanin shi da hoton fuskar sa, sajen sa da quarter million dinsa shi yafi komai tafiya da ita. Samun kanta tayi tana murmusawa, ta mike daga kan kafar Umman ta fad'a daki yadda zata more tunanin shi sosai ba tare da wani abu ya katse ta ba, wayarta ta jawo da nufin kiran Rauda ta tarar da missed calls da yawa sai text message dinsa guda biyu, budewa tayi tana fadawa saman gadon idon ta kyam akan wayar dadin kamalan na ratsa ta _"The first time we met, I can see that you and i are meant to be together... Your eyes were so gentle, your smile so true... You walked lightly into my heart, captivating and lovely to my mind. For you are my heart, my soul and my oneness. With you i know that I will find my completeness,my eternal peace of mind. You are the one I want to spend my life with. Both of our hearts will forever bond into all happiness, falls, pains and sorrows. I promise together we will meet tomorrow. I love you so much my wife."_ # Juyi ta dinga yi a saman gadon ita kadai kalamansa na ratsa ta, wayar da ke saman kirjinta ta yi kara, ta dan zabura kadan dan tayi nisa a tunanin, Rauda ce, dagawa tayi cike da zakuwa tace " Rauda." " Wayyo...Yaa Asma'u." "Wallahi da k'yar zan iya bacci yau, kinji yadda nake ji kuwa? Farin ciki kamar na ganni a gida wallahi,dan ma Umma tace kar muzo ne da tuni nazo " " Yau da goben duk daya ai, idan da rai da lafiya." " Haka ne,ya kika ji? Nasan ya hadu ba karya wallahi, irin wanda ya dace dake ba wanchan ya Adam din ba, fari kamar farin kosai. " " Ke ko? " " Allah kuwa, dan Allah kice ina gaishe shi da kyau da kyau, da wuri zan faso goben nan ba zan tafi ba sai na ganshi. " " Kyaji dashi dai, kije ki kwanta ki huta kinga ba ke kadai bace. " " Tom, sai da safe.* "Yawwa, sai da safe." Tasan da wuri duk zasu zo, shiyasa ma ta katse Raudan sun hadu gobe ayi duk maganar ma da za'a yi, Hidaya ta kira nan ma sukayi magana sannan ta kira Ya Hadiza, ita ce ma suka dan dade suna magana, har ta soma mata maganar gyaran jiki da duk abubuwan da ya kamata, ita dai jin ta kawai take bata ce komai ba, daga karshe sukayi sallama tace sai tazo goben. Page 31 RM Hafsat Rano ***Kokarin kwace kanta tayi, ya sake matse ta sosai kamar za'a kwace masa ita, jikinta ne ya hau rawa kamar mazari, ta saka karfi sosai ta ture shi,dan ita bata san duk abinda yake faruwa ba. "Bana so." Tace masa tana ware masa idonta sosai, bakin ta ya tsuke kalar tsiwa dan babu abinda ta tsana a rayuwar ta kamar irin wannan rayuwar yanzu da samari da yanmta sukeyi. Murmushi ne ya kufce masa ya saka hannun sa ya sake jawota da karfi ya matse ta gagam yadda ba zata iya kwacewa ba, ya zagaye ta da hannayensa masu taushi yana shakar kamshin jikin ta, kuka ta fashe masa dashi dan ganin abun nasa ya wuce gona da iri, ta dinga kokarin kwacewa amma sam ya hanata, be san me ya hau kansa ba, ji yake kamar idan ya cikata zata barshi, ga wani irin bugawa da zuciyar sa take kamar zata fito waje. Sautin kukan ta a hankali na shiga cikin kunnen sa, duk da haka be sake ta ba, sai da bugun zuciyar sa ta daidaita, sannan ya cikata yana matsawa baya, ta juya da sauri zata bar dakin, ya riko ta da hanzari "Karka kara tabani dan ni ba yar iska bace." "I'm so sorry ba zan kara ba." Ya kama kunnen sa ya rik'e yana so ya saka kwayar idon sa a cikin tata, rasa abinda zatayi tayi, kawai tayi shiru tana duban kasa, dan ta fad'a masa ita bazawara ce shine zai rungume ta kenan, mutane da yawa irin kallon da suke ma wadanda sukayi aure suka fito kenan, shiyasa ko mazan sun zo wajen su sai su bisu da maganar banza, bata zaci haka daga gareshi ba, amma kuma idan ta tuna duk mazan halin su daya, ba ka iya gane musu sai kawai ta sallama. Knocking akayi, kafin ya turo ya shigo hade da sallama. "Amaryar mu." "Uhumm." Tace tana sake yin kicin kicin da fuska dan ta lura ma bakin su daya "Kinga yadda abu ya kasance ko? Al'amarin Allah kenan, babu yadda bata kasancewa. " " Allah ya bada zaman lafiya da zuria dayyiba, I can't wait na ga na zama daddy wallahi, woo wa yaga Daddy Mudan. " Harara Abdallah ya watsa masa yana rik'e kansa, surutun MD yayi yawa wallahi, a duhu ya sakata Dan bata fuskanci komai a maganar tasa ba,tunani ta shiga yi, ta tuna dazu wajen magriba Abba ya shigo ya sameta, ya tambaye ta idan har ta amince da Abdallan, tace masa eh, daga nan ya fice da sauri bayan yace wa Umma yana zuwa da bayani. Bata kaao komai ba, ganin basu dade da tafiya ba, daga nan kuma ta shiga sabgar gabanta dan bata ma fito ba saboda Adam yana nan. Muryar MD ta katse mata tunanin ta, ta kuma kara tabbatar mata da abinda take tunani ya faru "Zamu shirya duk events din a satin sama in sha Allah, komai ake bukata ni za'a tambaya, please." "Yayi toh, can you please excuse us?" "Why not? Idan ma cewa kayi na tafi gaba daya anan zaka kwana kaga lafiya lou, idan kuma kayan ka ma zan kwaso maka ayi duk shirye shiryen kana nan shima daidai ne." Kunya maganar ta bashi, yayi masa banza yana masa kallon zaka sani, shi dai MD dariya kawai yake yi , ita kuma Asma'u tsabar shiga ruduni ta gaza cewa komai, idan har maganganun MD din gaske ne, kenan aure aka daura mata da Abdallan, ji tayi kafafun ta sun mata nauyi, taji tana bukatar ta zauna dan har yar rawa jikin ta ya dinga yi, a wajen ta durkushe MD na fita, yayi saurin zuwa ya durkusa akan guiwoyin sa yana rik'e hannun ta "Me yake damun ki!? Baki da lafiya? Wani abun ne?" Girgiza masa kai tayi, ya sauke ajiyar zuciya yana sakin hannun ta da ya tuna tace masa bata so, kasa kallon sa tayi, ta dinga jujjuya maganganun a ranta, ba zata ja da hukuncin Allah ba, ba kuma zata bijire masa a duka abinda ya zaba mata ba, zata karbi duk wani zabi da hannu bibiyu, hzd ehakan ta tabbata yana cikin kaddarar ta, babu wanda ya sake magana a cikin su, tana durkushe a wajen shi kuma yana tsaye kyam a kanta yana nazartar yanayin ta, be san a wanne matsayi ta ajiye shi ba, dan yana ji da ganin kamar ba'a kyauta mata ba, kamar an mata garaje da ba'a barta ta tantance shi sosai ba, duk da yasan hakan ba zai zama matsala ba,kuma hakan zabin Allah ne. Mikewa tayi bayan ta dau lokaci a durkushe sannan tace "Kayi hakuri." Be san hakurin me take bashi ba, amma sai ya samu kansa da jin dadi, ya daga mata gira yana sakar masa tsadadden murmushin sa, maida masa tayi tana sunne kanta k'asa kunyar shi na ratsa ta, "Zo ki zauna." Yace mata yana nuna mata gefen sa bayan ya zauna, ba musu ta karasa a nutse ta zauna da dan tazara kad'an a tsakanin su, matsowa yayi ya jone da jikinta har kafadarta tana gogar tasa, hannun ta ya lalubo ya rik'e cikin nasa yana dan murza su a hankali, yanayin bugawar zuciyar ta ya sauya nan take, ta dinga jin wani irin yanayi da bata taba fuskantar sa ba. Ta zata wata magana xasuyi amma sai taji shiru har ta dago da niyyar ganin abinda yake amma sai taga kawai ita yake kallo kuri, duk sai taji kunya amma shi ko a kwalar rigar sa., Sai ma sake tsattsareta da yayi yana kokarin lallai sai ya saka idon shi cikin nata, sun jima a haka kafin yayi ta maza ya daure ya cikata yana mikewa "Bana so na tafi, but i have to, kar Abba yaga rashin hakuri na." Shafa kansa yayi ya mikar da hannun sa zuwa gareta, ya mikar da ita tsaye suna fuskantar juna "My wife." Ya kawo fuskarsa daidai tata ta hanyar rage tsawon sa, dan tsaf zai sakata a cikin rigar sa ya boye ta, dago idon ta, tayi da niyyar kallon sa, sai yaga kamar tayi masa fari, wani yarrr yaji tun daga kansa zuwa tafin kafarsa, bakin sa ya kai kuncin ta s kasalance ya manna mata kiss, ta duka da sauri tana damke idon ta "Ki kula min da kanki kinji?" Bata iya amsawa ba sai daga kai da tayi alamar toh, cikin sakannin da basu gaza goma ba ya fice fit daga falon dan abinda yake ji zai iya sashi aikata abun kunya. Yana fita ya tarar da driver yana jiran sa, MD ya tafi shine ya kirashi yazo ya dauke shi, babu bata lokaci ya fad'a bayan motar ya ja suka bar layin. Tamkar wadda aka dasa a wajen haka ta kasa ko da daga kafarta ne, wani feeling me matukar dadi ya dinga mata yawo, soyayyar sa me sanyi da tsayawa a rai, bata taba experiencing hakan ba, baa taba nuna mata so irin haka ba, shiyasa take jin ta kamar wata bakuwa, kamar wadda aka chanja ta da wata ta daban. Da k'yar ta ja kafafunta zuwa cikin gidan nasu, kunyar Umma da Abba na sake dabaibaye ta. Idon Umma fes akanta ta shigo, sai taga kamar umman ta kara mata haske akan hasken ta da ta Santa dashi, bata sani ba ko tsantsar farin cikin da ta hanga a cikin idon ta ne ya sakata ganin farin nata ba, zuwa tayi ta zauna a gefen Umman tana jan mayafin jikinta ta sauke shi k'asa. "Umma ina Abba?" "Ya fita sallah, inaga ko ya tsaya wajensu liman." Sai kawai ta fad'a jikin Umma, ta dora kanta a kafar umman ta runtse idon ta, tana tariyo abinda ya faru yanzu. "Nasan ba dan dare ba, babu abinda zai hana yan uwanki zuwa, amma nasan gobe da wuri zaki gansu, dan duk munyi waya kowa murna wallahi." "Umma wai ya akayi haka ta kasance?" "Al'amarin Allah fa, ke dai ki bar sha'anin aure wallahi." Maida idon ta, tayi ta kulle tana jin yadda Umman take yabon abun, tana kuma kwararo addu'ar dacewar Asma'un da fatan nasara a komai ma, a ranta take amsa amin, tana saka ram samun nutsuwa da Abdallan, wanda a yanzu take jin kamar ya karbe rashin ta ya tafi dashi, kamar akwai wani gagarumin abu da take jin tana kewa. Daina jin maganar Umman tayi sai sama-sama, ta fad'a tunanin shi da hoton fuskar sa, sajen sa da quarter million dinsa shi yafi komai tafiya da ita. Samun kanta tayi tana murmusawa, ta mike daga kan kafar Umman ta fad'a daki yadda zata more tunanin shi sosai ba tare da wani abu ya katse ta ba, wayarta ta jawo da nufin kiran Rauda ta tarar da missed calls da yawa sai text message dinsa guda biyu, budewa tayi tana fadawa saman gadon idon ta kyam akan wayar dadin kamalan na ratsa ta _"The first time we met, I can see that you and i are meant to be together... Your eyes were so gentle, your smile so true... You walked lightly into my heart, captivating and lovely to my mind. For you are my heart, my soul and my oneness. With you i know that I will find my completeness,my eternal peace of mind. You are the one I want to spend my life with. Both of our hearts will forever bond into all happiness, falls, pains and sorrows. I promise together we will meet tomorrow. I love you so much my wife."_ # Juyi ta dinga yi a saman gadon ita kadai kalamansa na ratsa ta, wayar da ke saman kirjinta ta yi kara, ta dan zabura kadan dan tayi nisa a tunanin, Rauda ce, dagawa tayi cike da zakuwa tace " Rauda." " Wayyo...Yaa Asma'u." "Wallahi da k'yar zan iya bacci yau, kinji yadda nake ji kuwa? Farin ciki kamar na ganni a gida wallahi,dan ma Umma tace kar muzo ne da tuni nazo " " Yau da goben duk daya ai, idan da rai da lafiya." " Haka ne,ya kika ji? Nasan ya hadu ba karya wallahi, irin wanda ya dace dake ba wanchan ya Adam din ba, fari kamar farin kosai. " " Ke ko? " " Allah kuwa, dan Allah kice ina gaishe shi da kyau da kyau, da wuri zan faso goben nan ba zan tafi ba sai na ganshi. " " Kyaji dashi dai, kije ki kwanta ki huta kinga ba ke kadai bace. " " Tom, sai da safe.* "Yawwa, sai da safe." Tasan da wuri duk zasu zo, shiyasa ma ta katse Raudan sun hadu gobe ayi duk maganar ma da za'a yi, Hidaya ta kira nan ma sukayi magana sannan ta kira Ya Hadiza, ita ce ma suka dan dade suna magana, har ta soma mata maganar gyaran jiki da duk abubuwan da ya kamata, ita dai jin ta kawai take bata ce komai ba, daga karshe sukayi sallama tace sai tazo goben. Page 31 RM Hafsat Rano ***Kokarin kwace kanta tayi, ya sake matse ta sosai kamar za'a kwace masa ita, jikinta ne ya hau rawa kamar mazari, ta saka karfi sosai ta ture shi,dan ita bata san duk abinda yake faruwa ba. "Bana so." Tace masa tana ware masa idonta sosai, bakin ta ya tsuke kalar tsiwa dan babu abinda ta tsana a rayuwar ta kamar irin wannan rayuwar yanzu da samari da yanmta sukeyi. Murmushi ne ya kufce masa ya saka hannun sa ya sake jawota da karfi ya matse ta gagam yadda ba zata iya kwacewa ba, ya zagaye ta da hannayensa masu taushi yana shakar kamshin jikin ta, kuka ta fashe masa dashi dan ganin abun nasa ya wuce gona da iri, ta dinga kokarin kwacewa amma sam ya hanata, be san me ya hau kansa ba, ji yake kamar idan ya cikata zata barshi, ga wani irin bugawa da zuciyar sa take kamar zata fito waje. Sautin kukan ta a hankali na shiga cikin kunnen sa, duk da haka be sake ta ba, sai da bugun zuciyar sa ta daidaita, sannan ya cikata yana matsawa baya, ta juya da sauri zata bar dakin, ya riko ta da hanzari "Karka kara tabani dan ni ba yar iska bace." "I'm so sorry ba zan kara ba." Ya kama kunnen sa ya rik'e yana so ya saka kwayar idon sa a cikin tata, rasa abinda zatayi tayi, kawai tayi shiru tana duban kasa, dan ta fad'a masa ita bazawara ce shine zai rungume ta kenan, mutane da yawa irin kallon da suke ma wadanda sukayi aure suka fito kenan, shiyasa ko mazan sun zo wajen su sai su bisu da maganar banza, bata zaci haka daga gareshi ba, amma kuma idan ta tuna duk mazan halin su daya, ba ka iya gane musu sai kawai ta sallama. Knocking akayi, kafin ya turo ya shigo hade da sallama. "Amaryar mu." "Uhumm." Tace tana sake yin kicin kicin da fuska dan ta lura ma bakin su daya "Kinga yadda abu ya kasance ko? Al'amarin Allah kenan, babu yadda bata kasancewa. " " Allah ya bada zaman lafiya da zuria dayyiba, I can't wait na ga na zama daddy wallahi, woo wa yaga Daddy Mudan. " Harara Abdallah ya watsa masa yana rik'e kansa, surutun MD yayi yawa wallahi, a duhu ya sakata Dan bata fuskanci komai a maganar tasa ba,tunani ta shiga yi, ta tuna dazu wajen magriba Abba ya shigo ya sameta, ya tambaye ta idan har ta amince da Abdallan, tace masa eh, daga nan ya fice da sauri bayan yace wa Umma yana zuwa da bayani. Bata kaao komai ba, ganin basu dade da tafiya ba, daga nan kuma ta shiga sabgar gabanta dan bata ma fito ba saboda Adam yana nan. Muryar MD ta katse mata tunanin ta, ta kuma kara tabbatar mata da abinda take tunani ya faru "Zamu shirya duk events din a satin sama in sha Allah, komai ake bukata ni za'a tambaya, please." "Yayi toh, can you please excuse us?" "Why not? Idan ma cewa kayi na tafi gaba daya anan zaka kwana kaga lafiya lou, idan kuma kayan ka ma zan kwaso maka ayi duk shirye shiryen kana nan shima daidai ne." Kunya maganar ta bashi, yayi masa banza yana masa kallon zaka sani, shi dai MD dariya kawai yake yi , ita kuma Asma'u tsabar shiga ruduni ta gaza cewa komai, idan har maganganun MD din gaske ne, kenan aure aka daura mata da Abdallan, ji tayi kafafun ta sun mata nauyi, taji tana bukatar ta zauna dan har yar rawa jikin ta ya dinga yi, a wajen ta durkushe MD na fita, yayi saurin zuwa ya durkusa akan guiwoyin sa yana rik'e hannun ta "Me yake damun ki!? Baki da lafiya? Wani abun ne?" Girgiza masa kai tayi, ya sauke ajiyar zuciya yana sakin hannun ta da ya tuna tace masa bata so, kasa kallon sa tayi, ta dinga jujjuya maganganun a ranta, ba zata ja da hukuncin Allah ba, ba kuma zata bijire masa a duka abinda ya zaba mata ba, zata karbi duk wani zabi da hannu bibiyu, hzd ehakan ta tabbata yana cikin kaddarar ta, babu wanda ya sake magana a cikin su, tana durkushe a wajen shi kuma yana tsaye kyam a kanta yana nazartar yanayin ta, be san a wanne matsayi ta ajiye shi ba, dan yana ji da ganin kamar ba'a kyauta mata ba, kamar an mata garaje da ba'a barta ta tantance shi sosai ba, duk da yasan hakan ba zai zama matsala ba,kuma hakan zabin Allah ne. Mikewa tayi bayan ta dau lokaci a durkushe sannan tace "Kayi hakuri." Be san hakurin me take bashi ba, amma sai ya samu kansa da jin dadi, ya daga mata gira yana sakar masa tsadadden murmushin sa, maida masa tayi tana sunne kanta k'asa kunyar shi na ratsa ta, "Zo ki zauna." Yace mata yana nuna mata gefen sa bayan ya zauna, ba musu ta karasa a nutse ta zauna da dan tazara kad'an a tsakanin su, matsowa yayi ya jone da jikinta har kafadarta tana gogar tasa, hannun ta ya lalubo ya rik'e cikin nasa yana dan murza su a hankali, yanayin bugawar zuciyar ta ya sauya nan take, ta dinga jin wani irin yanayi da bata taba fuskantar sa ba. Ta zata wata magana xasuyi amma sai taji shiru har ta dago da niyyar ganin abinda yake amma sai taga kawai ita yake kallo kuri, duk sai taji kunya amma shi ko a kwalar rigar sa., Sai ma sake tsattsareta da yayi yana kokarin lallai sai ya saka idon shi cikin nata, sun jima a haka kafin yayi ta maza ya daure ya cikata yana mikewa "Bana so na tafi, but i have to, kar Abba yaga rashin hakuri na." Shafa kansa yayi ya mikar da hannun sa zuwa gareta, ya mikar da ita tsaye suna fuskantar juna "My wife." Ya kawo fuskarsa daidai tata ta hanyar rage tsawon sa, dan tsaf zai sakata a cikin rigar sa ya boye ta, dago idon ta, tayi da niyyar kallon sa, sai yaga kamar tayi masa fari, wani yarrr yaji tun daga kansa zuwa tafin kafarsa, bakin sa ya kai kuncin ta s kasalance ya manna mata kiss, ta duka da sauri tana damke idon ta "Ki kula min da kanki kinji?" Bata iya amsawa ba sai daga kai da tayi alamar toh, cikin sakannin da basu gaza goma ba ya fice fit daga falon dan abinda yake ji zai iya sashi aikata abun kunya. Yana fita ya tarar da driver yana jiran sa, MD ya tafi shine ya kirashi yazo ya dauke shi, babu bata lokaci ya fad'a bayan motar ya ja suka bar layin. Tamkar wadda aka dasa a wajen haka ta kasa ko da daga kafarta ne, wani feeling me matukar dadi ya dinga mata yawo, soyayyar sa me sanyi da tsayawa a rai, bata taba experiencing hakan ba, baa taba nuna mata so irin haka ba, shiyasa take jin ta kamar wata bakuwa, kamar wadda aka chanja ta da wata ta daban. Da k'yar ta ja kafafunta zuwa cikin gidan nasu, kunyar Umma da Abba na sake dabaibaye ta. Idon Umma fes akanta ta shigo, sai taga kamar umman ta kara mata haske akan hasken ta da ta Santa dashi, bata sani ba ko tsantsar farin cikin da ta hanga a cikin idon ta ne ya sakata ganin farin nata ba, zuwa tayi ta zauna a gefen Umman tana jan mayafin jikinta ta sauke shi k'asa. "Umma ina Abba?" "Ya fita sallah, inaga ko ya tsaya wajensu liman." Sai kawai ta fad'a jikin Umma, ta dora kanta a kafar umman ta runtse idon ta, tana tariyo abinda ya faru yanzu. "Nasan ba dan dare ba, babu abinda zai hana yan uwanki zuwa, amma nasan gobe da wuri zaki gansu, dan duk munyi waya kowa murna wallahi." "Umma wai ya akayi haka ta kasance?" "Al'amarin Allah fa, ke dai ki bar sha'anin aure wallahi." Maida idon ta, tayi ta kulle tana jin yadda Umman take yabon abun, tana kuma kwararo addu'ar dacewar Asma'un da fatan nasara a komai ma, a ranta take amsa amin, tana saka ram samun nutsuwa da Abdallan, wanda a yanzu take jin kamar ya karbe rashin ta ya tafi dashi, kamar akwai wani gagarumin abu da take jin tana kewa. Daina jin maganar Umman tayi sai sama-sama, ta fad'a tunanin shi da hoton fuskar sa, sajen sa da quarter million dinsa shi yafi komai tafiya da ita. Samun kanta tayi tana murmusawa, ta mike daga kan kafar Umman ta fad'a daki yadda zata more tunanin shi sosai ba tare da wani abu ya katse ta ba, wayarta ta jawo da nufin kiran Rauda ta tarar da missed calls da yawa sai text message dinsa guda biyu, budewa tayi tana fadawa saman gadon idon ta kyam akan wayar dadin kamalan na ratsa ta _"The first time we met, I can see that you and i are meant to be together... Your eyes were so gentle, your smile so true... You walked lightly into my heart, captivating and lovely to my mind. For you are my heart, my soul and my oneness. With you i know that I will find my completeness,my eternal peace of mind. You are the one I want to spend my life with. Both of our hearts will forever bond into all happiness, falls, pains and sorrows. I promise together we will meet tomorrow. I love you so much my wife."