❤‍🩹*SAFIYYAH*❤‍🩹 *By* *Maman Maama* *Episode One (1): Bon appetite!* Breakfast is Served💔 Bismillahir Rahmanir Rahim Ina rokon Allah ya bani ikon rubuta alkhairi, ya hana ni rubuta sharri. Assalamu alaikum dearies ❤️ Fatan munyi azumi da sallah lfy. Allah ya karbi ibadun mu ya sa muna daga cikin yantattun bayin sa Ameen. So, kamar yadda nayi alkawarin rubuta Safiyyah after sallah, gashi nan zanyi kokarin cikawa 😁. Ku dai ku taya ni addu'ar Allah ya bani ikon cikawar. Lol Believe me, dama nayi niyyar yi ne on an impulse, sai daga baya kuma na fara cewa "anya kuwa?" But then na riga na fada muku and duk sanda nayi magana ina matukar kokarin ganin na cika ta, sai dai when it is beyond my control, as nobody is perfect. So, we will try insha Allah, but you will have to be patient with me idan an samu rashin update akan lokaci, ina so ku saka a ranku cewa ina iyakacin kokari na. Kamar yadda na faɗa, littafin Safiyya hopefully zai zo a matsayin free tun daga farkon sa har karshen sa insha Allah, depending on in mun samu sponsors at least twenty, ku kuma readers ina rokon alfarmar ku bada haɗin kai wajen showing support to the sponsors dan suji dadin cigaba da siya muku littafin Safiyya kuna karantawa, idan babu sponsors, littafin Safiyya zai koma paid after the free pages. I hope we will enjoy this journey tare da Safiyya and Gidado, it is going to be rough 😁, but I promise you a smooth landing. *Him*👳🏻 "Tell me you love me" yaji muryar ta ta daki dodon kunnen sa kamar a yanzu ne take yi masa maganar. Ya saka hannayen sa biyu ya toshe kunnuwansa sannan ya rintse idanun sa da karfi amma sai ya zama kamar kara clearing vision and hearing dinsa yayi. Abinda ya manta shine daga cikin kansa muryar take fitowa ba daga surrounding dinsa ba. A idonsa yana ganin fuskarta, as clear as the moon when it is full. A zaune a cikin motarsa, fuskarta dauke da murmushin da ya kasance tamkar maganin dukkan damuwa a gare shi, idanuwan ta cike da soyayyar sa. "Tell me you love me" ta fada tana saita camera din wayar ta a fuskarsa, ya saka hannu daya ya kare fuskarsa yana murmushi. "Stop it!" Ya ce cikin muryar dariya, she giggled sannan ta chanja angle din camera din zuwa inda bai kare ba a fuskarsa. "Ka fada mana to, why are you shying away from a simple question. Do you love me?" Ya bude fuskarsa yana kokarin frowning amma ya kasa, baya iya bata rai in dai yana tare da ita. Ya jingina kansa a headrest din kujerar motar yana kallon camera din tata yace "do you need to ask?" Tace "of cause. I want to hear you say it" ya lumshe ido ya bude yace "what is with the camera then?" Tace "as evidence. I want to record you say it sannan in ajiye as evidence yadda idan nan gaba ka ce baka so na ina da shaidar da zan shigar da karar ka zuwa kotun masoya". Yayi dariya sosai yana kokarin ture camera din tata amma sai ta matsar away from his reaching hands, ta ce "confess! Say you love me" ya ajiye hannunsa ganin bata da niyyar bashi wayar yace "common! Why do I have to say it? Me yasa ke ba zaki fada ba sai ni?" Ta daga gira tace "because I say so... Kuma duk abinda nace ina so shi nake samu. Now I want you to say you love me". Ta karasa cikin turo bakin shagwaba. Yayi ajjiyar zuciya "you are impossible Piya. Me zan fada miki ne wanda baki sani ba?" Tace "that you love me?" Yace "you already know that ai, you just enjoy.... enjoy.....en.." ta karasa masa cikin kwaikwayon muryarsa "you enjoy teasing me " sai kuma ta yi dariya. "You are right, na san dama ba fada zaka yi ba. I only wanted to see that" ta fada tana nuna fuskarsa, ya shafa fuskar kamar mai neman wani abu yace "see what?" Tace "your face is red my dear. You are blushing" ta karasa tana sake wata dariyar. Yayi ajjiyar zuciya "Piya! You are...." "Impossible" ta karasa masa tana sake kwaikwayon sa. Ya harare ta "stop that" ta maimaita "stop that" ya fakaice ta ya zare wayar daga hannun ta sannan ya juya camerar zuwa fuskarta. Tayi saurin rufe fuskarta da hannayen ta biyu tana dariya, yayi zooming screen din yana karewa kyawawan fingers dinta kallo. "wa na kama?" Ya fada cikin tsokana, "now, tell me you love me" ta bude fuskar ta harare shi tare da murguda baki a lokaci daya, yayi murmushi "in dai har da gaske rashin kunyar kike ji da ita ki fada min inji. Say you love me" ya karasa yana rage murya can kasa. Ta fara laluben handle din kofar. "Ni ka bude min kofa. Ni hostel zan shiga" yace "kin isa ma, ai yau sai kin fada. Kuma inyi recording din ki in ajiye, in munyi aure mun haifi yara sai in nuna musu yadda maman su ta mutu a kaina" ta juya ido "wai ma, wa ya gaya maka haka?" Yace "I know...I just know. Tun ranar da kika fara gani na you just couldn't stay away from me, kinga dan farin bafulatani kin rikice, kince in ba ni ba sai rijiya" tayi dariya "ranar da na fara ganin ka, loving you was the last thing on my mind. Bana jin ma nasan menene love ɗin " yace "huh? Shi yasa kika bar seat din ki kika dawo nawa? Admit it Piya, you were attracted to me" ta juya idonta "shi yasa naga tun daga ranar duk inda nayi sai ka bini, bita zai zai" yace "tabbas, and this is just the beginning, duk inda kika je sai na biki. Naji na yarda ni bita zai zai din ne. Kuma nan gaba zan zama 'mijin kafin ta ce'" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, tana jin nauyin idanuwansa a kanta, ya sauke wayar tare da yin ajjiyar zuciya yace "Please Piya, I think it is about time ki kaini gurin Daddy, har yanzu baki gama jan ajin ba wai?" Ta dago kai suka haɗa ido "sai ka lallaba ni kuma ka bani cin hanci" ya gyara zama yana shafa aljihunsa sannan yace "whatever you want, just say it, kin san cewa I can give the world to you idan da tawa ce. I can go to the ....to the..." "End of the earth " ta karasa masa, yace "yeah, right, I can go to the end of the earth for you if you want me to" ta danyi murmushi tana kallon hannun ta, da alama hankalin ta ya fara tafiya wani gurin daban kamar yadda ta kanyi a duk lokacin da yayi mata maganar aure, absent mindedly tace "but earth doesn't have an end, it is spherical" yace "I don't care. Kin dai gane me nake nufi ai. I can do anything for you" bata ce komai ba sai ta juya kanta tana kallon waje, yayin da shi kuma ya rage ido yana kallon ta kamar mai tunani sai yace "but how do you do it?" Ta juyo tana kallon sa tace "do what?" Yace "finish my sentences. You always seem to know abinda yake raina tun kafin in fada" ta danyi kyakkyawan murmushin ta idanuwan ta suna reflecting tarin soyayyar sa da take cikin zuciyar ta tace "because I am your soulmate". ****.        ****.      ****.     ****.    **** "I am your soulmate" yaji muryar ta tayi amsa kuwwa a cikin kwakwalwar sa. Kansa yake ji kamar zai tsage gida biyu. Ya saka hannu ya dafe goshin sa amma kuma sai yaji ciwon kamar a tsakiyar kan yake, amma kuma kamar ba ciwo ba, kamar wuta ce ake hurawa a cikin kan nasa da zafin ta yake saka gumi tsiyayowa daga cikin gashin kansa zuwa fuskarsa zuwa sauran jikin sa. Ba ciwon kan ne ya fi damunsa ba, ciwon da zuciyarsa take masa ne yafi addabarsa. Wani irin zafi take yi masa mai kama da ƙaiƙayi , gashi tana lullube a kirjinsa dan haka babu damar sosa ta. Ya saka daya hannun ya dafe zuciyar tare da yin  ajjiyar zuciya da niyyar rage azabar amma sai yaji tamkar kara kaikayin yayi. Dama wannan shine heartbreak din da ake faɗa, wannan azabar shine abinda yan social media suke wasa da shi har suke kiransa breakfast? Amma lallai duk wanda yayi wasa da wannan to bai taba shiga irin wannan yanayin ba ne ba. Bai taba jin yadda ake ji ba, ba'a taba yi masa abinda aka yi masa yanzu ba. She was his life. For years, bai taba hango future dinsa ba tare da ita ba. Bai taba ko da tunanin cewa zata iya rabuwa da shi ba because she lead him on, ta nuna masa soyayyar da bai taba tunanin akwai algus a cikin ta ba. Ya gama shirin komai na auren ta. Ya gama plan din komai. A mind dinsa har yayan da zasu haifa yayi picturing din su da kuma irin soyayya da kulawar da zai basu. Gidan da zasu zauna ya gama shi tuntuni. Ita kawai yake jiya, green light kawai yake jira daga gare ta and then suddenly bayan tayi tafiya ta dawo she came to his office da katon ciki a jikin ta and said "I am married. I have been married for years. I am sorry" And then she said "it was all a misunderstanding. I never thought you love me. You never said you love me da na gaya maka cewa I am married ". "Damn it!" ya fada da karfi tare da mikewa tsaye kamar wanda aka yiwa allura. Sai kuma ya dafa bango sannan ya koma ya zauna, bai san ya akayi ba sai ya samu kansa da murmushi. "Ka zare Muhammad" ya fada wa kansa "ta haukatar da kai. Shi kenan ta ka ta kare. Yanzu ma gashi nan kana magana da kanka" sai kuma ya daki goshinsa da tafin hannunsa "damn you" sai kuma ya sake yin wani murmushin. May be haukan will be a blessing. At least in ya haukace gidan mahaukata za'a kai shi ayi tayi masa alluran bacci har karshen rayuwar sa. Then he wouldn't have to think about her. Then he wouldn't have to miss her, miss her smile and laughter, miss the feeling of blood rushing through his body whenever he gets close to her, miss the feeling of excitement whenever his phone rang and he saw her name "Piya❤️". He already miss tsokanar da take masa, tana enjoying tsokanar sa sosai saboda sunan kakanta ne dashi, she used to say "Malam Muhammadu dan fulani, ka ga yar kyakkyawar budurwa shine ka gudo daga riga ka zo ka makale mata" To ko wannan ma tsokanar ce? Yaji wani irin hope ya ratsa zuciyar sa . Cikin sauri ya fara neman wayarsa har yana zubar da wasu daga cikin takardun kan desk din, ya dauka da sauri yayi dialing number din ta sannan ya saka a speaker, a ransa yana karanto addu'ar da bai ma san addu'ar menene ba. Wayar ta shiga amma har ta gama ringing ba'a dauka ba. Ya kira daya layin nata shima ya gama ya katse bata dauka ba. Sai ya kuma kiran na farkon "The number you are trying to call is not available at the moment....." Ya katse. "Damn it!" Ya sake kira, still the same response. Wani bangaren na zuciyarsa ya fara gaya masa cewa blocking dinsa tayi. "she just blocked you guy" ya fada a fili. "she blocked me" ya maimaita da karyayyar zuciya. Ba wasan bane ba kenan. Ba mafarki bane ba kuma. Da gaske ne. Da gaske ne abinda tazo ta gaya masa yanzu. Abinda ya gani a jikin ta yanzu. But how can that be? How evil can she be? Ta yaya zata kasance mai aure through out all zamantakewar su? Ta yaya zai kasa ganewa? "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" Ya fada a fili. He told her that he hates her amma kuma few minutes later babu abinda yake son gani a duniya sama da ita. Babu abinda yake so sama da ita. Babu kuma abinda yake ƙi sama da ita. Is that even possible? ****.    ****.    ****.    ****.    ****.     *Her* 🧕🏻 Nayi kokarin dora thumb dina a ignition amma sai na kasa saboda yadda hannuna yake rawa. Na rike hannun da daya hannun da niyyar bashi support amma sai suke rawar a tare. Sai na hada su duk biyun na rungume a kirjina tare da jan dogayen numfashi sau uku ta hancina ina saki ta baki na da niyyar calming nerves dina down ko dan na samu damar driving zuwa gida, dan na tabbatar idan nayi driving a halin da nake ciki to kuwa akwai matsala ba karama ba, but part of me didn't care about matsala, a percentage of that part even hoped for matsalar, amma nasan in dai har matsalar da nake fata ta faru bisa ganganci ko son rai na to zan hadu da ubangiji na dan shine ya bani rai kuma shi kadai ne yake da ikon karbar ran nawa. Na sake attempting kunna motar, ta tashi sannan na saka ta a drive na dauki hanyar fita daga school ɗin, a raina ina tabbatar wa da kaina cewa wannan shine ganin da zanyi wa makarantar na karshe kamar yadda na yiwa Muhammad kallon karshe a yau. Absentmindedly na dinga driving ɗin, a hankali kamar mai shiga daki, ba tare da na damu da motocin da suke ta yi min horn a baya na ba, da yawan su in sun gaji da horn din sai su yiwa kansu hanya su zo su wuce ni a guje tare da jeho min kallon banza wanda ko kaɗan bai bata min rai ba. Ni yanzu naci dubu sai ceto. A hanya naga restaurant din da na kawo Muhammad last birthday dinsa, ranar da ta raba mu rabuwa ta har abada. Na tuna maganar da ya gaya min a lokacin. "Wata shekarar ba zata zagayo ba Piya in sha Allah sai da ke a dakina" nayi murmushi cikin yarda da hakan "insha Allah" ya bude ido "da gaske? Da gaske kike kin gama jan ajin?" Na lumshe ido na bude tare da langwabar da kai ina kallon sa "zaren nawa naga yana kokarin tsinkewa. Besides, na ga alamar ba zaka iya rayuwa babu ni ba". Yace "exactly. Ba zan iya rayuwa babu ke ba". Na dauke idona daga kan restaurant din ina kokarin cire tunanin ranar daga raina. In dai har na cigaba da tunanin ranar to ba zan iya karasa wa gida ba, maybe sai dai a karasa da ni. Ina tsayawa a bakin gate, tun kafin inyi horn mai gadi ya bude gate din, nasan dai ya gaishe ni amma banji me yace ba sai kawai na gyada masa kai na shige ciki. Addu'a daya da take raina ita ce Allah yasa kar in hadu da kowa har sai na shiga dakina, bana son ganin kowa a lokacin, bana son kowa ya ganni a halin da nake ciki dan bana son tambaya. Sai dai addu'a ta bata karbu ba, ina yin packing naga Yaya Mustapha shima yayi packing a kusa da ni. Na rufe ido na "ya Salam, not him, not now please God" amma ita ma addu'ar bata karbu ba dan yana fitowa daga motar sa direct window na ya taho, ina kallon sa through tinted glass dina ya tsaya ya gyara zaman hular kansa da kuma collar din rigar sa sannan yayi knocking glass din. Na rufe ido na tare da jingina kaina a jikin kujerar motar, "ya Rabbi" na fada a hankali "ya Rabbi give me strength" sannan na kashe motar na bude kofa da sauri na fita. "Fiyya" ya fada yana kokarin haɗa ido da ni. "Ina kika je haka? Daddy ya tayar da hankalin kowa a gidan nan yana neman ki" sai kuma yayi shiru yana karewa fuska ta kallo "are you okay? Are you crying?" Tambayar da yayi min ce ta saka na shafa fuskata sannan na kalli hannun, ni kaina ban san kukan nake yi ba sai lokacin na fahimci tun daga school nake kuka har gida. Ban ce masa komai ba na zagaye shi na wuce, har na shiga ciki ina jin idanun sa a kaina. "God Please... Allah dan Allah.... Allah kasa ba shi bane ba. I cannot take it idan shine". Sai dana dan tsaya a bakin kofa ina karewa parlor kallo ina lissafin ta inda zan bi yadda ba zan haɗu da kowa ba, duk da cewa ma dai gidan babu mutane sosai dan zuwan mu kenan gari jiya kuma gobe zamu sake barin gari. Kuma babu ma'aikata sosai a gidan tunda ba a garin muke da zama ba. Babu kowa da na gani, dan haka na fara tafiya a hankali making sure ban making sound ba har na kusa hawa stairs, a lokacin ne naji muryar Esther. "Madam? Are you okay?" Na runtse ido na tare da kokarin goge hawayen fuska ta amma ina gogesu wasu suka yi replacing din su. Wannan yasa ban juya na kalle ta ba nace cikin muryar da naji kamar ba tawa ba "I am fine. Don't let anyone enter my room" da haka na cigaba da hawa sama ina jinta tana cigaba da wata maganar da ban fahimci me tace ba. Ina shiga dakina na tura kofa na murda lock sannan na jingina da jikin kofar, a hankali kuma sai na zame na zauna a gurin sannan na dira goshina akan gwuiwowina. Abinda kawai nake bukata kenan tun dazu, seclusion din da zan saki kuka na son raina ba tare da wani yayi min magana ba. A lokacin waya ta tayi kara, da kida na musamman da na saka wa Gidado, kidan da yakan saka zuciyata cikin nishadi a duk lokacin da na jishi saboda dokin jin muryarsa. Na dauko wayar na tsaya ina kallon sunan sa da yake blinking akan screen din "Pyar❤️" Naji wani sabon kukan yazo min "Allah sarki Muhammad" na fada a fili. "Allah ka dubi bawan ka ka bashi sassauci" na tuna da irin bakaken maganganun da ya gaggaya min daxu a office dinsa, amma mintina kadan har hana kira na. It won't be easy for him. It won't be easy for me. Kiran yana katsewa na lalubo block button na danna wa number din sa. Abinda ban taba tunanin zan iya yi ba a rayuwa ta. Amma nasan halinsa a kaina, he won't stop calling hakan kuma yana nufin I might answer, in na amsa kuma komai ya rushe kenan. Sai dai ina dauke hannuna kiran sa yana sake shigowa through my other line. Shima jiran sa nayi ya katse sannan nayi blocking dinsa ta chan din ma. Abinda kawai nake hangowa a idona shine fuskar Gidado a yadda na baro shi a office dinsa da zu. I have never in my life seen someone as broken as he looked. And why won't he? Na yaudare shi iyakacin yaudara, na cutar da shi iyakacin cuta, na kuma tabbatar ba zai taba yafe min ba. Amma a ganina hakan shine dai dai, hakan shine zai fi masa alkhairi, he will heal with time dan ban taba jin wanda yaki warkewa daga heartbreak ba, he will find someone and marry and have children kamar yadda yake da buri, and life will go on while I face my demons alone. Na shafa cikina wanda shine silar komai, a raina ina jin ina ma dai zan iya gayawa Gidado gaskiya, ina ma dai zai iya sanin gaskiyar cikin. Maybe it will reduce his suffering na dan lokaci kadan, but it will torment him for the rest of his life. Ni kuma simplest way out nake nema masa. Karar knocking naji a kofa, banyi magana ba dan nasan muryar ba zata fito ba, aka sake wani tare da magana a lokaci daya, muryar Safina "Fiyya na san kina ciki fa, Daddy ne yake neman ki tun dazu" na girgiza kaina, a raina nace "Daddy, Daddy na" sai kuma na mike da sauri na bude lock ɗin kofar, saurin da na tashi da shi da kuma yanayin da nake ciki ya saka jiri ya debe ni, Safina da take tsaye a bakin kofa tayi ssurin rike ni. "Fiyya? Lafiya kike kuwa? What happened again?" Ban ce komai ba na ture hannunta daga jiki na na kama tafiya da sauri zuwa part ɗin Daddy. Safina ta biyo ni a baya tana cigaba da magana. "Magana fa nake miki Safiyya, at least ki tsaya mana kiji abinda nake ce miki. Ne yake damun ki ne? Nasan kina cikin wani hali and I sympathize with you but that doesn't gives you the right to be rude to us. Dazu naji Yaya Mustapha ma yana gaya wa Mommy cewa yayi miki magana kin share shi. Ko ba komai ai ......" Tana ta maganganun ta ni kuma ina kallon jerin hotunan da akayi wa stairs ɗin Daddy ado da su, hotunan segments na kamfanonin sa, kamfanoni na. A lokacin muka kawo bakin kofar part ɗin Daddy, na juyo da sauri ina kallon ta nace "what exactly do you want Safina?" Ta tsaya tana kallon na cikin mamaki, sannan kuma sai tace "I tried to help you, we, your family, are always trying to help you because we love you. At least a thank you would be....." "Thank you" na ce mata sannan na bude kofar na shiga na mayar na rufe. Ina shiga parlon idona ya shiga cikin nasa, Allah kaɗai yasan irin dadewar da yayi a zaune yana kallon kofa yana jiran shigowa ta. A fuskarsa naga alamun damuwa sosai, ya kalle ni ya kalli cikin jikina. Yanayin fuskarsa kadai ya isa ya saka mai karyayyiyar zuciya fashewa da kuka. Mommy tana zaune a kusa dashi itama tata fuskar cike da damuwa. "Am sorry Daddy" na fada tare da sunkuyar da kaina kasa ina kallon yan yatsun kafata. "You are sorry?" Ya maimaita cikin muryar da take kara nuna halin rashin lafiyar sa. Jirin da bai gama sakina ba ne ya sake ɗibana, na ga ya yunkura da sauri zuwa gurina sai Mommy tayi sauri ta rike shi ta zaunar da shi sannan ita ta taho gurina. Ta rike ni a jikin ta tare da fara faɗa. "Kin gani ai, zaki jawo wa kanki matsala ki jawo wa mahaifinki shima matsala, Safina me kike so ki zama ne ni Sa'adatu?" Sai kuma ta tsaya tana karewa fuska ta kallo. "Me ya faru da ke Safina? Kukan menene kike yi haka ?" Daddy na ga ya sake kokarin mikewa. Nayi sauri na saki Mommy na karasa inda yake na durkusa a gaban sa. Ya koma ya zauna yana kallon fuskata wadda duk da ban kalli mirror ba na san ta kumbura saboda nauyin da naji ta yi min. Ya sauke ajjiyar zuciya. "What am I going to do with you Safiyya?" na sunkuyar da kaina kasa. "Me zan yi miki ne wai?" Ya sake tambayar no one in particular. Ban amsa ba dan bani ya tambaya ba. Ko ni ya tambaya din ma bani da amsar da zan bashi. Mommy ta dawo ta zauna a kusa da shi. Sai naga ya juya yana kallon side ɗin sa, ni ma na juya na taya shi ganin abinda yake kallo Hoton ta ne, tayi kyau sosai tana murmushi kamar za'a ce Safiyya ta amsa. Sai naji ina jin haushinta dan ita ce silar komai. Daddy might not know it yet but ni na sani in my bones and soul cewa ita ce silar komai. Sai dai bani da wani evidence da zan nuna masa. Bani da yadda zanyi in kare kaina. To gain access to the book contact 👇 0704 203 0419 Ta manhajar telegram ****.    ****.    ****.    ****.     ****.     **** ❤‍🩹*SAFIYYAH*❤‍🩹 *Episode Two (2): The Young Passengers* Na sauke idona daga kallon hoton zuwa kasa, ita ta jawo min duk abinda yake faruwa da rayuwata na sani, amma kuma na san cewa dan Adam baya taba wuce kaddarar sa, rayuwar da tayi ita ce tata kaddarar, nima kuma halin da nake ciki shine tawa kaddarar, kuma na sani cewa addu'a tana chanja kaddara dan haka har yanzu ban gaji ba kuma ba zan taba gajiya ba wajan gyara rayuwata. She was my role model, she has always been. Courage da determination dinta su suke hana ni giving up a lokuta da dama. Yadda ta chanja rayuwar ta from worst to best haka nima nake fatan chanjawa. Giving up has never been in her dictionary and it is not in mine. Kamar yadda Daddy yake yawan yin comment a lokuta da dama, lokutan da muke good time da shi, cewa her fire is burning in me, cewa I have her zeal, strength, bravery and stubbornness, wannan shi nake so in yi proving right. Maganar Daddy ce ta dawo dani daga tunani na. "Safiyya, daga ina kike? gurin sa kika je ko?" Na dago kai na kalle shi, sai na yi sauri na sake sunkuyar da kaina dan ba zan iya cigaba da hada ido da shi ba. Mommy tace "baban Mustapha, kasan dai ɓata lokacin ka da ranka zaka yi a gurin tambayar Safiyya a game da maganar nan, ba zata yi magana ba, wata nawa ana fama? Wacce irin tambaya ce bamu yi mata ba?" Yayi ajjiyar zuciya cike da damuwa yace "na sani Sa'adatu, na kasa hakura ne, gani nake kamar watarana zata tausaya min a matsayi na na mahaifin ta" Naji hawaye na yana sauka akan hannayena da suke kan cinyata. "Am sorry Daddy " na fada a hankali "Sorry she said" ya maimaita. "Abinda ta iya fada kenan in anyi mata magana tace sorry" ya fada cikin kokarin daga murya, sai kuma yayi shiru yana mai da numfashi. Mommy tace "abinda yasa kika dage da nacin sai mun biyo ta Abuja kenan ko? Kika yaudare mu mukayi tunanin you are after your father's health ashe ke kina da plan din ki da kika shirya ko Fiyya?" Na girgiza kai da sauri amma kuma part of me knows gaskiya take faɗa, except maganar daddy's health, tabbas dan in ganshi na nace sai mun tashi ta Abuja. "Ba kuma zaki fadi ko waye shi ba ko?" Ta sake tambaya with hopelessness in her voice. Daddy yace "ba zata fada ba kin sani. Wallahi da na san zaki iya risking mutuncin ki da na family dinki ki fita ki tafi gurin sa da na ɗana miki tarko, da na saka an biki a baya an gano min ko waye shi, kuma wallahi da nayi masa abinda har ya mutu ba zai manta ba kamar yadda yayi min abinda har in mutu ba zan manta ba, da na rusa rayuwar sa kamar yadda ya rusa taki, da na....." Sai yayi shiru yana jan numfashi a kokarin daidaita numfashin sa da ya fara fita sama sama. Na fara tracing tun sanda na fita har zuwa sanda na dawo a raina, ina so inga ko na haɗu da wani da ya san ni ko kuma na bar wani hint da zai taimaka wa Daddy yayi tracing Gidado, har sai da na tabbatar babu sannan naji hankali na ya fara kwanciya. Ba damuwa ta abinda Daddy zai wa Gidado in ya kama shi ba, cos I doubt idan zai iya yi masa komai, damuwa ta shine in akayi tracing Gidado to zai san komai, zai san gaskiyar komai and his parents will be involved too, our school management will also be involved, wannan duk yana nufin bacin sunan Gidado, sannan yana nufin goga masa baƙin fenti na har adaba. Wannan kuma shine abinda nake gudu, shine abinda zuciya ta ba zata iya dauka ba. Ina cikin tunani na naji Daddy yana waya, "Mustapha kazo sama yanzu ina neman ka". Sai hankali na ya dawo jikina, wancan tashin hankalin ya marsa ya bawa wani sabon tashin hankalin gurin zama a cikin zuciya ta. "God, not him please" na fada a hankali ina mummurza yan yatsun hannuna cikin tsananin damuwa. Tabbas ni nace da Daddy na amince da duk wani hukunci da zai yanke a kaina duk a kokari na ganin na rage masa radadin abinda yake tunanin nayi masa, amma kuma zuciya ta tana kakkaryewa a duk lokacin da ta hasaso hukuncin nasa, na san aure zai yi min, kuma na amince da auren amma kuma damuwa ta shine wa za'a aura min? Wanene Daddy zai zaba min a matsayin abokin rayuwata ta har abada. Shin zai zama blessing to me or a curse? A raina nasan few choices ɗin da Daddy zai iya yi. A kokarin sa na kare mutuncina dana family din mu dole na san auren gida zai yi min. Wannan yayi limiting choices dinsa zuwa mutum uku kacal, mutum ukun da dukkan su babu wanda ba zai iya lasar tafin kafata ba in dai za'a aura masa ni, mutum ukun da duk kan su babu mai sona, mutum ukun da duk kan su babu wanda nake so. Mutum ukun da daya daga cikin su yake da hannu wajan bata tsakanina da Daddy, daya kuma yake da hannu dumu-dumu a cikin halin da nake ciki a yanzu. Sai dai bani da tabbas ɗin who is who. Ba kuma ni da shaidar nuna wa Daddy. But the fork is my only way out..... If only I can find the fork..... If only I can find it's marks.... Muryar yaya Mustapha ta katse min tunani na. Na dago kai muka hada ido sai nayi sauri na mayar da kaina kasa ina jin bugun zuciya ta yana ƙaruwa. Ya zauna a kasa nesa da ni kaɗan. "Daddy gani" Daddy yace "kaje motar Safiyya, check the dashboard camera, find out ina taje dazu, if possible, find out da wa ta hadu". Ban daga kai na kalle su ba har ya fita, sai dai yawun baki na gabaki daya ya dauke, numfashi na ya tokare a kirjina. "Why didn't I think of the damn camera?" Na rafa lissafin way out a raina. Tabbas camera ba zata nuna Gidado ba, amma zata nuna makarantar mu da kuma dai dai inda nayi packing wato kofar building din da yake dauke da offices na some staff. And weekend ne. Few staff ne suka shiga a ranar. If police got involved zasu iya gano wadanda suka shiga a ranar and it will take Daddy closer to Muhammad. Mara ta naji ta rike da wani mugun fitsarin tsoro. Hawayen ido na ya kafe. Na zauna zaman jira ina jina kamar akuyar da aka kai mayanka take jiran turn ɗin ta. Bai jima sosai ba ya dawo ya sake zama a inda ya tashi. "Daddy ta kashe camera din kafin ta fita" ya fada yana kallon Daddy. Na dago kai da sauri na kalle shi. Muka haɗa ido sai ya kuma dauke kai fuskarsa expressionless ya cigaba da kallon Daddy. Daddy yayi ajjiyar zuciya "I should have known. She is always too smart for her age, tun tana yarinya she has always been two steps ahead of mates din ta. But still ban dauka zata yi tunanin wannan angle din ba". Mommy tace "ban taba dauka kawaye zasu yiwa mutum rana ba sai akan case ɗin Safiyya. Da ace tana da kawaye na tabbatar zamu samu wani information ko yaya ne daga gare su. Safina kuma tayi iyakacin nata kokarin" Na tuna da kokarin da Mommy take nufin Safina tayi. A raina nace "munafuka ba" tunanin abinda tayi ɗin ya kara min zafi a zuciya ta. But yaya Mustapha, me yake up to da zai yi wa Daddy karya? Akwai wani abun da yake bukata tabbas. "Tashi ki tafi" Daddy yace Na mike still idona a kasa, har na fara tafiya naji Mommy tace "ko parlor ban yarda ki sake fitowa ba sai in zamu bar gidan nan. Kuma wallahi kika fita sai ranki yayi mugun baci". Na ɗan dakata sannan na juyo ina kallon ta nace "to Mommy" a raina nace na riga na gama abinda ya kawo ni abuja ai, na gama da Nigeria ma gabaki dayan ta, bana fatan wani abu ya sake dawo dani kasar nan. Na kai bakin kofa naji Daddy yace "kai Mustapha ka zauna, akwai maganar da zamuyi" na sake dakatawa tare da rintse ido na, sannan ba tare da na juyo ba, na yunkura na bude kofar na fita. Kafin in shiga dakina na haɗu da Esther duk a tsorace. Ta biyo bayana "Madam am sorry, ban san an shiga dakin ki ba. Sai dana ce mata kar ta shiga. Na dakata da tafiyar ina kallon ta ina mamakin yadda ta daga hankalin ta akan karamin abu nace "it is okay Esther, relax, she is my elder sister ni kaina ba zan iya hanata yin abinda take so ba". Na dauka Esther tana yi min maganar knocking da Safina tayi dazu a dakina ne, sai da na bude kofar dakin na shiga sannan na fahimci ba wannan bane ba. Duk an zazzage contents ɗin cikin jaka ta akan gado, da alama wani abun ake nema sai dai ban san menene ba ballantana in san ko an samu ko ba'a samu ba. Naga wayata a yashe a gefe, na dauka naga ta nuna alamar anyi ta trying budeta an kasa. Na zauna a bakin gado ina tsince tarkace na tare da mayar da su cikin jaka. Na bude wayar using face lock ina kallon hoton da na saka a matsayin screen saver dina. Hoton hannun Muhammad Gidado ne, ya dora akan sitiyarin motar sa, da zubunan azurfa guda biyu a yatsunsa, da agogo a wrist ɗin sa. Na tuna sanda na dauki hoton, muna cikin motarsa ne, motar da take holding most of our memories together. ****.      ****.    ****.    ****.    ****.    **** Lokacin yana yi min korafi ne kamar kullum, yayin da ni kuma nake ƙoƙarin mayar da korafin nasa wasa ta hanyar tsoakanar sa. "Abba yana ta yi min maganar komawa gurin sa da aiki" nace "inye, rich kid.... Irin born with a golden spoon din nan ko? Babu ruwan ka da neman aiki sai neman ka ma ake yi ko?" Ya bata rai "you know what I mean kina so ki chanja magana ko? Dazu har fushi yayi, he thought pride ne ya saka nake zaune a makarantar nan bana so inyi aiki a karkashin ss and I am hurt that he thinks that" na gyara zamana with a serious face nace "then do what he wants. You are just enslaving your self here and it is hurting me too" Yace "you think so? Tell me in na bar makarantar nan how am I gonna be seeing you? Safiyya ko gidan ku fa ban sani ba and it has been years muna tare, i know cewa ina barin makarantar nan ko ta kaina ba zaki sake bi ba" Nayi shiru ina kallon sa, yace "what? Ba gaskiya na fada ba?" Nace "kasan me yake damunka?" Yace "insecurity, yes, I am insecure when it comes to you, bani da wani concrete stand and I know anytime zaki iya ajiye ni a side and the thought alone is given me nightmares and...." Nace "you once jokingly asked me me yasa nazo makarantar nan out of all the universities in the world, you jokingly said I followed you here because I cannot live without you, I laughed then amma abinda ban gaya maka ba shine gaskiya ka fada a lokacin, I came here because you mentioned ranar nan da muka hadu cewa kana nan makarantar for the time being. I wanted to be with you. I wanted to see you again. I literally threw a tantrum a gaban Daddy akan lallai nan makarantar nake son zuwa" Na fada ina tuna yadda na kwanta ranar na ringa birgima a gaban Daddy ina kuka shabe shabe da hawaye. Bai ce komai ba ya saki baki yana kallona, na sunkuyar da kaina na cigaba "I was hoping in mun sake haduwa zaka karbi number ta. And maybe say you love me" Yace "Piya? Are you saying that you... " Na saka hannu na biyu na toshe kunnuwana "forget I ever said that. Lala la lala" yayi dariya amma naji relief da excitement a cikin muryar sa sosai, hankalin sa ya kwanta ya samu assurance ɗin da yake so. "Piya, you are impossible. But if that is true then ki kaini gidan ku mana please, at least let then know me yadda zamuyi all these the right way" Na gyada kai "soon insha Allah. Na gaya maka family house din mu yana kano shi yasa ban taba kai ka ba, and Daddy bashi da lafiya yana Pittsburgh ganin likita. In yazo gari I will talk to him and he will tell me what to do. We have nothing to worry about". Yayi ajjiyar zuciya "am sorry Piya, nasan ina ta damun ki kullum, i don't know why zuciya ta ta kasa nutsuwa, ina ta feeling restless kullum. But i promise zan gyara halina" ya fada guiltily. Nayi kokarin chanja topic ɗin ta hanyar daukar hoton hannun sa da ya ke kan stirring "wow! rich kid! Wa ya siya maka sabon agogo? Mommy ko Daddy" na fada cikin tsokana, ya kalli agogon sannan ya kalle ni da sigar harara "ni ne rich kid ɗin? An gaya miki mina ɗan zaman kashe wando ne irin ki? Ma'aikaci ne ni if you don't know" Nace "I don't know nawa suke baka but am sure albashin ka ba zai siya maka wannan agogon ba. So, tell me the truth, I promise ba zan fada wa kowa ba. Mommy ce ta siya maka ko Daddy?" Yayi dariya "ask those who call their parents mommy and Daddy that question, misali you. Ni dan gidan Mama da Abba ne. And I don't throw tantrums idan ina son abu" na dafe kai na "shi kenan kuma na shiga uku a hannun ka. Kayi ta tsokana ta kenan har illa masha Allah " yace "tabbas, har ƴaƴan mu sai na bawa labarin yadda kika makale min kike bina duk inda na tafi" na rike bakina ina jin haushin fada masan da nayi nace "me and my big mouth" yace "you and your cute lips". ****.    ****.    ****.    ****.    ****.    **** Karar knocking kofa ta dawo dani daga tunani na. Ba tare da na dauke ido na daga kan hoton ba nace "come in". Naji an bude kofa an shigo an mayar an rufe, a tunani na Safina ce, sai dai kamshin turaren da naji ya saka na dago kaina na kalli wanda ya shigo. Yaya Mustapha. Kallo daya nayi masa na sake mayar da kaina na cigaba da aikin kallon hoton da yake kan screen din wayata. Ya zauna akan side drawer yana kallo na. Ganin bani da niyyar yi masa magana sai yayi gyaran murya yace "babu godiya ma ko?" Still ban ce komai ba kuma ban kalle shi ba. Yayi ajjiyar zuciya sannan ya mike tsaye ya tsaya a gaba na. "I just saved you and your precious love a gurin Daddy amma ko godiya ba zaki yi min ba?" Na dago kai da sauri ina jin zuciya ta tana yin zafi nace "yaya Mustapha, what do you want? Me kake bukata daga gare ni?" Ya koma ya zauna muna kallon juna yace "at least a little concern. Fiyya ni yayan ki ne and I love you with all my heart amma I can't help but feel like kin tsane ni kuma ni har ga Allah ban san me nayi miki ba. Tunda abin nan ya faru babu abinda nake yi sai kokarin ganin na faranta miki na rage miki radadin abinda yake damun ki. Only God knows how many times nayi wa iyayen mu karya dan in kare ki. I have nothing to do with abinda kika yi, I have nothing to do with decision ɗin iyayen mu na haɗa mu aure. But why are you cold toward me bayan da ba haka kike min ba?" Na dauke idona daga kansa ina maimaita abinda yace a raina, decision ɗin iyayen mu na haɗa mu aure, so shine kenan, shi Daddy ya zaba, and he is the worst among the three. A hankali nace "Dan Allah.... Ka tashi ka fita..." Ya sake yin ajjiyar zuciya yace "okay zan fita. But just know that in akwai wani abu da kike bukata, just let me know " Bance komai ba har ya mike tsaye. Ban ankara ba kawai sai ji nayi ya kwace wayar hannuna. Na mike tsaye da sauri kamar wadda aka dorawa garwashin wuta a cinya, yayi sauri ya matsa daga kusa dani yana kallon hoton yana murmushi. "Wow. Nice hands...... And that skin...... I bet he is Arab" Ban ce komai ba na tsaya kawai ina kallon sa zuciya ta tana tafasa. Ya cigaba "and he is rich too..... Cos wannan wrist watch din nasa zai sayi kayan jikina kaf har da chanji" Ya dawo yazo ya tsaya a gaba na "I feel for you dear. But it is what it is. Allah yasa haka shi yafi alkhairi". Ya ajiye wayar akan gado kusa da ni sannan ya ce "lecturer ne ko student? Ko kuma non-academics ne?" Naji kamar in rufe shi da duka amma ko motsi ban yi ba. Ganin bani da niyyar ce masa komai sai ya daga kafada yace "okay. Whenever you want to talk I will be glad to listen" Daga haka ya juya ya fita. Na koma na zauna na dauki wayata na fara aikin goge ta kamar wadda aka shafa wa datti. "Munafuki" na fada a fili "munafukai. Bunch of munafukai. Dukkan ku munafukai ne" Na tuna tambayar da yayi min akan dalilin da yasa na tsane shi. Tabbas a yanzu kusan na tsani kowa amma tashi tsanar ta musamman ce. Wannan kuma yana da nasaba da sunan shi. Sunan shi aka ambata a lokacin da aka kira ni. Kiran da ya chanja dukkan rayuwar. "Fiyya! Kina ina? Mustapha ne. Jikin Daddy ya tashi mun tafi dashi asibiti. Hurry up" Na rufe idona ina jin maganar tana amsa kuwwa a cikin kaina. And it sounded just like him. "Allah ya isa" na fada a fili. *Him 👳🏻* Ya dauki hours a cikin office dinsa dan har sai da yaga magrib ta gabato sannan ya fita, shima kuma ya fita ɗin ne kawai dan yasan rashin zuwa gidan sa zai tayar da hankalin mahaifansa. A gidan su suna da wata doka da ya fahimci cewa ta samo asali ne tun daga kakannin sa na wajen uba, dokar kuwa itace kowa must be home before magrib komai girman ka in dai kana gari, dole tare zakuyi sallah magrib da Abba, tare kuma zakuyi dinner. A dinner din ne ake discussing must of the issues da suka shafi family. A dinner din ne kuma must of the times ake matsa masa da zancen aure. Ya dinner ɗin jiya ne yayi musu alkawarin yau Safiyya zata shigo gari, and yau din ne yake saka ran zata bashi go ahead na zuwa gurin iyayen ta. Ya rufe office din ya sauko daga stairs din blindly ya bude motar sa ya shiga. Kafin ya tayar da motar ya dauko wayarsa for like the hundredth time ya kira layin ta. Still baya shiga. Ya kuma san ba zai shiga din ba tunda ya tabbatar tayi blocking dinsa. Amma kuma ya kasa daina kiran ta. He just couldn't let her go. Ba zai iya ba. Ya tabbatar ba zai iya ba. Ya san cewa dating dinta da yayi a matsayin ta na matar aure ba laifin sa bane ba tunda bai sani ba, Allah kuma ba zai kama shi da laifi ba, amma kuma in ya cigaba da bibiyarta a yanzu bayan yasan tana da aure to tabbas Allah zai kama shi. Amma ya zaiyi? "I just want to confirm" ya fada a fili kamar mai kokarin kare kan sa. But confirm what? Wanne confirmation yake bukata bayan wanda ya gani a jikinta? Ciki ne fa da ita, cikin ma kuma ya kwana biyu, duk da shi ba mace bane ba amma yasan cikin zai kai around five to six months. Ciki a jikin Piyan sa. Ya rufe ido tare da dora kansa a jikin stirring yana jujjuyawa. Me zai yi ne? Ta ina zai rarrashi kansa? Wacce amsar zai bawa Mama a yau in ta tambaye shi game da maganar da suka yi jiya? Shi dai ba zai ce mata ashe Safiyya tana da aure ba, he can only imagine irin kallon da zata yi masa idan ya fada mata haka. Ta ina zai fara..... Ina zai samu ruwan da zai kashe gobarar da ta tashi a cikin kirjin sa? His worst nightmare have come to be. Safiyya ta barshi.... Bari na har abada. Ya daga kansa ya jingina shi a jikin kujera, komai ma baya yi masa dadi. A lokacin ne yaji danshi a fuskar sa, ya saka hannu a hankali ya shafa sannan ya tsaya yana kallon abinda ya shafo. Hawaye. Sai ya samu kansa da yin murmushin takaici. Kuka? Wai shine yake yin kuka? Ba zai iya tuna sanda yayi kuka ba tunda yake a rayuwar sa. He has always been strong, emotionally and physically. Mama tayi training dinsa to be a strong man. Amma kuma dama can when it comes to Safiyya to he is the weakest man alive, a hopeless romantic. Da ace labari za'a bashi cewa zai yi wa budurwa kuka da tabbas sai ya kusa faduwa saboda dariya. Amma kuma dama hausawa sunce duk abinda kace ba zaka iya ba to bai kama ka bane ba. Ya bude kofar motar ya dauko ruwa ya wanke fuskarsa, there is no way da zai bada damar a gane cewa yayi kuka, ballantana a gidan su, no way. Yana zuwa gida ya tarar har Abba ya fito zai tafi masallaci, Haidar yana take masa baya. Yayi sauri yayi packing a waje ya bisu a baya yana gode Allah daya kasance Abban sauri yake yi yasan da sai ya sha tambaya. Har suka yi sallah suka fito suka dawo gida bai yanke hukuncin amsar da zai bawa Mama ba. A parlor suka zauna kamar kullum suka kamo tashar labarai, ya wayan ce yana ta danna waya dan baya son yin magana da kowa, gani yake in yayi magana za'a gane me ya faru a cikin voice din sa. Sai dai ba abinda yake ganewa a wayar da yake danna wa dan hankalin sa sam baya tare da shi. Dariya yaji an kwashe da ita a parlon, ya dago kan sa sai yaga duk shi suke kallo suna dariya. "What?" Yace yana rarraba ido cikin tsoron kar dai maganar da yake yi a zuciyarsa ce ta fito fili. "Tunanin me kake yi ne haka?" Abba ya tambaya da dariya a muryar sa. "Tunanin Safiyya" Haidar ya fada shima cikin dariya. Amma maimakon Gidado ya taya su dariyar sai ya mayar da kansa ya sunkuyar ya cigaba da danna kira a layin Safiyya. Mama da ta gama guiding Hanifa ta zauna a kujera tana kallon Gidado, fuskarta cike da damuwa. " Me ya faru?" Ta tambaya tana kallon shi. Ya ajiye wayar tare da yin ajjiyar zuciya yace "babu komai Mama. I am just exhausted ne kawai. Tun safe nake aikin marking script har yanzu kuma ban gama ba". Ta gyara zamanta tace "abinda nake gani a fuskar ka ba stress bane ba, damuwa ce, in ma da akwai aiki to akwai wani abun daban. Me ya faru?" Ya mike tsaye yana kirkiro murmushin da ko lips dinsa bai wadatar ba yace "da gaske nake Mama. Bani da damuwa. Ko kadan. Yunwa dai nake ji" ya wuce su ya tafi dining ya zauna a kokarin sa na ganin ya gujewa cigaba da yi masa tambayoyi. Bai jima da zama ba suma suka taho. Yayi saurin wayancewa da zuba wa kansa abinci. Yana jin Daddy da Haidar suna maganganu akan karatun Haidar ɗin, Mufida tana saka musu baki kaɗan kaɗan, yana kuma jin idanun Mama a kansa. Ya debi loma ya saka a bakinsa, ji yayi gabaki daya bakin ya gauraye da daci kamar da ruwan madaci aka dafa abincin, makogwaron sa ya toshe abincin ya kasa wucewa ciki. Haka yayi ta taunawa dan babu damar ya zubar da shi, har daga karshe ya samu ya hadiye shi da kyar. Ya dago kai suka haɗa ido da Abba da Mama a lokaci daya, yayi sauri ya sake mayar da kansa kasa ya cigaba da juya abincin. Abba ya yi magana "Malam Muhammadu, what is it?" Ya ajiye chokalin hannunsa tare da yin kokarin bada uzurin da zai masking damuwar sa "uhmm.... Abba dama ..... Dama maganar aikin da muka yi da kai, ina ganin in ka yarda zan bar wannan din in dawo gurin ka kawai. Wannan ɗin is exhausting. Na gaji". Abba ya sake cewa "shi kenan?" Gidado ya gyada kansa kawai bai ce komai ba. Kamar daga sama yaji Mama tace "ya maganar Safiyyan? Tazo ɗin? Kunyi maganar?" Gidado ya sake daukan chokali ya cigaba da juya abinci ba tare da ya kalle ta ba yace "bata zo ba Mama. Bata samu damar zuwa ba" tace "but am sure kunyi magana da ita a waya ko? Kasan dai next week za'a zo saka ranar Mufida, ka kuma san na jima ina fadar cewa tare zan haɗa ku" ya gyada kai "na sani Mama. Bamu yi waya ba. Zamuyi amma". Sai kuma ya mike. "Bana jin dadi, bana jin cin abincin nan. Zan je in dan kwanta" Mufida ce tace "Allah yasa dai ba zazzaɓi zaka yi ba Hamma, fuskar ka tayi pale. Ya danyi mata murmushi yace "Ameen dear". Daga haka ya nufi hanyar da zata kai shi inda dakunan su suke. Har ya shiga ya rufo kofa yana jin idanuwan iyayensa a kansa. Yana shiga dakin sa direct gaban dresser ya tafi, ya tsaya a gaban full mirror dinsa yana kare wa kansa kallo. Ya saka hannu ya shafa fuskarsa yaji ta dauki zafi kamar mai zazzaɓi. Sai kuma ya lura da abinda Mufida tace fuskarsa tayi fari tas kamar takarda. Sai yaji muryar Safiyya a kunnen sa yadda take tsokanar sa. "Da wata farar fuskar ka anan" Tana fada ne a matsayin tsokana duk he knows she is saying it as a compliment, or so he thought. Duk sanda ta fadi haka shi kuma yakan mayar mata da cewa "da wata beautiful face dinki anan". Ya tuna ranar da ta fara ce masa me farar fuska. Ranar da ya fara ganinta a duniya. Shekaru da dama da suka wuce. Shekaru goma da suka wuce. He was just seventeen years old. And she was eleven years old. ****.    ****.    ****.    ****.    ****.     **** A cikin jirgi ne, ranar da zai bar Nigeria zuwa Manchester , United Kingdom dan fara karatun degree dinsa na farko. An riga an gama yi masa komai dan haka shi kadai aka saka a jirgi ya tafi. Wannan shine karonsa na farko na yin tafiya mai wannan tsahon shi kadai. Tun yana dan karamin yaro, ya kasance yana da aerophobia ma'ana fear of flying, duk sanda ya hau jirgi ya kan ji tsoro musamman a gurin tashi da sauka ko kuma in aka shiga turbulence. A duk sanda zasu yi tafiya tare da family yakan rike hannun Abba ko Mama, har sai jirgin ya daidaita sannan ya saki. A ranar kuma kasancewar babu Abba babu kuma Mama sannan babu kowa a seat din kusa da shi, sai ya kama handle din seat ɗin ya kankame tare da rintse idonsa. Sai dai duk da haka jiri yake ji, kansa juyawa ya ke yi. A cikin haka ne yaji an rike hannunsa. Ba tare da ya kalli waye ba sai ya damke hannun daya rike nasa ɗin da karfi har sai da jirgin nasu ya dai daita. Ya sauke ajjiyar zuciya tare da bude idonsa a hankali, sai kuma yayi sauri ya kalli side din da aka rike hannun nasa. Yarinya ya gani yar karama wadda ba zata fi sa'ar Mufida ba. Ta karkata kai side daya tana kallon sa fuskarta dauke da murmushi. Yayi sauri ya saki hannun ta yana yarfar da nasa hannun "You? Who are you? Where are your parents?" Ya karasa maganar yana duddubawa around them. Sai dai bai ga kowa da yayi kama da iyayen ta ba, kusan ma inda suke zaunen basu da yawa. Ya sake dawo da dubansa kanta yace "where are your parents?" Direct tace "my mother is dead. My father is in Manchester yana jirana" ya koma ya zauna sosai "are you telling me ke kadai aka sako a jirgin nan daga wata kasar zuwa wata?" Ta daga kafada tace "there is nothing to it really. Uncle Ahmad ya kawo ni airport ya danka ni a hannun cabin crew, they will take care of me har mu sauka and my Dad will be waiting" ya tsaya kawai yana kallon yadda take zarar magana yace "awwn, rich kids, yayan Daddy da Mommy. Now if you don't mind i need to sleep. Ki koma wherever it is that you came from. I don't want any trouble". Ta gyara zama. "i won't trouble you. I prefer sitting here" ya bata rai irin yadda yake yiwa Mufida "ke! Bar gurin nan nace miki" amma maimakon tabi umarnin sa kamar yadda Mufida take yi sai ta kyalkyale da dariya tare da kwaikwayon yadda yayi maganar "ke! Bar gurin nan nace miki" ta sake wata dariyar sannan tace "fillo". Yaji wani takaici ya kama shi kamar ya rufe ta da duka, amma maimakon haka sai ya mike tare da ɗaukan headphone dinsa da niyar bar mata gurin. Sai dai yana mikewa jirgin su ya shiga turbulence. Ya koma ya zauna da sauri tare da mayar da seatbelt dinsa, sai da suka fita daga turbulence din sannan ya lura cewa ya kuma rike hannun ta da hannayensa biyu. Ya sake cika ta yana gyara zamansa. Tace "you have aerophobia you cannot help it. There is nothing to be ashamed of" Ya bata rai a ransa yana tunanin wannan wacce irin yarinya Allah ya hada shi da ita yau. Yace "wai ke parents din ki basu warning dinki not to talk to strangers ba?" Ta gyada kai da sauri tace "Mommy did" yace "you just told me mamanki ta rasu" tace "yes, Mommy is my step mom. But she is more like a mother to me because she loves me so much" yace "ohh, shi yasa ba kya jin maganar ta kenan ko?" Ta yi shiru tana kallon sa da alamr bata gane me yake cewa ba. Yace "she told you kar kiyi magana da strangers, amma gashi kina yi min magana ni" ta girgiza kai "saboda you won't harm me" ya bata rai "ya akayi kika san hakan? You don't know me" ta daga kafada tace "I don't know how I know, i just know" yadda tayi maganar yasa yayi murmushi, sannan yace "you are too smart for your own good, zaki iya cigaba da zama anan, amma kar ki dame ni da surutu" ta yarda da hakan, amma kuma bata cika alkawarin ba dan for the hours da suka dauka suna tafiya sam bata barshi ya runtsa ba, labarai dai kam ya sha su, duk yan gidan su babu sunan wanda bai ji ba, Mommy, Daddy, yaya Mustapha, Hassan, Hussain, Safina har zuwa kan yan aikin gidan su. And he held unto her hands sanda jirgin su zai sauka. Sai bayan sunyi landing sannan yace mata "kim fada min sunan kowa a gidan ku amma baki fada min naki ba" tace "Safiyya. Sunana Safiyya Adam Muhammad. Amma yan gidan mu suna ce min Fiyya. I don't know why" "Piya?" Ya maimaita Tayi dariya "Fiyya. With an F and double y" "Piya" ya sake maimaita wa Tayi ajjiyar zuciya "fillo" ya bata rai, tayi dariya. "In kace Piya kana nufin something totally different from my name" ya bata rai yace "me Piya din yake nufi?" Tace "love ko beloved, in India" ya gyada kai yace "ohh" Tace "and ina da wata super power, I can tell you your name. You are Muhammad Auwal Muhammad" yayi sauri ya kalleta da mamaki, sai ta daga masa flight ticket dinsa da ya fadi kasa bai sani ba. Tace "har ka ji tsoro, da wata farar fuskar ka anan". To gain access to the book contact 👇 0704 203 0419 Ta manhajar telegram ****.    ****.     ****.    ****     ****.    **** ❤‍🩹*SAFIYYAH*❤‍🩹 *By* *Maman Maama* *Episode three (3): the two choices* *Her🧕🏻* Har dare yayi na kwanta bacci babu wanda ya kara shigowa gurina babu kuma wanda ya neme ni sai Mommy da ta shigo ta matsa min  naci abinci sannan nasha prenatal vitamins dina. Tun da na tashi da assuba kuwa nayi wankana na shirya na saka jilbab ɗin da nake fatan zai rage nuna wa mutane cikin da yake jikina. Dama kayana a hade suke ban fito da su daga jaka ba, duk abinda na fito da shi kuma nayi deciding cewa ba zan tafi dashi ba dan bani da karfi na jiki dana zuciya da zan iya yin wani abu akai. Na koma na kwanta a kan gado na nannade jikina da jilbab ɗin, na rufe idona da fatan bacci zai dauke ni ko na samu na ɗan rage ciwon da kaina yake yi min, amma sai dai a maimakon bacci, memories ne suka yi ta overlapping a cikin kaina, memories of yarintata, memories of relationships dina da family dina a da da kuma a yanzu, memories din Gidado and all the hopes we had for a future together, and the memories of daren da ya lalata komai a rayuwa ta, daren last birthday din Gidado. Na tashi zaune tare da dafe kaina da hannayena ina jin yana barazanar tarwatsewa. Sai kuma na daga kaina sama ina kallon hoton da yake facing ɗin gadona, hoton mahaifiyata a kwance akan gadon asibiti rike da yar jaririya a hannunta, fuskarta cike da tsantsar farin ciki. Nayi ajjiyar zuciya, ina ma dai rayuwa tana da control button, ina ma dai zan iya rewinding komai na koma yar jaririya na cigaba da jin dumin mahaifiyata, inama....... Sai nace a fili kamar mai magana da ta cikin hoton. "you set me up to be devoured by the blood thirsty vultures, yanzu gashi sun kassara rayuwata" nayi tsaki na juyawa hoton baya, sai kuma na sake juyawa nace "I miss you though". Knocking din da naji a bakin kofa ya saka na dawo da dubana kan kofar sannan na kalli agogo, 7:35. "Yes?" Nace ina gyara hijab dina tare da sake haɗe fuska. Sai dai kuma ana bude kofar yanayin fuska ta ya juya zuwa murmushi. At last, someone I can talk to, someone who truly loves me. Suka shigo a tare suma fuskokin su dauke da murmushi, na bude musu hannayena amma maimakon su fada jikina kamar kullum sai suka zauna a sides dina sannan suka rungume ni a tare. Nayi ajjiyar zuciya ina kara rungumar su jikina, ina jin yadda suka kara girma duk su biyun, a tsaho yanzu duk sun kere ni. "Yan biyun yaya Fiyya, I am glad you made it. Ina ta jin babu dadi na dauka ba zan ganku ba har mu tafi". Hassan ya dago kansa daga kafada ta yace "kinga gudun da muka yi a mota kuwa? Mommy tace mu hakura mu zauna tunda jiya ma evening paper mukayi amma muka dage sai da muka zo dan mu ganki kafin ki tafi" Hussain yace "Mommy tace zaki jima baki dawo kasar nan ba, haka ne? Amma zamu iya zuwa mu kai miki ziyara in mun gama waec ko?". Na gyada kai nace "duk sanda kuke son ganin mu kuyi min magana ko kuyi wa Daddy magana, za'a siya muku ticket ku tafi. And anything you need, ko menene, ku kira ni ku gaya min". Suka gyada kai a tare, Hassan yace "but this is not fair, Daddy is not being fair to you. Me yasa zai miki aure yanzu? Mommy tace aure zai yi miki da yaya Mustapha. Yaya Mustapha fa for God's sake. It shouldn't be. Kamata yayi a barki kiyi healing, ki kuma samu wanda kike so ku fahimci juna sannan sai kiyi aure"  na kalle shi ina murmushi nace "all that sounds so good. Amma kuma ba haka Daddy ya zaba ba, and I am sure Daddy ba zai zaba min abinda zai cutar da ni ba, da abinda ka fada ɗin shine zai fi min dai dai I am sure Daddy shi zai zaba min, you should be kinder to him". Hussain yace "but what about you. You are obviously not happy" nace "it doesn't matter. Maybe I will be nan gaba. Hussain, a yanzu haka happiness dina kadan ne a cikin irin abinda zan iya sacrificing dan in gyara relationship dina da Daddy, zan iya bayar da komai, ko da kuwa rayuwata ce to have Daddy hug me and say 'I love you Safiyya'" na karasa maganar ina share hawaye da bayan hannuna". Suka yi shiru gabaki daya sannan Hussain yace "he loves you, you know.  Yafi son ki akan kowa" na yi yar karamar dariya mai kama da kuka nace "my dear brother, am not sure about that. To him, I am just a big fat disappointment". Hassan yace "no you are not. He loves you. We all love you". Nayi kokarin chanja topic ta hanyar cewa "sooo, waye yayi driving a cikin ku, naji kunce kun sharara gudu" Hussain yana dariya yace "Hassan ne" Hassan yace "i passed my driving test last week, shine yanzu na gwada skill dina" nace "yayi kyau. Amma a daina gudu da yawa. An kawo muku motocin kenan?" Hassan yace "no... Ta wani friend din mu ne" na bata rai "why? Me yasa ba'a kawo muku ba? Kun sake yiwa Uncle Ahmad maganar?" Hussain yace "munyi masa fa, sai kawai ya rufe mu da fada wai me zamuyi da personal cars bayan akwai motoci a gida" Na fara girgiza kaina ina cewa "nasan akwai motoci a gidan ai, ni nayi niyyar zan siya muku motoci a matsayin gift na jamb da kuka ci. Zanyi masa magana. Allah yasa zai zo yau yayi wa Daddy sallama, zanyi masa magana". Hassan yace "uhm uhm, kar ki sa yayi miki faɗa kema. Yanzu kula da lafiyar ki yafi komai muhimmanci. Ki rabu da shi kawai". Na sake girgiza kai stubbornly "zan yi masa magana". A haka muka cigaba da hirar mu har sai da Esther ta shigo da tray din breakfast ɗina ta kuma sanarwa su Hussain da cewa nasu abincin yana kasa  sannan suka mike suka yi min sallama. Na tashi tsaye nima na rike hannayen su a cikin nawa nace "idan kunje gurin Daddy, be nice to him please, ku fada mishi maganganu masu daɗi and tell him you love him, hug him" suka tsaya kawai suna kallona amma kuma fuskokin su sun nuna cewa sun fahimci abinda nake cewa, a tare suka gyada kai, nayi musu murmushi sannan ta saki hannayen suka fita jiki a sanyaye. Suna fita Mommy ta shigo ta kuma saka ni a gaba sai da na ci abinci, ina ci tana yi min hira. "Gwara ki ci abinci ki koshi dan ba lallai bane ki iya cin abincin jirgi. Kuma gwara ki ci abinci a daki dan ban san waye zai shigo gidan nan yau ba, ko ma'aikatan gidan ma ban yarda su san halin da kike ciki ba, dan hausawa sunce munafukin ka tabarmar ka". Muna nan zaune Safina ta shigo ta zauna tana kallona ina shan tea din da Mommy ta hada min, tace "I will miss you little sister. Though na san ba dadewa zakiyi sosai ba. Kina dawowa kuma sai mu sha biki" ta karasa tana murmushi. Ban ce komai ba har sai da Safina ta mike zata fita sannan na daga kai nace mata "I will miss you too. Allah ya bada sa'ar karatu" tace "Ameen. Nagode" sannan ta fita. Ban fita ba har sai da aka gama saka duk kayan mu a cikin mota, sannan Mommy tazo da kanta tace inje in shiga mota, shima sai data tabbatar jilbab din jikina ya boye cikin sannan ta kama hannuna muka fita tare. Sai dai muna fita compound din gidan motar Uncle Ahmad tana shigowa, driver yana tukawa, Mukhtar a gaba, Uncle Ahmad a baya. Mommy ta tura ni gaba "sauri ki je ki shiga mota gani nan zuwa" amma sai na makale, ina so nayi magana da Uncle Ahmad akan maganar motocin twins. Mommy ta sake turani amma maimakon nayi hanyar motar da zamu tafi airport a cikin ta sai nayi hanyar inda su Uncle Ahmad sukayi packing. Kafin na karasa suka fito, kallo daya Uncle Ahmad yayi min ya dauke kai, yayin da Mukhtar kuma ya taho direct gurinna yana washe baki. Sai a lokacin nayi nadamar kin jin maganar Mommy. Ya tare min hanya yayin da ni kuma nake kokarin wuce shi na tafi gurin Uncle Ahmad. Yace "Fiyya ko gaisuwa babu? Ko nayi wani laifin ne wai? Ni ina ta jin dadin zan samu na ganki ke kuma ko kallo ban ishe ki ba ko?" Na tsaya tare da juyowa ina kallon sa. "Yaya Mukhtar, barka da zuwa, ya hanya. Nice to see you. Bye". Na juya zan tafi ya sake tarar gabana. "Dan Allah Safiyya ki tsaya. You don't have to be cold. Ki bani dama muyi magana ta fahimtar juna please. Minti biyu ya ishe ni" nayi ajjiyar zuciya ina lura da Mommy da ta bata rai a gefe tana kallon mu. Nace "ina jinka" ya gyara tsayuwa sa, na lura da yadda yake kokarin kar ya kalli cikina, yace "ina jin yau kusan shekaru biyu kenan da na fara gaya miki abinda yake zuciya ta. So kin riga kin sani. Ina so ne in gaya miki cewa babu abinda ya chanja a zuciyata a game dake duk da rejecting dina da kikayi the first time. Babu abinda ya chanja a zuciyata duk da wannan abin da kika yi" ya fada yana waving hannunsa around cikinta ba tare da ya kalli cikin ba, naji zuciyata ta tattare ta dawo wuyana, na nade hannuna a kirjina nace "what do you want, Mukhtar?" Ya dago kai yana kallon cikin idona, nima ban dauke nawa ba, yace "you know exactly what I want" nace "no, I don't. Just skip the whole preamble ka gaya min direct. Menene kake bukata daga gare ni". Ya sauke idonsa kasa yana hadiye yawu yace "idan kin amince ..... A matsayi na na dan'uwanki na jini, ina so in kin haihu, zan taimaka miki in aure ki, har abada babu wanda zai san me ya faru. Har abada babu wanda zai san me kika yi" na kankance idona a kansa nace "Mukhtar, a tsakanin ni da kai tabbas akwai wanda yake bukatar taimako, kuma daga ni har kai mun san waye". Na juya da sauri na bar inda yake, raina a matukar bace, blindly nake tafiya ina magana da kaina kasa kasa, ban ankara ba sai gani na nayi a gaban Uncle Ahmad, na dan ja baya sannan na gaishe shi a diririce "uhmm. Uncle. Ina kwana" yana danna wayarsa ya amsa. "Lafiya" har na wuce shi sai kuma na tuna da alkawarin da nayi wa twins dan haka na dawo da baya. "Uncle.....dama ina so zanyi maka magana ne ... Dazu munyi magana da twins akan cars din da nace a siya musu. Shine nace bara in tuna maka maybe ka manta ne". Wani mugun kallo daya watso min ne ya saka a lokaci daya naji ina ma dai jiya da na kwanta bacci yau ban tashi da rai ba. Na ja da baya taku biyu cikin sauri dan a tunani na rufe ni zaiyi da duka amma instead sai yace cikin daga murya "Safiyya? Yanzu rashin kunyar taki har ta kai haka dama? Zamani har ya kai haka lalacewa? Ke sam baki ma damu da wannan abun kunyar da yake jikin ki kike yawo da shi ba har kina da karfin halin tsayawa a gaba na da abun kunya a jikin ki kina bani umarni?" Na juya da sauri na yi gurin motar mu ina jin kafafuwa na suna harhadewa a cikin juna, ina kuma jin idanuwan duk mutanen da suke gurin a kaina. Kafin in kai mota hawaye sun jika fuskata, ta gefen idona na ga twins sun taho gurina amma sai nayi sauri na bude kofar gidan gaba na shiga sannan na rufe da karfi, still ina cigaba da jin muryar Uncle Ahmad yana cigaba da fadar bakaken maganganu a kaina. "Kaf dangin mu ba'a taɓa yin irin wannan abun kunyar ba. Saboda daurin gindi amma wai har tazo ta tsaya a gaba na tana gaya min maganar banza" na saka hannayena duk biyun na toshe kunnuwa na tare da kifa kaina akan dashboard ina cigaba da rusa kuka kamar wadda aka aikowa sakon Daddy ya bar duniya. A cikin kuka na naji shigowar Mommy cikin motar ta zauna a baya tayi min magana amma banji me tace ba, sai dai na dago kaina na fara kokarin goge hawayena. Yaya Mustapha yazo ya bude daya kofar bayan ya taimaka wa Daddy ya zauna sannan ya rufe ya dawo seat din driver ya zauna. Na cigaba da ƙoƙarin tsayar da kuka na dan sam bana son Daddy ya san abinda ya faru ballantana ransa ya baci. Sai dai yaya Mustapha yana tayar da motar naji Mommy tace "ki daina wannan kukan haka tun kafin ki saka wa kanki wata cutar kuma, ki gaya wa Daddyn ku abinda ya faru" nayi shiru ban ce komai ba, sai naji muryar Daddy yace "menene ya faru?" Na sake yin shiru amma kuma sai hawaye na ya dawo sabo. Ya sake magana cikin tsawa "magana nake miki Safiyya, menene ya faru?" Cikin kuka nace "Uncle Ahmad ne yayi min hayaniya a cikin mutane" yayi shiru kamar bai ji ne nace ba, sai kuma yace a hankali "me yace?" Nayi shiru a raina ina jin nauyin maganar. Mommy tace "zagin ta yayi, ya goranta mata akan abinda ya same ta, a gaban duk yaran gidan nan" Daddy ya sake yin shiru, amma duk da ban kalle shi ba nasan ransa yayi matukar baci, ni kuma abinda nake gudu kenan. Har yaya Mustapha ya ja mota sai Daddy yace "tsayar da motar nan Mustapha, zo ka kama ni in fita". Nayi sauri na juyo ina kallon sa hankali na a tashe. "Daddy please" Mommy ma ta rike hannun sa da sauri. "Dan Allah kar ka fita, dan Allah kar ka kula shi. Abinda yake so kenan dama. Mu lafiyar ka tafi mana komai. He isn't worth it. Ko babu komai yanzu mun san inda ya sa gaba". Daddy ya karbe hannun sa da ta rike ya kama handle din kofar yana kokarin budewa. Na juya na kalli yaya Mustapha cikin tashin hankali nace "rufe lock ɗin. Ja motar mu tafi" yayi abinda nace muka bar harabar gidan a guje. Har muka yi nisa babu wanda ya kuma yin magana. Sai daga baya naji Daddy yace "Mustapha kira min Ahmad a wayar ka ka bani shi" na dafe kaina. Ba zai hakura ba dai. Wata irin zuciya ce da Daddy da sam baya barin magana ta wuce sai ya rama. Ina kallo yaya Mustapha ya daukl wayar sa yayi dialing sannan ya saka a kunnen sa, aka dauka sai yace "Uncle Ahmad, Daddy ne yake son magana da kai" sai kuma ya mika wa Mommy wayar ita kuma ta bawa Daddy, ya karba direct yace "kar ka biyo ni airport, bana son rakiyar taka. Allah yayi min komai, bana bukatar komai daga gare ka". Daga haka ya ajiye wayar. Mommy tace "kash. Ni dai ban so ka kula shi ba wallahi" amma a raina sai nayi mamakin abinda yasa naji kamar farin ciki a cikin muryar ta. Bamu jima a airport ba aka kira jirgin mu, na rungume twins da suka biyo mu har airport a baya muka yi sallama, na tabbatar sunyi sallama mai kyau da Daddy sannan nabi bayan yaya Mustapha da yake tura Daddy a wheelchair zuwa cikin jirgi. Sai dana tabbatar Daddy ya zauna comfortably sannan na nemi seat dina na zauna nima tare da sauke ajjiyar zuciya. Bamu dade da zama ba jirgin ya tashi, daga can nesa dani na hango wata ta kankame hannun kujerarta. Nayi murmushi tare lunshe idona ina kallon seat din kusa dani wanda babu kowa a kan sa. Sai kuma na tuno da fuskar sa jiya. How hurt and broken he looked. Na kuma mayar da idona na rufe a fili nace "I am sorry Muhammad. Ina yi maka son da ba zan iya staining white din ka da datti na ba. Allah ya baka ikon cin wannan jarabawar. Allah ya baka wadda ta fini". Sai kuma naji ina jin kishin wadda Muhammad zai samu bayan yayi healing daga abinda nayi masa. Ina kishin rayuwar da zasu yi. Rayuwar da Gidado ya shirya mana zamu yi ni da shi, yanzu dole da wata zaiyi. Dole da wani zanyi. Zuciya ta naji tana tafasa, gashi na kasa cire tunanin daga cikin ta. Na dauko headphone a handbag dina na saka a kunne na na kunna karatun Alkur'ani tare da rufe idona a hankali ina motsa bakina ina bin kira'ar, da fatan zai sanyaya min zuciya ta. Ban san tsahon lokacin da na dauka a haka ba naji an taba ni. Na bude ido naga Mommy a tsaye a gaba na, tayi min murmushi sannan ta taba wuya na tana testing temperature dina. Sai kuma ta zauna a kujerar kusa dani tace "nace Mustapha yazo ku zauna tare ya debe miki kewa yace in ya zauna ma faɗa zakuyi" nayi shiru bance mata komai ba ido na a kasa. Ta cigaba "me yasa kuke rigima ne kullum wai Safiyya? Akwai abinda yake yi miki wanda ba kya so? In akwai ki gaya min ni zanyi miki maganin sa kinji?" Na gyada kai na kawai bance komai ba. Sai tace "ki je gurin Daddy, yace yana son magana da ke". Na mike da sauri tare da cire headphone ɗin kunne na na ajiye, ta rike hannu na "ki bi a hankali kar ki fadi" na sake gyada kai sannan na wuce na tafi inda Daddy yake. Ina zuwa ya dago kai daga karatun magazine din da take hannunsa, ya kalle ni, kallon da ya fi min ciwo akan komai sannan ya mayar da idonsa kan takardun hannunsa yace "seat" na zauna a kujerar da Mommy ta tashi daga kai ina wasa da yatsun hannuna ban ce komai ba. Ya ajiye magazine din yace "kin dai san maganar da nayi miki akan aure ko?" Na gyada kai, yace "baki da baki?" Na amsa da sauri. "na sani Daddy" yace "good. Da nayi niyyar sai dai kawai kiji an daura miki aure, banyi niyyar sanar da ke komai a kai ba. Amma ban san me ya hani ni yin hakan ba. Ban san me yasa nake tausayin ki ba, duk da kuwa cewa ke ba kya tausayi na, ko kadan" bance komai ba, dan ji nake yi duk duniya tayi min kunci. Jin banyi magana ba sai ya cigaba. "Ina tunanin mahaifiyar ki ce. Memory dinta ne yake hunting dina yake hanani aiwatar da duk wani hukunci da nayi niyyar yankewa a kanki. Komai nayi niyyar yi sai inyi tunanin in tana raye zata yarda? Kullum sai nayi tunanin in tana raye wanne hukunci zata dauka akan ki" ya yi ajjiyar zuciya yace "but I guess I will find out soon enough" na dago kai da sauri na kalle shi amma sai yayi sauri ya juya kansa gefe, ya cigaba "babban burina kafin in tafi din shine in ga rayuwar ki ta daidaita, yadda at least ubangiji zai rangwanta min akan  laifin negligence a kula da amanar da ya bani, yadda at least zan samu abinda zan gaya wa mahaifiyar ki idan na haɗu da ita a can". Na goge hawayen kan kuncina a hankali na fadi kalmomin da suka zamar min kamar karatun sallah a cikin watannin nan "Daddy I am sorry". Ya cigaba "wannan dalilin ne yasa nake son yi miki aure as soon as possible. Bana so in tafi ba tare da na yi miki aure ba Safiyya. Bana so in tafi ba tare da rayuwar ki ta daidaita ba. Wannan shine abinda nake tsoro fiye da mutuwar ita kanta" yayi ajjiyar zuciya ya cigaba "nayi magana da likitan da zai cigaba da dubaki a Germany, ya gaya min cewa zasu iya cire cikin idan yayi wata bakwai ba tare da illa ga ke ko babyn ba. Wannan shine abinda za'a yi. Ina so a rabaki da cikin nan ina raye. Sai dai kuma ban san yadda zanyi da babyn ba idan an cire shi. So for the last time ina sake tambayar ki Safiyya, waye uban cikin nan?". Na girgiza kai na da sauri amma na san yin shiru na zai kara bata masa rai, kamar yadda nasan abinda zan fada ɗin shima bata masa ran zaiyi. "Daddy wallahi ban sani ba" na fada cikin rawar murya. Yayi ajjiyar zuciya. "I thought as much. Kamar yadda na fada, ni ina tausayin ki amma ke ba kya tausayi na. Okay let's assume gaskiya kike faɗa. Ba ki san waye ba. Amma ai na tabbatar da cewa kin san waye saurayin nan naki ko? Ko shima ba ki san shi ba" na girgiza kaina sai kuma nace "na san shi Daddy " yace "okay, let's go over the whole story kamar yadda kika bamu. Kince a ranar da abin ya faru you were with him throughout the evening, har dare kuna tare. Haka ne?" Nace "haka ne" ya cigaba "da dare you look him to an eatery. Kuka ci abinci tare daga nan sai aka kira ki, someone claiming to be Mustapha, and that's when it happened. Ko?" A hankali nace "haka ne" yace "okay let me break it down for you maybe ko zaki iya bude idonki beyond soyayyar da kike yi masa ki ga gaskiya. You told him cewa a ranar zan zo gari. Haka ne?" Nayi tunani, tabbas na gaya masa, we were so excited saboda na gaya masa a matsayin another birthday gift da zan bashi, zan kai shi gurin Daddy idan yazo. Nace "haka ne" yace "kuma shi kadai kika gaya wa ko kin gaya wa wani?" Nayi tunani, ni bani da wasu friends da nake wata personal magana da su, na girgiza kai na "ba wanda na gaya wa" Daddy yace "good. And ya san bani da lafiya?" Nan ma na amsa in the affirmative. Ya kuma tambaya "kuma ya san kina da dan'uwa Mustapha, ya san tare zamu taho da shi?" Nayi shiru a raina bana jin dadin direction din da wadannan tambayoyin suke tafiya. Ya katse min tunani na "yes or no" nace "yes, ya sani" yayi murmushi "tambaya ta karshe. Sanda aka kira ki aka yi pretending to be Mustapha, yana zaune a gurin ko ya tashi?" Nayi shiru ban ce komai ba, zuciyata tana bugawa kamar zata bar kirjina. "Answer me!" Ya fada da muryar fada. Na tuno abinda ya faru a lokacin, muna zaune aka kira Gidado a waya, ya dauka baya jin abinda ake cewa sai ya tashi looking for network, and then my phone rang. Na lumshe ido na a hankali nace "baya gurin, ya tafi yin waya" Daddy ya sake yin murmushi yace "and you still think ba shi To gain access to the book contact 👇 0704 203 0419 Ta manhajar telegram **** ********* * * * * * *************** ❤‍🩹*SAFIYYAH*❤‍🩹 *By* *Maman Maama* *Episode Four (4): The Choices 2* ****. ****. ****. ****. ****. **** Awa 8 da rabi mukayi muna tafiya kafin mu isa garin Berlin, Germany. Daddy ya zaɓi Berlin ne saboda anan ne babban abokinsa Uncle Sufyan yake zaune da iyalinsa. Akwai kuma likitan da ya kware akan ciwon Daddy wanda zai kula dashi a tsahon lokacin da zamu zauna a can. It was almost 8 o'clock pm when we landed a birnin na kasar Germany. Already muka tarar da Uncle Sufyan da dansa Abdul suna jiran saukar mu a airport. Muna haduwa da su Uncle Sufyan ya tarbe ni da murmushi "Safiyya, as beautiful as ever" na sunkuyar da kaina ina murmushi sannan na gaishe shi, duk sanda muka hadu dashi haka yake yi min, ya amsa tare da miƙa wa Daddy hannu at the same time yana cewa "duk sanda na ga Safiyya sai na tuna da Safiya, a rear gem. Har yanzu banga mace irin ta ba. Allah ya kai rahama kabarin ta". Mommy tace "Ameen ya Rabbi. Safiyya is a photocopy of her ai" Daddy ya dago yana kallo na yace "anya kuwa, sunyi kama dai a fuska, amma hali kam basu da dangantaka" na kalle shi muka haɗa ido nayi sauri na mayar da ido na ƙasa. Abu biyu na karanta a idon Daddy a lokacin, akwai grief, wanda duk sanda akayi maganar ta sai na ga yanayin sa ya chanja, wannan yana daga cikin abinda yake kara min fahimtar irin soyayyar da yayi mata, yadda har yanzu, more than 20 years da rasuwar ta, amma bai daina jin mutuwar ta ta ba. Abu na biyu kuma wanda yafi daga min hankali shine disappointment. Daddy was really disappointed in me. Gani yake kamar duk duniya bashi da wani disappointment da ya wuce ni. Naji duk gwuiwowina sun sage, kamar kullum naji babu abinda nake so irin barin duniyar. A lokacin babban concern dina shine Allah ya sa hijab dina ya boye cikina tunda bani da tabbas din hosts din mu sun san da maganar cikin or not. Daga nan muka wuce zuwa inda suka ajjiye motar su, sai da muka je na fahimci cewa motoci biyu suka zo dasu. Daddy ya juyo yana kallona yace "ki shiga motar abdul ya kai ki gidan su ki huta, mu zamu wuce asibiti" na tsaya ina kallon sa idona yana cikowa da hawaye dan naso ace na bishi asibiti anyi komai a gabana, amma kasancewar yanzu bana iya yi masa musu sai nace "okay Daddy". Na tuna da Safiyyan da, da ace seven months back ne, da zan iya rusa kukan da zai tara masa mutane a airport din idan yace ba zan bishi ba. Da ba karamin aikina bane in zauna dirshan a kasa in rike kafafuwansa ina kuka da dukkan karfina, amma yanzu sai nayi taku biyu baya na tsaya ina kallon sa ina kokarin rine kuka na. Ina kallo aka saka Daddy a bayan mota daya, Mommy ta shiga kusa da shi, yaya Mustapha ya shiga gaba sannan Uncle Sufyan ya zauna a drivers seat, aka barni a gefe ina rarraba ido. Mommy ta sauke glass ta ce min "ki kwanta ki huta in kunje, ki sha maganin ki kuma, zan zo gidan in anjima" na gyada mata kai, Daddy kam ko kallo na bai yi ba suka tafi. Sai da motar su ta bar gurin sannan Abdul ya ce min "okay. Daddy's girl. Nasan yanzu zaki kama kuka. Let me take you home tun kafin ki rikice min". Na goge hawayen da ya fito tare da ƙirƙirar murmushi nace "I am not crying" yace "of cause you are not. Maybe someone is cutting onions around". Ya bude min kofar motarsa na shiga sannan ya rufe ya zagaya ya shiga side din driver muka dauki hanya. A hanya yana ta kokarin nuna min gurare amma ni bani da wani interest akan buildings and monuments dinsu, rayuwa ta kawai nake lissafa wa. Har sai da muka yi packing a gaban gidan su sannan ya juyo yana kallona yace "Safiyya, I want to use this opportunity da muke alone muyi magana. Magana nake so muyi as civilized people. Daddy na yace wai sun fara magana da Daddyn ki cewa akwai yiwuwar zasu yi mana aure" yayi shiru yana so yaga reaction daga gare ni sai yaga babu komai, ya cigaba, "so you knows about it kenan. Look, I want you to understand cewa I have nothing against you as a person, I like you. You are very beautiful and intelligent and I am very sure that akwai maza da yawa da suke layi suna son ki zabe su as your life partner. You can have any man you want. Wannan yasa na kasa gane dalilin su Daddy na bullo da wannan maganar. Gaskiya ni dai I don't want arrange marriage. Na fi son inyi aure for love. And I am sure ke ma haka. I know yadda daddyn ki yake son ki ba zai taba yi miki dole ba, and that's why I am begging you. Please idan an tambaye ki kice ba kya sona kamar yadda nima zanyi kokarin nunawa nawa daddyn haka. Let's join hands and fight this battle together. In kika yi min haka I will forever be grateful to you. I am sure kema kina da wanda kike so and I don't want to be the reason da zai saka a raba ku". Na gado kaina ina kallon sa, part of me yana jin dadin cewa bai san maganar cikin jikina ba, part of me kuma was sad that he maybe the one da zan aura and he just told me cewa baya so na. Na ce "I understand. Kana da wacce kake so" yayi murmushi, a lokaci daya na kara fahimta dan na san irin wannan murmushin. Na hadiye wani yawu mai daci ina hango irin murmushin a fuskar Muhammad, wata irin kewar sa tana kara lullube ni, yace "Yes, ina da wadda nake so. Ban ce ta fiki da komai ba but I love her and want to spend the rest of my life with her". Nayi masa murmushi. "I understand. Kuma ina so ka sani cewa nima akwai wanda nake so, so mai tsanani. So in auren mu ya kasance sai dai in kaddarar mu ce haka. But I am not promising cewa Daddy will listen to me because things are totally beyond my control" Na bude kofa zan fita sai na kara da cewa "and I am sorry you are dragged in to this". A gidan su na wuni ranar, mamansa mai kirki wadda dama kullum muka hadu bata da zancen sai na mamana and how close they were kafin rasuwarta. Wannan ya sa I always look forward to meeting her dan insha labaran da suka fi komai daɗi a kunnuwana amma a ranar sai na kasa zama muyi magana nace mata na gaji kwanciya nake so inyi. Ta bude min dakin da na fahimci an riga an gyara shi saboda zuwan mu, ta kuma kai min duk abinda ta tabbatar zan bukata ni kuma na karba nayi mata godiya, sai dai bata amsa ba sai ta bini da kallo kawai, and then I saw a look on her face, a look of disappointment and anger, sai dai bata ce min komai ba ta juya ta fita. But I knew it, a matsayin ta na uwa ta gane ciki ne da ni and she is disappointed in me, and angry at me, because she cared. Na zauna a bakin gado ina jin feeling ɗin da zuwa yanzu na saba da jin irinsa amma kullum intensity ɗin sa karuwa yake yi a zuciyata. Feeling na son mutuwa. Feeling na tsanar rayuwa. Na rufe ido na nayi addu'a a hankali "Allah ka ɗauki rai na a daren yau". Sallolina na tashi nayi sannan na janyo fillow na kwanta na rufe idona tare da fatan bacci zai dauke ni ko na manta da halin da nake ciki, ko da na yan mintuna ne, amma sai dai maimakon bacci sai tunaninnikan halin da rayuwata take ciki ne suka yi ta overlapping kansu a cikin kaina. Har ban san wanda zan dauka daga ciki in duba ba, batun rabuwata da Muhammad ne ko na halin rashin lafiyar da Daddy yake ciki ko kuma na auren da za'a yi min da wanda bana so ko kuma karatuna da nayi asarar shekara uku inayi wannan alakakan cikin da yake jiki na ko kuma tunanin hanyar binciken waye uban cikin ko kuma na vultures din da suka dira akan akaina suke tsatstsagar naman jikina da rai na? Na tashi daga kwanciyar na zauna ina lissafin rabon da inji dan cikina ya motsa tun a Nigeria. Naji wani irin relief a zuciyata "Allah yasa ya mutu" na fada a hankali tare da dora hannuna a saman cikin na dan danna da dan karfi, da karfin shima ya harbo kafa ya doke hannuna, naji wani kulukun bakin ciki ya tsaya min a makogwaro. Sannan na kara number a cikin list na abubuwan da ya kamata inyi tunani akai, "menene makomar abin da yake cikina?" Daddy yace za'a cire shi nan da wata daya da yan kwanaki, amma shi kansa yace bai san yadda zaiyi dashi ba in an ciro shi. Ni kam ko kallon fuskarsa bana bukatar yi and I will definitely not keep it with me. Dan watarana zan iya shake shi cikin dare... Nayi sauri na kawar da tunanin daga raina sannan na koma kan next in line, waye zan zaba a cikin choices din da Daddy ya bani? Definitely not Mustapha. I rather die than in auri Mustapha. And then Abdul dazu ya gaya min da bakin sa cewa baya sona, and bai san da maganar cikin nan ba and I don't know yadda zai dauki maganar idan ya fahimci cewa cikin shege nayi shi yasa a keso a makala masa ni, definitely he will hate me forever. Sai kuma Mukhtar. Mukhtar has been obsessed with the idea of marrying me a cikin shekarun nan. But he doesn't love me. Ni na san abinda yake yiwa, it is the same thing as abinda yasa Mommy take ta nacin a haɗa ni aure da Mustapha, Daddy ma kuma na tabbatar ya sani sai dai kokarinsa na binne abin kunyar da yake ganin nayi ne yasa yake kokarin chosing din su dan yasan zamu juya su suyi abinda muke so dan su samu abinda suke so. Then wanne ne zan zaba daga cikin su kenan? Naji maraici ya sake lullube ni. Babu abinda nake bukata a lokacin illa in samu someone older that I can talk to, wanda zai bani shawara ba tare da wani selfish interest a cikin shawarar ba. Naji ina kewar mahaifiyata kuma ina takaicin rashin sanin kowa a cikin danginta. Na dauko handbag dina na bude na dauko yar karamar purse dina na bude ta itama na dauko wani tsohon hoton katin da nake yawo dashi kullum a cikin jaka. Hoton wata mata ne a zaune akan kujerar gidan daukan hoto irin na kauye, da yara yan mata su uku a jere a bayan ta. Babbar zatayi sheakara goma, mai binta takwas, yar karamar kuma ba zata fi shekaru biyar ba. Duk su ukun da ita suke kama, nima kuma da ita nake kama. Na shafa hoton da hannuna ina lura da yadda duk su hudun suke murmushin da yake nuna yadda suke kaunar junan su, yadda suke cikin farin ciki duk kuwa da talaucin su wanda ake iya gane wa a cikin hoton ta yanayin kayan jikin su. They all had a rough life, a rough ending, but they are all fine now, they are all together now. In Janna insha Allah. Babu kuma abinda nake so a lokacin illa nima in bisu, illa in tafi gurin su. Na dora hoton akan kirjina na rufe ido na sannan nayi kokarin mantawa da komai sai tunanin yadda rayuwar mu zata kasance a Janna tare. A haka bacci ya dauke ni Cikin baccin naji an taba hoton dake kan kirjina. Na zabura da sauri kamar wadda za'a cirewa rai na damke hannun wadda ta dauki hoton. Ido na na shiga cikin na Mommy. Na saki hannun sannan na sauke ajjiyar zuciya na koma na kwanta na mayar da ido na na rufe. Ta juya hoton a hannunta tana kallon mutanen ciki, sai kuma ta zauna akan gadon tana kallona tace "baba Hadiza,  Saudat and the poor little Khadijah. Babu abinda Safiya take magana akai sama da su. They were her inspiration....." "And she is mine" na fada a hankali ido na still a rufe. Tayi ajjiyar zuciya sannan ta mayar min da hoton inda ta dauke shi tace "she is ours. Gabakidayan mu musamman babanku ita ce inspiration din mu. Duk hukuncin da zai yanke a rayuwa sai ya saka interest ɗin ta a ciki. What will she think? What will she say? What will she do? Kullum sune kalmomin sa. Bana kishin ta Safiyya, ban taba jin raina ya baci dan yayi considering dinta ita da bata raye before yayi considering di na ni da nake raye nake kuma matarsa ba, ban taba jin kishi ba, besides ina jin guilt ne na cewa she should be alive, ita ya kamata ta rayu ba ni ba, she should be here enjoying the empire she built with her blood and sweat. But ba haka Allah yaso ba Safiyya, and we can't question hukuncin ubangiji. I will understand if you don't like me Safiyya, maybe irin tunanin da nake yi kema kina irin sa cewa ina living the life that should be safiya's, but I cant wrap my head around the pact that you don't like Mustapha. Me yayi miki shi?" Na bude ido na amma ban kalle ta ba kuma ban ce komai ba. Ta sauko daga kan kujerar ta zauna a kusa dani ta cigaba "Daddy ya gaya min kince ba kya son Mustapha. I won't say nayi mamaki dan tuni na fahimci yadda kike yi masa but I thought kawai kin kasa accepting dinsa ne as a brother ban dauka kin tsane shi bane ba, ban dauka