_ # Juyi ta dinga yi a saman gadon ita kadai kalamansa na ratsa ta, wayar da ke saman kirjinta ta yi kara, ta dan zabura kadan dan tayi nisa a tunanin, Rauda ce, dagawa tayi cike da zakuwa tace " Rauda." " Wayyo...Yaa Asma'u." "Wallahi da k'yar zan iya bacci yau, kinji yadda nake ji kuwa? Farin ciki kamar na ganni a gida wallahi,dan ma Umma tace kar muzo ne da tuni nazo " " Yau da goben duk daya ai, idan da rai da lafiya." " Haka ne,ya kika ji? Nasan ya hadu ba karya wallahi, irin wanda ya dace dake ba wanchan ya Adam din ba, fari kamar farin kosai. " " Ke ko? " " Allah kuwa, dan Allah kice ina gaishe shi da kyau da kyau, da wuri zan faso goben nan ba zan tafi ba sai na ganshi. " " Kyaji dashi dai, kije ki kwanta ki huta kinga ba ke kadai bace. " " Tom, sai da safe.* "Yawwa, sai da safe." Tasan da wuri duk zasu zo, shiyasa ma ta katse Raudan sun hadu gobe ayi duk maganar ma da za'a yi, Hidaya ta kira nan ma sukayi magana sannan ta kira Ya Hadiza, ita ce ma suka dan dade suna magana, har ta soma mata maganar gyaran jiki da duk abubuwan da ya kamata, ita dai jin ta kawai take bata ce komai ba, daga karshe sukayi sallama tace sai tazo goben. RM    32 ***Kansa ya daga bayan motar ta paka a harabar gidan nasu, akwai alamun hadari a garin yadda iska me dadi take kadawa, taune bakin sa yayi yana zura kafafunsa wajen, sai a lokacin yaga motar Aunty Fati daga gefen sa, fitowa yayi yana nazarin harabar gidan, kansa tsaya ya wuce cikin gidan ya haura corridor ya tura kofar, ji yayi an watsa masa abu a jikinsa, "Congratulations 🎉." Suka hada baki wajen fad'a, daya bayan daya ya dinga bin su da kallo, su hudu ne cif sai MD dake bayan su yana dariya, Aunty Fati ce ta fara mika masa flower sai Aunty Asiya ta bi bayanta, ta mika masa tana masa dariya, Amira da Ihsan ne a karshe "Congratulations Yah." Suka fad'a a tare, murmushi ya dinga sakar musu daya bayan daya, daga nan suka dunguma zuwa cikin falon in da Mom da Ammi ke zaune a kujera daya, wajen su ya karasa cike da matsananciyar kunya, ya duka yana gaida su, kowannen su farin ciki ne kwance a fuskarsa, cikin yanayin da ke nuna tsantsar farin cikin su. "Ango kasha kamshi, baku ji wani kamshi ba wai da ya shigo?" Aunty Fati tace tana zama a hannun kujera kusa da Mom "Irin dai kamshin ango." Asiya tace suka saka dariya, "Sai muka ji daurin aure, saukinta ma akwai enough time na shirya komai, biki zamuyi irin wanda baa taba irin sa ba." "Ai sati zamuyi Muna biki Aunty Asy." Wani kallo ya watsa ma Ihsan din irin na waya saka dake, ta gimtse bakin ta, tana shiga taitayinta, dama ta zata yau daya dai zai bar su su dan sakata su wataya amma sai gashi yana ankare da ita tayi magana. Ganin haka ya saka Amira tsuke bakinta itama ta bar aunty Asy da Aunty Fati suke mishi maganar tunda sune daidai shi, duk abin nan yaki magana sai murmushi kawai yake idan sukayi magana, sun san dama ba yi zai ba, dan ma MD ya kwashe komai ya fesa musu da irin yadda yake narkewa a gaban Asma'un kamar bashi ba, dan har sun fara tausaya mata saboda miskilancin sa, ashe ashe ita ba haka yake mata ba.    Lallabawa yayi ya gudu ya barsu suna ta fama, ya rage kayan jikinsa ya zauna yana jawo wayar sa, yayi broadcast message ga dukkan mutanen da yake ganin sun chanchanta su san da maganar auren nasa ya tura musu, sannan ya kashe layin dan yasan zasu kikkirashi. Baya jin rage ayyukan sa a yau, wata irin kasala yake ji da son kasance tare da ita, ko da ya dauko system din sai ya gagara komai, ya rufe ta ya ture gefe yana mike kafarsa ya jingina da jikin kujerar, sha daya da rabi saura yan mintuna ya duba agogon dake jikin allon wayar sa, Private layin sa da ba kowa ya san shi dashi ba sai family members yayi amfani wajen kiranta dashi, tana kwance rigingine tana duba sakonnin whatspp din ta wanda yawanci group din sai na Adam da yake mata kusan kullum sai uku ko biyar bata ma budewa sun taru sosai, shiga kansu tayi tayi marking ta goge su dukka sannan ta jefa lambar tasa a block list, ta koma wajen call log nan ma tayi blocking dinsa. Zata fita daga kai kiran ya shigo, ta duba time taga kusan sha daya har da kusan rabi, haka kawai sai jikinta ya bata shine dan babu me kiranta a wannan lokacin, dagawa tayi tana dan karata a kunnen nata kamar me tsoron abinda zata ji, muryar sa ta tsinkaya a cikin wayar yana mata sallama cikin tausasa lafazi, "Baki bacci ba?" "Umm?" "Kina jiran na ko?" Dunkulewa tayi waje daya daidai lokacin iska ta kad'a alamun tasowar hadarin gaba daya, wani sanyi ya shigo ciki ya iske ta, hade da wani irin mixed feeling akansa "Tell me, me ya hanaki bacci?" "Ba komai." "Ba wani, tunani na kike ko?" "Um Um." Tace ta k'asa bud'e bakin tayi magana " Then tell me, me ya hanaki bacci." "Kawai yaki zuwa ne?" "Ni na sani, tunani na ya hanaki bacci, "Kinga message dina?" "Na gani." Tashi yayi ganin yadda curtains din dakin ke dagawa ya daga yana kallon yadda hadarin ya hado sosai, hannun sa daya na rik'e da wayar dayan kuma ya zura shi wajen yayyafi kad'an kad'an na sauka akan hannun nasa, yana son yanayin damuna a rayuwar sa musamman ruwan dare, yana yawan kwatanta kansa da mai iyali a irin wannan weather din, sai da yaji ruwan ya soma karfi sosai sannan ya zare hannun sa, ya rufe glass din yana cigaba da wayar, har kusan sha biyu da rabi sannan yayi mata sallama shima ba dan yaso ba, sai dan ganin dare yayi. Alwala taje tayi, tazo tayi raka'a biyu kamar yadda ya umarce ta da zasu ajiye wayar, tana idarwa ta haye gado nan da nan bacci me dadin gaske, irin wanda ta dade bata yi irin sa ba ya dauke ta, bata tashi ba sai da Umma tazo ta tashe ta sallar asubah. Ita kanta umma ta lura da chanji a tattare da ita, da taje tashin ta, da yanayin da taga ta tashi. Kiran sa ne ya shigo wayar tana kokarin shiga toilet, ta dawo ta daga cike da zakuwa "Kin tashi?" "Eh." " Na zata na sakaki makara, bari muyi sallah, bye." Jallabiyar sa ya zura ya fito, ya kwankwasa ma MD kofa ya wuce yana jin motsin sa alamar ya tashi. ***Fido na zaune ita da Faiza Adam ya dawo, ya shigo ba tare da ya kalli in da suke ba, ya shige dakin sa ya rufo kofar, tashi tayi ta bishi, taje ta murda kofar amma sai taji ta a rufe, tsaki tayi ta hau bubbugawa tana kiran sunan shi "Man ba zaka bud'e ba, wannan wane irin wulakanci ne?" Yana jinta yayi banza kamar baya dakin, ta dinga bugu kamar zata zare amma ko gezau be ba, bare ya tashi daga ruf da cikin da yayi a saman hargitsattsen gadon sa da ya kwana biyu baa gyara shi ba. Kwafa tayi ta dawo wajen Faiza, ta saka mata ido tana kwashewa da dariya "Saboda soyayya ta rufe miki ido, har kike ganin a kyale shi zai sakko ya kulali, ai wallahi in dai ba maganin sa kikayi ba a yadda yake hayakin nan tsaf zai dangara miki saki. " "Yanzu ai na dawo hayyaci na, kije kawai ki same shi duk abinda ya kamata kiyi, ki biya ko nawa ne, sai ya gane ni ya wulakanta wallahi, aure kuma babu saki ko yaji zai gane kurensa. " " Yanzu kike magana, da kin tsaya iyayi ai kallon ki kawai nake. " " Shiga ki dauko wani abu sai na wuce yanzu ma, kinsan da zafi zafi ake dukan karfe. " Tashi tayi ta shiga dakin ta, ta dauko mata kudi ta bata, ta tafi ita kuma ta koma kofar dakin nasa tana cigaba da bugu, bata ji takun tafiyar sa ba, sai kawai ji tayi ya banko kofar ya fizgo ta, ya zare belt ya shiga tafkar ta babu kakkautawa, sai da yayi mata shegen duka sannan ya watsar da ita a wajen ya haure ta ya fice daga gidan, be san in da zashi ba, kawai mota ya shiga ya dinga zagaye, sai chan dare sannan ya dawo gidan ya shige dakin sa, ido biyu sukayi tana zaune tana jiransa a dakin, yana shigowa tayi kukan kura da chakume shi, yadda tayi masa bazata ne ya bata sa'a a kansa, ta dinga kai masa duka da yakushi ko ta ina, kamar mahaukata haka suka koma a gidan, suka lalata abubuwa da yawa a dakin kafin ya rufo ta a ciki da key ya dawo falo ya kwanta. Kusan kwana tayi a tsaye tana dura masa zagi, yayi kamar be ji ba, tunda ya samu ya garkameta shikenan, ba zai iya da hayaniyar ta ba dan babu alamun zata gaji, shi kuwa yanzu ba ta ita yake ba, baya ma son ko ganin me kama da ita kuma yana jira ne da zarar ya samu kan Asma'u zai kada keyar ta, su dawo su ci zaman su da Asma'un cike da so da kaunar juna, duk abinda yake ita kawai yake gani ba zai kuma taba samun nutsuwa ba har sai ta dawo gareshi. Da duku duku ya tashi ya fice daga gidan duk da ya daina jin motsin ta wanda yake kyautata zaton tayi baccin wahala dan ya jigata ta sosai bayan uban cizo da yakushin da ta yi masa, baya saka ran dawowa gidan nan kusa dan ba zai juri ganin ta tana zuwa in da yake ba, sai yayi gaba kawai ya je ya samu daki a hotel ya biya kudin sati dan idan ya zauna a gidan su ma surutun Mama da mutane ya isheshi ***Duk yadda Hajiya Mama zatayi wajen boye masa maganar auren Asma'un tayi, ta kuma hana kowa gaya masa idan yayi mata maganar sai tace suna magana da Abban ne komai ya kusa daidai ta, hakan ya sakashi rage damuwar da yake ciki har yake tsayawa yayi wanka ya gyara jikinsa, tsakanin sa da Fido tun ranar da suka saida hali, tasan guduwa yayi, sai ta rabu dashi tana tama shi dan saura kiris ya shigo hannun ta,daga nan ne zai gane shi din karamin dan bariki ne dan sai ta zame masa tamkar rakumi da akala. _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* *RM*      33 **** Rauda ce ta fara zuwa tana kwance tana bacci bayan tayi sallar asubah ta koma sai ji tayi an danno kanta, ta bud'e idon ta tana ayyana Rauda din ce, da sauri ta tashi tana dubata "Amma Allah Rauda baki da kai sam, wai bakya jin nauyin jikinki ne?" Turo baki tayi tana dariya "Farin ciki ne wallahi, babu fa abinda nayi na fito zai tafi office yace nazo ya ajiye ni, yasan ba zan iya zama ba shima." "Shi yake biye miki ma Allah." "Ina umma?" "Wai bata san kinzo ba ma?" "Ai direct nan nayo, nasan tana dakin Abba luf zan sai ya fito ya tafi kar yayi min fad'a." "Aikuwa sai na fallasa ki." Tace tana sakkowa daga gadon tayi hanyar toilet " Ki rufan asiri dan Allah, kinsan Abba fad'a zai yace na fito na bar shi." " Aifa sai na fad'a." Ta shiga ta kuskure bakin ta sannan ta dawo ta zauna a gadon tana fuskantar Raudan "Yaushe zai zo?" "Wa?" "Yaya Abdallan." "Ban sani ba, kin karya?" "Banci komai ba fa, me akayi ne yunwa ma nake ji." "Nima yau umma bata tashe ni ba, bari na dubo mana kitchen din muga." Mike kafa tayi ta saka pillow a bayan ta bayan Asma'un ta fita, ta dauki wayarta ta shiga call log taga wayar da sukayi da shi, murmushi ta saki tayi saurin ajiye wayar ganin sako ya shigo alamar text kuma shi ya turo, dadi take ji sosai Asma'un ta samu me.sonta da gaske, halin ta na kirki yafi dacewa da miji na kirki na gari, jin ta dawo ya saka tayi saurin kife wayar tana kallonta dauke da flask da cups ta ajiye sannan ta koma ta dauko sauran kayan, kunu da kosai ne Umman tayi hade da taimakon sabuwar me aikinta da tayi bayan bikin Asma'un, sakkowa tayi da k'yar suka yi breakfast din suna hira, sannan Asma'u ta sake kwashe kayan ta maida kitchen, ta wuce dakin Abba dan ta gaishe shi, ta same shi ya shirya yana cin dumamen tuwo da Lipton da ya zamar masa al'ada, fuskar sa ce ta fad'ad'a da fara'a cike da farin ciki ya amsa gaisuwar ta yana dorawa da tambayar babu matsala ko? Be ga wani abu tattare da ita da zai nuna masa rashin amincewar ta ba, hakan ya kara masa karfin guiwa ya bita da addu'ar fatan nasara a dukkan al'amuran ta na rayuwa, sannan ya jawo drawer sa ta falo ya ciro sadakin ta ya mika masa "Ga sadakin ki nan Allah ya baku zaman lafiya." Kin karba tayi, ta tashi zata bar dakin yace dole ta dawo ta dauka saboda hakkin ta ne, ganin ya dage sosai ya sakata dukawa a kunyace ta dauka sannan ta sake mika masa "Abba gashi toh ko za'a yi wani abun dashi, ni babu abinda zanyi dashi." Girgiza kai yayi yana kin karba "Hakkin kine, abun da za'a yi miki kuwa hakki na ne, kamar yadda nayi wa kowa a cikin yayana, dan haka ki je ki ajiye anjima Abbati zai karba sai ya saka miki a account zai miki amfani ko gaba." Bata da zabi illa tayi godiya ta tashi rik'e da kudin ta fito tana juya su a hannun ta, dakin ta koma Rauda ta mika mata wayarta da sauri sanda kiran ya sake shigowa a karo na uku, tsoron haduwar su da Abba ya hanata kai mata wayar dakin Abba shi kuma ogan be daina kira ba, har ma ta yanke shawarar kai matan sai gata ta shigo, " Ya Asma'u Uncle Abdallah sai kira yake, gashi nan ya sake shigowa ma kiran." Hannu tasa ta karba sannan ta jefa mata kudin kan cinyarta tana fita zuwa dakin umma dan bata son yin wayar a gaban Raudan. Sai da ta shiga dakin sannan ta daga tana ji ya shaki iska ya fesar, sannan ya amsa sallamar da tayi masa "Ina kika shiga ne my wife?" "Wajen Abba naje, ashe ka kira." "Eh so nake naji muryar matata kafin na tafi office." "Uhmm." "Kar naje na kasa aikin Oga ya sallame ni, kinga ai da matsala ko? Abinki da karamin ma'aikaci." " Ka iya tsokana." " Ba wani tsokna, da gaske nake, kinsan yanayin aikin kasar tamu." " Ummm... Haka ne." " Toh kin gani?" Ya fad'a yana danne wayar a tsakanin kansa da kafadar sa, ya duka yana saka socks sannan ya saka takalmi ya mike wayar na makale da kafadarsa har lokacin yana magana k'asa k'asa, brush ya dauka ya sake kwantar da sumar kansa wadda tasha gyara, "Idan na gama daga office din zai biyo, sai muyi maganar abinda ya kamata ko?" "Tam shikenan.... Sai ka dawo. " " Yawwa, take care of yourself for me. " " In sha Allah." Tarkacen kayan sa ya dauka bayan ya tura wayar aljihun sa, ya rik'e dayar da tab dinsa a hannu ya fito falon, yasan ba zai samu MD ba dan yace masa yana da sakon da zai karba a airport da duku-duku, dan haka shi kadai ya shiga cikin gidan nasu, ya gaida su Mami sannan ya nufi wajen Baba Alhaji, ya tarar ya koma bacci be tashi ba, sai kawai ya fito ya bar gidan dan dama kunyar haduwar su yake bayan abinda MD din ya shuka masa, yanzu yasan duk wani kallo yan gidan zasu dinga masa bayan shi ba haka yake ba, MD ne duk ya jawo amma shima zai rama ne, yana kallon irin kallon da Mom take masa jiyan nan yasan idan ya dawo sai ta zaunar dashi dole ne, be san me zata ce masa ba dai amma yasan bata da zafi da tsawwalar da zata ce bata karbi auren ba. Be sani ba, tun a jiyan suka fara tunanin hada lefen sa bayan Baba Alhaji da kansa ya kirasu ya basu labarin duk yadda al'amarin ya kasance, kuma duk cikin su dama babu me ja da hukuncin Allah, shiyasa ma yayi komai kansa tsaya dan yasan yayi sa'ar mata na gari masu son duk abinda yake so, shi da kansa ya basu kudi yace a hada wa Asma'un lefe, Mami ce ta karba dan dama itace uwar Abdallan, ita kuma zatayi komai ita Mom yar kallo ce kawai. Aunty Fati ta dora itama akai nan da nan aka soma hada kaya na gani na fad'a a daren aka siya wasu online kafin yau da zasu shiga kasuwa sosai dan ma abin yazo a kure da Dubai Mami zata ta hado lefen Abdallan na nuna sa'a, amma duk da hakan ma zasuyi abu me kyau da tsari. Yana zaune a office din yana duba wasu motoci ya ga MD na shigowa cikin building din ta cikin CCTV din dake cikin office din wadda take nuna duk shige da ficen da ake a cikin compay, tashi yayi ya murda key a kofar tasa ya dawo ya zauna ya cigaba da aikinsa,kansa tsaye ya murda kofar amma sai ya jita a rufe, ya sake murdawa yaji da gasken a rufe take, sai ya juya a tunanin sa ko Abdallan baya nan, murmushin mugunta yayi lokacin da yaga ya juya dan yasan zuwa zai ya isheshi ya hana shi aikin gabansa gashi yana so yaje yaga matarsa kuma baya so aikin ya kai masa yamma sosai dan so yake ya dauki hutu daga satin da zai kama. Sai da ya gama aikin tas wajen biyu da rabi sallah kawai ta tashe shi sannan ya bud'e kofar ya dauki waya ya kira MD din yace yazo ya sameshi a office da yake building din da suke daban daban ne amma duk cikin gini daya, shi yana bangaren karan kansa shi kuma MD na kula da business din Baba Alhaji "Na zata ko Amaryar ce a office din dana ga ka saka key ai, shiyasa ma ban zafafa ba na koma." "Ina sane ai, damu na zakayi ban gama aikin ba. " " Nima fa aikin ne dani da yawa wallahi, ba zan iya zuwa ba gaskiya. " " Dan Allah kazo, abu zaka tayani dubawa, kayan sun zo suna nan Lagos, kazo mu duba sai ka zabi daya. " " Dan Allah da gaske? " " Idan ba zaka zo ba shikenan. " " Ah wallahi gani nan, jira ni yanzu zaka ganni. " " Ok kayi sauri kafin na chanja shawara. " " Yanzu kuwa. " Yana ajiye wayar yana shigowa, ashe suna wayar ma yana tahowa, murmushin mugunta yayi masa ya tura masa system din gaban sa bayan sun zauna " Kai ne mayen mota, ga latest nan, sai ka duba ka bani ta wajenka sai naga nawa zaka cika?" " Dan Allah da gaske? " " Oho. " " Wow..bari muga." Yaja system din gaban sa yana dubawa a hankali har yazo kan wadda tayi masa, wadda dama tun da ya saka order su ya kwallafa rai akanta, juya masa system din yayi yace " Wannan nake so. " " Banda ita. " " Why? Haba Abuya kaifa kace na zaba. " "Eh amma banda ita, it's for my wife. " "What?! " Ya mike yana kallon sa " Abinda kaji, ka duba wata dai ina sauri ne, zan tura ma wani Alhaji ya gani, sai na cire su a ciki "Amma ai this is not fair, kaifa kace na zaba na zaba kuma..." "Nace banda ita ba, it's for my wife." "Ai shikenan, tunda ta fini." "Wait... Wai ka zata daya kuke dama?" "Na fita ma nake tunani." "Tab! Zabi kayi sauri, na gaji da magana, ko ka jira next order idan sun sauka. " " Bari naga, ita din dai wallahi nake so, haba angon Ma'u, haba Alhaji Abdallah Motors, haba Yaya Abdallah me kudin duk Nigeria, pls pls ka bar min ita, ga ta mata nan masu kyau u can choose one for her, dan Allah, inaso na kare yawa da ita wallahi, akwai wata babe dana tama. " " Ajiye min system, baka shirya ba har yanzu, kuma wai a haka Baba yake cewa kai kayi min aure, wannan ai insult ne babba, idan baka nutsu ka shiga taitayin ka ba, sai dai kaga ana raba alawa da goro. " " Auren dole? Zaka min? " " Oho, ka dame ni kasa ina ta bata baki na, tashi zan kulle office dina. " " Ina kayi daga nan? " " Gari zan shiga, karma kace zaka bini. " " Nima garin zan shiga ai, hanyar ina kayi?" " Baka zo da mota bane?" " A ah zan dawo nan ai, bana so na fita da ita ne. " " Toh ba hanya daya zamuyi ba." " Why are you avoiding me, ko dai chan zaka? " " Ina? " Ya harare shi yana tura kofar ya rufo ta suka jera " Chan din, idan ma chan zaka ni ba zuwa zan ba, ba zaa barni a waje a shige ciki ba, kuna chan kuna shan dimi ni an barni waje, nah nima inada gata na. " Duka ya kai masa yana dariya " Allah baka jin magana MD. " " Ai gaskiya ne. " " Toh yafi maka ai, nima takura min kake. " " Yanzu sai ka dawo kenan? Ko gida zaka wuce daga chan? " " Noo zan tsaya zooroad, zan iya dare ma, anyways muyi waya idan akwai wani abun. " " Ok, safe! " Ya saki kofar ya rufe masa ita yana ja baya, juya motar yayi ya fice shi kuma ya koma saman dan ya tattare sauran ayyukan da zai kafin time din da zasu shiga meeting, lokacin ma ya taho shiyasa zai yi sauri yaga yayi rounding up idan yaso gobe sai ya fara wasu kawai. ***Siyayyar kayan ciye-ciye ya tsaya yayi, tare da fresh fruits masu yawan gaske sannan ya tura mata message din gashi nan, suna zaune suna maganar me gyaran jikin da Ya Hadiza zata kira wata neighbor dinta Amaryar Kb da tayi bala'in iya gyaran amarya har ma da uwargida, abubuwan da take siyarwa maganin mata na matsi dana ni'ima, turaren wuta, Khumra turaren wankan, vip humra, oils perfume sannan tana gyaran jiki na amare. Bangaren turaren wuta tana saida irinsu Sandal flakes , Kajiji ,Yellow sandal Mufaddal.Senegalese Kajiji Couscous. Green sandal,Sudanese mix,Shek Bakhur, Sandal coconut. Dorot , Hadut, Gabgab,Kajiji balls. Aroosa da sauran su. Ga kuma maganin infection sadidan, su tsumi, zumar chad da sauran kayan gyara na kankaro mutunci, ga hadaddun khumra masu masifar kamshi da kama jiki, turaren wanka da na gashi, ga kuma na carpet da na curtains musamman a yanayin damunar nan. Amaryar kb Global Enterprise dai ta hada komai na gyara da kankaro mutunci 08067558902 shiyasa ma Ya Hadiza taga ya kamata ta kirata, suyi magana ta gyara Asma'un ciki da waje, ana cikin maganar ne sakon sa ya shigo, shine ta zame ta shige daki ta fad'a toilet tayi wanka a gurguje ta fito ta shafa daya daga cikin khumran da Ya Hadiza ta taho mata dashi na cikin kayan da Amaryar Kb take saidawa ta shafa ta dan shafa powder da wetlips, ta sake bin jikinta ta feshe shi da wasu kalolin turarurrukan masu sanyin kashi sannan ta zauna tana tunanin yadda zatayi ta fita idan yace mata yazo, Hidaya ce ta biyota ciki, ta ganta a shirye tsaf tana danna wayar ta, basarwa tayi kamar bata ga shigowar Hidayan ba, juyawa tayi ta tseguntawa su Yaya Hadiza, suka yi dariya har Umma da dadi ya lullube ta, fitar hidayan da kad'an zai ga kiran sa, ta daga gabanta na faduwa yace yana waje, a kasalance tace toh ta tashi ta shiga zagaye a dakin ta rasa ta ina zata fita, kunyar su take ji tana jiyo hirar su a tsakar gidan, kuru tayi ta daure ta fito rik'e da flat shoe dinta a hannu, taki yarda su hada ido da kowa tace "Umma shine yazo." "Allah ya kiyaye, ki gaishe shi." Har tayi gaba Ya Hadiza tace bari ta tsokaneta "Cewa zakiyi Umma angon yazo." Dariya suka kwashe da, ta daga kafarta da sauri ta fice taji umma na cewa ya Hadiza ya kyale mata yarta. Bayan sa ta hanga ya juya shi yana facing din kofar shigowa, dogo ne me cike da haiba, ba shi da rama sannan ba shi da kiba jikinsa dai-dai ya dace da yanayin sa, riga da wandon yadi ne a jikin sa ash colour dinkin rigar daga dan ya wuce guiwar sa, kansa babu hula sai takalmin kafarsa sau ciki, duk a dan dakikun da basu gaza goma ba ta gama tantance shi, takun ta yaji ya juyo da sauri yana rik'e da car key dinsa da babbar wayar sa a hannu, murmushi ya sakar mata ita ma ta maida masa tana russunar da kanta ganin ya kafe ta da kallon sa wanda yake kashe mata jiki, a gefen sa ta tsaya ta gaishe shi, maimakon ya amsa sai ya mika mata hannu alamun su gaisa, a kunyace ta mika masa ya kama hannun ya rik'e yana dan motsa shi acikin nasa hannu. "Kinyi kyau sosai." Ya fad'a yana kallon lips dinta da suke shekin lips balms, kauda kai tayi cike da jin kunyar sa, har lokacin be saki hannun ta ba, kamar ma hakan na sashi nishadi, ciki tace ya shigo ya noke kafada "Ban gama kallon ki ba, nan yafi haske na more kallon matata." "Kai..." "Emana." "Dallah malam cika mata hannu! " Ya buga tsawa idonsa na kankancewa cikin tsakanin tashin hankalin ganin hannun Asma'un cikin na Abdallah, tahowa yayi gadan gadan, wani banzan kallo Abdallan yayi masa ya saka hannu ya matso da Asma'un jikinsa sosai sannan yace " Don't you dare, karka kuskura ka karaso kusa da matata." " Matar ka? Yaushe ta zama matar ka?" " Kaje ka tambaya kaji, kuma wallahi ko kusa da ita na ganka wallahi sai na daure ka kaji na rantse, shashasha kawai. " A karkace Umar yayi parking suka fito shida Abbati a dari suka fado gidan ganin motar Abdallan data Adam a kofar gidan, suna zuwa suka damke Adam din daya fara hauka yana kokarin jan Asma'un, hannun ta cikin nasa ya shiga takawa da ita, ya nufi gate din gidan ya fita da ita, Adam ya birkice ya dinga kwala mata kira su Abbati suka rik'e shi gam, gaban motar ya bud'e mata ya sakata, sannan ya dawo ya shiga ya tada motar suka bar layin, ransa ya kai kololuwa a baci amma calmness dinsa na tare dashi, satar kallon sa take, driving kawai yake da hannu dayan dayan kuma yana rik'e da nata be ce uffan ba, be kuma sake kallon ta ba bare ta saka ran zai mata magana. RM    34 ***Driving kawai yake da hannu daya, dayan kuma yana rik'e da nata be ce uffan, be kuma sake kallon ta ba bare ta saka ran zai mata magana. Yayi kokari sosai wajen maintaining coolness dinsa dan yadda yake ji kamar ya koma ya saka a kama masa Adam a kulle masa shi har sai ya manta da Asma'un da duk abinda ya shafe shi, kishin sa yake ji sosai a yau fiye da kullum, "Ka... Kayi hakuri.". Ta samu kanta da furtawa cikin rarrabewar kalmomi, kansa a gaba yana kallon titi ya dan matsa hannun ta kad'an amma bai ce komai,shiru ne ya sake biyo bayan motar, hanyar office ya dauka, akwai hadari sosai a area ba kamar baya da suka baro ba, har iska ta soma kadawa kad'an kad'an, rage tafiyar yayi ya shiga layin, har lokacin idanun sa na kan hanya hakan ya kara tabbatar mata ransa babu dadi. Kanta ta daga tana kallon building din dogon gaske, a chan sama ta hangi suna K'AREFA, bata gama karantawa ba aka wangale katoton gate din, harabar wajen cike take da motoci sababbi masu kyau, sai hadahadar mutane daga chan gefe, ciki sosai ya shiga da motar sannan yayi parking ya kashe ta, sai a lokacin ya juyo yana kallon ta, yana kallon mayafin da yake jikinta, babba ne amma kuma ba shi da kauri sosai, har yana iya hango rigar jikinta amma ba tar ba, sai ka saka ido sosai, kusa da ita ya matso sosai ya zura kansa bayan motar, ta sauke numfashi tana jin closeness din nasu na haifar mata da yanayi, rigar sa ya dauko jacket, ya kama mayafin nata yana kallonta cikin ido, dan motsawa tayi kadan ya karasa nannade mayafin ya dora mata jacket din akai, ya balle mata sannan ya maida mata mayafin ta, baya ya danyi yana so ya tabbatar da baa gani yanzu,sai ya fito yana zagayo side dinta ya bud'e mata. Fitowa tayi tana sadda kanta k'asa mamakin sa na cikata, tafiya ya soma yi bayan ya saka hannun sa a nata yabi hanyar baya mara cinkoso da hayaniya, ya shiga ta wata kofa inda suka tarar da mutane uku a zaune kowannen su na duba takardu a gaban su, daya mace ce sai sauran maza biyu, da sauri suka tashi tsaye suna masa sannu da zuwa dan rabon sa da bangaren kusan sati kenan MD ne yake kula da duk baangarorin, hannu ya daga musu kawai ya wuce da dan sassarfa ya danna bud'e kofar lift din ta bud'e ta shiga sannan ya mara mata baya, kus-kus suka hau yi bayan shigewar su, cikin yanayi na ban mamaki dan basu san komai game da maganar auren nasa ba, ba kuma su sanshi a mutumin banza ba. Duk iya hasashen su ba su iya hasaso komai ba, sai suka hakura duk suka koma bakin aikin su, suna masu kyautata masa zato.    Binsa kawai take kamar rakumi da akala, har suka dangana da babban office din nasa, ya bud'e suka shiga ciki sannan ya murza key din yana sakin hannun ta, ya wuce gaba da sauri ya shiga toilet din dake cikin office din, tsaye tayi a inda ya barta tana satar kallon office din da yayi masifar tsaruwa, ga wani sanyin dadi da kamshi irin wanda take ji a jikinsa a duk sanda yazo wajen ta, tana nan a tsayen tana more kallon komai a tsanake ya fito hannun rigar sa a nannade, ya kalle ta yana takowa zuwa wajen da take tsaye "Zo ki zauna." Ya nuna mata couch din dake gefe da hannun sa, wuce shi tayi ta zauna a dosane tana mamakin sauyawarsa kamar bashi ba, bata san wannan side din nasa ba, sai yau da ya nuna mata shi din miskili ne, na gaske. Iska ce ta taso da karfi, ya rufe dukka windows din, ya rage hasken office din ya zama dim, duk abinda yake tana ta satar kallon sa, aka soma ruwan da karfin gaske, kujerar sa ya hau, ya bud'e system dinsa yana so ya rage abinda yake ji a zuciyar sa, baya so tunanin da zuciyar sa take bashi yayi tasiri akan sa, duk in da ya shiga sai ya fita ba tare da ya iya aikata komai ba, haka ya dinga shiga nan ya fita nan har ya gaji ya ture system din yana jan dan siririn tsaki, baya jin zai iya jure tsawon kwanakin da Baban yace zata tare gaskiya, dan hankalin sa ba zai taba kwanciya ba in dai har Adam na kaiwawo a tsakanin gidan nasu. Wajen da take ya kalla sai yaji ta bashi tausayi musamman sharentan da yake, yasan ba ita tayi masa laifin ba amma ya rasa dalilin da ya saka shi jin zafin sosai, lura yayi da tana jin sanyi kamar, dan ta dage kafarta sama ta cure waje daya, remote din AC ya dauka ya kashe ta gaba daya, ya ajiye ya isa wajen da take, ya durkusa a gabanta yana kamo hannunta cikin nasa "Kayi hakuri." Ta sake ce masa a karo na biyu, hakan ya kara masa tausayin ta sosai, ya daga mata kai kafin ya furta "Baki min laifi ba ai." "Naga kamar kana fushi dani." "Um um." Ya sake girgiza mata kai "Haka nake Husna, ba komai nake magantuwa akai ba." Jinjina kai tayi, sai ya dauke zancen ta hanyar cewa "Ya kika ga office din nawa?" "Yayi kyau." "Really, taso kiga." Ya mike tsaye ya kama hannun ta, ya kaita har wajen kujerar da ya taso yace ta zauna, ta zauna ya zagayo ta bayan ta yayi mata rumfa, ya dora kansa a saman kafadarta numfashin su na gogayya da juna, hannun ta ya dora a saman mouse din sannan ya dora nasa akai, ya shiga wajen motocin da yayi order ya dinga scrolling sama. A zahiri idon ta na kan computer din sai dai a badini babu abinda yake ganewa face bugun zuciyar ta da ya karu sosai, shi kansa ya shiga wani yanayi amma ya kanne yana cigaba da scrolling har ya wuce abinda yake so ya nuna mata, sai da ya sake dawowa baya sau uku yana wucewa kafin ya tsaya a inda yake so ya tsaya da k'yar. "Ki tayani zabe, wacce zan dauka." Muryar sa very deep cike da kasala yayi maganar a kanta taji shi har cikin kwakwalwarta, kamar bashi ne yayi maganar ba. Motoci ne guda uku akan screen din, dukkan nin su sunyi kyau ainun, har ta rasa wadda zata zaba a ciki, ta dinga kallon sa tuna sakewa, da k'yar ta tsaya a kan wacce MD yace yana so "Wannan tayi kyau sosai." "Wannan fa?" Ya nuno wadda ya siya da sunanta, "Wow, wannan tafi kyau, amma kalar mata ce." "Tafi wannan kyau?" Ya sake nuno dayar "Tafi, ita kawai zata fi kyau a mace." "Kina so?" Yace yana sake zuro kansa sosai jikin wuyan ta, ya rufe system din da hannun sa. "Na'am?" Tace cikin inda-inda "Kina so?" Ya sake maimaitawa Girgiza masa kai tayi, "Tafi karfi na." Hannu yasa ya juyo da kujerar ta dawo tana kallon sa, ya sake durkusawa agabanta ya zube hannayensa akan cinyar ta "Taki ce, bata fi karfin ki ba, duk wani abu da Abdallah ya mallaka naki ne." Kamar almara haka taji maganar, ta rasa wane kalar farin ciki zatayi, murmushi kawai ta dinga yi me tsada, wanda ya sake dilmeyar dashi a cikin son ta, godiya tayi masa ba dan tana tunanin godiyar ta yi ba, sai dai dan kawai tana tunanin abinda zata iya furtawa kenan, tana jin kunyar sosai, ido ya zura mata yana kallonta, ta rufe fuskar ta da tafin hannun ta tana fitar da siririn sautin dariya, hannu ya rike ya bud'e fuskar yana marairace mata kamar zai yi kuka " Na fa biya, a barni na more kallon matata." Dariya suka saka a tare dan yadda yayi maganar yayi masifar bata dariya, be sake tunawa da wani Adamu ba, zaman su waje daya ya mantar dashi komai har yake jin ba dan kar ace yayi rashin kunya ba, da daga nan sai gida, amma ba zai iya ba, zai dai roki Abba a rage kwanakin a takaita, dan a matse yake kamar yadda MD yake tsokanar sa, be kuma san a matsen yake ba sai da ya gansu a Inuwa daya. A hankali a hankali ruwan ya dinga raguwa, ya zama sai da da yayyafi kawai, yunwa yaji yana ji sosai, gashi yasan lokacin lunch ya wuce, wayar sa ya ciro zai kira MD ya tarar da missed calls dinsa da na Baba Alhaji, Baban ya fara kira sukayi magana sannan ya kira MD yace ya saka masa order daga 10-10 two pack yana office, zai tsaya tambayar shi yaushe ya dawo ya kashe wayar dan yasan shi da bin kwakwaf. Kan couch din ta koma ta zauna ya gama wayar yazo ya zauna shima, daf da ita ya cigaba da danna wayar yana so yayi abinda Baba Alhaji ya sakashi, baya wasa da duk abinda da ya shafi Baban, very serious taga ya zama yana ta aika sakonni duk da bata ga me yake rubutawa ba, bata son bin kwakwafi sai kawai tayi baya da kanta dan ta bashi damar gama aikin sa, ji tayi ya jawo ta jikinsa, ya mana sashen ta a jikin nasa shashen ya sakalo hannun sa ta bayan ta,ta shiga jikin sa sosai ta barin sa, cigaba da abinda yake yayi kansa akan wayar tayi luf a jikin sa har sai da ya gama, sannan ya ajiye wayar yana yin baya dasu. Knocking akayi a kofar ya yi jim yana tunanin waye,dan ba kasafai ya ke zama a office din nan ba kuma ya tabbata babu wanda zai biyo shi nan din sai MD, tunowa da yayi da order da yace yayi masa yasa shi mikewa ya nufi kofar ya bud'e kad'an. MD ne a tsaye sai messenger rik'e da ledoji biyu manya masu dauke da tambarin 10-10 restaurant, karba MD yayi ya sallame shi yace "Matsa na wuce." Babbake kofar yayi yana hararar sa, ya mika masa hannu alamun ya bashi ledojin "Bamu taba haka ba, sai na kai maka har ciki sannan nake tafiya idan ba tare zamu yi lunch din ba." "Time da nake sa'anka ba, yanzu bana cin abinci da tuzuru, bani kayana ana jirana." " Amarya ce a ciki?" Ya bud'e baki cike da mamakin Abdallan Tura shi yayi ya rufo kofar ta waje yana mika masa hannu "Bani nace." Dariya ya kwashe da ita, ya mika masa yana karkade hannun sa "Dole ne ma nayi aure wallahi." "Kanka ake ji." Ya juya ya shige cike ya sake rufe kofar, sosa kai MD ya tsaya yana yi cikin jin dadi, ya kada kansa yayi gaba yana murmushi a ransa yana ayyana yanayin Abdallah da yadda zai iya tafi da mace, bashi da matsala ko kad'an kuma a duniya yana respecting din mace, yasan zata sha gata a wajen sa, bashi da haufi akan dan uwan nasa dan zai iya bugar kirji yace Asma'u tayi dace da sa'ar miji na gari. Yayi nisa a tunani cike da nishadi yake sauka da steps din masu yawa, be tsaya hawa lifter ba dan yana bukatar ya more tafiyar yana hasaso Abdallah da mace, macen ma wadda ya yarda yake so. A saman table ya ajiye ledojin ya dauka dan madaidaicin carpet ya ware shi a wajen, ya sakko da kayan ya ajiye sannan yace ta taso, girgiza kai tayi tace ta koshi dan bata san ta yadda zata fara cin abinci tare dashi ba, bayan haka ma ita din ba gwanar cin abinci bace sosai, kuma ba wai tana jin yunwa bane dan sai data ci abinci tare da su Rauda da Hidaya. Har ya zauna ya taso yana hararar ta a wasance, "Zaki taso ko sai na dauko ki? " Allah bana jin yunwa." "Ban yarda ba, baki san idan aka yi ruwa ciki rarakewa yake ba?" " Ni nawa bayayi. " " Comman, taso." Ya mika mata hannun sa, ba dan taso ba, ta mika masa ya taimaka mata ta mike, tabi shi zuwa wajen ta zauna tana tankwashe kafarta, abincin ya bud'e Chicken Mandi rice ce sai hadin salad a gefe sai shredded Beef hade da wata soup me shegen kamshi (abincin da nake kwadayin ci kenan! 