zaki iya putting future din ki da kuma martabar ki in jeopardy kawai saboda mere sentiment". Ta karasa maganar cikin daga murya. Na mayar da ido na na rufe na kuma mayar da hannuna na dora akan hoton kan kirjina. Ina jin ta tana kokarin daidaita muryarta sannan tace "am sorry Safiyya. Am sorry na daga miki murya. Amma ban taba tunanin haka daga gare ki ba. I love you with all my heart Safiyya. Haihuwar ki ne kawai ban yi ba. Idan ke baki sani ba shi mahaifinki ya sani. Soyayyar ki ce ta kawo ni gidan ku. I never expected cewa ke zaki ƙi jini na Safiyya. I never expect kuma daddy zai rufe idonsa ya goya miki. Not after all that has happened" ta sake yin shiru, nima kuma ban bude ido na ba ban kuma yi magana ba. Naji ta kama hannuna ta rike a cikin nata, ina jin yadda natan ya dauki zafi, ta kuma cewa "Safiyya, yanzu duk duniya wa kike tunanin kina da shi da zai rufa miki asiri bayan mu? Wanne family kike da su bayan mu? Ahmad? Kina ganin dai abinda yayi miki a cikin gidan babanki ballantana in kin je gidan shi. Ko kuma Abdul ɗin gidan nan da mahaifiyar sa tun kafin in karaso gidan nan ta kira ni tana tambayar ko abinda ta gani a tare da ke gaskiya ne. Ta yaya kike tunanin zata karbe ki a matsayin sirika? Safiyya idan ma ba zaki yi tunanin yadda zanji a raina in kika yi rejecting jini na ba think of your future and the future if your unborn baby. Think ki gani ina ne kike ganin yafi dacewa da ke". Sai ta saki hannuna ta mike ta shiga toilet. Na bude ido na ina kallon kofar toilet ɗin ina jin zuciya ta babu daɗi, tabbas Mommy tana nuna min soyayya da kulawa dai dai yadda ya kamata, bata taba cutar dani a bayyane ba, not that I know of, bata taba yi min mugunta ba tun ina yarinya har na girma, tun bata san gaskiyar wacece ni ba har ta sani. Sanin nata ya chanja abubuwa da yawa, the changes may be reality or just a pigment of my imagination dan bani da tabbas a kansu. Abinda nake da tabbas akai shine she doesn't deserve a cold treatment from me, Safina ma haka. Mustapha is a different case duk abinda nayi masa bani da nadama amma su dai, especially Mommy ya kamata inyi kokarin kyautata mata ko dan kaunar da take nuna min. Amma kyautatawar ba zata yi involving auren Mustapha ba, in na auri Mustapha da shi zan zauna ba da ita ba and I won't subject myself to lifetime of emotional torture saboda in kyautata mata. Ina kallon ta ta fito ta tayar da sallah nima na tashi na shiga toilet na sake alwala na fito nima na cigaba da sallolina. Sai bayan sallah asuba sannan na hau gado na kwanta bacci mai nauyi ya dauke ni. Cikin baccin naji maganganun Mommy da na Aunty Hajjo suna maganganu, nayi shiru ina son jin me suke cewa sai naji Mommy tace "to har yanzu dai bata fadi waye ba. Ko ta sani ko bata sani ba Allahu a'alam". Aunty Hajjo tace "ikon Allah. Kuma ku bakuyi komai akai ba? Kuka zauna kuka zuba mata ido?" Mommy tace "munyi iyakacin kokarin mu fa, babu abinda bamuyi ba. Munyi running duk options din mu amma ta rufe kowacce hanya da za mubi mu samo wancan yaron da muke zargi" Aunty Hajjo tace "makarantar su fa? Kun bincika ba'a can yaje ba?". Nayi juyi kamar a lokacin na tashi. Mommy tayi gyaran murya sannan tace "ki tashi Safiyya ki ci abinci ki sha magani. Zan koma asibiti gurin Daddy". Na tashi da dan sauri na sannan nace "Mommy zan biki dan Allah. Zanje in ganshi" ta tabe baki kawai bata ce komai ba, da alama har lokacin fushi take yi dani. Na sauko daga gadon na gaishe da Aunty Hajjo, ta amsa da ɗan sakin fuska kadan ba kamar jiya ba amma kuma babu annurin da nakan gani a tare da ita da. Da sauri na shiga toilet nayi wanka na fito jikina lullube da hijab, na debi kayana na koma toilet din babu wanda yayi min magana a cikin su, sai dana shirya na saka wani hijab ɗin sannan na sake fitowa na tarar sai Mommy ita kadai a zaune. Ina zama ta bare magunguna ta miko min tana cewa "na lura in dai bani na baki maganin nan ba ba kya sha Safiyya, ke baki damu da kanki ba ballantana ki damu da wanda ya damu da ke". Na fahimci magana take gaya min amma ban ce komai ba sai kawai na karbi magungunan a hannunta na watsa su gabaki daya a baki na hadiye. Ta tsaya tana min kallon mamaki, ta san da in zan sha magani wani lokacin sai ta kira Safina sun hadu sun danne ni sannan zasu dura min, in sun gama durawa kuma in ba sa'a suka yi ba in yi musu amai a jiki. But now I do not care about anything anymore. Except for Daddy. Ta ce "kinga yanzu ba zama zan ringa yi a gida tare da ke sosai ba. Ki ringa shan magani ko dan ki samu lafiya da karfin jikin da zaki rabu da abinda yake cikin ki lafiya". Na daga kafada "but I don't need it. Daddy yace I won't labour. Za'a yi aiki a cire". Ta saki baki tana kallona, na lura da bacin rai a fuskarta farko ban fahimci dalilin bacin ranta ba sai daga baya sannan na fahimta, Daddy bai gaya mata decision dinsa ba. Ta ajiye robar ruwan hannunta tace "yaushe ne kuka yi wannan shawarar ke da shi?" Na sunkuyar da kaina "ba shawarar mukayi ba Mommy. I thought you knew. Nima gaya min kawai yayi. I am sorry. Zan ringa shan maganin". Ta mike tsaye "ki dauki abinci ki ci ki fito mu tafi. In kuma shima abincin kunyi shawarar ba sai kin ringa ci ba shima sai ki gaya min in daina bata lokaci na akan kokarin baki. Na bar Safina ita kadai a gida, na bar twins a lokacin da suka bukata ta, and I am here a gurin da ba'a bukata ta". Ta juya ta fita da sauri Nima da saurin na hada tea na sha sannan na bita a baya. Ina fitowa sitting room dinsu naga Abdul ya shigo da sauri, yana gani na yayi murmushi "daddy's girl, ke muke jira" ban bashi amsa ba na bishi a baya muka fita. A asibiti muna zuwa muka shiga ciki, Mommy tana gaba ina binta a baya tunda ita tasan gurin. Muka je reception sai naji tana tambayar receptionist din da muka samu a gurin ko an shiga da Daddy gurin aikin da za'a yi masa. Na bude ido ina jin zuciya ta tana bugawa da karfi. Naji matar tace a'a ba'a fara ba an dai yi sedating ɗin sa. Ta nuna mana hanyar da zamu je dakin da aka kaishi. Mommy ta juya zata tafi na tari gabanta da sauri nace "Mommy aiki? Wanne aiki za'a yi masa kuma?" Ta bata rai tace "ba wani major aiki bane ba fa just a minor non surgical operation zasu yi masa suyi clearing airways ɗin sa dan ya samu sauƙin numfashi. I signed the consent yesterday kafin in tafi". Cikin daga murya nace "and why wasn't I informed?" Sai kuma na rufe bakins da hannayena biyu feeling terrible, na kama hannayen ta "Mommy I am sorry, I am very sorry. I don't know menene ya hau kaina, my emotions are all over the place. Please I am sorry" ta dafa hannuna tace "it is okay. I understand. Go and see him". Na juya da sauri mai kama da gudu na tafi dakin da aka ce yana ciki. Ina shiga na ganshi a kwance, flat on hus back, duk da cewa naji sunce allurar bacci suka yi masa amma sai da ganin sa a haka ya tayar min da hankali. Na tsaya ina kallon sa, trying so hard not to imagine ranar da zan ganshi a haka babu rai a jikinsa. Sai naga ya mirsa hannunsa ya bude idonsa ya sauke su a kaina. A hankali naga murmushi ya bayyana a fuskarsa, irin murmushin da yake yi da idan ya ganni. Ya miko min hannunsa "Safiyya. You are here? Zo nan" na tafi da sauri na kama hannunsa da duk hannayena biyu ina jin kamar in tsaga kirjina in saka shi a ciki. Yace "I just had a dream. A very bad dream. Wai wani abu ya faru dake, something terrible. I am glad it was just a dream. I am glad you are okay" sai ya mayar da idonsa ya rufe ya koma bacci. Na kankame hannun sa a kirjina ina kuka "I am sorry Daddy. I am really sorry". Sai da doctors din suka shiga sannan Uncle Sufyan ya fito dani ina ta kuka kamar wani major abu za'a yi masa. Da kyar ya lallashe ni nayi shiru, ina kallon Abdul yana yi min dariya but I didn't find his laughter funny. Sai da nayi shiru sannan Uncle Sufyan yace inzo muje gurin obstetric ɗin da zai ke dubani, I wanted to stay har Daddy ya dawo hayyacin sa amma yace an riga anyi appointment dole inje a ganni. Section daban ya kaini a asibitin, yayi musu magana sai ya tafi ya barni a gurin su, suka dauki duk vitals ɗina da duk wani gwaje-gwajen da ake bukata na masu ciki suka yi recording sannan suka shigar dani gurin doctor ɗin. Shima dai tambayoyin yayi min sannan ya duba duk results din tests din da akayi min. Sai kuma yace in kwanta zaiyi scanning. Na kwanta na rufe idona, ina jin sa yana goga abin scanning din a ciki na amma ban bude ido ba. Naji yace "a healthy baby. As happy as a puppy" sai kuma yayi dariya, ni kuma ban ga abin dariya a cikin maganar ba. Ya ce "will you like to know the gender?" Nayi sauri na girgiza kai na still idona a rufe. Ya sake cewa "open your eyes and look at it" na sake girgiza kaina. Haka yayi ta tsokana ta yana jana da hira dan in saki jiki amma ni ko a jikina. Sai da ya gama na dawo na zauna sannan ya fara yi min bayanin yanayin lafiyar babyn da kuma abinda zan iya fuskanta nan gaba kafin lokacin cire babyn yayi. Ya kara tambaya ta idan da gaske ina son a cire babyn at 7 months na amsa masa da yes, ni da zasu cire shi at 6 ma so nake yi. Har sai da ya gama yace zan iya tafiya, na mike tsaye sai kuma na dawo na zauna ina jujjuya hannu na. Ya tsayar da hankalin sa a kaina yace "is there something you want to talk to me about?" Nayi shiru kamar banji shi ba ina cigaba da jujjuya hannuna sannan na dago kai a hankali nace "when the baby is out. I want to give it up for adoption". Yayi shiru yana kallona fuskarsa da mamaki sannan yace "are you sure? Are you sure this is what you want to do?" Na gyada kaina "I am sure" ya girgiza kansa "I have to talk to your father about this. He didn't mention something like this. I need to....." Nace "I am 21 years old. I am legally old enough to make my own decisions" ya duba file ɗina, maybe to confirm the age, sannan ya sake kallona yace "what about the baby's father. We need to have his approval as well. He needs to.." Nace "there is no father. I don't know who the father is. I was raped" kalmar rape ɗin da na fada ta saka hawaye suka fara bin fuskata, and that caught his attention. Na ga alamun tausayi a fuskarsa, sai kuma yayi dan rubutu a cikin takardu na sannan yace "I am sorry for what happened to you. But I still need you to go home and think deeply about this. If it is still what you want when you come in for your next appointment then we will take the next step. There are papers that you will need to sign. And you have to decide if you want an open adoption or closed adoption. An open adoption is when you leave all your informations so that the baby and it's adoptive parents can keep in touch with you, while a close adoption is when the baby can never be traced to you, you will have no relationship of whatsoever with the baby ......" Direct nace "closed adoption. I want to give up the baby for a closed adoption". Ya cigaba da girgiza kansa. "Please Safiyya, reconsider. Think about this" nace "I have. I have made up my mind. This is what I want". Ya ce "okay. But this is protocol. You have to go and think about it. When you come back next week, then we will finalize your decision". Na gyada kaina. "okay. Thank you" na mike zan tafi, har sai da na bude kofa sai kuma na rufe ina kallon sa nace "one more thing please. I don't want my father to know. I don't want anyone to know. To gain access to the book contact 👇 0704 203 0419 Ta manhajar telegram ****. ****. ****. ****. ****. **** ❤‍🩹*SAFIYYAH*❤‍🩹 *Episode Five (5): The Path of Destiny* Ina fita na hango Mustapha yana tsaye a corridor din yana kallon kofar office din da na fito daga ciki, na dauke kaina nayi kamar ban ganshi ba na zo na wuce shi. Ya biyo baya na yana gyaran murya. "excuse me... Akwai mutum fa a tsaye tun dazu yana jiran ki" ban kalle shi ba ban kuma tsaya ba. Ya cigaba da bi na. "Nima bani na kawo kaina ba ballantana ki wulakanta ni. Cewa akayi inzo in jira ki in kin gama in mayar da ke gida, shi yasa na taho ba dan wai ina son hakan ba, kin san ni ina jin maganar Mommy da Daddy in sun gaya min bana tsallake wa". Na tsaya da tafiyar da nake yi na juyo ina kallon sa cikin ido, yayi murmushi, sai kawai na girgiza kaina na juya na cigaba da tafiya a raina nace he is not worth it, so yake in kula shi, in na kula shi kuma na bashi abinda yake so kenan. Ya cigaba da bi na. "excuse me??? Motar tana can side ɗin ba nan ba. You have two options here dear little sister, you can either come with me in kai ki gida kamar yadda iyayen mu suka ce or you can walk tun daga nan har gida, and in your condition, that will be very impossible". Still bance komai ba nayi hanyar inda side din da na bar Daddy dazu. Ya cigaba "okay. You have another option to get home. Maybe zaki samu wani ya baki lift. It won't be hard for you. I mean you are use to it tunda har tsaraba kika samu saboda shiga motar mutane". Na juyo a fusace na buga masa handbag ɗina a kansa, a raina naso ace tana da nauyin da zata ji masa ciwo. Ya dafe kan "aww. Me nayi? Daga fadar gaskiya? I guess ita dama gaskiya daci ne da ita" na juya na cigaba da tafiya ganin yadda mutane suka juyo suna kallon mu. Ya cigaba da bi na yana sosa inda na dake shi. "Kar ki damu. Na yafe miki. Ni bana fushi ai kin sani. Ko da zanyi fushi ma ba zan yi fushi da 'wife' ɗina ba. We will put all these behind us. Now, you will follow me muje in kai ki gida kamar yadda Mommy tace and in turn ba zan faɗa wa Daddy inda kika je ranar nan ba, ba zan bashi labarin me Tesla ɗin nan ba. I guess it won't be hard to trace him with that kind of a car, musamman in akayi considering da rashin girman makarantar ku. I bet shi kadai yake da irin motar a cikin makarantar". Na dakata da tafiyar da nake yi amma ban juyo ba sai da na rufe ido na na ja dogon numfashi da fatan zan hana kaina sauke mari kyakkyawa akan fuskarsa, na juyo da murmushi a tawa fuskar ina kallon sa nace "look Mustapha. Daga maganganun ka na fahimci cewa you are yet to receive the recent memo. Daddy ya fasa aura min kai, because I told him bana son ka. So stop following me around and find a life. And also stop threatening me because it is not going to work". Daga yadda yayi da fuskarsa na fahimci cewa Mommy bata gaya masa ba. Maybe tana fatan zata yi convincing dina na amince da auren so she thought he doesn't have to know. Yace "you are lying. You have always been a little liar" na daga kafada "of cause I am a liar, na sha yiwa mutane da yawa karya, people that matters a lot to me. But I won't waste my time lying to you because you are not worth it. In baka yarda ba ka tambayi Mommy" na juya zan tafi sai dai kuma har nayi taku biyu sai na tsaya na kuma juyowa ina kallon sa nace "and about cikin jikina. Ni na yarda akwai kiyama, na san kuma ni da kai zamu je can. A can ne kuma zamu karasa maganar". Sai da na yi nisa sannan na fahimci baya bina, kuma sai a lokacin na fahimci nayi batan kai na bi hanyar da ba ita ya kamata in bi ba. Sai da nayi tambaya sannan na gane inda na baro Daddy. Ina zuwana tarar da Mommy a zaune a waje. Na karasa gurinta ina haki saboda tafiyar da nayi kuma da sauri. Ta mike tana goge min gumin goshina da hanky din hannunta. "Ya naganki a kafa? Ina Mustaphan da na tura ya dauko ki ya mayar da ke gida ki huta?" Nace "ban san inda yake ba. Ba gida zan je ba. Ya Daddyn? Sun gama?" Ta koma ta zauna tace "eh sun gama. Na gaya miki fa ba wani abu bane za'a yi masa mai wahala ba. Bacci dai yake yi yanzu". Na wuce ta na shiga dakin, na ganshi yana ta bacci kuma ko daga yanayin yadda yake numfashi na fahimci aikin da aka yi masa ya saukaka masa numfashin sosai. Na zauna a kujerar kusa da gadon na kama hannunsa tare da sauke ajjiyar zuciya nace "I love you so much Daddy. And everything is going to be alright" amma ni kaina da na fada sai naji ban yarda da abinda nace ba, saboda a kasan zuciya ta ina jin cewa, this is only the beginning, saboda zuwa yanzu na fahimci cewa "tragedy" is another name for my family. Har dare ina tare da Daddy, duk kuwa da yadda Mommy take ta min maganar tafiya gida amma ban tafi ba na farko saboda bana son tafiya da Mustapha, na biyu saboda ina son spending time a kusa da Daddy duk kuwa da cewa ba kula ni yake yi ba. Sai da daren sannan Daddy da kansa yace ni da Mommy mu bi Uncle Sufyan mu tafi gida, sai a lokacin na sake ganin Mustapha dan tun sa da muka rabu dashi bai dawo ba Mommy ma ina jinta tana ta cigiyar sa. Naga sun tsaya sunyi maganganun su da Mommy sannan ta taho muka shiga mota muka tafi, tunda muka shiga motar kuma bata ce komai ba har muka je gida, da muka je ma bata yi min magana ba sai suka kama hirar su da Aunty Hajjo ni kuma nayi musu sallama na shiga daki. A dakin nayi sallah nayi shirin kwanciya bacci. Kamar kullum ina kwanciya dukkan damuwoyin da nake dasu suka saukar min, amma a daren yau abinda yafi tsaya min arai shine Muhammad. Maganar sa dazu da Mustapha yayi ta taba min bangaren da nake ta kokarin binnewa a cikin zuciyata a kwana biyun nan. Bana son in bude fejin tunaninsa dan bana jin zuciyata zata iya daukan halin da na san yana ciki a yanzu. Na cutar da shi iyakacin cutarwa. Amma kuma bana jin ko da a raina cewa abinda nayi ɗin ba dai dai bane ba. In na gaya masa gaskiya he will stick with me through thick and thin. And I am a walking and breathing tragic bomb waiting to explode. Bana son stains ɗina ya bata white ɗin sa. So nake ya tsane ni tsanar da zata saka ya manta da ni kar ya cigaba da bibiyata. So nake ya samu wadda ta dace dashi yayi aurensa ya gina kyakkyawar rayuwar sa da iyalinsa. Irin kyakkyawar rayuwar da muka fara tsarawa zamuyi ni da shi. Na fara kokarin picturing dinsa ya yanzu, ko me yake yi? Ko yayi bacci? Na duba agogo naga karfe tara, meaning karfe takwas kenan a Nigeria. Na san bai yi bacci ba yanzu. Ten mostly yake yin bacci. A wannan lokacin mostly mukan kasance muna yin waya ne. Na fara kokarin picturing dinsa a dakin sa. Bana jin akwai wani bangare a dakin sa wanda ban sani ba saboda yawan FaceTime da muke yi idan yana dakin. Na tina da wata hira da muka taba yi a cikin irin hirarrakin mu na planning rayuwar mu. ****.     ****.     ****.    ****.    ****.     *** "And you will look so handsome in white" Ya bata fuska "and who told you white zan saka?" Nace "angwaye ai white suke saka wa ranar daurin aure, and I will wear white lace with golden veil and we will snap pictures, irin Mr and Mrs din nan" yayi dariya "ohh Piya, so you think I am like most people da zanyi abinda most people suke yi? I am special. I will wear something special" nace "okay to menene special ɗin, wacce color zaka saka? Pink or yellow?" Ya kyalkyale da dariya, sai kuma ya juya bayansa yana kallon kofa "kinga kin saka ni ina ta dariya a daki ni kadai, kar mutanen gidan nan suce nuts din kaina sun kwance" nace "to ka bani amsa mana. Kasan kuwa har na hango ka ka saka yellow shadda ranar daurin aure?" Ya kuma yin dariya, fuskarsa cike da nishadi dan lokacin bashi da wata matsala a duniya. Nace "am serious fa farar shadda zaka saka" yace "to wai saboda me zan saka fara?" Na turo baki na kwabe fuska kamar zanyi kuka har da bubbuga hannuna akan katifar da nake zaune  "ni dai Allah sai ka saka fara, Allah in baka saka ba ranar kuka zanyi tayi" yace "okay okay shagwababbiyar Daddy. Naji zan saka fara, amma ba shadda ba, sai dai yadi" na danyi tunani sai kuma na gyada kai cikin nuna amincewa "okay. Allah ya taimake ka. Ranar da ka sha rigima" yace "in dai rigimar ki ce ai na saba da ita, in an tashi kawo kayan lefenki har da zanin goyo za'a saka. Dan naga alamar in kika fara wata rigimar sai na goya ki sannan zaki yi shiru". Na rufe fuska ta ina dariya, yace "am serious fa. That's something I can do. I just can't wait for the time". ****.    ****.    ****.    ****.    ****.    ****.    A cikin tunanin bacci ya dauke ni. A cikin baccin ne kuma nayi mafarki da shi. Sai dai a cikin mafarkin ba dariya yake kyalkyalawa ba, in fact fuskarsa a murtuke take da irin kallon da yayi min ranar da muka rabu dashi. Ina tsaye a kofar office dinsa hannayena biyu rike da cikina. "I hate you" ya fada min cikin dacin murya. "I hate you more than I have ever loved you" "You are the worst creature that have ever walked the surface of this earth" Sai kuma ya dauko bindiga daga cikin aljihunsa ya harbe ni da ita a kirji dai dai saitin zuciya ta. Na saki cikin da sauri na dafe kirjin. Ina cewa "I am sorry Muhammad. I am very sorry" Ji nayi an rike kafaduna duk biyun ana girgiza ni da karfi. "Safiyya? Ke Safiyya" da muryar Mommy. Na bude ido na a firgice saura kadan in fadi daga kan gado, sai a lokacin na fahimci, mafarki nake yi, daga alama kuma maganganun da nake yi a mafarkin sun fito fili. Nayi kokarin daidaita numfashina tare da karanto addu'a, sannan na dafe kaina da hannu daya, har a lokacin ina jin amsa kuwwar muryar Muhammad. "I hate you" Mommy tace "wanne irin mafarki kike ne haka Safiyya? Waye kuma Muhammad?" Nayi sauri na kalle ta idanuna a bude. "uhmm Muhamm... Waye Muhammad?" Na mayar mata da tambayar, tace "to ni kya tambaye ni? Ke kike ambatar Muhammad cikin baccin ki kina bashi hakuri" na girgiza kaina "ni ban san wani Muhammad ba. Mafarki ne kawai. Ni ba zan iya tuna mafarkin ma da nayi ba" sai nayi sauri na koma na kwanta tare da jan bargo na lullube har fuska ta tare da rufe idona da karfi ina sauraron yadda zuciya ta take bugawa da karfi, bakina yana furta "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ni na san a yanzu idan Mommy da Mustapha zasu hada informations din da suke da su a guri daya, to tabbas zasu iya tracing Gidado. And I can't imagine anyi knocking gidan su gidado an gayawa iyayensa cewa yayi wa dalibar sa ciki. Wannan mugun tunanin shi ya yanke min dukkan baccin wannan daren ****.    ****.    ****.    ****.     ****.     **** *Him 👳🏻* Kwanaki biyun nan suna daga cikin worse days of Gidado's life. Gabakidaya kwanaki biyun a daki yayi su, highest da ya fito shine parlor ya gaishe da Abba ya juya ya koma. In an tambaye shi me yake damunsa sai yace bashi da lafiya. Babu abinda bai ce yana damunsa ba. Yace kansa ne yake ciwo yace cikinsa, da daddare kuma da Mama ta shiga har daki ta matsa masa da tambaya sai yace kwakwalwar sa ce take ciwo. It should be funny but it didn't sound funny to Mama, dan sosai hankalin ta yake a tashe akan halin da gudan ranta yake ciki. It also didn't sound funny to Gidado dan shi a lokacin da ya faɗa din har ga Allah ji yake yi da gasken kwakwalwar tasa ciwon take yi, sai dai kuma bai san yadda zai misalta ciwon ba. Zuwa lokaci kowa a gidan ya fahimci halin da yake ciki, zuwa lokacin kuma kowa ya fahimci koma menene yake damunsa yana da dangantaka da Safiyya, saboda dama kowa a gidan ya san da zaman Safiyya ya kuma san da girman matsayin ta a zuciyar Gidado, har Abba. Sai dai duk da cewa sun san abin ya shafe ta amma basu san takamaiman menene ya faru ba, wannan shine abinda Mama take ta tambaya amma ta kasa samun amsa, daga baya dai sai tayi deciding tayi involving dan'uwansa kuma abokinsa, tana saka ran zai iya gaya masa abinda su ba zai iya gaya musu ba. Bayan ta yanke wannan shawarar sai ta kira Al'ameen a waya, wanda yake aboki kuma first cousin a gurin Gidado ta kuma nemi da yazo gidan ya duba halin da dan'uwan na sa yake ciki kuma suyi magana. Da yamma bayan ya taso daga gurin aikinsa ya zo gidan, ya gaishe da Mama ta tambaye shi lafiyar mahaifiyarsa Mami da amaryarsa Humaira, ya sunkuyar da kai yana jin kunya, sai kuma ya mike ya tafi dakin Gidado. Ya shiga ya tarar dashi a zaune akan sallaya ya jingina bayan sa da jikin gado yana jan carbi, idonsa a rufe sai bakinsa da yake motsawa a hankali. Ya zauna a kan kujera yana kallon sa, daga inda yake yana iya lura da yadda idanuwansa suka fada ciki kuma fatar idon tayi baki. "Muhammad" ya kira sunansa. Ya bude idon ya kalle shi sai kuma ya mayar da su ya rufe ya cigaba da jan carbin sa. Al'ameen yayi ajjiyar zuciya yace "ba tun yau ba na gaya maka. That girl is going to be the death of you" Gidado ya kuma bude idonsa yace "congratulations. You predicted right" Al'ameen ya sauko ya zauna a kusa da shi yace "ba haka nake nufi ba, believe me, I cannot say na san exactly me kake feeling right now but I know what loving a girl deeply means" bai ce mishi komai ba sai ya kuma mayar da idon ya rufe. Al'ameen yace "me ya faru?" Yayi shiru bai ce komai ba. Al'ameen ya sake tambaya "did you guys break up?" Gidado ya a girgiza kansa yace "no" sai kuma yayi nodding yace "yes. I guess we did. I don't know" Al'ameen yace "me kake nufi da you don't know. What happened?" Gidado yayi shiru kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace "she is.....she said she is.....she told me that she is....... I saw that she is...." Ya hadiye yawu ya kai sau biyar amma kalmomin sun kasa fitowa. Al'ameen yayi kokarin taimaka masa "she is with someone else? She loves someone else?" Gidado ya girgiza kai "no...... Yes. I mean..." Yayi ajjiyar zuciya sannan a hankali yace "I mean she has been with someone else all along. She is married. She has been married all along ". Al'ameen ya bude ido yana kallon sa cikin mamaki. Ya motsa bakinsa amma ya kasa magana. Gidado yace "what a fool I have been" Al'ameen ya girgiza kansa "she is lying. Karya tayi maka. Tana so ta rabu da kai ne shine tayi maka karya" Gidado ya sake girgiza kansa yace "no.... Ba karya take yi ba. I saw it da idona. She is pregnant. I saw her pregnant. She told me she has been married all along" Al'ameen ya gyara zamansa yana kare wa dan'uwan nasa kallo cikin mamaki "kai! Haba! It cannot be. Shekarar ka nawa da yarinyar nan. How can you not know? Ta yaya za'a yi ta iya boye magana kamar wannan" Gidado ya daga kafada "I don't know" Al'ameen ya sake cewa cikin fada "karya take yi fa. Ni nace maka karya take yi fake ciki ta saka a jikinta. There is no way da zaka kasa gane kana tare da matar aure for almost three years. Yadda kuke da ita there is no way da mijinta ba zai gane tana tare da wani ba. My guess is ta samu wani ne and she wants to ditch you shine tayi maka wannan karyar just to break you yadda zaka fi rabuwa da ita" Gidado ya mayar da idonsa ya rufe yana jin ciwon kansa yana karuwa. "I don't know what to believe Ya Ameen. A yanzu haka yaki akeyi a tsakanin zuciya ta da ƙwaƙwalwa ta. Zuciya ta tana son creating all the excuses in the world dan ta kare ta. Ƙwaƙwalwa ta kuma tana kokarin sanin gaskiya. Ni kuma babban abinda nake son sani shine 'why?' idan har da gaske tana da auren me yasa tayi dating dina ta saka min gubar soyayyar ta a cikin jijiyoyin jiki na sannan ta zabi yanzu dan ta watsar da ni. Idan kuma karya take yi kamar yadda kace me yasa zata yi min karyar" Al'ameen ya dafa kafadunsa da hannayensa biyu yace "saboda kamar yadda na gaya maka ta samu wani, someone da take tunanin is better than you. Dama can ba son ka take yi ba". Gidado ya ture hannun sa daga kafadar sa yace "idan akwai abinda nake da tabbas akan shi a cikin duk wannan maganar shine Piya tana so na. I will never believe cewa ba ta so na. Something...." Al'ameen yace "haa.. this is your heart talking. Dan tana son ta. Kamar yadda kace, tana kokarin kare ta ne kawai. How can she love you and then do this to you?". Gidado yace "i don't know. Shine abinda nake ta kokarin sani nima. Shine abinda zan iya sadaukar da komai a yanzu dan in sani. Sai dai bani da yadda zanyi in sani ɗin. Ta toshe duk wata hanya da zan bi in sani, ko kuma at least in ganta, she blocked me" ya fada yana nuna wa Al'ameen wayarsa kamar a jikin screen din ne aka rubuta haka. Al'ameen ya karbi wayar yana kallon hoton jiki yana girgiza kai, a ransa yana matukar tausayin dan uwan nasa saboda yasan zafi da kuma zakin so, ya kuma fahimci soyayyar tayi wa Gidado mugun kamu, sai dai bai yi dace ba. So baiyi masa adalci ba. Ya mika masa wayarsa yace "Muhammadu...... You should stop thinking about how to see or talk to her. You should start thinking about how to forget about her. Mama da Abba are very worried. She is not worth that. Nothing is worth that". Gidado yace "I can't. Ba zaka gane ba Ya Ameen. Ko da zan manta da ita ɗin ina bukatar in san gaskiya. Ina bukatar in ganta mu zauna muyi magana ta fahimtar juna ni da ita. In san ko akwai wani abu da yake damunta.." Al'ameen ya mike tsaye, baya son yaji haushin Gidado amma kuma ya kasa hana kansa. Yace "okay taso muje gidan su sai mu tambaya" Gidado ya kalle shi bai ce komai ba dan ya fahimci bakar magana yake gaya masa, ya sake cewa "ko kuma ka kira wani a cikin yan gidan su kaji abinda yake faruwa. Ko babbar kawarta haka, ai nasan ita ma zata sani". Gidado ya jingina kansa a jikin bango yana jin kamar ya tashi ya shake Al'ameen. Al'ameen yace "ohh haka ne fa. Na manta. Baka san ko daya a cikin wadannan ba. How are you going to know the answers to those questions kuma?". Sai kuma ya dawo ya tsuguna a gaban Gidado yace "look Muhammad, there is no way da budurwar da take son saurayi, so na gaskiya kuma na aure, zata ki kaishi gidan su, zata kuma hana shi sanin kowa nata, for over two years. A cikin biyu dole akwai daya. Ko dai rage dare kawai take yi da shi ba sonsa take ba, ko kuma kamar yadda ta gaya maka, matar aure ce take cin amanar mijinta da kai. I know it is hard Muhammad, but you must see reasons. You must be strong and accept the truth. You must let go ko ba dan kan ka ba ko dan mahaifanka" Gidado ya gyada kai, ba tare da ya bude idonsa ba yace "thank you " Al'ameen ya mike zai fita, har ya kai kofa Gidado yace "Muhammad. Kar ka gaya musu please. Kar ka gaya wa Mama". Sai da yaji alamar ya bar dakin sannan ya bude idonsa yana kallon kofar da Al'ameen din ya fita ta cikinta, amma ba kofar yake kallo ba dan hankalin sa yana can wani gurin daban. Ya dauki wayarsa a gurin da Al'ameen ya bar ta ya kalli hoton kan screen din zuciyarsa taki amince masa da first maganar Al'ameen cewa Safiyya bata son sa tun farko, ba ya jin kuma zai taba yarda da hakan. Ya tuna da rana ta biyu daya sake ganinta a rayuwar sa bayan haduwarsu ta farko a jirgi. Haduwar su ta biyu ta kasance ne shekara bakwai bayan ta farkon. Bayan ya gama first and second degree dinsa ya dawo yayi service. Shekaru bakwai sun wuce amma bai manta da yarinyar da ya taɓa haduwa da ita a jirgi ba. Kuma can a kasan zuciyarsa yana fatan zai kuma haduwa da ita. ****.     ****.    ****.    ****.    ****.     **** A hankali yake tafiya a motar sa, yana juya stirring cikin nutsuwa zuciyarsa cike fal da farin cikin da bai san dalilin sa ba, amma yana tunanin akan maganar da suka yi da Abba ne dazu. Ya kunna kida kadan kadan yana tashi yana kara masa nishadi, a ransa yana lissafa rayuwarsa and how successful everything has been going for him.  Yayi dialing number ɗin abokinsa da ya fito nema "kai ya? Gani fa a junction ɗin, ina zan juya" abokin yayi dariya yace "kai fa matsala ta da kai baka san gari ba. Abeg I can't direct you, ask Google map" ya katse wayar. Gidado yayi dan karamin tsaki "karamin dan is, sai in fasa zuwa ma" ya cigaba da driving a hankali da hannu daya dayan hannun kuma yana kokarin nemo direction din inda zai je. Ya dago kai dan tabbatar da inda yake. A lokacin ne ya ganta. Tana tsaye a gaban mota hannunta daya rike da key din mota dayan kuma rike da jakarta. Fuskar ta a murtuke da alamar bacin rai. Ga uwar ranar da ake kwallawa a ranar. Kallo daya yayi mata ya dauke kai ya cigaba da abinda yake yi, har motar sa ta gota inda take sai kuma ya dago kai da sauri ya sake kallon ta ta mirror din motar. Gabansa ya fadi yana ganin kamar yasan fuskar. Yayi slowing down ya sake gyara mirror dinsa dan yana kare mata kallo. Yaji wani excitement ya shige shi. Komai na features din fuskarta suna nan kamar yadda yake tuna wa da su but more matured, no longer child like but lady like. More feminine. More beautiful. More beautiful than he had ever imagined she would be. Ya tuno da ranar da suka hadu a cikin jirgi. Surutun da ta ringa yi masa, tsokanar sa da ta ringa yi, da kuma yadda suka rabu. Ita ta riga shi fita daga jirgin a ranar dan air hostess ce ta dauko mata jakarta daga inda ta barta ta taho gurinsa, ta kuma zo suka fita tare. A arrival yayi ta baza idon ko zai sake ganin ta amma bai ganta ba. He then wondered ko paths dinsu zasu sake crossing later in life. And it did ... Sai dai kuma bashi da tabbas din zata ma tuna da shi ballantana har ta gane shi. Yayi reversing motar a hankali still yana kare mata kallo dan ya tabbatar da cewa ita din ce dan kar yaje yayi wa wata magana. Sai dai yana zuwa saitin ta sai ta kara yin gaba kamar bata san mota ta tsaya a gaban ta ba. Ya bude kofar motar ya fito still idonsa a kanta. Yana jin zuciyarsa wani iri dan shi dai bai taba ganin macen da ta yi masa kyau kamar ta ba, bai kuma taba tsayar da mace a hanya yayi mata magana ba. Ta ƙara bata rai tare da juya fuskarta daya side ɗin, daga alama kallon da yake yi mata ya dame ta. Ya tako zuwa gabanta, sai ta zaro wayar ta ta fara dannawa kamar bata san dashi a gurin ba. Yayi mata sallama. "Assalamu alaikum" ta amsa, amma shi kansa da yake kusa da ita motsawar bakinta kawai ya gani amma baiji muryar ta ba. Ya danyi shiru yana tsoron kar ta wulakanta shi amma kuma yana son gwada sa'ar sa, ya dan leka fuskarta a hankali yace "Piya?" Ta dakata da danna wayar da takeyi ta dago kai tana kallon sa da alamar tunani a fuskarta, lokaci daya kuma sai yaga recognition a fuskarta, and farin cikin da yaji a ransa was more than he thought. "Malam Muhammadu dan fillo?" Yayi dariya, dariyar da yaji ts wanke dukkan tsoronsa. Ta nuna shi da dogon yatsan ta "Washington DC" ya girgiza kai "no. Manchester" tace "yeah. Right. Manchester. What are you doing here? How are you here?" Yace "ke zan tambaya. Never thought I will ever see you again" tace "me too. It has been five years?" Yace "seven" tace "wow. How time flies. Kayi girma sosai" ta fada tana kallon sa tun daga kan takalmin kafarsa har zuwa yalwatacciyar sumar kansa da bai rufe da hula ba. Ya shafa kansa "ke ma haka". Suka yi shiru duk su biyun, kowanne su trying not to look at the other. Sai kuma suka kalla a tare, suka hada ido, and then they smiled together. "uhmm ...... Trouble with the car?" Ya tambaya yana nuna motar da take tsaye a gabanta. Ta bata fuska "wallahi... Ta mutu.... I don't know why. Ina tafiya kawai ta mutu. Na kira kuma an hada ni da mechanic har yanzu kuma bai zo ba" yace "why not leave the car here in yazo ba sai ya dauka ba. You shouldn't be here standing under the sun" ta daga mishi key din motar "sai yazo zai karbi key ai" ya girgiza kai "still sai yaje gida ya karba. You shouldn't be here alone" tayi ajiyar zuciya bata ce komai ba. A hankali yace "can I take you home?" Ta juya ta kalli motar ta, sannan ta kalle shi fuskarta kamar zata yi kuka, yace "sai in dawo wa da mechanic ɗin key din, in bai zo ba kuma I can get another one for you" ta girgiza kai "ba wannan ne damuwa ta ba. Uncle Ahmad will kill me today. Yace kar in fita da mota. Yace ban iya mota ba. Baya son a bani mota ni kuma so nayi in nuna masa na iya" Gidado ya mika mata hannu yace "mu ga key din" ta bashi, hoping motar lafiyar ta kalau itace dai bata iya din ba. Ya bude ya shiga yayi ƙoƙarin tayar da ita amma sai yaji yana murda key din tayi wata irin kara. Ya fito yana kallon Safiyya yace "key starter din ta ta lalace. Maybe kinyi ta murda key din ne" ta fara bubbuga kafa a kasa "to ba ita ce taki tashi ba" yayi dariya "tuba take yi. Now call the mechanic and tell him key starter issues ne, tell him kuma zaki tafi gida yazo gida ya karbi key ɗin". Tayi abinda yace sannan ya bude mata passenger's seat din motarsa ta shiga ta zauna shi kuma ya zagaya ya shiga seat din driver. Suna kama hanya ya lura duk ta zama uncomfortable, sai yayi kokarin yi mata hira "you look good. You look really good" ta danji kunya "thank you. You too" yace "so... how have the 7 years been going?" Tayi ajjiyar zuciya "like the blink of an eye" yace "na dauka ba zaki gane ni ba fa, I was praying kar ki yarfa ni" tace "nayi niyyar yin hakan fa. But sai kuma ya kasance kai ne. Ni ma nayi mamaki dana gane ka. Amma kai ya akayi ka gane ni?" Ya daga kafada "ina da saurin gane mutane. Besides, I have thought about you a lot within these years. Ke fa" tace "ina tuno da kai ne kawai idan na shiga jirgi na hadu da me aerophobia" suka yi dariya a tare. Wayarta tayi kara, ta dauka. Shi kuma ya samu damar cigaba da kare mata kallo "Yaya Mukhtar na bar gurin fa. Na kira shi nace ya same ni a gida. Alright. Don't tell Uncle please. Thank you". Ta ajiye wayar tare da ajjiyar zuciya yace "I like the way you talk" ta juyo tana kallon sa tace "what?..." Ya maimaita "I like the way you talk. I am not sure if it is the way your lips moves or the sound of your voice or the body language, ban sani ba. I just like it. It is therapeutic" ta sunkuyar da idonta kasa tana murmushi, ya kara da cewa "and the way you smile too". Sai ta ja mayafin ta ta rufe fuskarta. Ya tsaya yana kallon dogayen yatsun hannunta. Aka kira wayar sa, ya dauka direct yace "kai na fasa zuwa fa. And don't call me again". Ta bude fuskar ta tana murmushi tace "babu kyau karya alkawari fa" yace "ba alkawari nayi ba  fa. Besides, there is no where I would rather be then here". Motarsa ce tayi wata yar kara sannan ta mutu. Suka juya suka kalli juna. Yayi kokarin sake tayar da ita amma taki tashi. Safiyya ta rufe fuskarta tana dariya yayin da shi kuma ransa in yayi dubu ya baci. Ta bude fuska tace "it is official. Yau da rashin sa'a na tashi" ya juyo yana kallon ta yace "ni kuma yau sa'ar dana tashi da ita bata ma misaltuwa". Tace "I am not sure. Maybe this is a sign that we are not meant to be together" ya bude kofa ya fita yana girgiza kai da sauri. "No. This is a sign that we will walk the path of Destiny together" ta fito itama tace "walking? Not driving" yace "I am ready to do it if you are" ta saka hannu tana kare rana tace "under the sun?" Ya zagayo gaban ta ya tsaya, jikinsa yayi blocking mata hasken rana yace "I will shield you". Suka fara tafiya a hankali, side by side, enjoying each other's company, breathing in each other's scent, suna kuma updating juna akan abubuwan da suke faruwa a rayuwar su. A lokacin ne ya gaya mata karatu dama yaje yi Manchester, kuma ya gama degree dinsa na daya dana biyu, ya kuma yi service. Ya kuma sanar mata da bukatar mahaifinsa akan yaje yayi aiki a ƙarƙashin sa, da kuma shi burinsa na yayi aiki a sabuwar jami'ar da baban masa da siblings dinsa suka bude in memory of mahaifinsu ambassador Muhammad Dikko, M.D University Abuja "ina so nima in bayar da tawa gudummawar wajan kafa jami'ar". Ta fahimta, sannan itama ta bashi nata labarin. Family dinta mazauna garin Kano ne. Ta gama Sec school dinta three years back, amma kuma sai babanta ya fara rashin lafiya. Jinyar sa ya saka bata fara jami'a ba saboda basa zama a kasar ko da yaushe suna yawon kasashe neman magani, sai yanzu ne yayi insisting dole ta dawo Nigeria ta zauna a gidan Uncle din ta anan Abuja ya nema mata admission a daya daga cikin manyan private universities ɗin da suke garin. Last week ta zo garin. Kuma already ta gaji da garin. A lokacin suka kai karshen junction ɗin suka hau kan babban titi. Suka tsaya suna kallon juna yace "we did it. The path was rough, tiring and very sunny. But we arrived at the destination, together" Kafin tayi magana mota ta tsaya a gabansu. Aka sauke glass din wani ya leko "Fiyya. There you are. Na kasa hakura shine na biyo bayan ki. Let's go home kafin ya dawo ya ga bakyanan" tayi ajjiyar zuciya, daga alama ranta bai so haka ba. Ta so su ci gaba da tafiya a kafa ita da shi. Duk da dai cewa a kwai wahala, but with him by her side, zata jure. Ta juya tana kallon Muhammad tace "cousin dina ne. Gidan su na sauka. Kafin kazo dazu shi na kira na gaya masa inda nake" Ya gyada mata kai "go" tace "okay. Zamu yi magana" yace "yes. I will call you" ta danyi shiru tana kallonsa. Ya sake ce mata "go... Rana tana dukan ki. It is not good for your skin" tayi murmushi. Ya bude mata kofar motar. Har zata shiga ta kuma juyowa tana kallon sa tace "are you not forgetting something?" Yayi shiru yana tunani sannan yace "no. Me na manta?" Tayi murmushi tace "I don't know. Kawai ji nayi kamar kayi wata mantuwa" na motar ya leko. "common. Let's go sauri nake yi fa" ta shiga reluctantly ta zauna, Gidado ya ja baya tare da yi mata alamar I will call you. Ta yi murmushi. Sai da motar tasu ta ja sannan hankalin sa ya dawo jikinsa. Sannan ya fahimci abinda take cewa ya manta. "God damnit" ya fada da dan karfi. "Damnit" Ya maimaita yana saka yatsun hannunsa duk goman a cikin gashin kansa yana jin kamar ya fincike gashin ya zubar. Bai karbi number wayar ta ba. To gain access to the book contact 👇 0704 203 0419 Ta manhajar telegram ****.    ****.    ****.     ****.    ****.    ****.    ❤‍🩹*SAFIYYAH*❤‍🩹 *By* *Maman Maama* *Episode Six (6): Mother* Knocking kofa ne ya dawo dashi daga tunanin da yake yi. Ya mike ya koma kan kujera ya zauna yace "yes". Mama ce ta turo kofar amma sai ta tsaya daga bakin kofa tana karewa dakin kallo tace "ina Al'ameen ɗin? Ko ya fita bai yi min sallama ba" Gidado yace "ya fita, maybe ba kya kusa" ta karasa shigowa da bacin rai a fuskarta tace "ko bana kusa ai sai ya neme ni, saurin me yake yi? Ni fa na kira shi kuma sai ya tafi ba tare da na sallame shi ba" Gidado bai ce komai ba amma ya san shi ya jawowa Al'ameen wannan fadan tunda shi yace kar ya gaya mata maganar da suka yi, ya san kuma Al'ameen ya gudu ne dan baya so ta tambaye shi ya suka yi. Ta shigo ta zauna akan gado tana kallon sa tace "ya jikin?" Ya ajiye carbin hannunsa tare da safa addu'a a fuskarsa yace "da sauki Mama, kar ki damu da ni. Zan je asibiti anjima" ta bata rai "in kaje asibitin me zaka ce musu? Ji nake dazu da na tambaye ka abinda yake damunka cewa kayi kwakwalwar ka ce take ciwo, haka zaka ce musu a asibitin? ta yaya zaka ce kar in damu? ji yadda ka koma cikin kwana biyu, me yasa ba zan damu ba? Akan ka aka fara faɗa da budurwa ne wai?" Gidado ya dago kai yana kallon ta, ya bude baki sai kuma ya mayar ya rufe. Shi bai san me zai ce mata ba. Baya son ya gaya mata abinda ya faru tsakanin sa da Safiyya saboda baya son ta tsani Safiyyan, duk kuwa da cewa bata san ta ba. Wannan shine zurfin soyayyar da yake yi mata. Yin shiru sa ya saka ranta ya kara baci. "Kai ba zaka gaya min ba kuma shima dana turo ya tambaye ka ya tafi bai gaya min ba. Wani abu ne mai muni ya faru? Ko wani laifin ka aikata kake boye min?" Yayi saurin girgiza kai tare da bude ido "no, Mama babu abinda nayi fa. Babu abinda ya faru, kawai bana jin dadi ne. Kuma zanje asibiti in an jima". Ta dauki wayarsa daga kasa ta mika masa tace "idan har babu wani abu da ya faru kira Safiyya ka bani ita mu gaisa" ya rike wayar yana jujjuya ta. "Bata kasar, kiran ba zai shiga ba" tace "WhatsApp call nko? Shima ba zai shiga ba? Ko kuma da ta tafi wata kasar a matsayin ka na mai neman aurenta bata baka layin da take amfani da shi a can ba?" Ya ajiye wayar akan cinyarsa tare da sunkuyar da idonsa kasa, abubuwa da yawa suna yawo a ransa. Ta kuma daukan wayar and kafin ya fahimci me yake faruwa sai ta kama hannunsa ta saka fingerprint dinsa ta bude wayar. Ya dago kai da sauri yana kallon ta, trying to process abinda yake faruwa "Mama! Mama Please don't!" Ta juyo tana kallon sa tace "ko zaka kwace wayar ne? Ko kuma akwai abinda kake boyewa ne wanda baka son in gani? I cannot just seat idle and watch you turn into this, sai dai in abinda yafi karfina ne". Yayi shiru tare da saka hannu biyu ya dafe kansa, shi dai yasan babu wani abin ashsha da yake cikin wayarsa wanda ba zai iya budewa a gaban ta ba, abu daya ne baya so ta gani wanda kuma ya san shine abinda take after, chats dinsa da Safiyya. Tun shekaran jiya Safiyya tayi blocking din calls dinsa, amma kuma ta manta bata yi blocking dinsa a WhatsApp ba, wanda dama shine kadai social media app din da yake yi anan ne kuma suka fi yin hira. Tun shekaran jiyan kuma yake tura mata sakonni, amma ya fahimci kamar data dinta a kashe take gaba daya dan sakonnin basa zuwa gare ta, amma hakan bai hana shi rubuta wa ba, hakan bai hana shi gaya mata duk abinda yake zuciyarsa ba, all the things that he wanted to say to her, hoping that zata bude ta karanta ko da ba yanzu ba ne ba. Ya tabbatar kuma idan Mama ta karanta sakonnin zata fahimci gaskiya abinda ya faru tsakanin sa da Safiyya, zata fahimci cewa Safiyya matar aure ce kuma har tana dauke da ciki. Bata jima tana danna wayar ba kuwa ta ga abinda yake boyewa, tun daga expression din fuskarta ya gane ta gani.  Da sauri take karantawa harshenta har yana hardewa. Wadansu maganganun a fili wasu a zuciyarta. Har tazo kan wanda ya warware mata warware mata damuwarta ya kuma ɗora mata wata damuwar data ninka waccan. "I only want to know me yasa kika yi min haka, me nayi miki da zaki yi min haka, how can you let me fall this deeply in love with you alhalin kina matar aure?" Mama ta saki wayar daga hannunta ta fadi akan carpet, "Muhammad!" Ya jawo hannayensa daga kansa ya rufe fuskarsa da su yana jin wani zazzaɓi mai zafi yana saukar masa. "Matar aure fa Muhammad. Yanzu Gidado dama da matar aure kake tare? Matar wani?" A muryar ta yana jin irin zafin da yake zuciyarta and how much disappointed she was in him. Ya zame daga kan kujerar ya sauko kasa "Mama.... Mama wallahi..... Na rantse miki wallahi ban sani ba" ta mike tsaye sannan ba tare da tace komai ba ta yi hanyar fita. Ya mike shima ya bita a baya da sauri "Mama, Mama" bata waiwayo ba har suka zo suka wuce Mufida a falo , Mufida ta bisu da kallo cikin tunanin abinda ya faru, har sai da ta shiga dakin ta sannan ya samu ta juyo ta kalle shi, sai dai ganin hawaye a idonta ya saka ya ji kafafuwansa sun kasa daukan sa. Ya zame ya durkusa a gabanta "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Mama dan Allah kar kiyi kuka a kaina. Wallahi ban san tana da aure ba. Boye min tayi" ta juyo da tsawa tace masa "ka tashi ka fita ka bani guri, ka tashi in daina ganinka a gaba na kar kasa inyi maka abinda ni da kai gabakidaya zamuyi nadama" ya mike da sauri ya fita, ta turo kofa ta rufe, amma sai ya kasa tafiya ya jingina da jikin kofar sannan ya zame ya zauna a gurin, babu abinda bakinsa yake furta wa sai innalillahi wa inna ilaihir rajiun, shi kansa ya kasa tantance me yake faruwa da rayuwarsa, a cikin kwanaki biyu rayuwarsa ta juya daga good zuwa bad and now it has turned to terrible. Tun tasowarsa he has always been Mama's boy, akwai shakuwa da fahimta sosai a tsakanin sa da ita. She raised him and his siblings with love, da soyayya ta raine su da soyayyar kuma ta tarbiyyan tar da su. Tun tasowarsa kuma ba zai iya tuna ranar da ya ganta cikin bacin rai irin na yau ba. He has always been a good boy. Da wahala yayi laifin da zata daga masa murya ma ballantana har ta kai ga zubar da hawaye a kansa. Ya tuna da maganar da Ya Ameen ya fada masa dazu, cewa Safiyya is not worth bacin ran iyayensa, a lokacin maganar bata dake shi sosai ba sai yanzu da yaga bacin ran na gaske. Yana nan zaune har Mufida da ta ji su shiru ta taso ta biyo bayansu, a lokacin ne ta ganshi a zaune a kasa a kofar dakin Mama, hankalin ta ya tashi dan bata taba ganin yayan nata a cikin irin wannan halin ba. Ta durkusa a gabansa tare da dafa kafadarsa "Hamma? Lafiya? Me yake faruwa?" Ta fada muryar ta tana rawa kamar zata yi kuka. Ya dago jajayen idonsa yana kallon ta yace "Mufida. Kiyi min addu'a. In kinyi sallah kiyi min addu'a" ta rike kukan da yake neman kwace mata tace "kullum ina yi maka addu'a dama Hamma, amma yau zan tashi cikin dare zanyi sallah musamman dan kai, zanyi maka addu'a, insha Allah Allah zai yaye maka dukkan damuwarka". Ranar cin abincin daren su sam bai yi armashi ba a gidan. Dan yau damuwar Gidado tafi ta kullum yawa, Mama ma kuma juya abincinta kawai take yi ba ci take ba. Daga baya ma sai ta tashi tace musu zata je ta kwanta. Gidado ba haka yaso ba, so yayi tayi masa fada, so yayi ta gayawa Abba in yaso sai ya samu damar yi musu bayani tare da kare kansa, amma maimakon haka sai ta bashi silent treatment. Kwanan su biyu a cikin wannan yanayin. A rana ta biyun ne Gidado ya samu Mama a kitchen tana aiki tare da Mufida ya ajiye mata wayarsa. "Mama dan Allah in ba zaki saurare ni ba ma fa wayar tawa nan ki duba, ki karanta sakonnin gabaki daya zaki fahimci gaskiya ta" ta juyo ta kalle shi, zuciyarta tana yi mata zafi akan yadda dan lelen dan nata ya koma saboda mace, tace "bana bukatar duba wayarka, na riga naga abinda nake bukatar gani. Kaje kawai, zanyi addu'a akan ka zan kuma yi tunani, sannan zan gayawa mahaifinka halin da kake ciki dan ya damu da ya sani, abinda duk muka yanke a kanka kuma dole shi zaka bi". Ya gyada kai cikin amincewa. Shi indai zata daina fushi da shi to kowanne hukunci ne ya yarda zai dauka. Washegari ya fahimci cewa ta gaya wa Abba abinda ya faru, dan sanda ya gaishe shi bayan sun dawo daga masallacin sallar asuba kin amsawa yayi, rana ta farko a rayuwarsa daya gaishe da mahaifinsa bai amsa masa ba. Wannan ya sa a ranar ko dakinsa bai koma ba anan falo ya kwanta anan falon yana jiran Abba ya shirya ya fito ya sake gwada sa'ar sa ko zai samu ya kula shi, yayi masa fada, kai ko dukansa ne ma ya yarda yayi in dai zasu daina fushi da shi. Yana nan kwance Mufida ta fito, yaji tazo tana taba wuyansa sannan ta koma suka dawo tare da Hafeez, yana ji suna ta maganganun su sannan Hafeez din ya tafi suka dawo tare da Abba. Yaji Mama tazo itama. Ya tashi zaune yana jin sanyin acn falon tayi masa yawa a jikinsa. Abba ya aika Mufida yace ta kawo masa abinci daga nan kuma sai ya sallame su ita da Hafeez. Gidado ya dauki cup din tean da aka ajiye a gabansa ya kai bakinsa amma bai kurba ba sai ya ajiye shi, pretending kamar yasha. Mama tace "dauki ka shanye" babu musu ya dauki kofin ya shaye tas duk da kona mishi baki da yake yi. Abba ne yayi magana yace "mamanka ta bani wani labari da ban taba tunanin jinsa ba. Tace min yarinyar da kake ta maganar za'a je nema maka auren ta, Safiyya, matar aure ce, haka ne" Gidado ya gyada kai, har lokacin zuciyarsa ta kasa sabawa da jin sunan Safiyya tare da kalmar matar aure a hade a sentence daya. Abba yace "to me zaka ce game da haka?" Gidado yayi gyaran murya yace "ban san haka bane ba. Sai last gani na da ita take gaya min hakan" mama tace "take gaya maka me?" Yace "tace min..... Tace she is married". Abba ya gyara zama "amma kai tun da kuke da ita ba ka taba gane cewa matar aure ba ce ba? Ta yaya? Kana me zata ninke ka a baibai tsahon lokaci baka gane ba? Wanne irin so kake mata da zai rufe maka ido from the obvious?" Gidado yace "Abba ban san ya zanyi bayani ku gane ba. Da ace kun santa zaku fi yarda da magana ta. Babu wani alamun aure a tare da ita. Ban taba zuwa gidan su ba ballantana in gane daga nan...." Mama tace "baka taba zuwa gidan su ba? All these while har ka yi gini ka saka ni hada kayan lefe amma baka taba zuwa gidan su ba?" Gidado ya dafe kansa "how foolish he might have looked a idon iyayensa, how foolish duk wanda yaje abinda ya faru zai dauke shi, amma kuna it is easy to judge idan har abin bai faru da mutum ba. Yace "Mama, Safiyya student ce a MD, a hostel take zaune, asalin iyayenta yan Kano ne, mahaifinta ba mazauni bane kusan ko da yaushe baya kasar. Duk sanda akayi hutu itama tana binshi whichever kasa yake a lokacin. A cewar ta kullum tana kokarin samun chance idan yazo gari ta kaini. Tace bata son kaini gurin kaninsa, wanda yake zaune a garin nan, tafi so in ganshi direct because of some family issues that she didn't mention. I didn't push sosai saboda baban bashi da lafiya, kusan ko da yaushe yana asibiti. She ......" Mama ta katse shi "wannan shine abinda ta gaya maka? To bara in gaya maka gaskiyar magana. Babu wani gurin babanta da take zuwa. My guess is gurin mijinta take zuwa in anyi hutun. Yana kasar waje ita kuma tana nan tana karatu, in anyi hutu kuma ta tafi gurinsa. In ta dawo kuma kai gaka. Ta jefi tsuntsu biyu da dutse daya". Gidado ya rufe idonsa yana tuno hotunan Safiyya da Daddyn ta, most of them a asibiti, ya girgiza kansa, baya son yayi tunanin abinda zuciyarsa take hasaso masa. Abba yace "to a karshe kuma ya akayi ka sani?" Ya bude idonsa yace "taje holiday kamar yadda ta saba, and she have been acting off for months, she came back tace tana son ganina, muka hadu a office dina, and she told me". Abba yace "and kai me kake tunani? Do you believe she is really married ko kuma she is lying tana so ne dai kawai ta rabu da kai?" Gidado yayi shiru because that was a million dollars question, bai san amsar ba, zai kuma iya bayar da komai dan yasan amsar. Cikin jikinta shi yake convincing dinsa akan cewa tana da aure din, amma kuma yanayin yadda tayi masa magana, da abubuwan da suka gudana kafin ranar, suna so su gaya masa cewa da akwai wata a kasa. Amma ya kasa fahimtar if those things are real ko kuma zuciyarsa da take cike da sonta ne take imagining dan ta bata kariya kamar yadda Ya Ameen ya gaya masa. Ya dago kai yana kallon Abba yace "I don't know Abba. I don't know what to think. I don't know what to believe " yayi shiru kuma sai yayi deciding ya gaya musu all he knows, idan akwai wanda zai taimaka masa kaf duniya to su ne. Sai ya kara da cewa "she is pregnant". Da sauri Mama tace "ita ta gaya maka?" Yace "gani nayi" tace "to wannan shine dalili, ta gaya maka gaskiyar ita matar aure ce saboda cikin jikinta. Shi ciki ai ba'a boye shi. Bata yi niyyar fada maka ba sai data tabbatar in bata fada ba ma zaka gani da idonka" Abba ya gyada kai cikin amincewa sannan yace "that will be all. Tashi kaje". Gidado ya mike, a ransa yana jin mix feelings. Na farko yana jin dadin iyayensa sun fahimce shi duk da dai har lokacin suna ganin da laifin sa a ciki, amma kuma yana jin babu dadin yadda suka dauki maganar, a gurinsu a yanzu babu halitta worst than Safiyya. Yana rufe kofa Abba ya juyo yana kallon Mama da bacin rai a fuskar sa yace "da ace nasan wacece yarinyar nan da ta mayar min da ɗa haka wallahi da sai na san waye uban ta a Nigeria" Mama tayi murmushin takaici tace "she can be traced, tunda daliba ce a MD, shima kansa Gidadon zai iya tracing danginta idan yayi niyya but to what end? Menene amfanin hakan? Allah zai saka masa kawai. What we should concentrate on a yanzu shine ganin ya dawo hayyacin sa". Ya gyara zamansa yace "abinda muka yi magana akai kawai shine" tayi ajjiyar zuciya tana girgiza kanta. "I don't know dear, what works for some might not work for others. Aure kuma is a life sentence. Bana son garin neman gira mu rasa ido". Ranar Gidado wuni yayi da wayarsa a hannun sa. Ya daina kiranta ya kuma daina tura mata messages amma wuni yayi yana kallon pictures da videos dinsu together, trying to figure out a ina hint din cewa tana da aure yake, trying to see beyond the obvious amma babu abinda ya gani sai soyayya, tsantsar soyayya. A karshe sa yaji kamar zuciyarsa zata fashe sai ya rufe wayar ya kuma rufe idonsa, a haka bacci ya dauke shi, cikin baccin ne yayi mafarki da Safiyya a tsaye a kofar office dinsa hannayenta biyu rike da cikinta, hawaye sharkaf a fuskar ta, ta mika masa hannu daya tana kiran sunan sa "Gidado please, I am sorry. Muhaammaaad...." Yayinda shi kuma ya saka hannu biyu ya hankada ta waje sannan ya rufe kofar. *Her* 🧕🏻 Kwanaki ukun nan sun wuce wa min very slowly. Bawai ina ganin rashin saurin kwanakin bane saboda kasancewarsu event-less, a'a, abubuwa ne da yawa suke faruwa not one after the other but all at the same time, abubuwan da suka cika min kwakwalwa ta har suka sa ka bata gane komai. Mommy ta saka ni a gaba da zancen auren Mukhtar, Mukhtar ya takura min da kokarin chanja min ra'ayi a kansa, Abdul ya cigaba da rokon na akan kar na zabe shi a matsayin miji, yayin da Daddy ya cigaba ta tambaya ta akan wanene zabina. Ni kuma a gurinta zancen aure shine least of my problems, babban matsalata shine lokaci yayi sauri yazo a raba ni da cikin jikina ko na samu freedom ɗin da zan ji daɗin jinyar Daddy, ko hakan zai bani damar rekindling relationship din mu. Sai dai kuma shi Daddy kullum maganar sa ita ce "bana son in tafi in barki a wannan yanayin Safiyya. So nake in gyara rayuwarki kafin in tafi in barki". And through all these, Gidado weight heavily in my heart.💜 Tunanin halin da yake ciki ya kara wa wuni na tsaho, mafarke mafarken sa kuma sun hana min bacci mai nauyi. A ranar da muka kwana biyar a garin ne na samu nayi dogon bacci da safe irin wanda na jima ban yi irin sa ba. Har Mommy ta tashi ta shirya ta tafi asibiti gurin Daddy ta barni bacci. San da na farka na danji dadin jikinta sosai, dan rashin baccin ma yana daya daga cikin abubuwan da suke toshe min tunanina. Na tashi nayi wanka na fito ina shirya wa ina tunanin yadda zan kai kaina asibitin tunda babu kuɗi a hannuna dan tunda muka zo ban yi chanjin kudi ba. Na zauna tana lissafe lissafen abun yi sai ga Aunty Hajjo ta shigo dakin. Na gaishe ta ta amsa sai naga ta samu guri ta zauna akan kujera, wannan ya saka ni feeling uncomfortable na sunkuyar da kaina, hoping cikina bai fito sosai ba. Sai naji ta fara magana "Safiyya dama ina ta so muyi magana da ke amma bana samun damar kasancewa da ke ke kadai, kuma maganar da zan yi miki da ke kadai nake son yinta. Na cigaba yin shiru ban ce komai ba, ta cigaba "Sa'adatu ta bani labarin abinda ya faru dake, ko kuma ince abinda ke kika gaya musu cewa ya faru da ke, dan a yadda na fahimta basu yarda da labarin ba nima kuma har yau labarin bai kwanta min a rai ba. Amma kuma na kasa ganin laifinki ballantana in zauna inyi miki fada ko inji na tsane ki ko inji ina kyamar ki. Hakan kuma yana da alaƙa da mahaifiyar ki. Allah ne shaida ta har ta rasu ina yi mata kallon yaruwa ta, in fact zan iya kiranta da role model dina dan nakan kwaikwaye ta akan abubuwa da yawa musamman harkar kula da miji da kuma nuna soyayya ga yaya. Ina iya tuno da sanda ta haife ki Safiyya, ina tuno irin tarin soyayyar ki da na gani a idonta a lokacin da naje yi mata barkan haihuwar ki. Ban yi mamakin yawan soyayyar ba saboda la'akari da nayi da jimawar da tayi tana neman haihuwa kafin ta same ki, na kuma kara fahimtar soyayyar sanda ta gaya min cewa likitoci sun tabbatar mata da cewa bayan ke ba zata sake haihuwa ba". Na saka hannu na goge hawayen da already ya fara bin fuskata, ta cigaba "ina kuma iya tuno lokacin rasuwar ta Safiyya, a gaba na aka yi mata sutura. Abinda nafi iya tunawa a lokacin shine sautin kukan ki. You were barely two years old. Kowa a gidan yayi kokarin ya rarrashe ki amma kina ta kuka kina kiran sunan da kike gaya mata 'ammi', abinda yafi tayar min da hankali a lokacin shine idan na kalle ta a kwance babu rai kuma na tuno da cewa ruhinta yana gurin kuma tana jin kukan ki amma bata da damar rarrashin ki duk kuwa da irin tarin soyayyar da take yi miki. It broke everyone's heart, musamman saboda yadda mutuwar tata ta kasance". Ta dakata tana kokarin daidaita muryarta, daga alama kuka ne yake kokarin kwace mata. Ta cigaba "wannan shine nightmare din kowacce uwa, and I couldn't help but think about dan karamin dana Abdul Hakim, na lissafa idan nice na mutu what will happened to him? Nayi kuma tunanin taki rayuwar ya zata kasance? Tun a lokacin na fahimci kina cikin jarabawa babba kuma kin rasa wani bangare na rayuwar ki da ba za'a iya replacing ba, amma kuma ban dauka gibin da aka samu zai kai ki ga matsayin da kike ciki a yanzu ba. I offered to take you, dan inyi kokarin cike wannan gibin, bayan ni mutane da yawa sunyi kokarin daukan ki amma babanki ya hana, yaki bawa kowa ke yace shi zai raini abarsa da kansa. Ina iya tuna wata rana da muka je tare da mai gidan nan dan mu duba halin da kuke ciki, muka tarar da shi ya goya ki da zani a bayansa kina tayi masa rigima, duk da ma'aikatan da suke gidan ku amma ba zai iya bawa kowa ke ba saboda girman soyayyar da yake yi miki". Ta sake yin shiru. Muka yi shiru baki daya sai sautin kuka na kadan kadan, ta cigaba "ban sani ba ko ma'anar labarin nan da nake baki tana fitowa, ban sani ba ko kina gane me nake nufi. But you are so precious Safiyya. You are far greater than yadda kika mayar da kanki. And you have enemies everywhere. Labaran da Sa'adatu ta bani akanki, ban san wanne ne gaskiya wannan ne akasin hakan ba. Ba zan kuma yi claiming nasan abinda yake zuciyar mutane ba. Ta gaya min cewa za'a hada auren ku ke da Mustapha idan kin haihu. Amma kuma mai gidan nan shima ya gaya min cewa suna son idan kun amince zasu hada auren ku ke da Abdul. Ban san wanne ne gaskiya ba. Amma ina son gaya miki har yanzu a raina ina da niyyar daukan ki in rike ki in dai har zan samu wannan damar. In kin zabi Abdul zan so hakan. In baki zabe shi ba kuma ina so ki san cewa I will be here for you whenever you need a mother". To gain access to the book contact 👇 0704 203 0419 Ta manhajar telegram ****. ****. ****. ****. ❤‍🩹*Safiyya*❤‍🩹 *By* *Maman Maama* *Episode Seven (7): The Good and the Bad Choices* A ranar ban je asibiti ba sai dare, na zauna a daki ni kadai with my thoughts thinking in nayi spending a day with my self zan iya yanke wa rayuwata shawara. Amma sai dai har daren ban zamu na yanke din ba, sai dai kamar kullum, ranar ma nayi adduoi sosai akan Allah ya dube ni ya kawo haske a rayuwata. A ranar ne kuma na fahimci dalilin da yasa na kasa samun zabi a cikin samarin da Daddy ya lissafa min, dalilin kuwa shine Gidado. In dai har zan cigaba da yiwa aure hangen da muka yi masa ni da Gidado to kuwa sai dai in Daddy yayi zuciya ya zabar min da kansa dan ba zan iya zabar kowa ba. Amma kuma sai naji cewa ina ma dai zaiyi hakan? Da ya dauke min wani babban nauyi a kaina, da ya cire min guilty feeling da nake ji a raina a duk lokacin da nayi tunanin zabar wani ba a matsayin miji wanda ba Gidado ba. In dai har ba Mustapha zai zabar min ba to bani da matsala. Abdul na san idan na zabe shi bani da matsala da iyayen sa, dan maganar da Aunty Hajjo tayi min yau ta kuma tabbatar min da kaunar da take yi min, sannan Uncle Sufyan kuma zan iya kiran shi da second father dina dan duk duniya Daddy bashi da aminin da ya amince wa kamarsa. Amma kuma Abdul yana da wadda yake so kamar yadda ya gaya min baki da baki. Kuma experience dina da soyayya ya saka na fahimci cewa kowace ce ma yana kaunar ta sosai. Duk sanda nayi tunanin zabarta sai in hasaso cewa Muhammad ne sanda muke tare muke tsara rayuwar mu tare sai iyayensa su haɗa shi aure da wata saboda selfish reason ɗin su. It would have destroyed our lives. And I do not want to destroy someone else's life dan ni in samu farin ciki. Mukhtar on the other hand yana so na, dan yana daga cikin few mazan da suka taba physically confessing soyayyar su gare ni. Mukhtar ya jima yana so na, soyayyar da ni a gurina na fara daukan ta obsession har ta fara irritating dina kuma tasa yayi loosing girmansa na yaya na a idona. In na aure shi at least zan zauna da wanda yake sona ko da kuwa ni bana son nasa amma kuma iyayensa fa? Uncle Ahmad shine dan uwa daya tilo da Daddy yake dashi a duniya, komai namu a hannunsa yake tunda Daddy ya fara rashin lafiya more than five years ago, sai dai kuma tun ina karama nake samun problem dashi da matarsa dan suna min kallon spoilt girl da bata da tarbiyya, problem din namu kuma ya karu a shekarun bayan nan, sannan ya zama worst bayan bayyanar ciki na. Zasu karbi aure na dole, and zasu iya farinciki ma da hakan, sai dai hakan baya nufin zamu daidaita dasu ko kuma zasu kasa goranta min ko nan gaba. And Mustapha, in na zabi Mustapha rayuwa ta will be a disaster, dan ban taba tsanar mutum ba kamar yadda na tsane shi and there is no way da zan iya neman aljanna ta a karkashin sa. Sai dai kuma Mommy tayi min dukkan halaccin da mutun yake nema daga wani mutum, ba ita bama, danginta sunyi wa Ammi na halaccin da duk mutum yake bukata daga mutum, musamman wanda ba dan uwansa ba. Duk da dai nasan a yanzu ba wai dan soyayya ko halacci ne yasa suke son hadin auren mu ba, but I do not care about that, da ace zan iya 'managing' zama da Mustapha, da tabbas shi zan zaba. Kamar kullum tunda muka zo garin, sai na samu kaina da yin adduoin istikhara da neman Allah ya bayyana min zabin sa a fili ya kuma tsayar min da zuciya ta akan zabin nasa. Kwana biyu bayan nan, da dare ina kwance kamar kullum ina kallon ceiling na kasa bacci, a lokacin babu abinda nake nema irin abinda zaiyi taking ɗina away from my thoughts. Na tuno da twins sai naji guilty feeling dan tun da muka rabu a Nigeria bamu sake yin magana ba. Na dauko wayata na kunna ina lissafin time ɗin Nigeria amma sai na lura dare yayi sosai a can, maybe ma sunyi bacci. Amma sai nayi tunanin hawa online in duba su. Sai dai ina kunna data din wata ta naji gaba na ya fadi, sai a lokacin na tuna cewa banyi blocking Gidado from Whatsapp ba kuma na tabbatar ya neme ni ta can. Na bude Whatsapp din na tsaya ina kallon yadda messages din suke shigowa a guje, har suka gama suka tsaya. And like I  expected, akwai da yawa daga Muhammad. Na kasa bude sakon nasa saboda tsoron abinda zan gani, zuciya ta ba zata iya daukan wasu karin bakaken maganganu daga gare shi ba. Idan kuma rokona yake ba zata iya jure cigaba da butulce wa soyayyar sa ba. Sai dai kuma a lokacin na sani har cikin zuciya ta cewa rabuwa da shi shine abu mafi alkhairi da zan yi masa a rayuwa. I couldn't stain his clean life with my dirty and tragic life. Idan ma gaya masa gaskiyar abinda ya faru da ni ba zai taɓa rabuwa da ni ba, iyayensa kuma ba zasu taɓa amincewa ya aure ni ba, nawa iyayen kuma zasu kama shi da zargin yana da hannu a cikin abinda ya sameni. So in whatever way shine a ruwa. And I rather drown myself then get him wet. Wannan shine zurfin soyayyar da nake yi masa. Message dinsa na karshe kawai na karanta. "please Piya, I just want to know why". Na rufe ido na ina jin damshin hawaye na a akan kuncina na danne conversation din mu sannan na danna delete, knowing fully well that nayi deleting dukkan chats dina da shi. Sai da nayi deleting dan kar in karanta sannan na bude nayi masa reply, duk da ban san complete abin da yace ba. Na gama rubutawa na tura masa sannan nayi blocking dinsa from my Whatsapp chats. Na saka hannu na biyu na rufe fuska ta, nayi kuka na mai isa ta sannan na bude fuskar na goge hawaye na na cigaba da scrolling through the chats ko zan samu abinda zai dan kwantar min da hankali na ko yayane. A lokacin nayi karo da messages din Yaya Mukhtar. Na bude, duk kuwa da cewa a raina na san shima wani karin bakin cikin zai kara saka wa zuciyata. Maybe ma gorin cikin jikina zai yi min. Amma kuma sai na tarar hakuri yake bani "Fiyya ban san da wanne kalaman zanyi amfani ba in baki hakuri, daga ni har Abba na san mun bata miki, a lokacin da ya kamata mu zama mune masu share miki hawaye sai kuma muka zama mune masu saka ki kuka" "Kin san halin Abba, it was just his temper talking not him, and he loves you shi yasa yake takaicin halin da kike ciki. Please kiyi hakuri ki yafe masa" "And ni kuma. You of all people know what my problem is, kishi ne yake damuna ba wani abu ba. I know I shouldn't have said zan taimaka miki in aure ki because like you said, ni ne nake neman taimako a wajen ki, cos nine nake tsananin son ki. And it would be my pleasure to marry you ko da kuwa nakasa ce ta same ki. And whatever kika haifa, zai zama ɗan mu ne ni da ke babu wanda zai san abinda ya faru. This I promise you with my life" "Please Safiyya in kinga messages ɗina ki kira ni. Ko ki kira Abba if you are still angry with me. We are worried about you. Bama samunki a waya and Daddy baya daukan kiran mu daga ni har Abba". And the last message "Ki gaya wa Mustapha, duk sanda ya shigo Nigeria sai yayi regretting. Na rantse sai na chanja masa kamanni". Na ajjiye wayar tare da yin ajjiyar zuciya. Na rufe ido na ina jujjuya kalaman Mukhtar a raina sannan kuma ina tunanin abinda ya haɗa shi da Mustapha. Dama can basu fiya jituwa ba tun muna yara. Shi Mukhtar muguwar zuciya ce da shi irin ta Daddy da Abba, shi kuma Mustapha silent killer ne, da wahala kaga bacin ransa. Ga ladabi da biyayya a gurin manya. Da haka ya siye zuciyar Daddy. But only I know who he really is. Da safe na tashi nayi wanka ina shiryawa kenan yayin da Mommy ita kuma ta shiga wanka, sai naji wayata tana kara, sai dana dan tsorata dan na manta da cewa na kunna ta. Sai kuma na fara murna ina saka ran twins ne suka kira ni, amma dana dauki wayar sai naga Uncle Ahmad ne. Nayi ajjiyar zuciya na zauna a bakin gado sannan na dauka tare da sallama. "Abba ina kwana" Ya amsa "lafiya lau Safiyya. Tunda kuka tafi sai yau kika kunna waya ne?" Nace "jiya da dare na kunna" yace "saboda menene? Saboda kima ganin babu wanda ya damu da ke da zai neme ki a waya? Ke kin kashe waya shi kuma Yaya na kira wayarsa yafi sau cikin charbi amma ba'a barinsa ya dauka. Na san kuma matar sa tare da wannan tsinannen yaron Mustapha. Har Mustapha ne ni zan kira Yaya ya dauka yace min wai bacci yake yi yace kar a dame shi. Ni fa?" Na dafe kaina saboda already har naji ya fara yi min ciwo da safiyar nan. Nace "kayi hakuri Abba, in sha Allah yau in naje asibitin sai in kira ka in bashi wayar kuyi magana" Ya danyi shiru "eh ina son magana dashi sosai, ke ma kuma ina son magana da ke. Ina son in baki hakuri akan abinda ya faru ranar nan. Na fahimci shine dalilin da yasa Yaya yake fushi da ni. Ni ba dan wani abu nayi miki fada ba sai dan ina ganin na isa inyi miki fadan ne. Uwa daya uba daya ne suka haife mu ni da Adam. Ke a matsayin ƴa kike a waje na. Ban dauka dan nayi miki fada Yaya zai dauki fushi dani har ya daina yi min magana ba. Ban dauka dan nayi miki fada zaki je ki kai kara ta gurin sa ba". Na girgiza kai kamar yana kallona nace "Abba wallahi ban kai karar ka ba. Ba da niyyar kai karar ka nayi masa magana ba....." Ya katse ni "I know Safiyya. I understand. Wannan matar tasa ce zata hada. She have brainwashed you two ba kwajin maganar kowa sai tata. Ba kwa daukan kowa da mutunci sai ita da yayanta. Ni na san ita ce ta saka ki kike ta bina akan wai sai na dauki kuɗin ki na siya wa ƴaƴan ta motoci " na sake girgiza kaina "Uncle ba ita ta fada min ba, ni ce .." yace "ba zaki gane ba Safiyya. Ba zaki gane ba. Kamar yadda nace, she have brainwashed you". Nayi shiru ban ce komai ba a lokacin da Mommy ta fito daga toilet tana kokarin shiryawa. Yace "in kinje asibitin ki gwada hada ni da Yaya ko Allah zai sa ya sauko muyi magana. I am not feeling comfortable with you two tare da su. Hankali na ba'a kwance yake ba" na gyada kai ina kallon Mommy da ta tsaya da abinda take yi tana kallona. Nace "insha Allah, zan yi masa magana in naje. Insha Allah, komai zai dawo dai dai" yace "good. Idan kinyi haka kin kyauta mana gabakidaya. Dan duk duniya baku da wadanda suka fi mu. Muma kuma duk duniya bamu da wanda wadanda suka fi ku". Na cure wayar daga kunne na na ajiye ta a gefe, Mommy da har lokacin take kallo na tace "waye?" Nace "Uncle Ahmad ne " ta bata rai "Ahmad ba shi da kunya wallahi. Me kuma yake ce miki bayan irin wulakancin da yayi miki a cikin mutane? Me kuma zai ce miki?" Nayi shiru da farko, amma ganin alamar amsa take jira sai nace "yana so yayi magana da Daddy ne. Yace baya samun sa a waya" tayi tsaki, "to ba dole yaki daukar wayarsa ba. Ta yaya za'a yi mutum ya cire maka zani a kasuwa sannan kuma yazo gida yace zai daura maka? Na dauka ma maganar wannan marar kunyar yaron zai yi miki. Wannan yaron ko maye ne shi to sai dai yaci kansa wallahi dan kin fi karfin sa". Haka ta cigaba da maganganun ta ni dai har na gama cin abinci na na kammala shiryawa ta. Sannan ita na taci muka fito muka yi wa Aunty Hajjo sallama muka tafi. Tun a mota ta bawa Mustapha labarin nayi waya sa Uncle Ahmad, ina jinsa yana bata hakuri wai kar ta sawa kanta damuwa shine maganin daga Uncle Ahmad ɗin har Mukhtar. Ni dai bance musu komai ba duk kuwa da kokarin saka ni da suke yi a cikin maganar. Muna zuwa asibitin muka tarar an yi discharging Daddy. Sun gama bashi duk wani treatment ɗin da zasu bashi babu kuma sauran wani abu da zasu iya yi masa. Wannan shine dama mostly abinda ake yi masa a duk asibitocin da muke zuwa. Sai dai suke mana muje gida in wani symptom din ya sake bayyana ko wani ya zama worst sai mu dawo. Amma cutar sa babu magani. Har yanzu ba'a samu maganin ta ba. Sai a lokacin nake jin ashe Daddy ya saka an kama mana apartment din da zamu zauna kafin sanda za'a yi min aiki. Plan dinsa dama shine in an sallame shi mu samu gida mu zauna baki daya har sai na rabu da cikin jikina sannan zamu koma Nigeria. Damuwarsa kuma har lokacin ita ce bai san yadda zaiyi da abinda za a ciro daga cikin nawa ba and definitely baya son mu zauna tare da abinda zan haifa. Bai san already na samo solution to that ba. Sai da na bari ya tura Mustapha ya karbo sauran magungunan da akayi masa prescribing, Mommy kuma ta fita gurin nurses zata yi making some inquiries sannan na jawo kujera kusa da shi kaina a kasa nace "Daddy, Uncle Ahmad yace yana ta neman ka a waya baya samun ka". Ya bata rai "ina ganin kiran nasa ai. Me zai ce min? Ban dauka yana daga cikin wadanda zasu goranta min a duniya idan wata kaddara ta fada min ba". Na girgiza kaina "ba gori yayi min ba Daddy. Faɗa yayi min" ya dauke kansa yace "haka yace miki kenan? Da ke yake so yayi amfani ya dawo gare ni kenan. Na riga na yanke hukunci, in Allah ya sauke ki lafiya mun koma Nigeria zan karbe komai namu da yake hannunsa. In kinyi aure lokacin your husband can take care of everything for us" naji hawaye yana taruwa a ido na. Na sake cewa "Daddy, duk duniya fa bamu da wanda ya fishi. Blood is thicker than water" yayi dan karamin murmushi "haka yace miki?" Na sunkuyar da kaina ina wasa da yatsuna ban ce komai ba. A lokacin na kammala yanke hukunci na. Na dago kai nace "Daddy na yanke shawara, akan zabin da ka bani" Ya juyo yana kallona amma bai ce komai ba. Nace "na zaɓi Mukhtar. Mukhtar zan aura". ****.    ****.    ****.    ****.    ****.    ****.     A bangaren Gidado ya dan samu sauki, ba wai saukin zafin da zuciyarsa take yi masa ba sai dai yanzu iyayensa sun dan sauko duk da dai basu dawo yadda suke da ba. Still suna blaming dinsa for being negligent, for being vulnerable, for letting a small girl toyed with his emotions. Two days after zaman da suka yi dashi ne suka sake kiran sa suka gaya masa hukuncin da suka yanke a kansa. "Ba za'a fasa haɗa bikin ka da na Mufida ba kamar yadda muka yi niyya. You are going to get married" Ya dago kai yana kallon su, feeling confused. Abba yace "ka duba cikin yan'uwa, tun daga yalleman zuwa Kano zuwa Abuja, ka fitar da mata, cos you are getting married in the next two months". Ya juya yana kallon Mama, hoping ko zai samu wani hope daga gare ta, amma sai ya ga taki yarda su haɗa ido kuma a duk sanin da yayi wa iyayensa duk maganar da daya yayi to dayan ma ita yake goyon baya. Abba ya cigaba da magana "believe us Muhammad, it is going to be the best thing that has ever happened to you. Duk kan mu mun san bayan abinda yarinyar can tayi maka, it will take time for you to heal and trust women again, and from our experience, the best feeling ever is to fall in love after marriage. And it is the most easiest. To make things easier for you, mun baka zabi. Choose wadda duk kake ganin zaka iya so later on, mu kuma zamu yi wa iyayen ta magana and if bata da wanda take so, shikenan" Gidado ya sake juyawa ya kalli Mama, ta fahimci yana bukatar ta, tayi ajjiyar zuciya tace "It is going to be okay Gidado. Wannan shine decision ɗin mu. Kuma sai da mukayi dogon tunani kafin mu yanke shi. And ba zamu taɓa yin abinda zai cutar da kai ba. Kuma in kayi biyayya a gare mu ba zaka taba nadama ba" Ya sunkuyar da kansa kasa a zuciyarsa yana hoping ina ma dai shi mace ne, ina ma dai zai iya zama yanzu a gaban iyayensa yayi ta rusa kuka har sai sunce sun janye hukuncin da suka yanke. Jin yayi shiru ya saka Mama ta sake cewa "ina fatan yarinyar nan bata saka dafinta a zuciyar ka har level ɗin da zai kai ka ga bujirewa maganar mu ba". Ya dago kai yana jin zazzaɓi yana neman rufe shi yace "ɗan Allah Abba, ina neman alfarmar a bani lokaci in yi...." Mama tace "dawa zaka yi shawarar? Da ita?" Ya girgiza kai da sauri "ba da kowa zanyi shawara ba Mama. Zan dan tattauna maganar ne da zuciya ta. I just want to have some time to think " Mama ta sake cewa "babu komai a zuciyar ka Muhammad sai soyayyar waccan matar. I have seen the kind of messages da kake tura mata. I have read yadda kake begging dinta kamar wadda take rike da ranka a hannunta" ta karasa maganar cikin dacin murya and he can literally feel irin tsanar da take yi wa Safiyya. Abba yace "tomorrow. You have until tomorrow". Ya maimaita "tomorrow. Okay" sai kuma ya mike da sauri ya fita waje. Sai da yaje wajen sannan ya tuna babu abinda zaiyi a wajen. Babu gurin wanda zai je wanda zai iya hana iyayensa abinda suka yi niyyar yi. His grandparents will definitely back his parents up musamman in suka ji abinda ya faru, his auntie and uncles too, and then marriage proposals will start flying from alla angles. Babu irin tunanin da bai zo kansa ba. If only he can see Piya maybe he can convince her leave her husband tazo su yiwa iyayensa karyar cewa maganar da ma ba haka bace ba misunderstanding aka samu, and then get married. Sai kuma ya dafe kansa yana tunanin ta yadda aka yi ma har yayi irin wannan tunanin. Lallai soyayya babu abinda bata sakawa dan a lokacin abubuwa kadan ne ba zai iya aikatawa ba dan ya samu Safiyya. Love yana kokarin turning the good boy he is into a bad boy. Ya dauko wayarsa and for the nth time ya kira number ɗin Safiyya. "Common Piya" ya fada yana jin ransa yana kara baci. How can you love and hate someone so fiercely at the same time? Ya buɗe motarsa ya shiga, ya kalli side ɗin da take zama hoping to see her appear ko da na second daya ne. Sai kuma ya dauke kansa ya tayar da motar ya fita daga gidan a guje. Sai dai kuma shi kansa bai san inda zaije ba. Bai san abinda zaiyi ba. MD University ya dosa, the first time da ya shiga tun ranar da suka rabu da Safiyya. Kamar yadda yayi tsammani babu mutane sosai a cikin makarantar saboda dalibai suna hutu, but yana hoping wanda yaje nema yana nan. Ko baya nan ma zai nemo shi duk inda yake. File din Safiyya yake so a dauko masa, address din ta yake so a bashi, kano zai je a yau yaga babanta or her husband, whatever the case maybe. In yaje sai ayi duk wacce za'a yi. Ya dauko wayarsa da niyyar kiran wanda zai karbi informations din a hannun sa, sai dai garin neman number ɗin ya lura da notification din da ya shigo masa wanda bai ma lura da sanda ya shigo ba. A message from Piya 💝. Wani faduwar gaba yaji, and then cikin rawar hannu ya bude message ɗin ya karanta. "Dear Muhammad. I am very sorry for what happened. Please find it in your heart to forgive me ko ba yanzu ba. But for now, please stop trying to contact me. And don't look for me dan Allah. I have made a mistake naci amanar mijina with you. Now I have repented bana son in kara aikata kuskuren da na aikata a baya". "Mijina bai san abinda nayi ba and I want to keep it that way. Bana son in breaking heart dinsa because I love him so much. Please, do not break up ny happy home. You will soon get over me and move on as I have gotten over you". "Dan Allah, for the sake of the love that you have for me. Don't let my husband know". Ya maimaita jaranta message din ya kai sau uku, sai ya rufe shi ya sake budewa hoping it will disappear amma still yana nan. Wayar ta zame daga hannun sa ta fada kan kafarsa, yayinda shi kuma ya saka hannu biyu ya rungume kirjinsa dan ji yake yi kamar zuciyar sa zata fito. Sai kuma ya kifa kansa akan stirring motar. Ya jima a haka kafin da dago, ya kunna motar ya jata a guje ya fita kamar yadda ya shigo a guje. Ya jima yana zagaya gari ba tare da yasan inda zashi ba, har sai da yaga rana tana neman faduwa sannan ya doshi gida, zuwa lokacin already ya yanke decision ɗin sa. Yana shiga gida ya samu Mama a zaune a falo suna hira da Mufida. Suka bishi da kallon mamaki da kuma tausayin yanayin sa. Ya zauna daga can gefe sannan yace "Mama na yanke shawara akan maganar da kuka yi min dazu" ta gyara zama tana kallon sa tace "ba sai gobe ba?" Yace "babu bukatar hakan. Babu bukatar jiran gobe. Babu abinda zan chanja tsakanin yau da gobe. Na amince da maganar auren da kuka yi. Allah ya sa albarka. Amma ina neman alfarma guda uku. Na farko ina so ku zaba min da kanku, bana jin zan iya zaba da kaina. Na biyu ina son dan Allah duk wadda zaku zaba ya zamanto ta amince da kanta ba takura mata aka yi ba, zan so kuma ace tana sona ne dama, at least that will make things easier. Na uku, Please, kar ku zaba daga cikin yan'uwa, nafi son bare". Mama ta bata rai tace "why not? Me yasa bayan muna da yammata masu hankali da tarbiyya da ilimi, wadanda kuma muka yarda da su muka yarda da asalin su sai mu tsallake su mu tafi nema a wani wajen? Ta yaya gida bai koshi ba zamu bawa daji?" Ya girgiza kai "Mama, there is a chance that this may not work. And I value zumuncin mu da yan'uwan mu a lot that bana son in zama sanadin samun sabani tsakanin mu. Please ku nema min bare yadda ko ba'a dace ba effects din ba zai zama da illa sosai ba". Mama tace "to ni yanzu Muhammad ta ina zan fara nema maka mata a cikin dan lokacin da muke da shi. Yaushe aka samu matar har aka yi neman auren da bincike da komai?" Mufida da take kwance tana jin su ta mike zaune tace "Mama in kin yarda akwai friends ɗina. Akwai wallahi da yawa da sun sha yi min maganar suna son sa ni kuma ban taba yi mishi magana ba saboda nasan ba kula su zai yi ba. Idan kin yarda sai in bashi pictures din su ya zaba, duk yayan manyan mutane ne, babu kuma wacce iyayen ta ba zasu iya aurar da ita a cikin wata biyu ba" Ya sake cewa yana kallon Mufida"I don't want to choose" shi a cikin zuciyar sa gani yake yi kamar idan ya zaba yace ya zabi wance kamar yaci amanar Safiyya ne. Mama ta kalle shi kawai tayi ajjiyar zuciya, bata jin zata daina tsinewa yarinyar nan. Mufida ta sake cewa "to bara in nuna wa Mama ta zaba maka ita, ta san most of them already, har iyayen su ma ta sani" ta fada tana dauko wayarta. Sai kuma ta tsaya kamar wadda ta tuno wani abu tace "oh my God. Oh my God" Mama da Gidado duk suka juyo suna kallon ta. Gidado ya juya mata hannu alamar tambaya, ta koma ta zauna sosai tace "akwai wata yarinya, kusan shekara guda kenan tana yi min naci akan in haɗa ta da kai" ya bata rai yace "wacece?" Tace "I don't know her. Kawai a one of the northern blogs na Instagram naga ta tura irin hide my ID post din nan da hoton ka, wai tana cigiyar ka ko kuma wanda ya sanka, wai tana son ka. I commented cewa kai yayana ne amma already kana da wadda kake so. She followed me into my DM tana ta yi min nacin in bata ko da number din ka ne ta gwada sa'ar ta, na gaya mata ba zaka kula ta ba taki yarda, I gave her your number dan ta tabbatar da kanta. She later told me ta kira ka baka dauka ba, she sent you a message kace mata tayi hakuri kana da wacce kake so and you blocked her " Gidado yayi shiru yana tunani, ba zai iya gane wacece ba because a lot of that scenario has happened, yammata da yawa sukan gwada sa'ar su a kansa and all the times ya kan basu hakuri and then blocked them dan baya son ciwon kai. Mufida ta cigaba "tun lokacin bata hakura ba. Har daina daukan wayarta nayi na kuma daina replying messages dinta amma bata daina kira na da kuma turo min sako ba. She even sent me some of her pictures wai in nuna maka. And she is beautiful gaskiya. Daga alama kuma yar manyan mutane ne ce. Let me see it I still have the pictures" ta fada tana bude wayarta Gidado ya mike tsaye "unknown girl. With no link or connection to the family. She is perfect. Call her and ask her if she is still interested. And if she can get married in the next two months. Then get her information. Duk abinda ta gaya miki sai ki gaya wa Mama" ya juya ya fara tafiya zuwa bangaren sa. Mama ta daga murya tace "haka kawai kake tunanin zamu aura maka yarinyar da ba'a san asalin ta ba, daga haduwa a social media?" Ya juyo yace "in akayi bincike za'a samo asalin ta. In asalin baiyi muku ba sai Mufida ta samo wata unknown din" Yana jin ta tana cigaba da magana amma baya fahimtar me take cewa. Tafiya kawai yake yi yana jin zuciyarsa tana breaking into thousand pieces. To gain access to the book contact 👇 0704 203 0419 Ta manhajar telegram ****.    ****.    ****.    ****.    ****.    ****.    *❤‍🩹Safiyya❤‍🩹* *Episode Eight: The Acceptance* *Her🧕🏻* Ya dago kai yana kallona da fuskar mamaki, nayi sauri na mayar da nawa idanuwan kasa tare da rike numfashi na dan na san abinda zai biyo baya "Mukhtar?" Ya tambaya cikin mamaki "Mukhtar fa kika ce? Are they blackmailing you? Cewa suka yi in baki aure shi ba zasu gaya wa duniya abinda kika aikata?" Na fara girgiza kaina amma ban ce komai ba, na fahimci dama tunda yana jin zafin uncle Ahmad dole zaiyi retaliating akan zabin nawa duk kuwa da cewa shi ne da kansa ya lissafa min har da Mukhtar din a cikin options dina. Amma ban dauka zai dauki zafi haka ba. Cikin fada ya sake tambaya ta "baki bani amsa ba, are they threatening you?" Mommy ta shigo da takardu a hannun ta, ta tsaya tana kallon sa sannan ta kalle ni cikin alamar tambaya, ban ce komai ba ta mayar da tambayar ta kansa. Cikin dacin rai ya nuna ni yace "wai Mukhtar. Wai Mukhtar zata aura" Ta zame ta zauna akan kujera tana dafe kirjin ta "na shiga uku ni Sa'adatu. I thought you hated that guy. You said it yourself several times." A hankali nace "I never hate him, he is my cousin. I just don't love him. Kuma har yanzu bana son sa. Bana masa soyayya irin ta aure amma duk kunsan cewa shi yana so na and at least that is something". Mommy ta nuna waje da hannun ta "and so does Mustapha. In dai soyayya ce Mustapha yafi Mukhtar son ki. Yafi su son mahaifin ki da yanuwanki. Yafi kowa dace wa da auren ki. Da kika ce ba zaki aure shi ba na dauka Abdul zaki aura knowing fully well cewa ba kya son auren Mukhtar. Ashe zaki iya zaben wanda kika ambata xewa ba kya so akan Mustapha? Gwara kikai kanki inda na tabbatar ba son Allah da Annabi suke miki ba akan ki zauna a inda za'a fi ko ina mutunta ki?.........." Ta cigaba da fada muryarta har shakewa take yi yayin da ni kuma na saka hannayena biyu na toshe kunnuwana tare da rintse ido na. Da bi ar da nake yi a duk sanda ake kokarin chanja min ra'ayi akan abinda na riga na yanke shawara akan sa. Sai da naji na daina jin muryarta sannan na dube ido na ina kallon Daddy shima yana kallo na idonsa cike da mixed emotions. "Wani abun Ahmad ya gaya miki a waya sanda ya kira ki wanda ya saka kika yanke wannan hukuncin?" Ya tambaya muryarsa da sanyi akan dazu. Na girgiza kaina tare da goge hawayen da bansan sanda na fara zubar da su ba nace "bani da wani zabin ne Daddy. Ba zan iya auren Mustapha ba. Abdul baya sona. Bazan iya auren wanda nake so ba. Bani da zabi Daddy" ya gyara zamansa "waye wanda kike so ɗin? Ki gaya min waye shi ni kuma zan aura miki shi in dai har na bincike shi naga ya chanchanta. Zan aura masa ke kuma in mayar masa da ɗan shi. Waye shi?" Na mike tsaye "ba ɗan shi bane ba Daddy. Ba ɗan shi bane ba. Ban san waye uban ɗan ciki na ba amma ba nashi bane ba. Ba zan makala masa laifin da nake da tabbas ɗin ba shi ya aikata ba. Ba zan bata tsakanin sa da iyayensa in kuma bata masa suna a gari ba" Ya dafa kujera ya mike shima, bacin rai yana sake dawowa fuskarsa "kina da shaidar cewa ba shi bane ba kenan? In har ba ki san waye ba zai iya zama shi ɗin ne kenan. Wato da ki bata tsakanin sa da iyayensa gwara ke kin bata da naki iyayen ko? Da ki bata masa suna gwara kin bata naki sunan kin zauna da tabo na har abada a tare da ke, gwara kin auri wanda ba kya so wanda shima kuma ba son Allah da Annabi yake yi miki ba, gwara kin zauna da ɗan da in ya girma ya tambaye ki waye ubansa baki da amsar da zaki bashi ko? Gwara kinyi watsi tare da fatali da duk sacrifices da mahaifiyar ki tayi domin ki, domin ki samu kyakkyawar rayuwa ko? She gave you everything, she gave her very life for you". Ya karasa cikin daga murya. Nace "but I never ask for it. I never ask for any of this. I wish she didn't do what she did. I wish she let me die" Na juya da sauri na fita daga dakin ina kuka, ina jiyo muryar sa yana kwalla min kira "Safiyya, come back here" ban waiga ba ballantana in koma. A waje na samu kujera na zauna na kife kaina ina cigaba da rusa kuka na. Har cikin zuciya ta a lokacin fata nake ina ma dai Ammi bata yi duk abinda tayi ba. Da yanzu ban samu kaina a cikin wannan matsalar ba dan ko shakka babu abinda tayi din shine silar shiga ta halin da nake ciki. Ina cikin kukan naji an zauna a kusa da ni. Ban dago kai ba thinking wani stranger din ne. Sai da naji an ambaci sunana "Fiyya?" Na dago kai da sauri na kalli side ɗin, duk da kuwa na gane muryar wanda yayi min maganar tun kafin in kalle shi. "Fiyya what happened. Me ya saka ki kuka har haka?" Na saka hannu biyu ina goge fuskata duk kuwa da cewa ba tsayawa hawayen suke yi ba. "Fada muka yi da Daddy " na fada cikin sheshshekar kuka. Ya gyada kai "yes. Ina tsaye ai kika wuce ni baki ganni ba. Amma Fiyya mai zai kai ki fada da Daddy a halin da yake ciki? A halin da kike ciki? Me ya haɗa ku" ya fada yana miko min hanky. Na karba tare da kokarin tsayar da kuka na. Ya sake cewa "talk to me.... At least let it out of your chest " na girgiza kaina "ba zaka gane ba Abdul" ya gyara zaman sa "Try me. Wata kila zan gane har ma in baki shawara. And just so you know, Mama ta faɗa min komai a kanki. She told me about your situation. She said she wants me to marry you" na juyo ina kallon sa na fahimci da gaske yake abinda ya fada, but I still noticed the sadness in his eyes. Na danyi murmushin tausayin rayuwata nace "Allah sarki Aunty Hajjo. Lallai ta cika kawai kwarai. Ammi would be very proud of her" yayi ajjiyar zuciya "yeah. I guess so" nace "but I will not marry you Abdul" ya jiyo da mamaki, nace "na riga na yanke shawara, Mukhtar zan aura. Hakan shine sanadin fadan mu da Daddy. And I am not changing my mind. Tunda ai shi ya bani options ɗin kuma na zaba" ya danyi shiru yana tunani sannan yace "but why him? Me yasa kika zabe shi? Why not me?" Nace "I am not sure why. Kawai dai nayi addu'a and naji a raina shi ya kamata in dauka. And personally, na farko I believe yana so na da gaske. Cos ya jima yana ta bina da maganar soyayya ina ƙi, nacin da yake yi min da kuma goyan bayan sa da uncle Ahmad ya fara yi shi ya saka na bar gidan su da zama a Abuja na koma hostel. Shi kuma Daddy ya goya min baya yace ba za'a yi min dole ba. Wannan shine silar fara rikici tsakanin Daddy da uncle. And secondly, ina ganin auren mu zai gyara tsakanin Daddy da dan uwansa. He needs him a yanzu. Su biyu iyayensu suka haifa, bashi da kowa sama da shi" Abdul ya gyada kai cikin fahimta "at least in yana son ki auren will be much easier on you" na ce "yes. And kai kuma abinda yasa ban zabe ka ba shine, akwai wani wanda nake so, shine dalili na biyu da yasa muka yi faɗa da Daddy. I love him so much shima haka. So ina imagining yadda muke dashi idan da ace wannan kaddarar bata fado min ba, ace kawai a gidan su a yanke shawarar cewa ba zai aure ni ba wata yar abokin babansa wadda tayi cikin shege zai aura. It would have destroyed him and me. I don't want destroy you and your girlfriend" Yayi murmushi, I can see his love for her a idonsa, yace "thank you. I really appreciate what you did. Kin yiwa soyayya halacci. And ina ganin zabin ki shine dai dai. Amma pardon me for asking, ya labarin wancan guy din da kike so ɗin? What happened to him? Ya san halin da kike ciki?" Na yi shiru ina kallon yatsun hannuna, ban so nayi mishi magana akan Muhammad ba dan ko tunawa da Muhammad bana son zuciya ta tayi saboda irin damuwar da nake shiga idan na tuno shi, nace "I can't even imagine halin da yake ciki. Soyayya ta bata yi masa halacci ba. It destroyed him". Waya ta tayi kara. Na dauko ta daga cikin jaka ga mamaki na sai naga number ɗin Mukhtar. Na kife ta akan cinyata tare da rufe fuskata da hannayena. Na fahimci Daddy ya hakura kenan saboda fushin da yaga nayi, har ya kira uncle Ahmad ya gaya masa zabina shi kuma har ya gaya wa dan na sa. Or not. Ni na zaba da kaina amma yanzu a raina bana jin zuciya ta zata karbi zabin nawa, da zata so Mukhtar da tini ta so shi. "Ana kiran wayarki" Abdul ya fada yana kallo na. Na bude fuskata tare da daukan wayar na amsa kiran "hello?" Daga daya bangaren aka amsa "Hello Habibty" *Him👳🏻* Bai tsaya ba har saida ya shiga dakinsa sannan ya rufe kofa ya jingina bayan sa da jikin kofar tare da rufe idonsa yana jera numfashi kamar wanda yayi gudu. Sai kuma ya bude idon ya fara magana da kansa. "Yes. Wannan shawarar tayi. I will get married and I will forget about her, and fall in love with my wife and have kids like every other person. Babu wani abun da zai chanja. There is nothing special about her. She is just like every other girl". Ya kwanta akan gado ƙafafuwan sa a kasa yana kallon ceiling, a ran sa yana jera yadda zai cigaba da tsara rayuwar sa step by step. Farko, da farkon fari kafin ya fara komai zai fara da cire Safiyya daga ransa dan in dai har tana yawo a cikin zuciyarsa babu abinda zai iya aikatawa. And to forget about her sai ya fara raba kansa da duk wani abu da yake tuna masa da ita. Ya mike zaune yana karewa dakin kallo, bata taba shiga dakin na sa ba amma kusan a kowanne angle na dakin akwai memory dinta, ko dai wani abu da ta bashi ko kuma abinda suka yi maganar sa ko ta saka ya siya da kansa. Yayi tsaki tare da yanke shawarar cewa dakin zai bari gabaki daya ya koma wani. Nan da two months ma gidan zai bari gabaki daya ya koma nasa gidan shi da matarsa. Sai dai kuma shima wancan gida babu abinda babu memories din Safiyya a ciki. Ya sake yin wani tsakin. One step at a time. Dole zai manta da ita amma one step at a time, tunda dama ai ba lokaci daya ta shiga rayuwar sa tayi zurfi haka ba. Ya dauko wayarsa ya fara da step din farko. Numbers dinta ya nemo duk yayi blocking sannan yayi deleting. Sai kuma ya nemo dukkan messages dinsu da chats dinsu duk ya haɗa kansu ya goge. Ya ajiye wayar tare da rufe fuskarsa da hannayensa, a ransa yana jinjinawa kansa. "You can do it" ya fada wa kansa. Ya bude fuskar tare da sake daukan wayar yana jujjuya ta. Tare ya siya musu wayar iri daya shi da ita. Too many memories. Ko dai ya ajiye wayar kawai ya chanja wata? Amma in ya ajiye ma zuciyarsa zata iya rinjayar sa wata rana ya dauko ya kunna ya duba pictures da videos dinta da suke fal a ciki. To completely forget about her dole sai ya goge wadannan ma. Ya bude wayar da sauri ya fara nemo pictures da videos din da duk take ciki yana marking, yayi marking da yawa har yazo kan wani video da bai tabbatar nata be ko ba nata bane ba sai ya bude shi dan ya tabbatar. And then he saw her face, as clear as a lokacin ne yake daukan ta video ɗin. Kuka take yi shabe shabe da hawaye a cikin video ɗin tana bubbuga kafa a kasa irin yadda shagwababbun yara suke yi. Yana jin muryarsa a ciki yana dariya "wai da gaske kukan kike yi? La ila! Mutane fa suna kallon ki" ta turo baki tare da tabe shi, sak yar yaye, "ni wallahi ba zan daina kukan ba sai ka siya min ice cream". Ya kife screen din wayar akan gadon tare da kife fuskarsa akan wayar yana jin zuciyarsa kamar zata fado kan gadon. Ya tuna ranar da ya dauki video din. Ranar sun haɗu a school da safe tace masa mura take yi, daya tambaye ta abinda ya saka ta murar sai ta bashi labarin cewa ruwan sama aka yi da assuba ita kuma ta shiga ciki tayi wanka. A ranar da ya kira ta da dare sai yaji muryarta har ta dashe saboda mugun kamu da murar tayi mata. Babu shiri ya dauki mota ya tafi hostel ɗin su ya dauke ta da niyyar kai ta pharmacy ya siya mata maganin mura. ****. ****. ****. ****. ****. ****. A hanya ya lura da yadda take ta takurewa a cikin hijab dinta. Ya kalle ta yana lura da yadda idonta yayi ja. Yayi tsaki "pharmacy din nan ba zai yi ba Piya, asibiti zamu tafi, naga alamar ma harda zazzaɓi a jikin ki" ta bude ido tare da saurin sakin jikinta. "babu zazzaɓi fa. Allah babu. Mura ce kawai ita ma yar kadan" ta karasa maganar tare da yin atishawa. Ya harare ta "yar kadan? Wannan murar ce yar kaɗan ɗin? Asibiti zan kaiki. Let me call our doctor inji in da yake. Ya kamata a duba ki sosai" ya fada yana daukan wayarsa. Tayi saurin karbe wayar daga hannunsa. "Please kar ka kira shi. Ni na warke ma" yayi slowing down yana kare mata kallo, sai kuma yayi dariya "yanzu na gane matsalar ki. Tsoron allura kike yi" ta tura baki "babu wani tsoron allura, kawai ni lafiya ta kalau ne shi yasa" yayi kokarin juya steering motar "okay tunda ba kya tsoron allura muje asibitin kawai" ta saki wayar tare da saurin rike hannunsa "na shiga uku. Dan Allah kar ka kai ni asibiti" ya cigaba da yi mata dariya yana kallon yadda take zazzare ido kamar wadda za'a yanka "wannan tsoron asibitin naki Piya, duk ranar da zaki haihu bansan yadda za'a yi ba". Sai kuma taji kunyar sa ta rufe ido. Sun jima suna rigima a mota, daga karshe pharmacy ɗin ma cewa tayi ba zata je ba sai da kyar sannan ta yarda amma da sharadin cewa ba zata shiga ba shi kadai zai shiga ya karbo mata magani ya fito. Haka da suka je ya barta a mota ya shiga shi kadai, sai dai ga mamakin sa ya na tsaye a gurin cashier sai ganin ta yayi ta shigo gurin ta shiga bangaren da suke siyar da kayan ciye ciye, jimawa kadan sai gata da manyan robobin ice cream guda biyu, ta ajiye a gaban cashier tana kallon sa tace "one for you and one for me" ya girgiza kansa "no, no, no. Babu yadda za'a yi kina wannan murar ki sha ice cream. I won't allow it ". Ta kwabe fuska "ni Allah sai na sha. Ai naji wani doctor yace ba shan abu mai sanyi ne yake kawo mura ba, mura viral infection ce, kuma ......" Yace "oh! Viral infection? Shi yasa naga kin shiga ruwan sama kin fara mura? Ko virus ɗin a cikin ruwan saman yake?" Ya karasa maganar yana daukan robobin da niyyar mayarwa. Ta bishi da sauri "ni dai kazo ka siya min. Allah in baka siya ba ba zan fita daga shagon nan ba zama zan yi in yi ta kuka" ya juyo yana kallon ta da mamaki. "kuka? Really? To kiyi ɗin mu gani. Ni kuma I will record you and show our kids" Ai kuwa ranar yaga rigima. Tun da ya hadu da ita dama ya fahimci shagwababbiya ce amma bai san irin girman shagwabar tata ba sai ranar. A dole sai da ya sai ice cream din nan har da karin chocolates, mai shagon yana ta yi musu dariya. Suna shiga mota ta darko roba daya ta buɗe ta fara sha. Ya zauna kawai yana binta da kallo. Tayi atishawa ta kara diban wani ice cream din ta sha. Ta juyo tayi masa gwalo. Yayi ajjiyar zuciya. "This has to change. My no has to mean no and my yes yes. Dole ki ringa jin magana ta in nayi miki ita" ta juyo tare da saluting dinsa irin yadda sojoji suke yi tace "Yes Sir!". ****. ****. ****. ****. ****. *** "Hamma. Hamma Gidado. Yaya Gidado". Kamar cikin mafarki yaji muryar Mufida tana kiran sunan sa, duk kuwa da yasan cewa ba bacci yake yi ba sai dai yayi matukar nisa a cikin tunanin sa. Ya dago fuskarsa ya sauke jajayen idanun sa akan Mufida da take tsaye a bakin kofar dakinsa da waya a hannun ta. Ta dan tsorata kadan sai kuma yaga tayi sauri ta rufe mic din wayar hannunta da daya hannun, tace "uhm dama waya ce aka ce in kawo maka. Amma bara in ce mata kawai you are busy zaka kira ta an jima" ya tashi ya zauna sosai ya a shafa goshin sa yace "who is it?" Tace "yarinyar da muka yi maganar ta dazu ce. Mama tace in kira ta dan a samu information ɗin ta. Shine na kira ta ita kuma tace in kawo maka" ya sauke ajiyar zuciya, with all his heart yana son yayi rejecting kiran ya fadi wani excuse ɗin amma kuma yasan bashi da wani excuse ɗin fadi. Ya san shi yayi choosing wannan option ɗin amma accepting ɗin choice din nasa yana kokarin ya zamar masa nightmare. Ya mika mata hannu. "Give me the phone " ta bude mic din sannan ta mika masa. Yana karba ta juya ta fita. Ya zauna yana kallon timer din kiran tana cigaba da reading, sai da yayi ajjiyar zuciya sannan ya saka ta a kunnen sa, "Assalamu alaikum " yace, daga daya barin yaji ance "Ameen wa alaikumus salam Habibi" yayi shiru bai ce komai ba, sai ta sake cewa "Mufida ce ta kira ni. She told me the most wonderful news ever. Ina so ka sani cewa tunda nake a rayuwata ba'a taba gaya min labari mai daɗin wannan ba" ya sake yin shiru sai kuma ya fahimci shi take jira yayi magana sai yace "okay. I am glad you feel that way. But uhmm, this is just a procedure, I don't want to give you any false hope. Maganar aure ce and dole sai an gudanar da bincike. Am sure she told you abin yazo ne lokaci daya. I have been giving two months in fito da mata. So I am going to need some information from you and if the background check comes back okay then that's when we will celebrate" ta dan yi dariya kadan "it is going to come out okay. Everything will insha Allah be okay. And I am going to make you the happiest insha Allah. And ." Ya katse ta "Okay. Uhmm. First, menene sunan ki? Ni sunana Muhammad Lawan Muhammad. Ana ce min Gidado" tace "I know. I know a lot about you. Ni sunana Safina. Safina Ibrahim" To gain access to the book contact 👇 0704 203 0419 Ta manhajar telegram *❤‍🩹 Safiyya*❤‍🩹 *Episode Nine: Safina* *Him 👳🏻* "Safina?" Ya maimaita da mamaki a muryarsa, ta ɗan yi shiru sannan tace "eh. Uhmm, ko ka san wata Safina Ibrahim ne?" Sai daya ɗan ajiye wayar akan cinyar sa ya yi tsakin jin haushin kansa, why must he relate everything to Safiyya ne wai? Kawai daga jin Safina sai ya dangantata da yar uwar Safiyya? Ya sake daukan wayar yace "uhm. Sorry Please. Akwai wata Safina da na sani ne, in fact ita ce the only Safina dana sani. Though ita ma sunan ta kawai na sani. Yar uwarta ce wacce na sani" ya kuma ajiye wayar tare da dafe kansa "damn it. Must I talk about her?" Ya sake daukan wayar sai kuma yayi shiru gudun kar ya cigaba da maganar Safiyya. Tace "hello? Ina jin ka. I guess you know the sister very well ko? I want to know. Tell me" yace "there is nothing to tell. Just tell me about your self, like, yar wanbe gari ce ke? Kano?" Sai kuma ya sake jin haushin kansa. Tace "noo, not Kano. Ni yar Katsina ce" yace "really? But hausarki doesn't sound like hausar yan Katsina" ta danyi dariya "I get that a lot from people that don't know me. Bana son dialect ɗin so ina kokarin cire shi, musamman saboda duk makarantu na ba anan na yi su ba" yace "okay. Uhmm, I think that's all I need from you now. Please ki bawa Mufida number ɗin wani haka da za'a yi magana da shi, like your uncle or something. My family will contact them and do all the necessary stuff. That's all for now" Tace "all? I thought zaka ce zaka zo muga juna ko?" Ya girgiza kai "no. My family will meet yours and do all the necessary things. I will see you idan komai ya daidaita. But now I am very busy" ya ji bacin rai a muryar ta "amma idan da zaka zo ɗin zanji dadi sosai, you have no idea how much I waiting and prayed for this. And ko suma su Abba zasu fi bawa abin muhimmanci idan suka ga kazo gurina" yace "no, zasu fi bada muhimmanci idan suka ga elders dina sun zo gurin so. I am sorry but I cannot come" tace "okay. Then how are we suppose to know and understand each other?" Yace "I will call you when I need more informations" tace "how can you call me bayan baka da number ta?" Yace "ki karbi tawa a hannun Mufida ki kira ni" tace "how can I call you bayan kayi blocking number ta " ya rufe idonsa yana jin kansa yana sarawa yace "okay. I will collect your number and unblock you. Shikenan?" Tayi murmushin da yaji sautinsa a cikin wayar "shikenan, naji dadi sosai. You have......" Ya katse kiran ya jefar da wayar akan gadon tare da dafe goshin sa da hannu biyu. Zuciyar sa tafasa take yi, kokari take sai ta lissafo masa aibun yarinyar da suka gama waya da ita. Safina she said. But why? Upon all the names na mata a duniya why did she have to be Safina, bayan kuma Safinan ba wani suna ne irin wanda ya cika gari sosai ba. Yana ta so ya goge duk wani abinda zai ke tuna masa da Safiyya and then all of a sudden yarinyar da yace zai aura tana da sunan step sister din Safiyya. Safiyya used to talked a lot about her, ta kan ce "she is more like a sister to me, tare muka taso, a daki daya, a hannun uwa daya da uba daya". Lokuta da dama ya kanji su suna waya, and daga yadda suke hira suna dariya ya fahimci akwai shakuwa da kaunar juna  sosai a tsakanin su. Ya mike tsaye tare da daukan wayar ya fita. A parlor ya tarar da Mufida da Mama suna zaune suna hira, ya ajiye wa Mufida wayar a gabanta yace "ki samo wata. Na fasa wannan ɗin" Mama ta mike tsaye tana kallon sa amma sai ya dauke kai yayi hanyar fita, ta riko hannun sa ya dawo baya, tace "kai Muhammadu, dago kai ka kalle ni" ya kasa kallon nata amma sai ya samu guri ya zauna a gabanta "akan menene kace ka fasa" yayi shiru yana jujjuya kai still idonsa a kasa. Ta kara karfin muryarta "a bayanan da ta baka ne wani abu bai yi maka ba? Ko wata magana mummuna ta gaya maka wadda za'a iya fasa aure saboda ita?" Ya dago kai "Maaama! Ke ma fa ba sanin yarinyar nan kika yi ba kamar yadda ni ma ban santa ba. It wouldn't hurt anyone idan aka ce an fasa ɗin tunda dama ko maganar ba'a fara ba" ta koma ta zauna tace "I don't care much about her Gidado, in fact she lost some things a gurina tunda har ta iya fitowa social media tana neman namiji. But still that earned her something saboda hakan ya nuna tabbas tana son ka. And I do care about you a lot. I don't like hanyar da rayuwar ka take dauka akan mace. Now tell me, me yasa kace ka fasa auren ta?" Sai da ya dan yi jim sannan yace "sunan ta Safina" Mama tace "and?" Yace "sunan yar uwar Safiyya ne" Sai da ya fadi maganar sannan ya fahimci wautar da yayi, bai kalle ta ba amma a jikinsa yana jin mugun kallon da take bin sa da shi. Yayi shiru yana jiran yaji ta rufe shi da fada amma sai kuma yaji ta sake tambayar sa "Okay, ka tambaye ta kenan ta kuma tabbatar maka da cewa ita ɗin ce?" Ya girgiza kai "ba ita ba ce ba. Ita wannan yar Katsina ce su kuma yan Kano ne". Ya cigaba da jiran fada, amma sai yaji tayi ajjiyar zuciya tace "Gidado, Allah ya kwato min kai a hannun waccan matar. Allah kuma ya saka min abinda tayi min. Tashi kaje tun kafin kasa zuciya ta ta buga. Ba za'a fasa ɗin ba. In an samo wata kuma cewa zaka yi a cikin yan uwanta akwai mai suna Safiyya. Ko in anyi auren kazo kace kai ka fasa saboda suna da makociya Safiyya. Allah ya shirye ka". Ya mike ya fita, feeling silly. Ita Mama ba zata gane ba, shi a ganinsa wannan is enough reason to call the wedding off, dan shi duk abinda zai ke tuna masa da Safiyya gudun sa yake yi, shi kadai yasan abinda yake ji a ran sa. Sai after two days sannan ya karbi number ɗin daga gurin Mufida, shima Mufidan ce ta dame shi da maganar cewa Safina tana tayi mata maganar, da ya karbi number ɗin ma bai kira ba har sai bayan wasu kwana biyun da Mama ta yi masa magana "idan baka kira yarinyar nan ba wai ta yaya zaku samu fahimtar juna ne? Musamman considering baku da isasshen lokaci? Idan kuma da gaske ba zaka auren ta ba dan sunan yar uwar waccan mayaudariyar ne da ita to sai ka fada mana muji in yaso mu nemo maka wata a dangi, in ma kuma auren ne ba zaka yi ba gabaki daya shima sai ka fada musan cewa bamu isa mu saka ka ba". Da suka zo dinner da daddare ma sai da Abba yayi masa maganar" ka kira yarinyar can kuwa? Ya kuke ciki? Yaushe zaka je ka ganta?" Ya juya yana kallon Mama wacce ta tabe baki bata ce komai ba. Ya sunkuyar da kansa yace "zanje Abba, ina dan so in samu lokaci ne" Abba yace "lokaci? Lokaci kuwa ai shine babban abinda baka dashi. Shekara nawa muka baka? You have only two months my friend, ko ka je ku daidaita da wannan ɗin ko kuma wallahi kaji na rantse sai ranar daurin auren ka zaka san dawa aka daura. Stupid" Ya cigaba da jujjuya cokali a cikin abincin, sama sama yana jin Abba suna cigaba da maganar da Mama, tana gaya masa cewa yarinyar ta turo number din uncle dinta, Abba kuma yana nuna cewa ba za'a yi contacting dinsu ba har sai sun tabbatar cewa Gidado is fully committed dan kar suje suyi magana biyu. Gidado ya mike tsaye, Mufida ta rike hannunsa "hamma ba ka ci abincin ba" muryarta cike da damuwa, murya can ciki yace "am not hungry" sannan ya wuce ciki. Dakinsa ya shige zauna a kan kujera, staring into nothing, babu abinda yake gani idan ya rufe idonsa sai hoton Safiyya da ciki, cikin wani, waye wanin amma? Waye mijin Safiyya. Ya tuno da maganar da Mama ta fada sanda ya gaya musu cewa Safiyya tana da aure, she said wanda Safiyya take cewa Daddyn ta ne, wanda take zuwa kasar waje gurin sa, shine mijinta. Ya san pictures din Daddy, tabbas ya haife ta ko ma wadda ta fita, amma kuma yana da kuɗi, yana da bala'in kuɗi, yammata kuma a wannan zamanin sukan auri sa'an kakansu ma saboda kuɗi. But Safiyya doesn't look like a gold digger, she never sounds like a gold digger. He just couldn't picture her and that man as husband and wife. Yayi kokarin kawar da tunanin daga ransa dan gudun illata zuciyarsa. Ya fara mayar da tunanin kan issue at hand, issue ɗin wannan yarinyar Safina. He regretted cewa ya zabe ta. Bai san dalili ba but he just doesn't like her tun kafin ya ganta, kuma in zai gaya wa kansa gaskiya ya san aibunta kawai shine dan sunanta Safina, which is not fair to her. She couldn't possibly be Safinar Safiyya, like is not that cruel is it? Ya tashi ya koma kan study table dinsa ya bude laptop dinsa, in da akwai inda zai samu aibun yarinyar to tabbas a social media ne, anan zai samu abinda zai nuna wa iyayen sa yadda zasu yarda a fasa auren ba tare da sun jingina fasawar da Safiyya ba. Ya bude goggle sannan ya tsaya yana tuno sunan da ta gaya masa "Safina Ibrahim" amma da ya fara typing sunan sai ya samu kansa da typing "Safiyya Adam Muhammad" "damn it" ya faɗa a fili, subconsciously yana son yin bincike ne akan Safiyya. He saw a lot of results da basu da dangantaka da Safiyyan da yake nema, he saw her Instagram account with the few posts she made most of which na abinci ne. Yayi murmushi "acici" sai kuma yayi sauri ya fita ya cigaba da binciken sa amma bai ga wani abu da zai yi linking dinta da aure ba ko kuma ya yi directing dinsa to mijinta. Ya koma search engine din sannan yayi typing "Alhaji Adam Muhammad" a cikin results din ya ga wanda yake nema, ya gane hotonsa from the pictures dinsa da yake gani a wayar Safiyya. Anan yaga biography dinsa da aka yi publishing, ya shiga idanunsa suna searching abinda ya ke nema, anyi rubutun ne akan a lot of achievements dinsa da irin tarin arzikin da yake da shi da kamfanonin da ya mallaka, he was even listed a cikin manyan masu kuɗin Nigeria. Yayi ta wucewa har yazo kan abinda yake nema, a cikin biography ɗin nasa anyi listing spouses dinsa, sunan farko shine "Safiya" sai kuma "Sa'adatu". Ya kife fuskar laptop din da karfin da shi kansa ya san ta lalace. Ya mike sannan yayi jifa da kujerar da yake kai a zaune. Sai kuma ya zauna akan gado tare da rintse idanunsa. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya furta a hankali. How much more pain does he have to endure. How much more pain can his heart take. When will this end? Ya koma da baya ya kwanta yana kallon sama. Ba san me zai yi tunani ba, bai san me zaiyi ba, bai kuma san tsahon lokacin da ya dauka a haka ba. Daga baya ya koma ya zauna sannan ya jawo wayarsa ya bude number ɗin Safina sannan ya kira. Ba'a jima ba aka dauka "alhamdulillah. Allah shine abin godiya. Tunda nayi sallah nake zaune akan sallaya ina gaya wa Allah bukatu na akan ka. Gashi kuma ban tashi ba sai da Allah ya amsa min ya juyo min da hankalinka gare ni". Yace "listen Safina. If we are going to do this, then we are going to do it the right way. I am really heartbroken right now. I am in love, deeply in love with someone else, someone that I cannot have. Wannan ne dalilin da yasa aka matsa min akan auren nan. Bana son shiga hakkin duk wacce zan aura, so I want you to know what you are getting yourself into. Babu rufa rufa. I will marry you saboda ina son in farantawa iyayena rai, but chances are I might never love you, or anyone else. Me kika ce? Kin amince?" Sai da tayi shiru na wasu lokuta, daga dukkan alamu maganar ta sa ta dake ta sosai. Sannan tace "I don't know what tomorrow will present to us. Babu wanda ya san gobe. Yanzu na sani, abinda na sani a yanzu kuma shine ina son ka, ina matukar son ka. Na kuma san cewa in na aure ka zan baka dukkanin kulawar da miji yake bukata daga gurin matarsa. Na kuma san cewa ita zuciya an halicce ta ne a bisa son mai kyautata mata, so chances are high that you will love me. Maybe one day in ka tuna da waccan har sai kaji haushin kan ka ma kana tunanin what made you love her. So yes, I am going to take my chances. Na amince, a bisa alkawari guda daya, cewa you will try your best akan sauke dukkan nauyin da addini zai gindaya a tsakanin mu. Kuma ba zaka wulakanta ko goranta min soyayya ta ba". A cikin sati biyu aka gama bincike, kuma a iyakacin abinda aka samu babu wani abu da zai hana aure a musulunci. An gano asalin ta, an kuma yi bincike akan tarbiyyar ta. Daga nan uncles din Gidado, Uncle Habib, Faruk da kuma mijin aunty dinsa Maimunatu suka je har Katsina suka nema masa aurenta, a take kuma kanin mahaifin ta ya basu auren ta. Aka saka rana sati shida yadda zai zo dai dai dana Mufida kamar yadda iyayen angon suka nema. Daga nan kuma sai aka cigaba da gudanar da shirye shirye a duk bangarorin biyu. ****.     ****.    ****.    ****.    ****     **** *Her🧕🏻* Sama sama muka yi magana da Mukhtar, nayi kuma iyakacin kokari na na ganin cewa banyi masa wulakanci ba tunda yanzu ni ce da kaina na neme shi, sai dai kuma na katse maganar da cewa akwai abinda nake yi amma zan kira shi idan na gama. Na mike ba tare da na kalli Abdul ba nace "zan shiga ciki, thank you for...... For listening" ya mike shima "amma da zaki ji shawara ta kar ki koma ciki yanzu, ki dan basu space ki bari su huce tukunna. Ke ma ki huce" na tsaya amma ban ce komai ba, ya mike shima "let me take you home" na juyo "ba gidan ku zamu koma ba, mun samu gurin zama for the time being" yace "I know, amma zaku dauko kayan ku daga gidan na mu ai ko? Let me take you there sai ki debo muku kayan ku". Ban cigaba da musu ba saboda nima bana son komawa gurin Mommy da Daddy a lokacin. Muka shiga motar sa muna tafiya a hankali na jingina kaina a jikin window tare da rufe idona, hoping ina ma dai mutum yana iya hana kansa tunani? Na jima a haka sannan naji yace "Fiyya. Wata tambaya nake son yi miki. Ban san yadda zaki dauke ta ba. Please kar ki ji haushi bana nufin komai sai alkhairi. I will only ask the question dan naga yau mun samu fahimtar juna. You can choose not to answer it if you will" na dago kaina tare da bude ido nace "ina jin ka" kamar ba zai yi magana ba sai kuma yace "akan wannan da kika gaya min kina so, shine baban babyn ki?" Nayi sauri na kalle shi. Ya daga hannu "am sorry. In ba kya son amsawa forget I ever asked it" na juya kaina na cigaba da kallon gefe, sai da na jima a haka sannan nace "ba nashi ba ne ba. But kasan wani abu? Sometimes in akayi min irin wannan tambayar I wish cewa nashi ɗin ne. It would have made everything easier for both of us. Da sai dai Daddy yayi fadan shi ya gama, maybe ma ranshi ba zai kai yanzu baci ba, shima nashi iyayen in suka ji ransu ya baci suyi fada, but duk kan su ba zasu iya disowning din mu ba saboda suna son mu, at the end zasu nema mana mafita ne, which would be to get us married, muyi aure mu rike babyn mu, and live happily ever after. The end". Ban jima a gidan Aunty Hajjo ba na gama hada mana kayan mu, tare muka tafi da ita zuwa gidan da Daddy ya kama mana muka danyi gyare gyare kafin su Daddy su zo. Ita ta kira Mommy ta gaya mata muna tare. Da furnitures da komai a gidan dan haka kayan sakawar mu kadai muka shiga dashi, sai yan few abubuwan da naga babu nayi mana order za'a kawo mana har gida. Tunda su Daddy suka zo daga shi har Mommy babu wanda ya kula ni, Mustapha ne ya kai shi dakin da aka shirya domin shi sannan ya shirya masa kayan sa da duk abubuwan bukatar sa. Ni dai da naga na gama abinda zan yi kuma babu wanda yake yi min magana sai na wuce na tafi dakin da yake a matsayin nawa nayi kwanciya ta. Sai dare sannan Mommy ta shigo. "Ki tashi ki ci abinci" tace min. Na mike zaune kawai bance komai ba, sai ta zauna a bakin gadon tana kallo na tace "Safiyya wannan ita ce magana ta karshe da zanyi miki a kan auren ki. Duk da cewa yanzun ma ba wai zanyi miki maganar bane ba dan ina saka ran zaki chanja ra'ayin ki ba, zanyi ne kawai dan in nuna miki irin yadda rai na ya baci akan maganar. Ba kiyi halacci ba Safiyya, daga ke har mahaifinki ba kuyi min halacci ba wallahi. Ai na san kin san komai, duk da dai ni ban taba zama na gaya miki ba dan bana son ki dauki maganar kamar gori amma na san duniya ta gaya miki, kin san irin halaccin da nayi wa Safiya, ni na dauke ta a matsayin yar aiki sannan na mayar da ita mutum, duk abinda Safiya ta zama a rayuwar ta wallahi ni ce sila. Haka kema kuma, tun kina zanin goyon ki na dauke ki na rike tamkar nina haife ki amma yanzu ni ce abin gudu a gurin ki. Shi kuma mahaifin ki ya goya miki baya as always. Babatun sa da fadansa na banza ne in dai a kanki ne baya iya juya ki sai abinda kike so shi kikeyi. Ba'a saka ki ba'a hana ki. Kuma kowa ya dan dalilin da yasa kika samu kanki a halin da kike ciki kenan. Amma har yanzu bai dauki darasi ba. Da wasu iyayen ne ma har wanni zaɓi za'a baki? Bayan abinda kika aikata kuma ace sai an baki zabin mijin da zaki aura? Da wasu iyayen ne da tuni baki fadi uban shegen cikin ki ba? Kuma na san abinda zakuyi nan gaba, tunanin ku yanzu shine in an haifi shegen a dauko shi a kawo min ace in rike shi saboda ni ce karkatacciyar kuka mai daɗin hawa ko?. To wallahi kar ku sake ku doso ni da shi ma. Na fada miki wannan ne dan ki sani, zan cigaba da sauke nauyin ku da Allah ya dora min daga ke har mahaifin ki amma na daina going extra for any of you. Na daina saka bukatun ki a saman na ƴaƴan da na haifa da cikina. Tunda kun tabbatar min da cewa bani na haife ki ba. Kun tabbatar min da matsayina na matar uba kuma na dauki matsayin nawa". Har ta gama bance komai ba, tana gamawa ta mike ta bar dakin ni ma kuma na koma na kwanta na cigaba da kallon ceiling. Shin da gaske na yiwa Mommy butulci? Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar min, har tsahon sati uku, Mommy ta janye jikinta sosai daga gare ni haka Mustapha ko magana baya yi min, nima kuma dama ba so nake yayi min maganar ba, Daddy ma kamar ko da yaushe sama sama yake min magana in dai har munyi doguwar magana to faɗa ne. Kullum dakina ne gurin zama na akan sallaya ta, anan nake sallah ta, anan nake kuka na, anan kuma nake bacci na. Na cigaba da zuwa asibiti ganin likita, na tabbatar masa da ra'ayi na na bayar da ɗan cikina for a closed adoption idan na haife shi. A ranar da muka cika sati uku a gidan ne bayan na tashi da safe na fita da niyyar gaishe da Daddy da Mommy kamar yadda na saba kullum, ina fita parlor sai naga Daddy shi kadai a zaune akan electric wheelchair dinsa da kofin tea a hannunsa. Na karasa na gaishe shi ina lura da bacin ran da yake bayyane a fuskarsa, a raina har na fara lissafin ko nayi wani sabon laifin ne. Amma sai naji bai yi min faɗa ba bayan amsa gaisuwa ta da yayi. Na mike ina dube dube. Na shiga kitchen na fito na kuma shiga dakin su Daddy na fito amma ban ga Mommy ba. Daddy naji yace "she is gone" na juyo ina kallon sa. "Gone? Gone where?" Yana kallona shima yace "home. Sun tafi Nigeria ita da Mustapha. Wai auren Safina za'a yi. Safina ce wai aka bayar da ita ba tare da ko faɗa min anyi ba. Suka shirya tafiyar su ba tare da sun gaya min ba. Sai da safe kawai suka fito da akwati wai Nigeria zasu tafi bikin Safina. She said wai na nuna mata cewa ke ba yar ta bace ba shi yasa ita ma ta nuna min cewa Safina ba yata ba ce ba". Not edited. Forgive the typos please. To gain access to the book contact 👇 0704 203 0419 Ta manhajar telegram *❤‍🩹 Safiyya ❤‍🩹* *By* *Maman Maama* *Episode Ten: Soul Mates* Free Episode Na zame na zauna akan kujera cikin mamaki "aure Daddy? Safina ce zata yi aure amma ni ban sani ba? How? Why? To wa zata aura ma?" Yace "ba ta gaya miki ba kema? Kuna magana kuma?" Na gyada kai. Na san mun dan samu falling out da Safina kwanan bayan nan, and must issue din mu na san laifi na ne saboda yadda na zama very rude to her a watannin nan, hakan kuma yan ada dangantaka da mood dina da kullum bashi da kyau. Amma ban dauka har zata iya yin aure ba tare da na sani ba. And ko shekaran jiya munyi chats da ita. We even talked about magana ta da Mukhtar. Nace "muna magana Daddy, amma ko alama bata nuna min ba. Wa zata aura kuma?" Ya girgiza kai "ban sani ba, they didn't tell me and I didn't ask tunda sun nuna ban isa ba. Ba ki san samarin ta ba?" Na yi shiru ina tunani "Safina bata da saurayi. Ni dai ban san wani saurayi da take kulawa ba" na tuno da yadda takan takan yi min kallon zautacciya duk sanda muke tare in taji muna waya da Gidado. Tace soyayya irritating dinta take yi. "How can she do that?" Na fada a fili. Daddy yace " ba laifin ta bane ba. Am sure Sa'adatu ce zata hana ta fada dan tana so ta bata min rai, tana so ta nuna min nata ikon" nayi ajjiyar zuciya "babu komai Daddy kar ranka ya baci, we don't need them. We can do this alone. Su je suyi mata aure, Allah ya sanya alkhairi. All we have to do now is hire someone, kamar a nurse haka that can take care of you, sai kuma mu nemi a house keeper da zata ke shigowa ko da twice a week ne tana kula da gidan, and I can drive, duk inda zamuje zan iya kai mu" yayi shiru yana kallo na da murmushi a fuskarsa, sai kuma ya girgiza kai "Safiyya kenan. Kin dauka damuwa ta kenan? Wanda zai kula da ni? Damuwa ta shine wanda zai kula da ke idan babu ni. I don't want any enmity between you and them saboda ko babu dangantaka ta jini su yan'uwanki ne, ba na son in babu ni ki rasa wanda zaki yi turning to. Ke ba yanuwan uwa ne da ke ba, and in akayi auren ki da Mukhtar yan uwans sun zama na mijin ki, ke ba older siblings ne da ke ba. In na mutu ya zaki yi?" Na koma na zauna ina jin wani kadaici yana lullube ni. Tamkar Ni kadai ce a duniya. Ya cigaba "shi yasa da farko naso auren ki da Mustapha, at least it will strengthen the bond between you kuma ba zasu yi spilling secrets dinki ba. And you will still have Ahmad a matsayin uba ba matsayin uban miji ba, zai kuma saka ido ya ga cewa basu cuce ki ba. But now, now I don't know what to do sai dai addu'ar Allah ya kara ara min lokaci" Na gyara zama "amma Daddy ba ka ganin wannan tafiyar da suka yi suka barmu ta nuna true intentions ɗin su? Ta nuna cewa ba soyayyar Allah da Annabi suke yi mana ba?" Yace "Allah kadai ya san abinda yake ran bayin sa. I don't know abinda ke ran Mustapha, amma na san Sa'adatu is not cruel, stupid but not cruel, she is just scared that she will loose everything" nayi kokarin gane maganar amma ban fahimta ba sai na chanja magana "I still have the twins" yayi murmushi "yes, and they are the more reasons why dole in gyara tsakanin ku kafin in bar duniya, if not, you will loose them too, dan babu yadda za'a yi su juya wa uwarsu baya saboda ke". Daga nan na tashi na shiga kitchen na hada wa kaina smoothie na zauna ina sha ina jimamin abinda ya faru, har lokacin na kasa yarda wai da gaske Safina ce zata yi aure amma wai daga ni har Daddy bamu sani ba, kuma naji a raina babu abinda nake son sani irin wanda zata aura ɗin, waye shi? Yaushe suka hadu? A ina suka haɗu? Nayi kokarin mantawa da abin in fuskanci abinda yake gaba na amma sai naji na kasa. Na koma daki na dauko waya ta na kira Hassan, dole ai na san twins zasu sani musamman tunda suna Nigeria. Hussein ne ya sauka da murna a muryarsa ya gaishe ni "yaya da ke za'a taho? Kun fasa zama acan din? Mun dauka ai cewa kuka yi sai kin haihu zaku dawo Nigeria" nace "no Hussein ba dani za'a taho ba, kun yi waya da Mommy kenan?" Yace "eh dazu ta kira mu tace gasu nan zasu taso. I thought gaba daya zaku taho ai" nace "a'a, ita da Mustapha ne ka dai, ni da Daddy muna nan" naji chanji a muryarsa "but why? Me yasa zasu taho su barku ku kadai? Gashi Daddy babu lafiya ke ma kuma haka?" Nace "Mommy tace bikin Safina za'a yi. Kun sani?" "Bikin yaya Safina?" Ya mayar min da tambaya ta, nayi ajjiyar zuciya, basu sani ba suma, ya sake tambaya "wa zata aura?" "I don't know Hussein. Actually abinda na kira ku in tambaya kenan, daga ni har Daddy bamu san komai akan auren ba, and it hurts ne that bamu sani ɗin ba" ina jin sa yana magana da Hassan a kusa da shi, sai Hassan ɗin ya karba ransa a bace "but this is not right. Kawai tace mana zata je Katsina tun last two weeks kuma har yanzu bata dawo ba. She didn't tell us anything" nace "babu komai. In sun karaso kwa tambaye su details din sai muji" ya cigaba da fada sai na kashe wayar dan nasan idan ya fara ba dainawa zai yi, shima yayo gadon zuciya irin ta su Daddy. Daga nan kuma sai na mayar da hankali na gurin sama mana solution ni da Daddy, na kira Abdul na nemi taimakon sa na gaya masa abinda nake bukata, ina son a samo wa Daddy nurse namiji da zai ke taimaka masa with his day to day activities, sannan kuma da house keeper macw da zata ke shigowa two times a week tana gyara gidan, ni zan iya girki da dan sauran kananan aiyuka. Shima yayi mamaki da yaji cewa su Mommy sun koma Nigeria. Zuwa yamma sai gashi nan shi da Uncle Lukman sunzo, suka zauna a gurin Daddy har dare sannan uncle Lukman ya tafi ya bar Abdul ya kwana da Daddy, sai da safe sannan nurse din da aka yi hiring yazo. Aunty Hajjo ta kira ni tace in koma gurinta amma sai na nuna mata nafi son zama anan tare da Daddy, ina son inyi spending as much time as I can with him. Kuma naji daɗin days that follows dan na samu ina dan motsa jikina wajen zirga zirgar kula da bukatun mahaifina, abinci sai inyi masa kala biyar a rana, mu kan ci tare sometimes, in kuma yan fadan sunzo ya balbaleni da fada sai in tashi in shiga daki, daga baya sai na fahimci ganin cikin jikina ne yake triggering fadan sa, sai na koma yin iyakaci kokari na wajen ganin na saka kayan da zasu boye cikin. Kwana hudu da tafiyar su Mommy Safina ta kira ni. Ni tunda su Mommy suka tafi ban kuma yi mata magana ba ko a chats ita ma haka. Ranar sai ga kiran ta. Kamar ba zan dauka ba dan in kara nuna mata bacin raina amma kuma curiosity ya saka na dauka. "Kinyi fushi ko kanwata?" Nace "ohh dama kina da kanwa a duniya? I thought yan Katsina ne kawai yan uwanki" tayi dariya "wallahi ba laifi na bane ba, Mommy tace kar in gaya miki dan kar ki gaya wa Daddy, tana fushi dan yaki yarda da auren ku da yaya Mustapha. Sai yanzu nace mata ni dai zan miki magana, tsakanin su daban tsakanin mu daban" cikin bacin rai nace "but how can you do that Safina. Ni ban damu da rashin gaya min da baki yi ba amma Daddy fa? Daddy fa Safina. Ace wai ba za'a gaya masa maganar auren ki ba?" Tace "na gaya miki ba laifi na bane ba" nace "but you can convince her otherwise, ko kuma kibi ta wata hanyar da za'a sanar da shi" tace "what do you want me to do? Yanzu sai kawai in kira Daddy in ce masa anzo neman aurena an saka rana?" Na girgiza kai "a gani na Daddy yafi karfin haka a gurin ki, a tunani na duk wanda zaki aura gurin Daddy zai zo ya nemi auren ki sai ya amince sannan shi zai kai shi gidan ku na Katsina" tace "to yanzu dai an riga an yi an gama. Ni dai ke zaki taya ni bawa Daddy hakuri dan Allah. Nasan in yayi fushin sa ke kadai kike sauko da shi" nace "ni ba zan shiga cikin wannan maganar ba, nima lallabawa nake yi dan laifuka na sun fi na kowa yawa a gurin Daddy". Daga baya dana tambaye ta game da wanda zata aura sai ta bani labarin cewa a waya suka haɗu, kawai friend request ya turo mata tayi accepting shikenan cikin kankanin lokaci suka fara soyayya, ashe dama a gidan su kuma an fara matsa masa ya fitar da mata, shine ya fitar da ita. Nayi mata murna tace "I can't wait for you to meet him. I am sure you will like him". Bayan mun gama wayar da ita na tashi na shiga wanka, bayan na fito sai na samu kaina da tsayawa a gaban mirror ina kallon kaina ina tunanin yaushe rabon da in kalli kaina a madubi? Zan iya cewa ma ni har na manta da kamanni na. Na lura da yadda nayi baki na rame sosai idunwana suka faɗa ciki, duk glow din fata ta yayi diminishing. Ga uban ciki na da sai kara girma yake yi abinsa. Na dora hannu akan cikin ina kallonsa a madubi, Allah ne kadai ya san irin azabar da cikin nan ya bani tun daga samun sa har zuwa wannan lokacin, laulayi babu irin wanda ban sha ba, ciwo babu irin wanda banyi ba, azaba ta duniya kam na ganta akan cikin nan. Na tuna da Fiyyan da da irin gatan ta da irin shagwabar ta, na hango ina ma ace da aure na samu wannan cikin, da auren Muhammad. Na lissafo irin shagwabar da zan zuba masa ina jin ko bandaki ma sai ya goya ni ya kaini, na hango irin son da Daddy zai yi wa abinda yake ciki na, watakila ma sai ya kwace min fada a gurin sa, na hango irin son da Muhammad zai yi wa cikin nan da ace nashi ne, nayi murmushi ina tuna kalamansa, kullum baya rasa aabinda zai fada da zai referring to auren mu ko yayan mu, kullum in yana so ya tsoka ne ni sai yace zai gaya wa yayan mu abinda nake yi masa. Na tuno sanda ya gane ina tsoron asibiti yace duk ranar da zan haihu za'a sha drama. I wondered idan da munyi aure da yaya haihuwa ta zata kasance a gidan sa, maybe tare zamuyi labor, ko kuma doctor ya kora shi waje dan in ina ganin sa a gurin kara rikicewa zanyi. "ai kuwa ba zai fita ba" na fada a fili, dan karamin hauka zaiyi musu. Nayi murmushi. Sai kuma na bata rai ina tuna reality ɗina, I lost everything. The person who raped me took away not only my virginity but my everything, bai barni da komai ba radadin zuciya marar misaltuwa. Ni yanzu ba komai bace ba sai fanko, an empty shell without hopes and dreams, without even a zeal to live, without hope for a future. Karar wayata ta dawo dani cikin hayyaci na, na goge hawayen da ya sauko kan kuncina sannan na kalli screen din, sunan Mukhtar na gani. Na dauke kaina gefe ina cigaba da kallon reflection ɗina a madubi. I hate breaking his heart every time amma shi ya kasa ganewa, ya kasa fahimtar cewa dan nace na zabe shi ba wai yana nufin ina sonsa ba ne ba, na zabe shi ne dan bani da wani option left. I sometimes wondered ya auren mu zai kasance da shi, dan ni bani da burin komawa Nigeria ko da na rabu da cikin nan, too many memories. Ya sake kira. Na dauka na saka a kunne na bance komai ba "Habibty" ya fada, nayi shiru ban ce komai ba "ko bacci kike ne na tashe ki" nace "uhm uhm" "ko ba kya jin dadi?" Nace "uhm" "okay bara in barki ki huta. I just want to check on you inji ya kuke, wallahi bana jin daɗin zaman ku ku kadai daga ke sai Daddy, so nake in taho amma Abba ya hana ni, yace in bari sai kin haihu tukunna sai in taho. And guess what? I think suna shirin zasu daura auren nan ne kina haihuwa, maybe shi yasa yace in bari, watakila sai a ango zan taho". Naji kamar in rushe da kuka amma na cigaba da rike wayar a kunne na. Ya cigaba "ke har yanzu baki gaya min plans dinki ba for the wedding. Su Abba sunce daurin aure kawai zasu yi, ba sa son anything that will call attention na mutane kan mu, amma ni ina son ki samu everything da kike da burin yi a auren ki. Amma baki taba fada min ba ko akwai wani abu special da kike so?" A hankali nace "ni babu abinda nake so. In an daura auren kawai shikenan". Ya danyi shiru "i know ba kya so na, but this is not about me but about you. I want you to have all your heart desires. I know mata da son biki, am sure you had plans....." Na katse shi "mata daban daban ne ai, kowa da akwai abinda take so. Ni bana son biki. Bana son yin komai" na fada ina jin raina yana kara baci. Ya sake yin shiru. Sai kuma a hankali yace "I am sure da shi zaki aura da baki bata rai dan ance ki fadi events din da kike son yi ba. I am sure da Gidado ne da kin fi kowa murna........" Na mike tsaye kamar wadda aka yi wa allura "don't" na fada cikin sarkewar murya, "don't you dare mention his name ever again" ya danyi dariya kaɗan "okay, okay. Na daina. I just want you to talk kin barni ina ta magana ni kadai shi yasa na dan taɓa button ɗin da yake activating ɗin ki. Amma nima kishi na ba zai barni in kuma ambatar sunan sa ba. Kin san...." Na kashe wayar nayi jifa da ita kan gado sannan na koma na zauna tare da dafe kaina, wani irin bacin rai nake ji, wani irin ciwo zuciya ta take yi min. Na san Mukhtar ya san Gidado kamar yadda shima Gidadon ya san shi, amma basu taba magana da juna ba kuma wani daga cikin su bai taba yi min maganar dayan ba. Ban san mai yasa jin sunan Gidado a bakin Mukhtar ya bata min rai har haka ba. Na jawo wayar tawa ina kallon hoton kan screen din. Hannun Gidado ne a ajjiye akan steering motar sa "Allah sarki Muhammad" Na fada a fili "Allah ka dubi bawanka". Na sani, ina son Muhammad son da ba zan iya kwatanta shi ba, na kuma sani shima yana min son da ban taba ganin irin sa ba. Na tuno da haduwar mu ta uku, na tuna da yadda ta kasance. ****.     ****.     ****.    ****.    ****.    **** Tunda muka rabu da shi a ranar da muka yi haduwa ta uku zuciya ta bata samu sukuni ba, naji haushin sa sosai a ranar, haushin rashin karbar number ta da baiyi ba, na kuma ji haushin kaina akan me yasa ni ban karbi tashi ba tunda shi ya manta bai karni tawa ba? Amma kuma ni nasan kaina, nasan pride ɗina na ƴa mace ba zai barni in karbi number ɗin saurayi ba ko kuma inyi making first attempt, na san cewa na kamu da son sa, duk kuwa da cewa a lokacin ban san so ba amma nafi so ace shine da kansa ya fara ambata min yana sona ba ni ba. Wani lokacin kuma in ina tunanin sa sai inji haushin kaina, ina ganin kamar shi bashi ma da interest a kaina shi yasa ma bai karbi number ɗin ko kuma ya nemi address dina ba. I mean wanne saurayi ne zai ga budurwar da yake so suyi magana sosai kuma har su rabu amma bai karbi number ɗin ta ba, who does that? Tun ina daukan abin wasa har ya zamar min gaske, kullum in ina zaune ni kadai shi nake tunawa, sai inyi ta bitar maganganun mu a raina ni kadai ina murmushi. In kuma na kwanta bacci Muhammad sai ya bini cikin bacci na, amma a baccin nawa yana karbar number ta har ya kira ni a waya muyi ta hira, ina ta murna, sai na farka sai inga ba haka bane ba. Lokacin dama Daddy ya kawo ni Abuja da niyyar uncle Ahmad ya nema min jami'a a cikin manyan jami'o'in Abuja saboda in samu in zauna a guri daya in daina binsa ƙasa ƙasa, uncle Ahmad ɗin kuma yayi kokarin samar min admission ɗin, jira kawai yake a fara registration ya kaini inyi, a lokacin ne wata dabara tazo min. Ina tunawa a cikin maganganun da muka yi da Muhammad ya fada min family dinsa sun bude sabuwar jami'a in honor of his late grandfather. Ya kuma shaida min yana son yin aiki a can. Duk da dai lokacin da muka yi maganar bai fara aikin ba. Sai na yanke shawarar why not in saka a nema min admission a makarantar, maybe mu sake haduwa a can. Maybe ma in ganshi a aji a matsayin malami na. Na tuna sunan makarantar "MD University". Naje na samu uncle Ahmad da maganar "uncle wata sabuwar jami'a da aka bude kwanan nan, MD University, can nake so a nema min" ya bata rai "ban gane ba. Ita kuma wannan da aka nemar miki menene matsalar ta?" Nace "babu komai uncle, kawai dai ni nafi son waccan ne, akwai kawayena da suka ce min can zasu je, kaga zan samu abokan karatu". Haka nayi ta bugawa amma uncle Ahmad yaki yarda, ranar nan ma cewa yayi in na sake yi masa maganar sai ya kwada min mari. Mukhtar yana ta yi min dariya. Ni kuma naki hakura dan gani nake makarantar ita kadai ce chance ɗina na haduwa da Muhammad again. A haka Allah ya kawo savior dina kasar, Daddy, ai kuwa ranar da yazo da maganar na tare shi, "Daddy ni MD University nake son a nema min, ni bana son wannan da aka samu" ya juya yana kallon uncle Ahmad "wacce ce kuma MD?" Uncle Ahmad yace "kar ka biye mata yaya, wata sabuwar jami'a ce da ko kafuwa bata yi ba ballantana musan kyanta ko akasin haka. Wannan shekarar fa suka fara daukan daliban su na farko" na zamo daga kan kujera na fara kuka "ni wallahi Daddy ita nake so. Dan Allah ni dai a kaini can. Allah in ba'a kai ni ba ba zanyi karatun ba" Daddy ya fara fada "ba za'a kai ki ba ɗin. Wannan da aka samo ɗin ita zaki je". Amma daga ni har duk wanda yake gurin mun san cewa kamar an kai ni ne an gama. Wata guda bayan nan har na gama registration na fara zuwa lectures. Tun daga nan kuma sai na fara abinda ya kai ni makarantar, neman Muhammad. Farko na fara neman sa a cikin malaman department din mu, amma ban same shi ba, sai na fara nema a na sauran departments amma na rasa a ina zanyi concentration neman tunda ni ban ma san me ya karanta ba ballantana in san me zai koyar. Sai na fara shiga cikin yan wani department din da ba nawa ba, in ana hira sai ince something like "ai naji labarin wannan malamin naku Muhammad Lawan, ance bashi da kirki" and they will be like "mu bamu da malami Muhammad Lawan" and I will be like "Okay ba department din ku bane ba ashe". A haka har sai da na fara fitar da rai, thinking ko ya chanza shawara bai karbi aikin ba. Amma kuma na kasa hakura. A haka har semester ta kare aka fara shirye-shiryen exams. A lokacin ne kuma naje zanyi submitting wani assignment ɗina a office ɗin wani malamin mu. A lokacin ne kuma na ganshi. Building din hawa biyu ne, duk offices din lecturers ne, office ɗin wanda zan kaiwa yana sama, ina hawa hawa saman idona ya sauka akan Muhammad a kofar wani office yana budewa. Sai dai bai ganni ba ya bude ya shiga ciki sannan ya mayar ya rufe. Na karasa da sauri ina jin wani irin excitement amma kuma zuciya ta tai yarda da cewa shi din ne. Naje kofar office din da ya shiga na tsaya na karanta sunan jikin office din "Muhammad Lawan Muhammad" naji wani dadi ya rufe ni kamar in taka rawa a gurin. Amma kuma what next? Gani dai gashi, katanga ce kawai a tsakanin mu amma me zanyi kenan? Shin zanyi knocking ne in ya buɗe ince hi? Ko kuma shiga kawai zanyi inyi pretending kamar batan kai nayi ba nan zan shigo ba, in yaso sai in nuna mamakin ganin sa a office ɗin. To amma kuma ai ga sunan sa nan baro baro a jikin kofar, in na shiga dole zai gane neman sa nake yi. Na dafe kaina, ga koshi ga kwanan yunwa. A karshe haka ina ji ina gani na wuce office din ban shiga ba naje nayi submitting assignment dina na sake wucewa na koma gida. Amma hankali na ya kwanta tunda na ganshi na tabbatar yana makarantar, sai na kudiri aniyar zan san yadda zanyi ya ganni kuma ya fara yi min magana. Daga nan na fara monitoring dinsa, na lura da sanda yake shigowa makarantar da kuma sanda yake fita. Sai na shirya plan dina. Sai da na daidaici lokacin da yake fita sannan na kwashi littattafai da takardu na tafi kan stairs din offices din nasu na baje wai ni lallai karatu nake yi. Ina zaune da uban takardu a gaba amma hankali na yana kan duk motsin da za'a yi a sama. A haka har na ji taku, na dan duba ta gefen ido na ga shine sai na dauke kai na cigaba da bude littafin gaba na amma ina jin zuciya ta tana ta bugawa da karfi. Ban ankara ba sai gani nayi yazo ya wuce ni ba tare da ko kallon inda nake yayi ba, yaje ya shiga motar sa ya tayar ya fice daga makarantar. Naji takaici ya kama ni. Amma na gaya wa zuciya ta cewa bai gane ni ba musamman saboda bayana zai gani sanda yaje saukowa. Sai na chanja shawara. Washegari takanas na samo kujeru guda biyu da dan karamin table na dasa a direct opposite stairs din su. Na baza takardu sannan na sawa kofar office ɗin sa ido, a haka har naga ya fito ya rufe kofa sannan ya fara saukowa, sai da naga ya kusa gama saukowa sannan nayi dabara na zubar da takardun gaba na, kamar irin iska ce ta zubar da su ɗin nan, ko bai ganni ba na san hasken takardun zai dauki hankalin sa. Naji takunsa ya doso inda nake, ina jin kamar a cikin zuciya ta yake taka kafafunsa, sai kuma ya tsaya a dai dai sai ti na. A lokacin na tabbatar cewa ya ganni kuma ya gane ni amma ban kalle shi ba sai na cigaba da bude pages din littafin da yake gaba na. Naji Muryar sa "oh my God" still ban daga kai ba. Ya kara matsowa "oh my goodness. Piya? It is really you" na dago kai ina bata fuska, sannan na bishi da kallo tun daga kan takalmin kafarsa zuwa fuskarsa da take reflecting wani irin annuri da farin cikin da zuciyar sa take ciki. Na bayyana mamaki a tawa fuskar "wow. Malam Muhammadu dan fillo. What are you doing here?" Ya ja kujerar da dama dan shi na ajiye ya zauna "ke zan tambaya Piya, what are you doing here? How comes? Taya kika zo nan? Shin ko mafarki nake yi ne?" Nayi murmushi ina nuna masa takardun gaba na "karatu nake yi. Anan makarantar nake. Kai fa?" Yace "I work here. Ga office dina can. I can't believe this. You have no idea yadda na sha wahalar neman ki a garin Abuja" a raina nace "taka wahalar ka sani ba ka san tawa ba". Yace "ranar nan was the best and the worst day of my life. I can't believe I let you go ba tare da na karbi number ɗin ki ba. I went back to your car na zauna jiran mechanic dinki yazo daukan mota in karbi number ɗin ki a hannunsa, amma that good for nothing mechanic bai zo ba, anan nayi sallar la'asar da magrib" na rufe bakina ina dariya, shima yayi dariyar "stop laughing at me. Nasha wahala fa. Har dare bai zo. Da sassafe kuma dana koma gurin already har ya dauke motar". Nace "to ai Allah ya yi yanzu, gashi mun sake haduwa" bai ce komai ba sai ya dauko wayar sa ya ajiye min a gaba na "i won't repeat the same mistake. Dauki ki saka min number ɗin ki" na dauka na saka, na mika masa amma sai yaki karba yace "save it" nace "okay, me zan saka maka yadda zaka gane. Safiyya Adam Muhammad kamar yayi tsaho, ko in saka maka Fiyya?" Ya girgiza kai "Piya. You will always be Piya to me" nayi murmushi ina jin zuciya ta fari kal. Nayi saving da Piya💝 na mika masa still sai yaki karba yace in kira, sai dana kira ya tabbatar ta shiga sannan ya karbi wayarsa. Na dauko tawa wayar a jaka nayi saving tasa number ɗin, farko na saka Muhammad, sai kuma na goge na saka "Pyar💝" To gain access to the book contact 👇 0704 203 0419 Telegram Only... ❤‍🩹 *Safiyya*❤‍🩹 *By* *Maman Maama* *Episode Eleven: The First Visit* Free Episode Assalamu alaikum Mun kusa gama free episodes insha Allah. And the paid episodes will insha Allah come on telegram. Na gaji da replying cewa ba'a fara payment ba 😅, so zanke including payment details a kasan episodes daga nan har zuwa sanda za'a gama free episodes ɗin. Nagode sosai da kaunar da kuka nuna mini kullum, Allah ya bar mu har gaban abadan. Safiyya will be worth your money and time, that I promise you 💕. Nayi sauri na mayar da wayar cikin jaka ta dan kar ya ga abinda nayi saving number ɗin sa da shi. Ya fara yi min tambaya game da department din da nake da kuma yana yin da nake ciki, ni kuma nayi masa duk bayanin da nake ganin ya dace sannan na sanar masa da cewa ina gidan uncle ɗina ne, zuwa nake yi kullum. Muna haka aka fara kiran sallar magrib dama yamma tayi sosai, muka tashi ya taya ni tattara takarduna da ba katantawa nayi ba na zuba su a cikin jaka sannan yace "let me take you home" na bude ido ina kallon sa "ya hade hannayen sa "Please" na girgiza kai da sauri "no. In dai ba so kake yau in kwana a gadon asibiti uncle Ahmad ya balla min kafa ba" yace "saboda me?" Nace "in yaga wani ya kai ni gida, ai karshen karatu na kenan. Besides, nazo da mota" yayi ajjiyar zuciya "Finally an baki motar kenan" muka fara tafiya inda nayi packing nace "da kyar. Farko ai bai yarda a bani motar ba tunda na lalata waccan, sai yace sai dai Mukhtar yake kawo ni school kullum kuma yana zuwa yana daukana, ni kuma....." ya bata rai "waye Mukhtar" nace "cousin dina ne, a gidan su nake zaune" yace "ohh, that guy that picked you up the other day?" Nace "yes, shi" ya girgiza kansa "I don't like that" na tsaya ina kallon sa da mamaki "why not. Menene matsalar?" Ya daga kafada "kawai dai. But tunda kinyi mota ai shikenan ko? Yanzu ke kike zuwa da kanki ko?" Nace "yes" and then I saw relief a fuskarsa. Muka karasa na tsaya a gaban motar ina kokarin dauko key. Yabi motar da kallo, noticing cewa daga ledar ta aka bare ta "wow. Rich kid" nayi murmushi "zaka fara ko?" yace "na daina. But it is a good one. Really. Congratulations" na shiga na zauna nace "thanks". Ya rufo min kofar yace "I will call you, for real yanzu dai" nayi murmushi "i will be glad if you do". A lokacin duk mu biyun tunani muke munyi hitting jackpot, bamu san cewa kaddarar mu a chakude take da several heartbreaks ba, heartbreaks ɗin da zasu barmu with nothing but bitter sweet memories. ****.    ****.    ****.    ****.    ****.    **** Nayi ajjiyar zuciya na ajiye wayar a gefe, da ace a lokacin na san kaddarar da take bi na da ban neme shi ba, da ko ya neme ni ba zan bari ya same ni ba ballantana har in tarwatsa rayuwarsa kamar yadda nayi a yanzun. Na mike na dauko kaya na na saka, doguwar riga mai fadi sosai da hula, ba zan iya tuna rabon da in saka comb in taje kai na ba, na tabbatar yanzu ko na saka comb din ba zai wuce ba, ban kuma san ranar da zan taje shi ba and I do not care. Na fita na tarar da Daddy suna yin physiotherapy da nurse dinsa, an siyo masa wani machine da zai taimaka masa wajen motsa hannunsa automatically ko da yana bacci ne dan a dan karawa muscles din hannun karfi. Na zauna ina kallon su ina jin yadda zuciya ta take cigaba da karyewa, a duk abinda ya same ni babu abinda yafi dukan zuciya ta kamar rashin lafiyar mahaifina, zan iya sake going through duk abinda nayi going through and more idan da ace in nayi haka zai samu lafiya. Na tashi na koma kitchen na kira Hassan ina son inji ko sun samu wani sabon labarin, a lokacin ne yake gaya min uncle Ahmad ya kawo musu motocin da nace ya siya musu tun kafin in taho, ni na manta ma da maganar dan na dauka ba zai siya ɗin ba, yanzu  ma nafi tunanin ya siya ne kawai saboda yaji daɗi na zabi auren Mukhtar akan Mustapha, na tabbatar da Mustapha na zaba da ba zai sayi motocin nan ba sai dai ni insan yadda zanyi in siya musu, suna ta murna, ya bawa Hussein shima yayi ta min godiya, sai na tambaye su labarin su Mommy "ya maganar auren Safina? Any development?" Yace "ana ta shirye-shirye, kamar dai a Katsina za'a yi daurin aure, I don't know ko za'a yi wani event din again a can. Amma naji Mommy tace za'a yi dinner anan Abuja sannan zata yi yini a gidan Hajiya, kuma kamar a Abujan zasu zauna" nace "okay. That's nice. Angon fa? Kun haɗu da shi?" Yace "chafdi. Ni wannan mijin nata already ma bai yi min ba tun kafin in ganshi. Can you believe har yau bai je ya gaishe da Mommy ba? To katsinan ma Mommy tace sun ce bai je ya gaishe su ba. Kin taba jin irin haka?" Nayi dariya "kai Hassan kar ka zama mai yaɗa kananan maganganu mana kamar mace, tunda dai ita tana son kayanta shima kuma yana sonta ba shikenan ba, na tabbatar ai yan katsinan sunyi binciken su kafin su ce sun bashi ita". Sai kuma yayi min maganar abinda yake raina tun tafiyar Mommy "dazu da nayi maganar Hajiya sai na tuna da sakon ta, munje gaishe ta ranar nan tace mu gaya miki ki kirata. Kamar fa itama tana fushi ne akan batun yaya Mustapha. Ki kirata kinji yaya?" Nayi ajjiyar zuciya nace masa zan kirata ɗin, sai dai a raina nasan bani da karfin zuciyar yin hakan, I already have enough problems on my plate. A haka muka gama wayar mu na zauna ina ta jujjuya wayar a hannu, wani irin uneasiness nake ji a raina duk sanda aka yi maganar auren Safina, haka kawai na kasa cire maganar da ga raina duk kuwa da cewa ina da abubuwan da suka fi maganar muhimmanci a gurina. *Him 👳🏻* Duk abinda ake yi na shirye shiryen bikinsa yana sane, sai dai sam baya shiga cikin maganar, in an tambaye shi abu sai yace ayi ko menene ma. Abba da Mama suna sane da hakan kuma dama sun saka ran cewa hakan ce zata kasance amma su a lokacin a ganin su babu abinda zai dawo musu da hankalin dan nasu zuwa gare shi sai idan ya manta da Safiyya, babu kuma abinda zai mantar da shi Safiyya sai wata macen, musamman da Mama taga hotunan Safina kuma ta ga cewa tana da dukkan abinda ake bukata a gurin mace idan za'a kira ta da mai kyau, sun kuma samu nasabar ta mai kyau ce kuma a iyakacin binciken su basu tarar da wani halin ta marar kyau ba. A ganin su idan suka hada auren, musamman yadda suka fahimci Safina tana mugun son Gidadon nasu, to tabbas zata yi duk abinda zata yi dan ta mantar da shi Safiyya, dan ta dawo dashi cikin hankalinsa. Yana ji yana kallo aka dauki kayan lefen da aka haɗa da sunan Safiyya, aka chanja sizes din wasu abubuwan musamman undies saboda sizes din Safina yafi na Safiyya, aka kai Katsina. Da kyar dai ya samu Abba ya amince aka chanja masa gidan da zai zauna, wancan da ya gina da sunan Safiyya ya ajiye shi aka siya masa wani. A bangaren abokansa kuma suna jin an fara maganar auren sa suka fara murna, sai dai kuma da suka fahimci ba da Safiyya bane ba duk sai suka dame shi da tambaya "guy, what happened? Ina Safiyya kuma? Ban taba dauka zaka auri wata ba Safiyya ba musanman saboda yadda ka susuce a kanta. Ina take?" "Ta mutu" ya amsa musu direct "Allah yayi wa Safiyya rasuwa". Duk suka dauki salati "innalillahi wa inna ilaihir rajiun! Yaushe? Kuma ba ka fada mana ba? Ko gaisuwa ba muyi maka ba ballantana muje gidan su?" yayi shiru sannan yace "sometimes it is hard to admit something. Fadar a baki yana kara zafi a zuciya" duk sai suka ji tausayin sa ya kama su, dan babu wanda ya san Gidado bai san cewa akwai yarinyar da yake so mai suna Safiyya ba. Daga nan kuma duk jikin su yayi sanyi, sun kuma yarda da maganar sa musamman ganin yadda kwana biyu duk ya zama wani iri ya rame ya lalace spirit dinsa duk ya bar jikin sa. Wannan ya sa da yace babu abinda zaiyi na wannan bikin nasa sai suka goya masa baya, sun fahimci cewa auren hadi ne komai iyayen da suka hada su suke shirya abin su. Babu wanda ya san gaskiya sai Al'ameen, shi kuma Gidado avoiding dinsa yake yi dan sam baya son su hadu ballantana har yace zaiyi masa maganar Safiyya ko ya nemi bashi hakuri akan abinda ya faru. Ya fi son kawai a barshi shi kadai with his thoughts. Sai da ya rage three weeks biki sannan Mama da kanta ta nemi Mufida ta karbar mata number ɗin maman Safina dan su samu suyi maganganun yadda abubuwa zasu kasance, tunda a gurin angon ya kamata su samu duk information din da ya kamata shi kuma baya basu haɗin kai. Sai da ta kira ta ne sannan suka tsara duk yadda bikin zai kasance. Za'a yi kamun amarya Thursday a Katsina, shima ango za'a yi nashi kamun Thursday a Abuja. Friday za'a yi daurin aure a Katsina, sannan a taho da amarya Abuja, Saturday Mommy zata yi yinin ta anan Abuja ita ma kuma Mama zata yi nata, a Saturday din ne kuma za'a yi daurin auren Mufida anan Abuja, Sunday za'a yi dinner, a sunday din kuma za'a kai amare. Sai bayan da suka gama maganganun su ne sannan Mommy ta yi wa Mama korafi. "shi dan namu ne nace har yanzu bamu ganshi ba, ya kamata yaje katsina ya gaishe da iyayen yarinyar nan su ganshi ido da ido, wasu ji dadi sosai su ga cewa an girmama su" Mama taji babu dadi a ranta, tabbas tasan Gidado baya kyauta wa, tace "insha Allah a cikin wannan satin zai je. Shi din ne sabgogi sunyi masa yawa amma insha Allah zanyi masa magana. Tabbas ya kamata yaje" Mommy tace "yauwa. In yayi hakan ya kyauta. In ya dawo daga katsinan kuma sai yazo muma nan ya gaida Hajiya, Hajiya yayata ce a gurin ta na girma anan Abuja, kamar uwa take a gare ni. Zata ji dadi idan yazo" shima nan Mama ta sake alkawarin zai je. Sai dai suna gama maganar ta ajiye wayar ta dafe kai, bata san ta yadda zata lallaba Gidado yayi wannan ba. Ta san in ta matsa masa dole zai yi, amma kuma ba zaiyi cikin son zuciyar sa ba. Abinda kuma yake damunta kenan, she wants him to be happy, but he is getting sadder every day. Sai da suka shigo gidan tare da Abba bayan sallar magrib sannan tayi mishi maganar zuwa Katsina. "Yaushe zaka je ka gaishe da iyayen yarinyar nan ne? Ya kamata kaje su ganka. Zasu ji dadi sosai. Shi tuwon girma hausawa sunce miyarsa nama". Ta ga yanayin sa ya chanja lokaci daya. Amma bata hakura ba ta cigaba "ita kanta yarinyar har yau ba kaje ka ganta ba Gidado. Ya kuke ciki ne wai?" Ya nuna wayarsa "muna waya Mama, ina kuma ganin ta a waya. She understands cewa akwai nisa. Kuma kwana nawa ya rage" tace "minti nawa ce katsinar a jirgi? Ko ce maka akayi ka dauki mota ka tafi?". Yayi shiru sai kuma tayi ajjiyar zuciya "Gidado, kulawa ma ai yabawa ce. Ina laifin wanda yace yana sonka? Wanda yake hakuri da duk abinda kake masa saboda yana son ka? Ko a haka ai yarinyar nan tayi kokari. Ka daure kaje kaji babana?" Yace "to Mama, zanje insha Allah" tace "yauwa, Allah ya yi maka albarka" yaji dadi a ransa yace "Ameen Mama" Abba yace "sai ka nemi friends dinka ko mutum biyu sai su raka ka. Yaushe zaka je?" Gidado yayi shiru yana shafa fuskarsa data cika da gashi sannan yace "zanyi magana da Ya Ameen inji sanda yake free, sai muje tare da shi". Ya zaɓi tafiya da Al'ameen ne shi kadai saboda shi kadai ne a friends dinsa ya san gaskiyar halin da ake ciki, shima kuma dan Mama ta saka shine a ciki tun farko. A waya suka yanke sanda zasu je. Suka saka next weekend. A take Al'ameen yayi musu booking flight ɗin safe da kuma return na yamma. Bayan sun gama wayar Gidado ya zauna yana jujjuya wayar a hannunsa. Tun kiran wayar da yayi wa Safina na farko bai kuma kiranta ba, in ta kira shi kuma daga ya dauka sai yace mata yana busy ne zai kira ta. Daga baya ma sai ya saka layin shi da take da shi a DND (do not disturb), yayi excluding mahaifansa da siblings dinsa. Wannan yasa babu wanda yake kiran shi a layin ma gabaki daya sai su, sai ya cigaba da using dayan layin nasa for his friends and relatives. Yayi tsammanin zata yi korafi gurin su Mama cewa bata samun sa a waya amma sai yaji shiru Mama bata yi masa faɗa akan hakan ba. Ta kan turo masa messages, shima kuma ya kan bata amsa akan abinda ya ga ya chanchanci amsar. Amma yanzu yasan dole ya kira ta, tunda in sunje katsinan bai san inda zasu dosa ba. Kuma shi bai isa ya samu iyayen sa yace su bashi address ba. Ya nemo number ɗin ta ya kira. Ta dauka sallama "Assalamu alaikum Habibi" yaji kamar ya ajiye wayar amma sai ya amsa sallamar, ta gaishe shi ya amsa, sai ya tsaya yana jiran tayi masa korafin rashin kiranta da kuma rashin samun sa da bata yi. Amma sai yaji bata yi ba. Yace "dama ina so ne ki samarwa da su......ki sanar a gida, zamu zo ranar Saturday insha Allah mu gaishe su" yaji yana feeling awkward, remembering sanda yake ta yiwa Safiyya nacin yana son zuwa ya gaishe da Daddy. Tace "alhamdulillah. Zan gaya musu. Nasan zasu ji dadin hakan sosai. Nima kuma zanji daɗi. Amma in saka ran ganin ka ko kuma zuwan nasu Baba ne su kaɗai?" Ya shafa fuskarsa yana jin babu daɗi, kamar yadda Mama ta fada, ina laifin wanda yace yana son ka? Yace "zamu haɗu, insha Allah" tace "masha Allah. I can't wait" yana jiyo farin cikin ta daga cikin wayar. Sai kuma ya tambaye ta abinda ya kira ta saboda shi "sai ki turo min address ɗin" tace "babu matsala, kawai ka gaya min sanda zaku sauka, I will pick you up from the airport". Ranar Saturday ɗin kuwa suka tafi. Mama ta haɗa musu kayan ciye ciye exotics ta basu ta ce su kaiwa yar tata. Sai da suka zauna a jirgi sannan suka samu damar yin magana. Al'ameen ne ya fara ce masa "so? Anything new?" Ya juyo yana kallon sa yace "concerning what?" Al'ameen yace "you know what. I don't believe ka bar maganar waccan yarinyar ka karbi wannan. And I don't want any surprises. So if you are planning something now is the right time to tell me so that I can talk you out of it" Gidado ya danyi dariya kadan yana girgiza kansa yace "I wish. I wish cewa akwai abinda nake planning, something that can get me out of this mess, amma babu komai, my brain is no longer working. Ban san me nake yi ba ban kuma san me zanyi ba next. I just want all of these to be over so that at least su Mama su san cewa I obeyed them and did my best" Al'ameen ya rage ido yace "and you are sure baka searching for that girl under ground?" Gidado yana kallon sa yace "there is no need. Ba zan neme ta ba. I have given up on her. All what I want to do now with all my heart is to forget about her. But the mission is impossible". Sai da suka sauka sannan ya kira number ɗin Safina ya gaya mata sun iso, sai ta ce masa Baba ya hana ta zuwa daukan su yace ba dai dai bane ba, amma ya turo yayanta ya dauko su. Suna fita wanda yazo daukan su ya gane su. Ya karaso tare da mika musu hannu suka gaisa "kaine Muhammad ɗin" ya fada yana kallon Al'ameen. Al'ameen yayi masa murmushi yace "eh nima Muhammad ne. Amma ga Muhammad ɗin da kaje nema nan" mutumin yasake mikawa Gidado hannu yana fadada murmushin sa yace "Muhammad Gidado, barka da zuwa katsinan dikko gidan kara da mutuntawa. Sunana Mustapha. Saura kadan mu gama free episodes 😅. Get your 500 naira ready and subscribe to an amazing journey with Safiyya and Gidado. I can't wait to share all of the story with you. Har hango yadda fuskokin ku zasu kasance nake yi when the drama really began to unfold. 🤣 Ga masu son kama seat ɗin su da wuri, send your *500* naira to the following account 0779484494 Nafisa Tafida Usman Access Bank And send your evidence to the following number via telegram 0704 203 0419 Posting of paid episodes is going to be strictly on telegram. Please no phone calls. Just send the evidence and I will reply you. Thank you. One love 💕 *❤‍🩹 Safiyya ❤‍🩹* *By* *Maman Maama* *Episode Twelve: Twisted* 💕 Gidado yayi taku biyu baya yana kallon hannun da mutumin ya miko masa, sai kuma ya kalli fuskarsa kamar mai kokarin gane wani abu "Mustapha? Mustapha kace" mutumin ya sauke hannun sa ganin gidadon bai yi shaking ba, Al'ameen yace "eh Mustapha yace, ka san shi ne?" Wani murmushi Gidado yayi, a zuciyarsa yana jin kamar an dauke masa wani babban dutse, yace "no. Ban san shi ba. At least not yet" mutumin ya mayar masa da murmushin sa yace "Yes. I believe we will soon know each other a matsayin in laws". Yayi gaba su Gidado suka bishi a baya zuwa mota, sai a lokacin suka lura da cewa su biyu ne suka zo. Suka gaisa da dayan shima sannan suka shiga bayan motar su kuma suka shiga gaba, wanda ya kira kansa da suna Mustapha yana driving. Gidado ya juya kansa yana kallon waje yana jin daɗin iskar da take dukan fuskar ta sa, iskar yanci. Yanzu tabbas yana da tudun dafawa. Safiyya tana yawan ambaton Mustapha a maganganun ta kamar yadda take ambaton Safina. Ya kuma san cewa shi Mustapha ɗin yayan Safina ne uwa daya uba daya. It cannot be a coincidence ace wannan yarinyar sunan ta Safina sannan kuma tana da yaya Mustapha. Ya san idan ya tabbatar wa da Mama cewa Safina yar uwar Safiyya ce to tabbas zasu yarda a fasa auren, ko ba dan komai ba ya san yanzu babu halittar da suka tsana irin Safiyya. Ya juyo da kansa, fuskarsa still dauke da murmushi, Al'ameen da yake ta kallon sa ya yi masa alamar tambaya "what?" Dan ya san ba da irin wannan fuskar suka taho ba. Amma Gidado bai kula shi ba so yake yi suje gidan ayi maganar a gaban Safina a gaban kuma Al'ameen yadda Al'ameen din zai zamo masa shaida a gurin iyayensa. Dan yanzu duk wani abun da ya shafi Safiyya ba yarda suke yi da maganar sa ba. Basu yi nisa sosai ba suka sauka daga kan titi suka shiga wani layi sannan suka shiga wani gida. Gidado ya bude ya fito yana kallon gidan, gida ne na masu rufin asiri, not luxuriously rich but middle class rich. Daga gani kuma gida ne mai mutane da yawa a cikin sa. Wadanda suka kawo su suka yi musu jagora zuwa bayan gidan, sannan suka shigar da su wani ƙaramin parlor. Suna fita Al'ameen ya tambayi Gidado "what? Menene kake ta fara'a haka? Don't tell me daga ganin yayanta har ka matsu da ka ganta" ya karasa cikin tsokana "Gidado ya zauna ya dora kafa daya akan dayar yana jujjuya ta yace "yes, in a way zaka iya kiran abinda nake ji a raina haka. Kai dai ka jira. You will be surprised with the outcome of this visit" Al'ameen ya zauna, trying as much as he can to be comfortable akan kujerar yace "to Allah ya sa muji alkhairi". Basu dade da zama ba wasu samari suka shigo su biyu suka fara jera musu kayan ciye ciye bayan sun gaishe su. Gidado ya yi tilting kansa yana kallon yaran kokari yake lallai sai yaga kamannin Safiyya a tare da su, sai da suka gama sannan yace "are you guys twins?" Suka juyo suna kallon sa sannan suka kalli junan su suka yi dariya. "no" daya yace dayan kuma yace "a'a. Abokina ne wannan. Dan makotan mu ne". Gidado ya koma ya jingina kansa a jikin kujera tare da rufe idonsa, yana jin al'ameen ya bawa yaran wani abu suka yi masa godiya suka fita. Sai da suka fita Al'ameen yace "kannen ta ne twins din da kake nema?" Bai bude idon ba yace "kannen Safiyya ne" Al'ameen yayi ajiyar zuciya yace "Gidado, gidan su Safina muka zo nan ba Safiyya ba. What is wrong with you" gidado ya gyara zama yace "na sani, akwai abinda nake tunani. You will understand idan ta fito. Ba'a jima ba kuwa ta fito ɗin. Kamshin turaren ta ne ya fara iso musu kafin ta karaso. Kyakkyawace son kowa kin wanda ya rasa. Fara tas mai cikar jiki da shape mai kyau wanda ta tabbatar ya fito a cikin doguwar rigar lace ɗin da ta saka, ba irin fitowar da za'a kira da tsiraici ba amma irin fitowar da zai dauki hankalin duk wanda ya kalle ta. Fuskarta da kwalliya dai dai gwardado. Tayi daurin dankwalin da ya zauna ɗas a kanta ya kuma bayyanar da yalwataccen gashin kanta ta baya. Ta yafa mayafi a side daya ya rufe rabin kirjinta. Ta tsaya a bakin kofa tayi sallama. Suka amsa mata a tare sannan ta shigo kanta a kasa ta zauna a kujera ta gaishe su "sannun ku da zuwa. Da fatan hanya bata gajiyar da ku sosai ba" duk suka yi shiru babu wanda ya amsa. Kowa yana saka ran dayan zai amsa. Sai kuma suka kalli juna a tare suka amsa "lafiya lau" "yauwa". Suka sake yin shiru gabaki daya. Ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da fingers dinta, Gidado kuma ya tsare ta da ido a ransa yana son ya ga ko zai iya tuno kamannin Safinar Safiyya, maybe ko ya taba ganin ta a hoto amma ya manta, yayin da shi kuma Al'ameen yake kallon Gidado da mamakin kallon da yaga yana yiwa Safina. Al'ameen ne ya katse shirun ta hanyar yin gyaran murya tare da cewa "malama Safina ya shirye shirye?" Ya fada already feeling awkward, dan shi ba gwanin magana bane ba musamman ga wadanda bai sani ba. Ta dago ido suka hada ido da Gidado, tayi murmushi tare da sake mayar da idonta kasa sannan tace "alhamdulillah. Ya naku?" Kafin ya amsa mata Gidado yace "ina twins?" Ta sake dago ido tana kallon shi, shi kuma yayi kokarin studying fuskarta yana neman yanayin mamaki amma sai yaga confusion. "Twins kuma? Wadanne twins?" Yace "naga Mustapha shi ya dauko mu dazu, na dauka tare da twins suka zo" ta sake bata fuska tare da girgiza kai "still ban gane abinda kake nufi ba. Mustapha daga ina yazo? Ai dama yana nan. But ka san shine wai?" Yace "shi Mustaphan ba yayan ki bane ba?" Ta gyada kai still cikin nuna rashin fahimta tace "eh yaya na ne, dan kanin baban mu ne. Ka san shi ne?" Gidado ya mayar da kansa baya tare da rufe idonsa, yana jin dutsen da ya daga daga kan zuciyarsa dazu yana komawa yana cigaba da danne ta. Al'ameen yayi saurin cewa "kamar naga kin kawo mana snacks, ɗan zuba min" ta mike da sauri ta dauki dan karamin plate ta na zuba masa samosa amma hankalin ta yana kan Gidado, ta durkusa ta mika wa Al'ameen still tana kallon Gidado tace "is he okay? Ko baya jin dadi?" Al'ameen yace "fine, he is fine, akwai serviette ne?" Ta dudduba gefe sai ta mike tace "bara in kawo". Tana fita Al'ameen ya ajiye plate din da ta bashi ya taba kafadar Gidado yace "kai lafiyar ka kuwa? What are you doing. What is with wani Mustapha and twins" Gidado ya bude idonsa, duk annurin da ya sauka a fuskarsa dazu ya kauce yanzu, yace "Piya tana da step sister mai suna Safina, and a step brother mai suna Mustapha. When I saw that guy yace min shi yayan wannan Safinar ne kuma sunan sa Mustapha, I thought......" Al'ameen yace "Muhammad! Must you relate everything to her? Komai na rayuwa sai ka jingina da ita sannan zai baka ma'ana. Are You telling me kazo gurin yarinyar da zaka aura and the first thing da kake kokarin tambayar ta shine ko ta san dangin tsohuwar budurwar ka? Does that even makes sense to you?" Gidado ya dauki robar ruwa ya bude ya daga ya shanye gabaki daya sannan ya ajiye robar. Yayi murmushin takaici yace "maybe I am loosing my mind. But yes. To me everything relates to her. Nothing makes sense to me in dai ba'a haɗa da ita a ciki ba" Al'ameen yace "then I don't think you are fit to marry " Gidado yace "ha! Finally someone ya fahimta. Go and tell that to Abba and Mama watakila su ma su fahimta" A dai dai nan Safina ta dawo hannunta rike da sabuwar serviette. Ta ajiye a gaban Al'ameen amma shi kuma sai ya mike. Tace "ba ka ci samosar ba" ya kalli samosar, shi ya manta ma ta ajiye masa, yace "thank you, zan dan je waje ne inyi waya" yana fita ta zauna akan kujerar da ya tashi daga kai tana kallon Gidado cike da damuwa tace "Habibi, kamar ba ka jin dadi ko? Ko tafiyar ce ta gajiyar da kai?" Ya dan juyo ya kalle ta "am fine. Kar ki damu. Yanzu zamu ga su baban? Gwara mu gama mu zo mu tafi" Ta dan bata rai "tafiya fa ka ambata, yanzu fa kuka zo and ko gaisawa bamu yi ba sosai musamman tunda yau muka fara haduwa. Ya kamata mu danyi hira ai ko?" Ta karasa tana langwabe kai gefe. Ya gyara zamasa yana kallon ta yace "hira? Okay what do you want us to talk about?" Tace "at least ka fada min ya ka ganni? Tunda yau ka fara ganina. Gwara in san cewa nayi maka ko ban yi maka ba. And maybe tell me abinda yake damunka, watakila ina da maganin sa" yace "does that really matter? Kina ganin ra'ayi na akan ki yana da muhimmanci?" Ta mike ta ta bi ta gabansa zuwa inda kayan abincin suke ta zubo masa juice ta hado da snacks a plate ta dawo inda yake ta durkusa a gabansa ta mika masa juice din sannan ta koma ta zauna ta dora snacks din akan cinyarta tace "ra'ayin ka a yanzu shine yafi komai muhimmanci, musamman ni a gurina. Abinda kake so shine abinda zan saka a gaba na, abinda ba ka so shine abinda zan fi ki fiye da komai" yace "tell that to my parents" ya kurbi juice din ya ajiye yace "send me your account details, zan turo miki kuɗin da zaki yi hidima, am sure kina shirya wani abu da kike so kiyi. And if you need anything, message me". Ranta ya baci har fuskarta ta nuna, tace "yanzu dai ba zanji cewa nayi maka ko banyi maka din ba? Duk wannan kwalliyar da nayi?" Ya mike tsaye "ban boye miki komai ba Safina. And you agree to take your chance with me. Wannan shine dai dai lokacin da zaki fara hakurin da kika yi alkawarin zaki yi" ta mike ita ma "kayi hakuri. Kar ka bata rai dan Allah. Kawai dai kasan mu mata muna da son yabawa, and when I walked in I noticed kana ta kallona, I thought na samu wani bangare na zuciyar ka" ya juya yayi hanyar fita, har ya kai bakin kofa sannan ya juyo yace mata "I was looking at you because I thought you were someone else, it turned out ba ita ce". Sai ya juya ya fita. A waje ya hango Al'ameen yana waya, ya tafi gurinsa ya tsaya har ya gama, ya fahimci cewa da matarsa Humaira (read *Aisha Humaira*) yake magana saboda yadda yake ta zabga murmushi shi kadai, love is truly the most beautiful feeling ever. Sai da ya gama sannan ya juyo yana kallon Gidado yace "wai fitowa kayi ka bar ta ita kadai?" Yace "kai ma ba fitowa kayi ka bar ni ni kadai da ita ba?" Al'ameen ya danyi dariya "guri fa na baku ku gaisa sosai" Gidado yayo dan karamin tsaki "I can't stay inside with her. It is suffocating". Haka suka cigaba da tsaiwa a waje duk su biyun, har sai da Mustaphan da ya dauko su dazu yazo yayi musu magana sannan suka koma ciki tare, basu tarar da ita ba. Ya zauna ya saka su a gaba sai da suka dan ci abinci kadan sannan ya nuna musu toilet suma yi alwala suka zo suka yi sallah, daga nan kuma ya fita sai gashi sun dawo tare da manya su biyu, wadanda duk suka baiyana wa su Gidado kansu a matsayin wan baban Safina da kuma kanin sa, suka tabbatar musu da cewa suna goyon bayan auren suka kuma bawa Gidado assurance ɗin cewa ba zai samu matsala da Safina ba. "Tun tana jaririya mahaifinta ya rasu. Ni na rike ta tamkar ni na haife ta, ko bayan aure gurin na zaka zo akan duk wata bukata, kar ka yarda wani daga baya ya fito yazo yace maka shine yake da iko a kanta. Mune dangin ubanta mune komai nata" Babban cikin su ya faɗa. Da zasu tashi Al'ameen ya ajiye musu kudi masu kauri yace su sayi turare Sai da zasu tafi sannan Gidado ya tuna da sakon ta da Mama ta bashi ya kawo mata, ya mika wa Mustaphan da yake tare da su yace ya kai mata, yayi dariya "kai dai kawai kace inje in kira maka ita kuyi sallama" ya kira wata yarinya "je ki cewa Safina tazo angonta yaƙi tafiya yace sai ya ganta". Ba'a jima ba ta fito, ta yafa mayafi sosai wannan karon ta rufe jikinta. Gidado ya mika mata ledar hannunsa "inji Mama" ta karba tana murmushi "Nagode sosai. Zan kira ta inyi mata godiya" yace "good. Mu zamu tafi. Ki turo min sakon da nayi miki magana a kansa" ta girgiza kai "no ka barshi kawai. I already made plans" ya daga kafada "okay. Alright" har ya juya ssi kuma ya dawo "I just heard cewa babanki ya rasu, you never tell me" ta daga kafada itama "you never ask" yace "maman ki kuma fa?" Tace "tana Abuja. Da ya rasu ta koma gurin sister ɗin ta a Abuja. Yanzu ma tana can. A can zan sauka lokacin bikin. A can zata yi nata taron" ya gyada kai. "Okay. Alright. Am sorry for your lost. Allah yaji kansa" ta langwabe kai "Ameen. Na kusa daina maraici ai. Insha Allah. Am sure mijina zai kula da ni sosai". Har suka je airport basu yi magana da junan su ba, har jirgin su ya tashi ya kuma sauka a Abuja basu tattauna akan komai ba. Gidado was consumed in his thoughts yayin da shi kuma Al'ameen ɗin ya rabu dashi dan ya fahimci baya cikin mood din maganar. Sai da suka sauka suka shiga mota zasu je gida sannan Gidado yayi wa Al'ameen magana "Ya Ameen, please tell me the truth, do you think I am loosing my mind and imagining things?" Al'ameen ya rage gudun da yake yi yace "i don't think you are loosing your mind. But I believe you are overthinking everything" Gidado yace "then advise me? How can I stop thinking? How can I stop thinking about her?" Al'ameen yace "I am not expert in this thing, amma ina ganin you need to get something that will keep you busy, wani abu da zai dauke maka hankalin ka daga tunani, maybe shine dalilin su Abba na yi maka aure thinking matar zata dauke maka hankalin ka, but I advise ka samu wani abu ka dinga yi, ka daina zama kai kadai, ka gajiyar da jikin ka da ƙwaƙwalwar ka yadda ko dare ne yayi kana kwanciya zaka yi bacci. Sannan get rid of anything da zai ke tuna maka da waccan yarinyar" Gidado ya danyi murmushi yace "I tried doing that. But she is everywhere. Har cikin bacci na take shiga. I always dream about gani na da ita na karshe. And the more I saw her a cikin mafarkin the more I feel the need to get back to her. Gani nake kamar kokarin mantawa da ita da nake yi yanzu ba dai dai bane ba. Gani nake kamar nayi betraying dinta, she needed me and I shut the door on her face" Al'ameen ya tsayar da motar ya juyo sosai yana kallon sa "I can't believe this. You betrayed her fa kace? How? I thought ita ce ta yaudare ka ta saka kuka yi soyayya alhalin tana da aure? Ko kayi bincike ne ka ga cewa bata da auren karya take yi?" Gidado yace "she is married. Wannan bani da shakku akan sa a yanzu. But ....." Al'ameen ya bude hannu yace "but what Muhammad? She is married and pregnant for her husband. Kai kace min kaga cikin da idonka. For God's sake stop creating things in your head and blaming yourself alhalin kai ne victim din" Gidado ya dago kai yana kallon Al'ameen da wani irin kallo yace "ranar da tazo gurina na karshe, ranar da ta gaya min cewa tana da aure. She looked broken, sad, and devastated. She looked like a shell of her former self. Akwai wani abu da ya faru da ita, wani abu da ya mayar da ita haka. Ba haka take ba. She was the most cheerful person I have ever seen. And sanda na kore ta daga office ɗin, ta tsaya a bakin kofa ta miko min hannu and called my name, kamar tana neman taimako daga gare ni, but i did not listen. I shut the door. And now duk sanda na rufe ido na scene din da nake gani kenan. Har cikin bacci na nake jin tana kiran sunana" Al'ameen ya dafe kansa tare da rufe idonsa, Gidado yace "you really think I am loosing my mind, right " Al'ameen ya bude idonsa yana kallon Gidado yace "no. I think you love that girl too much, and I think you need to see a therapist, you need to see Mammy". Gidan su Gidado suka fara zuwa, suka yi packing Gidado ya bude kofa ya fita sai kuma ya dawo ya zauna yana kallon Al'ameen yace "one more question, ka taba ganin Safiyya, do you think she loved me ko kana ganin tun a lokacin she was playing me?" Gidado yace "guy! Anya kuwa kana kallon kan ka a madubi, anya ka fahimci irin haduwar da kayi? Bana jin a duniya da akwai wata ya mace mai jini a jika da zaka ce kana so kuma ya kasance bata son ka. Tabbas a lokacin da na ganku da Safiyya tana son ka. But that doesn't matter now. Don't tell that matter". Gidado yayi murmushi fuskarsa tana nuna jin daɗin maganar yace "thank you ɗan uwa, I really appreciate this". Forgive the typos please Dan Allah kar kuce yayi kaɗan 😅🤫 Littafin Safiyya is 500 naira via 0779484494 Nafisa Tafida Usman Access Bank Send the evidence via telegram or WhatsApp to 0704 203 0419 Posting of paid episodes will be on telegram only. Nagode sosai. I really appreciate all the love. ❤‍🩹*Safiyya*❤‍🩹 *By* *Maman Maama* *Episode Thirteen: One Day Apart* Free Episode Littafin Safiyya is 500 naira via 0779484494 Nafisa Tafida Usman Access Bank Send the evidence via telegram or WhatsApp to 0704 203 0419 Posting of paid episodes will be on telegram only. Kwana biyu bayan zuwan su Katsina, Gidado ya saka Safina ta turo masa address ɗin matar da aka ce yaje ya gaisar anan Abuja, sunan ta Hajiya, kuma kamar yadda Safina ta gaya masa mahaifiyar ta ma tana tare da Hajiyar a lokacin. Dan haka ya shirya ya ɗauki Haidar suka tafi tare. Tun daga gate ɗin shiga gidan suka fahimci cewa wannan gidan masu kuɗi ne, real kuɗi, tsohon kudi. A bakin gate mai gadi ya tambaye su gurin wanda suka zo, Gidado yace "Hajiya, ina fatan tana nan ai ko. Am sure ta san da zuwan mu" maigadin yayi murmushi yace "ko sirikin na mu ne? Tun safe Hajiya tace zata yi bako, tace mai neman auren Safina ne zai zo, ai Mommyn Safina ma tana gidan. Allah ya sanya alkhairi ya sa da mu za'a yi" Gidado ya danyi shiru yana kallon sa, babba ne sosai kuma daga ganin sa kasan ya san jiya ya kuma san yau, irin masu aikin gidan nan da suka zama yan gida. Sai yayi amfani da damar sa yayi kokarin sanin wani abu akan Safina. "ka san Safina kenan sosai" mai gadin yace "sosai ma. Safina ai kamar jika take a gidan nan. Mahaifiyar ta ma a gidan nan ta tashi tun tana karama har aka aurar da ita har yau kuma nan shine gida a gurin ta. Ai yayar mahaifiyar ta ce matar gidan nan. Kuma tunda ita ta rike ta sai ta zama kamar ƴa ce a gidan. Safina kuma kaga ta zama jika ce. Kai kuma ka zama sirikin mu. Allah dai ya sanya alkhairi" Gidado yayi murmushi "na kusa zama. Not yet. Nagode Baba. Ameen. Dan Allah a sanar musu mun zo" Mai gadin ya bude musu gate suka shiga da mota sannan ya kira wata yarinya da tazo wucewa yace ta je ta gaya wa Hajiya baƙin ta sun zo. "Saurayin safina ne?" Yarinyar ta tambaya cikin rada amma su Gidado sunji, mai gadin ya fara yi mata fada "maza ki tafi aiken da nayi miki, ku baku da aiki sai shegen tsegumi". Su Gidado suka fito daga motar a tare, Haidar ya zagayo side ɗin Gidado yace "tana nan ne?" Gidado ya kalle shi yace "wa?" Haidar yayi murmushi "ita ɗin dai" Gidado ya bata rai "zaka koma gida wallahi" Haidar yayi dariya "wai naga sai wani bobboye ta kake yi ne. I just want to see her in lissafa mata irin abubuwan da nake so da kuma wanda bana so. Kasan ana gama bikin ku can zan koma. Though ba Safiyya bace ba amma wancan alkawarin bai karye ba. Har na zaɓi daki ma" Gidado yace "tsakanin ku ne wannan, ni ina ruwa na?" Haidar yace "to ai baka haɗa ni da ita ba dan haka akwai ruwanka a ciki, dole kai zan bawa sako ka isar mata. Ina fatan ta iya girki, ina nufin girki irin five stars standard ɗin nan". Kafin Gidado ya bashi amsa aka yi musu magana aka ce su shiga. Suka jera suka tafi, sai Gidado ya samu kansa da murmushi yana tuno irin soyayyar da take tsakanin Safiyya da girki. She and Haidar would have been friends. She even promised him that. Ya tuna da wani lokaci da tayi wannan alkawarin. ****.     ****.     ****.     ****.     ****.    *** Waya suka yi da safe a muryarsa ta fahimci cewa he was stressed. Da ta tambaye shi dalili sai yayi mata complain cewa aiki ne yayi masa yawa a office, har zuwa rana ma da suka kara wayar still bai kammala aikin da yake yi ba. Da yamma sai gata ta baro hostel dinsu ta dauko motar ta tazo har office ɗin sa ta kira shi a waya tace ya fito ya ga wani abu. He complain cewa aiki yayi masa yawa amma shi kansa ya san cewa ba'a cewa Safiyya "no" dan yanzu sai ta saka masa kuka. Dole ya rufe office ya fito ya same ta a mota, ta bude masa gaba tace "get in" ya shiga yana kallon ta "what?" Tace "to ka rufe motar mana so kake mutanen da suke waje su ga abinda zan nuna maka. Sirri ne" yayi ajjiyar zuciya "Piya! Aiki nake yi wallahi. Dole a yau zan gama aikin nan kuma ko rabi ban yi ba. Ko kina so a kore ni ne?" Tace "waye zai kore ka? Abba ko uncle Habib? You own dis school. Oya, close the door" ya jawo kofar ya rufe "yes ma'am" sai kawai gani yayi ta saka mota a giya ta fara tafiya, ya bude ido "what are you doing Piya? Ina zaki kai ni?" Tace "I am kidnapping you, kuma sai an biya ni ransom zan dawo da kai". Ya gyara zaman sa yana kare mata kallo, abaya ce a jikinta da mayafin abayar a kanta. Fuskarta fes babu kwalliya, fatarta kamar kullum tana kyalli da daukan ido. Ta kalle shi ta gefen ido. "ka daina kallo na. Ko so kake inyi tuntube ne" yace "you are driving, not walking " tace "to in na buga motar fa?" Yace "tunda kin hana ni yin aiki na ba gwara in zauna inyi ta kallon ki ba, kar inyi biyu babu" tayi murmushi "believe me, you are going to enjoy this. Zaka gode Allah cewa I kidnapped you today" yace "zan rubuta a diary in ajiye wa yaran mu, in gaya musu maman su taje har office ɗina tayi man-napping ɗina" tayi dariyar kalmar da yayi amfani da ita a dai dai lokacin da suka zo gate din fita daga makarantar. Sai da suka fita yace "seriously, ina zaki kai mu ne wai?" Tace "park. You need a rest. I couldn't take jin ka a gajiye. It doesn't suit you" ya bude ido "baby ni namiji ne fa? Dole sai nayi aiki. In banyi ba da me zan kula da ke da yaran mu?". Sai da suka yi nisa sannan ya juya yana kallon seat din baya "wai abinci ne a bayan motar nan? Kamshi nake ji" tace "abinci ne mana. We are going to have a picnic. And I know ko lunch baka yi ba. Ya shafa cikin sa, ko breakfast din kirki bai yi ba kuma yanzu kamshin abincin ya kara masa jin yunwa. Ya juya yana kallon ta yace "you are amazing Piya. Thank you. Zan iya fara ci yanxu?" Ta girgiza kai da sauri "not in my car" ya daga hannu "nayi alkawari ba zan bata miki ba" and he knows he dare not. Dan muguwar tsafta ce da ita. A karshe dai haka ya hakura har suka je gurin. Shi yayi musu shinfida da abin shimfidar da tazo tashi, ita kuma ta jera musu abinci, sannan ta jera masa a plates ta ajiye masa a gabansa. Farko har zaiyi mata dariyar ta zuba masa da yawa, saboda shi ba mutum ne mai cin abinci sosai ba, amma yana ci tana bashi labarin dramar da ake a hostel dinsu bai san sanda ya cinye ba sai gani yayi tana kara masa. Ya hadiye lomar bakinsa yana jin daɗin abincin yace "Piya, duk sanda aka yi bikin mu, ina jin Haidar gidan mu zai dawo da zama" tana kallon sa itama tace "saboda me kace haka?" Ya nuna plate din abincin gabansa yace "abinci, saboda kaunar da yake yi wa abinci. Saboda ke kuma kin iya abinci" tayi murmushi fuskarta tana nuna jin daɗin maganar sa tace "bayan bacci, the second thing da na iya a rayuwata shine girki. I can cook. Irin I can really cook" yace "banda yabon kai dai. In mutum ya iya abu ai bari yake yi mutane su yaba ba wai shi ya zauna yayi ta yabon kansa ba" tace "saboda me? Abeg let me brag about my achievement tunda bani da abubuwan bragging for da yawa. I can cook. Na iya girki wato nake gaya maka" yace "there is something else da kika iya kuma ai, wanda ya kamata a baki medal a kansa" ta gyara zamanta tace "what? Tell me please, in kara shi akan list of achievements ɗina a rayuwa" yace "crying. You can cry for Africa. Ni ban taba ganin ma mai saurin kuka irin ki ba". Tayi dariya "haha. Duk kuka na ai mai dalili nake yi, is either an hana ni yin abinda nake so ko kuma an takura min sai nayi abinda bana so. In ba'a so inyi kuka kawai a barni in yi abinda raina yake so" yace "ai na fahimci haka. Kuma na fahimci laifin Daddy ne. Shi ya shagwaba ki beyond repair. Ni yanzu an barni da sabon raino. In mun haihu ban san wa zan goya ba, ke ko yaran" ta bata fuska "wanda kafi so. A lokacin zan gane matsayi na ai" yayi murmushi yana cin burger din daya ajiye masa a gabansa da zafinta, duk kuwa da cewa jin cikinsa yake yi kamar zai fashe. Yace "wai in tambaye ki Piya, yanzu in muka haihu, in yaron yana yi miki kuka ya zakiyi da shi?" Tayi shiru tana tunani sannan tace "zama zanyi nima in yi masa kuka" ya ajiye burger din yana dariya sosai, sai da ya gama sannan yace "I can't wait for that time. You will look so cute with kids" tayi murmushin ta mai kyau tace "I can't wait either. I love kids. Ban san yadda ake musu ba saboda gidan mu babu yara but I will learn. I will be the best Mom ever". Sai da suka gama cin abincin sannan ya kira Haidar a waya. "albishirin ka. Ka kusa barin gidan Abba. Dan na tabbatar duk sa da akayi bikin mu da Safiyya gida na zaka koma" Haidar yace "saboda me?" Gidado yace "saboda ta iya girki. Kuma tana kaunar girki. She will just keep feeding you har sai ka kasa tashi. Nima abinda ya faru da ni kenan yanzu" sai kuma ya mika wa Safiyya wayar "gashi yace in baki" ta bude ido tana girgiza kai "in kuma suna tare da Mama ko Baba fa? Ai sai suce bani da kunya" yace "shi kadai ne fa" tace "to in ya basu labari fa? In yace musu munyi waya fa?" Gidado yayi ajjiyar zuciya "ba zai fada ba, zan gaya masa kar ya fada" ta langwabe kai "kayi alkawari?" Yace "yes, nayi alkawari" sai ta karbi wayar ta saka a kunnen ta, taji muryar Haidar yana dariya yace "nima nayi alkawari" sai taji kunya ta rufe fuskarta kamar yana gurin. Suka gaisa, yana ta tsokanar ta, sannan a karshe tayi masa alkawari "ka kusa dawowa gidan yayanka da zama. Kai zaka fara zabar daki a gidan. Abinci kuma sai wanda ka zaba za'a ke girkawa a gidan". Sai da suka gama wayar ta mikawa Gidado sannan taga ashe shi kallon ta yake tayi, ta sunkuyar da kai tana jin kunya yace "you know what? I am glad you kidnapped me. And I am looking forward to you kidnapping me again. I get to look at you instead of papers. ****.    ****.    ****.    ****.    ****.    ****.    Suna shiga cikin gidan wani katon parlor aka kai su. Suka zauna aka fara hidimar kawo musu fruits da snacks da drinks iri iri. Haidar zai fara ci Gidado ya harare shi sai ya koma ya zauna yana bata fuska. Basu jima ba wata dattijuwar mata ta fito tare da wata yar budurwa, yarinyar ta taimaka mata ta zauna a kasa sai su Gidado suma duk suka sauko suka zauna a kasan. Tace "bana iya zama kan kujera yanzu, ciwon kafa ya sako ni a gaba. Kun san jikin tsufa. Ko da yake ku ba zaku fahimta ba". Suka yi murmushi sannan suka gaishe ta a tare, ta amsa musu da sakin fuska sosai tare da tambayar su mutan gida. Ta nuna Gidado tace "na gane mai gidan nawa, waccan marar kunyar ai takanas ta aiko min da hotonsa ta waya wai ta samu mijin xa yafi nawa kyau, ni kuwa na san ko a yanzu kuka jera kai da Alhaji sai yammata sun dauki Alhaji sun barka" ta karasa maganar tana dariya. Suma suka yi murmushi. Ta cigaba "naji daɗin zuwa da kayi ka gaishe ni, hakan yana nufin ka girmama ni kenan. Ina kuma so ka dauke ni tamkar uwa ba ma kaka ba, ni uwar kowa ce. Ni ka ganni nan Allah bai bani haihuwa ba amma kuma yayi min baiwar mutane. Wannan ya sa gashi dai shekarun girma sun zo min amma bana kukan rashin yaya, yaran da na rike sun zama gata na. Yayan yanuwana da na mijina duk dauka nake yi in rike su kamar ni na haife su, sannan kuma in debo marayu in rike su suma in basu duk kulawar da ya dace iyaye su bawa yaya, ko yan aiki aka kawo min na lura basu da cikakken gata a gidajen su sai in mayar da su yayana in rike su har in aurar da su. Ba zan iya lissafa yan aikin da na rike ba, tun daga kan Safiya har zuwa wannan yarinyar ta gaba na Lubabatu. Allah sarki Safiya Allah ya kai rahama kabarin ta. Duk da bata raye amma har yanzu ina morar gatan da na yi mata". Su Gidado suka ce "Ameen" ta cigaba "ina gaya maka wannan ne dan ka saki jikin ka, nan gidan mutane ne, kowa kuma namu ne ballantana kai da aure zai hada mu. Ka fahimta ai ko?" Gidado yayi gyaran murya yace "na gane. Na gode kuma sosai. Allah ya kara lafiya" tace "Ameen ya Rabbi. Ai an gaya min cewa kai jika ne a gurin marigayi ambassador Muhammad Dikko. Mutumin kirki. Allah ya kai rahama kabarin sa. Na san shi ai lokacin da yana da rai, na kuma san matarsa Hajiya Fatima, ban sani ba ko zata gane ni amma in kaje kace mata Hajiya Maryama matar Alhaji Nasiru Atafi tana gaishe ta" Gidado yace "insha Allah za'a gaya mata". A lokacin wata mata ta sauko daga sama, kallo daya Gidado yayi mata ya fahimci cewa ita ta haifi Safina, kamar su daya sai dai safina zata fi ta farar fata sannan da kuma bambancin shekaru. Ta zauna akan kujera a gefen su Gidado, suka juya suka gaishe ta ta amsa musu babu yabo babu fallasa sannan tace "sai yau ka samu damar zuwa gaishe mu kenan". Hajiya tace "menene haka Sa'adatu? Tunda yazo ba shikenan ba?" Tace "ni kinsan bana barin magana a ciki na. Amma muna gari daya ace sai few days to auren Safina sannan zamu ga mijin da zata aura? A hakan ma kuma sai da nayi waya nayi wa mahaifiyar sa korafi sannan yazo, da bai yi niyyar zuwa ba ai. Da sai dai ranar bikin muma mubi cikin mutane muna tambayar ina angon yake" Hajiya tace "tunda dai ita amaryar ta san shi ba shikenan ba?" Sai kuma ta juya gurin Gidado tace "rabu da ita, ita in dai idonta ya ga abu sai bakin ta yayi magana, haka halinta yake, zaka saba da ita a hankali. Tana da kirki sosai sai dai zaka sha faɗa" Mommy tana daga gefe ta kuma cewa "an anyi abu ba dai dai bane ba ai nake yin fadan" Hajiya ta chanza maganar ta hanyar yi musu korafin ba su ci komai da aka kawo musu ba, su kuma suka bada uzurin cewa sunci abinci a gida kafin su fito. Amma duk da haka sai ta saka aka kwashe komai da aka kawo musu aka kai musu mota. Da haka suka yi musu sallama suka tafi. Suna shiga mota tun kafin su bar gidan Haidar yace "I don't like wannan surikar taka" Gidado yace "that makes the two of us" bayan sun dauki hanya kuma sai Haidar ya fara dariya yace "ka san tunanin da nayi, ina ma ace tare da Aunty Hafsat muka je gidan nan matar nan tayi mana wannan mulkin" Gidado yayi murmushi yace "da anyi yaki kuwa. She will humble her. Zan so inga yadda zasu kare da bikin nan". *Her* 🧕🏻 Kwanaki suna ta tafiya har ya rage saura sati biyu lokacin da likita ya saka za'a yi min aiki yayi, amma sai naji sam bana jin tsoron aikin da za'a yi min ban damu da cewa wai cikina za'a yanka a fito da ɗan mutum ba, ni dai kawai burina shine in rabu da mayataccen cikin nan ko na samu in shaki iska mai daɗi, ko na samu in dai na ganin disappointment a fuskar Daddy a duk lokacin da ya kalle ni, ko na samu in manta da abinda ya same ni. Sai dai ni kaina na san cewa rabuwa da cikin ba zata taba goge abinda ya faru daga zuciya ta ba, babu abinda zai fari da zai saka in manta da abinda aka yi min. Zalincin da aka yi min. Babu kuma abinda zai saka in yafe wa wanda yayi min. Har abada. A lissafin Daddy naji yace aiki na zai kama washegarin daurin auren Safina. Ni kam ban ma rike date din da aka saka na auren Safina ba. Dan ni ba ma na gane ranaku a yanzu. Akwai kawayen mu da yawa da suke ta yi min magana a chats akan bikin Safina, ni kuma na kan basu amsa da cewa nayi tafiya jinyar Daddy dan haka bana nan za'a yi. Safina kam sai shirye shiryen ta take yi. Ta kan turo min pictures na kaya tace in taya ta zaba, har kayan da zata saka na kowanne event da zasu yi sai da ta turo min, sometimes na kan yi ignoring dinta dan ni abinda yake gaba na yafi karfin zaban kayan sawa, sometimes kuma sai in bata amsa dan kar ta ga kamar dan nasan kudin indirectly daga gurina zasu fito shi yasa na ke wulakanta ta. Kamar yadda nayi tunani, su yan uwan nata da ta tafi Katsina gurin su dan suyi mata aure babu abinda suka yi mata na kayan daki, haka a dole Mommy ta sauko daga fushin da tayi da Daddy ta dame shi da waya akan ya bada kuɗin da za'a yi wa Safina kayan daki, direct yace mata bashi da kuɗi, besides, ai tace masa Safina ba yar sa bace ba. Sai ta koma gurin Uncle Ahmad shi kuma yace mata ta tambaye ni amma sai ta kasa tambayar tawa ta cigaba da bin Daddy, har sai da Daddy ya tabbatar tayi laushi sannan yace da Uncle Ahmad ya bata. Haka suka yiwa uncle Ahmad bill tun daga kan kayan daki har zuwa kayan da zasu saka na fitar biki, shi kuma ya raba biyu ya basu rabi yace ba zai bayar ga baki daya ba. A lokacin ne Safina ta yi min dogon message akan maganar, wai uncle Ahmad zai saka suji kunya, wai tun yanzu ya fara nuna musu cewa su ba yanuwan mu bane ba, dan Allah inyi masa magana. Banyi masa magana ba sai na yiwa Daddy magana, tunda na fahimci shi sulhu yake so yayi a tsakanin mu shi kuma uncle Ahmad so yake a raba gari kowa ya kama gabansa. A ƙarshe dai Daddy ya saka Uncle Ahmad ya cika musu kuɗin suka yi duk siyayyar su suka gama. A ranar da yake saura sati daya aikina, na tashi da safe kamar yadda na saba na shiga kitchen na haɗa smoothie na sha sannan na shiryawa Daddy breakfast. Na dauka na kai masa dakinsa na tarar yana kwance idonsa a rufe amma daga gani na gane ba bacci yake yi ba. Na jawo table gabansa na dora abincin na zauna a gefe nace "Daddy ga breakfast. Ka tashi ka ci". Ya tashi zaune da kyar, na lura da effort din da ya saka yanzu gurin tashin yafi yadda yake yi da, ciwonsa yana kara cigaba a kwanakin nan fiye da yadda yake da. Ya zauna ya debi oats din dana dama masa a hankali ya kai bakin sa, na kara lura da yadda hannunsa yake rawa sannan da kuma yadda ya hadiye abincin da kyar. Ya lura da kallon da nake yi masa yayi gyaran murya yace cikin muryar da ta kara zama weak "doctor yace nan da wata uku, that's idan na kai nan da wata uku, I will be needing a feeding tube, ba zan iya cigaba da hadiye abinci da kai na ba. Kin gane?" na gyada kai na da sauri tare da sunkuyar da kaina ina kallon ciki na da yanzu baya boyuwa a cikin riga ta. Ya kira sunana "Safiyya" na dago kai na kalle shi yace min "don't cry" na sake sunkuyar da kaina ina jin hawaye na suna zuba kan cinyata. Nayi saurin goge su. Sai ya sake kiran sunana "Safiyya" na dago kai, yace "munyi magana da Ahmad, za'a daura auren ki da Mukhtar washegarin da akayi na Safina, in anyi miki aiki da safe, da yamma za'a daura miki aure. Saboda baƙin da zasu zo na Safina ba sai sun koma ba sai a daura naki. Do you understand?" Na sake gyada kaina ina rike hawayena. Sai na mike na yi hanyar fita, har na kai kofa ya sake kiran sunana "Safiyya " na juyo yace "kin fahimci dalilin yin auren nan ko?" Na sake gyada kaina ban ce komai ba na fita da sauri. Daki na na wuce da sauri na rufe kofa sannan na zube a kan carpet din gaban gadon dakin na fara rera kuka. Kukan abubuwa da yawa. Kukan da ban san ranar da zan daina shi ba *❤‍🩹 Safiyya ❤‍🩹* *By* *Maman Maama* *Episode Fourteen: Consolations* Free Episodes One more Free Episode remains 😃 Send your 500 naira to 0779484494 Nafisa Tafida Usman Access Bank And send the evidence through telegram to 0704 203 0419 And enjoy the tell of Safiyya and Gidado. Posting is on telegram only. Na jima a zaune a wannan halin, sai naji alamar an bude kofar dakin an shigo, ban dago kai na ba amma a raina na san waye saboda mu biyu ne kadai a cikin gidan, besides, motsin wheelchair dinsa daban yake da motsin tafiyar sauran mutane. Ban juya na kalle shi ba amma nayi kokarin sassauta kuka na tare kuma da kokarin goge goge hawaye na. Ya jima anan a zaune yana kallo na sannan yace "I knew it. Dana na san kina nan kina kuka. But what I do not know is kukan menene kike yi? Uhmm, fada min, kukan me kike yi". Na cigaba da goge fuskata da bayan hannun rigata, ina jin yadda already fatar idon ta kumbura. Ya sake tambaya, "ina jin ki? Kukan menene kike yi?" Nace "I want you to get better. I need you to get better" yayi shiru na wani lokaci sannan yace "you know it is not going to happen. Sai kuma menene again?" Na girgiza kaina "shikenan dama. Shine kadai abinda nake yi wa kukan" yace "liar. You are also crying saboda maganar auren ki. Haka ne?" nayi shiru banyi magana ba. Ya sake tambaya ta "ba kya son auren Mukhtar? Kina so a fasa yi da shi?" Nayi shiru still ban ce komai ba. Ya zagayo kujerar sa gaba na yace "Safiyya. Ina so inyi miki aure kafin in tafi in barki. Idan na mutu na barki babu miji this people will tear you apart. Kuma dole in aura miki wanda ba za'a yi bincike ba ballantana a tono abinda ya faru da ke. Wannan ya bar ni da very limited options. I gave you the options. And you chose. Wanda kika zaba ba shi zuciya ta take so ba, ni zuciya ta tafi yarda da ki auri Mustapha. But you adamantly chose Mukhtar. And now you are crying. Tell me why". Na dago ido na ina kallon sa "Daddy, me yasa kake son Mustapha?" Yace "saboda a hannuna ya tashi, ni na bashi tarbiyya. Saboda mahaifiyarsa ce ta raine ki, ita ta baki tarbiyya. And sometimes family means more than blood. Sa'adatu will never harm you. But I am not so sure about Ahmad" Na dauke kaina gefe nace "you know what they want" yace "and what makes you think cewa su Ahmad ba the same thing suke so ba?" Nayi shiru ban ba shi amsa ba sai ya sake cewa "a rayuwa Safiyya, most of the relationships if not all da zaki shiga, ko ta auratayya ko business ko zamantakewa to trade by batter ake yi, to get something you have to give something. The best logic is ki san abinda mutum yake so daga gare ki, and then use that to get kema abinda kike so". Nace "Amma Daddy Mustapha fa..." Yace "he didn't do it. Ban san how many times zan gaya miki ba. He didn't do it" nayi shiru ban ce komai ba, bana son gaya wa Daddy abinda Mustapha yayi, bana son inyi using the only card din da nake amfani da shi gurin taming Mustapha. Jin nayi shiru bance komai ba sai yace "are you changing your mind or not?" Na goge hawaye na tare da girgiza kaina "no. Am not. Ina neman alfarma dai guda daya. Dan Allah Daddy bana son komawa Nigeria. I want to live here. Or somewhere else. Anywhere that is not Nigeria". Ya juyo yana kallona, sai kuma ya juya kujerar sa yayi hanyar fita ba tare da yace min komai ba. Har ya kai bakin kofa sannan ya juyo yace min "about Mukhtar, ko da ana gobe daurin aure ne in kika chanja shawara let me know ni kuma zan tsayar da maganar". Ban amsa ba nima har ya fita, ban kuma bar space a zuciya ta da zan yi tunani akan maganar ba. Na riga na yanke shawara and I am not going back on it, duk kuwa da zafin da zuciya ta take yi min akan hakan. Yana fita waya ta ta kama kida, na san waye tun kafin ma in kalle ta dan mostly ya kan kira ni by this time. Sai dai sam bana son daukan wayar ta sa. Zuciya ta bata so. Sai nayi murmushi ina mamakin rayuwa ta, yanzu na gama ja in ja da Daddy a kan sa, akan nace shi zan aura, amma kuma still zuciyar ba son sa ta ke yi ba. Har ta katse ban dauka ba sai da ya sake kira sannan na dauka. Na saka wayar a kunne na banyi magana ba yace "ko baccin ne dai? Na ga alamar ke ba kya gajiya da bacci" nace "na tashi, kawai dai yau na tashi bana jin dadi ne" yace "ni kuma yau cikin jin dadi na tashi. Have you heard the good news? In the next eight days you are going to be my bride. Duk da dai su Daddy suna ta insisting babu taron biki, but I want us to have ko da yar walima ne haka in kin dawo nija...." Nace "yaya Mukhtar, I am sorry, but I don't want any walima dan Allah. And I also don't think zan dawo Nigeria." Yace "why not? Fiyya komai da ya faru ai ya wuce kuma. Daga anyi daurin auren nan shi kenan we will put everything behind us muyi facing sabuwar rayuwar mu and the ways to build a new family ko? Gashi ma Allah cikin ikonsa we will soon have a child to start the family with. Abeg, ki shafa min kansa ko kanta and tell them they are already loved at home". Abinda ya fada was supposed to made me feel better amma sai naji raina ya baci dan a lokacin bayan uban dan cikina babu abinda na tsana sama da dan cikin nawa. Amma sai na daure zuciya ta nace "kayi hakuri yaya Mukhtar. I can't. Abun zai wuce physically, but the trauma will always haunt me, and the best thing to do idan mutum yana son moving on from a traumatic experience is to change environment. Idan na dawo Nigeria ba zan iya bawa family na kulawar da suke bukata daga gare ni ba" yace "kina ganin zaki ke tunawa da shi ne?" Nace "not just him. Zan ke tunawa da komai" amma a raina na san babban abinda nake gudu a komawa Nigeria shine Muhammad. A yanzu da na dan saka distance a tsakanin mu gani nake kamar na samu wata kariya daga ciwon son sa, amma ina komawa Nigeria na san zanji tamkar an rushe katangar kariyar ne, and there is a chance na cewa zamu iya haduwa da shi, and that would be a disaster. A haka dai ya hakura ya bar ni amma bai ce ya amince ba kamar yadda Daddy ma bai ce ya amince ba, ya dai ce min zaiyi tunani a kai. Daga ranar sai na kara cigaba da  lissafi na. Ina lissafa ranar aiki na kuma ina lissafa ranar daurin aure na. Safina kept calling me har sai da na daina daukan wayarta wai taji labarin daurin aure na and tana son mu shirya wani abu special ni da ita tunda muna da friends daya musamman yan secondary school din mu. Sai da taga na nuna mata bacin raina sosai sannan ta rabu da ni. Mustapha ma ya kira ni ban dauka ba, sai gashi ya turo min dogon message a Whatsapp wai yana yi min fatan alkhairi and he wants us to put everything behind us a cigaba da zumunci, and whenever I need a big  brother he will be there for me. A karshe ya kara da cewa duk sanda nake bukatar a dan sassama min Mukhtar I should just give him a call. Ya rage kwana biyar daurin auren Safina ni kuma nawa shida sai ga Mommy ta kira ni. Na dauka na gaishe and she lost the words to say to me, sai kuma ta kama fada "yanzu wato da ban kira ki ba ke ba zaki taba daukan waya ki kira ni ba ko?" Nace "kiyi hakuri Mommy" ta cigaba "na dauka a ranar da muka taho yarinyar nan a ranar zaki fara nema na amma ke ko ajikin ki ma sai kika cigaba da sabgar gabanki ko?" Nayi shiru bance komai ba, ta cigaba "ance min nan da six days za'a yi miki aiki. Kina shan magungunan ki dai ko?" Na ce "eh ina sha" amma a zahirin gaskiya rabon da insha magani tunda ta bar kasar. Tace "good. Ki kula da kanki. Ki kuma kwantar da hankalin ki, kin san a haihuwa babu abinda ake gudu irin hawan jini" na yi shiru ban ce komai ba sai ta sake cewa "ko ba ki auri Mustapha ba still ke ya ta ce" nace "Nagode Mommy". *Him* 👳🏻 Kwanakin sauri suke tayi a gurin Gidado, so yake su tsaya, dan ya samu at least ya shaki numfashi amma sun ki tsayawa and every day there is something to do. Gidan su already har ya fara cika da mutane musamman saboda bikin biyu za'a hada, gashi kuma bikin farko ne da za'a yi a gidan na su. Wannan ya saka a dole ya rufe dakin sa ya tattara ya koma gidan sa, gidan da aka fara siya masa yanzu kuma da ya takura aka sake masa wani. Babu shiri Haidar shima ya tattara nasa kayan ya bishi, duk da hakan bai yiwa Gidado daɗi ba dan yaso ya samu these days to himself dan in suka kare kuma shi kenan zai shiga cikin sabuwar rayuwar da bai ma san ta inda zai bullo mata ba. Yana sane yaje ya kamawa abokansa da suka zo gari musamman dan bikin hotel rooms duk kuwa da cewa akwai wannan spare gidan amma shi so yake ya zauna shi kadai. Haidar din ma sai ya bude masa part din da ya kamata ace shine nashi, shi kuma ya shiga wanda ya shirya saboda Safiyya. Ya san cewa hakan da yayi ba karamin emotional damage zai jawo wa kansa ba amma ya zabi hakan. Babu komai