😂 Lol) a nutse yayi Bismillahi ya fara ci a hankali kamar wanda baya son ci, juya spoon din ta dinga yi yana kallon ta, ya dan ci sama-sama ya ture yana furta Alhamdulillah, tsattsareta yayi da ido alamun taci, ta marairace masa kamar zatayi kuka "Allah na koshi." "Shikenan tam, bari na maida ki gida ko? Ko zaki bini mu tafi namu gidan?" Murmushi tayi, ta tattare kayan ta hade waje daya, dan dayan ko bud'e shi ba'a yi ba, toilet ya sake shiga ya kuskure bakin sa da mouthwash yayi alwala ya fito, , yace ta tashi tayi alwala dan yana jin ana kiran magriba idan suka fita ba zata samu ba, alwala taje tayi dan dama a matse take da fitsari, ta same shi akan carpet din yana gyara botir din hannun rigar sa, a bayan sa ta tsaya ta gefen sa, ya jasu sallar. Bayan sun idar ne yace su tafi, ta tashi shi kuma ya dauki ledar da ba'a bud'e ba, wanda yaci kuma ya barwa cleaner idan yazo gyara office din bayan sun fita, yanzu ma kamar dazun hannun ta na cikin nasa suka fito, duhu ya samo yi sosai babu kowa a wajen da suka ga mutanen dazu alamun sun tashi aiki, ta kofar bayan ya sake bi da ita, suka tarar an gama wanke masa mota tayi tas, yasan aikin MD ne, murmushi yayi ya bud'e mata ta shiga ta zauna sannan ya koma ya shiga ya tada motar, maimakon taga sun yi hanyar gida sai taga sun baude, bata ce komai ba har ya tsaya yace mata yana zuwa, be dade sosai ba ya dawo ya saka ledojin da ya siyo a baya sannan ya ja suka tafi. Motar Abba na kofar gida sanda suka iso, amma babu kowa a layin watakila saboda ruwan da akayi ne, juyowa yayi gaba daya bayan ya tsaya ya matso sosai daf da ita, ya dora hacin sa akan nata yana gogawa kad'an kad'an, ba'a son ransa ya dawo da ita ba, ga wani irin feeling dake taso masa musamman yanayin ruwan da akayi, ji tayi ya hade bakin su waje daya, ta dauke numfashi cikin wani irin yanayi ya shiga kissing dinta passionately, yadda yake koman sa a nutse da class haka ma a yanzu, tana jin yanayin nutsuwa a tattare da abunda yake yi, kusan minti daya sannan ya cikata yana yin baya, jikinsa na kare macewa sosai, he can't wait this long gaskiya, dole ya nemi ragin kwanakin, dan yasan zai cutu, musamman da ya riga ya san ita din halaliyar sa ce, daga shi har ita babu wanda ya iya magana, ya daga mata lock din motar ta bud'e murfin ta zura kafarta waje sannan tace masa "Sai da safe." Maimakon ya amsa sai ya tsare ta da ido, tayi murmushi tana rufe masa kofar ta zagayo ta bangaren sa, balle kofar yayi ya fito, ya bud'e bayan ya ciro ledojin ya mika mata biyu ya rike sauran, suka shiga takawa zuwa cikin gidan nasu, a ciki suka hadu da Abbati, ya karbi kayan ya shiga dasu, ya dan yi jim kad'an sannan yayi mata sallama ya juya yana tafiya a hankali. Sai da taga ya tafi sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, ta kutsa kanta cikin gidan nasu tana ayyana kalar kunyar da zata sha musamman idan ta tarar su Rauda basu tafi ba. *RM* 35 ***Da sand'a ta shiga gidan tana addu'ar Allah yasa har ta shige daki umma bata wajen, muryar Rauda ta soma ji tana tambayar Abbati abubuwan da suke cikin ledar, lebewa tayi sai taji Umma tana cewa su daina bud'e mata su bari tazo, kamar ta koma haka taji, ta daure dai ta shiga da sallama ciki ciki, bin ta duk sukayi da kallo, tayi saurin zama daga gefen Rauda ta gaida umman kamar wata bakuwa, dariya ce take cin Rauda amma ta kanne. "Babu matsala ko!? Abin da Adam yayi masa Ina fatan hakan be zama matsala ba." Umma tace tana mikewa "Babu komai, ya dai ji babu dadi amma kuma be wani nuna ba." "Toh masha ALLAH, Adam be kyauta ba, amma dai Abban ku yayi ma tufkar hanci, yace kar ya sake ganin kafarsa har sai kin tafi, idan bakya nan kuwa babu me hanashi zuwa amma yanzu kam kar ya sake ganin sa, ya ma rage kwanakin tarewar yace sati daya sai kawai a siya kayan ko readymade ne, tunda wannan na Hajiya Maman sai da su za'a yi sai ayi miki wasu kawai. " " Ok. " Kawai tace tana hango yadda Abdallah zai ji idan tace masa an rage kwanakin, tunanin shi ta tafi gaba daya har bata ji sanda Rauda take cewa ta matsu a bude kayan ba, sai data dan taba ta sannan ta wayance tana cewa " Me kika ce? Bari na shiga ciki. " " Wai kayan fa zaki bud'e duk na matsu wallahi. " " Rauda kwadayi." Umma tace tana dariya " Allah Umma na matsu, nasan kayan kwalam ne, Allah ya taimake ni da na tafi shikenan ba ni za'a kwashi gara. " " Ki bud'e mana, sai ni dole? Kin jiki. Ni bari kiga ma. " Ta tashi ta shige ciki tana jiyo Rauda da Abbati suna bud'e ledojin suka saki ihun murna. Jacket dinsa da har lokacin take rik'e da ita ta saki akan gadon ta cire kayan jikinta ta saka wasu riga armless da dogon skirt sai ta dora rigar tasa akai saboda garin da dan sanyi dan ma taga alamar ruwan da akayi a chan yafi yawa sosai. Rik'e da ledojin Rauda ta biyota da Abbati, suka baje su a tsakiyar dakin, suka ci sukayi nak, Raudan take ce mata anan zata kwana yaje garin su shima achan zai kwana sai da safe zai biyo su wuce, umma ce ta leko tace Abba yana kiran Asma'un, ta tashi zata dauki hijab dinta sai a lokacin Rauda taga jacket din, ta bita da kallo har ta fice kafin ta tashi ta haye gadon. Dawowar sa kenan Abban ta shiga da sallama, yana tsaye ko zama be ba a tsakiyar falon, zamewa tayi k'asa ta gajshe shi, ya amsa cike da kulawa irin ta da da mahaifi, sannan yace "Adam bashi da hankali sam, bansan haukan nasa ya kai haka ba, nayi magana da Alhaji Ibrahim dan dama saboda a samu damar shirye-shirye nace musu sati biyu, yace in dai akan abinda za'a zuba ne na kayan daki su ba'a yi musu, miji shi yake zuba komai, dan haka ko yanzu muka ce Abdallah yazo zaizo ya dauki matar sa, toh amma na shawarci mahaifiyar ki gata nan, tace dai dan Allah a barki ko kwana uku ne ko sati, akwai abubuwan da zasu karasa naku na mata, dan haka ni yanzu magana bata hannu na, tana hannun mijinki idan har ya amince shikenan, idan be amince ba, gobe yazo ya dauki matar sa." Kamar an buge mata kafafu haka taji maganar ta Abba, ta zauna sosai a dakin ta gaza dago kanta, tana jin Abban ya cigaba da kokarin chanja channel din TV, umma kuma ta fita ta sake dawowa tana nan a zaune bata san me zata ce ba, sai da ya zauna sosai sannan yace " Ki nemi izinin shi idan har ya amince bani da matsala, yadda kukayi dashi sai naji idan Allah ya kaimu, Allah yayi miki albarka ya baku zaman lafiya, ayi hakuri dole baa cin ribar rayuwa sai da hakuri, bani da haufi akanki amma dole sai kin kara hakuri akan wanda kike dashi a dah, Allah yayi miki albarka." Wani kuka ne ya taso mata, a karo na biyu amma na sake bada ita ga wani tamkar yadda ya faru a farko, sai dai akwai banbancin na farkon da na biyu, kuka ta soma yi ba dan bata son auren ba, sai dan tana jin kamar Abban ya gama mata komai, kamar ita shikenan kuma, tasan zata shiga sabuwar rayuwa ne me banbanci da rayuwar gidan Adam, bata san da wani kalubale zata zo mata ba, amma koma wanne iri ne tana fatan ta samu sassauci a cikin sa. Tashi tayi bayan tayi ma Abban godiya ta fito, ta samu umma a dakin ta, tana zaune tana jiran fitowar Asma'un, tana shigowa ta ce " Ki lallabashi ya barki ko satin ne, kinga akwai gyaran da ya kamata ki samu ko? Ki lallabashi dan Allah dan har Yarku ta biya kudi gobe za'ta fara aikinta." " Umma toh me zance masa?" " Kice masa dai akwai shirin da baki gama ba." " Shikenan, zan fada masa." " Karki kauron baki Asma'u na san halin ki, taimakon ki ne." " Ba zan ba Umma." " Yawwa, Allah ya baku zaman lafiya, wai yanzu Abban ku da ya shigo yake cewa Adam na asibiti, kamar wai jininsa ma ya hau a yadda likitoci suka ce." " Allah ya bashi lafiya." " Toh Amin." Tare suka fito da Umman ita tayi dakin Abba ita kuma ta wuce nasu dakin tana sak'a yadda zata tambaye shi dan ta lura zai iya ki musamman yaji cewa Abba ya barshi shi zai yanke hukunci, dakin ta shigo Rauda ta hau waka "Soyayya dadi, tafi zuma dadi, kinga yadda rigar nan tayi miki kyau?" Sai lokacin ta tuna da rigar jikinta, ta harari Raudan kunya na kamata "Yar sa ido, wai me ma yasa ya barki ki kwana ne?" "Ai dakin umma ma zanje na kwana kar na hanaku more daren." "Kyaji dashi." Tace tana isa gaban mirror ta dauki wayarta da ke kai ta zauna ta rubuta masa text message ta tura bayan ta goge ta sake rubutawa wajen sau uku, da k'yar ta daure ta tura na karshen, yana shiga ko minti daya baa yi ba, yayi reply "Ban amince ba, ki shirya gani na." Saroro tayi rik'e da wayar, ta kalli Rauda ta fara fad'a mata yadda sukayi da Abba, dariya ta saka tace mata " Ki kirashi Allah, ki marairace masa zai hakura. " " Zan iya? " " Sosai ma, kiyi sauri kar yace gashi a waje. " Tashi tayi da sauri ta koma dakin umma da ba kowa, ta kirashi tana rik'e da kirjinta da yake faman dukan uku uku, sai da ta kusan katsewa sannan ya dauka yana kishingida bayan ya ajiye cup din da yake shan bakin shayi a cikin sa. " Wife? " " Umm, dan Allah kayi hakuri kar kazo? " "Kar nazo? Me yasa? Gani a hanya ma ki shirya kinji? " " Dan Allah kayi hakuri, na shiga uku. " " Baki shiga uku ba, kina tare dani wanne shiga uku zaki? " " Ba zaka zo ba ko? " " Yanzu kuwa, na ma fito ki shirya ina zuwa sai tafiya, wow I can't wait to have you in my arms, yadda gari yayi dadin nan.... " Toshe bakin ta tayi da sauri tana ganin tsantsar rashin kunyar sa, magiya ta cigaba da yi masa yana sake biye mata, da gaske ta dauka zuwan zai sai da yace mata wasa yake amma kwana uku kawai, tace dan Allah sati, da k'yar da magiya kamar zata masa kuka ya hakura amma sati daya kawai, ajiyar zuciya ta sauke tayi masa godiya, yace baya son godiya sai dai ta bashi wani abun, shiru tayi tana tunanin me zata bashi, yayi breaking shirun nata ta hanyar cewa " Sai kin ce I Love you Abdallah sau goma, shine na kara yarda da sati amma idan baki fad'a ba, kwana uku kawai na yarda. " "Tirkashi. " Ta furta tana rik'e haba, " Zan kashe, idan kin shirya zan kira dan dai Allah kawai dan an fi karfi na ne, da yanzu zan zo wallahi. " " Zan fad'a toh." " Oya, na bud'e zuciya ta, da kunnuwa na. " " I lo... ve.. ueeew. " " Ni a hade. " " I love you." Ta fad'a kamar wdda aka hankada, ta kashe wayar da sauri tana kifa ta, sai kuma ta saki murmushi tana jin wani sabon so da kaunar sa na ratsa ta, so me zafin gaske. Kyalkyalewa yayi da dariya cike da mamakin ta, kunyar ta tayi masifar yawa, dole sai ya koya mata yadda zata so shi, har ta iya kallon cikin idon sa ta fad'a masa irin son da take masa. Shafa kansa yayi yana bud'e gallery dinsa , ya shiga folder din hotunan da yayi mata dazu, ya dinga zooming dinsu yana karewa dan mitsitin bakin ta da yake tunanin yadda chokali yake shiga kallo. Tunanin moments din dazu ya shiga yi, softness din lips din su suka fi tafiya dashi fiye da komai, ga wani warmness da yake ji duk sanda ya samu close contact da ita. RM*    36 ***Dakin ta koma ta samu Rauda har tayi bacci, cike da tausayin ta, ta gyara mata gefen gadon dan daga gani baccin dauke ta yayi babu shiri, wajen kayan ta, ta nufa ta zauna tana rarrabe su tana hade wanda data hada waje daya, har ta kammala sannan tayi shafa'i da wutri taje dakin umma ta dauko katifa ta saka a k'asa ta kwanta ba dan tana jin bacci ba, tunani ta shiga yi, tana ganin komai tamkar almara, kamar ba ita ba, tasan a aji da komai Abdallah ya fita yayi mata fintinkau, bata taba kawo irinsa ko kwatankwacin sa a irin mijin da zata aura ba, sai dai kuma tasan komai hukunci ne na Allah, duk abinda Ya tsara shine daidai. Wato ita rayuwar baki dayan ta challenges ne, daga wannan sai wannan. Juyi ta dinga yi har ta samu bacci barawo ya kwashe ta, me cike da mafarkan Abdallah. Da wuri Ya Hadiza ta kira Umma tace Asma'un ta shirya Amaryar Kb zata zo ta fara yi mata idan Abban ya amince, zuwa umma tayi dakin ta tarar da Asma'un a zaune tana tilawa, Rauda kuma na bacci, "Umma ina kwana?" Ta gaishe ta bayan ta kai karshen shafin, "Lafiya lou, Rauda bata tashi ba!? " Komawa tayi, tace bata jin dadin jikinta ma. " " Yanayin ne, ga watan haihuwar ne kinsan sai a hankalin, idan tana jin ciwo dai tayi magana. " " In Sha Allah. " " Ya kukayi dashi? Abban ku yana jiran feedback "Ya bari, sati daya wai." "Yayi ai, anjima kad'an Amaryar Kb din zata zo, sai ta fara, idan yaso juma'a sai ayi walima kawai." Juyawa umma tayi, tace "Anjima sai kizo ki sanar da Abban dan yanzu be tashi ba." "Ok tam." Fita umman tayi ita kuma ta cigaba da karatun ta, sai da tayi daya cif sannan ta ajiye ta fito zuwa kitchen domin taga abinda zai samu na breakfast kafin Rauda ta tashi dan wasu masu ciki akwai saurin jin yunwa. Wajen tara da rabi Abba ya kirata, ya tambaye ta yadda sukayi ta fad'a masa, Madallah kawai yace ya fita, ta koma daki tana zama Amaryar Kb na zuwa, ta jiyo muryar bakuwa suna gaisawa da Umma ta tashi ta leka ta window. Rauda na toilet tana wanka umma ta kwala mata kira, ta tashi da sauri ta fita, ta gaida Amaryar Kb din ta amsa tana tsokanar ta dan ta gane ita ce amarya, dakin Umma aka kaita Asma'un na zaune a gefe ta hada komai da zata bukata a gefe, Sudanese Scrub/Dilka aka fara mata cike da kwarewa irin ta gogaggun wanda suka san ta kan gyara ciki da waje, ita kanta ta yaba yadda take aikin nata balle ga Rauda a gefe tana sake kurantawa, tun kafin ma a gama na ranar kamshi ya bad'e ko ina na dakin, zuwa gabatowar azahar suka gama lokacin Rauda ta tafi sai Asma'un kawai da Umma a gidan, sallama suka ji ana kwalawa, umma dake zaune a kujerar dake kan hanya ta amsa tana zura kanta waje, Nadeeya ce tare da Fadeela sai wata yar uwar su Abba da take zuwa idan ta bushi iska daga Sumailan take zuwa tayi musu kwana biyu ta tafi, tashi umma tayi ganin masu sallamar tana musu lalle da zuwa, kunya Nadeeya take ji tun sanda adam ya saki Asma'u kamar ita tayi haka take ji shiyasa bata taba iya sakewa da su musamman Asma'un da suke shiri amma yanzu ko doguwar magana basa yi, yanzu ma Hajiya Mama ce tace suzo su kawo Inna balkin daga nan sai ta samu damar magana da Asma'un, ta farko bata so ba amma ganin halin da Adam din yake ciki ta saka ta zuwa, dan akwai hakkin ta sosai akan adam idan bata yafe masa ba haka zai ta shiga masifu dan ta cutar dashi, yanzu ma a kwance yake asibiti tun da ya samu labarin auren Asma'un ya fita hankalin sa har suma yayi. Tashi Asma'u tayi daga zaunen da take, suna shigowa tayi hanyar fita bayan sun gaisa dasu, dakin ta, ta shige tana jin wani sanyayyan kamshi na tashi daga jikinta, wayarta ta dauka ta shiga whatspp tana dubawa, yau be kirata ba tun dazu take dakon kiran nasa amma ko da ta dawo dakin ma ta dauka zata ga missed calls dinsa amma sai taga babu komai, gashi ita ba abin ta kirashi ba, kunya ba zata barta ba, cigaba da dakon kiran nasa ta yi tana fatan ya kirata nan kusa, kwala mata kira Umma tayi, ta tashi ta ajiye wayar ta sameta a waje "Ki shiga wajen su, zakuyi magana da Nadeeya, ashe Adam din ma yana asibiti ba lafiya, Allah ya bashi lafiiya." "Amin." Tace tana shiga ciki, ta samu Nadeeya ne kawai da fadeela a dakin babu Inna balkin, tun kafin ta zauna Nadeeya ta soma mata magana "Dan Allah Asma'u ba dan ni ba, dan Allah ki yafe ma Adam abinda yayi miki dan Allah, soyayyar ki zata haukata shi, he's insane har baya iya tantance daidai da ba daidai ba, nasa yanzu ke matar wani ce, ba kuma na miki fatan sake dawowa wajen Adam a karo na biyu ko da bakiyi aure ba, duk da ina da yakinin ya shiryu, amma bana miki fatan zama dashi. " " Ba komai fa Allah Ya Nadeeya, ni ban rik'e shi ba, Allah ya bashi lafiya. " " Ki yafe masa dan Allah,. " " Na yafe masa duniya da lahira, Allah ma muna masa laifi ya kuma yafe mana, kuma Allah yana son mutum me hakuri da yafiya, ina masa fatan alkairi. " " Nagode sosai Asma'u, hakika Adam yayi rashin mace ta gari, ina miki fatan nasara a dukkan al'amuran ki, ya baki zaman lafiya da zuria dayyiba, idan na samu time zanzo naga dakin ki. " " Nagode sosai. " Tafiya sukayi suka bar Inna balkin anan, daga nan asibitin suka wuce suka tarar da Adam din a cikin mawuyacin hali, Fido ce a dakin kawai mama taje gida ta dawo, bata kula su ba har suka