na furnitures a gidan dan haka sai katifu suka je dasu suka shimfida suke kwana akai, sai kuma boxes din kayan sawan da zasu yi amfani da su da sauran abubuwan da zasu bukata. Kullum da safe yake fita gurin hidimomin sa and they kept his emotions on check har sai ya dawo gida tukunna, shi farko ya dauka in ya gaji bacci zaiyi saurin daukansa kamar yadda Ya Ameen ya gaya masa, amma kuma sai ya ga shi ba hakan bane ba a gare shi. Ko ya gajin, in ya kwanta sai dai yayi ta juyi, amma bacci baya zuwa idanun sai gari ya kusa wayewa. Kullum a ransa babu abinda yake yin bita sai rayuwar sa da Safiyya, babu abinda yake so irin ya fahimci abinda yayi missing, ya fahimci inda hint din cewa tana da aure yake wanda yayi missing a baya amma ya kasa gani. Except kin kai shi gidan su da tayi. She kept on delaying and delaying giving all sorts of excuses. Farko excuses din nata akan cewa tana gidan uncle dinta ne kuma uncle din zai yi mata fada in ya ganta da saurayi because yana tunanin cewa bata isa yin saurayin ba, daga baya da ya fara nuna mata shi fa da gaske aure yake son yi, aurenta yake son yi, sai ta koma yi masa maganar rashin lafiyar babanta and the fact that baya zama a kasar sosai, and ranar nan da ya takura mata she said bata son ta kaishi gurin uncle dinta sai dai babanta, saboda uncle din yana son hada ta aure da dan sa Mukhtar. Ya san Mukhtar. Tun the second haduwar su da Safiyya ya san Mukhtar, kuma tun a lokacin jikinsa ya bashi cewa something was going on at least a zuciyar shi Mukhtar din, tun sanda ya ganshi din kuma yaji cewa baya son sa. Amma kuma a zuciyarsa ya san cewa kishi ne yake yi. Ya san cewa kishi yana daga cikin weaknesses din sa akan Safiyya, yana da mugun kishin da har tsoro yake bawa kansa sometimes, ya kuma san kishin nasa a yanzu yana daga cikin abinda yake cin zuciyarsa. The memory of her dauke da cikin wani, knowing fully well abinda ya faru kafin a samu cikin shine babban abinda yake hana mishi bacci a yanzu. A yau ma bai dawo da wuri ba sai late, hopping to fall asleep as soon as possible, yana shigowa ma da yayi packing bai shiga cikin gidan ba sai ya cire dogayen kayan jikinsa ya bar singlet ya zagaya bayan gidan yana jogging da niyyar karawa kansa gajiya. A bayan ne kuma yaga wani guri da Safiyya ta saka musamman ya ware mata bai yi paving ba "spices  zan shuka a gurin, akwai spices din da ba a samu sosai a kasuwa ko kuma ba za'a samu fresh one ba, to gwara in samu seeds ɗin su in shuka da kaina in ringa using". Ya tsaya a gaban clearing din yana hakin jogging ɗin da yake yi. "damn you. Damn you Safiyya" ya faɗa a fili, sannan ya wuce da sauri ya cigaba da jogging ɗin sa. Yana cikin haka yani alamar an buɗe gate, ya san Haidar ne ya dawo amma kuma baya son kowa yayi masa magana a yanzu, dan haka yayi sauri yayi kwana ya shige gidan ta kofar baya ya shige dakin da yake kwana. Direct toilet ya wuce ya kunna wa kansa shower ya rufe idonsa yana jin dadin sanyin ruwan. "Komai zafi bana iya wanka da ruwan sanyi, mura yake saka ni" Yaji muryar ta kamar a yanzu take gaya masa. Ya tuna da amsar da ya bata a lokacin. "Kar ki damu, zan koya miki ne. Ita kan ta murar sai ta hakura ta bar mu". Ya fita daga shower din ya goge jikinsa, yana kallon fuskarsa a mirror din toilet ɗin, "Da wata farar fuskar ka anan" yayi murmushi. "Burge ki tayi" Ya fito daga toilet din ya saka pajamas sannan ya ƙaro karfin AC ya kashe fitila yayi addu'a ya kwanta, hoping to center his mind on something important, anything apart from Safiyya, amma babu abinda ya gani a idonsa sai Safiyya da ciki a office ɗin sa. Babu kuma abinda yake son sani a lokacin sai abinda Safiyya take yi a wannan lokacin, babu abinda mind dinsa take saƙa masa sai different scenarios na abinda Safiyya take yi ɗin. Ya mike tsaye ya kara wa kansa fanka sannan ya koma ya kwantatare da zagaye kansa da pillows, few minutes after that kuma ya sake mikewa zaune ya jawo wayarsa ya nemo number ɗin Safina ya kira without realizing cewa karfe sha biyu ne na dare har da rabi. Sai da ta dauka sannan yayi realizing mistake ɗin sa. "Hello Habibi. Ba ka yi bacci ba?" Ya matsar da watar daga fuskarsa yace "shit!" a hankali cikin jin haushin kansa. Sannan yace "hello? Uhmm, I think I made a mistake ba wannan number ɗin zan kira ba" ta danyi shiru sannan tace "wa za ka kira to? By this time?" ya fara tunanin karyar da zaiyi, another of his weakness shine karya, bai iya karya ba kwata kwata. Yace "my friend, akwai wani friend dina Sahabi shi zan kira yanzu" ta sake cewa "by this time?" Yace "eh, baya bacci da wuri, nima haka" tace "ko dai ita zaka kira?" Ya dan bata rai "wa kenan?" Tace "your ex da ka fada min. Ko ita zaka kira Allah ya sa ka kira ni" ya danyi shiru sannan yace "I wish I can call her, there is nothing da ba zan iya bayarwa ba a yanzu to be able to call her. But she blocked my number. And beg me not to find another way to contact her. So to answer your question, ki kwantar da hankalin ki, ba ita zan kira ba". Tace "okay. Because I don't want to ruin the memory of the first time you call me da dare. Ba na son sunan wata ya shiga cikin memory din. It has always been a dream of mine. In ga ina waya da kai irin yadda yammata da samari suke yi" yace "I told you abokina...." Tace "right. At least let me pretend ni ka kira. And since you called ya kamata mu danyi magana ai ko? At least tell me something about you da kake ganin ya kamata in sani, maybe about your friends or family ko aikin ka, anything, just talk to me " yace "okay. Let me start with the things I like, I like honesty, na tsani karya. I like tsafta a lot. Bana son hayaniya, bana son mita, bana son tsegumi ma'ana telling me something that do not concern me. And most importantly, I love my family, a lot" tace "yauwa, about the family, ban san su ba sam in banda Mufida, ita ma kuma a waya ne kadai ko hoton ta ban taba gani ba, ya kamata in san su ko?" Yace "zaki san su ai. A hankali. But the immediate family basu da yawa, daga Mama sai Abba sai Haidar and then Mufida. I am the eldest. Akwai cousins da yawa. I can't list them all. You will get to know them watarana" tace "haka ne. And your friends, aside Sahabi" yace "waye Sahabi?" Tace "Sahabi dai da zaka kira yanzu" yace "ohh that Sahabi, Sahabi my friend. Yes, akwai Sahabi and the rest. Zaki san su suma later. Now, let me call Sahabi kafin yayi bacci". Tayi ajjiyar zuciya "okay, shikenan. At least we are one step ahead. Good night Habibi". Sai dai daya ajiye wayar, maimakon ya koma ya sake gwada baccin sai ya tashi ya zauna ya dauko takarda da biro a cikin takardun da Abba ya bashi zai yi cike cike na sabon aikin da zai fara, ya juya bayan takardar kawai ya kama zane a jiki, zanen fuskar Safiyya. Sai da ya gama zana ta tas kamar zaka kira sunan ta ta amsa, sai kuma ya dukunkune takardar yayi jifa da ita ya koma ya kwanta. Da safe bai tashi da wuri ba dan baiyi bacci mai nauyi ba sai bayan sallar asuba, ya manta cewa a ranar zasu fita da Abba maganar chanjin aikin sa. He is going to take over some parts of managerial work na Company ɗin Abba bayan bikin sa. Sai dai bai tashi ba har sai da Abban yazo gidan da kansa daukan sa kamar yadda suka shirya, ya kuma shigo har cikin gidan har dakin da yake kwance ya same shi yana bacci, takardar da ya gani a kasa ya sunkuya ya dauka ya warware. Sai ya samu guri a gefen katifar da Gidado yake kai ya zauna yana kallon zanen yarinyar da yake hannunsa. Gidado yayi juyi sannan ya bude jajayen idonsa ya dora su akan Abba, sai kuma ya karasa bude idon da sauri tare da mikewa zaune yana shafa fuskar sa a kokarin kore saurin baccin da yake kansa "Abba ka shigo? Ina kwana" Abba ya bishi da kallo sannan ya sake kallon takardar hannun sa. Sai lokacin Gidado ya lura da takardar, ya kara gyara zamansa yana shafa kai tare da kallon takardar da gefen ido. Abba ya nuna masa zanen tare da tambayar sa "Safiyya?" Gidado ya gyada kai bai ce komai ba. Abba ya nannade takardar ya ajiye a tsakanin su yace "ba ka son waccan yarinyar, zaka aure ta ne kawai saboda ni da mahaifiyar ka muna son kayi aure" babu alamar tambaya a cikin maganar dan haka Gidado bai bada amsa ba. Abba ya cigaba da cewa "abu na farko da na san ka riga ka sani shine we only want what's best for you. And right now, mantawa da wannan yarinyar shine the best thing for you" ya fada yana nuna zanen Safiyya with bitterness in his voice, abinda yake nuna irin haushin Safiyya da yake ji a ransa. Ya cigaba da magana, "mun yanke shawarar aure shine babban abinda zai taimaka maka wajen mantawa da ita maka kayi moving forward. Sai dai daga ni har mahaifiyar ka are not perfect, kuma bama ganin gaibu, zata iya yiwuwa abinda muka zaba maka ba shine alkhairi a gare ka ba, amma ni na san wanda yake perfect wanda kuma ya san gaibu, Allah. Ina son zan baka wani assignment, idan kayi shi dai dai zaka samu reward mai girma. Ina so kuma inyi maka wani alkawari. A cikin kwanakin nan da suka rage kafin daurin auren ka, ina so kayi istikhara, idan har kafin daurin auren ka cigaba da jin a ranka cewa still ba ka son aure to ka gaya min, ko da kwana daya ya rage zan dakatar da abin domin ya tabbata ba alkhairi bane ba. Amma idan kaji a ranka cewa ka amince kana son auren yarinyar, to sai mu cigaba da shirye shiryen mu har mu tabbatar da faruwar abin". Ya mike tsaye yana kallon sa yace "ka tashi ka shirya, your new job awaits you ". *❤‍🩹 Safiyya ❤‍🩹* *By* *Maman Maama* *Episode Fifteen: A Forever Thing* Free Episode Salam all 🙋🏻 This is the last Free Episode of Safiyya. To continue this journey with Safiyya and Gidado send your 500 naira to 0779484494 Nafisa Tafida Usman Access Bank Sai a tura evidence to this number through telegram 0704 203 0419 Posting of paid episodes will insha Allah only be on telegram. Please in kin turo evidence ta Whatsapp ban saka ki a group ɗin telegram ba to na duba ban ganki a can ba, ayi min magana ta telegram ɗin Please. Nagode. Nagode da soyayya. It means a lot to me. Nima ina son ku sosai. Gidado ya karbi shawarar Abba sosai, dan tun da suka yi maganar ya dukufa da yin adduoin neman zabin Allah. Babu dare babu rana. Ya kuma cigaba da shirye shiryen duk da suka kamata na bikin. Yan'uwansa sunzo na kusa da na nesa, maza da kuma mata. Da yake Abba da Mama first cousins ne sai ya zamana yan uwan duk daya ne babu banbanci, duk kuma treatment daya ake basu. Yan'uwansa samari da suka zo gari suka kuma fahimci a gidan da yaje ya boye kansa duk sai suka tattaro suka dawo gidan, sa'annin Gidado suna bangaren da yake while sa'annin Haidar suma suka tare a bangaren da yake. Gidado bai ji dadin haka ba saboda an takura masa an hana shi zama yayi hira shida zuciyarsa, shi da safiyyan shi. Sai dai kuma a wani bangaren yaji dadin hakan dan cikin kwanaki biyu kacal sai gashi yana hira da dariya sosai a cikin su. Wani lokacin idan suka nutse a cikin hira har mantawa yake yi da cewa wai aurensa ake yi, kuma wai baya son yarinyar da zai aura. Sai dai kuma yana iyakacin kokarin sa gurin danne wa dan baya son yanuwansa su fahimta har suyi ta yayata maganar a cikin dangi. Sai dai kuma yanuwan are making it extra difficult for him. Casually someone would ask him "ina yarinyar nan kuma da ka susuce akan ta kwanan baya?" His answer to that question was always "Allah yayi mata rasuwa" daga haka ba sa sake tambayar sa. In wani ma ya dauko tambayar sai a samu wani ya hana shi dan kar su taɓa wa angon feelings din sa. Sometimes kuma su kan tambaya "wannan gidan na ka ai yafi wancan girma Gidado, me ya sa ka chanja?" And shi kuma ya kan amsa musu da cewa "amaryar ce tafi son wancan". Alhalin ita amarya ko ganin gidan ba ta taba yi ba sai da masu yi mata jere suka je suka yi suka dauko mata pictures da videos. Gidan da za'a kai amaryar mai kyau ne, dan sosai iyayensa suka nuna masa gata a siyan gidan kamar yadda suke nuna masa gata a komai. Part dinsa daban na matar daban sannan a waje kuma akwai bangaren baƙi maza sannan da part din ma'aikatan gida (boy's quaters). A bangaren sa akwai bedrooms biyu da parlor, a nata bangaren akwai bedrooms uku da parlor. Part din baƙin kuma parlor ne karami da dakuna biyu. Kamar yadda iyayen ango suka yi kokari wajen kure adakar su akan gidan Gidado haka bangaren amarya su ma suka yi nasu kokarin, dan duk dakunan da suke part dinta babu inda ba'a cika shi da kaya ba, kaya kuma na gani na fada wa da suka yi dai dai kuma suka dace da tsaruwar gidan. Abin har sai da ya bawa dangin angon mamaki, dan a binciken da suka yi wa iyayen amarya basu samu labarin cewa suna da irin wannan kuɗin ba. A bangaren amarya tun a week to bikin Mommy ta tafi can Katsina suka cigaba da kammala shirye shiryen su, duk wani shiri da za'a yi wa amarya na gyaran jiki anyi wa Safina shi, ita kanta ta san tana da kyau, ta kuma shirya siye zuciyar angon na ta da wannan kyan nata da kuma duk kan wata kissa da kisisina da Allah ya halicci mata da ita. Ta san cewa akwai challenge a gabanta amma kuma ta shirya karbar sa hannu bibbiyu dai har zata samu muradin zuciyarta. Ta yarda da kalmar hausawa da suke cewa mahakurci mawadaci. Mommy tayi mata shirin duk da akeyi na gyaran amare dan taimaka musu wajen sauke hakkin aure da zai hau kansu, amma Mommyn ba ta san cewa ita ma da kanta Safinar ta gama siyan duk wadannan kayan har ma da wadanda suka fi na Mommyn. A shirye take tsaf da yin amfani da dukkan baiwar da Allah yayi mata wajen ganin ta mallaki Habibin na ta. Ranar Lahadi ta tafi garin Abuja. A ranar ne kuma bayan kiran wayar angon sau ba adadi kamar yadda ta saba kullum ba tare da kiran ya shiga ba sai ta tura masa message. "Na shigo Abuja. Dan Allah ka zo in ganka. Ina gidan Hajiya" Sakon ya shigo masa ya karanta ya rufe ya ajiye. A ranar da ya rage saura five days daurin aure ne gidan da angon ya ke ciki ya kara cika fiye da kullum, yan uwan sa da suka zo gari suma sun gayyato abokan su da suke gari, wasu abokan kuma sun gayyato nasu abokan. Gidan ya zama kamar wani dan karamin biki ake yi amma na maza zalla. Mama kuma ta daure musu gindi ta hanyar aiko musu da kulolin abinci kala kala. Daga nan sai hira ta balle, aka fara zancen aure da rayuwar cikinsa da challenges din sa, masu auren ciki suna baje fasahar experience ɗin su, yayin da samari suka baje kunnuwa suna daukan darasi. Wannan ya sa angon ya zame ba tare da sun sani ba ya fice ya bar musu gidan. Sai da ya shiga motar sa kuma sannan ya fahimci bashi da gurin zuwa, dan duk friends din sa da zai iya zuwa gurin su suna cikin gidan sa, a lokacin ne sakon Safina ya sake shigowa. "Na gama abinda zanyi a Abuja. Gobe aka ce in koma. Dan Allah ka shigo". Ya rufe idonsa yana tunani for some seconds sai kuma ya bude ya kira number ɗin ta. Tana dauka yace "gani nan zuwa" bai jira amsa ba ya katse kiran. Mintuna kaɗan suka kaishi kofar gidan, mai gadi ya taho da sauri da fara'a a fuskar sa amma sai Gidado ya bata rai tare da daga masa hannu alamar baya bukatar zuwan sa, sai da mai gadin ya juya sannan kuma sai yaji babu daɗi a ransa tunda mutumin bai yi masa komai ba. Ya dauko wayarsa ya sake kiranta "ina waje" yace tare da sake ajiye wayar. Few minutes sai gata ta fito. Jikinta sanye da hijab fuskarta babu kwalliya. Ta bude kofar gaban motar ta shiga ta zauna, sai ya dauke kansa yana jin haushin ta zauna a seat ɗin Safiyya. Amma kuma ai shi ya kira ta. And only God knows me Safiyya take yi with her husband, why won't him enjoy himself too? Ta fara mishi magana "har na fitar da rai na dauka ba zaka zo ba. But now I am glad tunda kazo" ya juyo yana kallon ta fuskarsa a matukar daure yace "me yasa kike nemana?" Tana kallon sa tace "what's with that face? Ko nayi wani laifin ne kuma ban sani ba, I just wanted to see you kuma banga abin laifi dan ina son ganin ka ba". Yace "what's wrong with my face? I thought ita kika gani kika ce kina so" ta sunkuyar da kanta kasa fuskarta tana nuna damuwa tace "na san nina ce ina son ka ba sai ka goranta min ba. Kawai naga ranka a bace ne. Ni face ɗin da nayi falling in love with is always happy always smiling" yace "you better get use to the unsmiling face. Because you are going to see a lot of it" suka yi shiru gabaki daya, sai da aka jima sannan da dago kai tace masa "dama nazo gari ne zanyi kunshi da saloon, and da akayi min kunshin sai na ga yayi kyau sosai, and I thought ya kamata kai zaka fara gani. I never thought hakan zai zama laifi". Yace "are you telling me kin taho tun daga Katsina zuwa Abuja kawai dan kiyi kunshi? Duk masu kunshin da suke Katsina ba zasu yi miki ba?" Ta dago kai tana kallon sa tace "actually, na fadi haka ne kawai a gida dan su barni in taho, Mommy like classy things and ta san a Abuja zan fi samun taste ɗin ta, but in reality I just wanted to get away from her" yayi mamakin jin haka yace "why?" Tace "faɗa. Tun da taje Katsina take yi min faɗa. She is not happy with this marriage saboda bata san ka ba, she kept complaining cewa bata san sanda muka haɗu ba ballantana sanda muka saba har zamu yi aure. Farko bata kasar, da tazo cewa tayi sai an daga. Da kyar ta yarda za'a yi ɗin" tayi shiru tana jujjuya hannunta sannan tace "she said you don't love me. Tace ko waya bata ga muna yi ba. There is no love vibes at all". Ya juya fusakarsa yana kallon window, sai kuma ya juyo yace "you know our agreement. And you agree with my conditions" tace "yes, I know. And ba complain nake maka ba. I just need a little bit of gesture from you. At least make it easy for me". Yace "let me ask you a question. Why do you agree to this? Me yasa kika saka kanki a wannan situation ɗin?" Tayi shiru tana tunani sannan tace "I love you. That is all that I know. Kuma na san I am an easy going person, bani da matsala. You may not love me know saboda yarinyar da kake so, but eventually you will fall in love again. And the easiest way to make you fall in love with me is to marry you. Yanzu misali ita yarinyar da kake so ɗin, I don't want to know her name, idan da zaka samu chance din auren ta even though bata son ka, won't you take the chance?" Yayi shiru yana tunani, sai kuma yayi sauri ya kawar da tunanin daga ransa yace "she loves me, so I can't relate to that" tace "she loves you and she left you?" Bai amsa ba sai ya dauke kansa gefe yana kara jin haushin ta, amma kuma yasan abinda ta fada gaskiya ne, shi kansa kuma a yanzu bashi da tabbas din in Safiyya tana son sa. Suka sake yin shiru a motar sannan yace "if that's all. Zan koma. I have things to do" tayi ajjiyar zuciya "Okay. Nagode da ka samu damar zuwa. Ina neman alfarma amma guda daya. Please ka bari in ringa kiran ka. At least saboda hankalin Mommy ya kwanta" ya bata rai "can't you call someone and pretend cewa da ni kike? I am a little bit busy for phone calls" ta dago ido tana kallon sa, kawai sai yaga hawaye yana bin fuskarta, ta saka hannunta da ya sha kunshin amare yayi kyau a farar fatar ta ta goge hawayen sannan tace "okay. Na fahimta. Thank you". Ta bude kofa zata fita sai kuma yaji babu daɗi a ransa yace "Safina wait" ta dakata amma bata juyo ba sai dai yana jin alamar kuka take yi yace "I am sorry. Okay. Zamu ke yin waya. Sai menene kuma kike so" ta juyo hawaye yana cigaba da zuba a fuskar ta tace "at least stop being mean to me. Ko baka nuna min soyayya ba ka daina wulakanta ni. It hurts a lot. You have no idea how much I have sacrificed for this relationship. The least you can do is to be nice to me". Bai sake magana ba ta fita daga motar ta rufe masa kofa. Sai da yaga ta shiga gida sannan ya tayar da motar ya tafi yana jin zuciyarsa duk tayi masa nauyi. Baya jin dadin yadda yake treating yarinyar amma baya iya hana zuciyarsa gaya mata abinda yake cikin ta. Kuma kamar yadda ta fada masa, ko da bai so ta ba the least he can do is to treat her nice. Treat her kamar yadda yake treating sauran mutane, or more. Albarkacin tarin soyayyar da take yi masa. Gidan Abba ya wuce, ya tarar ana ƙoƙarin shiga sallar magrib sai ya bisu suka yi sallar tare. Bayan sun fito daga masallacin ya samu ya shiga ciki ya gaishe da sisters din Mama da ya gani a parlor sannan ya wuce cikin bedroom dinta ya gaishe ta itama. Har ya tashi zai tafi sai ta tambaye shi ko akwai abinda yake bukata yace a'a, sai kuma ta sake tambayar sa "ya kuke ciki da Safina kuwa? Kuna waya ma kuwa?" Ya dawo ya durkusa yana shafa kansa yace "yanzu ma daga gurinta nake. Tazo gari taje gurin kunshi" Mama tayi murmushi, yaga alamar jin daɗin hakan a fuskarta sannan tace "to madalla, hakan yayi kyau sosai. Allah yayi maka albarka" yace "Ameen" a ransa yana jin dadin abinda tace din sosai. Tun a mota kafin ya bar gidan ya cire wayar sa daga do not disturb din da ya saka ta saboda Safina. Washegari da safe da ta kira shi sai kiran ya shiga ta sanar masa cewa zata koma shi kuma yayi mata fatan alkhairi. Da ta sauka a Katsina ma ta sake kiransa ta gaya masa cewa ta isa, yayi mata sannu, sannan reluctantly yace ta gaishe masa da Mommy. Daga nan suka fara magana, sama sama, yana replying messages dinta in ta kira kuma yana amsawa. A haka har ta turo masa hoton kunshin da aka neme shi musamman dan a nuna masa amma yaki gani, and he replied with "yayi kyau". Kamar yadda aka tsara ranar alhamis aka fara bikin, akayi kamun amarya a can katsina a gidan wan babanta.  Mommy ta gaiyaci mutanen ta sosai sun je anyi komai da su, yan uwan ango ma an ware representatives sunje anyi kamun a gaban su a inda kuma suka samu tarba ta musamman daga gurin Mommy dan sai da ta tabbatar ta fitar da yar tata daga kunya a idon su. A ranar kuma aka shirya za'a yi kamun ango shima a nan Abuja. Sai dai kuma, tun a safiyar ranar ne da samari yanuwan ango suka tashi a gidan da suke zaune tare da shi sai suka neme shi suka rasa, sai maigadin gidan ne ya gaya musu cewa tun assubar fari ya fice daga gidan a motarsa. Aka yi ta kiran wayar sa kuma bata shiga. Wasa wasa har rana ta yi sosai babu ango babu labarinsa. Tun suna boyewa suna cigaba da bincike su kadai har suka sanarwa da iyaye halin da ake ciki. Ango ya gudu. Ana ta kiran wayarsa kuma tana ta ringing amma baya dauka. Farko duk wanda aka gaya wa cewa ango ya gudu sai yayi dariya thinking cewa wasa akeyi, sai daga baya kuma sai a fahimci cewa babu wasa a cikin lamarin. Neman duniyar nan akayi wa angon aka rasa shi har lokacin kamun yayi. A gidan kakannin su aka tsara cewa za'a yi kamun. Amma rashin ganin angon ya saka aka tattaro aka dawo nan gidan su angon ana ta lissafin yadda za'a yi, auntyn sa Maimoon sai dariya take yi dan ita dai ta san Muhammad Gidado ba zai bata ba kamar wani key din mota, yayin da Aunty Amina ta dage sai fada take yi akan ya basu kunya sun tara mutane ya gudu ya bar su, da ya san ba zai tsaya kamun ba ai da sai ya fada musu da wuri su san abin yi. Hafsat kuwa sai kallon su kawai take yi dan dama ita bata ga amfanin kamun nan ba, daga baya dai da taga magana taki ci taki cinyewa sai ta kira Al'ameen ta zare masa ido tace sai ya fadi inda Gidado ya shiga, yayi ta rantse rantsen cewa shima wallahi bai sani ba, sai da ta fahimci da gaske yake sannan ta rabu da shi. Ana cikin haka Abba ya shigo, ya zauna yana binsu da kallo yana murmushi. Amina ta kalle shi tace tabbas yasan inda Gidado yake tunda bai nuna ya damu ba. Yace "to ni akan me zan damu? Tsakanin ku ne da shi ni babu ruwa na. In kuka kama shi duk abinda kuka ga dama kuyi masa" sai kuma ya saka hannu a aljihu ya dauko wayarsa ya kira number ɗin Gidado, shi ya san indai da ran Gidado da kuma lafiyar sa babu yadda za'a yi ya kira shi yaƙi dauka. Yana kiran nasa kuwa ya dauka ɗin, direct yace masa "kana ina?" Gidado yayi shiru kamar ba zai amsa ba sannan yace "ina daki na" yace "wanne dakin?" Yace "dakina na gidan mu". Abba yayi shiru yana jin yadda muryar Gidado tayi kasa sosai, and he can almost feel halin da zuciyar dan nasa take ciki. Yace "iyayenka suna neman ka zasu kama ka" Gidado yace "Abba ni da ba criminal ba me nayi da za'a kama ni?" Abba yace "tsakanin ku ne wannan. Ni dai yanzu ka ban amsa ta. Za'a yi ko ba za'a yi ba mu?" Daga Gidado har abban nasa sun fahimci cewa ba wai maganar kamu suke yi ba yanzu. Gidado ya sake yin shiru. Abba yace "yau kadai ta rage maka" still bai ce komai ba, Abba yace "ina jin ka" Gidado yace a hankali "za'a yi. Na amince ayi". Daga nan Abba ya katse wayar ya juya yana kallon yan'uwan nasa da suka saka shi a gaba suka tsare shi da ido. Ya kalli Amina yace "na ga kin damu dai da cewa sai kin jika yaron nan da nono, me zaki bani idan na gaya miki inda yake?" Tayi shiru tana tunani sai kuma tace "in dai ka gaya min inda yake daga yau zan dinga gaishe da matarka ina ce mata yaya" duk suka kwashe da dariya. Shekara da shekaru dama suna wannan rigimar tsakanin Amina da Zainab. Zainab kamar kanwa take a gurin Amina amma kuma mijinta kamar Yayan Amina ne (if you know you know 🤣) dan haka kowa a cikin su ya dage lallai sai dayan ya bashi girma. Abba ya mike tsaye yace "yana dakin sa" sannan ya fice ya bar musu gidan. Ai kuwa Amina ta sunkuci turaren da ta taho dashi tayi dakin Gidadon sauran yan'uwa suna binta, taje kuwa tayi ta gudun kofar duniyar nan yaki budewa sai da Mammy tayi masa magana tare da yi masa alkawarin ba za'a zuba masa nono akai ba sannan yayi magana. A bangaren Gidado ranar tun da assuba daya tashi ya yanke shawarar amsar da zai bawa Abba. Saboda shine abinda yaji hankalin sa yafi kwanciya dashi, bawai dan yaji a ransa yana son Safina ba, but yaji a ransa cewa auren shine abinda ya dace dashi, shine abinda hankalin sa ya kwanta dashi a wannan lokacin. The decision made him sad but free at the same time. Sad that he will have to made the final acceptance of the fact that Safiyya ta bar shi har abada, that his life has changed forever. Wannan yasa ya lallabo ya shigo gidan su ya shige dakin sa ba tare da kowa ya ganshi ba, making sure cewa ya boye motarsa a inda ita ma ba za'a ganta ba. Farko kwanciya yayi yayi baccin sa sai azahar ya tashi yayi sallah sannan ya kama yin aikin da yazo dakin da niyyar yi, aikin tattare duk wasu kaya nasa da duk wani abu nasa da yake da dangantaka da Safiyya, including his phone and his laptop da suke cike da hotuna da pictures dinta, ya hada su ya zuba a wata locker ya rufe. A binciken nasa ne ya dauko wata rose flower single stem da Safiyya ta taba bashi. Ya tuno lokacin da ta bashi din da kuma dalilin da ya sa yake ta ajjiye da ita. Suna tafiya ne ranar nan a hanya kamar kullum yana yi mata korafin har yanzu bata kai shi gidan su ba, kar yaje ayi mata miji a gidan su a raba shi da ita tunda ba'a san shi ba, she kept telling him cewa ba za'a iya raba su ba amma a karshe yace dai shi bama shi da tabbas din tana son sa da gaske ba wasa take yi masa da hankalin sa ba, suna maganar ne tayi ta tsinkar flowers a jikin bishiyoyi tana hadawa, sai da ta tara da yawa sannan ta cire ribbon din data daure gashinta da shi ta daure flowers ɗin da shi ta bashi, tace symbol ne na son da Safiyya take wa Muhammad. Yaji dadi sosai kuma ya karba, but He jokingly said "wannan ai gaibu ne, ana jima wa zasu yi wilting su bushe su mutu. I need something that is a forever thing. Wanda zai nuna min matsayina is a forever one a gurin ki. Something like zuwa gaishe da Daddy". A week after that, a jewelry company delivered that rose to him. Single stem ne na kyakkyawar red rose flower. An nannadeta da transparent plastic sheet. A jikin sheet din anyi rubutu da golden color in her own handwriting. Muhammad, This feeling is a forever thing. Your's Piya Amma abinda ya saka shi mamaki a lokacin shine kasancewar jewelry company ne suka yi delivering sakon. Sai da ga baya ya fahimci dalili. A kasan rose din, dan box ɗin da aka zura stem ɗin rose din a ciki, was made of gold, pure gold molded into the shape of a heart with their initials scribbled on it "MS". It was too much of a gift da yaji a ransa cewa bai kamata yayi accepting ba, that gold is a fortune. Ya tabbatar a gida ba'a san tayi wannan kyautar ba. Amma kuma he so much love it da ya kasa mayar mata. Wannan ya sa ya boye ta a inda yasan babu wanda zai ganta da niyyar in sunyi aure sai ya bata abinta. But now it is never going to happen. Sai ya samu kansa da jujjuya rose din a hannun sa yana wondering me zaiyi da iya yanzu. A karshe sai ya koma kan gado ya kwanta rigingine ya dora rose din akan kirjinsa ya rufe idonsa. Yana jin wayarsa tana ta kara, kuma a ransa ya san cewa nemansa ake yi amma haka yayi ta kwanciyar sa, sai dai damuwar sa bata saka a ransa yaji cewa ya fasa yin auren ba. A haka akayi la'asar ya tashi yayi sallah ya koma ya kwanta, deciding cewa ba zai je gurin kamun sa ba. Duk wadanda suke kiransa yana gani, kuma ya yanke shawarar ba zai dauka ba. A haka har wanda ba zai iya kin daukan wayar ta sa ba ya kira shi. Ya dauka, ta tambaye shi game da decision dinsa kuma ya gaya masa amsar. Bai jima da ajiye wayar ba yaji bugun kofa da kuma muryar Aunty Amina tana mishi magana da filatanci "na san kana ciki, ka bude kofar nan" ya tashi zaune yana dafe kansa. Suka cigaba da hayaniya da kuma bugun kofar. Bai ce musu komai ba sai ya tashi ya kammala adana dukkan kayan da yake bukatar adana wa including the forever rose sannan ya tsaya a bakin kofar, a lokacin yaji muryar Mammy tana masa magana. Yayi murmushi ya amsa mata da fulatanci. "Amma banda nono za'a zuba min" tace "eh banda nono" yace "kinyi alkawari?" Tayi dariya tace "nayi alkawari" sannan ya bude kofar, yana budewa suka feshe shi da turaruka kala kala sannan aka dauki guda. Duk da cewa turarukan sunyi masa karfi aka, amma sai ya samu kansa da yin murmushi yana jin daɗin ganin iyayen nasa cikin farin ciki. Zuwa dare sai gashi yana hira a cikin su harda dariya, ranar gabaki daya familyn anan suka ci abincin dare sannan suka raba dare suna hira, sai da bacci ya fara cin ƙarfin sa sannan ya zame jikinsa ya koma dakinsa ya kwanta acan. Da safe ya tashi da wuri kamar yadda aka tsara ya shiga wanda, saboda da wuri zasu tafi gurin daurin auren, yana fitowa daga wanka da bathrobe a jikin sa sai ya ga Mama a zaune akan gadon sa da kayan sawa na maza a hannunta tana fesa turare a jiki. Ya rissina ya gaishe ta yana jinsa wani iri saboda babu kaya a jikinsa amma sai yaga ita ko a jikinta. Ta mika masa kayan hannun ta, fuskarta dauke da alamar damuwa, tace "ga kayan da zaka saka nan. Dan banga ka tanadi kayan sakawar yau ba" ya karba tare da yi mata godiya, bata amsa ba sai tace "kayi sauri ka shirya, baban ku har ya shirya" ya ce "to" amma sai ua cigaba da tsaiwa da kayan a hannun sa tunda dai ai ba zai saka kaya a gabanta ba. Ta mike a hankali kamar bata son fita. Har takai bakin kofa sai kuma ta juyo tana kallon sa tace "Muhammad?" Ya amsa, sai tace "are you happy?" Yayi shiru yana kallon damuwar da take rubuce a fuskar ta sai ya girgiza kansa yace "no. I am not happy Mama. But I am contented, alhamdulillah" tace "good. That's a good start. Allah yayi maka albarka". Sai da ta fita sannan a hankali yace "Ameen Mama" Ya shirya ya saka kayan da Mama ta bashi. Farin yadi ne tas da akayi wa aiki mai kyau kalar ruwan toka mai haske, wanda ya dace da hula da takalmin da ta ajiye masa. Ya tsaya a gaban madubi yana kallon yadda yayi kyau, shi kansa ya san yayi kyau ba kadan ba. Ya tuna maganar Safiyya "You will look so good in white" Sai yayi murmushi. "Good bye Piya". Daga nan ya juya ya fita tare da rufe kofar dakin, knowing he will come back a changed man, a married man. Maybe even a happy man. Abinda bai sani ba shine a yanzun ne zai bude babi mai cike da rikici da sarkakiya a rayuwar sa. Yanzun ne matsalolin zasu fara. *Her 🧕🏻* Ranakun gudu suke yi, musamman idan ina lissafa su a matsayin kwanakin da suka rage a daura min aure da Mukhtar, amma kuma lakaki suke yi idan na kalle su a matsayin ranakun da suka rage ayi min aiki a raba ni da abinda yake ciki na. Duk shirye shiryen aikin sun kammala a asibitin da za'a yi, sun dauki dukkan vitals ɗina sun tanadi dukkan abinda suke ganin zan bukata. Sun kuma tanadi dukkan abinda babyn da za'a ciro zai bukata tunda zai zamanto premature ne kuma zai bukaci kulawa ta musamman. Yayinda ni kuma na kammala dukkan shiryen shiryen bayar da babyn kamar yadda na riga nayi niyya. Sharuda na sune bana son ganin shi, bana son Daddy ya ganshi, bana son kuma in an samu parents din da suke son sa a basu wani information da ya shafe ni ballantana har nan gaba yayi amfani da information din gurin sanin ko ni wacece. A gida kuma kullum muna cikin rigima da Daddy, muyi rigima yayi fushi ya sauko da kansa ko kuma ni inyi fushi ana jima wa kuma in sauko inje in bashi hakuri. Duk da ya amince da maganar Mukhtar amma yaki hakura da kokarin chanja min ra'ayi na. Sannu kuma har yanzu bai yarda da magana ta ta cewa ba zan koma Nigeria ba. He kept saying akwai plans din da ya shirya min in na koma Nigeria. But he wouldn't say what. Mutanen kadai da nake samun fahimtar juna da su sune twins. Kullum sai munyi hirar mu a waya. Suna kuma updating dina akan duk abinda yake faruwa a gidan. Su suka bani labarin rikicin da ake tayi tsakanin Mommy da Safina, a fahimtar su ita Mommy hankalin ta bai kwanta da wanda Safina zata aura ba. A kalaman ta kamar yadda suka fada min "shegen girman kai ne da shi da isa kamar wani dan sarkin Makkah" Sun so Daddy ya bar su su taho su zauna tare da mu amma yaƙi, ni na fahimci baya son Mommy ta sake jin haushi tace ya kwace mata su, shi lallai so yake a daidaita. Kusan kullum kuma in muna waya sai sunyi min maganar Hajiya, tana ta damun su da tambaya akai na, ta damu da ni, musamman da taji cewa za'a daura min aure. "Kin san bata san halin da kike ciki ba. Mommy bata gaya mata ba. Tace Hajiya bakinta bashi da linzami" "Bata gaya mata ma maganar rikicin da suka yi da Daddy ba, tasan idan da ta gaya mata da zata iya yiwa yaya Safina kayan daki amma kuma da kowa a gidan bikin sai yaji labari" Nayi murmushi, na yarda da maganar Mommy a nan, Hajiya tana da kirki sosai, amma indai magana ta shiga ta kunnen ta to sai ta fita ta bakin ta. Kuma ba wai da niyyar munafunci ba. Haka Allah yayi ta bata san wani abu wai shi sirri ba. Da ake zata san da zancen cikin nan nawa, zata tausaya min sosai ta bani dukkanin kulawa, bayan ta gamai min fada, amma kuma kowa da yake gidan da wanda zai shigo gidan sai ya san maganar. Safina har da turo min pictures din gidanta sanda aka gama jerenta, sannan tayo min message din godiya. Ranar kamun ta ma haka ta turo min pictures din kyalliyar da tayi, telling me that taso ace ina nan. Sannan sai washegari, washegari ranar daurin aure. Ranar dama ban samu baccin kirki ba saboda lissafin rayuwa. Haka na gama daren akan sallaya ta. Gari yana wayewa nace saura kwana daya. Ina nan kan sallayar har lokacin cin abincin Daddy yayi naje na hada masa, yanzu baya iya cin abinci mai tauri sai mai ruwa ko kuma wanda aka dafa yayi laushi sosai. Naje na kai masa na tashe shi zaune ya dauka yana ci, baya son inke bashi abinci a baki yace cin abincin da kansa ma wani exercise ne. Yana ci yake tambayata ko na gama hada kaya na na zuwa asibiti nace masa na gama, dama da yamma zan tafi, a can zan kwana. Ya sake tambayar ko akwai abinda nake bukata nace masa a'a. Ni kuma na sake yi masa maganar cewa bana son ya bini asibiti gwara yayi zamansa a gida tunda Aunty Hajjo zata je amma ya nuna min ba zai zauna a gida ba. Sometimes na kan yi tunanin a gurin sa na gado taurin kaina duk kuwa da cewa shi kullum cewa yake yi a gurin Ammi ne. Sai da nurse din shi yazo ya haɗa masa ruwan wanka zai taimaka masa yayi sannan na fita na koma parlor na zauna. Gaba na sai faduwa yake yi. Nayi tunanin maganar aiki na ce take damuna amma kuma ban taba damuwa da ita ba why will I now. Ina nan zaune har wajen azahar nurse din ya fito yace zai je ya dawo, ni kuma na tashi na shiga kitchen zan nema mana abinda zamu ci da rana. A lokacin ne wani tunani ya fado min. Twins sunce 11am za'a daura auren Safina. Na kalli agogo naga 12:30 ma'ana 11:30 kenan a Nigeria. Sai nayi tunanin ko an daura? Na shiga kitchen ɗin na dora abincin sai na dawo daki nayi sallah kafin abincin ya kammala. Sai da na idar nayi adduoi na sannan na dauko waya ta zan duba ko twins sun turo min labari. Ina shiga kuwa naga message from Hussein. "Yaya an daura auren Yaya Safina. We are missing you here ke da Daddy" Naji babu daɗi a raina, nima ina missing ɗin su. Sai naga ya dora status, nayi sauri na bude dan nasan pictures din daurin auren ne. A lokacin ne na ganshi. Sai da na ajjiye wayar na saka hannayena biyu na murza idona dan in kawar da gizon da yake min, saboda kwanan nan ba a mafarki ba har a ido biyu gizo yake min in ganshi kamar ya shigo gidan ko kuma inji kamar muryarsa. Na sake daukan wayar na sake dubawa. Muhammad ne, Muhammad ɗina, yayi kyau fiye da yadda na taba tunanin zai yi. Yana tsaye Hussein yana tsaye shima a kusa da shi. Hussein yayi captioning hoton with "Nayi sabon wa" Menene wa? Shine tambayar da na fara yiwa kai na. Me Muhammad yake yi a gurin daurin auren Safina? Sai dai hoto na gaba shi yayi kokarin amsa min tambaya ta. Muhammad din ne dai again, this time sho da Hassan da Hussein. Hussein ya rubuta "With the groom. Allah ya sanya alkhairi" Naji cikina ya daure, ƙwaƙwalwa ta ta toshe. Na sake tambayar kaina "menene groom? Me kalmar groom take nufi?" Hoto na gaba ne ya hau da kansa ba tare da na tura shi ba. Muhammad ne a tsaye da Safina a kusa da shi. Ta ci kwalliya cikin farin lace ɗin da na siya mata. Fuskarta dauke da tsantsar farin ciki. A kasan hoton Hussein ya rubuta. "Amarya da ango" Na ajiye wayar tare da girgiza kaina kamar mai kokarin tashin kaina daga bacci, amma kuma ba baccin nake yi ba. Na dafa gadon da yake gaba na na mike ina jin kamar kaina yafi dukkan sauran jiki na girma saboda kamar dukkan jinin jikina ya tattare ya koma cikin kan, shi kansa bugun zuciya ta a cikin kai na nake jin sa. In dai har da gaske ba mafarki nake yi ba, ba kuma haukacewa nayi nake hallucinations ba, to tabbas auren Safina da Muhammad Gidado aka daura shi. Na dafa bango na fara kokarin fita waje sai, kuma na dawo dakin na dauki handbag dina da take ajjiye akan side drawer na rataya, na cigaba da laluben hanya har na fita parlor. "Daddy!" Na fada da karfin da bansan ina da shi ba. Na cigaba da tafiya ina ganin gaba na yana kara duhu duk kuwa da ba dare ne yayi ba. Sama sama naji muryar Daddy yana magana, "Safiyya! Lafiyar ki. Me ya faru? Ina zaki je" na juyo inda naji sautin muryarsa nace "gida zanje. Nigeria zan tafi. Daddy Muhammad ne fa. Wallahi Daddy shine. Daddy mutuwa zanyi. Daddy zuciya ta zata fashe. Daddy mutuwa zanyi" na cigaba da fadar sauran maganganun da ban san me nake cewa ba yayin da jiri ya debe ni nayi kasa. Dishi dashi naga motsin Daddy ya mike daga kan wheelchair dinsa yayo kaina, sai dai kafin ya karaso ya yanke jiki ya riga ni kaiwa kasa. Sai da kaina ya daki center table din gurin sannan ya karasa kasa. Na hango Daddy ya sake yunkurawa zuwa inda nake fuskarsa da cike da tashin hankali. "Not my daughter. God please take me instead" ya fada a hankali. Sannan kuma da karfi yace "who is there? help us please. Help!" A hankali na sake ce masa "Daddy Muhammad ne". Sannan na rufe ido na into nothingness.......... Longest episode ever 😃 Shin kina son wannan episode din ya zamar miki taliyar karshe ko kina son kari.......... Muhammad dai ya auri Safina, while madly in love with Safiyya, ba tare da yasan dangantakar dake tsakanin Safina da Safiyya ba. Ga Safiyya kuma ta dauki hanyar lahira bamu sani ba ko zata yi rai ko akasin haka. In bata tafi lahirar ba ma she is set to marry Mukhtar Yaya wannan badakalar zata kare .... Yaya wadannan aurarraki zasu kasance. Menene ainahin labarin Safiyya da mahaifiyar ta Menene dangantakar su da Mommy And above all, wanene uban cikin jikin Safiyya. Kina son wadannan amsoshin? Na tabbatar kina so. 😅 Turo naira 500 dinki zuwa wannan account din 0779484494 Nafisa Tafida Usman Access Bank Sai ki kuma turo evidence of payment dinki zuwa wannan number ɗin 0704 203 0419 Ta manhajar telegram Posting of paid episodes will be on telegram only. Nagode. Sai na jiku.