zauna, ta cigaba da danna wayarta dan bata jin ko digon tausayin Adam din musamman da aka ce akan mace ne yake wannan ciwon, jira take kawai ya dawo gida ya fara cin ubansa dalla dalla a hannun ta, dan ta samu tabbacin aikin yayi kuma zai fara aiki ne da zarar ya gama ciwo ciwon son nasa. Turo kofar akayi, ta tashi ta taro su, su Faiza ne su uku, suka hau hayaniya a dakin kamar ba dakin mara lafiya ba, tashi fadila tayi ta fita, Nadeeya ta kalle su tace "Ku dan rage muryar ku dan Allah, baa son hayaniya musamman shi da jinin sa ya hau, hakan zai hana jinin sauka." Kamar wadda tayi magana da duwatsu haka suka maida ta, suka cigaba da shewa shewan su da hirar su mara amfani, ranta ne ya baci ta kalli Fido din tace "Fiddausi ki kaisu waje su zauna baa son hayaniya akan mara lafiya." "A matsayin ki nawa? Mijinki ko nawa? Ko dan kin tsofe a gida baa da aiki sai gantali a kwararo shine zaki min bakin ciki dan kinga ni nayi auren?" "Ikonn Allah,." "Ikon gaske, idan ta miki zafi sai ki kaini gaba. " " Allah ya kyauta. " Tace ta bar dakin da ba zata iya dasu ba, tana fita Hajiya Mama na dawowa tare da yar aikinta ta riko kayan abincin, a wajen ta ajiye kayan ita kuma Maman ta shiga dakin, babu wanda ya nuna alamun mutum ya shigo bare su daidaita kansu, Matsowa tayi tana kokarin duba Adam din amma sai Fido din ta babbake wajen tana tauna cingam ta gefen bakin ta "Fiddausi ya jikin nasa." Tace bayan ta matsa baya "Gashi nan ai." Ta sake juya kanta gefe Dan jim Hajiya tayi a tsaye, sai kuma ta juya ta bar dakin dan mugun shakkar yarinyar take ji, har bata iya yarda su hada ido sam, maganar ta samu Nadeeya da Fadila na yi, taki saka baki sai ma ta saka sallaya daga gefen su tayi zaman ta, su kansu sun gano bata son laifin Fido din ko kad'an, gashi ita kanta bata raga mata bare su. ***Kwana hudu da fara gyaran jikin Asma'u ta chanja, tayi wani irin masifaffan kyau, kamar ba ita ba, ga wani kamshi me sanyin dadi da ke tashi daga jikinta, ko gifta ka tayi sai kaji shi gwanin dadi, tun bayan zuwan da Abdallan yayi be sake zuwa ba dan ya gane zuwan nasa akwai matsala, sai dai waya da chatting da suke kusan raba dare suna yi, a yan kwanakin suka sake shakuwa da juna shakuwa ta ban mamaki. Da safe yana shiryawa yaji ana danna masa door bell, sai da ya gama fesa turare sannan yaje ya bude ya tarar da Ihsan a tsaye har ta soma kosawa da jiran sa ta kuma san yana ciki dan motar sa tana nan, "Ya akayi?" "Anty faty ce tace idan ka shirya ka shigo ciki." "Tazo ne?" "Eh dazu tazo ita da Anty Asy." "Ok zanzo." Ya maida kofar ya rufe, ya karasa shirin sa a tsanake sannan ya fito ya shiga gidan, tun daga shigowa ya hangi manya manyan akwatunan na alfarma a ajiye a gefe, sai wasu yan kwanduna masu kyau da akayi musu ado da purple kyalle, zama yayi yana kallon kayan, suka gaisa sannan Anty Faty tace ya duba kayan ne, anjima zasu je su kai da rana. Sama sama ya kalla dan ba zai iya tsayawa kallon komai ba, yace yayi kawai suyi duk abinda suke ganin ya dace, daga nan ya wuce ya gaida Mami tayi masa maganar events din da zasuyi idan Asma'un ta tare, sama sama itama ya jita dan ba wani interest yake dashi akai ba dan ma sun kafe dan har sun yi gayyata da komai hatta hall da komai dai sun gama tanada, dakin Mom ya shiga ya sameta a gefen gado me aikin ta na shirya mata kaya a cikin wardrobe din. A k'asa ya zauna ya gaishe ta, ta amsa masa cike da kulawa sannan ta tanbaye shi Asma'u, kamar ya bud'e rami ya shige dan kunya dan tunda aka fara maganar bikin bata ce komai ba, ya zata ma bata sane da komai ashe tana ankare, sai tsabar kara da kawaici irin nata da ta bar Mami akan komai dan tasan zatayi abinda ma yafi natan, hatta Faty da Asy kannen ta ne amma yadda suka shaku da Abdallan zaka dauka ma yayyen sa ne, shima kuma yana respecting dinsu kamar yayyen nasa na gaske. Nasiha ta hau yi masa akan aure da abinda ya dace mutum yayi a matsayin sa na wanda Allah ya bawa shugabanci, sosai maganganun suka ratsa shi, ya kara fahimtar aure ya wuce duk yadda mutane suke tunani ko hasashe,godiya yayi mata ta dinga saka masa albarka sannan ya baro dakin bayan ta bashi dabinon ajwa guda bakwai tace ya cinye su maganin sihiri ne. Har ya bud'e motar sa zai shiga ya tuna da gift din Asma'un da yake so a tafi mata dashi, komawa yayi part dinsu ya dauko box din me dauke da spare car key din da ya siya mata sai alkur'ani me girma me kyau da wani littafi akan al'adar mata a musulunci. Anty Faty ya kaiwa yace a hada shi car key ne, kafin su tafi zai aiko a kawo motar, harda rawar ta, ta taka ya girgiza kai kawai ya fice yana mamakin karamcin su. _ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_ _ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ _BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_ _KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._ _WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH _KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_ _SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰 _BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍 _MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰 _HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️ _NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍 ***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_* *RM*       37-38 Barka Da Sallah! ****Jikinsa sosai ya matsa masa,ga effect din shaye-shaye da ya kusan taba masa kwakwalwa ga sam Fido ta hana kowa rabar sa, ita kadai take kula dashi shima ba sosai ba sai zaman hira da shewa ita da su Faiza, duk mama ta rame ta zama abun tausayi a dan kwanakin, ita dama rayuwar duniyar nan baki dayan ta wa'azi ce, tasan tayi kuskure a tarbiyyar Adam in da ta dauki son duniya ta dora masa bata ganin laifin sa, duk da deep down tana jin kamar ba haka ya kamata tayi ba amma so ya rufe mata ido, bata tsawatar masa ba bare har yasan daidai da akasin hakan. A darare tazo yau ma kamar kullum dan yadda take tsoron Fido ko mutuwar ta albarka, abinci ta kawo masa tana kuma son ganin sa taga halin da yake ciki amma bata iya dogon zama a dakin sai dai ta koma waje ta tsuguna har dare sannan ta tafi gida, a zaune ta hange shi yana kallon kofar shigowa ya rame sosai yayi baki, cup ne a hannun Fido din tana bashi tea yana sha amma be ce mata komai ba, murmushin jin dadi ne ya subuce ma Hajiyan ta karaso da dan saurin ta amma sai taga kamar Adam din be damu da ganin ta ba, sai ma kallon Fido din yake da ta sauke cup din hannun ta, ta tashi ta ajiye a saman dan madaidaicin fridge din dake dakin, maimakon yayi magana sai ya zame ya kwanta yana maida idon sa ya kulle hakan ya daki Maman sosai har taji tana kokarin zubewa a wajen, dafa karfen gadon tayi ta kasa cigaba da tafiyar, sai addu'a da ta shiga karantowa har ta samu sauki a yadda take ji. "Sannu da zuwa." Fido tace tana karbar kayan hannun ta, ta kaisu gaban gadon daga gefe ta ajiye dan dama abincin gidan Maman take jira ta kwashi girki, dan dama ita ke cinyewa dasu Faiza kullum. Toilet tayi shigewarta bayan ta ajiye ta bar Maman tsaye ta kafe Adam din da ido wanda yake motsi kad'an amma idon sa a kulle kamar me bacci. "Adam?" Ta kirashi cikin muryar rada rada kamar wadda bata so a ji, motsi yayi ya juya dayan bangaren be ce mata komai ba, rik'e bakin ta, tayi da sauri kuka na kokarin kwace mata, shigowar likita da wata nurse ya sakata daurewa suka gaisheta a mutunce sannan ya matsa ya duba Adam din ya tambaye shi jikin sa, kai kawai ya nuna masa yace ciwo yake? Ya kada kai alamar eh amma be bud'e idon ba "Zai daina, sake gwada bp dinsa sister." Likitan yace yana daukar result din test din da akayi masa ya hau dubawa, bp ta sake gwada masa ta fad'a ma Dr din ya daga kai kawai ya chanja masa wani maganin sannan suka fita, sake matsowa Mama tayi ta sake kiran sunan sa, gani tayi ya dame baki alamun ta dame shi, ya yamutse fuska ba tare da ya tanka ta ba "Sun ce kar a matsa masa da magana saboda ciwon kan nasa." Kofar toilet din ta kalla dan bata san ta fito ba, da sauri tace " Toh toh, bari na jira a waje toh. " Ta juya da sauri ta fita daga dakin, tabe baki tayi ta matsa gaban gadon tana leken sa " Kice ta tafi bana son ganin ta. " " Hajiyar ka ce fa. " " Ita din. " " Ok oo, nawa ido kunfi kusa. " Ta bar wajen tana jin dadi a ranta, ta samu abinda take so, Adam sai ya raina kansa ya gwammace be wulakanta ta ba. Zaman kurame Mama tayi ita kadai har su Fadila suka zo sannan ne ta dan saki ranta, suma duk basu dade ba suka tafi dan ba zasu iya zaman takaicin Fido din ba, Nadeeya ce kadai take taya Maman zama idan ta gama aikin ta, sai dare suka komawa gida, tana jin tausayin Maman musamman yadda Adam din ya zama a yan kwanakin nan, kamar be san ta ba, ba kuma ya zancen kowa sai Fido din amma ko su basu ishe shi kallo ba, kamar ma zuwan da suke takura shi sukeyi. Washegari aka sallameshi Fido bata fadawa kowa ba, suka tattaro suka dawo gida, sai da Mama ta dauki kafa taje asibitin sannan ta san sun dawo, hakan yayi mata ciwo sosai ta dawo gida da takaicin amma kuma ba zata iya magana ba, yadda take ji kamar an saka abu an daure mata baki haka take ji, ko ta yi yinkurin yin magana idan taga Fido sai ta k'asa taji wani bala'in tsoron ta. Bata shiga gidan nasu ba, sai kawai ta wuce dakin ta, ta kwanta ciwon bayan da ya matsa mata kwana biyu da kafa na sake damun ta sosai. ***Anty Faty, Anty Asy sai kannen Mom su biyu da wata sister din Baba Alhaji sune zasu kai kayan Abuya, MD ne akan komai duk shirye shiryen da za'a yi da duk abinda ake bukata, gidan ya soma cika da yan uwa na kusa da na nesa dan ma katin gida ne ba zaka gane cikar ba saboda ba'a cinkushe waje daya ba, tsayawa wajn fadar haduwar kayan bata baki ne dan basu duba matsayin Asma'un na bazawara ba, komai kamar na auren fari haka sukayi mata dan ban da su na cikin gidan babu wanda ya san da maganar duk yan uwa, kuma su din ma ba zasu taba fad'a ba dan Mami da kanta ta ja musu kunne akan maganar dan ko Baba Alhaji idan yaji zai iya fad'a sosai dan tun ranar farko shi kansa ya tsawatar musu domin ya san halin mata da kananun maganganu akan abinda yake wata al'adah ba addini ba, manzon Allah SAW ma Nana Khadija ya fara aura kuma bazawara ce dan haka ba sabon abu bane ba kuma haramun bane face ya kasance sunna mai kyau wanda hausawanmu suke ganin kaamr be dace ba saboda wata al'adah tamu mara asali da tushe. Mota biyu sukayi, motar Anty Faty sai ta MD sai guda daya da aka zuba kayan a ciki wanda suka kasance akwatuna bakwai masu kyau da tsari, babu karya ko fariyar akwatuna a ciki amma kuma an kashe kudi daidai da arzikin su dan babu karamin abu a ciki komai me tsada ne da aji kuma na amfani. Bayan tafiyar su ya dawo gidan a gajiye dan ko magana be samu sunyi da ita ba tun da ya fita, bayan ya bayar an kawo motar ya shiga wata sabgar wadda ta cinye duk lokacin ranar tasa, be zauna ba dan baya jin ko ruwa ya saka a cikin sa, har zai wuce part dinsu ya tuna da kiran da Mom take masa, sai ya juya akalar sa zuwa shashen cikin gidan. Cikin babban falon babu kowa da alamun tafiyar su Anty Faty ta saka aka tashi dan ga alamun kayayyakin su nan a barbaje a falon, wucewa yayi zuwa ciki a daidai corridor din da zai kaishi dakin Mom din Amira, Ihsan da wata cousin dinsu Siyam na zaune suna magana k'asa k'asa, har zai wuce sai yaji kamar an kira sunan sa, sai ya dakata yana tsaye curtains din dake wajen ya dan kareshi "Ai ya Abuya dai wallahi ya cika abu local, bazawara dai?" Siyam din tace tana tabe baki "Eh haka mukaji mu ma." "Kuma su Baba suka barshi?" "Eh, baki ga ma fad'an da sukayi mana ba, kar suji kar su gani Mom da Mami kuwa har da cewa idan suka ji zancen sai mun gwammace kida da karatu." "Tab! Amma gaskiya ya kwafsa, zamu ganta ai gobe kuwa ko ta hadu, ni duk kun saka bikin ya fita a kaina wallahi." " Muma ai, ni wallahi dama Ya Feena ya aura tafi wallahi." " Wallahi, ga ta yar gayu sosai, kuma har yanzu tana son shi wallahi, cewa ma tayi ba zata zo ba, ga bikin ko dan dinner babu,wai walima kawai kamar wasu malamai." " Hmm, sai dai bikin Ya MD, amma wannan kam sai dai mu yi kawai." " Wai kyakkyawa ce!?" " Bamu santa ba ai." " Tab!" "Dan Allah amma karki fadawa wani, ana ji an san ni da Amira ne, kuma kinsan shi zai iya karya mana kafa akan haka wallahi." "Bama zan fada ba." "Ku sameni a part dina." A razane duk suka dago, suka mike a lokaci daya amma tuni ya bar wajen ko kallon su be ba, rik'e kai Amira tayi tana kallon Ihsan da ta fara kuka wiwi, Siyam kuma kamar ta saki zawo a wajen tana wurga ido tana neman hanyar barin gidan. "Mun shiga uku mun lalace!" "Wallahi guduwa zan ba zan zauna ba." "Wallahi karki gudu, kika gudu har gida zai turo Ya MD wallahi, muje kawai." Amira tace zuciyarta fal tsoro amma taurin kai ya hanata nunawa, Ihsan kuwa kuka take har suka isa part din, suka tsaya cikin tsoron wanda zai fara shiga, Amira ce tayi karfin halin bugawa, shiru sai ta kama handle din ta bud'e, suka shiga da sanda amma babu kowa a falon sai takalminsa da ya cire da hular kansa a saman center table, a k'asa suka zube a tsorace. "Malama ki daina kuka dallah." Ta zunguri Ihsan tana hararar ta, kin shiru tayi sai dai ta rage sautin sosai. Fitowa yayi ya sauya kayan jikin sa zuwa jallabiya fara kansa sanye da hular da ake kira da tashi kafiya naci alamun sallah yayi, waya ce a sakale da kunnen sa yana magana k'asa k'asa, "Send me the address, I'll come and pick you." " Owk, sai nazo." Yace yana zama a kujera, ya ajiye wayar a gefen sa ya dauki remote ya rage karar tv din, satar kallon sa suke dukka ya tamke fuska babu alamun dariya ko kad'an, " Dan Allah kayi hakuri, wallahi ba zamu sake ba. " Ihsan ta fad'a cikin kuka, be ko kalli in da suke ba bare yayi magana, dama kuma ya riga ya santa da shegen tsoro ga bakin tsiya, takardun da yazo dasu ya karasa arranging tas suna durkushe a wajen sai da ya gama sannan ya juyo yana kallon su daya bayan daya, dududu ba zasu wuce sha takwas ba amma sun iya zama su tsara zance haka kamar wasu iyayen mata, ji yake kamar ya hadasu dukka yayi musu shegen duka amma ba zai iya ba, fushin sa kadai yasan ya wadatar ba zasu sake gobe ba, yara ne yanzu duk sun zama sai a hankali, ba zai bari ire iren maganganun suyi tasiri ba, har Asma'u ta samu matsala da family dinsa, ba ita ta sakawa kanta hakan ba, babu kuma wanda zai ga laifin ta domin ta zama bazawara, Allah da kansa ya halasta saki idan har shine maslaha akan zaman auren. "Ba zan maimaita abinda naji kuna fad'a ba, naji komai kuma this should be the first and the last da zan sake jin irin wannan maganar a cikin gidan nan, wallahi sai na mugun saba muku, mutanen banza!" "Kayi hakuri." Amira da yake kallo tace tana sunkuyar da kanta. "Ku tashi ku bani waje!" Da sauri suka mike suka fice, ya maida kansa jikin kujerar yana lumshe idon sa, kafin anjima ya fita, part din da zai zauna yana cikin gidan amma ta baya sosai, an gama gyara komai ko yace MD ya gama gyara komai dan kwana biyu rabon da ya shiga ya duba, so yake idan zai fita ya shiga ya gani ko akwai abinda yake bukata da baa saka ba. Da gudu gudu suka karasa shiga dakin su, suka kwashe da dariya Amira na kwaikwayan Ihsan da take kuka, duka ta kai mata ta goce tana sake kyalkyalewa "Shegen tsoro kamar farar kura." "Ba zaki gane ba, ni zai fi cin uba dan nafi zakewa, ke kuwa taku tafi zuwa daya zai iya daga miki kafa, Siyam kuwa be ce mata komai ba." "Amma yasin na tsure da naga fuskar sa, wai gumurzu, shi fa dama Ya Abuya baya dariya asalin sa." "Yana yi wallahi, sai yaga dama amma nasan yana ma Anty Asma'u." "Hadda su Anty?" "So kike yaci ubana kenan ko?" "Ya MD zai hada ka dashi ya sassamaka wallahi,." "Yayye Maza ko wahala." Siyam tace tana dariya "Da wuya da dadi, amma ana cin uban ka daidai gwargado,." " Ni ko da yake bamu da maza manya, bansan wannan ba. " " Ai ki gode Allah, ta wani bangaren wallahi, mu fa idan suka ga dama kallo ma bamu isa muyi ba, sai kiga ance Ina books din ku. " " Tabdin, kuna fama. " " Kin shiga tarko kema, yanzu Ya Abuya ba zai barmu shigar masa gida bama wallahi, ni dama ban saka aka ba, dan zai iya cewa mu daina masa sintiri a gida, da dai Ya MD ne yawwa. " " Dama gari banza ma hana mu zai, bare ya kamamu dumu-dumu cewa zai gulma muka zo. " " Allah dai ya rufa asiri wallahi, sai a kiyaye gaba. " Ihsan da sai a lokacin ta dawo daidai daga mugun tsoron da taji tace sannan tace " Bari naje wajen Mom na dawo. " Ta fice ta bar su su kadai **** RM 39-40 ***Alwala ya tashi ya sake daurowa domin ance alwala tana wanko zunubai shiyasa baya taba hada alwala daya a salla biyu, masallaci ya wuce na cikin gidan ya hangi motocin da suka je kai kayan a harabar gidan hakan ya tabbatar masa da sun dawo kenan. Bayan sun idar ne suka jero da MD yana fad'a masa yadda zuwan nasu ya kasance, yana jin sa har ya kai karshe kafin yace masa "Thank you for everything." "Me akayi!?" "Ban sani ba." "Toh shi na gani." "Muje naga gidan kafin na fita, nasan ma an gama komai." "Eh an gama gaskiya, console ne kawai ya rage zasu kawo shi gobe, shima ba wanda aka zaba suka kowa ba shiyasa ma da tuni an gama hada komai. " " Owk, that's good. " Rage murya MD yayi kamar wanda zai rada yace " Plate dina ya dawo gidan ka. " Murmushi yayi yana bud'e kofar, " Gidan zaka dawo gaba daya da zama kawai. " " Rufa min asiri, yafi karfi na. " " Zakayi bayani." Ya wuce ciki ya barshi a falon yana dariya, duddubawa yayi ransa fes yana jin kamar ya bud'e ido ya ganta a gabansa a cikin gidan, komai yayi kyau sai kamshi ke tashi ko ina, da k'yar ya baro dakin ya karasa dudduba sauran dakunan da toilets sannan suka tafi, ya shirya zuwa kananan kaya riga da dogon wando ya dauki hanyar gidan kunshin da tace masa taje a unguwar gidan Ya Hadizan.    A hankali yake driving din cikin wani yanayi ya saka wakar Westlife cikin raguwar sauti sosai har ya karasa address din data turo masa, yayi parking daga gefen gidan ya fito daga mazaunin driver ya dawo na gefe ya kwantar da kujerar baya sosai ya kwanta ya ciro wayar sa ya tura mata da text message "I'm out!" Karasa mata ake dan yau ne karshen gyaran jikin da Amaryar Kb take mata dalilin masu kawo kayan yasa ta taho nan din, sosai ake mata gyaran yau dan tun safe ake abu daya har da wasu hadaddun turarukan tsuguno da na wanka. Babu in da baya kamshi a jikin ta ga wani santsi da sulbi da fatar jikinta tayi wanda ita kanta da kanta ta san babu karya ta hadu. Kunshin take turarawa yanzu a cikin wani rami aka saka turaren ta zura kafarta da hannun ta bayan kunshin yayi, sai ga text dinsa, reply tayi masa ta ajiye wayar a gefenta. Cikin mintunan da basu gaza talatin ba Amaryar Kb ta gama hada ta tsaf, dama tun jiya tayi gyaran gashi sai turara su da aka yi yau din. Doguwar riga ce abaya a jikinta baka, ta saka flat shoe dinta ta dauki yar karamar hand bag dinta ta saka wayarta tayi ma Amaryar Kb sallama ta fito tana cike da kunyar sa, hango motar tayi daga gefe chan bayan yaga fitowar ta yayi mata fitila, ta nufi wajen kai tsaye ta zagaya bangaren me zaman banza ta bud'e, duhun da ya mamaye wajen ya hana mata ganin sa, ta sako jikinta sosai sai ji tayi an riko ta, ya jawo ta jikinsa gaba daya kamshin ta na ratsa jiki na jijiyoyin sa, wani irin cool kamshi me sanyin dadi, "Subhallah!" Ya furta sanda ya ji ya kama hannun ta da ya kara taushi sosai har wani tubus tubus yaji yayi, "My wife." "Ashe kana nan, ban lura ba." "Ina sane na dawo nan din ai, I just wants to hold you, ." Yayi mata whispering yana dan cizon gefen kunnenta, a saman chest dinsa ta dora fuskar ta tana murmushi k'asa-kasa, hakan da yayi ya haifar mata da kasala kwarai, kokarin tashi tayi daga jikin nasa ya sake rukunkume ta, ya manna ta da jikin nasa sosai yayi crossing kafarsa da tata waje daya, ya dago da ita a jikin sa ya jawo kofar motar ya rufe ta. "Zaki rakani wani waje? Inaso naga kunshin da komai da komai, yadda zan ga nawa ya kamata na biya matar da ta gyara min ke." " Ya Hadiza na jirana." " Aina?" " A gida, kasan gobe ne walimar." " Gaskiya tayi hakuri, idan ba haka ba sai kawai mu wuce gida gobe sai na kawo ki walimar. " " Wai,.. su Rauda su sakani a gaba kenan, yau da goben duk daya ne." " Za'a min wayo, ni dai gaskiya a'ah, hakuri na ya kare. " Shiru tayi bata sake cewa komai ba, yayi murmushi kawai ya fito ya koma wajen driver ya kunna motar suka bar layin. Wayarta ta ciro daga jakarta taga missed calls din Ya Hadiza, ta kirata tana ayyana me ma zata ce mata? Tana dagawa kuwa tace "Asma'u shiru wai baku gama ba har yanzu?" "Na'am, am ammm mun gama." "Ok, bari Abbati yazo ya dauko ki toh." "A ah ba sai yazo ba, mun taho ma amma wai zamu biya mu siya wani abun sai mu taho gidan." "Oh toh shikenan sai kun dawo." Ta kashe wayar, kallon sa tayi shima ya kalleta yayi mata dariya "Kin cika kunya, kice kin wuce gidanki kawai amma shine kike ta kwana kwana ko?" "Ba zan iya ba." "Da ma ni kika bawa na fad'a mata ai." "Kamar gaske." Tace tana dariya, dariyar ya saka shima ya maida hankalin sa kan driving din da yasan ko me yasha ba zai taba iyawa ba, shi din ma kunyar ce dashi kamar itan, a wajenta ne kawai yake ajiye kunyar a gefe shi kansa kuma be san dalilin da ya saka baya jin kunyarta ba sam. "Your hand is very soft." Ya kamo hannun ya dora a saman geer, ya dora nasa akai yana murzawa. "Me ake saka ma hannu ya zama haka ne? Kinji kuwa?" "Uhum." "I love it, I love everything about you in particular." "Ka daina fasa min kai." "Ba wani hyping, it's the truth, Alhamdulillah Ya Allah!" Sautin murnushin ta kawai yaji, yayi murmushin shima yana jaddada godiyar sa ga Allah, yana kuma addu'ar samun nutsuwa da kwanciyar hankali a tattare da ita. Office din nasa yau ma suka zo, yayi parking a daidai in da sukayi last, ya kuma kama hannun ta suka shiga ciki kamar wanchan lokacin amma wannan babu kowa kamar wanchan lokacin, bud'e kofar yayi suka shiga ciki. Ya kunna hasken office din, sai a lokacin ya ganta sosai, ya bud'e baki ba tare da yace komai ba, kamar wadda aka sauyata da wata ta daban, ga wani fresh da ya ga ta kara hade da wani shihirtaccen kyau na ban mamaki, be san lokacin da ya rungume ta tsam a jikin sa ba, ya dinga shakar kamshin jikinta. Ji yayi kamar zai zame a wajen, ya cikata yana rik'e hannun ta, ya bud'e wata kofa dake gefe a cikin kofar, suka shiga ciki. Dan karamin gado ne wanda be fi yaci mutum biyu ba a ciki, sai tarin wasu kaya a gefe kamar takardu ne ma suka fi yawa. Wajen gadon ya kaita ya zauna yana jawo ta saman kafarsa, ya zaunar da ita yana fuskantar ta, kanta a k'asa ta kasa bari su hada ido dan ta lura kamar akwai matsala a yanayin sa. "Husnaaa." Ya kira sunanta cikin muryar sa me zurfi, kasa dagowa tayi ya sake kiranta a karo na biyu muryar sa na sake shigewa ciki sosai, dagowa tayi a hankali ta kalle shi tayi saurin sauke kanta k'asa ganin yadda fararen idanun sa suka shiga ciki sosai kamar wanda ya sha wani abu, gabanta ne ya hau dukan uku uku tunawa da tayi komai zai iya faruwa, bata manta kalar wahalar da tasha ba a hannun Adam duk da ta san ba zata taba shan irin ta ba amma kuma har ta gama zaman gidan Adam bata daina shan azaba ba, duk da nashi har da tsana amma ta taba karantawa wata macen har sai tayi haihuwar farko sannan take samun sauki, tsoron ta ne ya karo kokarin da taji yana shafa ta yana kokarin lallai sai ya saka idon sa a cikin nata "Hakuri na ya kare Husna, I can't, I just can't! Ba haramun bane, ba laifi bane." "Shikenan!" Ta furta zuciyar ta na tseren gudu, ta saddakar yau me rabata da Abdallan sai Allah, a hankali cike da nutsuwa da kamala ya shiga biyar da ita cikin salon sa me matukar kayatarwa, bata san lokacin da ta saki jiki ba, har ya samu nasarar maida ta kasan shi, yayi mata rumfa akanta yana hade bakin su waje daya, bayan ya gama furta mata kalamai masu ratsa zuciya. A duk yadda tayi tunani ko hasashen abun ya wuce nan, soyayya ce me taushi da dadi ta danne duk wani ciwo da wahala da take tunani da hasashe, ba zata ce babu ba, musamman saboda gyaran da tasha na musamman amma kuma be barta ko da na sakan daya bane bare har hakan yayi tasiri a gareta, she's so gentle cike da charisma, full of energy amma ba na banza ba irin na Adam, a nutse yayi koman sa bakin sa dauke da addu'ar da annabi Muhammad SAW ya koyar damu a lokaci irin wannan. Sannu yake ta faman jero mata babu kakkautawa, hade da saka mata albarka, tana kwance a saman kirjin sa hannun sa na zagaye da ita dayan kuma ya tura shu cikin gashin ta da ya wargaje yana tattaro shi, santsin sa da kamshin na shigar masa hanci. Sai da ya tabbatar ta dawo daidai sannan ya tashi ya nufi toilet ya hada mata ruwa me dumi sosai, ya zo yace ta taso,idonta a rufe da ya shigo dan wata sabuwar kunyar sa ce ta sake kama ta, har bata jin zata iya hada ido dashi , ga Ya Hadiza da tasan ta gaji da jiranta, da wanne ido ma zata fara shiga gidan su me ma? Za'a iya harbo jirginta wallahi, dan mara gaskiya ko a cikin ruwa gumi yake yi, bare iyayen da suka haife ka duk motsin ka sun san me kake nufi. Da taimakon sa ta tashi tayi abinda yace din, ya tayata suka gama, kansa tsaye yake komai ko kunyarta baya ji, tayi ta jinjina hakan a ranta dama namiji in dai anan bangaren ne toh basu da kunya ko kad'an, kamar ba zai aikata ba, nan nan kawai yake da ita har ta gama ta saka kayan ta, ta dawo cikin office din ta zauna ta barshi a ciki, sai gashi ya fito rik'e da riga a hannu be saka ba, tayi saurin dauke kanta dan bata saba ganin namiji a haka ba, ko Adam iyakar ta dashi ya shigo yayi abinda zai ya kara gaba, yana lura da ita kunya taji, sai yazo ya tsaya a gabanta ya mika mata rigar yana marairace mata "Help me pleaseeee." "Um Um." "Kina so mu kwana anan? Dan dama ni wallahi bana so ki koma." Da sauri ta tashi zata karbi rigar ya rik'e yana girgiza mata kai " Na ma fasa, anan zamu kwana kawai. " " Dan Allah. " " Zo ki kwanta ki huta sai gobe, ba zan iya fita yanzu ba. " Ya juya ya shige ciki, tsaye tayi a wajen cike da tunanin abinda ya kamata tayi, shiru be fito tayi tunanin da gaske yake kawai sai ta bishi, ta same shi a kwance a gadon be kuma saka rigar ba. "Please dan Allah." "Um um, bacci nake ji, zo mu kwanta, inaso naji heartbeat din matata. " " Dan Allah. " Lumshe idon sa yayi yana tariyo abinda ya faru yan mintunan da suka wuce, murmushi ne ya subuce masa, ta kalli yadda yake murmushin sai ta samu kanta da murmusawa itama, tana tsaye sai da ya gama yangar sa sannan ya tashi yana mika mata rigar "Samun kafin na chanja shawara." Da sauri ta karba ta shiga saka masa, duk da ya kere ta nesa ba kusa ba a tsayi, amma babu yadda ta iya dan ba zata zo ta kwana ba saboda kunyar da zataji. Tana gama saka masa ya rungume ta yana jujjjuya su a dakin. Da k'yar ta samu ya dauki car key dinsa suka fito, suka tafi. Ya tsaya ya siya mata dinner da wasu tarkacen kayan sannan ya wuce da ita gida. A kofar gidan ma sai da tayi da gaske sannan ya kyale ta, ya fito ya raka ta har cikin harabar gidan nasu, ya kama hannun ta ya saka mata kudi masu yawa "Kudin kunshi da kitso, MD zai kawo drinks da safe, da sauran abubuwan da za'a bukata, da daddare zanzo mu wuce. " " Allah ya kaimu, thank you so much, jazakallah bhi khair Allah ya kara budi " Murmushi yayi mata yana me jin dadin addu'ar, ya amsa da Amin k'asa k'asa. Har ta juya ta soma tafiya ya tsayar da ita, ta tsaya tana juyowa, ya taho suka hadu, ya rankwafo zuwa daidai saitin kunnenta "You are very sweet." Ya furta in a romantic voice and way, da sauri tayi ciki kamar wadda aka tunkuda, ya kyalkyale da dariya ya juya ya bar gidan yana shafa kansa, yana jin sa kamar wanda yake yawo a saman gajimare! RM    41 ***Duk suna tsakar gidan wannan karon ma, dan duk a gida zasu kwana saboda shirye shiryen ranar goben, kamar wadda aka sarawa kafa haka taji, amma sai taga kamar basu fuskanci komai ba, sannu da dawowa suke mata dukka sai Ya Hadiza da ta dan harareta cikin sigar wasa tace "Kika barni ina ta jira." Bud'e baki tayi zatayi magana ta katse ta Kuma "Jeki ajiye kayan kizo dan Allah, gwara a kitse kan kafin gobe dan ba lallai na samu damar yi miki ba." "Wai kitso zakuyi Ya Hadiza!!?" Rauda tace tana waro ido "Ba gwara a kitse shi ba, da ta barshi haka." Umma ta sako baki tana daga gefe tana duba sauran kayayyakin da aka siyo "Allah gwara a bar mata, ai yafi yasha mai tayi parking din sa wallahi." "Kufa kun fiya shiririta, kitson be fi umma?" "Allah Umma gwara dai ta barshi haka daga baya sai tayi kitson." " Ke Asma'u me kike so?" " Zanyi daga baya umma." Tace da sauri dan tabbas a yadda kan nata ya koma sai duk sun harbo jirginta, shiyasa da Rauda tayi maganar taji kamar taje ta rungume ta saboda tsabar dadi. " Ai shikenan, sai a barshi a hakan ai." Daki ta mike ta shige da sauri, ta sauke ajiyar zuciya tana sakin murmushi, da ba dan Rauda ba da ta sha kunya yau, dan har lokacin a jike gashin yake da ruwa gashi kuma duk sun san da maganar gyaran kan zasu ce Ina ta samo ruwa akanta, toilet ta shiga da sauri bayan ta dauko hand-dryer dinta a cikin kayanta da Hidaya ta hade mata su waje daya, ta shiga da ita ciki dama rechargeable ce ta shiga busar da kan. Sai da ta gama sannan Hidaya ta shigo dakin ta ajiye abu ta fita, sauya kayan jikin tayi ta fito wajen su, ta samu sun koma cikin falon saboda wutar da aka kawo, tana zama wayarta tayi kara, Abdallah ne yake kiranta, da sauri ta kashe hasken wayar tana kallon su, sake kira yayi bayan wanchan din ya katse, "Ki daga mana, ba kiranki ake bane!? " Wata number ce take ta kirana, idan na daga sai ayi shiru shi yasa bana dagawa kawai." "Ki sakata black list kawai." Ya Hadiza tace tana cigaba da hirar da ta dauko Text message ya turo mata jin bata daga ba "Baby.. How are you feeling? Hope babu wata matsala ko? Take care of yourself.. xoxo" Murmushi tayi kawai ta sake kifa wayar aka cigaaba da hirar da suka kusan kai dayan dare sunayi bayan sun gama kallon lefen Asma'un a karo na kusan uku, sai an gama sai a sake tuno kaza sai a sake budewa cike da yabawa, Rauda tuni ta sulale tayi bacci sai ita da Ya Hadiza, Ya Amina, Batul da Hidaya. Ita ta fara tashi dan gaba daya kawai daurewa take amma gabobin ta ciwo suke mata sosai, wanka ma take so ta fara yi kafin ta kwanta amma kuma bata jin zata iya, so kawai take ta ajiye hakarkarin ta a k'asa ko zata ji saukin jikin nata. Tana kwanciya bacci me nauyi ya kwashe ta, cike da mafarkin Abdallah. Babu wanda yayi mata maganar motar ta, yadda suke shirya dama sai da safe idan an tashi, bayan an yi breakfast sai kuma ayi breaking mata news din, Abbati ne gaba a tsara hakan umma dai bata ce komai ba a lokacin sai murmushi kawai da take cike da jin dadin yadda rayuwar Asma'un take sauyawa zuwa wani bigire na daban. Da safe ta tashi da karfin jiki dana zuciya, ranta fes kamar an mata bushara da gidan aljanna, har yan uwan umman sun iso saboda tayin aikin abincin da za'a yi tun duku-duku sai karin ma'aikata uku da aka karo, tana nade akan gado tana kallon duk abinda yake wakana Hidaya ta kawo musu fanke da Lipton suka ci, sannan ta dauki waya ta masa reply din text din da yayi mata jiya da daddare. "I'm fine, how about you?" Ta rubuta masa ta ajiye ta mike ta fita. Yana tsaye kusa da Baba Alhaji da yake nuna masa wata takarda a harabar gidan text dinta ya shigo, cigaba da abinda suke yayi har sai da Baban ya sallame shi bayan ya saka hannu a takardun sannan ya wuce zuwa chan gate ya samu bencin da gateman dinsu yake zama ya zauna ya zaro wayar ya shiga message yayi mata reply yana daga kansa sama, sanyayyiyar iskar safiyar na busawa cike da wani yanayi da be taba riskar irin sa ba "Alhamdulillah, thank for yesterday, kin biya ni har da kari ma, Allah yayi miki albarka ya barmu tare har abadah." Sosai yayi relaxing a wajen har rana ta soma isowa in da yake, ya cigaba da shan ta kafin ta soma dukan fuskar sa, sannan ya tashi ya koma ciki ya hau shiryawa, dan so yake ya gama komai yau da wuri ya dawo gida, ana magriba zai je ya dauko matar sa ba zai jira ba, ba kuma wani zai wakilta dauko masa ita ba, shi kadai ya isa. Dawowa dakin tayi da zumudin ganin reply dinsa, ta dauka tana karantawa tana murmushi, sai kuma ta lunshe idon ta, ta zauna tana sake maimaita text din tana tuno tsadaddun kalaman sa na jiya da duk in da ta motsa sune suke mata amsa kuwwa a kanta, bata san haka soyayya take da dadi ba sai a wannan lokacin da ta hadu da gwarzo tamkar Abdallan, wanda ita kadai ta san wannan bangaren nasa, idan ka ganshi a haka zaka rantse ko hannu aka saka masa a baki ba zai ciza ba. ***Sosai hidima ta kankama kan kace menene gidan ya kacame sai kaya kaya kawai ke tashi, tayi wanka ta saka wani lace me kyau golden da yellow, wanda ya haska ta sosai ta fito amayar ta sosai ba kamar bikin Adam ba, tun da ta fito tsakar gida mutane sukayi mata cha, kinyi kyau kinyi kyau. Murmushi kawai take har ta isa wajen da kanwar Umma Anty sadiya take a zaune, ta durkusa a gabanta tana mata magana sai ga Hajiya mama sun shigo da ahalin ta, wani irin sak tayi ganin Asma'un kamar wadda aka sauya ta da wata ta daban, bata jin dadin jikinta tunda Adam ya dawo gida dan ko lekowa be yi ba tun bayan dawowar sa bare yazo ya gaishe ta, sau biyu tana shiga gidan bata ma ganin sa sai Fido tace mata yana sama baya son hayaniya, abun yana damun ta har ciwo tayi amma haka ta hakura, kamar ba zata fito yau din ba ma amma ta daure sai kuma tazo taga Asma'un sai duk taji damuwar ta, ta karu da tunanin damar da ta kwace musu ita da Adam din, Allah yayi musu gamdagatar amma suka wofintar da ita har ta kubce musu. Kowa sai da ya lura a wajen da yadda take kallon Asma'un kamar ranar ta soma ganin ta, ita kanta Asma'un sai data tsargu da kallon ta shige dakin umma da saurin ta sai a sannan Hajiya Maman ta dawo hayyacin ta, ta hau wayancewa cike da borin kunya. Daki umma tabi Asma'un tace mata ta dinga addu'a saboda baki, ta amsa da toh umman ta fita ita kuma ta zauna a wajen da sauran sisters din umma suka cigaba da zaman su a dakin har aka zo lokacin walimar, dakin ta, ta koma ta sauya kaya zuwa wasu daban suka fita zuwa compound din inda aka gabatar da walimar, aka ci abinci aka sha abun sha sannan Anty Hauwa ta sake tunatar da mutane akan rayuwar aure da kuma hukunce hukuncen da suke kan mace wanda ya zama wajibi ta sauke nauyin domin samun rahmar ubangiji, daga nan ne kuma Abbati ya shigo mata da motar wanda ta shiga tsananin mamaki, Itace motar da ta nuna a ranar, duk da ya nuna mata da gaske yake amma bata ji a ranta cewa ta chanchanci mallakar hadaddiyar motar ba, har kukan dadi sai da tayi dan farin. ***Sabuwar shadda ce a jikin sa wadda tayi matukar dacewa da fatar sa, kansa babu hula ya ajiye ta a gefen sa, ya dauki turare yana fesawa MD ya turo kofar jikinsa sanye da wando 3quarter da riga armless, ta cikin mirror ya kalle shi ya cigaba da abinda yake yi yana kallon sa yana duba babbar rigar da ke ajiye a saman gadon sa. "Are you for real!?" "What?" "Kai kadai zaka je!? Ba zan raka ka ba?" "Bana bukata, ni kadai na isa." "Allah sai naje, bari kaga." Ya haura ta saman gadon ya isa gaban wardrobe dinsa ya ciro sabuwar shaddar sa shima ya hau sakawa, be kula shi ba ya cigaba da shiryawa bakin sa na bitar suratul bagra, agogo ya daura a tsintsiyar hannun sa ya kafa hular yana gyara mata kari, nan da nan MD din ya shirya ya zo ya tsaya kusa dashi yana budawa. "I'm ready, muje ko?" "Shuganan yan naci da sa ido." Ya wuurga masa car key din yana ficewa daga dakin, dariya ya saka ya bishi suka jera gwanin sha'awa. Afwan pls, yau nayi baki ne. RM    42-43 ****Cikin gidan suka nufa kai tsaye maimakon su tafi, MD na gaba yana bin bayansa, babbar rigar ta zauna a jikinsa, yayi kyau ainun sai kamshin turare ke tashi daga jikinsa masu dadi kamshi. Gud'a su Anty Faty suka saki suna shigowa, yayi murmushi yana zama a daya daga cikin kujerun dake falon, su ya su ne yan gidan a falo ya kalli wajen da su Amira suke zaune, daya bayan daya suka zame daga falon sukayi daki cike da tsoron abinda zai biyo baya, tunanin su ko zai fadawa su Anty Faty abinda sukayi, duk sai suka tsure suka kasa zama a dakin da suka koma suna tsoron yadda zata kasance. "Dauko amaryar tamu za'a tafi ne!? Wannan wanka haka." "A'ah, zance zan rakashi kinsan ya kyello wata fa, biyu zai hada." "Banda sharri Mudan, wai haka Abuya?" "Indirectly yake fad'a muku aure yake so ba wani abu ba." "Haka nace maka oga?" " Action speaks louder than voice, action dinka ya nuna." " Naji, is it a crime? After all ai na girma ko Anty Asy?" " Ba ruwana a cikin wannan maganar, ni team Abuya ce." " Duk bakwa sona kenan?" " Gaskiya, ga latest ango wa zai bi bayan gauro." "Ni kuma potential ango ba, ku jira IV." " Kamar gaske, muje karka cinye time Malam." Yace yana mikewa " Ina munafukan yaran nan suka shiga?" " Su Amira wai?" " Su, ko kafar su na gani a part dina ku shaida sai na kakkarya su na zubar." " Me sukayi maka?" " Sunfi kowa sani, muje bari mu dawo Anty Faty." " Ok Ango, muna nan muna jiranku." " Wai moctail din ne? Ba za'a hakura ba?" " Ai har na kira tribes din, sun gyara mana wajen ma, we just eat and snap, nothing more, tunda ka hana mu biki sosai." " Shikenan, zan fada miki idan mun kusa isowa. " " Owk sai kunzo, zamu shirya muma kafin nan. " " Ki fad'a ma su Mom. " " Owk. " Tace tana mikewa ***Wanka tayi da ruwan turare me kamshi cikin kayan da Amaryar Kb ta aiko mata dasu na tafiya gidan aure, ita kanta tasan ta sauya ta zama wata ta musamman, ga fatar ta da ta zama kamar ta jarirai dan taushi. Kayan da aka turara su da turaren kaya wani material ne me sulbi da akayi masa dinkin doguwar riga fitted, daga kasa ta dan bud'e, ta saka ya kamata sosai daga sama, wuyan sa me v shape hakan ya sake fiddo da kyawun dinkin da kuma zaman da yayi a jikinta das kamar ma material ba. Mayafi madaidaci ta yafa a saman kanta tare da taimakon ya Hadiza ta gama shiryawa, ta kama hannun ta, ta kaita dakin Abba, sannan ta fito ta barsu a ciki yana yi mata nasiha me ratsa jiki, kuka ta samu kanta da yi wiwi, sai ga Abbati ya shigo yace wa Abban Abdallan ya karaso, cewa yayi ya shigo dashi ciki, ya koma yayi masa iso suka shigo a tare, har zuwa dakin Abban wanda shine karon sa na farko na shigowa har ciki sosai haka, zama yayi ya tankwashe kafarsa cike da girmamawa ya gaida Abban kansa a k'asa, amsawa Abban yayi sannan ya cigaba daga in da ya tsaya "ABDULLAHI kaine shugana, kai Allah ya dora ma nauyin kula da hakkin iyalinka, sannan dole ne sai kayi hakuri da sha'anin mata ka dauke kai a abubuwa masu yawa sannan zaman ku zai yi dadi, ga Asma'u na amana ce a gareka, dan Allah karka ci amanar ta, ka kula min da ita duk da bani da haufi akan tarbiyyar ka, na gamsu da kai dari bisa dari." "In sha Allah Abba." "Madallah ke kuma Asma'u, ABDULLAHI mijinki ne, wanda aljannar ki take karkashin kafafunsa, ki bishi kiyi mishi biyayya kamar yadda Allah ya hukunta a gareki, kar naji ko na gani, kiyi koyi da halin mata na gari ki zauna da mijn ki lafiya da yan uwansa, kiyi hakuri ki ji kiki ji, Allah yayi muku albarka, ya baku zaman lafiya ya kade fitina a zamantakewar ku. " Abdallah kadai ya amsa da Amin a ciki, ita kuma kuka kawai take wanda yake jin kukan har cikin ransa, shi Abban ya fara sallama ya fita ya tsaya a wajen su umma ya gaishe su sannan ya fita waje yana jiran ta, MD na zaune a mota yana danna waya ya fito ya jingina da jikin motar maganganun Abban na dawo masa, lallai aure wani girma ne da Allah ya bawa namiji wanda idan be yi wasa ba tsaf zai iya kaishi wuta, dole ne ya jajirce wajen ganin ya sauke dukkan nauyin da ya rataya a wuyansa ko dan samun rabauta. Kamar me kirga taurarin dake sararin samaniya haka ya daga kansa yana kallon hasken farin watan da yafi kama da dan kwana goma sha biyar saboda hasken sa, iska ya shaka ya fesar dai-dai lokacin da suka fito da ita kanta a lullube da mayafi, da sauri MD ya bud'e musu kofar, ta saka kafarta bakin ta dauke da Bismillah ta shiga, Ya Hadiza ta rankwafo tana fad'a mata wata magana kafin su juya su koma ciki. Bayan ya bud'e ya shiga MD ya juyo bayan yana dariya "Yanzu shikenan na zama driver ko?" "Face your front." " Ai shikenan, Amarya barka da dare, welcome to the family Anty Asmy! " " Ina wuni? " " Lafiya lou Anty. " Murmushi tayi me sauti, ya matso kusa da ita yana leka fuskar ta, har yanzu kunyar nan ta jiya bata bar ta ba, hannu yasa ya janye mayafin da ta rufe fuskarta, tayi saurin sadda kan k'asa ya saka hannu ya dago fuskar tata yana kallon cikin idon ta "Kunyar ce wai?" Daga masa kai tayi "Oh! Toh I'm sorry toh... Bansan me yasa ba, na kasa resisting." Sai ya dan sosa kansa yayi murmushi, duk maganar da suke MD baya ji dan k'asa k'asa yake maganar sosai ga sautin dake tashi a motar. Shiru ne ya biyo baya sai hannun ta da ya rik'e yana motsa su a cikin nasa, ta lura yana son hakan dan duk sanda suka hadu sai yayi kokarin rik'e mata hannu. Waya taga ya dauka yayi kira, kalma biyu ya fad'a ya ajiye yace "Mu wuce chan kawai, sun riga sun tafi." "Ok!" Yace yana juya motar zuwa hanyar tribes din.      Parking yayi ya fita ya bar su a ciki, ya kalli mayafin jikinta ya saka hannu ya gyara mata shi yadda zai sauko sosai, sannan ya cire babbar rigar tasa ya ajiye yace mata " Ba zamu dade ba, dan sun takura ne ma kawai. " " Fita zamuyi? " Tace tana kallon sa ta hasken da ya shigo motar " Eh, ciki zamu shiga, your new family suna ciki suna jiranki. " Sai ya bud'e murfin motar ya fita ya zagayo wajenta, ya bud'e yana mika mata hannu " Kunya nake ji. " " I'm with you, ki saki jikinki kawai kinji?" " Zasu karbe ni?" Dan dam yayi yana kallon ta yana hada maganar ta da wani tunani na daban, itama kallon sa take ta kasa motsawa daga zaunen bare ta karbi hannun nasa ta fito, " Um?" Tace ganin kamar he was lost in thought, murmushi ya sakar mata ya kamo hannun nata ya taimaka mata ta fito, sannan yace "Duk wanda be karbi Husna tah ba nima ban karbe shi ba, ko waye. So just relax, you are safe! " Wani gwarin guiwa ne taji yazo mata, ta rik'e hannun nasa kamar yadda ya bukata suka shiga takawa zuwa cikin ginin da ya tsaru, mutane ne birjik a wajen kowa na aiwatar da abinda ya kawo shi, mafiya yawancin su saurayi da budurwa ne sai yan tsirarin mata da miji ko kuma gang din abokai a gefe, sama suka haura hasken fitilun wajen na sake kayatarda ita, yau ne karo na farko da ta fara zuwa irin wannan wajen, su din basu da yawan wayewa duk da daidai gwargado sunyi bokon amma kuma basu da irin wannan exposure din ko dan irin takunkumin da Abban ke saka musu a dukkan stage din rayuwar su, idan basa makaranta toh suna gida suna taya umma aikace aikace, ballantana ita da ta kasance daddawar daka ko yaushe tana manne da gida bata son yawan yawo ko gidan yan uwa ne.     Suna zura kafarsu a kofar suka ji saukar abu a kansu, sai tafin mutane da kalmomin congratulations dake tashi, gefe wasu maza ne su biyu bakin su rik'e da abun busa suna musu busa me dadi dake dauke da taken aure me dadi, murmushi kawai taga yanayi hakan ya sakata itama yin murmushin suka cigaaba da takawa har wajen da aka tanadar musu na zama, suka zauna sannan aka shiga daukar hotuna da mutanen da bata san kowa a ciki ba, yawancin su yan mata ne sai manyan da ta gani basu fi hudu ba, sai su MD da su uku ne ma kachal maza a wajen, duk abinda yayi itama shi take yi dan bata san yadda ake gabatar da abu irin wannan ba. Komawa sukayi suka zauna bayan an gama hotunan kafin a shiga gabatar da abubuwan ci da na sha dangin su virgin mojito, da dangogin su snacks da wasu kalolin drinks din da bata ma taba ganin su ba, sai gashin nama da kaji da wani abu da ta hanga kamar shrimps ne ko scorpion ce ita bata ma gama tantancewa ba. Nasu daban special aka jide musu a gabansu, ya dauki cup din da aka zuba wani mint drink yayi sipping kad'an sannan ya mika mata, a kunyace ta sha ya ajiye yana kallon sauran kayan, bashi da plan din dadewa a wajen dan su kansu sun san wannan din ba al'adae sa bace sam. Da hannu ya yafito MD yazo ya duka ta side dinsa yace "Just 10min ya rage mu wuce, we can't stay long!" "Ok, bari na fad'a ma Anty Faty, nasan dama ba zaka zauna ba, suma sun sani. " " Yawwa. " Zuwa yayi ya fad'a mata, ta biyo shi suka dawo wajen Abuyan tace " Haba Abuya, 10min yayi kadan ina laifin 30min, amarya pls ki saka baki ku dan zauna, dan ku fa muka taru, pls kayi hakuri ka kara mana, yau ne kawai shikenan fa. " " Mu zauna? " Yace yana kallon Asma'un da taji kamar ta nutse dan kunya, ita mene nata da zai tanbaye ta, kin magana tayi sai ya kalli Anty Faty " Ta gaji da yawa, kinga kawai gwara mu tafi. " " Haba amaryarmu, please! " " Zamu zauna Anty, har a tashi ma." " Kai yawwa, hakan shine nan da 1hour kowa ya kama gabansa, thank you amarya. " Sai ta juya ta bar wajen, kallonta yake amma taki bari su hada ido sai ma gefe da ta kalla, MD ne ya bigi kafadar sa cikin sigar tsokana yace " Woman wrapper. " Ai be bari ma ya gama tantance kalmar ba, yayi wuf ya bar wajen sai hango shi yayi a wajen su Amira suna magana, girgiza kai kawai yayi ya matse mata hannu da dan karfi ganin taki kallon sa, ta juyo da sauri ya kanne mata ido "Kinji wai nine woman wrapper, amma gaskiya MD ya yanke ni, anyways yadda kika ce haka za'a yi hajjaju na, your wish is my command, idan ma kwana kika ce muyi anan din so be it." Dariya ya bata yadda yayi maganar, a daidai lokacin romantic photographer ya dauke su a hoto, tana kallon sa tayi dariya shima yayi dariya, hoton da yayi masifar kyau, shi kansa sai da ya yaba hoton dan ya dade be ga couples din da sukayi masa kyau ainun kamar su ba, cigaba yayi da daukar duk wani motsin su, dan yasan hotunan zasu kawo masa kasuwa sosai. Kamar yadda tace din kuwa be sake complain ba, sai da aka tashi tas bayan an cika Asma'un da kyaututtuka masu yawan gaske, aka lode musu su a mota hade da take aways dinsu dan babu abinda suka ci a wajen daga ita har shi. Gidan suka wuce dukka har su Anty Faty, kuma a kusan tare suka isa, Anty Faty yayi wa magana yace ta kaita wajen su Mom, shi kuma ya wuce sabon part din nasu dake chan baya. Rik'e hannun ta Anty Faty tayi suka shiga ciki, su Amira na bayan su suna yaba Asma'un da basu yi tunanin haka take ba, su a tunanin su da aka ce bazawara sun dauka zasu ga wata katuwar mata, sai gashi sun ganta fiye da yadda sukayi tunani. Suna shiga Mami ta taso ta rungume Asma'un, duk suka saka dariya har Mom dake zaune a gefe "Mami tayi sabuwar 'ya mun shiga uku." Anty Asy tace aka sake yin dariya "Ya ranku, sannu kinji 'yata, sannun ki da zuwa." Zamewa tayi ta zube a kasa ta gaishe da Mamin ta amsa a sake tana sake dagota, "Mike karki zauna a k'asa kinji, tashi." Tashi tayi a kunyace ta zauna a gefen carpet din dake malale a wajen sannan ta gaishe da Mom ta amsa fuskar ta cike da fara'a, duk da kanta a kasa yake bata kuma kalli fuskar kowa acikin su ba, amma muryar Abdallan ta sak a cikin maganar matar da suka gaisa wanda kai tsaye ta raya ita din mahaifiyar sa ce, nan nan kawai suke da ita har yan matan da ta lura kannen sa ne. Wajen minti talatin tayi a wajen su, sai da Mami tace Anty Faty ta tashi ta rakata shashen ta a barwa gobe, idan yaso ko Baba Alhaji sa gaisa goben saboda dare, an bar mata danta shi kadai yana kallon hanya. Babu wanda maganar bata bawa dariya ba, banda Asma'u ta taji kamar ta haka rami ta nutse, tayi musu sallama Anty Fatyn ta rakata har shashen nasu da yake da yar tazara tsakani, a kofar ta ja ta tsaya tace "Asubah ta gari amarsu, sai mun shigo gobe." "Nagode." Tace ta turo kofar da take half way a bud'e, ya barta ne daman saboda dawowar ta, yana jin an turo ya fito daga kitchen din jikinsa sanye da wando short babu riga a jikin sa saboda yanayin zafin da ake tun rana, duk da akwai AC amma shi mutum ne me matsanancin jin zafi shiyasa da wuya yake zama da cikakken kaya in dai yana dakin sa ne, sai dai idan zai fita ya dora jallabiya yana dawowa ya cire sai dai idan fita zai yayi nisa sosai. Kin kallon sa tayi ta zauna da sauri a kujera, yayi murmushi ya ajiye cup din hannun sa ya dauki singlet dinsa dake ajiye a saman kujerar ya saka sannan ya dauki cup din ya kai bakin sa yana zama a gefenta. RM 44-45 ***Tsaye yake a jikin window yana leka harabar gidan sanda yaji mota ta tsaya, Fido ce tare da Faiza suka dawo a motar sa, kansa da yake masa ciwo sosai ya rik'e da hannu ya dawo ya zauna a gefen gadon tunanin ta na sake bijiro masa, wani irin zafaffen son ta ne yake nukurkusarshi, ga kuma tsoron Fido da ya cika kirjin sa har baya so yayi ko da kwakkwaran motsi a gabanta. Yana jin takun hawowar su saman yayi saurin kwanciya ya dintse idon sa tamkar me bacci, turo kofar tayi tana da kofar ta kalle shi tunanin ta bacci yake sai kawai ta juya suka shige dayan dakin suka rufo, yana jin haka ya lallaba ya fito, ya sauko k'asa duk da jikinsa babu kwari har lokacin dan babu inda yake zuwa yana kunshe a daki, ji yayi hasken ranar yayi masa gau, kamar zai disashe masa ido saboda kwana kin da yayi a daki yana bin umarnin Fido din, kallon kofar gidan su yayi kamar zai shiga sai ya fasa ya shiga takawa a kafa har zuwa titi ya samu napep ya fad'a masa in da zai kaishi. Suna cikin tafiya ne ya lalubi wayar sa yaji wayam ya manta ta a daki gashi be fito da wallet din sa ba, be ma san in da take ba a takaice dan be ganta ba tun da suka dawo daga asibiti, gashi sun yi nisa sosai dan daf suke da gidan Abban ba abun yace su juya ba, tunda ma har yazo this far gwara kawai ya karasa dan be san yaushe zai sake samu wani chance din irin wannan ba. "Oga idan muka je zan shiga na karbo maka kudin ka, ashe ban fito da wallet dita ba." " Ba damuwa." Me napep din yace a ransa mamakin Adam din yake dan kana ganin sa kaga wanda yake cikin yanayi amma kuma maganar sa ras sai rashin kuzari da wani uban gashi da ya bari a fuskarsa babu kyawun gani, da fari ma ya dauka ko bashi da hankali dan da ya tsaida shi har da ba zai tsaya ba sai kuma ya tsaya, sai da yayi magana sannan ya fita daga shakku har ya dauke shi ma. A kofar gidan Abban suka tsaya ya sakko ya tura kansa ciki, Abba na tsaye dasu Abbati yana musu magana akan gyaran wajen gidan sai ga Adam, da kallo duk suka bishi ya rissina ya gaida Abban ya amsa yana nazarin yanayin sa "Dan bani 300 Abbati na sallami me napep na manta wallet dita a gida ne." "Ungo bashi Abbati, muje ciki Adamu." Abba ya ciro 500 a aljihunsa ya mikawa Abbati su kuma suka wuce cikin gidan, umma na tsakar gida suka shigo ta dan zabura da ganin Adam din amma kuma sai batayi magana ba suka wuce dakin Abba shi da Umar da Abban, suna shiga Abba yace Umar yaje ya kawo ma Adam din abinci, tashi yayi ya shiga gidan ya karbo a wajen a umma ya kawo masa, Adam da ya kwana biyu ko isashen abinci baya samu yaci ya karba ya hau ci babu kakkautawa, tausyai sosai ya kama Abba, tausayin yadda Adam din ya zama a dan kankaninin lokaci wanda yake kyautata zaton matar da ya aura ce baya jin dadin zama dan babu wanda zai kalle shi ya ce yana cikin nutsuwar sa, sai da yaci ya koshi sannan Abban yace ya taso shi da Umar din suka fita ya kaishi shagon aski yace a sama aski, a mota Abban ya zauna ya barsu da Umar da ya tamke fuska tamau dan ba yadda zai da Abban ne amma mutum irin Adam ba abun a tausaya masa bane ba. Bayan an gama ne suka sake komawa gida Abba ya Shashi yayi wanka sannan ne yace ya fad'a masa abinda yake damun sa. Shiru yayi dan bashi da abin fad'a, ba kuma zai yi gigin fadar laifin Fido ba dan yanzu haka ma tunanin sa yana chan dan dadewar nan da yayi yasan ta neme shi, kuma dole ne ranta ya baci idan ya koma sai yasha cin mutunci. "Zan tafi Abba, dama zuwa nayi na gaishe ku." "Ka tabbata babu wata matsala? Yaya tace rabon da ta saka ka a ido tun ranar da aka sallame ka, haka ne?" "Eh." Yace yana kada kansa "Adamu mahaifiya ce fa? Kasan halin da ta shiga akan hakan?" "A ah." "Toh lallai kaje ka ganta ka kuma bata hakuri." "Toh in sha Allah." "Yawwa, idan akwai wani abu sai kayi magana, zan fita kasuwa dama zuwan kane ya dawo damu ciki da tuni munyi nisa ma. " " Da... Dama.. Abba cewa nayi Asma'u fa? " " Kana da hankali kuwa Adamu? Baka san Asma'u tayi aure bane? " " Na sani. " Yace a wani yanayi " Toh ka fuskanci rayuwar ka, bana son shirme. " " Tashi Umar muje kar Abbati yayi ta zaman jira. " Ganin sun tashi ya saka shima ya tashi, suka fito a tare ya riga su fita dan Abba ya leka falon umma yana mata magana Adam din ya fice daga gidan. Yana tafiya a kafa suka tadda shi, Abba yace ya shigo su rage masa hanya yace a ah ba komai, kafin ma ya gama magana Umar ya figi motar, nuna shi Abba yayi yana murmushi yace "Ka ganka ko Umar? Bana so duk lalacewa Adam dan uwanka ne." Shiru yayi be ce komai ba, yana hango Adam din yana cin tafiya ta cikin mirror din baya, yayi murmushin mugunta ya sake take motar a ransa yana ayyana kad'an ma ya gani. ***Gaba daya Fido ta rikice tana neman sa, har gidan Hajiya Mama ta shiga ta samu Fadeela a tsakar gida ta tanbaye ta ko Adam ya shigo, tayi mata banza dan dama haushin ta take ji, falon ta leka ko zata ganshi ko takalmin sa amma bata ga alamar shi ba, sai ta fice da sauri tana sake komawa saman ta shiga dakin shi anan taga wayar sa a ajiye akan gado da tayi ta faman kira babu amsa, bata son alakar shi da yan uwansa dan hakan zai kawo mata cikas a aikin ta shiyasa take kaf kaf dashi, dama tun da ba aiki yake ba, dukiyar su da mahaifin su ya bar musu ake juya musu anan yake samun kudin sa na kashewa be san wata wahala nema ba, duk kwanan duniya akwai ribar da ake bashi yana daga kwance a gida yanzu da Fido tazo sai ys zama ma ta hannun ta kudin yake shigowa take yin yadda take so itace mijin itace matar be isa tayi magana ya musa ba. Yasha wahalar napep duk wanda ya tsaida idan yace har ciki za'a shigar dashi saboda babu kudi a jikinsa sai anje zai dauko sai yaki dan sun fison na hanya, wani ne na karshe ya yarda ya dauke shi Amma shima sai da ya zabga masa kudi haka ya shiga a gajiye tiikis ga uwar ranar da ake yi me shiga jiki. Duk yayi wuri wuri kafin ya isa gidan ga kuma Fido na jiran sa dan akan idan ta me napep din ya sauke shi, ta taho wajen napep din tana kallon gyaran da yayi a kansa da fuskar sa, "Bani 500." Yace mata yana kallon cikin napep, cikin rigar ta, ta saka hannu ta ciro ta mika masa ya bawa me napep din sannan ya wuce tabi bayansa cikin rashin gansuwa da yanayin sa, na rashin gaskiya. Bata barshi ya shiga falon ba ta tare shi ta hanyar yin sauri tasha gabansa ta babbake kofa "Ina kaje?" Ta kafe shi da kallo "Aski naje nayi da gyaran fuska, baki gani ba?" "Shine ka dade haka, har da hawa napep da tsada haka? Malam karka raina min hankali mana." "Baki yarda ba? Bayan ga shaida nan kin gani." "Ban yarda ba kuma ba zan yarda ba , sai ka fada min inda kaje har ka dade haka nayi ta neman ka, baka kuma tafi da waya ba." "Nace miki aski naje, wajen tsohon me aski na. Akwai layi shi ya sa na dade wayata kuma manta nayi har ma wallet dina, baki ga sai da nazo na karbi kudin ba, hadda na askin zuwa zai ya kaiwa me asken 300 shi kuma ya rik'e 200 na kawo ni da komawa." Wani banzan kallo tayi masa, bata yarda dashi ba amma for now bata da hujja, matsa masa hanyar tayi ya shige tabi bayansa kamar wata uwarsa. ***Kiran Abba ne ya shigo wayar Maman tana rik'e da wayar bayan sun gama magana da Nadeeya, dagawa tayi ta zauna suka gaisa yake ce mata Adam yazo, sai data zabura kamar bata ji dai-dai ba, ya sake maimaita mata sannan ya fad'a mata yadda sukayi, godiya ta hau yi masa da sa albarka, hadda hawayen ta dan dadi, naka sai naka dai, babu wanda zai iya mata abinda Abban zai mata kaf duniya, shi din mutum ne na gari me matukar zumunci amma idan wani ne ai ko kallo Adam be ishe shi ba, bare ya tsaya ya saurare shi har yayi masa wannan gatan. Ji tayi hankalin ta ya kwanta, ko babu komai taji halin da yake ciki, ta kuma san yana lafiya, hakan ma ya isheta. Nadeeya ta kirawo ta fesawa labarin abinda ya faru, ta tayata murna sannan suka ajiye wayar. Duk abubuwan da ta gujewa Hajiya Maman sai da suka faru, shiyasa kawai komai zakayi kayi shi tsakanin ka da Allah sannan banda son kai, karka wulakanta dan wani ka fifita naka dan baka san wanda zaka mora a rayuwa ba. Ita kanta Maman tasan Asma'u tafi karfin Adam a yanzu amma duk da haka ba zasu daina yi masa addu'ar samun mace ko da rabin Asma'un ce a hakuri da nagarta ba. ***Cup din dake hannun sa ya mika mata bayan ya sha rabi, ta girgiza kanta alamar a'ah, sai kawai ya kafa mata a baki yana kallon cikin idon ta, bata da zabi illah tasha, kunun aya ne me sanyi da dan karen dadi, dan zata iya cewa bata taba shan me dadin sa ba, sai gashi ta zuke shi tas a kunyace ta janye kanta ya kalli cikin cup din ya kalle ta "Ana so ana kaiwa kasuwa." Toshe bakin ta, tayi da tafin hannun ta, ta saki dariya, ya ajiye cup din yace ta taso su shiga ciki, shine a gaba tana bin bayan sa har suka dangana da first bed room din da yake tsakanin dan corridor da falon, hasken fitilun dakin daban da na falon hakan ya sake fito da kyawun dakin da yake a share a gyara tas tas kamshin turaren wuta na tashi a cikin sa. Toilet din dake makale a dakin ya nuna mata yace taje tayi alwala, yana zuwa, ya fita ita kuma ta shiga toilet din da shi kansa abun kallo ne ta dauro alwalar ta same shi a dakin ya shinfida babban abun sallah ya sako jallabiya, sannan ya fito mata da dogon hijab a cikin kayanta, mika mata yayi ta saka ya nuna mata inda zata tsaya daga saitin bayan sa. RM    46-47 ***Nafila sukayi rak'ah biyu sannan ya juya ya kama kanta yayi addu'a, addu'ar da ya manta jiya be yi ba, shi da kansa yaga baiken sa na gaggawa da rashin hakurin da yayi, amma kuma a wani bangaren ba zai iya hana kansa bane musamman sanin cewa abinda ya aikata din ba haramun bane, yan tambayoyi yayi mata dangane da addini ya gamsu kwarai da amsoshin da ta bada ya jinjina kansa yana saka mata albarka a bayyane, murmushi kawai take har suka gama ya mikar da ita yace ta zauna gefen gado yana zuwa, ya sake fita ya dawo dauke da ledojin da akayi musu takeaway, sai plate da silver spoons ya ajiye a gaban gadon kan dan madaidaicin carpet din ya nannade hannun jallabiyar sa ya zauna yana tankwashe kafarsa "Let me feed my wife, na fara cika duties dina." Zamowa tayi daga gadon ta zauna a daf gefen sa ya zuba mata abincin ya saka spoon ya debo ya kai bakin ta, "Oya! Bud'e bakin" "Zan iya ci ai." "Ba wani, ba ci zakayi ba nasan, ni ne zan baki har sai kin koshi, muga ma dai cikin ki." Ya kai hannu ya daga hijab din jikinta, sai a sannan ma abun yazo kansa, ya zare hijab din yana cewa "Bakya jin zafi?" Kasa ta kalla da sauri daga ita sai fitted gown din dake jikinta me V shape wuyan da ta kamata sosai musamman da take a zaune, shi kansa sai da yaja numfashi kafin ya daidaita kansa ya shafi cikinta da ya cika ciki sosai yace "When last kika ci abinci ma wai?" "Nayi lunch." "Lallai, kalli cikin ki fa very flat kaman baa taba saka masa abinci a ciki ba. " " Let me feed you, bud'e bakin." Budewa tayi bayan tayi bismillah ya bata abincin, a nutse har ta soma jin ta koshi, ta girgiza masa Kai da ya sake nufo bakin nata alamar ta koshi, be yi musu da ita ba, ya ajiye yana siyaya mata ruwa a glass cup tasha kad'an ya ajiye sannan ya tashi zai tattare kayan tayi saurin tashi, "Zan kwashe!" "Yau dai ba ranar aikinki bace, zauna ina zuwa." Yace mata yana tattare kayan ya fita dasu, mayafin ta dauka ta sake rufawa ta koma ta zauna a kasan tana nannade kafarta. Wajen mintuna biyar ta zata zai dawo taji shiru, sai ta fad'a toilet din tayi fitsari sannan ta wanko bakin ta, ta fito ta hange shi a saman gadon ya rufe iya kasan kafarsa yana kokarin saita AC din dakin dan shi zafi yake ji. Gaba daya dakin ya dau sanyi har ya soma shiga cikin jikinta amma shi ko a jikin sa, hakan shine daidai yayi mugun sabawa, da hannu ya yafito ta ganin tayi tsaye, ta karaso kusa dashi ya jawota zuwa kan gadon ta saman jikinsa zuwa dayan sashen gadon, "Wannan kayan ba zai dame ki ba?" "Zan chanja." "Ok, chanja kizo kiji." Yace yana sakinta, ta yunkura ta sauka ta dayan side din zuwa gaban wardrobe din ta bud'e tana kallon kayan ciki da ake jera su gwanin sha'awa, da k'yar ta hango wata doguwar riga mara nauyi kuma da dan tsawon ta dan ta wuce guiwa sosai ta kusan kai idon sahu, dauka tayi ta nufi toilet ta saka ta sake yafo mayafin ajikinta ta dawo dakin, dan kallon ta yayi, ya maida hankalin sa kan wayar sa da yake duba sakonnin mutane, gadon tazo ta hau ta kwanta akan dayan pillow din ta kalli dayan barin ta juya masa baya. Ajiye wayar yayi bayan ya saka ta a flight mood ya saka hannu ya juyo da ita suna fuskantar juna. "Kina jin bacci?" "A ah." Ta girgiza kanta "Ok bari na baki labarin mijinki." Ya sake jawota sosai ta shiga jikinsa kanta na saman kirjinsa "Sunana ABDALLAH IBRAHIM K'AREFA, d'a ga Alhaji Ibrahim, mu biyar ne a wajen iyayen mu, nine babba sai MD (Mudan) sai Ibrahim (Aby baya nan yana karatu a Sudan) Aysha (Amira) sai Khadija (Ihsan). Baba Alhaji shine mahaifin mu da matan sa biyu Mom da Mami, tun da na taso ban san wani abu wai rabuwar kai ba, mun taso dukkan mu cikin so da kaunar juna, ni da Ihsan ne kadai yayan Mom, amma kuma mun fi shakuwa da Mami fiye da mahaifiyar da ta haife mu. Hakan ya kara mana kaunar junan mu kamar yadda zaki gani a tsakani na da MD, bani da aboki kamar sa haka shima bashi da tamka ta, mune koman juna babu wata baraka a tsakanin mu tun tasowar mu kawo yanzu. Mahaifin mu dan kasuwa ne tun da muka taso muka bud'e ido, hakan ya saka mana so da kaunar kasuwanci duk da be barmu mun tsunduma a harkar kasuwancin ba har sai da muka kammala first degree dinmu daga nan muka fad'a harkar, ina kokarin kamalla degree na na biyu Allah ya dafa min har na bud'e company nawa na kaina da nake yin order motoci ina saidawa wanda na fara kamar wasa. Tun daga nan MD ya karbi ragamar kula da harkokin Baba na waje ni kuma nake kula da duk wani abu da ya shafi cikin gida. Wannan shine tarihi na da gidanmu a takaice, bayan boko nayi karatun addini me zurfi har ta kai na sauke al'qur'an me girma kuma na kammala littafai da dama." " Masha Allah." Tace tana jinjina kai, " You will get to know me better in sha Allah, "In Sha Allah." A gajiye yake ranar, dan haka kawai rumfa yayi mata da hannun sa, yace mata goodnight bayan yayi kissing forehead dinta. Nan da nan bacci ya dauke shi, ta dinga kallon sa ta dan hasken da ya shigo cikin dakin, tana admiring din sa. Da safe ta riga shi tashi bayan yayi sallar asubah ya koma sai ta sulale wajen bakwai da rabi ta bar dakin zuwa na kusa dashi, sai a lokacin taga dakin, ta cire kayanta ta zuba su a laundry basket din da ta gani a tsakanin toilet da dakin, ta bud'e akwatin da tazo da ita jiya me dauke da tsofaffin kayanta ta dauki wata bakar abaya ta saka ta fito zuwa falon, babu datti babu komai sai kawai ta wuce kitchen ta tsaya tana tunanin abinda ya kamata tayi, ita ba yarinya bace karama bare ta zauna ta shanya baki bata yi musu komai ba, doya ta dauka ta feraye ta wanke ta tas sannan tayi mata yankan da zata soya ta haka ba tare da ta yanka ba, ta ajiye a gefe ta dubo kayan miya da veggies wasu fresh an jera su akan wani abu shima me kyau wanda duk aikin MD ne da Anty Faty, sai dangin su garlic da fresh ginger suma a gefe daya, sauce zatayi da fried yam din sai ta yayyanka tomatoes tayi grating bell peppers da scotch bonnet, ta yanka albasa me yawa, da hada da half green pepper tayi sauce din me dan karen dadi da kamshi, sannan ta soya doyar bayan ta gama miyar. Sai ta dafa ruwan tea me kayan kamshi ta saka a sabon tea flask ta hada komai akan babban tray ta kaisu falon ta jera a tsakiya. Turare ta kunna a cikin bunner sannan ta koma dakin ta shiga wanka, ta shirya cikin wani hadadden lace mint green da touches din golden, cikin kayan lefen ta ne yayi kyau sosai kuma kana gani kasan me tsada ne. A hankali ta tura kofar dakin taga ya sake dunkulewa waje daya, sai ta dauki wayarta a saman mirror ta fito ta sake jawo masa kofar a nutse. Karatun al'qur'an me girma ta kunna a wayar ta ajiye a saman kujera ta koma kitchen din ta dan sake gyara shi ta jawo kofar sai taji ana knocking a kofar shigowa part din, wajen kofar taje tace "Waye?" "Mune." Amira tace suna rik'e da warmers din abinci da tea flask,bud'e musu tayi tana fad'ad'a fara'ar fuskar ta, suka gaishe ta a tare suna satar kallon ta dan ba karamin kyau tayi ba, kayan sun zauna das a jikinta sannan daurin yayi mata kyau sosai. "Sannun ku, Amira da Ihsan ko?" Dadi ne ya kamasu jin ta fadi sunan su, suka amsa mata da eh, tace su zauna, "Mami tace karmu zauna wai yayi safiya, zamu dawo anjima breakfast tace a kawo muku. " " Toh shikenan,mun gode ku gaishe su " " Sai anjima. " Suka juya ta rufe kofar tazo ta bud'e warmers din taga farfesu ne da chips sai kunun gyada, plate ta dauko ta zuba ta ajiye sauran a wajen da ta jera kayan abinci ya zauna taci sosai, ta gama tasha tea dan bata fiya son kunun gyada ba ita, ta wanke kwanukan ta dawo ta zauna kenan sai gashi ya fito. Idansa fes akanta ya sakar mata murmushi yana nufo ta, tashi tayi tsaye ya karaso ya bud'e hannun sa ya rungume ta. "Good morning Baby!" "Ina kwana!?" "Lafiya lou, kin tashi lafiya?" "Lafiya lou." " Masha Allah, shine kika gudu kika bar ni ko?" " Bana jin bacci ne." " Sai kika zo kina bawa kanki wahala maimakon ki huta ko?" " Ba wata wahala fa." " Ba wani." Yace yana zama a wajen kayan abincin " Wanne ne yaran chan suka kawo wane ne kika girka da hannun ki?" " Dama kaji zuwan su?" " Ina jin su, na ganki ma kina zuba loma baki jira ni ba." " Laaaa..." Tayi saurin rufe fuska da tafin hannun ta, yayi dariya ya bud'e flasks din yace ta zauna, ta zauna ta zuba masa doyar da sauce din kamar yasan shine wanda tayi, yaci sosai da ruwan bunu hakan yayi mata dadi sosai, ya gama ta tattare wajen ta gyara shi kuma ya shiga wanka, sai da ya tsokane ta akan tazo ta tayashi ta gudu kitchen ya dinga dariya shi kadai yana wankan har ya kammala ya fito ya shirya irin shirin da yake weekends yace tazo su shiga cikin gidan. Mayafi ta yafa madaidaci ya fito suka nufi chan part din iyayen tana karewa ko ina kallo. Tarba ta musamman ta samu a wajensu, musamman Mami da take ta nan nan da ita, duk sai taji tsoron da take ji ya kau, taji wani gwarin guiwa na zuwar mata, har falon Baba Alhajin Mami ta kaita ta gaishe shi, ya dinga saka mata albarka, sai da MD suka shigo tare da Abuyan sannan suka koma cikin gidan ta zauna dasu Amira a falon suna kallon wani film me kyau. Sai wajen twelve sannan yayi mata text yace ta dawo, ta tashi tace ma Mami din zata tafi, sai tace mata ta shiga wajen mom ta sameta a daki, ta shiga ta gaishe ta again sannan tace zata tafi ne dama, dadi taji sosai ta saka Ihsan tace ta rakata. Sosai Asma'un ta kwanta mata ta gamsu da ita a matsayin matar Abdallan nata. Satin sa biyu iyakar sa yar karamar unguwa su fita da MD shima basa dadewa, ba karamin sabo tayi dashi ba a yan kwanakin har takan ware suyi ta hira kamar ba gobe, ga wata irin zazzafar soyayyar sa da ta sake kamata. A dan zaman nan nasu ta gane wanne irin miji Allah ya bata, me cike da tarin abubuwan mamaki, mutum ne me tsananin addini da kankan da kai, baya taba ketare iyakokin Allah yana kums kokari sosai wajen sauke nauyin dake rataye a wuyan sa, ba zata ce tafi kowacce mace sa'a ba, sai dai tana da yakinin zata iya jerawa a cikin matan da sukayi dace da sa'ar miji a wannan zamanin. Washegari zai koma aiki duk kuwa da shine ogan kansa amma ta lura baya sanya wajen aikata duk abinda yake ganin zai sake kafashi, a hakan ma yana gidan ko yaushe yana kokarin rage ayyukan nasa ne, wanda yake daukar kaso mafi rinjaye a aikin company din nasa, be zauna ya nade hannu da kafa ba, shiyasa har yanzu yake samun cigaba a al'amarun sa. Da wuri tashi ta shirya masa abin kari ta kuma taimaka masa wajen shiryawa, ya tsuke abinsa a cikin suit ash colour, ya makala necktie ya saka half cover shoe da black socks saboda bakin da zasuyi yau din wannan shigar ita ta dace da zama dasu. Be sani ba, ta dauke shi hoto ya juya yana tattaro wayoyin sa da system dinsa, fuskar sa a kasa ya dan dukar da kan, yayi kyau a hoton ga wani irin haske da ya kara tun bayan auren su, so take ma ta tambaye shi zuwa gida amma ta kasa, gashi yau yace mata zai iya kai magriba be shigo gidan ba, dan ma su Amira na zuwa ko ita taje anan zata dinga rage zaman. "Kayi kyau." Ta samu kanta da furtawa bayan ta karbi jakar hannun sa ta rataya a kafadarsa suka shiga takawa zuwa falo. Hancin ta ya lakace mata yana murmushi "Har na kaiki kyau? Kin ganki kuwa? Gaskiya na iya kiwo wallahi, bul-bul fa ko ina, har nan." Yace yana pointing din kirjinta, hararar sa tayi a wasance tace "Dama a haka nake." "Ummm... Ba wani." "Allah!" "Shikenan bani jakar nan kar nayi late, MD na waje yana jirana ba sai kin rakani ba." Mika masa tayi sannan tace "Allah ya kiyaye ya bada sa'a." "Amin my wife, nagode ki kula min da kanki." ***A birkice yake tunda ya tashi a yau din baya jin komai baya ganin kowa sai ita, ga Fido a gefe da ta hana masa sakat idanun ta na kan duk motsin sa, kwana biyu kenan yana bibiyar motsin Abdallan har office dinsa yaje akace baya zuwa, gashi babu damar zuwa unguwar tasu saboda polisawan nan dan ba karamin aikin su bane su nada masa na jaki yanzu bashi da kwari. Ganin yau Monday ya saka shi son sake komawa yaga ko yazo, ga Fido taki fita dan tun sassafe yake saka ran zata fitan,amma shiru, yana nan zaune bayan ya gama shan tea da slice bread biyu yaji tana wayar zata fita, murna ya hau yi ya labe yana kallo ta shirya, tazo ta sameshi ta ja masa warning, ya amsa da toh tana fita ya saka kai shima ya fice sai K'AREFA MOTORS